Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR SADIK book 3 Complete Hausa Novel Document by MATAR SADIK book 3


MATAR SADIK   book 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9661



MATAR SADIK book 3

Reading Time: 0 Hours

Added On: 22, Sep 2024

Author: Zainab Dodo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : TASKIRA WRITER'S FORUM

Author Phone : 09046495943

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 54.54 kb

File Type: txt

Views: 385+

Download: 176+

Last download: 3 days ago

Description/Story: 🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣0️⃣➡️3️⃣1️⃣


Lafewa tayi a jikin sa tana sauke ajiyar zuciya, hannun sa ya zuwa bayan ta yana shafawa, zuwa can kamar wacce ta tuna da wani abun ta zabura ta Mik'e daga jikin sa ta sauka saman gadon, ta bud'e wardrobe d'in ta ta d'auko zane ta d'aura,

Tun da ta sauka yake kallan ta, ganin ta kama hanyar fita ne yasa sa saurin cewa " Ina zakije? " Wanka zanyi " ta basa amsa a tak'aice " jira ni nazo muyi tare" Ya fad'a yana k'ok'arin sauko wa

Ko kafin ya sauko harta fice da sauri da d'auki boket ta d'ibi ruwa tayi toilet tana shiga tasa sakata tarufe, koda ya fito d'aure da guntun towel a k'ugunsa ya nufi toilet d'in, yana zuwa ya tura yajisa a gark'ame k'wank'wasa wa yayi a hankali tana jinsa tamasa banza, shi kansa yasan tana jin sa ganin tak'i bud'ewa yasa ya koma d'aki ya jira ta harta fito shi ya shiga



Falo ta tarar dashi zaune bata ko kalli wajen da yakeba ta wuce ciki, Mik'e wa yayi ya fita dan tsarkake jikin sa

Tana shiga ta d'auki guntun towel ta zane ruwan kanta tayi kwanciyarta hannun ta dafe da mararta tanajin ta k'ulle mata ga ciwon da take mata sama_sama, bacci yayi awon gaba da ita,

Koda sadik ya shigo bata ko sani ba ta dai ji yana tadata ta tashi an fara sallah, sannan ya wuce masallaci, ta Mik'e taje tayi alwala tayi sallah takoma gado dan wani irin bacci takeji sosai


Cikin bacci taji ana shafata, bud'e idanuwan ta tayi da suke jajirr cike da bacci ta zube su saman face d'in sadik, suna had'a ido ya sakar mata murmushi, gimtse fuska tayi ta tashi zaune tare da fad'in "Lafiya dai ko? " Qlau ina buk'atar k'ari ne" ya fad'a tare da kashe mata ido d'aya, wani kallo ta watsa masa tare da fad'in " Dan Allah ko kunyar ma fad'ar wannan kallar bakayi ba " Kamarya? " Auu kamanta abun da ka fad'a kenan nida ba haihuwa zanyi ba miye amfanin mu'amalartarta gwaunda kaje inda kasan idan ka zura gugarka zaka janyo ruwan da zasu anfaneka har ka samu k'aruwa ba wajen da bazaka samu komai ba" khadija wai ke magana bazata wuce a wajen ki ba ne " Wace maganar zata wuce a wajena ? " Ta fad'a tare da k'ara kallan sa idanuwan ta cike da hawaye


" Kai a tunanin ka wannan maganar zata wuce a wajena abun da ban ta'ba tsammani zakamin ba sadik da ace wani ne yazo ya fad'a min zaka iya bud'e baki ka fad'i wannan furucin akaina wallahi zan iya rantsuwa da al'Qur'ani nace k'arya ne amman sai gashi ido da ido ka bud'e baki ka fad'a min wai har kace ina maka hassada da bak'in ciki" Ta k'arshe maganar tare da fashewa da kuka, jikin sa yayi sanyi sosai yasa hannu zai ta'ba ta, tayi saurin d'agowa tare da girgiza masa kai kana tace " Wallahi karka kuskura ka ta'ba ni wallahi bana ma san ganin ka kusa dani 😩 katashi ka tafi" Subhanallah khadija kin san kuwa me kike fad'a? " Ni ko nasan me nake fad'a idan baza ka tashi ba ni bara na tashi na baka waje" ta fad'a tana k'ok'arin tashi, ya dakatar da ita ta hanyar cewa " Kiyi zaman ki ni bara na tashi " Ya sauka saman gadon ya nufi falo yayi zaune saman doguwar kujerar falon ya dafe kansa maganganun ta na masa yawo a k'wauk'waulwa




Yana fita taja tsaki tare da gyara kwanciyarta taci gaba da bacci




Washe gari haka suka wuni ba mai cema d'an uwansa uffan gwauda ma sadik yana mata magana ita ke kyalesa abun na damun sa, da dare haka suka kwana tana ciki yana falo


Yau ta kama girkin samira khadija sanin samira ba girkin zata musu ba yasa tasa ayo mata awara d'anya ta kwano d'aya aka kawo mata, tabayar aka siyo mata rabin kiret d'in kwai da kayan ciki, raba awarar tayi biyu tasaka rabi cikin fridge rabi kuma ta yamutse ta fasa kwai guda bakwai ta zuba akai tasa magi da kayan k'amshi da tarugu da albasa ta d'auki kayan cikin da aka siyo mata ta tafasa ta zuba akai ta motse su sosai suka shiga cikin awarar, ta zuba mai kad'an aciki yarda idan ta saka a leda bazata kama ledar ba, ta d'auko ledar ta fara ta k'ulli ta rik'a d'aura awarar a ciki sai da ta d'aure duka, ta bud'e tukunyar ruwan zafin ta dake kan wuta ta juye awarar a ciki ta koma ta samu roba ta k'ara fasa kwai biyar tazuba tarugu da albasa da magi da kayan k'amshi wad'an da zasu kashe garnin kwain ta kad'a, sannan ta ajiye


Zuwa 20 mints ta sauke tukunyar, ta kwaushe awarar, ta had'e sosai kamar alale kwai ya shige jikin ta tayi kyau sosai, kunce ledar ta riga yi bayan ta gama ta fara yayyanka awarar tana manyan yanka, bayan ta gama ta d'auko tallen suyar ta ta d'aura akan wuta ta zuba mai a ciki sai da yayi zafi ta d'auko awarar tana zubawa cikin ruwan kwai tana soyawa, nan da nan gidan ya d'au k'amshin dad'i samira na d'aki k'amshi ya kaima ta ko yaya ta fito tayi zaune tana had'iyar yawu tana lek'en talle, khadija da ta gama sauran kwain da ya rage tayi masar kwai da ita, ta d'auko kula ta zubama mama ta kai mata samira na zaune tana jiran ita ma a zubo mata nata, taga khadija ta tattara kayan ta takai d'aki, kayan da tayi amfani dasu ta had'a ta wanke ta share wajen ta gyara komai, ta d'ibi ruwa tayi toilet dan yin wanka da niyar idan ta fito sai taci




Tana shiga samira na nan fake da ita sai da taji saukar ruwa alamun ta fara wanka Sannan tayi d'akin khadija, duddubawa tayi can ta hango kular ta saki murmushi tare da nufar wajen ta bud'e kular ta fara ci


Khadija na fitowa daga wanka sadik na shigowa, " sannun da zuwa" ta fad'a tare da wuce, bayan ta ya biyo kusan a tare suka shiga d'akin tsaye suka ja ganin iKon Allah samira durk'ushe gaban kulla aka shiga kallan_kallan " Jar uban can" .....................................................


🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK


Ina ma kowa barka da sallah ubangiji Allah ya nuna muna wata shekarar lafiya, Eid Mubarak 🩷 kar a manta da mar'atussaliha 🧕☺️ sannan aci nama ahankali kar a b'arke🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Ahhh to

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣2️⃣➡️3️⃣3️⃣

"Jar uban can" Khadija ta fad'a tare da k'arasa shigowa d'akin ta rik'e k'ugu, samira tayi zumbur ta Mik'e tsaye tana lasar faratan ta " Wallahi tallahi yau ko sama da k'asa zasu had'e sai kin biyani kayana iyyeee lallai ma matar nan ko tsoron allah bakyaji nagama wahalar girki na kizo ki shige d'aki kiyi zaune ki bud'e kula kiyita ci kega mai abu ko wato haryanzu baki sanni ba but kar ki damu zan nuna miki truer color ta wallahi sai kin biya ni kuma nawa nake so nawa wanda na had'a da kaina bana buk'atar na wani"

Sadik ya d'an matso tare da fad'in"Khadijjj" wani irin kallo ta watsa masa wanda yasa sauran maganar tak'ewa kana tace " Kar ka kuskura ka tsoma min bakin ka cikin magana wannan maganar bata shafeka ba kayi gum da bakin ka idan kuma bazaka iya ba ka fita dan allah" haba kema kinsan hakan bazai yuwuba"To shikenan wallahi duk abinda nama kai ka jama kan ka "Wai Khadija miyasa gabaki d'aya bakya jin magana ta ne nace bana son fitina da tashin hankali a gidan nan ki fad'i nawa kika kashe a biya ki"



Cikin jin mamaki da takaici da Khadija ta zuba masa ido tana kallan sa har ya kai k'arshe" iKon Allah ohhhh wato nice ma na tada fitina lallai ma mutumen nan ita da
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR SADIK book 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album