Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ƙaruwa amma a haka kuma skipping Days Kuna latti Taya Zaku koyi Abinda ya Kamata Ire-iren kune Suke Gama BNSC Nursing su Ƙare a Aikin polio...."

"Subhanallahi Please Ma We're Really Sorry,Bazamu ƙara ba"

Juwee ta Bata baƙuri Ganin tana neman Shan corner.

"Ke dalla rufe wa mutane baki ba Gara ke ba yau ne karo na biyu da kikayi latti,Amma ita fa ?, duk randa da Ashman yayi fashi itama Sai tayi,kina biye masa kar ki manta fa shi Doctor ne in yaga Dama karyazo Na Wata ɗaya babu Abinda zai faru, Amma Nurse fa?, dole Ki zauna tareda Patients Ɗinki through out your shift ,Wlh Ki daina Ganin Nan Asibitin Uncle ɗinki ne zaki iya yin duk abinda kikaga dama ,Wlh nan Gaba Zan iya Sawa a soke Lisence Ɗinki Aiki ya gagareki dole kinaji kina Gani Shiga Abitin Uncle ɗinki ya gagarek....."

Gyaran Muryar da taji anyi ta Cikin wayar Hannun Aeesh ne Ya dakatar da ita,Saurin Kallon Fuskar wayar hannunta tayi tama manta video Call sukayi da Ashman Ganin Fuskar Aareef da tayi ya mantar da ita komai.

Tsaki Matron Wusshe taja Cikin tarin borin kunya tana watsawa Aeesh Mugun kallo,Watoh Koda yayi tafiya basu rabuwa akoda yaushe Suna tare ita mayya shi maye Banza dashi ko Aji bashida, da Girmanshi yana Biye wa Ƙaramar yarinya Irin Aeesh.

Kurama wayar ido tayi Aikau saita fashe da kuka, harda shesheka kamar wanda akayima tsinannan duka.

Sakin baki Matron Wusshe tayi tana kallonta.

Ashman kuwa Ganin abin nata bana qarewa bane, saiya gyara zama ya hau rarrashi.

Aikam yasha Wahala kafin ya samo kanta.

Dago watery eyes dinta tayi ta kalleshi tana Turo baki kaman yana gabanta, sannan ta sadda idanu tana saka bayan hannunta tana share hawayenta.

"Yaya Dan Allah ka Dawo, Ma'aikatan Asibitin nan basu ƙaunata Ko kaɗan..."

"Na kusa dawowa ai ,Ba gashi Kullum da ko yaushe muna tare a waya ba"

Gyaɗa masa Kai tayi tana Murmushi

"Yaya har yanzu Ka kasa Zuwa Gida ko?”

Guntun murmushi kawai yayimata yana dan lumshe idanu jin ta kamo dai-dai gaɓar da dama shine dalilin kiranta da yayi.

Kwantar da murya tayi tace

"Ahky....kaifa Namiji ne, You Are Strong ,You might have Problem With ur family, You might decide not to talk to them again ,They might break your heart Amma dangantaka ta Jini ta fi gaban wasa ,muna iya Fuskantar Matsalar Ahali ako wane lokaci Amma ƙaurace musu shine babbar kuskure ,....yanzu ka Ɗauka babu wani abu da ya taɓa faruwa a tsakanin ku na rashin kyautatawa ,Kasa a ranka Su kaɗai Gareka Sannan Ka Tunkari Gida Babu Abin da zai faru da yardar Allah"

Tsaki Matron Wusshe taja ta bar Wurin Don tarin takaici, Murmushi Ashman yayi yace

"Jiya kwana nayi ina Tunanin yanda zan tunkari Gida bayan jarfar da muka aikata nidake,Duk iya tunanina na kasa hararo yanda zan Kalli Idon Abba da kawu bayan irin cin Mutuncin da kikayi ma Shalelen su,Amma sai gashi Cikin Wasu 'yan sakanni kin Nuna min hanya, Gaskiya ke ɗin ta daban ce........"

"Student Aeesh,You have a new admission , *BED 007* "

Muryar Sister Khadeey ta katse shi.

"Laah yaya Budurwarka ,Bari in kai mata ku gaisa...."

Kittttt ya datse wayar, Dariya ta saki tana Girgiza kai, Al'amarin Soyayyar yayanta da Sis Deejah Dariya yake bata babu tattali babu Kulawa baya son Jin Muryarta ,Ko haɗa hanya baya Son Suyi Amma da Anyi magana Yace yana Sonta..!, Ina soyayyar yake anan?.

Ɗagowar da zatayi ta haɗa Idanu dasu,Duk Sun zuba mata ido kamar Mayu, Itafa Shafff tama Manta a inda take ,Su ko kunyar Yin Gulma Basua ji?.

Kallo tabisu dashi na yan daqiqu tana Nazarin yanayin Kowanne daga Cikinsu, Dukkanninsu Babu wanda hassada da Baƙin ciki baya Dayawainiya dashi.

Gajeruwar tsaki ta saki sannan tasaki wata bushashiyar dariya Wanda daga ji iyakarta fatar bakine duk don ta Kunsa musu baƙin ciki.

Miƙewa tayi ta fita ta karɓo file a hannun Reey wanda Deejah ta bayar ta bata don bazata iya jure jira ba.

Nan ta hauyin Abinda ya kawota....

*********

*KANO*

Yana Katse wayar yaja Motar a hankali, Bai tsaya ko ina ba sai Cikin wani Sabon estate ( *Summer Estate* ) .

Estate ne hadadde Wanda ya amsa sunanshi estate, Dukda Sabon Estate ne Amma Daidaikun Gidaje ne Suke Empty.

Estate din shiru kamar babu mutane aciki , Sai dai haushin Karnukan da ke Wanzuwa Jefi jefi.

Gidajene Jere duk iri daya.
Bazaka iya banbancesuba saika duba number dake liqe a kowanne kofar gidan kasancewar gidajen Jere suke according to their numbers Kowanne gida an kewayeshi da furranni masu kyau ,Da Abubuwa mabanbanta masu ban sha'awa.

Gaban Gida na *077* yayi horn Saida Maigadin Ya leƙo Sannan Ya buɗe masa ya shige Ciki ,yayi parking a parking lot.

Ta madubi ya hangi mai gadi yana Kiran Waya,ko ba'a gaya masa ba yasan Mutan Gidan yake Sanar ma Zuwansa.

Gajeren tsaki yaja a ransa yana Jinjina halin Mutan Gidan ba masu Gidan ba hatta ma'aikatan Gidan halinsu ɗaya (wato Gulma).

Jakarsa ya jawo ya Ciro wata 'yar takalmi ya cire ta ƙafarsa ya Saka , saboda last time da yazo ƙusoshi suka jejjera masa a ƙasa yayta tattaka su lokacin Saida ya ɗau Tsawon Lokaci Yana jinya

Baƙar Glass ɗinsa mai taken *NO RESPECT* ya ɗauko ya Ƙwama, Fuskar nan tasa a tamke tamau Kamar An Aiko masa da Mala'ikan mutuwa.

Jakarsa ya ɗauka ya fito ya kulle Motar sa, Ya tunkari Ciki Gadan gadan, Cikin wani irin ƙasaitaccen taku.

Bai ida ƙarasa Shiga ba yaji saukar wheat Flour A jikinshi daga Sama.

'daga Kan sa yayi don yaga daga ina Flour Din ke saukowa Amma ya kasa Ganin komai Sakamakon Rufewa da Idanunsa sukayi, Saurin Saukar dakansa yayi ya Cire Tabarau ɗinsa yana zazzare Idanu.

Da Gudu Mai Gadi yaqaraso wajen da wasu ma'aikata biyu , Driver da cleaner.

"Subhanallahi Sannu Sir, Garin yaya haka"

inji Driver aladabce Saidai deep down dariya yake mishi.

Takaici ya hana Ashman cewa komai don sai yanzu yaga irin ɓacin da Kayansa yayi ,Gabaki ɗaya baƙar Suits ɗinsa Sun Chanza kala Zuwa Flour white. 🤣

Sautin Dariyar Ƙannensa yaji daga Sama har suna Tafawa ,Ɗagowar da zaiyi ya kallesu yaji Saukar ragowar Flour ɗin a fuskar Sa, Take Fuskarsa ta koma tamkar ta Dodo.

Wannan karon ba ƙannensa kaɗai ba, harta Driver da sauran Ma'aikatan dake wajen Dariya Suka Kece masa Dashi Mai Gadi kuwa harda faɗuwa ƙasa don Tsabar Mugunta 💔🤣.

Shi kad'ai yasan azabar dayakeji a Zuciyarsa, Da k'arfi ya cije lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori ,ya nufi Ciki yana fidda huci mai zafi, takawa yake Garin Flour na binshi Saboda Yawan Da yay mishi a Jiki.

A parlour Yayi TTurus Ganin Dukkanin ƙannnensa Mata zaune a Parlour Suna Jirar Isowarahi .

Ihu suka Saki Gabaki ɗayansu suna nuna shi, suka kyalkyale da dariya kamar sabbin kamu.

Jiki a mace yaja jiki Yayi Sashen su zuciyarsa na ƙuna.

_Wannan kenan_ 👌🏽

*KADUNA*

Yau Kowa yaganta yasan tana cike da farin Ciki Duba da yanda take aiki Cikeda Nishaɗi, ƴar wayar da Sukayi da yayan nata ɗazu Ya Antayata Cikin Shauki na Musamman.

Ƙarfe Ɗaya da Rabi Afternoon Nurses Suka zo ,Suka Amshesu ,Sai a lokacin Suka Taso bayan sunyi sallar azahar a Masallacin Asibitin.

Suna Fitowa suka hangeshi Zaune Ya zubawa Gateɗin Idanu da Alama Fitowar su Yake Jira.

Aikam yana Ganin Su yayi zumbur ya miƙe ya nufosu.

"Allah Sarki Sadauki Na, Wlh tausayi yake bani"

Cewar Aeesh tana duban Reey .

Guntun tsaki Reey taja

"Wlh bakida Aji ko kaɗan"

"Eh ɗin wa ya gaya miki Akwai Aji a soyayya"

"Wait... Don't Tell me Biye mishi Zakiyi"

"Ahhh Sosai ma kuwa, Haba Reey Ki tausaya ma zuciyata mana, idan Shine bakia so Nifa?, kinsan irin Ƙaunar da nake mshi kuwa?, He's my Everything, wannan babbar dama ce, Bana so nayi wasa da dama ta wata ta ƙwace mn sh....."

"Ke Dallah chan,wlhy idan kin kulashi in tafi a tsaye ,in son Gaske yake miki he'll keep following you Until he gat u"

"Dan Allah Besty Ki jirani inji me Zai gaya mn , Please Just one minute”

Tsaki Reey ta sake ja cikin takaici ta damƙi Hannun Aeesh ,Cikin takaici tace

"Ke ba Shegiya Bace idan Sonki yake da gaske ya nemi Gidanku, hanya ba Wurin taɗi bane"

Kwa6e fuska Aeesh tayi tana turo baki.

"Besty nidai kina Wahalar Dani Wlh, ki barni nayi Rayuwa ta Kema kiyi naki mana"

Ta faɗa a zuciye tana juyawa don ta ganshi, Saura kaɗan ya iskosu Dan Sauri suke zubawa sosai.

Hannu ya ɗaga Mata Yana Murmusawa, Kauda dubanta tayi daga Kallonsa itama ta saki Murmushi.

"OMG, wayyo Besty Zuciyata Zata Buga, He smiled"

Guntun tsaki Reey taja don takaici ma kasa cewa komai tayi.

"Sannnun ku"

Sukajiyo Muryarsa kamar Daga Sama, sake Damƙe hannun Aeesh Reey tayi dan taga Take takenta na Neman Kwacewa, ta Ɗage ƙafa Suka ƙara sauri kai kace wani Mugun Abu suka Gani.

Sosai jikin Aeesh yayi liqis, Kanta ta duqar Sai hawaye.

Wani nauyi taji zuciyarta nayi mata kamar an doramata qaton Dutse a qirji da Juwairiyyah tasan yanda takeji da bata hanata jin ta bakinshi ba.

Sosai hawayen keta silalowa batareda tayi wani yunqurin taresu ko sharesu ba.

Digar Ruwan hawayenta a hannun Reey ne yasatayi saurin ɗagowa, Mamaki ya kamata Ganin hawaye Shaɓe shaɓe a Fuskar ta ,Burki taja ta tsaya tareda sakar mata hannu.

"Subhanallahi, yanzu fisabilillahi AISHA kuka kikeyi?"

Banza tayi da ita Saidai hakan besa hawayen sun tsayaba.

"Aeesh menene? Dan na hanaki kula wannan Brat ɗin shine zaki tozarta ni?"

Nanma shiru saima juyamata baya datayi.

"Aeesh Indai Namiji ne Gaki Gashi,Ni nayi Gaba In kin Gama kya iskoni".

Reey ta faɗa a fusace Sannan tayi Gaba , Turo baki Aeesh tayi ko a Jikinta dama takura mata tayi.

Gefen Kimonon ta tasa Ta share hawayen ta Sannan ta tsaya har ya Iskota Yana Nishi da Alama Saida ya haɗa da Gudu kafin ya iskota.

Kauda kai tayi Daga Kallonsa Ta Haɗe Fuska Batareda ta bashi Damar Sanin Abinda ke Zuciyarta ba tace

"Me kake so?, kabi ka Takurawa Rayuwata"

"Takurawa Rayuwa Kuma?, Tsakanin nida ke bai wuci muyi tarayya Irin ta saurayi da Budurwa ba"

Juyowa tayi ta watsa mashi Percy eyes dinta sannan ta dauke kai tana cewa

"Niba irin Wa'ennan matan Bane Ok?"

Shima watsa Mata Irin Kallon da tayi mshi yayi Cikin wani irin Murya Chan Ƙasa ƙasa yace

"Koma dai Wace iriyar macece ce ke inada tabbacin Bazan taɓa rasaki a matsayin Muradin Raina ,Kuma Aboyiyar Rayuwa ba"

Shiru tayi , ta kauda Kai tana lumshe ido tana budewa ahankali don itakadai tasan abinda taji daya watsa mata idanun nan, Haka kalamansa Sunyi matuƙar tasiri a Zuciyarta.

Shirun da tayi ne ya bashi tabbacin Kalamansa Sun ɗanyi Tasiri a Zuciyarta, hakan ya bashi ƙwarin Gwiwan Cigaba .

"Ki Fahimce ni, Ki karɓi soyayyata, Rayuwa babu Soyayya tamkar Shekara ce babu Damina a cikin ta, Idan Kina son wani wani abu ne ,haka idan wani yana Sonki shima wani Abu ne ,Idan Kikaso wanda Yake Sonki Shine komai,Abinda yafi komai Kuwa Shine ki kasance da wanda yake Mutuwar ƙaunar ki......"

Ɗan Tsagaita wa yayi yana Duban Fuskar ta wacce ke manne da Sihirtaccen Murmushi wanda ita kanta batasan tana yi ba, Saɓanin Farkon Zuwansa Da ta haɗe rai, Shima Murmushin yayi ya lura tarkon sa ya kama tsuntsu.

"Bazan Iya saki ki Soni ko ki Fahimce ni ba,Amma Ina sa rai Wata Rana zaki Fahimceni, Koda zan Iya mantawa da komai a duniyar nan Bazan Iya Mantawa da wannan Ranar ba, Ranar da Abar ƙaunata ta Bani lokacin ta"

Wannan Karon Zahirtaccen Murmushi tayi Wanda ya Bayyanarda Fararen haƙoranta.

Shagala yayi da Kallonta don ba ƙaramin kyau tayi masa bA, Da kyar ta iya dakatar da Murmushin Nata, Ta Kawar da kai tana Blushing.

Cikin wani irin muryan da ita kanta bata san tana dashi ba tayi mgn

"Ya kamata ka sani So Alƙawari ne, kuma so kyauta ce wanda ake badawa So ɗaya kuma baya ɓacewa har Abadah,Tun daga kallon Farkon da nayi Maka jini na ya hau Amma sam ya kasa Haɗuwa da naka,Haka yasa Na kasa Damƙa maka wannan Gagarumin Kyautar Saboda Ko kaɗan Baka Chanchanta ba''

Saurin ɗagowa Yyi ya dubeta Cikeda Dimbin Mamaki,Bata bari kallon da Yayi mata ya Yi Tasiri akanta ba ta cigaba da Faɗin

"Ka Cigaba da Gwada sa'ar ka, ina maka Fatan Rashin Nasara"

Tana Dasa Aya tayi Gaba Abinta tana Murmushi, Saidai tayi Taku uku Tayi taji Ƙarar takunsa Alamar ya biyota.

Chak ta tsaya ta juyo

"And You Dare Not Follow me....!"

*Kano*

..........

Yau akeyinta

sainaga ruwan comments idan basu gamsheniba kuma zakuji shiru💁.

More comments, more post.

Gaskiya aqara flow din comments sunyi kadan.

Aqara ko in nad'e hannu😏

Sunday

8 May 2022✍️

*BINTOU* 💙

Nayi Gabas🚶🏽‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏽‍♀️
[7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:




NAYI GABAS🚶🏾‍♀️🚶🏽‍♀️
[7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:                        
                    🔪*WUƘA A ZUCIYA*🔪
                   💔( *_Bleeding hearts_* )💔

       
                          *004*
           _The Engagement_

                       *KANO*
Yana shiga Part ɗinsa ya Cire kayan Jikinsa ya dora Towel Ya Shige Bathroom.

Tara ruwan dumi yayi a jacuzzi sannan ya hada mayyukan wanka Masu Ƙamshi,Yana Yamutsa Fuska Sosai yakejin Kyamar Jikinsa A Rayuwar sa ya tsani wani abu Ya taɓa masa Fatar Jikinsa koda Turare wani ya Fesa masa bazai ji Ƙamshin ba Illa ma Kyamar Da Zai haddasa masa .

ruwan  yashiga yayi shuru Zuciyarsa na zafi, Lallai yaran Nan Sun manta koshi waye.

Lumshe idanunsa yayi Dumin Ruwan na Ratsashi ,a hankali Brain ɗinsa yay Masa Recapping Abinda ya faru Recently.

WHAT! ....

Ya furta awkwardly yana ware lumsassun Idanunsa, Lallaima raini ya shiga tsakaninsa da wann yaran, a yau sai yaga Wanda ya tsaya Msu Sai ya ladabtar dasu ta yanda Ko a hanya Suka Gansa Bazasuyi gangancin Hada hanya dashi ba.

Ya Dade cikin ruwan saboda dadinsu don harya fara gyangyadi sannan ya Cuccuɗa Fatarsa ,Gashinsa kuwa yasha dirza Kamar zai Fiddasu ,Ya daɗe yana wanke ko'ina na Jikinsa Kaikace Wani Mugun Abu aka watsa masa, Saida ya gaji don kanshi sannan yafito ya jawo wani Milk din towel dake gefe hange.

Yadaura sannan ya fasa sabon brush ya matsa toothpaste yayi brush daganan yayi alwala yafito.

Wata doguwar jallabiya yasaka ya haye sallaya Wanda dama already a shimfide yake a kusurwar dakin yayi sallar Azahar da ta Riga ta wuceshi Tun A hanya.

Ya Dade zaune tana kwararo addu'o'i sannan ya shafa yamike horn Ɗin Motocin da Yaji ne yasashi leƙawa ta Window.

Taɓe baki yayi Ya Sako takalmansa ya shiga Kitchen ya haɗa coffee.

Yau ran Ashman yafi Garwashi Zafi jira yake a taɓa ta ya ƙona Koma waye  .

Kwance yake Amma hankalinsa na wajen daddynsa Wanda ya hango ɗazu sun dawo.

Tun dazu yake ganin kiranshi Amma ya kasa Ɗagawa Gudun kar Ɓacin ran nasa Ya shafi Abbansa, Su Baffa kuwa da tuni sukaji Labarin Ya Shigo Gidan Allah Allah yake ya sauko Ya Fesa masa Labarin da suka taho masa Dashi wanda yana Kyautata zaton Sai ya ɓata Ran Ashman Fiye da Tunani shi ,Shi kuma a duniya babu abinda yake kauna Irin ganin Ɓacin ran Ashman.

Bari Mu leƙa Kaduna ,Mu taɓo masoya❤️

*Kaduna*

Fuskar ta ɗauke da Wani irin Ƙayataccen Murmushi ta Isa Gidan Su Juwairiyyah.

Tun a Bakin Kofa ta fara Ƙwalla Uban Sallama Reey na zaune a Dinnin tana Cin Abinci , tana Jinta Tayi Saurin 'daukar Plate ɗinta Tayi ɗaki.

Burki taja a parlon tana Binsu da Kallo Suma  ƙannen Reey da kallo Suka Bita Ganin yanda Ta faɗo Musu a Guje, Kwatancen Kurame tayi Musu tana Tambayansu Reey?

Suma da Kwatancen Kurame suka Bata Amsa suna Nuna Mata ɗakin Reey.

Aikam Da gudu ta Ƙarasa Ɗakin, Ta Banko ƙofar babu ko sallama.

Reey na Ganinta ta haɗe Rai ta Sake Tankwashe Ƙafarta ta Cigaba Da Abinda takeyi.

"Ke wai Aljanna ce?, yaushe kika dawo?, har kin cire Uniform Kin fara Cin Abinci?"

Aeesh ta faɗa tana Cire Kimonon da takalmanta haɗe da Ajiye jakar Hannunta.

Ko ɗagowa batayi ba,Bare tasawa Ranta Zata tanka ta.

Aikou Batai Wata wata ba Ta haye Gadon ta Jawo Plate ɗin Shinkafar da takeci Wacce tasha Barbaɗen Cowslow.

Kafin Reey tayi wani yunƙuri har ta Arce a Guje ,A Dinnin ɗin parlor taja Burki Ta zauna Tasa Cokali ta fara ci ,Tana Ganin Reey ta kusa Iskota ta Cire Cokalin tasa Hannu bibbiyu ta Wawuri Abincin takai bakinta.

Fuska Reey Ta yatsine tace

"Yama Yama Dirty Nurse....."

Shaƙewa Sosai Aeesh tayi ,Abincin ya tsaya mata a Maƙoshi yaƙi wucewa , Kofin Ruwa Reey ta Miƙa mata ta Zauna Kusa da ita Tana Mata sannu.

Saida ya lafa mata Sannan tace

"Har Kun Gama Hirar Kenan?"

Murmushi Aeesh tayi Ganin Bestyn nata Ta sauko daga Fushin  nata ,Gyara zama tayi ta ture Plate Ɗin Gabanta.

"Hmmm....In Gaya Miki Saura Kaɗan in Furta Masa yasan Komai,Amma ikon Allah Sai na Tsinci Kaina d Fadar akaso haka!,Amma fa Na bashi Assignment ne, Shine zai zama nawa inshaAllahu”

Tsaki Reey taja

"Allah ya Raka Taki Gona"

"Ameen "

Aeesh ta faɗa tana jawo Plate ɗin Shinkafarta, tasa Spoon ta Cigaba da Ci.

"Besty Pls Meyasa Kika Tsane Sadauki Na?"

”Ba Tsanar sa Nayi ba”

"I see it in You, Idanunki Sun kasa Ɓoye zazzafar Ƙiyayyar da kike masa Besty why?"

komawa tayi tayi balancing akan kujerar tareda lumshe idanu, zuciyarta kamar ana hura wuta, ya zatayi Aeesh Ta Fahimce Irin Haɗarin dake Cikin Soyayya da Ɗan Titi?, ya za'ayi ta fahimtar da ita Illar Soyayya da Gogaggen ɗan Majalisa Mai Yawo da Gangband?.

"Please Besty Tell me...?"

Muryar Aeesh Ta katseta.

"Saboda Shi kyakkyawa ne ,I hate Handsome men, Mayaudara Ne”

Murmushi Aeesh tayi harda Tafa hannu.

"Hhhhhh  Bravo....kinyi Tunani mai Kyau, Shirmammiyar Besty tah, shikenan saboda Shi kyakkyawa ne Sai akace Miki an Rubuta cikin Ƙaddarar sa Dole sai ya Yaudare mace?"

"What Ever .... it's your life, I hated him Koda Ya Aureki bazan Ta6a Kaunarsa ba Koda na Second ɗaya ne....Aeesh i hate Your Sadauki"

Jikin Aeesh Ne Yayi Sanyi ƙalau, Ji tayi kamar Reey ta Chaccaka Mata *Wuƙa ne a Zuciya*

Ahankali ta Ture Plate ɗin gabanta idanunta na kawo ruwa, Ta Miƙe Haka taita takawa ahankali har takai sama  dakyar tashige wani dakin da babu kowa ciki (dakin kannen Reey ne) ta fada kan gado tana lumshe idanu Wanda hakan yaba hawayen idanunta damar gangarowa.

Bin Sahunta Reey tayi Ta Shiga Rarrashi,ita kanta bata taɓa Zaton Soyayyar da Aeesh kema Sadauki yakai ga haka ba,Da ƙyar ta Samu tayi shiru ta daina kukan Amma , Sosai Walwalarta ta ragu.

Dakin Reey ta koma ta sauya kayan Jikinta zuwa Wata baƙar jallabiya , Lokacin Reey na zaune kan Gado tana daddana wayar Aeesh.

Text message ne Ya shigo Ai batayi wata Wata ba Ta buɗe,Ganin Sabuwar Number ce yasata fara karantawa a fili.

*Tsakanin Aiki me Kyau da wanin sa Akwai wani Gurbi...."*

"Thofa Aeesh Dama kinyi Applying Aiki ne?"

"A'a Amma cigaba"

Farowa tayi daga Farko

_*Tsakanin Aiki Mai Kyau da wanin sa ,Akwai wani Gurbi, kuma zan Nemeki a wajen*_

*_Kinsan Ko wacece ke?_*
*_ke ɗin Wata Rubutacciyar Al'amari ce Mai Girma Daga Allah_*

_*Ke wata Madubi ce wacce Kika haska Wata fuska mai daraja*_
*_Wannan Duniyar Ba a wajen ki take ba, Ki kalli chan Cikin kanki_* *KECE DUNIYAR*

_*Duk Abinda kike burin Zama Kin Riga da kin samu*_
_*Kece Makullin Tawa rayuwar, Don Allah Ki bani Dama Ko sau ɗaya ne in Nuna Miki Tsantsar Soyayyar Da nake Miiki*_

Sadaukinki akoda yaushe
Aareef
❤️💙💚

"Wow Besty! ,he's Amazing This is the best message I've ever set eyes on"

inji Reey tana tafawa kallo ɗaya zaka Mata kasan tayi hakan Ne don Farantawa Bestyn nata.

Nan kuwa Aeesh tabi sahu tanata tafawa.

Yar dariya tayi Still tana tafawar tace

"thank you, thank you, Shebi I Told you,Yafi haka ma fa Wlhy , Now lemme Reply".

Ta faɗa tana kokari karɓar wayar daga wayar Reey tayi tace

"No....This is unethical If he really loves you he'll keep chasing you"

Babu yanda Ta iya haka nan ta Haƙura ba dan Ranta yaso ba, She Can't imagine her Self Vomiting Her Feelings to Aareef.....

Mika Hannu tayi tace Ta bata Wayan Babu musu ta bata, Karɓa tayi, Tayi ta Karantawa Daga Ƙarshe tayi Saving Sunanshi da *_my Endocardiac_* (sashen Zuciyata Ta chan Ciki)❤️

           *KANO*

Bashi ya sauko Ƙasa ba Sai arrond 4:30pm bayan Ya Idar da Sallar ASRI Duk hankalinshi yayi gun Dad Bayan ya iske Tulin Misscalls ɗinshi.

'Meyasa dad Ke neman shi haka? I hope all is well' yafada acikin zuciya.

Farar jallabiyarsa ya zura ya sauko yabi hanyar baya Ya Shiga Part ɗin Abban sa,Da sallama yashiga parlourn, can ya hango Dad da kawu a dining Suna Sipping Coffee da Alama Tattaunawa Sukeyi.

Murmushin Gefen baki Yayi Ta Wani Ɓangaren Gabansa na Tsananta Faɗuwa don Har yanzu Hankalinsa bai kwanta da Wannnan kiran da Dad Yayi Masa ba, Da sallama ya shigo.

Amsamashi sallamar Duk sukayi cikin fara'a , Yayin Da Fuskar kawun nasa Babu yabo babu fallasa.

Taɓe baki Yayi a ransa Yana Jinjina baƙin hali irin na kawun nasa Ko kaɗan Baya Ƙaunar ganinsa Ya Tako Cikin Gidan Ubansa yafiso yagansa A waje yana Rara gefe.

Ƙarasawa Yayi Shima Fuskarsa babu Yabo babu Fallasa.

"Sorry dad,a silent na saka wayata Shi yasa Banji ringing Ba"

Hararar wasa yayi masa,sosai Mamaki ya kama Ashman yau mahaifinsa da kansa Yayi masa hararar wasa,Bai gama Tsinkewa da lamarin ba sai da yaji Muryar da ɗin nasa yana Cewa

"Silly Brat , harna fara damuwa danaji shiru, Ance Ka Shigo garin Tun Jiya,Amma ko Call baka mn ba,Ko nayi maka Laifi ne?" yafada yana shan masa Ƙeya.

Mamaki Ya kuma kamashi sosai ,a iya saninshi  Abbansa Ko gaisuwan sa baya Amsawa, Da Alama Akwai wata Kullalliya Da suka shirya shida Kawun Nasa ne.

Shafa Keyansa tana yayi yana turo baki

"Ai Dad Baka damu daniba, shi yasa banyi Expecting call ɗin ka ba"

Murmushin Mugunta Baffa yayi ya kurbi Coffee Ɗinsa,  Dad Yayi Murmushi yace

"i have been taking Care of u Since childhood,Rashin Kulan Da ka ga ina nuna Maka Sanda Ka Girma ba don Komai bane sai don ka San Kaɗaici, I want you To learn How to be Alone Saboda Halin Rayuwa, Shi yasa Na Damƙa maka Ragamar Lura da Asibiti na Nakaduna ,Saboda Baka san kowa ba Achan , Kuma hakan Zai Sa ka Ƙara ƙaini Gun Gudanar da Aikin ka"

Jan kujera Ashman yayi ya zauna kusa dashi, yana Taɓe baki Sam Ko kaɗan Bai yadda da zancen Abban nasa ba yasan Komai Akan Gabar da Abban nasa keyi da shi,Duk akan Aeesh, Ko kaɗan Abba baya Ƙaunar tarayyar Ashman Da Aeesh ,Badan komai ba Sai dan sonta da yakeyi Shima, A tunanin sa Son Aeesh Ashman Keyi bai san Babu Abinda Ke Tsakanin su ba face Ƙauna irin na 'yan Uwantaka.

"So daddy how far? ,you know in kaji kira Samu ne"

Bugu yakai masa ya kauce yana dariya,Shima Baffa da Tun ɗazu yake zaune bai ce  komai ba dariya yayi.

Ya lura Akwai Wani muhimmin Abu wanda Suke so su sanar dashi ,Kuma koda ba'a gaya masa ba yasan ba Alheri bane ,Haduwar dad ɗinsa da Baffa bai taɓa zama Alheri ba haka wannan Karon ma yana kyautata zaton Ba alheri ke tafe dasu ba.

Ya lura So suke su dauko  maganar daketa cin ransu Amma Kwarjininsa ya hana.

Can Baffa ya nisa ya kalleshi da yanayi na seriousness yace "ASHMAN....!"

gabansa ne  yafadi dajin yakira  sunan da Gabaki ɗaya dangin mahaifinsa Suka Tsana, Sun Fi kiransa da Sufyan.

Kasa kai haɗa Cofeen da Ya fara haɗawa yayi ya mug ɗin sannan ya maida hankalinsa katokan  kansu.

Shiru ya ratsa falon suna tunanin yadda zasuyi masa introducing din maganar, can Baffa ya nisa yace

"Ashman, ka Shigo Kano Jiya baka kwana Gida ba"

Ajiyar zuciya yasauke da qarfi, Gabansa na Cigaba da bugun Uku uku, Jiya babu wanda yasan ya shigo Kano in Banda Abokansa Biyu da ya ziyarta ba ,Lallai Tabbas Akwai Manafiki a cikinsu.

"Sorry Baffa"

"Sorry For yourself da ace Ka Shigo jiyan da Munji ta bakinka kafin Mu zartar da namu Kudirin Amma tunda ka nuna mana Bamu isa ba ,Mu mun zartar da Namu We don't Care ko hakan yayi maka Ko baiyi Maka ba"

Kallon rashin fahimta yayimashi

"Ban Fahimce ka Ba , Menene kudirin ku akaina Dama?"

"Khadijah Yarinyar da ka Nemi muje Gidansu Mu nemi izinin iyayenta akan Kana Son ta, Itace dama Muka Je Yau aka Saka Ranar Aurenku!!...."

Tunda yafara magana ya zubamashi idanu yana kallo ko kiftawa baiyi ba don shi harga Allah bai ma san inda yadosaba.

Koda yakai aya bai bar kallon shiba.
Shima kallonshi yake don

Please Login or Register in order to submit comment