Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

            *_Wu'ka a zuciya❤🔪*_
             (_Bleeding heart💔_)

~Love❤️,Touching Story💔~

_Story and written_
                _by Bintou_

__Marubuciyar__
*_hawan jinina_*
*_Maqaryaci (fake life)_* 

                           *001*

''_Bismillahir Ramanirrahim
Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai_
_Ya Allah ka ban ikon kammala wannan littafin  Nan sannan kasa in isar Da sakon Da nake San isarwa Ameen,_'''

*_Wannan littafin badan cin zarafiN wani ko wata zanyiba*_

*80% True Life Story Ne*

               _*The Beginning *_

               *Kaduna-Kabalan doki* 

3:35Am

Dare Ne Sosai,ko ina yayi tsit, Baka jin sautin komai Sai Na tsuntaye, The sky was aglow with bright city lights, wata da Taurari Sai Walqiya Suke Kaman azurfa a sararin samaniya Jefi  Jefi haushin  karnuka  Na cigaba da Ratsa  Ni'imtaccen Shurun Daren  Hasken street light ne Mamaye da ko Ina na fadin Anguwar, a daidai  lokacin da kowanne halitta ke ganiyar hutawansa,  yayin da wasun mu suka duqufa kan darduma SuNa kai kukansu ga Mahalicci .

Kofofi  Uku Ne Ajere Milk Color , dan madaidaicin gini ne Mai dauke da matsakaitan dakuna guda uku ma tsakaita.  .  *da kaga ginin zaka gane gidan tazurai ne*


Tsugunne take tana jan numfashi Idanunta yayi jaa sosai da ƙyar take buɗewa, zamanta ke nan taji aman, kakarin aman ta fara amma yaƙi fita sai wahala take sha, gashi babu kowa a Wajan da ƙyar ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin tafiya Jiri najan ta, ta Koma bakin Ƙofan ɗakin shi ta duƙunƙune ta cure Guri guda, Batareda ta damu da tafiyan Daren ba, Burin ta kawai Tayi ido huɗu dashi ta bashi haƙuri yace ya yafe Mata bakuma taso ya kwana da ɓacin rai, Hakan kadai shi zai sa ta iya rintsawa a yau dinnan.

Jikinta yayi Nauyi,bata Iya ɗaga koda dan yatsanta ne, Numfashi take saki sama Sama ga wani irin Yunwa dake gallabar yan hanjinta, tana nan Zaune banda Kakkarwa babu Abinda takeyi.

kofar farko da ta ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya saninta babu kowa a dakin farkon .

Motsin da yaji ne yasa ya kai dubansa kanta yana haskata da Yar touch light dinshi.

"Subhanallah Aeesh me kike yi anan Cikin daren Nan to 4aM fa."

Shima a tsorace ya faɗi hakan don Zuciyarshi bata tabbatar masa da ita dince ba.

Cije Lips dinta Tayi cikin azaba, Hawaye suka gangaro mata, ta miƙe da ƙyar kanta na sara mata ta nufoshi.


"Uncle Kamal please Tell him ya fito Muyi magana bazan iya Komawa Gida yayinda yake fushi dani ba "

Ta qarashe cikin breaking Voice haƙoran ta na hardewa.

Sosai Aeesh xata baka tausayi Sbd gaba ɗaya Yanayin ta ya koma Gwanin ban tausayi.

sakin baki Kamal yayi cikin Mamakin Da ya gaza ɓoyuwa a Allon fuskarsa, Taya zai yarda ita dince Ma?, Kodai Aljannu Ne suke Neman Suyi masa Siddabaru ba?.

Da touch din Hannunsa Ya haska ƙafafun ta yayi don ya tabbatar da ita din ce, tabbas itace, ya haska fuskar ta, tasa hannu tana share hawayen dake bin fuskarta...

Girgiza kai kamal yayi yace

"Karkice Min tun bayan isha''i Dana jiki dashi baki koma gida ba"

Numfashi Aeesh taja ta kasa ce wa komai sai hawaye da sukafi 'karfin ta.

Kamal jiyayi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, wannan wace irin Masiface? Akan soyayyar 'da Namiji Mace ta kasance a waje har wannan lkcn? ,In Ka bibiya ma Abinda ya hadasu bai taka kara ya karya ba.


Tabbas Aareef yana bata wahala sosai akan soyayyar Shi, Don yaga tana Sonshi sosai, ta nuna masa Soyayyar *kaine rayuwata* shi ko a labari bai taba ganin Irin soyayyar da Aeesh take nuna ma Aareef ba bata iya sarrafa kanta akan shi ba at least even For once ta nuna masa ita mace ce ko zaiga girman ta.

Aareef bai cancanci Soyayyar gaskiya irin haka ba, kodan Fasiƙancin da yake aikatawa da yaran Mutane.

Aeesh duk tagama canja kamanni, tarame sosai, Ga uban haske datayi sai kace Ba Aeesh ba, a halin yanzu ko mak'iyinta ya ganta dole ya tausaya mata

Kamal hawaye na Cika masa idanu yace

"A haka Arrow ya shige ciki Ya bar ki a waje?, Kuma yasan kina nan? "

Kai tsaye tace

"Yasani "


Duban Unguwar yayi, yana ayyana ƙarfin Zuciya irin nata, What if something Wrong happened to her?, Bata Tsoron a saceta?, Bata Tsoron wani Wani abu ya cutar da ita??, Bata Tsoron sharrin ɓata garin Maza su mata fyaɗe ?, A irin daren Nan da babu kowa a cikinta babu Abinda bazai iya faruwa ba, amma da alama duk bata tunanin Waennan Ƙwaƙwalwar ta ta riga ta cushe da soyayya.

Lumshe idanunsa yayi, ya dubeta itama shi take kallo

"Ya kamata ki koma gida, zamanki anan nada Had........"


"You're not helping Please You can Go"

Ta dakatar dashi hawaye na fita a Idanunta.

Dubanta yayi da mamaki ,ta kauda kai hawaye na zubo mata tace

"Idan bazaka iya Hada ganina da nashi ba, You can Go please"

Cikeda Jin tausayinta Ya shiga bubbuga ƙofar Batareda yayi la'akari da Amsa kowwar Yake yi cikin daren ba,yanda kasan matattu ne a ɗakin.

Duk bubbugar kofar din da'ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he's so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lakka ga barcin dake jan shi.


Saida Kamal ya haɗa da Roko da magiya da dabara Sannan A fusace ya miqe yana jan tsaki tareda duba agogo qarfe 3:52am

Ransa a ɓace ya buɗe ƙofar, Kamal Najin Alamar ya fara bu'de 'kofar yayi azamar Shigewa Dakinsa da 'yar Butarsa don baya Son abinsa zai Kai ya kawo, a ɗakinshi yayi Alwalar yatada sallah.

Aareef na hada ido da ita yaji Gabansa ya fa'di, Shi fa har ya mance da ita fa.

Girar sama da ta qasa ya hade ya Kauda fuska rai 6ac3 yace

"Bakida hankali ne?, Me kikeyi anan cikin Wannan daren?"


"Sadauki Please............. "

"Wait Tambayan ki nake Me ya kawoki nan Cikin Daren Nan?, wae ke wace irin Mayya ce? "

Hawaye na Zubowa tace

"Beer har yanzu Baka haquraba? "

Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa

"Tambayanki Mey kikeyi a Nan at this time of night?, Wai ke wace irin Mahaukaciya ce?, a haka kike so Na Aureki?, in Na Aureki ince Na Aura me kenan? rashin Aji?, ko Rashin Kamun kai ko Kuma Yawon dare? "

Dago jajayen idanunta tayi Duk ilahirin jikinta rawa yake zuciyarta Na bada wani irin sauti Na bugawa kanta na sarawa. Ga hawayen dasukaqi Tsayawa dubanshi tayi da Watery eyes ɗinta.

"Albeer Ni kk kira Mahaukaciya…?, Ni kake Alaqantawa da irin munanan maganganu irin wannan, Ni zaka tozarta Aarrow?, I have been waiting for u Since 8:30 just to hear the word of forgiveness from u, a ganina I don't deserve All these From you All I need is forgiveness, pease... please Don Allah... Please forgive me on Reeyyer's Behalf 🙏... "

Ta Dan dakata don saisaita Numfashin ta dake siezing, fuskar ta cikeda ƙwalla tace

"I payed for happiness please Don't break our promise "


KO kadan bai ji digon tausayinta ya dirsu a ransa ba illa ma 'kara haushin ta da taji, kenan tazo wajenshi ne da yaƙinin Zai yafe mata saboda Kuɗaɗen da take bashi, kenan Gori zatayi Masa?.

Yayi mata Kyakkyawar kallo a wulaƙance

"Awww Gori zaki Min ?,akan kin bani wasu 'yan chanji for us to be happy❓, Amma Ina so ki tuna wani abu!, Ban taɓa roƙon Wani abu a Wajen ki ba don haka Bakida ikon da Zaki min karar tsaye akan wasu kudade ,and let me Tell you Something Yes na ci kudin kine don Buƙatarr ki, and Right now Subscription Din ki ya qare baki da hurumin In yafe miki, bayan Cin mutuncin Da kika Turo ayi min"

"Wlhy bani na Turo ta ba..."

"Shut up bake Kika turota ba,Amma bake na Kira a waya ba kika bata wayan donta ci Min Mutunci?"


"Sadauki but i paid I don't deserve this"

"Wait You're still talking about the money you gave me?, Ina so ki san wani abu bakikai standard din zaki Siya haappiness Dina ba koda daidai da second dayane, taimaka miki nake yi Ina amsar Kudinki, amma Bakida wannan quality din, and also kudinki basu isa susani yafe Miki ba saboda I don't fucking care about your goddamn money! Ke suka Dama ni ko ajikina, lastly kisan wanda zaki dinga bibiya dadaddare domin yayinda kike bin wasu kamar karya kina ikirarin kin zo bada haquri wasu a lokacin Suke sanin kin wanzu a duniyarnan , koda Wasa karki Sake Nuna kin Sanni Ni Aareef nace na fasa Soyayyar in kinso ki kaini kotun duniya, nace bana sonki kiyi zuciya kema ki ƙyale ni, mutum da mijinta Amma sai bibiyan samarin Mutane, ....ki kyale Ni Na Huta nima dole ne?"

Kallonshi take Jikinta ɓari da kakkarwa kawai yake idanunta na juyewa yana yin wani irin kalar launi, yayinda takejin kamar ana buga mata guduma a tsakiyar kanta ga cikin ta dake daɗa kaimi wajen Murɗawa, Jikinta na wani irin rawa haƙora ta har hardewa sukeyi wajen fadin

"... Ni...."

Batareda yaji tausayinta ba yace
"Eh din ke, ke uwata ce? , if u wish Ki kwana a nan don't go home I don't fucking care!, Ba laifinki bane laifin Iyayen ki ne da suka Gaza baki ingantaccen tarbiyya, basu damu susan ya Rayuwar ki take ba BASTARD! "

ya 'karashe maganar da shigewa ciki banging kofar da karfi yayi Shigewarsa.

Har tsakar kanta taji Kalamansa dakuma bugawar kofar ako da yaushe bata Ganin laifin sa koda Me yayi Mata Amma ayau ta6o Iyayen ta da yayi yasa taji zafin maganganun Sa sosai, take taji bugun zuciyarta na daɗuwa.

Bin inda yake da kallo kamar zai dawo wajen.

Kalaman sa sai faman yawo suke Mata a qwaqwalwarta.

ji tayi Kafafunta sunyi sanyi, Wani irin yam, yam takeji yana yawo a jikin ta, tanaji kaman ana Ɗagata sama Izuwa wata duniyar Cikin takaitaccen lokaci Duhu ya Mamaye Mata ganin ta tayi baya ta fa'di ƙasa sumammiya.


               _*Asalin labarin *_

Zaune yake a tamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan shan iska (open  shirt)  dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin.

turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba,duk da Qamshin turaren Su Na Black Lady ya bayyana Masa ko su waye,   yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa.

Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa yayinda Juwayriyyah ta qarasa da Sallamarta, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, 6acin ran da ta shigo dashi ya ware.

Bata san meyasa ba kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take,  komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa da miskilancin sa Wanda dama zamu iya cewa Gado sukayi Gabaki 'dayansu ita dashi.

    cikin takunta Na qasaita tasoma takowa zuwa cikin office ɗin,    Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi ta Shigo .

jiyayi  ya rasa duk wani Nutsuwa tasa Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba,  cikin muryar shagwaɓa tace. 

  "Kai Ahky kasan fa mun Shigo "

Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita, 

Turo baki tayi kamar zatayi kuka tace

"Yaya Ashman Dakai fa Nake "

Batareda ya 'dago ba yace ta fita tayi sallama sannan in ya amsa ya bata umurni sai ta shigo.

Ranta baiso ba haka ta fice Juwayriyyah Nata Faman yi mata Dariyaa.

A bakin qofa ta tsaya tayi Sallama sai a lokacin ya 'dago, ya Amsa Sannan ya bata umurnin ta Shigo.

Ta Shigo tana kumbura Fuska, ko kallon su baiyi ba yace

"Kuje parlor ku jira Ni "

Tun daga yanayin Maganar sa suka fahimci yau kam hali ya Motsa, Basu Musa ba Suka Shiga ciki.

Saida ya Gama Abin da yakeyi Sannan ya iskosu zuwa lokacin Aeesh ta cika tayi Fam sai kumburo fuska take.

Dariya taso ta bashi Amma ya basar ya dubi Reey daketa Faman gaidashi yace

"Ihty Me Zan kawo Miki?, liquid ko Solid Ko kuma swallow kike So Na san yunwa ce ta kwaso ku"

Magana yakeyi Ahankali Cikin Nutsuwa Fuskarsa Na kalloN Side Din Reey sai ka rantse da Reey din yake.

Dariya Aeesha tayi don ta fahimce Shi da ita yake, Hakan wai duk Salon kaucewa A rarrasheta ta saki fuska Ne.

Cikin dariya takai mishi jifa da Pillow CusSion ya  kar6e Shima Dariya yace.

"Nasa P. A mutuniyarki ta kawo muku Abinci kafin Nan meke tafe da ku?,  Naga Alama kamar an 6atawa ihty rai tun a waje shiyasa ko arzikin Gaisuwa ban Samu ba "

Guntun tsaki taji
"Mtsww.... Wlh wani Gayene yake ta Faman Bibiyar Rayuwata, yau harda Zuwa gida yana gayawa Ammie wai Aurena zaiyi, jibeni fa Ahky yar kucul dani ko hankali ba cikawa nayi ba, Wai Aure na zai yi"

"This is Serious "

Ya fada yana gyara Zaman shi sannan ya cigaba da cewa.

"You mean kin Samu life partner Right.... …? "

Sai ya kwashe da dariya, Irin dariyar da bata ta6a Ganin yayi irin shi ba tunda suke.

Murmushi mai ciwo tayi ganin yadda yake dariya harda tafa Hannu, ita ta kawo masa serious case, Amma ya maida ta tamkar mahaukaciya.

Wato ga mahaukaciya , kodayake duk wanda yasan yanayin Alaqarta da Samari yakuma ji abinda takecewa yanzu saiya yimata dariya.

"Is it funny?" Ta tambaya tana kallon yadda fuskarsa ke qara annuri.

"Very funny" yafada cikin dariya.

Murmushi  tasakeyi

"It may sound funny but amma am not joking..am serious 😒, I need ur help"

"Yes, it's a joke, a creepy joke Abege change the topic"

Yafada murmushi akan fuskarta

"Ahky Saidai yanzu ba lokacin barkwanci bane, we're discussing a serious issue, magana ta hankali"

tafada tana ha'de fuskarta .

Ajiyar zuciya ya sauke ganin serious mood dinta a zahiri, Murmushi Reey tayi ta gyara zama ta zuba musu ido don In Suna abinsu ba'a Shiga tsakani.

Ashman yace

"Ok miss yace yana Son ki Me kikeso Nayi? "

Ta narkar da fuska kaman Zatayi kuka

"Haba Ahky Yanda kayiwa fatahi haka zaka Masa please kace an badani wa kai"


"No I can't....."

Ya fa'da Calmly yana runtse idanu.



Alhmdlillah
Ya Allah yanda Na fara da Sunanka kasa Na qare Da Sunan ka  🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Ina jiran ra'ayoyin ku Akan wannan page din.....

4th March

Bintou ❤
[7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:                 💔 *WUƘA A ZUCIYA* ❤️🗡️
                     _(Bleeding hearts)_

                            *002*

             *Let me decorate each and every ray of the sun before it shines bright on Eid....With happiness and success, prosperity and glory ,Ya ALLAH kasa Azumin da muka yi  karɓaɓɓu ne ,ka biya mana Buƙatun mu,YA Allah🙌👐🤲 EIDBARAK 💙💙💙*

                               *002*
                        *Still the beginning*

...ki bashi Dama"

Kusan a tare Reey da Aeesh suka dago Suna dubansa a mamakince

"In bashi Dama Kuma"

Cewar Aeesha Cikin tsananin mamaki.

"Eh.....Ya nemi soyayyarki ne kuma tunda kikaji ya sako iyaye, Yana neman ki bashi Daman da bakibawa sauran samarin bane, At least give him a chance"

Ya qarashe Maganar da Zuba mata idanu , itama Zuba masa Idanun tayi tana turo baki  ,saiya sakar mta harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamata.

Ita kam sunkuyar da kanta tayi Saboda wani irin Abu da taji ya ratsa Duk  ilahurin jikinta.

duk da kwarjinin dayamata saida ta sake turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasota baiga hararba.

"Nifa Zuciyata nada Wanda take so"

Kallon mamaki ya mata, ya zuba mata idanu, Murya Chan qasa Cikin sigar ra'da yace

" Wa ...kenan.....?, Ke har kinsan Menene so?, Kinsan yanda ake fa'dawa a so?, me kika sani akan so"

"Yaya bansan So ba, Amma masana so sun fasalta yanda so yake"

Ta fada Emotionally Murmushi manne a Fuskar ta, ta Lumshe idanu a hankali hoton Kyakkyawar fuskar sa ya bayyana a cikin idanunta, ta dafe zuciyarta cikin shauƙi tace

"Ko ban kamu duka ba nasan na kamu ta wani 6angaren bugun Zuciya ta 'karu daga lokacin da na kalli qwayar idonsa ,dogo ne sosai kyakkyawar fuskarsa a Koda yaushe Dauke take da wani irin shauqi ta musammman ,Salon sa daban yake a Cikin Al'umma, Shikadansa ke Maye gurbin Aboki da na 'yan uwantaka ya mamaye gabaki Daya Cardiac Region Dina 💘, Bai barma wani Koda mashaqar iska a Zuciyata bah, jarumi yake, Sadauki na Bai Chantanci na ha'da Alaqarshi da wani ba Koda bana sonsa hakan kamar cin Amana ne"

Hararara juwayriyyyah ta Wurga mata hadi da jan tsaki wlh da tasan Maganar da ta kawo su kenan bazata yarda ta rakota ba ,Wannan ai cin fuska ne🤕.

Ashman kam idanunsa ya lumshe yana sakin wani k'asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.

"....okay if I may ask who is he?, how can I get to know him?"
Ya fada a hankali yanayin muryarsa na chanzawa

"Me zai hana"

Tayi maganar tana kallon Reey , Nan ma hararar ta sake Wurga mata tana  dogon tsaki"

Dariya tayi don tasan dalilinta nayin haka.

   K'asaitaccen murmushinsa yayi yana gyara zamansa

"Lallai koma waye na tabbata yayi babbar Sa'a  kamar yanda qanwata take mai Babbar Sa'a itama, Waye Wannan luckiest guy din...tell me"

"Wani Handsome ne a  kabala yake, I think bayada nisa da Asibitin ka You might know him sef, yanada good Qualities da ake buqata ya zama Abokin rayuwata but dukda haka i don't know why Besty hates him"

Ta ƙarashe maganar cikin marairaicewa tana duban Reeyah.

"If he makes you happy he doesn't have to make sense to Her, ke zaki zauna dashi ba ita bah"

Da mamaki Reeyah ta kallesa saiya d'agamata gira Sai kuma yad'an ta6e baki .

"Yaya na tabbata da ka taɓa ganinshi bazaka Goyi bayan soyayyar su ba, He's Rough bashida nagarta ko kaɗan"

Cewar Reey

"What ever....bake Zaki zauna dashi Ba"

Dariya Esherh tayi mata mai haɗe da fakaitaccen gwalo.

Shima Mmurmushi yayi yadan ja hancin ta ,saitin kunne ya ya ra'da Mata.

"Your courage was ur crown and u wore it like a queen I like ur smile"

  Kallonsa tayi sannan ta kalli juwayriyyyah wacce ta basar tunda ya kafa mata ƙusa, ya d'aga mata gira da cije lips sannan ya mik'e.

     Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo Wasu abubuwa na cigaba da yawo Cikin jininta.

gaban filing cabinet dake office d'in ya nufa, ya dauko wani key ya dawo inda ya barta tamkar wata gunki, hannunta ya kamo ya damqa mata key ɗin.

"Key din office ɗina ne ,In kinje asibiti Gobe, ki ba Hisham akwai surgeries 2 da ya kamata muyi gobe.... Dr Naseer ne zai wakilce Ni , cus Bazan samu zuwa gobe bah ,Zan je Kano..."

"What...! kano kuma?...."

Ƙasa ƙarasawa tayi sakamakon wani mugun kallon daya watsa mata wanda ya hargitsa y'an cikinta da tunaninta, Tunda take bai taɓayi mata irin kallon nan ba hakan yasa ta tsorata Sosai.

A ransa kou cewa yayi ~Anzo wurin~

Ta6e baki yayi yaɗan janye idonsa daga gare ta, Shiru yayi na ɗan Wani lokaci kafin yace

"Wani abu ne ya taso na Gaggawa,So I have to go”

"Ayyah Yaya we gonna miss u"

Reey ta fada cikin sanyin murya.

"I feel like crying ..."

Aeesh ta faɗa cikin rawar Murya Kamar mai Shirin kuka.

Saurin ɗagowa yayi ya dubeta, ta Sunne kai tana Matse Ƙwalla.

~Yasan za'a Rina ko ɗazu da zai taho office daga Asibiti saida yasha faama da ita dan cewa tayi binshi zata yi,Alhalin lokacin barin aikinta baiyi ba~

Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi, yasani yanzu nan sai tayi masa kuka, Wani irin Shaƙuwa ce ta musamman a tsakanin su da Basua iya rabuwa koda na wasu awannin ne .

Haɗe fuska yayi ya kauda kai daga kallon ta gudun kar Kukanta yayi tasiri wajen karyar masa da zuciya.

"Kar ki Mn kuka anan"

Daidai lokacin Door Bell yayi ƙara ya bada izinin a shigo.

P.A ɗinsa ce ɗauke da Tray ,Shigowa tayi tana wani irin karaikaya As usual, cusa kai babu kwarjini .

Wani Irin harara AEESH ta danna mata, Bata san meyasa ba she just hate her , ji take kamar ta maƙuro wuyarta ta aikata chan inda in an tafi ba'a  dawowa, Tunda take a duniya bata taɓa tsanar wani Abu kamar yanda ta tsani Meenal (P.A) ba.

Ƙarasowa tayi Cikin ƙasaitaccen takunta mai jan hankali Tana ƙoƙarin Ajiye Tray ɗin ya miƙe tare da ɗaukar Keys da phones ɗinsa Batareda ya kalleta ba yace

"Amina.... ki ba ma Gateman Abincin , am off for today"

Diff komai nata ya tsaya She can't believe What he just said!, Ya ko san Wahalar da tasha Wajen Girka shayin kuwa not Even what she went through When Oning gas!, Saura ƙiris ta ƙona ƴar yatsar ta Don ita tunda take Bata taɓa kusantar Kitchen da Sunan yin Girki ba.

"But sir......"

Kasa ƙarasawa tayi sakamakon dakatar da ita da yayi ta hanyar daga mata hannu.

"Ihkty Ku tashi mu tafi"

Wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyar Aeesh A lokaci guda ,ta saki wani ƙayataccen murmushi , kusan a tare suka Miƙe ita da Reey Yayi gaba suna binsa a baya,Babu yanda Meenal ta iya dole ta fita Zuciyarta na ƙuna kamar Garwashi, ta kudurta a ranta saita ɗauki fansar wulaƙancin da Yayi mata a gabar mara kunyar ƙanwarsa.

Kai tsaye Gidan Su Aeesh

Please Login or Register in order to submit comment