Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

look alike, da zakiga hoton a guje zaki yadda Dani".

"Haba Surayyyah Bana Son Irin Wannan Wasan Please I like Love Stories please Go ahead to the point"

Ta Fada cikin zumudi

"Aisha Am not kidding , Wlhy Ammie ba Kanwar Daddyn Yaa Maan bane, Cousin din Daddy ne"


"So How comes Kuma Taya kika Sani?"


Sureey ta sake Gyara zama

"Daddy na Alhaji Faisal asalin Yan kurah ne, ban Sani ba but Yanda ya bani Labari he mean bashida Kowa sai Parents ɗinshi, his parents Irin fulanin Nan Matafiya So bayan sun Baro Kauyen su tareda mahaifansa da Kanwar mahaifin Shi Watoh Aisha suka sauka a kd, a kd Suka Cigaba da Rayuwa har Allah ya Karbi ransu, Bayan Rasuwar Parents ɗinshin (Faisal)) mum aisha ita ta zame Masa Kaman Uwa, Ana nan Ana nan Aishan tayi Aure Ta auri wni attajiri Proff Salman Kurah ya Rage shi ɗaya Tal a gidan Da Mahaifansa suka bari, a first-year ɗinsu Suka haifi Ammie a asibitin Kawo dake Nan KADUNA, Bayan an sallamesu, Suna Hanyar dawowa daga Asibiti Sukayi accident Allah ya Karbi Rayuwar Su, cikin Ikon Allah, sai Allah ya kaddara Ammie nada Sauran Shan Ruwa a Gaba, Bayan an kaisu asibiti aka Gane jaririyar nada Rai Bata Mutu ba , Nan Danan Aka Bata taimakon Gaggawa akayi admitting ɗinta, Sannan Kuma akayiwa gawawwakin iyayenta sutura Aka kaisu makwancinsu, Daddy (Faisal) yaji mutuwan Su sosai, Tunda Iyayensa Suka rasu bai Taɓa kukan Maraici ba sai Da ya rasa Wacce Yake Gani a matsayin Dangi a gareshi, ya dau babyn da suka Haifa Watoh (Ammie) ya rasa Ina zai kaita a Lokacin da ya tabbatar Bashida Kowa a duniyar Nan Kuma at Early Age dinsa baisan Ina zaije ba, baisan Ina zai Fara rainon kansa da baby ba,Don lokacin Bai wuce Dan shekaru Goma ba, Faisal biasan dagin Salman (mahaifin Ammie) Ba, Balle yayi tunanin zai Kai musu jaririyar, Haka Ya cigaba da rainonta Cikin wahala Ba don Rashin kudi ba ko Kayan Abinci no, sai dai he's too young to take care of the kid and Yaƙi yarda ya badata ga makota ,tun Yana karami Ya kasance Mai Wayon Tsiya, Baya yarda a cuceshi, shiyasa Ya iya rike gidan Shi daya ya Kuma san dabaran da yayi Ya siyo Baby supplement Yana Bata, da kansa ya Zaɓa mata Suna NOOR Yana Kiranta da NOORY Watoh haske na, You know ko ke da Kike mace kika Sha wahalar daukan Ciki da haihuwa kinsan Rainon Baby ba karamin Abu bane a kwana na biyu ya fara Sarewa, Ranar sai Kuka takeyi Babu Irin rarrashin da baiyi Mata ba, taki yin shuru, haka ya fito da ita waje yanata faman Jijjigata Duk dauriyansa a Wannan Ranar saida yayi Kuka ,kukan Tausayin kansu da Halin Maraicin da suke ciki ,Kaman Daga sama, Saiga Wata katuwar mota tayi parking a gabanshi, Goggo da mijinta Alhj Ahmad suka fito cikin Tausayawa Goggo Ta Karbi Baby ta fara Jijjigata, Abin mamaki sai gashi tayi shuru, Tambayan sa tayi Ina Iyayensa?, Cikin Kuka Yace sun rasu, Basuda Kowa, cikeda Tausayawa Goggo tace Idan ya yarda zasuje police station su sa hannu su dawo wajenta,Ta Cigaba da renonsu, Babu musu Ya Amince Don A Lokaci ɗaya Yaji ta Shiga Ranshi, nan Take Akaje police station aka cika Takardu under Shari'a aka Kawo shaidu Daga nan NOOR ta dawo hannunsu,Don
Faisal kin yarda yayi ya koma wajensu, Shi Kadai y Koma Kwana a gidan Iyayensa kullum Sai yazo sunyi Wasa da Da Abbanki da Abban Su Yaa Maan Saboda Sune mate ɗinshi a Gidan, Kasancewar Daddyna Akwai zuciya ,kafiya , Rike abu a rai da Surin Fushi Shiyasa Basua shiri da Abban Yaa Maan Saboda kusan hallayyan Su daya ne, Akwai wata Fada da ya Taba Hadasu On Daddy's Birthday, Sukayi kaca kaca cake dinda Granny Ahmad Shettimah ya siya masa ma watsa watsa Suka masa, Tun daga ranar Bai sake takowa Gidan ba, Suna Haduwa a hanya Kowa ya bangaje kowa Duk Su Wuce Babu mai tankawa wani, Haka iyayen Har gajiya Sukayi da Nasiha Amma sun ki komawa yanda Suke ada, a Haka har Noor ta Shiga makaranta , Shima sai a Lokacin ya Shiga school Don ya rinƙa ganinta kullum yasa aka sasu aji ɗaya,dukda girmansa a Lokacin Bai damu ba, tare suke karatu a makaranta in an Tashi ta biyoshi gidansa su tafi Islamiyyah a tare sai da yamma take dawowa gida Wani Irin Shakuwa ta Musamman Ta Kullu a tsakanin su, Faisal Bai yarda da babu ba, bai yarda ya jira a bashi ba, Zafin nemanshi Shi ke sa masa Abinci akan Table, Sannan koda ya kasance Su Goggo na iya kokarin Su Wajen kyautata masa, bai yarda ya zauna babu Sana'a ba, at his young age shi yake ciyar da kansa Yake Kuma taimakawa Kanwarsa da wasu Abubuwan Irinsu suturun Sallah, In takaice Miki Har yakai ya Kawo ya dauke mata Nauyin Karatun ta Gaba ɗaya, a Lokacin da suka Gama Secondary school ya nemi a Maida masa da Kanwarsa, Sai Alhj Shettimah Yace Gaskiya bai kamata ya dauketa daga garesu ba, Saboda bata da masaniya akan waccece ita Kuma Hakan Zai iya samar da matsala babba, Sai Yace Tho a aura masu ita mana Tunda yana sonta tana sonshi?, Sai sukace A'a Gaskiya sai ya Gama Makaranta, Koda Ya Gama Makaranta ya zo masu da zancen Cewa Sukayi Bashida Aiki ya fara neman na kanshi,ya nemi Kudaden da Zai Iya kula da ita da kanshi"


Sureey Ta dakata wasu Hawaye Suka zubo a saman Fuskar Ta, jikin Aeesh yayi La'asar Kallonta take idanunta suka kawo ruwa don tunda take beta6a jin magana mai Sanyaya Jiki irin wannan ba.

Cikin Kuka sosai Sureey Ta Cigaba

"He went through a lot har barin ƙasar yayi ,Don ya Zama billionaire and ya Zama, A Lokacin da ya dawo Nigeria sai ya tarar ana Bikin Sunan mu, by means Ammie tayi Aure har ta haifi Yaa Sadeeq Mune Second borns dinta, sunci amanar Sa Sun Aurawa dansu Ammie ,a ranar Sunyi Kuka Shida Ita, Baisan tana sonsa ba sai a ranar a ranar Tayi nadama Mara Amfani don Daddy ya riga ya Zuciya, Anan Take yasa aka Sato Masa ni ya bar kasar Dani dan ya Huce takaicinsa akaina sabd Sunfi karfinshi Ta ko Ina,suna da iko A hukumance, Ga kudi da Hadin kan dangi.

Tunda Daddy ya daukoni bai Taɓa Cin zalina ba, hasalima Kula dani Yake Kaman Kwai, Bai yarda Kuda ya Raɓeni ba, ya zame min Uwa ya zame min Uba, Ga Uban Jami'an Tsaron dake gadina Ta Ko Ina, Ko Wanka zanyi Akwai Masu Kula dani Abinci ma akwai masu Bani a Baki, Ban San komai ba face gata, hakan yasa na Taso a sangarce Ga Tsiwan Tsiya da rashin Kunya, duk girman Mutum In Bai min Ba Sai na taboshi Saboda nasan Akwai Mai Tsaya Min, Hakan Yasa nayi Bakin Jini a Wajen Mutanen Da nake tarayya dasu, Ban Damu ba, All I want Was My daddy love, Ina Secondary school na hadu da Babyna (Zeeyk) photographer, Ranar Graduation dinmu yazo ya yima Seniors dinmu Grad Pics...."


Sai tayi shuru tana Hararo Lokacin, Murmushi Mai dauke da Hawaye ya Subuce Mata

"A Kallon farko naji Na kamu dan Son Bawan Allahn nan, Ya Shiga Zuciyata a Lokaci ɗaya, He's handsome ,Unique and Jovial Bashida Damuwa Ko kadan Kowa nasa ne, Ni na fara bayyana Masa soyayyata a Lokacin ,nasha Wahala kafin Ya Amince Duk Rahanshi Idan Ya ganni Haɗe rai Yakeyi, A ɓoye nasa aka nemo Min Gidansa, Idan An kaini Makaranta sai in sulale in Je gidan sa, Har wjen aikinsa nake binshi, Uhky... Haukar da kikayi akan Sadauki Kadan ne akan Wanda Nayi akan Baby, Tun Ina Rokon guards Dina su rufa min Asiri kada Su gayawa Daddy Har daddy Yazo ya gane, dakansa, Ya hanani Zuwa Ko Ina, zoki ganni a Lokacin Kaman Zan Haukace 😭, na Koma Tamkar mahaukaciya da kyar ya Amince na cigaba da Zuwa makaranta, Ban dandara ba sai ma abinda ya ƙaru, Nasa akayi min Extra key na Gidansa Idan Ya fita sai in bude in Shiga Inyi masa wanki Wanke Wanke Harda Girki sannan In dau Wanka in zauna Jiransa,Koda Ya dawo Baya cin Abincina,baya kallona Shigewa dakinsa Yakeyi ya kulle kansa bazai Fito ba Har Saina Tafi, baya Wulakantani Amma Baya son ganina, ba don baya Sona ba sai Don Ciwonsa baya so ya mutu ya barni da kewa, Lokacin da na Gano dalilin da yasa Ignoring dina Sai na kulla abota da Dr ɗinshi Har na gano Irin Ciwonsa da Magungunan da yakesha,nima na fara Shan Magungunansa, Cikin Ƙankanin Lokaci na farayi ma kaina Illa, na daina Zuwa makaranta , Na daina Zaman Gida Daddy ya kasa Gane kaina, Gashi na kulle Bakin Guards da kudi duk Sun Rufa Min Asiri.

Wata Rana na je Gidansa kaman yanda na Saba, nayi Masa Girki, nayi Wanka a Bathroom dinsa, Don ko a gida daina Wanka nayi , Wanka a Gidansa Har Wani Shauki na Musamman Yake Sani, Ina fitowa na duba agogo, 12:00 na rana Lokacin Shan Maganinsa Na rana yayi ,sai na dau maganinsa na Balla don Na manto nawa a gida, Na jefa a Baki Ina Shirin Korawa da Ruwa Naji an Riko gorar, sai Maganin Ta Maƙale a Makogoro na Na fara Tari harda Jini, tashin Hankali, a ranar na gane Yana Sona, a ranar na ya gya mn dalilinsa na Kin amincewansa, nace na Yarda naji na gani zan Soshi a kowane yanayi Zan Zame Masa Kidney and Anti Brain Cancer,Idan Ya kini Mutuwa zanyi ,

Daga Ranar Soyayya Ta Kullu a tsakanin mu , a Lokacin da Daddy Ya gane kuwa Naga Tashin Hankali Irin Wanda ban Taba Gani ba a Rayuwata akansa Ya fara dukana ya Kuma Tsaurara Tsaron da Yake bani suka ninku fiyeda da, Dana ga Alama in nayii Taurin Kai Daddy zai iya illatani sai nayi slow na daina Nuna Soyayyar da nakewa baby a Zahiri , Hakan Yasa ya dauka da Gaske na daina Sonshi ne, a ɓoye muke soyayyar Mu har na Gama Secondary School, na Shiga jami'a ,inada Passion akan rubutun Novel but I want Media as Profession haka Yasa na zaɓi nayi Karatun Jarida, sai na fara rubutun Novel online Da Littafina Na farko wato Auren Titi _Street Bounding_ By then I don't know what am Doing am just chasing my Dream , Bansan Inayin abu mai muhimmanci ba saida na fara Rubutun Second Novel Dina (Maƙaryaci _Fake life_ a Lokacin na fara samun more followers a pages Dina Twitter, IG, Watpad friends were adding me on Telegram tiktok etc.

Koda na bar school Ban Bar rubutun Littafi ba, A Lokacin da na fara Neman Aiki, Akwai wani Zain Ali Wannan Guy din Mugu ne, ya kanainaye duk hanyoyin da Zan bi In Zama Yar jarida yaki approving project dina Wai sai na haɗa Masa da Labarin Soyayyar Gaskiya Touching story, babu inda Zan Samu, I went home Crying Then I overheard Daddy's conversation with some men a man was saying.....


_"Ka kashe Alhaji Hassan ka maida Hussainarsa yar aiki a gidan Mijinta ,kayi nasarar wargaza Zumuncin dake tsakanin zuri'ar mijinta , ka haddasa Gaba mai tsanani Tsakanin Yayyi da Kanne ,Har yanzu Alhaji Naseer da ƴar uwansa basua Jituwa Haka yaran Alhaji Naseer Sun ware kansu Basu Yan uwantaka da Komai ba, in fansan Ka akan Ahalin Hassan ne dai ka kashe shi Ka haddasa Gaba a tsakanin Matarsa da Dan uwanta Amma ka kasa Cinma burinka,Ina rokon ka don Allah dakatar da wa......"_ . (Page 9)

Tsoro ya shigeni sosai, na Tsorata sosai Dukda Bansan ma'anan Wadannan kalaman Ba, but I know Daddy was devil, Tun daga Lokacin na fara Bincike ina Bibiyar Rayuwar Sa, sanda ba gane bashine ubana ba, Nayi intending guduwa but I have no evidence, Da nace ya bani Labarin Soyayya sai y bani Labarin Soyayyar da Ya Gwadawa Ammie but in directly, Bai Gaya min Akanshi abin Ya faru ba, he narrated it as a story ,so ni Kuma Sai labarin ya kayatar na Fara rubuta shi as a novel and I named it WUKA A ZUCIYA (BLEEDING HEARTS) , Abinda Baki Sani ba Uhty, Daddy Shi Ya kashe Daddyn Ki (my biological Dad) yayi Wanka da Jininshi"

Da sauri Aeesh ta dubeta da rinannun Idanunta da Suka Jike sharkaf da Ruwan Hawaye tana Girgiza Kai , Sureey Ta gyada kai

"Tabbas akan Ammie daddy Ya Zama Mara Imani Har China Yake Zuwa Don Ya karbo Maganin da Zai Karawa Ammie Bakin jini a idon Mazajen Duniya ,Bayan Ya kashe Mijinta kenan fa, sannnan Ya Wargaza Family dinku ya Kuma haddasa fitina a tsakanin Ahali 😢 , he did Allot Bazan Iya Fada Miki ba, But daddy yayi Abubuwa da dama Ciki Kuwa harda Alwashin Dandana wa zukatan Mu (nidake) kwatankwacin Zafin da Yaji a soyayya, Akwai Wani Dr a asibitin Yaa Maan , Dr Sabo Ake kiranshi, Bashida Imani Shine P.A dinsa duk Wani Rashin Imani Da yake turowa ayi a Asibitin, Shine Gaba , But... You know what"

Aeesh ta girgiza Kai .

"With all these ,Still Ina son Daddy na, Bai taɓa Cutar Dani Ɗaiɗaida Rana Ɗaya Ba, Kullum Cikin Addu'a Nake Allah Ya shirye shi Yasa Ya gane Gaskiya Har Yanzu yaki Aure Saboda Tabon da Tabar Masa a Zuciya koda Yayi Aure bazai Iya bata Kulawan da ya kamata ba"

Aeesh ta share hawayenta tace

"Taya akayi kika san Shine ya kashe Abbana?"

Tafada muryarta na cracking.

"A diary dinsa na gani, he wrote everything"

Cikin Kuka Aeesh tace

"Ya kasheshi Kuma Yayi Wanka da Jininshi Wannan Wane Irin Rashin Imani ne? Inalillahi wainnailayhirraji'in😭"

Wannan Wane Irin Soyayya ce? Soyayya Ai ba Hauka bane, Don an shige maka Gaba a So Wannan bashi zai Hana Allah Ya musanya maka Da mafi Alheri ba, Duk abinda Kaga baka Samu ba Barabon Ka bane, Idan Rabon Ka ne sai Ka fara tunanin Kayi Rashi Sai Allah ya Musanya Maka Da Mafificinshi, So tari Muna Son Abu Amma Bashine mafi Alheri a garemu ba, Idan Mun rasashi Mun kumayi Hakuri Sai Allah Ya Mana sauyi da mafi Alheri, rashin Hakuri da Rashin daukan Kaddara, Shi ke Kai Mutum Ga Halaka.

Kuka suke tayi kamar ransu zai fita,mutuwan Abban Aeesh ya Dawo mata sabo tarasa me innocent Dad ɗinta yyiwa Faisal Da Zai hukunta Shi haka?, Bayan ya kasheshi saida yayi Wanka Da Jinin sa?😭 haba, Abin Ai yayi yawa 😭,ranar sunuyi kuka har sun godewa Allah.

Shari'ar da Ammie batayi tsakanin Aeesh da ASHMAN b Kenan Don Kasa Gane kanta Sukayi , Sureey Ce mai Dauriyar da ta iya kareta da Cewan Mutuwan Abban ta ta Tuna shiyasa take kuka.

Cikin Fushi Ashman Ya bar gidan, Ganin Abin nata ya koma Kaman Rainin Hankali, don Ta ga ya damu Shi Yasa take Neman Takashi😏😡


A ranar Yini sukayi cikin qunci Kuma Kaman an Kame bakinsu babu wanda Yasan Dalilin Kukansu.

Ko kadan Aeesh ta kasa nunawa Ammie tasan Wani abu dangane da Rayuwar Ta ba, Illa tausayin da take Bata sosai .


Haka Ta kwashe Satin a sanyaye, Ammie ta zage sai Sai gyara Yar ta take ciki da bai.

Da farko taso ƙin yarda da Gyaran , a cewar ta ai ya sake ta kuma tunda ya kawota Gidan bai sake Sake waiwayan ta ba,Ba don tasoba aka fara gyarata.
Gyara sosai akema Aeesh,Some times har Kuka takeyi Itafa ta gaji bata so, Menene amfanin Gyaran da za'a yiwa Mutum Bayan Auren ma Ya riga ya mutu?.

Cikin yan kwanaki Aeesh tafara rikidewa,tayi Ɓulɓul dama yaya lafiyan giwa?, dama can mai kyauce shirme da Shiririta ya bata ta,dukda bata da haske amma tana bama fatarta muhinmmanci sosai hakan yasa take sheƙi barin ma yanzu da Ta samu gyara na Musamman Na Yan Maiduguri.

Hakan a ɓangaren Kayan maganin Sanyi Duk ba'a barta abayaba,Ingattatun Kayan gyara na Gida da aka hada da Ingantattun itatuwa ake bata, Ammie kullum Cikin nasiha take, Ita kuma in ta fara sai ammien tayi ta bata tausayi , sai Tasa kuka, A tunanin Ammie nasihar ke shigan ta shiyasa take kuka bata san Yanda Nasihar ke shiga ta kunnen hagu haka yake fita ta dayan kunnen ba, ko kashe ta za'ayi a tsareta da wukake ace ta faɗi Abinda ta Fahinta game da nasihohin da ake Mata, Saidai in kashe tan za'a Yi kila kwakwalwarta ta Dan Motsa.

Ranar da za'a Kaita Tasha Kuka kaman Ranta zai fita ,tunda Aka Farayi mata Gyara Sadeeq ya kira Ashman Ya fesa masa, Aikou mutumin Ya Fara Gyara gida Yayo mata Komai Sabo, Part daya Ya wata Yasa Aka Sauya Komai Zuwa fav colour dinta, Hatta Paintin Gidan Sauyashi akayi

Ranar da za'a Kaita Tasha Kuka, kaman Ranta zai fita, Ita kanta Bata San Dalilin Kukan Da takeyi ba, Chan Kasan Ranta murna takeyi , Tayi missing other half dinta Sosai.

Da yamma bayan an idar da Sallah Magrib

Sadeeq dakansa ya Kai Kanwarsa Dakinta Reey tayi mata Rakiya, Sadeeq na Gaba shida Reey tana baya Sai Hira Suke Yi kasa kasa ,duk Gulmar Aeesh sai Kasa Kunne takeyi Amma ta kasa jiyo abinda Suke tattaunawa

Tsaki taja Cikin Takaici, Ji take Kaman Tace su Daka ta Fita Abinta ,turo baki tayi tace

"Ni Zafi nakeji a kunna Mana Radio"

Banza Sukayi Mata Kaman Basu ji ba, Haushi ya Sake Kuleta ,bata sake Cewa Komai ba, har suka isa Gidan, Suna Farkawa Ta fito, Babu wanda ya biyo ta, har Takai Entrance zata Shiga taga Alamun Basu biyo taba, Tho meye Amfanin Biyotan da Sukayi?, dama Haka Ake Kawo Amarya dakinta, Ta Tafi Yan rakiya su Zauna a mota?.


Jin Takaici ya isheta Idan Ta Cigaba da tsayuwa zata iya kunduma Ashar yasa ya Shiga Kai Tsaye Part din Deejah ta nufa Don Bata san Yayi mata nata Part din daban ba, tanufi matattakalar benen da Zai sadata da Dakinsa kai Tsaye

Ahankali take taka mattatakalar harta kai sama Tana Jijjiga Aeerah dake sakale a kafadarta, Dakinsa ta nufa, ta Murde handle din kofar a Hankali.

Tsayawa tayi tana kallon Shaidar kafar da Ta gani a jikin Entrance door Carpet sai Yanzu ta Tuna Ashe tanada kishiya take Taji jikinta yayi Sanyi, ta nemi kwarin gwiwan da ta shigo dashi ta rasa.

Tsaki taja cikin takaici Ta juya zata Tafi Muryar Deejah ya dawo da ita.


"Haba Doctor, ya kamata Ka Kwatanta adalci a tsakanin Mu, Ji Uban Kayan da Kasa akayi Mata Order Babu wnda aka siyo a KADUNA ,Ga Kuma Gidan Da Ka siya Maku, Ka Gyara Mata Part dinta Ni Kuma Sai Ka Barni Cikin Kazamen part dinnan?, Ko Painti babu"

Ai Aeesh Bata jira ta karasa ba ta Zura Kai Cikin ɗakin Da Sallama, shuru Deejah tayi Tana Kallonta a yatsine.

Aeesh ta banka Mata harara, dubanshi tayi Shima Kallonta Yake da Mamaki, Cikin takun Isa Ta Iso gabanshi ,ta aza Aeerah a kafadarsa.

"Ahky muje Ka Nuna Min Sabon part Dina This part is irritating"

Ta Fada Cikin yatsine Fuska

Kasa cewa komai yayi sai kallonta da yake ga wani Irin Abu da ya tsirga Daga tafin Kafansa Zuwa Tsakiyan kansa, Ta Kara kyau tayi fresh Sosai Kaman Ba Ita ba.

Jin duk sunyi shuru yasata dubansu da Mamaki

"Lafiya?, Yawwwa Ahky....Kasani yau Kwana na ne,Ina binka bashin 1week Already ,So let's Go..."

Murmushin Da baiyi niyyan Saki ba ya kufce Masa, ya shafa gemunsa a Hankali ya furta

"Dama Ai ni naki ne,All my life time is urs"

Dagowa Deejah tayi a firgice tana kallonshi don bata ta6a zaton hakaba awajenshi.

Shima kallonta yake fuska a hade yana kallon direct tsakiyar kwayar idonta like _Da magana ne?_


Juyarda kallonta tayi Kan Aeesh

"Idan Baki Da tarbiyyah , Ya kamata Kisan Shiga Shirgin abokiyar Zama haramun ne"

"Sannu Malama Khadijah Zaujahn Shehyk,Kice Kin Fara Zuwa Islamiyyah kenan Ko a radio Kika Fara Daukan Lectures?"

"Abinda Ya shafeni da Mijina Bai Shafeki ba,Don Haka Ki Fita in na Gama Dashi sai ya dawo gareki"

Aeesh tayimata wani kallon up and down sannan Tace

"Ke ma ya shafe ki ballantana ni Uwar Yarsa?, Karfa ki manta nice uwar Yarsa sannan kuma ni ya fara aura, Nice na zauna dashi Da dadi da ba dadi har ya zama turaren da kika jiyo ƙamshin shi kika biyo kika ce kina so"

"Gaskiya ne Fitsararriya mara Kunya!, Ina magana Da Mijina shine zaki Shigo ki sa min baki??"

Aeesh taja tsaki

"Sannu shafaffia damai, Saboda Kin samu ya aureki shine kike Tunanin zaki iya raba alakar dake tsakanin Mu be? ,Tho tunanin ki ya yaudareki Ni da Ahky mutu Ka raba, Ko bai aureni ba Alakar mu yafi karfin ki Sa Min iyaka"

Tsawa Ashman Ya daka musu yace duk su ɓace masa da gani, Aeesh tasa kuka

"Nidai Na gaji da Abinda Ake min a cikin Gidan nan, Daga dawowana har an fara nuna min banbanci inaga Nan gaba, kodai ka daina sona ne?, Ni dai Gaskiya zan Koma gidan Mu Dama basu gaji Dani ba"

Fita tayi tana kuka, Trolleyn ta da ta bari ya dauko mata, Aeerah na kafadarsa Tana Kuka,Cikin Gargadi Yace

"Ya Kamata Kisan Irin Maganganun da zaki rika mata, Ihty Batada Lafiya Sosai"

Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa, Da kallo ta bisa har ya fice, kuka mai Karfi ya kufce mata.

Kwance ya iske ta, ta dunƙule waje ɗaya, tare da lulluɓe duka jikinta da bargo,Hawaye take sosai,a Bakin kofa ya Tsaya Yana Kare Mata kallo Ya ɗau tsahon 3mins yana kallonta duk da ba fuskarta ce a buɗe ba Yasan Kukan kishi takeyi, a Hankali ya tako cikin ɗakin sosai fuskarsa a tsuke har yanzu da takaicin fadar da Sukayi bai barshi ba,zama yayi gefen hakan ya bashi damar jin yanda take sauke ajiyar zuciya a jajjere har tanayi kamar zata shiɗe.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasa hannu ya ɗagota,ƙin dagowa tayi sai Kukan ya karu.

Sosai take cikin fargaba, bata son Kishiya, tana fargaban irin zaman dazasuyi da Deejah, wacce take burin Ganin bayanta .

Kallonta kawai shima yake, jikinsa a sanyaye Amma Har Yanzu Fuskar Nan babu rahama a cikinta.

Hannunshi yakai yakamo tsintsiyar hannunta dayasha ƙunshi ya riƙo hannun a hankali.

Hakan yasa kukan nata ya ƙaru ,gabanta yashiga faduwa kadan kadan.

Ta dago watery eyes dinta tana ƙoqarin amsar hannunta amma takasa don ya riqe sosai.

"Muje na Maidaki gidanku😏"

Ya fada sacastically yana Sake damko hannun nata, bayan Ya Shimfidar da Aeerah a Baby Bed ɗinta.

Shiru tayi kanta a Cikin bargo tana Sheshsheƙa, tanajin wani iri sakamakon riƙemata hannu dayayi,Ahankali yadan jawo hannun Ya tada ta zaune.

Haka yasa ta dago saidai kanta aqasa, ta manna kanta a kafadarsa ahankali sannan ta Shiga Goga mshi hawayenta a jikin Farar shirt dinsa, Kasa hanata yayi jikinsa asanyaye feeling so awkward and weak.

Fadawa Jikinshi tayi, ta saki Kuka

"Ni dai ka Chanza Min Gida bana Son Gidan nan ,bana Son Zaman Gidan Nan😭"

Dago kanta yayi Yana Kallon yanda Hawayenta ke diga, ya kama kafaɗanta yana matsawa ahankali ta tura baki tana hararansa .

yatsarsa yasa ya make bakin nata tayi saurin dafe wurin idanu waje ya lumshe idanunsa a Hankali, cikin rada yace

"inkina min tsiwa sai na riqa dukanki"

ta had'e rai tace

"ai kuwa da kadaki aurenka don bazan zauna da Mugu ba, kuma ka tashi kafitamin a ɗaki"
Ta fada tana murguda baki

"in na ƙifa?"

" Inma ihun kwarto yashigomin ɗaki"

cikin zafin nama ya fisgota ta faɗo kansa yasa hannu Ya yaye bargon da ta Rufe jikinta dashi

"Bari inyi abinda Kwartaye sukeyi kinga sai kiyi ihun da Hujja"

Ya faɗa yana kokarin jan Rigar ta ƙasa, ta ture Hannunshi da ƙarfi

"malam nidai kafice min aɗaki, Daga Dawowa zaka tayar min da hankali...!"

"bazan fitaba sai naji kin min ihun kwarto"

Waro ido tayi
"me kake nufi?"

Ya Sake matsowa, tayi saurin Jada baya idanunta a waje,cikin zafin nama yasoma jan blanket ɗinda take kokarin rufe jikinta da shi .

Cikin Kankanin lokaci Idanunsa da sukai jajir ya buɗe akanta yana Sake matsowa yana binta da wani irin kallo, ita kanta sai da yanayinsa ya bata tsoro, with a very low tune Yake cewa

"Yau kwananki ne Ihty, kuma kina bina bashin 1wk "

Ya fada Yana Kokarin fadawa jikinta,ganin da gaske yakeyi yasa ta ƙalla

Please Login or Register in order to submit comment