Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne a ciki ,yanayin Fuskar ta kadai ya isa ya bayyana Irin Ciwon Da Takeyi, kasancewar sa Gynecologist Kallo Ɗaya Yayi mata ya Gano Abinda Ke damunta.

Umurni Ya bata da Ta shiga Mota, babu musu Ta buɗe Front seat na Gefen shi ta shiga Kasancewar a tsorace take dashi

Kallon Face dinta yake kaman Yau ya fara Ganinta, shatin Yatsun da ya Gani Shimfiɗe a fuskar ta Yake bida Kallo Yana Ayyana Abubuwa Da dama a ransa.

"Wa ya Mare ki?"

Kallon Mamaki tayi masa, taya Ya gane an mareta

"WHO slapped you?", Ya sake Auna Mata Tambayan A Karo na biyu

"D...da..Dama Uhmmm....Fada Mukayi a Hostel Shine ....na Mari Wata Uhmmm....Shine Ta Rama"

Aeesh Bata iya Ƙarya ba Hakan yasa Aduk lokacin da yayi Ake saurin Kamata

"Karya kike!, fada Min Gaskiya"

"Uhmmm Na rants....!"

"Karki kuskura ki min Rantsuwa anan Tell me The Truth!"

Kuka ta fashe Masa Dashi Hakan yasa hankalinsa Ya tashi, Amma shatin Marin Da ya gani Shinfide a fuskarsa Yafi tayar masa Da hankali.

Tsawa ya daka Mata Wanda Hakan Ya tilasta mata yin shuru Jikinta na Rawa.

"Har Yanzu Ni mijin ki ne, Don Tun Ran da Na Sakeki Na dawo dake Ɗakin ki,Na barki Ki huta ne Saboda A ganina In na Komar dake ba tare da Amincewar ki ba Na ci zalinki da yawa, Amma naga Da Alama So kike ki koma dakinki a yau dinnan, don na tabbata idan kina gida na Babu Wanda Ya Isa Ya mareki ki ƙi gaya Min"

Ya fada yana tada Motarsa

"Dan Allah Kayi Haƙuri zan gaya Maka"

"Gaya min!"

Cikin Shessheƙa tace

"AREEF ne"

"AREEF Kuma?, namiji ne ya Mareki Dama?"

Gyada masa Kai tayi cikin Tashin Hankali Ga Hawayen da ta kasa tsaidawa

"Wanene shi Aareef din?"

"Tsohon Saurayina ne Wanda Aka sa Mana Rana Kafin kazo”

"Oh Wannan ɗan Iskan Yaron?, shine Ya mareki?, ke kuma ga Kwalta Kika shimfida Masa Fuska Ya mara!"

Cije Lips ɗinsa Yayi da Ƙarfi

"Nasan Guyen Zai Gane Ƙurenshi"

Juyowa yayi ya dubeta da jajayen idanunsa

"Fitan Min a mota"

Da gudu ta fice, Dama Abinda take jira kenan

Yar karamar jakarsa ya dauko, Ya zaro Rafan yan Dari bibbiyu Guda Biyu, Har tayi nisa Ya Kwala mata kira ta juyo, da hannu yayi mata Nuni da tazo

Tana Zuwa Ya Jefe ta da kudaden

"Sun Isheki ki Aiki Kowacce Yar Talaka a makarantar nan, Kar In sake Ganin kin Fita in ba lecturers Zaku ba, Zan dawo anjima idan Basu ishe ki ba Ki gaya Min , Zan Ninka miki Su"

Daga Nan Ya Figi Motar da karfi Ya bar Harabar Makarantar.

*Ashman*

Cikin takunsa mai Cikeda Izza Da Taƙama na kasancewar cikakken namiji mai tashen kuɗi Ilimi da Kuruciya yafito daga Motarsa Sanye Cikin Ash din Suits, waya ce manne a kunnensa.

yayinda ɗayan hannunsa ke cikin aljihun Ash Trouser ɗinsa, key din Hannunsa Yasa yayi Locking Motarsa,

Masu Gadi Da Sauran Ma'aikatan Sa na kwasar gaisuwa, ko Kallonsu Baiyi ba kansa kawai yake ɗaga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da SADEEQ wadda suke Canada Har yanzu Jikin Umma sai a hankali Amma dai za'a iya cewa Da sauƙi akan Lokacin da Suke nan Ƙasa Nigeria Domin kuwa A halin Yanzu Magana Kadai Take Iyayi bata Iya motsa Ko wanne Gaɓɓa Na Jikinta.

Da sallama Ya Shiga Part dinsa, yana Kallon Ko ina tsafff ba Kamar Yanda Ya saba iske Gidan A hargitse babu Shara ba.

Deejah ta ƙaraso gareshi a hanzarce zata Rungume Shi tana Fadin

“welcome back baby ”.

Jada Baya Yayi Yana Yamutse Fuska,hakan Yasata Kifewa Da Ƙasa, Ta buge baki sai Jini

Ko Kallonta baiyi ba zama Yayi Akan Sofa ya Fara Cire Takalmar sa, Still Wayar na mannne a Kunnensa.

Tissue ta dauka a Centre table, Ta goge Bakinta Dake Digar jini.

"Haba honey Laifin me nayi Maka da nayi Deserving Treatment Dinnan Daga Gareka pleasee?, Yau watannin Mu Uku da Sati daya Amma Ko hannunsa Baka yarda ka riƙe b, Baka Min Kallon Matarka kallon Da kake min yafi Kamada Da kallon Mara daraja A idonka"

‘tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantaba.


Ɗ'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da cire Safar ƙafarsa fuskar sa a murtuƙe kaman Dai kullum.

Cikin Harshen Fullatanci Suke Maganar don Haka bata gane Komai Daga Abinda Yake cewa.

SADEEQ na sanar dashi Irin razanar da Gigicewar da Umma Ta yi Sanadiyyar Labarin Auren Aeesh da SALEEM Da taji, Abu mafi Muni ma Sakin Da yayi Mata ,kuma aka Ɓoye mata na tsawon Lokaci, gashi tace ya kira Aeesh din Layinta baya shiga ,daga Ita har Reey, Tunda Suka koma makaranta Network dinsu ya zama Ba'a Samunshi, Rokonsa SADEEQ Keyi akan Yayiwa Allah Yaje Makarantar su ya kai Mata Wayar Zai kira ya Haɗa su Da Ammi, Sosai Ammi ke son Magana da Aeesh.

A halin Yanzu Baya kaunar Abinda zai Hadashi da Aeesh ko yaya ne!, ya fiso Su nisanta da juma kaman yanda Allah ya nisanta Su A halin yanzu babu Mai ganin Wani Babu Mai jin Muryar wani.


Ita dai Deejah tana tsaye tana kallon yanda yake Sarrafa Harshe Cikin Kwarewa harya kammala wayar da SADEEQ ya kashe.

Had'e fuskarsa yayi yana hararta,

“to Mayya miya faru kuma? kika tsaya Min aka?"


Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla

“amma dai ai Kaji Abinda Na faɗa Kuma Kana Sane Kake Wulaƙanta Ni Baka taɓa haɗa Jiki na da Naka ba, Watanni Uku kenan Fa Ko hannuna baka Taɓa riƙewa ba"

Tayi maganar batareda ta damu da Fasa mata bakin da yayi ba


Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace

“To aini bana da Buƙatar Mace a tare dani, Bani Na Auro ki ba ke Kika Auro ni, Idan Kina Buƙata na Sai Kiyi Magana da wuri So that I'll fix a time For you ok?"


Ya Ƙarashe Maganar Da Ɗage mata Gira ɗaya.

Harya juya zai Haye sama tarik'o hannunsa tana Kumburo Fuska idonta na zubar da hawaye.

"Please Honey, ka tsaya ka saurareni ”

Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma ya fasa, yaɗan cije lips ɗinsa yana auna Mata Kallon Banza

“ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Nace bana yinki Dole ne?”.

"Eh Dole Ne Ashman,Na gaji da Ɓoye Abinda Nakeji a Dangane da kai, na Gaji"

Murmushin Gefen Baki Yayi Yana auna mata matsanancin Mugun kallo, Bata damu ba ta cigaba da faɗin

" Naga Sai na Fito maka a Mutum kafin Ka gane yanda nakeji a kanka, Na Gaji da Azabtar dakaina Akan Abinda Nasan Nafi Ƙarfinshi Ashman Kai Miji na ne,Ina Buƙatar ka, a yau Ko ka ƙi ko kaso Sai na Fanshe abinda Nakeji akanka wlhy"

Ta ƙarashe Maganar da fadawa Jikinshi, Ta zura hannayenta Cikin budarden Shirt dinsa Ta Shafo kirjinsa, da hanzari yafara k'ok'arin rabata da Jikinsa.

Bai Ankara ba Sai gani Yayi ta hadashi da Bango, Tasa ahannunta Ɗaya ta Dafe saman Bangon ya zamana Babu Hanyar da zai iya kwantar kansa

Waro idanu yayi ganin ta nufo Bakinta gadan-gadan tana kokarin Hadashi da Nasa, duk yanda yaso ya kauda fuskarsa Abin ya gagara.

Wani irin kasala ce Ta dirar Masa a lokacin guda ,Cikin Rashin kuzari ya datse hakwaransa da sauri, ya Daga Hannunsa toshemin hanci Da iya karfinsa a lokacin, hakan yasa ta janye bakinta dan dole, dan tana buk'atar shaƙar numfashi.

Hannu Ɗaya Yasa ya Tureta

"real Women don't Rape Men, Koda Kinyi Yunƙurin Rabani da Mutunci na Bazaki Samu yanda Kike so ba, Rayuwar ki zaki ɓata a banza Domin Kuwa banada Karfin Gamsar da Mace, Kuma Bana Haihuwa Ni Dinnan Da kike Gani Ni Hoto ne, zaman Lafiyar Ki Ki bini a yanda Nake''


Kuka Deejah ta fashe dashi tana Faɗin Bazata Yarda ba ,tsabar Mugunta ce Irin Tasa,Amma taya za'a yi Kosasshen Mutum irin Shi yace bazai iya Gamsar da Mace ba?, ta dau Alwashin Duk kauce kaucenta Sai ta biya Buƙatarta akansa.

"AREEF*

Hankali Sa tashe ya Shigo Gidan ,ko gama Parking Baiyi ba Ya sauko

"Arrow "

Kamal ne ya Kwala Masa Kira

Ko Amsa shi Baiyi ba ,ya shige ciki da Gudu yana Huci Shima Kamal din binshi Yayi da gudu, Direct Bathroom Ya Shige yasa Jamlock.

Shower Ya sakar ma kansa Nan take Rigar dake jikinsa Ya Jiƙe sharkafff.

Da Karfi Ya bugi kansa Da Bango, Saiga Jini Ya Fara bin Ruwan dake Kwararowa Ta saman Shower

"Aisha Whyyyyy....!, why...!, Meyasa Zaki dawo rayuwata?, Whyyyyy!"

Ya fada da karfi Yana Jifan Mirrorn bayin da hair Clipper, Nan Take Komai ya Tarwatse Mirrorn ya Faɗin wanwars.....




Asalin Labari har Yanzu bamu Fara ba✍🏼
Nayi Gabas 🚶🏽‍♀️

Bintou ✍🏼

14th August 2022

Tunasarwa Ta musamman 🙏
Akan SHAYE-SHAYE...

Da farko menene SHAYE-SHAYE??

SHAYE-SHAYE: Shine Cusawa Gangar jiki duk wani abu da zai sa mutum Maye ko ya fita daga Hayyacin, Tunanin dama hankalin sa na dogo ko gajere lokaci sannan daga bisani ya dawo Hayyaci sa (normal state). Abinda yasa nace Cusawa Gangar jiki wani abu shine Bata hanya ɗaya ce kaɗai ake SHAYE-SHAYE bah akwai hanyoyi da yawo shiyasa nayi amfani da kalmar Cusawa.

Wannan Matsalar bata yau bace ba kuma ta jiya bace domin an kwashe shekaru Da dama ana yi.

ta lalata rayuwar mutane haka ta kai wasu da dama har zuwa ga sun rasa rayukansu Kaman Yanda Ta Raba wasu Da Hankulansu Gabaki daya.

Domin ko akasarin masu aikata ta'addanci daga nan suke farawa kuma bincike ya tabbatar da cewa suna amfani da kayan SHAYE-SHAYE kafin suyi dukan wani mummunan aiki da sukeyi.

HANYOYIN DA AKE YIN SHAYE-SHAYE Sun Kasu Kala kala, Kadan Daga Ciki Sun hada da

1-Shaƙa: Shaƙawa kamar misalin Hodar ibilis (Cocaine) shaƙar ta ake yi ta Hanci
2-Sha: Kamar misalin Giya, Magungunan tari da sauran su
3-Haɗiya: Akwai ƙwayoyi da ake hadiyar su
4-Allura: Shima anayi(Kamar dai yanda zakuga AREEF Yana yi, Kuma Zan Iya cewa na Allurar Tafi Illa domin Kuwa akwai wanda Ake infusing Through IV intravenous _ta Jijiya_ Wanda Ke zuwa Directly to the Heart, Irin Wannan So tari Yafi Muni Da Farko Fatar Jikin mutum ta inda Ake Allurar ne zai Fara Riɓewa , Bayan ta Ciki Sun Gama Lalacewa Sannan Kuma zai iya Haifar da Mummunar Illa ta Bugawar Zuciya) don Haka Mu kiyaye Kwaya Ko wace Iri Ce

Akwai Kuma na hayaki
5-Hayaƙi: Ana amfani da wannan hanyar wurin yin SHAYE-SHAYE kamar misalin Tabar wiwi da dangogin ta
Da Sauran su domin akwai wasu.

ILLOLIN SHAYE-SHAYE
1-Tana karya Garkuwar jiki
2-Tana Lalata Rayuwar Ɗan Adam
3-Tana Lalata Ƙwaƙwalwa (yana kawo Hauka)
4-Sata
6-Tana Zare Imani
7-Tabbatuwa cikin aikata dana sani
8-Tana Raba mutum da mutanen kirki
9- Bashewar zuciya
10- Kangarewa
Da sauran su

INA MAFITA?
Sanin kowa ne wannan matsalar ta daɗe tana buwayar Mu sannan tana kawo mana cikas wurin Tarbiyya musamman a ɓangaren matasa maza da mata. Amma wani Hanzari ba gudu ba akwai abinda yake laifin mu ne musamman a ɓangaren iyaye.

Eh Ɓangaren iyaye domin da yawa a wannan zamanin akasarin iyaye sunada wata matsala ta mugun son 'ya'yan su duk da kasancewar Ni yadda na fahimci hakan sam ba soyayya bace Wannan matsala itace yanxu iyaye basu so ace 'ya'yan su sunyi kuskure Barema ka tunkare su kace ɗa ko 'yar' su sunayin wani abu wanda yake bai kamata ba, Barema ka Hukunta su. Daga nan duk yadda kuke dasu zaku iya ɓaɓewa. hakan yasa mutane suke tsoron tsawatarwa yara hakan kuma yana bada gudunmawa mai tarin yawa wurin cigaban wannan al'amari.

Kasantuwar mun manta cewa 'GYARA KAYAN KA'...Sannan da akwai wata matsalar itama dai ta shafi iyaye damu duka masu rayuwa cikin Al'umma. Wannan matsala itace magidanci ne zaka ganshi tsakiyar Iyalan sa Amma baya shakkar ya ɗirkawa sigari ko Tabar wiwi wuta.

Haka zakaga Magidanta sunyi dandalin a majalisa suna zuƙar Sigari. Ko kuma dai mutanen da Yakamata ace sune masu bada tarbiyya amma sun dage suna aikata wani abu maras kyau yanxu a haka wani saƙo muke ƙoƙarin isarawa yara masu tasowa. Idan kai uban sa kasha taba a gaban sa ko wiwi kaga kace shi yasha Abinda yafi hakan kenan. Kuma ta yaya zaka iya tsawatar da yara ka nuna masu illar abu bayan kanayin abun suna gani akan idon su. Ko mun manta Cewa 'KO WANI TSUNTSU KUKAN GIDAN SU YAKE YI" kuma "MAGAJI MAFIYI"
Dole sai mun gyara kafin muga daidai domin duk abinda mukayi akan idon 'ya'yan toh fah kamar munce suyi ne.

TA YAYA ZA'A IYA MAGANCE MATSALAR SHAYE-SHAYE ???
1- Addu'a
2- Kulawa da kai kawo na Yara
3- Nuna masu Yaran Illolin da ke Tattare da Abin
4- Kulawa da irin Makarantar da Yakamata muka ɗiyan mu
5- Ko gida zaka gina ko siya Yakamata ka Duba irin yanayin wuri da ɗabi'un Al'ummar da suke wurin
6- Ƙoƙarin Sakawa 'Ya'yan ka Tsoron Allah da bin Tafarkin Manzon sa
7- Sa ido da kulawa da wasu irin yara 'ya'yan ka suke mu'amala
8- Kada ka zama mai tsanani ko zafi Akan 'Ya'yan ka domin hakan cikin Sauƙi zai kai su faɗawa Wannan Matsalar
9- Kazama Tamkar Abokin wurin 'Ya'yan ka
10- Kazama mai Yawan Tattaunawa da 'Ya'yan ka
11- Bayyanar Masu duk wani Abu da zai iya zama illa cikin Rayuwar su a fili
12- Gujewa Aikata duk wani Abu da ya saɓa da Addini Akan Idon Yara
Da Sauran Abubuwa masu kama da hakan.

Mu a karan kan mu matasa Yakamata mu san wanene Abokanan mu kuma waye muke Mu'amala domin Bahaushe yace 'ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA'... Sannan ba wurin kowa ne zaka ci ko kasha abin sha bah. Bakuma kowa ne zakaje neman shawara wurin sa bayan ka tsinci kanka cikin damuwa bah domin akasarin masu SHAYE-SHAYE daga haka suke farawa. Da akwai wata muguwar hali da masu wannan ɗabi'ar suke da ita shine yaudarar mutum zuwa faɗama Harkar wurin bashi duk abinda zai sha kyauta ba tare da sisin shi ba idan yayi nisa sai su zame jiki su barshi da Bala'i.

Haka Malamai zasu iya bada nasu gudunmawar kamar yadda wasun su sukeyi wurin jan hankali da nunawa mutane Illolin wannan abu. Haka zalika Kamar yadda en jarida suke wayar da kan mutane Yakamata a ƙara basu ƙarfin gwaiwa wurin ƙirƙirar labarai ko wasannin kwaikwayo tare da ɗaukar nauyin su a haskawa jama'a Illolin wannan abu. Haka suma jami'a tsaro Yakamata mu ƙara basu ƙwarin gwaiwa wurin fatattakar wannan mummunar aikin.

MU HAƊA ƘARFI DA KARFE MU YAƘI HARKAR TA'AMMALI DA KAYAN MAYE...

Allah yasa Sakon Ya isa Inda ya Kamata 🙏


Bintou ce✍🏼
14th Aug
[10/19, 9:09 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*
_BLEEDING HEARTS_

*028*

Gudu Sosai Yake Sharawa Akan Titi Dishi Dishi yake Gani, kadan ya rage ya Bigi wani mai Babur, Sam Hankalin sa baya kan tuƙin da yakeyi.

Gidan kamal (Abokin AREEF) ya Nufa,yana Yin Parking ya tura yaro Ya Kira masa Aareef.

Yana Zaune a motarsa yana kallon Hanyar Fitowa Daga Gidan banda Huci babu Abinda yake yi sai Huci, Chan ya hangoshi ya fito.

Hannunsa Sai digar Jini yake Sakamakon Mirron da ya Fasa a banɗaki, ƙugunshi Daure da Towel , Daga shi sai Vest Fitowanshi Daga Wanka kenan, ko kunyar Fitowa a haka baiyi ba, hakan yasa na fahimci ya saba Fitowa a haka.

Baiyi Niyyar Fitowa ba saboda Tsananin fushin Da yake Tattare dashi,Amma Jin yaron da Aka Aiko yace mai katon Mota ne ke neman sa Sai ya fito , a zatonsa Nurse dinda ya Kira Zatayi masa Allurar ce.

AREEF kyakkyawane sosai Ga tsawo ga kyan ƙira , Take kishin saleem Ya motsa, Dole Aeesh ta ruɗe akansa,jikin Motar AREEF ya Matso ya kwankwasa Glass din Motar .

Fitowa Saleem Yayi daga Cikin Motar Cikin Natsuwa ya jingina da Motarsa .

AREEF ya tako gabansa ya bashi Hannu don su gaisa, Saleem baiyi wata wata ba ya Daga hannu ya wanke shi da Razananniyar Mari a Kuncinsa ta hagu.

Marin ya shigeshi sosai yayi saurin daga hannu ya Dafe Kuncinsa a gigice

"Marin da kayiwa mata tah, Wannan Somantaɓi ne,Next time idan Na ganka Kusa Da Ita ,yanke Kafafunka zanyi...!, Bastard"

Shafa Kuncinsa Yayi ,Ya Ɗago Jajayen idanunsa Ya sauke akan Saleem Daketa faman Huci.

"Me nayi maka da nayi deserving wannan cin mutuncin daga gareka ka?, And who are you?"

Kallon banza Saleem ya watsa masa yace

"Ni mijin A'isha ne!, wacce ka Mara ɗazu,a hagu ka Mareta Shiyasa na barka a haka ban haɗaka da Yan sanda Ba, da ace A dama Ka mareta da karnukana zansa Subika a unguwa"

Saukar da Kansa Areef yayi a ransa Yace

" _Her husband? Mijinta?,I deserve it, I deserve the Slap!, I deserve everything"_

Dagowa Yayi a karo na Biyu,wannan karon a sanyaye har kwalla sun fara kawowa a idonsa, da sauri ya Juya ya tafi batareda ya Furta komai ba.

Ganin Yanda Yanayinsa Yasa Jikin Saleem yayi sanyi sosai, har ya so yayi nadamar marinshida yayi, da ya sani da Ya fara Jin ta bakinsa yaji dalilin da yasa Ya Mareta Wataƙila laifin ta ne ,ita ta jawo.

Tuƙi yakeyi yana tunani, a sanyaye saɓanin yanda Ya saba Zabga gudu a hanya in Yana driving.

*AREeF*

Ya jima yanaa shafa fuskarsa dan da gaske marin ya shige Shi Sosai,

_I deserve it!, I deserved everything!!, I deserve the Slap!!!_

Sai Maimaita hakan Yake a ransa Zuciyarsa na Rawa, Baiga Laifin Saleem ba don Ya rama Ma matarsa Marin da yayi mata ,koma me yayi mata shi yaja Laifinsa ne da Bai Nuna mata Matsayin ta ba tun farkon haɗuwarsu,Ganin Reey da yayi ya Taso masa Da Tsohon Jiɓin da ya riga ya binne a zuciyarsa.

Tunda Yake bai taɓajin son Aeesh a ransa ba ko kadan , Haɗuwarsu ta farko Reey ya gani Yake so, Amma ko kallo bai isheta ba, hakan yasa Ya fara gwada Kaunarsa akan Aeesh a Ganinshi Ta wannan Hanyar ne kadai zai iya karkatar da hankalinta Izuwa Gareshi, Sai Kuma aka samu akasi Tun farkon Haduwarsu da Aeesh ta kware masa Shiyasa bai sha wahalar Samo Kanta ba, Kullum Fuskar Reey a daure bata taɓa sakin Masa fuska ba, Shiyasa Ya kasa samun damar Furta mata abindake ransa .

Koda Aeesh tazo Masa da batun Aure ,Yaso Ya Fada Mata Gaskiya inyaso kome zai Faru ya faru, baiki ta kife ba, Amma Tsantsar Soyayyar da Aeesh ke nuna masa ne yasa Shijin tausayinta Yaji aransa zai Iya Aurenta Koda Daga Baya ne sai ya auri Wacce zuciyarsa Keso wato Reey, Ga kuma Uban Kudaden da Dr Sabo da su Deejah Suke bashi akan Ya taimaka musu Ya aureta , Idan Ya aureta zasu Yi masa babban Kyautar da ba'a taba masa Irin sa ba a rayuwa, su dai Burin su suraba Alaƙar dake tsakanin Aash da Aeesh.

AREEF mutum ne wanda Keda bala'in son Kuɗi zai iya sadaukar da Komai akan Kuɗi akan Kuɗi Baisan Mutunci ba, Ya rayu cikin Talauci da matsi na rayuwa, ya San Talauci ciki da wajensa.

Ada Mahaifinsa Rikakken Talaka ne, yasha Gwagwarmaya dadama kafin daga Bisani Allah ya azurta shi da Kudi, ya daukakashi a lokaci guda Rayuwa ta chanza masa, Sai dai kuma yana Samun arziki ya fara Wulaƙanta mahaifiyar Areef,Gori da wulaƙanci Kullum sabon Chapter yake buɗe mata don yaga batada Iyaye kuma zata iya hakurin zama dashi a ko wane irin yanayi daga Bisani ya auro mata Wata itace tayi sanadiyar Rabuwarsu, Rabuwansuw tasa Ta shiga gwaramar Rayuwa da ita da ɗanta Ya taso Cikin matsi da Rayuwar babu Sai su jera sati Basu daura Tukunya a gidan Ba, Ga Wulaƙancin Gidan Haya da Suka Fuskanta, garin Yawon Areef ne ya Taɓa Tsinto wata dutse ya kawo gida Yana Wasa Dashi Mahaifiyar sa ta gani, ba Dutse bane Zinari ne asalin zinarin da ba'a Riga an Sarrafa ba.

Take ta amshe ta shiga kasuwa don Ta siyar, da kyar ta samu ta siyar bayan anyi mata Siyan Wulaƙanci , aƙalla idan An siyeta da daraja zata kai kimain Miliyan Goma, Amma kwata kwata Dubu dari Tara Aka siya.

A lokacin AREEF Nada Shekaru Ashirin , Har zuwa lokacin Baisan Darajar Zinari ba,Murna Ya shiga yi wai ya samo musu kudi, wata yar ƙaramar fili Ta siya na dubu Ɗari biyar, A lokacin Fili Baiyi tsadar Da yy yanzu ba.

Areef da kansa Ya Gina musu yar ƙaramar Gidan Ƙasa ya maida Sauran Filin Gona, Akayi ma gidan Plaster da Painti gidan ya Koma tamkar Gidan yan gayu.

Daga Nan sai Mahaifiyar sa ta koma siyar da awara a kofar Gida suna Samun riba, Allah yasa Ma Sana'ar Albarka sosai Da wannan kudin Ta samu Ta biya ma AREEF kudin Makaranta yayi NCE dinsa inda ya karanci PhyCom , Yana Gamawa Ya fara Koyarwa a Government primary School Tudun Wada ,bayan Shekara Daya Ya tara Kudi ya shiga Jami'a ya fara B'Ed dinsa Inda ya karanci Computer Science, a halin yanzu ya gama Bai samu Aiki ba, kuma yace bazai Koma Koyar da yara Ba, ya raina Teaching.

Har yanzu mahaifiyarsa Na siyar da Awara a ƙofar Gida, Abokansa da Students ɗinsa Da ya Taɓa Koyarwa In yazo wucewa sai ayita nunashi ana cewa Ga Yaron Mai Awara, yayi yayi ta daina Siyarda Awara Amma Firr ta Ki tace Awara ne Rufin Asirinta.

Dalilin da yasa Ya bar mata Gidan Kenan Ya Koma Gidan Abokansa Kamal Da Bash Da Zama , Bash Yahoo boy ne kullum Yana Kan system yana Satar kudaden jama'a ta yanar Gizo Da haka Yayi Kuɗi.

Shi Kuma Bash Dan masu Kuɗi ne Mahaifinsa ne ma ya kama masa Gidan ,Amma shi ba dan Garin Bane Dan Yobe ne karatu ne ya kawo shi Kaduna, Sai aka Kama masa Gida Don yaƙijinin zaman Hostel, Kafin Su gama makaranta ya Gina Wani Gagarumin Cafe tanan yake samun Kudin Da yake rarraba ma Abokanansa, hakan Yasa Koda ya gama Makarantar Baiji sha'awar Komawa Yobe ba Saboda ya rigada Ya saba Da Garin, Saidai Ya koma Gida A Kowanne Watanni Uku ko Karshen Rabin shekara .

Areef dan zaman Banza ne, bai san zafin nema ba, yafi Ganema a nemo a bashi yaci yasha Ya nemi Ƙari, ko sau daya basu taba masa Gori ba hakan Yasa Yake jin dadin Zama dasu.

So tari yakan Dan Leƙa Cafe din Kamal, anan Yake samun Nasa Na kansa,mata dayawa Takoina Binshi Suke Ganin yana dakyau da Iya wanka, yana da girman jiki da tsarin halitta mai kyau, ga uwa Uba Iya ado da Kudi, yanada Nutsuwa, Amma baya iya Kauda Kai akan Mace ,Duk kazar Da ta kawo Masa Kansa In tayi masa Fige ta yake, Daga Bisani Ya watsar da Fiffike.

Bai Taɓa Neman Mace ba, Mata ne nemansa abokansa Har bakin ciki suke masa akan Farinjinin Da Allah ya masa akan mata.

Haduwar su Da Reey ne ya sauya Komai, Ya Zauce dayawa akan Ta Amma Ba Ita ya samu ba, haka Haduwar Sa da Aeesh ta sama Masa Alkhayrai da Dama Wanda Bazai taɓa mantawa dasu ba, Ciki Kuwa Akwai Makudan Kudaden da yake karɓa a hannun Dr Sabo Da Su Deejah da Abokiyar karawarta Yumnah, Kowannensu da Dalilinta sun hadu a Buri daya nason Raba Aeesh da Ash Tareda Son Cusawa Areef Auren Aeesh, Bugu da Kari Ya karɓi kudade a hannun Abba Shima Dai Burinsa Ya hakura da Auren Aeesh And Again Aeesh ta bashi Kudin Aurensu Ya kashe, yanzu haka ma Kullum Sai Dr Sabo ya dameshi da kira Yana Skipping calls Ɗinshi.

Bai gane ya fada Dayawa a soyayyar Reey ba sai bayan kwana biyu

Halin daya shiga a cikin kwanakinnan biyu ya tabbatar masa cewa ba qaramin nutso yayi ba a kogin soyayyar Reey ba kuma bayajin zai iya rayuwa idan ba Tareda ita ba.

Duk yadda yakejin soyayyar Reey a zuciyarshi yana iya bakin qoqarinshi na dannewa yayi acting normal musanmman ma a gaban Aeesh da Ta musu mai dukda wani sa'in Dakyar yake iya controlling din emotion dinshi,Yana forming Fake Love da Aeesh.

Sosai soyayyar ta ke qara hauhawa a duk kowacce bugun zuciyarshi abin har tsoro yake bashi don wani sa'in har kuka yake yana fargabar kar allah ya jarabce shi ta wannan fannin don tasan ba qaramar wuya zai sha ba idan Ya rasa Reey, Yafiso ya Rabu Da Aeesh cikin Salama Ya koma ya lallaɓa Reey Ya aura.

Auren Aeesh tayi yi masa Daidai Domin Kuwa gani yayi kamar Allah ya Rabashi da Kaya, Tun washe Garin Aurenta ya Makata a Black list.

Ya Tattara ta Gabaki Daya ya Zuba a kwandon shara ,yasha wahala sosai kafin Ya saba da Rashin Reey, Amma Dole ya haƙura da ita a ganinsa kila ba Alheri bace a gare shi ,Tun Shigowar ta rayuwarsa Rayuwar sa ya shiga Garari.

Ganinta da yayi a yau

Please Login or Register in order to submit comment