Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ko ina na Jikinsa malale da jini dubawa gefen da zaiyi yaga abinsa a guntule, ya kalli jikinsa yaga Shafayau babu Komai , ihu ya saki wanda ya karade ko ina na gidan, Amma shi ɗaya kejin abinsa.


wata Busasshiyar murya mara Daɗin ji yaji cikin hargagi da hayaniya yaji ana cewa

"Ba kaine wanann Mugun lauya mai amfani da hukuma kana lalata Mutuncin Mata da kananun yara ba?,tho yau ka taɓo kuliyar mu, cikin Yan matan da kayiwa fyade satin da ya gabata akwai Jikar mu Gumdisiyya, Wanann Shine hukuncin ka na yau idan ka warke zamuyi maka na biyun.

Ihu ya Ƙwala cikin azaba, Abdul yazo a firgice cikeda tashin hankali ya kaishi asibiti nan take akayi moving dinshi to Emergency akayi masa aiki , kafin safe ya kumbura due to kidney failure saboda lalataccen kidneynsa da ya Fara rubewa a cikinsa, sbd baisha da yake sha ba.


*AREEF*


Tun Randa Aeesh Ta haihu ya fara girban Abinda ya shuka, ya fara yin Dana sanin Da mahaifiyarsa tace zaiyi, daya daga Cikin Yan matansa tazo masa har gida da sakamakon likita tace tanada ciki kuma babu inda zata a gidanshi Zata Haifeshi, sunan Yarinyar Sarah Bata gudun Abin kunya don mahaifanta sun rasu, yunwa da rashi yasa ta fara Kulashi yana Bata kuɗi har yayi nasarar Rabata da Mutuncinta bayan yayi mata Alkawarin Aure, Tarayyar ta dashi Yasa idanunta Suka buɗe sosai , amma Shi ɗaya take kulawa shi Kuma yana ɗauke mata Bukatunta na ci da sha School fees sutura etc, duk kudin da Aeesh take bashi akanta Yake karar dasu, yayi iya Ƙoƙarin sa wajen ganin Sarah Bata samu Ciki ba, Amma saida ya Shiga, Zama tayi a dakin sa tace babu inda zata sake dagawa har sai ta haihu , Sarah Yar Bala'i ce ga karfi kaman namiji Ga manyan iskokan kanta da basu kyau in sun tashi, bai isa yace uffan ba, yanzun ga zata hau sama Ta najada Masa na jaki.


Suna zaune a gidan har aka Sako Su Deejah da Bash bayan An Gano wanda ya haɗa abin wato Dr SabO ,yaso ya kashe Aareef ne sakamakon Bijere musu da yayi, a zargi Aeesh Kaman Yanda Shugabansa ya tsara masa sai tsautsayi ya faɗa Kan Kamal, Bash na fitowa ya karɓe gidansa ya siyar ya koma gaban iyayensa, babu yanda Aareef ya iya dole ya koma Gaban nasa Uwar , wacce ita ɗaya ta rage masa kuma dashi ya dogara Sarah Bata barshi ba Saida ta bishi har Gidan, kullum cikin tashin Hankali a mata faɗa aljannu su tashi,ya susuce ya fita hayyacinsa , ga wani Son Aeesh da yakeji a cikin zuciyarsa wanda ya maye gurbin na Reey, Hakan Yasa ya Auri Shayeshayensa ya zame masa Breakfast, lunch and dinner, Cikin Kankanin lokaci ya koma tamkar zautacce..


Cikin Kan kanin lokaci savings nasa ya kare a shaye shaye, ya siyar da Motar da Aeesh ta bashi a banzace, Ya kuma karar da kuɗaɗen Ajiyan sa, duk Kadara nasa ya kare, wayarda ta bashi Ta 250k ya siyar a 90k,suturun sa duk ya siyar , yanzu bashida komai gashi babu Aiki, jarin da Aeesh ta bashi Duk ya cinye, zuwa gidan Su Reey da yakeyi ba don komai bane , yana zuwa ne don yasan Ita kadai zata iya bashi numbern Aeesh don a halin yanzu Tunaninsa gaba ɗaya ya karkata ne akanta yana so ya bata Haƙuri sannan yace ta dawo gareshi (kunji majnun 🙄) don Ji yake idan Bai sameta ba mutuwa zaiyi.

Duk inyaje gidan Su Reey sawa take a fitar dashi ko kallon Arziki baya samu daga gareta, gashi yana ce sai zuwa yake, yauma Zuwa yayi kaman yanda ya saba yaga zata fita zata gidan Aeesh Ta tayata zaɓan anko saboda Har yanzu Aash yaƙi bari ta riƙe waya, ta haye napep shima Ya bita, a kofar gidan Ashman aka sauketa ta shiga

Aeereef baisan Aeesh tayi masa Nisa ba sai yanzu da idanunsa sukayi masa Tozali da Tangamemen gidan da take zaune, duk da ba yau ya fara ganin Gidan ba Amma ya girgiza domin A halin yanzu halin da yake ciki bai kai matsayin da zata Ajiyeshi a matsayin Mai bawa flowern su Ruwa ba.


Reey na shiga tagaya ma Aeesh tayi bako, da mamaki Ashman je duban ta, baƙo kuma?, "Eh In so samu ne ku ganshi Tare don na lura bakoncin na ku biyu ne"

Tare suka fito Aeesh da Ashman, Reey na biye dasu Aeerah na kafadarta.


Aareef Kallo ɗaya yayiwa Mai gadin Yaji jikinsa ya fara rawa jibgegen mutum ne a tsaye one blow zaiyi Masa ya shige ƙasa a tsorace yake ja da baya, yana rarraba ido, chan ya hangosu Suna fitowa.

Baiyi zaton Zata fito ba, Amma ganinta tareda Ashman Yayi matuƙar tsorata shi, gashi tayi wani kyau tayi haske alamar zaman lafiya da kwanciyar hankali .

Kallonda Ashman ke auna masa kadai ya isa ya razanar dashi, hannu Ashman Ya miƙa masa don su gaisa, ya maida hannunsa baya yana Girgiza kai cikeda fargaba.


Ashman Ya taɓe baki, Reey sai harara take faman Banka masa

A ƙule tace
"Me ya kawoka?"

Duban Aeesh yayi

"Wurinki nazo"

Ta gyara tsayuwar ta, gabanta na cigaba da faduwa, ganin yanda ya koma ya ƙara tayar mata da hankali, ya fige Kaman ba Aareef dan gayu ba, a hankali ta maida Dubanta kan Kayan jikinsa duk sunyi dauɗa bashi cikin hayyacinsa gaba ɗaya, tayi saurin Haɗiye hawayen Tausayinsa da yazo mata tace

"Ina sauraronka sadauki"

Ashman ya harareta, ta saƙalo Hannunta cikin nashi tana sakin Murmushi.

Jikin Aareef na rawa ya duka ƙasa, yayi Kneeling

"Please A'isha....."

Shuru tayi Ta tsareshi da ido

"Ki yafe Min......”

Reey taja tsaki don Wallahi haushinsa take ji kaman Ta shaƙo wuyar sa ta aikashi barzahu a fusace tace

“ta yafe maka akan Me?, Dama kayi Mata laifi ne?"

Ya saukar dakansa idanunsa na fidda kwalla, Reey ta cigaba

" kazo ta yafe maka ne akan Illar da kayima zuciyarta ne?, *Ko Wuƙar da ka Danna mata a zuciya kazo ta ƙara shigar dashi So that Bazata sake moruwa ba?* , ko marin da kayi Mata kazo ta yafe maka?, Ko kwanan da kasa Tayi a gaban ɗakinka da Ciki a jikinta kazo ta yafe maka?, Mr Arrow The heart pointer Which one among?.."

Ta karashe maganar tana tsareshi da oily Eyes ɗinta, Aeesh ji tayi hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa Sun zubo, Ta kwantar da kanta a kafadar Aash Tana Shessheka, ta kasa gane dalilin da yasa take jin Sonsa a duk lokacin da ta haɗa ido dAshi, amma In zatayi shekara bata ganshi ba, bazataji komai akanshi ba.


Aareef ya Sunkuyar dakai cikin Takaici, Reey ta gyara Noor a kafadar ta, Ta Girgiza kai hawayen takaici suka silalo saman Fuskarta.

"Aareef...iya abunda ka sani kenan, Aeesh tayi shaye Shaye tayi hauka duk Saboda kai da cikinta kasa Ta zama tamkar mahaukaciya duk wannan Basu isheka ba Saida ka dauko Yan sanda Suka zo har gida suka kamata ,kayi Mata Sharrin Kisa, Aeesh bata taɓa Taka police station ba, Amma Saboda kai har Shari'a akayi da ita da haka kake Son ta yafe maka?, Me ka aikata mata mai kyau da zata duba ta yafe maka?, Ko ta yafe maka ina zaka kai hakkin yarinyar nan da bataji ba bata gani ba?, Yarinyar da ka cutar da rayuwarta tun a cikin mahaifiyarta?, Ina zaka kai hakkin Mijinta da ka karɓe sadakin Matarsa ka karɓe Kyautar da yayi mata?"

Tasa bayan hannu ta share hawayenta

"Aareef....!, You deserve to die....!"

Aeesh Kanta taji yana sarawa wani abu taji ya tokareta yawun bakinta ya kafe, har wani daci daci takeji a makoshinta , Arayuwa ganin Aareef shike taso mata da soyayyar sa, da zata yi shekara bata ganshi ba har mantawa dashi zata yi, gashi yau da ta ganshi a mummunan yanayi yasa ta rasa nutsuwar ta, duk ya fita hayyacinsa , tausayinta na ratsa ta, kirjinta taji yana bugawa da karfi kaman zai fita

A Hankali ta ɗago kanta, fuskarta malale da hawaye Muryarta a dishe tace

"Na riga na yafe maka Aareef..... Na yafe maka , ba laifin ka bane duk laifina ne, Ni na dora wa kaina , i did it to my self...."


Sai ta dakata tana Goge kwallar Fuskarta

" Please ina so kamin Wata alfarma"

Da sauri yace

"Ina jinki"

"Please daga yau bana So na sake ganinka a rayuwata, ka Min wannan Alfarmar, ka fita daga duk hanyar da zan haɗu Da kai"

Ta zura hannu cikin Side trouser na Aljihun Ashman ta Zaro Kuɗi ta kirga, dubu biyar ne

"Ahky Bari mu bashi Sadaka"..

Ta faɗa tana Miƙa masa, ya karba da sauri yana godiya, bata tsaya jin Godiyan sa ba ta shige ciki, Reey tabi bayanta , Ashman ya tsaya ya dau 3mins kafin Ya shigo fuskar nan nasa kaman Kullum, a murtuƙe kaman ta maigadin makabarta.


kallonShi tayi tana Kago Murmushi

"Ahky kaga yanda kake yin kyau in kana fushi?"

Bai jita ba, saboda airpos dake manne a kunnensa. Hannu takai ta cire kunne ɗaya, ta ɗora hannayenta a kafadarsa, ya ɗago ya dubeta yana sake tsuke fuska.

“Am sorry, kaji?”.

"What is the sorry for?"

Yafada yana huremata idanu hakan yasata saurin lumshesu wanda hakan yaba hawayen da take dannewa damar gangarowa

Shigowa tayi jikinshi ta maƙaleshi tana turo baki cikin shagwa6a tace

"I love you Ahky"

Ɗago Fuskar ta yayi

"Repeat what You just said ihty"

Ta girgiza kai tana sakin Murmushi
"
سرق شخص ما قلبي وأنت الأعلى في قائمة المشتبه بهم
_saraq shakhs ma qalbi wa'ant al'aelaa fi qayimat almushtabah bihim_

"wani ya sace min Zuciyata and you are the highest on my list of suspects"


Ya Lumshe Idanunsa,Murmushi yasaki sannan yasa hannu yana shafan bayanta yace

"Fassara min da Hausa bana jin Larabci"

Tasa yatsarta ɗaya tana mai yawo a ƙirjinsa, cikeda shauƙi tace

لص

"(Barawo)"


Ya Zaro ido yana rike hannunta don har tsakar kansa yakejin abinda tayi masa

"Ihty Rufa min Asiri Ki bari kada Zuciyata ta buga"

Da alama dai wadannan jama'un sun Mance baƙuwar su Reey fa🤔🤔, ganin Suna Shirin Shan Corner sai Reey ta miƙe sumul Sumul ta haye Sama, gudun Kada su lalata mata Tarbiyyan ido.

Ashman Da yaga shigewan ta yace

"Hankalin ki ya kwanta Tunda Kin kora mana Baƙuwa"

Fadawa tayi jikinshi tana mintsilinshi a qirjinshi tana kukan shagwa6a shikau sai Dariya ya dagota yayi cupping face ɗinta ta harareshi,



سأحبك طوال حياتي وعندما أموت سأظل أحبك إلى الأبد وما بعده.

_sa'uhibuk tawal hayati waeindama 'amut sa'azalu 'ahibak 'iilaa al'abad wama baedahu_


"I will love you all my life and when I die I will still love you through eternity and beyond♥️"


Ya faɗa emotionally


Nayi Gabas 🚶🏽‍♀️

Bintou ✍️



Comments dinku yayi Ƙasa sosai Gaskiya 😔


Gaskiya akara flow din comments sunyi kadan.


13th Jan
[1/19, 07:06] Bintou Abdul: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_


*068*

Ya ɗora kanta a wuyanta yana Shaƙar Ƙamshin Humrah dake neman Tafiya da Imaninsa, ya Lumshe idanu a hankali kaman Mai koyon magana yace

"Ihty...wannan wane Ƙamshi ne nake yawanji a jikinki?, Ƙamshin Nada dadi sosai"

Karamin Dariya tayi tace

"Humrah ce , wanda Ammie ke siyo min daga Zaria"

Sake Lumshe Idanunsa yayi yana jin Ƙamshin na Shiga every Conner of his body With a gift of emotions, Muryar sa kaman an tilasta shi yace

"Ƙamshin nada daɗi Sosai, Allah ya saka ma Ammmie"

Taji daɗi sosai ,ta amsa da Ameen a sanyaye bugun Zuciyarta na daɗa tsananta ,bata san Me yasa Ba, tunda idonta yayi Tozali da Aareef taji ta Rasa natsuwarta, Binnanniyar soyayyarsa da ta jima da Rufewa a zuciyarta na Neman Tasowa, hawaye Taji sun sauko mata, a hankali ta furta

"Ohhh Allah Have mercy On me, Allah Ka rabani da wannan Masifar, ka bani Ikon Farantawa Mijina Yanda Ya kamata ,ka Cire min Son Sadauki a Raina".

Bata San A fili take magana Ba, saida taji Ya ɗago Fuskarta yana Dubanta cikin ido , muryarsa a raunane yace

"Ihty....Am Sorry Nasan Baki Sona, Am sorry For Forcing You into my life...."

Hannu tasa ta toshe bakinsa tana Girgiza kai

"No Ahky don't say that.....No Ahky Ina sonka, you're my forever ka daina Cewa bana Sonka , sai inji kaman Kaman Kana Turani cikin Wani halaka ne, ina so Ka fahimce Ni Ahky....ka taimaka min, nasan Kai kadai zaka iya taimako na ,kana Min Uzuri wanann Karon Ma ina bukatar Uzuri"

T kamo Hannunsa ta kai Saitin zuciyar ta, hawaye suka gangaro mata

"Feel my Heart beat is it normal"
Ta faɗa cikin karyayyiyar Muryar ta mai ban Tausayi.

Zaro Ido yayi yana jin yanda Zuciyar ta ke pumping abnormally Kaman zai tsaga ƙirjinsa ya fito, ta Lumshe Nauyayyun idanunta, taba hawayenta damar Zubowa ,cikin muryarta dake tada Tsikar jikinsa tace

"My heart Beat changes A duk Lokacin da nayi Ido hudu da Sadauki, nasan Ina sonsa Amma bansan kalar soyayyar da nake masa ba, idan yana gabana Ganinsa nake kaman Wani Sarki Gani Nake duk duniya Zuciya ta batada wani sarki bayanshi, Amma da zarar ya ɓace wa gani na, sai Naji Duk na tsaneshi, i know I had crush on Him for a long but Wlhy Tun farkon Haduwa na dashi Banji ina sonshi ba, i just got crush on Him Duba da yanda Yake daukan Wanka yana burge Ni sossi ,Amma Zuciyata kai take so tun ƙuruciyata, You Are the owner Of my heart Since then, Haushin Amincewa da soyayyar Deejah da kayi bayan nayi maka tayinta byasa na Fara Kulashi, I don't Know how, when and why na zama crazy akanshi?, I don't know why Am dying on him, I Sold my Life to him, he used and misplaced it he play rough with my baby heart"

Aeesh ta dubeshi da hawayen dake gangarowa duk Jikinshi yayi sanyi, shi kadai Ke fahimtar ta akoda yaushe, da yanzu zata gayawa wani ,laifinta za'a gani ace batada Hankali, but he feels same as she feels, ta murza hannunsa a hankali.

"Ahky Kai kadai kake fahimtar Halin da nake ciki , nasan Banida Lafiya, i really need help,Ina bukatar Taimakon gaggawa in ba haka ba zuciya ta na gab da Kamuwa da Ciwon zuciya....! ,Zuciyata zata fashe Ahky zan Mutu, Son Sadauki zai kashe ni..."

Kuka Takeyi sosai, yanda take yin Kukan dole ta baka tausayi, ya jawota ya Rungume yana bubbuga bayanta


"Bazaki Mutu ba Ihty, bazaki Mutu ba InshaAllah bazaki Mutu ba, kiyita maimaita innalillahi Wainnailayhirraji'un, Zakiji sauƙin Abinda kikeji a zuciyar ki, lamarin ki Ya fara Tsorata Ni, tabbas Akwai Wani Ɓoyayyen Sirri dangane da Wannan Lamarin InshaAllah Anjima zan Kira Abokina Salahuddeen Abubakar mai zuma, yayiwa mahaifinsa magana Akan Lamarin Ko kuma in nemi numbern wayansa na kirashi da kaina in masa bayani, Ihty we Really need Help"

Reey ganin Sun ɓata mata lokaci gashi She has a long way to go yasa ta fito , Zaune ta gansu tana Hawaye idonsa yayi ja kaman Garwashi

,ganinta tana Hawaye yayi matukar bata mamaki , da mamaki Ta shiga Tambayan ta Dalilin da ya sata kuka Amma ta kasa cewa komai, ya kamata Reey ta sani ko don Ta taya ta Addu'a da shawarar samun Mafita, don Reey shaidace akan Irin Son da ta nunawa Aareef Duk mai hankali in yaji Irin Son da take ma Aareef yasan It isn't Normal, dole akwai abu a ciki, sai a lokacin abubuwa suka fara dawo mata ada Aeesh ba haka take ba, she has small brain Karamin ƙwaƙwalwa gareta tana da saurin Shigar da abu a cikin Ranta, but This one too much , tunowa tayi Da fadan da suka sha yi da ita akan Aareef, da kuma sadaukarwan da tayi masa ,a lokacin da komai nata ya ƙare ya zamana batada komai ta siyarda kayan sawanta mai tsada don ta siya Murmushinsa, Kafin ta samu farin ciki a wajensa sai ta fidda kuɗi ta siya, soyayyar su ta zama Kaman Datar Airtel Kayi Sub yanzu kana kunna data su kwashe abin su.

Reey tace bai kamata ayi sanya ba , ya kamata a kira Salahuddeen Ya sanar Da mahaifinsa Mal Abubakar Mai zuma, aikou Cikin Yan Mintuna da basu wuce talatin ba Aka hadasu da Malam Abubakar Mai zuma Sukayi Masa bayani, Murmushi yace baya bayani a waya amma Su Sami lokaci suzo Gidan Zuma Kongo Don A gano daga Inda matsalar take.


🚦🚥🚦🚦🚥🚦🚦

Da Gudu Gudu sauri Aareef ya karasa Gida don Kada matarsa Ta zarge shi da biyawa wani wuri, ce mata yayi zashi Gaida ummansa ta bashi Hour Ɗaya gashi yanzu Har ya cinye Minti 57.

Shiga gidan yayi yana Huci, ganinta yayi a tsaye ta ɗora dammara a ƙugu sai Faman Huci takeyi.

"Daga ina Kake?"

Mummunan muryarta ta sauka a kunnensa, cikin Daburcewa yace

"Ehrm uhmm"

"This means Bakada gaskiya ,ba Gidan Umma kace zaka ba?"

Ta faɗa cikin tsawa, yanda take Magana Yasa hantarsa ta hau kadawa yaji Jikinsa ya fara mazari ya kasa yi mata karya cikin In ina yace

"Ehrm... uhmm dama....Naje wajen Aeesh ne, Naje rokon gafararta"

Gani yayi ta fara nufoshi,daskarewa Arrow yayi don Firgici, Tsuuu kakeji Aareef ya saki Fitsari, ta cigaba da kusanto shi tana zare ido habawa k'afa me na ci ban baki ba, AAREEF ya juya zai arta a guje ta rikoshi

"Ina Zaka?....."

Jikinsa babu inda baya Rawa, sanin Indai akan Kuɗi ne Sarah Zata iya yin Komai yasa ya lalubo Yar Dubu goman Da Aeesh ta bashi ya damƙa mata,

"ga baki"


Ya faɗa muryarsa na rawa

"Aareef ban Yarda Da kai ba, ba duka kenan ba"

Tafada tana Lalube Aljihunsa, nan Ta lalubo Bundle ɗin Dubu ɗarin da Aashman Ya bashi ya ja jari, bayan su Aeesh sun Shiga ciki, tsayawan da yayi ya Bashi Kuɗi dubu darin dake cikin Aljihunsa kenan ya bashi Duka ,kokuwa ce ta kaure a tsakanin su Ganin Tana shirin Kwace kuɗin a hannunsa ta karfi da yaji, Yana Tsoron ta Amma The money was his life Bazai bar mata ba, dambe sosai Sukeyi har Suka fara yaga kudaden Duk ya mata jina jina, ya haɗa mata Jini da majina duk Yanda taso Aljanunta su tashi su tayashi chaskar sa basu tashi ba saida Ta gama wahala aikou a lokacin ya wahala Don Saida ta Rama tayi Masa jina jina sannan Ta Ƙyaleshi ta kuma tafi da Kudin, ta Bashi a zero.


*Pollokshields GLASGOW* (United Kingdom)


Tasssss yaji saukan razananniyar mari Mai tsananin firgitarwa a kuncinsa, Dr Sabo yayi Saurin dafe kuncinshi yana Kallon Kallon Alhaji Faisal A gigice

Cikin tsananin Fushi Alhaji Faisal Ya nuna shi da yatsa

"Kayi Kadan Sabo, kayi kadan Kaci Amanata ,nayi kuskure da na shigo dakai Cikin Rayuwata, Ni daya na tarwatsa Ahalin Shettima, na wargaza Family nasu na ɗaiɗaita su, Na Hana ƴaƴansu zaman Aure, na Sa an tura Aljannu Su ƙwanƙwasa ƙwaƙwalwar Ashman ,Su hanashi zaman Aure , Na riƙe Surayya a wajena na Tsawon Shekara Ashirin Da ɗaya babu wanda ya sani, Nasa Malam ya busar da Zuciyar A'isha ya kasance bata ganin Kowa sai Wani, ta karfi da yaji nake Son Soyayyarsa ta kasheta, Taya zaka Gaya min Ta haihu?, dama Baka zubar da Cikin Ba?, Na sako ka cikin wannnan Aikin ne ba dan Na gaza ba, ba dan Bazan Iya ba sai dan banshirya zuwa Nigeria Dakaina ba, ya zama Dole inyi wani abu"

Dr Sabo Ya Sunkuyar dakai

"Kayi Hakuri Boss , nayi iya ƙoƙarina na ganin Na zubar da cikin ,Amma idon Saleem da Ashman Na kan Cikin Basu ba kowa damar raɓarta ba, yanda Muke Aikin Mu a ɓoye suma haka suke bata kariyar a ɓoye bansan dalilin su na yin haka ba?, ina Tsoron Su Gano Ni Asiri na ya tonu"


"ni akwai wanda ya isa yagano shirina?, Koma waye yayi kadan, wallahi duk wanda naga zai ɓatamin shiri ko asirina zai tonu sanad'in shi to wallahi saina kawar dashi , i can die for revenge , I serve To win"

Cikin ƙuncii Alhaji Faisal ya maida hannayensa baya yana safa da marwa tsabar tashin Hankali kwance a Fuskar sa, ya tako gaban Dr Sabo yana haki

"Bazan bar Aisha ba, kasani wallahi bazanbar A'isha tahutaba, Mahaifiyar ta itace tajamata na sata cikin wannan Halin, a rayuwata babu macan danaso kamar Noory har gobe Kuma babu wacce nikeso samada ita amma ta ƙini taje ta auri wancan Gawan tabarni naji zafin hakan sosai har yanzu Kuma inajin zafin haka shiyasa bazan bar Noor taji dad'in rayuwa, Bazan Ƙyale dangin Shettima ba saina gigita rayuwarsu tasanad'in ƴaƴan da suka haifa yazama dole waccan yarinyar tamutu duk yadda Za'ayi ka wato min ƴarda Aeesh ta haifa, sannan ka kashe A'isha , Na lura wannan Yaron Ashman Shike wargaza mana Duk wani shirin Mu, hakan Yasa Na tura Munanan Aljannu Su Birkita minshi sunsa ya sake ta Amma da yike su mayu ne Sun ce ba'a hayyacinsa yake ba, Ashman baya Wasa da Addu'a Ga sallar dare da yawan Istigfari itamaa A'isha halayyar sa ta dauko shiyasa Bamu cika samun nasara akansu ba, da Ashman ya gane yanada Matsala Sai ruwan zam zam da ruwan Addu'a ya Zama Ruwan shan sa na rasa ya zanyi dashi Gashi ya toshe duk wata hanyar cuta da zanyi ma Matarsa, Ƙofa ɗaya Ya bar Mana a buɗe Inda Muka yi nasarar Cusa mata son Wanda Bai kamata ba, kuma Muke burin Son da take masa ya zama ajalinta, Amma Dan banzan yaron nan duk Hanyar da nabi sai ya wargaza ya zame mata Garkuwa, nafiso yarinyar tamutu sanadin Son Yaron nan, Sannan In kashe ƴar da ta haifa yanda zan Sake Cusa Baƙin ciki a zuciyar Noor, inaso zuciyarta ta buga cikin Ƙunci ta yanda nawa ke bugawa a ko wane second ta dalilinta, sannan barin yarinyar nan Sureey atare dasu wata barazanace ga cimma burina , Tasan Sirri na Tasan Komai akan Rayuwata ya kamata ku gaggauta dawo min Da ita, Amma kada Ku cutar da ita saboda ita din mallaki nace, mtsew"

Sai kuma yaja tsaki

"Da Kun bari yaron nan ya aureta tun farko da Duk hakan bata faruba"

Dr Sabo Ya Sunkuyar dakai Yana jin Jawabin Ogan Nasa

"Am sorry Alhaji, sorry sir, matsalar Badaga Ni bane,daga Yaron ne, muna Tsoron Muyi masa Abinda Zamuzo muna danasani '

"Ban Fahimce ka ba"

"Aareef Ɗanka ne, Mahaifiyar Sa itace Kande ƴar hutunka wacce tazo kaduna Cirani , ka sama mata masauki a gidan ka kafin Kazo UK "

Sai yayi shuru a rashi yace
_,inaganin itace dalilin da yasa ALLAH ya hanaka Noor saboda Babu Yanda za'a yi Wanda yayi zina Da ƴar mutane ya Auri Kamilalliya, koda ya Aureta Dole sai an ɓata masa Zuri'arsa Shima, Allah ya duba Innocent Soul ne yasa Ya raba ku tun wuri da yanzu Aareef shine ɗanta, Shima ya zama mazinaci Mai neman Mata, kai Mace ɗaya ka Nema Shi kam mata Sune Abincinsa, ya koma kaman Bunsuru_

Alhaji Faisal Ya koma da baya Yayi a Ruɗe, ya dafe kirji cikin kidima da gaske yana da ɗa a duniyar nan?, Ashe yanada Magajin da zai Gajeshi a duniyar nan bayan ya mutu?, A Tunaninsa in ya faɗi Ya Mutu babu mai cin gadonsa wacce take da hakkin ci kuma tayi masa nisa, Shiyasa yake shiriritar da Kudaden yana Amfani dasu wajen ganin ya Tarwatsa kan familynsu.


Washegari Salahuddeen ya hadasu Da Mahaifinsa Alhaji Abubakar Mai Zuma ya masu kwatancen wurin.

Aash da Aeesh Harda Reey da Ammie sukayi masu Rakiya Gaban malam a *Gidan Islamic Medicine ABU Congo tudun Wada zaria*

bayan Ashman ya karanto ma Mallam Matsalolin da suke fuskanta. Mallam Abubakar ya jinjina kai, yace

"Alhamdulilah, wannan labari da kuka bani akwai 'kulalliya, ko ba sihiri zamu taimaka da adduoi, balle wannan ma daga ji an san akwai Sihiri, ta iya yiwuwa Ita matarka dasa mata son wannan Yaron Akayi, Tunda tace tana Sonka kuma Zuciyarta bata wannan Bugawan sai ta ganshi, idan Ta ganshi kuma sai ta rasa natsuwarta, da Alama wani ne yake son Ya ɗauki fansa akan Ta"

Ya dubi Aeesh yace
"Ƴata..., Kin taɓa Yaudarar wani ne?"

Aeesh ta girgiza kai

"Akansa na Fara soyayya"

Malam Ya dan nisa yace

"Abu na farko ,Ina so ku sa a ranku cewa duk abunda ya samu bawa muƙaddari ne, ku kasance masu Adduoi da takaita Allah, Zanyi muku magani da yardar Allah, zan bata maganin da zai daidaita mata bugun da zuciyar ta keyi, kai kuma zaa baka maganin da zai sa Hankalin ka ya daina Gushewa a duk lokacin da ka Tuna abinda ya faru a baya"

Nan ya kawo masa Ruwan addu'a mai ɗauke da Ruwan Karatun Kurani mai girma da Addu'oin Shifa, wanda Aeesh da Aaash zasu maidashi Ruwanshansu, Allah zai tsare su daga Sharrin mai

Please Login or Register in order to submit comment