Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

BLEEDING HEARTS Complete Hausa Novel Document by BLEEDING HEARTS


BLEEDING HEARTS

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 286865



BLEEDING HEARTS

Reading Time: 23 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Bintou ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.54 mb

File Type: txt

Views: 346+

Download: 977+

Last download: 10 minutes ago

Description/Story:             *_Wu'ka a zuciya❤🔪*_
             (_Bleeding heart💔_)

~Love❤️,Touching Story💔~

_Story and written_
                _by Bintou_

__Marubuciyar__
*_hawan jinina_*
*_Maqaryaci (fake life)_* 

                           *001*

''_Bismillahir Ramanirrahim
Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai_
_Ya Allah ka ban ikon kammala wannan littafin  Nan sannan kasa in isar Da sakon Da nake San isarwa Ameen,_'''

*_Wannan littafin badan cin zarafiN wani ko wata zanyiba*_

*80% True Life Story Ne*

               _*The Beginning *_

               *Kaduna-Kabalan doki* 

3:35Am

Dare Ne Sosai,ko ina yayi tsit, Baka jin sautin komai Sai Na tsuntaye, The sky was aglow with bright city lights, wata da Taurari Sai Walqiya Suke Kaman azurfa a sararin samaniya Jefi  Jefi haushin  karnuka  Na cigaba da Ratsa  Ni'imtaccen Shurun Daren  Hasken street light ne Mamaye da ko Ina na fadin Anguwar, a daidai  lokacin da kowanne halitta ke ganiyar hutawansa,  yayin da wasun mu suka duqufa kan darduma SuNa kai kukansu ga Mahalicci .

Kofofi  Uku Ne Ajere Milk Color , dan madaidaicin gini ne Mai dauke da matsakaitan dakuna guda uku ma tsakaita.  .  *da kaga ginin zaka gane gidan tazurai ne*


Tsugunne take tana jan numfashi Idanunta yayi jaa sosai da ƙyar take buɗewa, zamanta ke nan taji aman, kakarin aman ta fara amma yaƙi fita sai wahala take sha, gashi babu kowa a Wajan da ƙyar ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin tafiya Jiri najan ta, ta Koma bakin Ƙofan ɗakin shi ta duƙunƙune ta cure Guri guda, Batareda ta damu da tafiyan Daren ba, Burin ta kawai Tayi ido huɗu dashi ta bashi haƙuri yace ya yafe Mata bakuma taso ya kwana da ɓacin rai, Hakan kadai shi zai sa ta iya rintsawa a yau dinnan.

Jikinta yayi Nauyi,bata Iya ɗaga koda dan yatsanta ne, Numfashi take saki sama Sama ga wani irin Yunwa dake gallabar yan hanjinta, tana nan Zaune banda Kakkarwa babu Abinda takeyi.

kofar farko da ta ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya saninta babu kowa a dakin farkon .

Motsin da yaji ne yasa ya kai dubansa kanta yana haskata da Yar touch light dinshi.

"Subhanallah Aeesh me kike yi anan Cikin daren Nan to 4aM fa."

Shima a tsorace ya faɗi hakan don Zuciyarshi bata tabbatar masa da ita dince ba.

Cije Lips dinta Tayi cikin azaba, Hawaye suka gangaro mata, ta miƙe da ƙyar kanta na sara mata ta nufoshi.


"Uncle Kamal please Tell him ya fito Muyi magana bazan iya Komawa Gida yayinda yake fushi dani ba "

Ta qarashe cikin breaking Voice haƙoran ta na hardewa.

Sosai Aeesh xata baka tausayi Sbd gaba ɗaya Yanayin ta ya koma Gwanin ban tausayi.

sakin baki Kamal yayi cikin Mamakin Da ya gaza ɓoyuwa a Allon fuskarsa, Taya zai yarda ita dince Ma?, Kodai Aljannu Ne suke Neman Suyi masa Siddabaru ba?.

Da touch din Hannunsa Ya haska ƙafafun ta yayi don ya tabbatar da ita din ce, tabbas itace, ya haska fuskar ta, tasa hannu tana share hawayen dake bin fuskarta...

Girgiza kai kamal yayi yace

"Karkice Min tun bayan isha''i Dana jiki dashi baki koma gida ba"

Numfashi Aeesh taja ta kasa ce wa komai sai hawaye da sukafi 'karfin ta.

Kamal jiyayi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, wannan wace irin Masiface? Akan soyayyar 'da Namiji Mace ta kasance a waje har wannan lkcn? ,In Ka bibiya ma Abinda ya hadasu bai taka kara ya karya ba.


Tabbas Aareef yana bata wahala sosai akan soyayyar Shi, Don yaga tana Sonshi sosai, ta nuna masa Soyayyar *kaine rayuwata* shi ko a labari bai taba ganin Irin soyayyar da Aeesh take nuna ma Aareef ba bata iya sarrafa kanta akan shi ba at least even For once ta nuna masa ita mace ce ko zaiga girman ta.

Aareef bai cancanci Soyayyar gaskiya irin haka ba, kodan Fasiƙancin da yake aikatawa da yaran Mutane.

Aeesh duk tagama canja kamanni, tarame sosai, Ga uban haske datayi sai kace Ba Aeesh ba, a halin yanzu ko mak'iyinta ya ganta dole ya tausaya mata

Kamal hawaye na Cika masa idanu yace

"A haka Arrow ya shige ciki Ya bar ki a waje?, Kuma yasan kina nan? "

Kai tsaye tace

"Yasani "


Duban Unguwar yayi, yana ayyana ƙarfin Zuciya irin nata, What if something Wrong happened to her?, Bata Tsoron a saceta?, Bata Tsoron wani Wani abu ya cutar da ita??, Bata Tsoron sharrin ɓata garin Maza su mata fyaɗe ?, A irin daren Nan da babu kowa a cikinta babu Abinda bazai iya faruwa ba, amma da alama duk bata tunanin Waennan Ƙwaƙwalwar ta ta riga ta cushe da soyayya.

Lumshe idanunsa yayi, ya dubeta itama shi take kallo

"Ya kamata ki koma gida, zamanki anan nada Had........"


"You're not helping Please You can Go"

Ta dakatar dashi hawaye na fita a Idanunta.

Dubanta yayi da mamaki ,ta kauda kai hawaye na zubo mata tace

"Idan bazaka iya Hada ganina da nashi ba, You can Go please"

Cikeda Jin tausayinta Ya shiga bubbuga ƙofar Batareda yayi la'akari da Amsa kowwar Yake yi cikin daren ba,yanda kasan matattu ne a ɗakin.

Duk bubbugar kofar din da'ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he's so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lakka ga barcin dake jan shi.


Saida Kamal ya haɗa da Roko da magiya da dabara Sannan A fusace ya miqe yana jan tsaki tareda duba agogo qarfe 3:52am

Ransa a ɓace ya buɗe ƙofar, Kamal Najin Alamar ya fara bu'de 'kofar yayi azamar Shigewa Dakinsa da 'yar Butarsa don baya Son abinsa zai Kai ya kawo, a ɗakinshi yayi Alwalar yatada sallah.

Aareef na hada ido da ita yaji Gabansa ya fa'di, Shi fa har ya mance da ita fa.

Girar sama da ta qasa ya hade ya Kauda fuska rai 6ac3 yace

"Bakida hankali ne?, Me kikeyi anan cikin Wannan daren?"


"Sadauki Please............. "

"Wait Tambayan ki nake Me ya kawoki nan Cikin Daren Nan?, wae ke wace irin Mayya ce? "

Hawaye na Zubowa tace

"Beer har yanzu Baka haquraba? "

Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa

"Tambayanki Mey kikeyi a Nan at this time of night?, Wai ke wace irin Mahaukaciya ce?, a haka kike so Na Aureki?, in Na Aureki ince Na Aura me kenan? rashin Aji?, ko Rashin Kamun kai ko Kuma Yawon dare? "

Dago jajayen idanunta tayi Duk ilahirin jikinta rawa yake zuciyarta Na bada wani irin sauti Na bugawa kanta na sarawa. Ga hawayen dasukaqi Tsayawa dubanshi tayi da Watery eyes ɗinta.

"Albeer Ni kk kira Mahaukaciya…?, Ni kake Alaqantawa da irin munanan maganganu irin wannan, Ni zaka tozarta Aarrow?, I have been waiting for u Since 8:30 just to hear the word of forgiveness from u, a ganina I don't deserve All these From you All I need is forgiveness, pease... please Don Allah... Please forgive me on Reeyyer's Behalf 🙏... "

Ta Dan dakata don saisaita Numfashin ta dake siezing, fuskar ta cikeda ƙwalla tace

"I payed for happiness please Don't break our promise "


KO kadan bai ji digon tausayinta ya dirsu a ransa ba illa ma 'kara haushin ta da taji, kenan tazo wajenshi ne da yaƙinin Zai yafe mata saboda Kuɗaɗen da take bashi, kenan Gori zatayi Masa?.

Yayi mata Kyakkyawar kallo a wulaƙance

"Awww Gori zaki Min ?,akan kin bani wasu 'yan chanji for us to be happy❓, Amma Ina so ki tuna wani abu!, Ban taɓa roƙon Wani abu a Wajen ki ba don haka Bakida ikon da Zaki min karar tsaye akan wasu kudade ,and let me Tell you Something Yes na ci kudin kine don Buƙatarr ki, and Right now Subscription Din ki ya qare baki da hurumin In yafe miki, bayan Cin mutuncin Da kika Turo ayi min"

"Wlhy bani na Turo ta ba..."

"Shut up bake Kika turota ba,Amma bake na Kira a waya ba kika bata wayan donta ci Min Mutunci?"


"Sadauki but i paid I don't deserve this"

"Wait You're still talking about the money you gave me?, Ina so ki san wani abu bakikai standard din zaki Siya haappiness Dina ba koda daidai da second dayane, taimaka miki nake yi Ina amsar Kudinki, amma Bakida wannan quality din, and also kudinki basu isa susani yafe Miki ba saboda I don't fucking care about your goddamn money! Ke suka Dama ni ko ajikina, lastly kisan wanda zaki dinga bibiya dadaddare domin yayinda kike bin wasu kamar karya kina ikirarin kin zo bada haquri wasu a lokacin Suke sanin kin wanzu a duniyarnan , koda Wasa karki Sake Nuna kin Sanni Ni Aareef nace na fasa Soyayyar in kinso ki kaini kotun duniya,...


Read / Download BLEEDING HEARTS

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album