Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sauke su Batareda ya shiga ciki ba ya juya ya koma nasa Gidan inda yake ɗan hutawa.

Itama Juwayriyyyah bata Wani Jima a gidan su Aeesh ba Aeesh ta rakota Ta koma gida.

Tunda Ashman ya Gaya mata zai tafi Gida kano take jin Wani iri,Taji Gabaki ɗaya tafiyar tasa bata Kwanta mata ba, Jikinta yayi sanyi Sosai, Har Umma ta fahimci Akwai Abinda ke damunta , aranar jiki a sanyaye ta wuni har dare.

Yau kam har dare bai shigo gidan ba, har Sun Fidda ran Zaizo

Bayan An idar da sallar Isha'i suna Zaune itada Habeeb ƙaninta tana masa  Assignment ,Umma ta shigo parlorn tana cewa

"Har tara saura Sufyanu Baizo ba, kije ki ɗau Abincinki kici kuje ku Kwanta kunsan Gobe Akwai Aiki"

"Ammie Zaizo ƙila yana hanya ne"

Aeesh Ta faɗa Cikin turo baki.

"Tho Anty ki kirashi Mana"

Cewar Habeeb, Aeesh ta harare shi

"Banida numbern shi"

Wannan Furucin da tayine ya fallasa dalilin rashin Walwalarta Tunda ta dawo _(Ƙila saɓani Suka Samu a tsakanin su)_
_cewar Umma Cikin Ranta_

A fili kuma Taɓe baki tayi ta ce

"Kunfi kusa..."

Sallamarshi Ce ta dakatar da ita duk suka ɗago suna Amsa Sallamar.

"Kaga Ɗan Halak kaƙi ambato, Yanzu muke Zancen ka nace hala yau Bazaka zo bane, kasa Zata kwana da Yunwa"


"Ammie wlhy aiki ne yaso ya ɗan makarar dani"

Ammie Tace

"Ai Gani nayi yau ka jima baka shigo ba shi yasa nace taci nata abincin karta kwana da yunwa, kabi ka Sangartata abincin ma Sai ta ganka takeci"

Ashman yayi Murmushi yana shafa kanshi

"Ayyah aiko ban kyauta ba na bar Ihty da yunwa, Amin Afuwa na Samu Emergency call ne a asibiti and you know I can't Ignore it ,.....Ina wuni umma"

Yayi maganar yana durƙusawa har ƙasa Yana gaida Ammie


"Lfy lau, ya gajiya? Shine yau ko kashigo? , infact dazu Ina Ganin Shigowar Motarka Amma Ka kasa Shigowa kayi Wucewarka"

Sake Duƙar da kai yayi yace

"Wlh Umma ɗazu agajiye nadawo ne kuma nayi tunanin baki nan, yanzui ma tunanina kunriga kunyi barci ,tunda dare yayi nisa"

"Taya kake tunanin Zamuyi bacci?, jelar ka bata ganka ba?"

Tayi magana tana Kallon Aeesh da idanunta ke kansa tana kallon sa ko ƙyaftawa batayi.

Zama yayi kusa da ita, hakan Yasa Ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga .

Miƙewa Habeeb yayi yanufi hanyar Kitchen Yana faɗin

"Aunty wannan irin kallo haka? Sai kace zaki cinye shi"

Murmushi duk sukayi ,Aeesh tace

"Ahky, anyi surgery lfy ?"

Murmushi kawai yayi Batareda ya bata Amsa ba

Ammie dake Tattara Plates dinda ta Gama dinner Dasu tace

"Sufyan Ashe Gobe zaka gida ko kuma gaya mana? ,Ai ko ƴar daddawar Nan na baka Ka ba Uwata Goggo"

Shiru yayi yana Murmushi don dama yasan arina Aeesh ta riga ta gaya mata .

"Umma kiyi haƙuri tafiyar Gaggawa ce ta zo Mn nima ban shirya Masa ba,Kuma ae ko yanzu bata ɓaci ba In Akwai daddawar Sai ki bani na bata"

Murmushi sosai tayi

"Aikam akwai Daddawanni ma kala kala In zaka Tafi kamin magana in haɗa maka da Citta harda Kanumfari nasan tana so "

"To umma"

"Yaya tare zaku da Anty?"

Inji Habeeb lokacin yake jera msu Abincin su saman carpet

"Nope"

Ya bashi Amsa a Takaice yana karɓar Plates din a hannunsa, ya ƙosa yaji abincin a cikinsa, don Wani irin yunwa ya kwaso.

Hawaye ne suka gangaro a idon Aeesh tayi saurin taresu da bayan hannunta gudun karsu gani ,Amma inaa ta makaro tuni Duk suka Ganota.

Miƙewa Umma tayi da kwanuka a hannunta,ta kai kitchen daga nan Tayi ɗakinta tana musu sai da safe.

Habeeb ya dubesu cikin nazari yace

"Yaya Na lura kaida Aunty ɗayanku bazai iya Rayuwa Batareda ɗayan Ba”

Saida Ashman ya wanke hannunshi da Ruwa, Ya buɗe ledar Tsaftacen Tuwon Shinkafan Dake gabansa sannan yace

"Me yasa kace haka?"

Habeeb ya Gyara zama yace

"Yaya Aash kaida ita Tare kuke komai tun tasowar ku,Alaƙar dake tsakanin ku tayi ƙarfinda bazamu iya Alaƙanta shi da Alakar yaya da Kanwa ba, zaku fi dacewa da juna a matsayin MATA DA MIJI ,Bazan manta ranar da ta dawo Gidan nan Ba Ammie Da yaya Sadeeq Sunyi Sunyi taci abinci Taƙi ci wae Sai kazo, kamar da wasa ranar kwana tayi taƙi cin komai sai kuka ,Kai kuma kamar kasan komai Da sanyin sassafe kayi Mana dirar Mikiya, Ranar Naga Abin Mamaki Naga tsantsar Shaƙuw......."

"Kai dallah rufe mana baki...."

Aeesh tayi Saurin Dakatar dashi

"Yen yen yen yen ,Surutu babu Comma babu Full Stop .....!, Abege carry ur books and Go to bed"

"Ikhty ..."

Ashman ya kirata Cikin Sanyin Murya yana kai sauke hannunshi daga Abincin da yake ci.

"Na'am yaya na"

Itama ta amsa Cikin Sanyin Murya.

Duban cikin Idanunta yayi, yana Shakkar faɗan abinda ke zuciyar sa a hankali yace

“ZAKI AURENI....?”



"In Aureka inyi ya da Sadauki Na?”

Ta faɗa innocently tana Kai Hannu cikin Kwanon Tuwon.

Bude idanunshi yayi ya kalleta Batareda ya iya cewa komai ba, chanza maganar yayi da Cewa

"Am hungry let's eat”

Habeeb ya taɓe baki, ya kwashe littafan sa ya nufi ɗakinsa yana musu saida safe..


Abincin sukeci amma kanta a ƙasa Duk yadda yaso su hada ido taƙi yarda, Yayi Expecting Fiye da haka daga Gare ta, Wannan Shine karo na Farko a rayuwarta da zaiyi tafiya har na Tsawon kwanaki Biyar Batareda ta bishi ba , Dole taji wani iri , ya saban mata da Hakan Basua iya Kwanaki biyu basuga juna ba duk uzurin da wanin su keda shi

Tare Suke Abubuwa da dama tare suke Cin Abinci a kwano ɗaya, idan ta kama ba yadda zasu yi Sai dai Su ci tare ta Video Call,suna ci suna kallon juna Shaƙuwar dake tsakanin su ya Samo asali ne tun Sanda Mahaifinta ya Rasu ta dawo Hannun Mahaifinsa da zama lokacin da Gabaki ɗaya ahalin Gidan Suka tsaneta Basu ƙaunar Ganinta a lokacin ya ɗauketa ya maidata tamkar ɗiyarsa wacce ya haifa ta cikinsa babu Abinda ya isa ya taɓa ta babu Abinda ya isa ya Rabata dashi, shi yake mata komai kama daga Wanka wanki shike Kaita makaranta ya dawo da ita yay mata girki Suci tare , har lkcn da takai matakin SS2 a Secondary School ya koya mata Yin Wasu Abubuwa Dakanta Irinsu Wanki da Shara,Amma bai koya mata girki ba Gudun kar Tayi kasada ta Ƙone ko don wata rana,Tana kammala karatun ta Secondary dakansa ya samar mata da Gurbin karatu A KASU inda take Karantar BNSC NURSING a lokacin yana Shekararsa ta Ƙarshe na masters ɗinsa a Jami'ar Bayero Ta Kano inda shima yake karantar MS(master of surgery) dinshi bayan ya kammala MD (Doctor of medicine) ,Yanzu yana aiki a asibitin da Mahaifinsa ya bar masa inda yake aiki a matsayin MSSDoctor , a halin yanzu Aeesh tana Shekarta Na ƙarshe a jami'ar strike ɗinda ASSU Suka je ne yasa take Zuwa Asibitin yayan nata dan Ƙarin Experience ,Dama chan tana zuwa Voluntary in ta samu Time.

Tuttura Abincin taitayi har saida taci rabi sannan ta ture plate din tana goge bakinta da tissue.

Kamo hannunta guda yayi ganin tana niyyar tashi hakan yasa ta fasa tashin Saidai ko dagowa batayiba.

"Ikhty Fushi kikeyi da Yayanki?"

Shiru tayi kanta Kasa

"Am so sorry , banyi hakan don na ɓata miki Rai ba ,nima banida choice I have to go Alone...."

Har yanzu shiru tayi batace komai ba kuma bata dagoba.

"Ikhty idan da inada yadda zanyi nima Tun farko da Ban shirya tafiyar nan ba Amma a halin yanzu tafiyar was my last hope"

Ɗagowa tayi idanunta na tara ruwa ,Murya na rawa tace

"Kasan I couldn't stay back without you for 5hrs, And u want to Go for 5days"

Matsowa Yayi gab da ita ya matse Hannunta  cikin nasa, cikin Wani irin Muryar da shi kansa baisan Yanada itaba yace

"Na daɗe banje Gida ba Tun sanda Kuka Samu saɓani da Su zainab ,And....Akwai Abubuwa masu muhimmanci da zanyi a Chan I missed home, didn't u care about my feelings  More than 7Mounths Without Setting my Eyes On my fam Just because of u?"

Yafada Cikin wani irin ɓoyayyen lamarin dayake dannewa yaqi dannuwa.

Kallonshi take idanunta na cigaba da kawo ruwa don tunda take beta6a yimata maganaba cikin wannan yanayin ba ,Tausayinsu ne ya kamata ~Masana Sunce Idan Mutun na Shaye Shaye yakan Sha matukar wahala kafin ya rabu dashi, ita nata ƙaddarar ba ta Shaye Shaye bace, Shaƙuwar Da tayi da yayan nata ne yasa take Ganin kaman Rabuwa dashi na ɗan wani lkc zai Iya Zama Barazana Ga rayuwarta~

Hannayen ta dake cikin nasa ya Matse a hankali wanda hakan yaba hawayen da suka taru a idanunta daman Digiwa Saman Hannunsa.

"You care about them but they hate u, Basua ƙaunarka ko kaɗan"

"I know but what about my siblings"

Shuru tayi ta sadda kai Hawaye na cigaba da ɓulɓulowa daga Kwarmin idanunta .

"Ammma In ka tafi we need to be in touch"

Tafada cikin cracking voice

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take ƙoƙarin taro hawayen dasuka cika idanunta ta Dakatar dasu daga zubowa.

Yasan yadda takeji, she's in pain, kallo daya zaka mata kagane ,Kukan da take Daga Zuciyarta take tahowa direct.

Cikin kwantar da murya wanda yafi kama da rad'a yaja kumatunta yace

"Sure Girly"

Hawayen datake dannewa ne suka kufcemata suka gangaro kan kumatunta.

Ji take kamar idan Ya tafi bazai dawo ba, ji take kamar tafiyar da zaiyi itace silar da zata Rabata dashi har Abadah.

Dagowa tayi ahankali ta kalleshi da rinnanun idanunta dake sheƙin hawaye, zuciyarta na zafi.

Shima kallonta yake yanajin kowanne digar hawayenta har cikin zuciyarshi, idanunshi suka fara chanza kala yanajin kamar shima yafara zubda nashi hawayen, Ko kuma ya fasa tafiyar Gabaki ɗaya.

"Ƙarfe nawa zaka tafi Goben"

"May be 9:00 na safiya"

Lumshe idanu tayi taba hawayen dasuka cika idanunta damar gangarowa sannan tabude ta kalli Agogon dake manne a parlon 9:25.

"Kenan Saura  12hrs ka tafi Please Stay with me All these while”

Murza hannunta yayi ahankali yana jin shesheqanta harcikin ranshi,  yasa hannu yashafo kumatunta da ya gama Jiƙewa da leman hawaye, Ya share mata Sannan yaja hancinta cikin  wani Irin murmushin sa Na musamman yace

“Sure Baby”

"Idan Zan dawo zan taho mki da jirgi da Mota da komai dakomai ,Zakiyi ta wasa dasu har sai kin gaji, ....kuma daga wannan lokacin bazan ƙara barinki ba, Zan dawo na zauna ko yaushe muna tare dake har Randa kika Zama cikakkiyar matar aure gun  Sadauki a ranar kinci ado Sai Ƙamshi na Musamman kike Zubawa Hannayenki Sunsha Zanen lalle Fuskar nan taki na Fidda Annuri da haske na musamman A ranar Darajarki ta Ninku Akan nada,Ranar da Zan damƙawa sadauki Amanarki in zaunar dake in Miki nasihar zaman Haƙuri a Gidan Aure daga Ƙarshe in ɗora da Addu'ar Allah ya dawwamar daku Cikin Inuwa ɗaya Har Abada ......"

Kanta ta ɗora bisa kafaɗarsa kawai tayi tana Murmushi.

Sosai take jin daɗin kalamansa Hakan yasa taita kaɗa kai tana murmushi .

Ahaka ya cigaba da Kwantar mata da hankali da daɗaɗan kalamansa had barci  ya dauketa, Bata farkaba sai four shima Umma ce ta tadata tayi Sallah,lokacin ya tafi masallaci.

Ƙarfe Shida saura ya dawo ,Watsa ruwa yayi a bandakin daki Yaa Saleem sannan yafito.

Lkcn har Umma ta shirya masu Abin karyawa, Sama sama Suka tsakura don Gabaki ɗaya su yau a Sanyaye suka farka.

Saida Ya kimtsa Sannan ya bar Gidan tareda Rakiyar Ƙanwar tasa da ƙaninta Habeeb Bayan Umma ta bada saƙo a ba Goggo.

Ranar Da ƙyar ta iya Shiryawa taje Asibiti , a Ranar kuwa Ba iya na kusa da ita ba Hatta majinyatan da take kula dasu Suma sun fahimci Akwai damuwa a tattare da ita .

Ƙarfe Goma sha biyu na Rana Ashman ya sauka Garin Kano, kai tsaye bai nufi nasu gidan ba ,Zarce wa Gidan Abokinsa Bilaal yayi kusan nace nan ya wuni suna tattaunawa Don rabon da su haɗu kusan 7 months kenan, ko kaɗan bai Bari kewan Aeesh Ya hana shi walwala ba ,Hasali ma tattara Duk wani abin da ya shafe ta yayi ya ajiye a gefe ,Tsakanin Tahowansa izuwa yanzu sunyi Waya ya kai sau Goma.

Sai Dare ya baro Gidan Ya nufi Gidan Gonar Abbban sa nan ya kwana, Sosai yake tsoron tunkarar Gidan Mahaifin nasa Bai san me zai taras a chan ba ,idan ya tuna yanda Suka Rabu lokacin Zuwansa na ƙarshe sai yaji kamar ya kama hanya ya koma inda ya fito(kd) ,Amma duk da haka babu yanda ya iya dole ya daure ya shiga Gidan Gobe ,ya jure Duk Abinda zai faru dashi.

*kaduna*

Washe Gari bata wani damun kanta wajen shirin Asibiti ba, don bazata jeba, wanka kawai tayi ta kimtsa kanta sannan tahau danne danne a wayanta.

Haryanzu fuskarta a cunkushe yake don haryanzu bata bar kewan yayan nata ba.

data ta kunna tahau WhatsApp

Kamar jira ake saiga message din Reey na "Kehh.....!".

'Mayyar chatting' tafada cikin zuciyarta sannan itama ta tura mata

" hyy"

"Ke banza Gani Hanyar Gidan ku Ki shirya Mu tafi Asibiti, Akwai drama"

"Manafuka A hanyar Gidan namu Kike Chat?"

"Ke banza Faɗa ake yi Tsakanin Dr Dan da Sister Ushey"

Dirowa tayi daga kan Gadon da take zaune ta waro manyan Idanunta kamar tana Gabanta hannunta har Ɓari yake wajen typa

"Da gaske?"

Aikam kaman Jira Take tayi mata Reply

"Wlh serious, Nima ban Riga naje ba Hajara ce ta Kirani ta koramin"

"Okay Gani nan ....Gani nan "

"Be fast Please"

"Babe Uniform ne jikinki ko Scrub?"

Sticker din dariya Reey ta turamata sannan ta rubuta

"Pink Scrub na Saka, Hala Ko wanka bakiyi ba"

Sticker din kallon kin ma rainani ta turamata sannan ta tura

"Ke nake jira kizo ki wanke Ni"

Sauka tayi ta kashe datarta sannan ta miƙe da azama ta shige banɗaki Wanka tayi sharp Sharp ta fito, ta sanya  Pink Scrub ɗin ta wanda yasha Guga, Ƙaramar farar Hijab ɗinta ta Saka ta ɗauko Baƙar After Dress ɗinta ta ɗora akan Scrub ɗin ,baƙar Canvas ɗinta Mara nauyi .

Masha Allah tayi kyau sosai musanmman data Saka farar Medicated shade a idanu mai taken High Index Lenses.

saukowa tayi ahankali, a Store ta ga Umma tana Jera Kayan Abincin da Zubairu Ya Kawo msu, kallo ɗaya tayi mata ya dauke kai.

Murmushi tayi taqaraso wajenta tana cire glass din idonta.

"Umma na , Na samu Emergency Call a Asibiti na tafi"

Harararta Umma Tayi

"Tunda ga Likita ba"

"Oho dai ni Na tafi "

Tana Fadar haka Ta maida farar tabarau ɗinta,Sannan tayi waje da sauri.

Binta da kallo Umma tayi  ta Girgiza kai .  _Aisha Kenan Sarkin Shirme_

Fitowar ta yayi daidai da isowar Reey a Napep.

Leƙowa tayi Tana harararta bayan Napep din ya Tsaya , Murmushi Aeesh tayi Ta ƙarasa Ta hau, me adaidaita Ya jasu suka wuce.

Suna hanya saiga kiran Ashman ya shigo ta whatsapp video call dannawa tayi tare da d'auka Tana Sakin Wani ƙayataccen Murmushi.

Daga shi sai jallabiya yana Zaune a Cikin Motar sa ,Ya Gama shiryawan sa na zuwa Gida amma ya kasa tada Motar yanzu haka ma kiranta yayi Don tayi Motivating ɗinshi , ko zai Samu Ƙwarin Gwiwa daga Gare ta.

Aash yana ganin fuskanta ya saki murmushi tare da fad'in

"Inye Sister Nurse kin Sauya Ra'ayine?"

Itama murmushin ta saki tare da fad'in

"Tausayin Patients Ɗinka naji,Nasan they can't do without Me”

Murmushi kawai yayi, sannan yace

"Kicewa Juwairiyyah in ba hello Akwai Hi "

Dariya ta saki tare da Kara wayar saitin Fuskar Reey da ta kauda Kai tana haɗe rai

"Ka ganta She doesn't miss u"

"Ayyah har Yanzu Bata huce ba?, Give the phone to her"

"No Ahky,We doesn't Deserve people Who care less about us, Forget her Abege We can still Do without her"

Yanda tayi maganan cikin shagwaba yasa shi yin murmushi Sosai, Daidai lokacin Mai adaidaita ta iso ƙofar Asibiti.

Saukowa Reey tayi ta Sallame shi,Itama Cikin sauri ta fara yunkurin Fita,Cikin rashin Sa'a Ta taka Kimonon Jikinta,Wayarta ta Suɓuce zata Faɗi, ƙara ta saki da ƙarfi wanda Yasa Ashman dake kallonta Ya toshe Kunnensa da ƙarfi.

Kamar daga Sama ta ga an taro wayar kafin ta kaiga faɗuwa Ƙasa.

Wani irin Relaxation breath ta Saki Tareda faɗin Alhamdulillah.

Hannu takai Zata karɓi wayar tareda faɗin

"Thank y...." cak maganarta ta tsaya da wani Ƙamshin Turarensa ya bugi hancinta.

Saurin dagowa ta yi cikin rashin gasgata da mammaki bayyananne.

yankewa gabanta yayi yafadi ganin shi dinne tsaye a Gabanta Riƙeda Wayarta a hannunshi ya zubamata piercing eyes ɗin shi.

Mutuwar tsaye tayi tana kallonshi idanunta adan ware alamun mammaki qarara a fuskarta.

Meyasa Take yawan Ganinshi a Inda bata zata ba?, meyasa Zuciyarta take yawan bugawa a duk Lokacin da Ta Gansa?, meyasa Take kasa Janye idanunta daga Kallonsa a duk lokacin da ta Gansa?, Meyasa take jinta a cikin wani irin Yanayi mara misaltuwa a duk Lokacin da ta Ganshi?,Gashi Ita ko ko sunansa Bata Sani ba, A duk lokacin da suka haɗu Kalaman Soyayya yake zuba mata yay tafiyarsa, ita kuma a duk lkcn da taji yana Wa'ennan zantuttukan Kasa yunƙurin komai yake,Shiyasa bata taɓa furta masa wata kalma ba,All she knows is SHE LOVES HIM.

Binshi tayi da kallo daga sama har qasa Zuciyar ta na Tsere.

Sanye yake cikin qananun kaya, tsadadden jeans trouser da top NAVY blue mai Gajeren hannu, kansa babu hula Sai sheƙi yakeyi,Yar sumar kanshi a kwance luff sai qyalli take, kullum qara mata kyau kwarjini da haiba yakeyi.

kallonshi take tana jin wani irin shauqin da bata ta6a jiba na dibarta yayinda qaunarsa ke qara hauhawa acikin birnin zuciyarta.

Jitake kamar ya ta Goyashi tayta zagaye Duniya dashi tana Shaida msu Irin Tsananin ƙaunar da takeyi masa.

Shi yafara janye idanunsa akanta yana Smiling sanadin Ganin Dr Ashman da Yayi a fuskar Wayarta .

"Sorry.."

Ya furta Cikin Sanyin Murya tare da Mika mata wayar.

Karɓa tayi Cikin mutuwan Jiki, Cikin ƙanƙanin lokaci Ganinsa yasa ta mance da wayar da suke yi Yaya Ashman, In har Zata dinga Ganinshi a ko wane lokaci tho babu Shakka zata iya Manta da kowa ya zamana Sai an Tuna Mata Kowa Zata gane kowa...

Shi kansa Ashman Zuba ido Yayi yana jiran Abinda zai faru Next,Don Shi kansa Ya Shiga Tunani Ganin irin Yanayin da Ƙanwar tasa ta shiga daga bayyanar Bawan Allahn Nan..........






*NIMA JIRA NAKE NAJI ME ZAI FARU?*

*WANE NE SHI?*

*MEKE TSAKANIN AASH DA AEESH?*
_*SHAKUWA CE?*_
KO
*SOYAYYA CE?*

DROP UR COMMENTS 😉

THANKS 💙💙💙

MAY 2ND💙💙

EID MUBARAK 💙



[7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:


*003*

Daga cikin wayan Ashman ya zuba masu ido yana kallon ikon Allah, mamaki ya kamashi ganin irin rudewan da Aeesh tayi daga Ganin Wannan bawan Allahn.

Cikin takaici Reey ta Fizgota suka shige asibiti,tana huci.

Shiru Aareef yayi yana kallon bayan su har suka ɓace masa da gani batareda ya iya cewa komaiba don yadda zuciyarshi ke gudu.

Me yarinyar chan take nufi?, Meyasa bata Ƙaunar Ganinsa Kusada ƙawarta?, meyasa ta tsaneshi haka?, me yayi mata? ,yau Akalla 2months kenan yana Bibiyarta Amma da Yayi Yunƙurin Bayyana mata Abinda ke zuciyarsa Sai Ƙawarta Ta ɓata komai.

Wani gauron ajiyar zuciya yasaki ya fesar da iska daga bakinsshi murmushin takaici ya bayyana akan fuskarshi.

"Don't worry Dude I Know How you Feels ,Indai Aeesha ce kasa a ranka kamar ka sameta”

Saurin Juyawa yayi Yana duban me maganar ,Kallon Sama da ƙasa yayi masa Sanye yake Cikin Baƙaken Suits Kafaɗarsa Rataye da Labcoat idanunsa Sanye Cikin fararen Glasses da Alama Shima Likita ne Kuma ma'aikacin Asibitin.

"Kai Kuma waye kai?"

Aareef ya faɗa yana Ƙare Masa Kallo Cikin Rashin Fahimta.

"Sanin koni waye Bashi ne yafi Mahimmanci a halin yanzu ba, Abu mafi muhimmanci Shine yanda Zaka Samu Zuciyar Abar harin taka"

"And Waya gaya maka harinta nakeyi?, Ƙaunarta nake Kuma Aurenta Zanyi"

"What Ever I can help you"

Wata ƴar dariya Aareef yayi yace

"I have been trying For almost two months Ban Samu ta furta mn koda Sunanta ba taya kake tunanin zaka iya karkato mn Da ita cikin Sauƙi?"

Dafe jafaɗarsa Dr Sabo bako yayi

"Nasan Eesh More than yanda nasan Yunwar Ciki na ,Ko Rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Eash tana Matuƙar ƙaunar ka,Duba da Irin Kallon da Naga tana maka ,Naga Tsantsar Soyayyarka a Cikin Ƙwayar idonta ,Don na jima ina kallon ku , akwai dai abinda ya hanata Bayyana Maka ne ,Amma inshallah Nayi maka Alƙawari idan Ka bani haɗin kai Yau Yau ɗinnan kafin faɗuwar Rana Sai A'isha ta furta maka Kalmar Tana Sonaka Ni nayi maka Alƙawarin haka"

'yar Gajeruwar tsaki Aareef yaja

"HOW did you Expect me to trust You kaida ko Sanin ka banyi ba, haka Akeyi daga kaga Ta kalleni Shikenan hakan ya nuna tana so na kenan?, mtswwwww Aikin banza I wonder taya Ka samu Courage ɗin Tunkarata da wannan Maganar Sefff Aftetall I don't even know You"

Ya faɗa Yana Ƙoƙarin Barin wajen

"Nima zan taimaka maka wajen Shawo maka kanta”

Cewar Wata doguwar Nurse Mai Sanye da Blue Scrub.

Kafin Ya Ida Waigawa yaga Mai magana Yaji wata Muryar ta bayan sa.

"Ni kuma Zan Taimaka maka wajen Mallake Gabaki ɗaya Zuciyarta"

Nan ma Waigawa yayi,Amma kafin ya ida Waigawa har ya sake Jiyo wani Sabon Muryar ta gefen sa.

"Ni Bazan Ɗaukar maka Alƙawari ba,Amma Ga Card ɗin ta ka fara Gwada sa'ar ka dashi"

Da kallo ya bisu ɗaya bayan ɗaya yana Nazarin Kowanne A cikin Su , Dukkannin su Sanye Cikin Uniform da Alama Abokan Aikinta ne,Amma saidai Abin da ya lura daga Gare su shine Ba don Allah Kowanne su keson Ya haɗa Ta dashi ba, da akwai Wata ɓoyayyiyar Kudirin su Wanda inba tsaga zuciyarsu yayi ba bazai taɓa gane Kudurin ba,Kuma Gabaki ɗaya su Fuskokin su ya kasa ɓoye irin Wutar Ɗaukar fansar dake Ruruwa a Cikin zukatan su.

Shi dai koma dai menene Don Allah yake Sonta Inma Manufarsu Ba mai kyau bace Su suka Sani Aniyar kowa ta bishi.

Katin Da Ta ƙarshen Ke miƙa masa ya ƙarɓa yayi gaba Batareda ya tanka wa kowannen su ba.

Murmushi Dr Sabo yayi a Fili ya Furta

_Mission Completed!, Alhaji Khamis dakai da Ashman 0-0_

Ita Kuma Sister Rabi,wacce tazo bayan Dr Sabo Tace

_Finally Lokacin Rabuwan su yayi_

Sister Khadeey ta ukun kuma cewa tayi

_Ni kuma Lokacin da zan Mallaki Rabin Raina Yayi, Lokaci yayi da Za'a Saka Mana Ranar Auren mu, Burina ya kusa Cika_

Ta Ƙarshen Kuwa dariya tayi Sosai tace

_Ni kuma lokaci yayi Da zan Cika nawa burin da burukan mutane Uku_

Gabaki ɗaya su juyowa suka yi Suna dubanta.

Ɗage msu Gira tayi Cikin Wayancewa ta basar tace

"Dukkan Mu mu huɗu,Mun haɗu akan Abu Guda Wato Auren Aeesh da Wannan Ɗan talakar, me zai hana Mu haɗa Kai Mu zama Team,In yaso Idan burukan mu Sun Cika Mu watse mu koma hatters kamar D....."

"Hey Ga Matron Chan ....."

Cewar Sister Khadeey bayan Ta hango tahowar Matron Ɗin Asibitin ta karyo Kwana.

Da Gudu Duk suka watse Ko wannensu ya shige Asibitin.

Ko kaɗan Aeesh bataji daɗin Kawar da Ita da Juwee tayi Ba Amma Ta kuduri Aniyar Ci mata mutunci in sun Koma Gida Don A halin yanzu babu halin Ramawa Tun da sun Shigo Asibiti.

Suna Shigowa Direct Female ward Suka Nufa Inda Suke tabbata Zaton Nan ne Ake Faɗar Aikuwa da isarsu Suka tarar ana tada jijiyar wuya Ana ba hammata iska tareda 'yar Jifa da Manyan kalamai Masu Tsauri Dr Daniel harda tuɓe Labcoat da jacket Wai zai Zane Sister Ushey.

Samun wuri Sukayi Suka zauna Suna kallon ikon Allah, Yayinda Mafi akasarin Patients ɗin suka hau IG LIVE suka fara haska su, da yake Asibitin Private ne Kuma Sananne wanda ake jidashi a Cikin Garin kaduna Majinyatan Asibitin Sai ƴaƴan wane da wane .

Juyowan da Dr Daniel Zaiyi Sukayi six Eyes da Aeesh da Reey, Aikam take yasha Jinin Jikinsa yaja baya yana Turo baki, Batareda yace komai ba ya ɗau Labcoat ɗin shi da Jacket Yayi hanyar waje.

"Dr Daaan...."

Aeesh ta kirashi, Juyowa Yayi a hankali Ya kalleta, da baki tayi masa Alama da Patients ɗin da suka shagala wajen haska shi a IGLive.

Ya Waro Ƙwalaƙwalan Idanunsa Ya Jefesu Da lap Coat ɗinshi a ƙoƙarinsa na kwaɓar su daga Daukan da suke masa, Dariya Suka fashe masa Dashi Aikam da Gudunsa ya bar Wurin da ƴar Guntun kunyar sa.

Su kansu Aeesh Da Juwee harda Usheey Dariya sosai ya Basu Hakan yasa Suka shiga darawa.

Banko Ƙofar Da Akayi ne yasasu Saurin Waigawa da hanzari,Matron Wusshe CE ta Shigo Sai huci take.

"Students A'isha And Juwairiyyah Sadeek imaam Where're You "

DDumm gabansu yafadi dajin irin kiran da Matron Keyi msu dagaji babu Lafiya.

_Innalillahi wa'innailayhirraji'un_

Suka Furta a Tare Suna shigewa Nurses Station Gudun karta dizga su a gaban Patients.

Har Nurses Station ɗin tabisu tana ta kumfar baki.

"Inba Rashin rashin Hankali da Rashin Ethics ba Taya Morning Duty nurse zata Dinga Zuwa A irin wannan lokacin?, check the time 11:30Am fa?, wannan Wane irin Sakarci da toshewar kai ne?, As a Student Nurses kune ya kamata Ku zo By 7:00am Kafin Incharge da Morning Nurse suzo Ku Amshi Dutyn mai night, Ta haka ne kawai zaku iya

Please Login or Register in order to submit comment