Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin azaba yayi baya ya fadi yana fidda Numfashi sama Sama.


VINGO VULCH
A Harabar Wurin ta parka Motarta ta fito Fuskarta a daure, haka kawai takejin gabanta Na faduwa ,ga wani irin kasala dake saukar mata.

Tasha Jin labarin Wajen nan VINGO Amma bata taba Zuwa ba, Babban Wuri ne sosai Wanda aka tanada wajen Hutawan Manyan mutane wadanda Suka jiku d naira, Tsarin Wajen Kaman Shop Rite, Amma kai tsaye baza'a kirashi da Shop rite ba, Saboda Dakunan Hutawa sunfi Shopping Places yawa a wajen.

Location din take bi har ta iso wajen, Escalator ta hau ya kaita up floor, Saida Ta sake hawa Stairs ya kaita chan Sama ,inda Taga location din ya tsaya nan Ta tsaya, kamshin Turarensa yayi mata Sallama.

Binshi tayi da kallo daga sama har qasa.

Sanye yake cikin Jampa,tsadadden yadi Brown dinkin fitted mai hannun knils Kansa babu hulla.

Yar sumar kanshi a kwance luff sai kyalli take, sosai yaqara mata kwarjini da haiba

Shima a bangarenshi kallonta yake yana jin wani irin shauqin dabe taba jiba na dibarshi yayinda wutar qaunarta ke ruruwa a zuciyarta.

Jiyake kamar ya saceta ya gudu don kwana biyun nan dayayi baiganta ba gani yayi an Sauya mata komai, tayi masa girma da tsawo tareda wni irin kyawu Na musamman, Kayan da tasa sun amsheta Sosai

Daurin dankwalinta ya kalla Yau ba Ture kaga tsiya bane ,da Alama yan Arzikin Na kusa yau, Amma Wanchan daurin ya fiyi mata kyau.

Ita tafara janye idanunta akanshi tana Kauda kai gefe sanadin tunawa da wani Abu da tayi.

Nan take taji wani irin kunya ya rufeta ta sunkuyar dakai.

"Mummy.."
Muryar ayyan Ya dira a kunnenta.

Tana dagowa suka hada ido da Saleem ,ta turo baki

"Wannann kallon yayi yawa"

Sosa kansa yayi yace

"Uhm ,Monstang kenan...Ramawa nayi ai kuma kayana nake karewa Kallo, da ace Mun taba kebewa dake da nace na yi ajiya Wlhy bakiga irin kyan da kikayi ba"

Dubanshi tayi ,Taga hankalinshi nakan Ayyan yana bude masa Ledar Chocolate, Fuskar nan tasa a hade kaman Bashi yayi magana ba.

Maida hankalinta tayi kan Saman inda take tsaye ta dafe Stair case tana Kallon down floor da mutanen dake Shawagi a chan kasa kaman Kudaje.

Dagowa yayi bayan Ya mika ma Ayyan Chocolate din ,yana kallon yadda taqara tamke fuska .

Takowa yayi ahankali cikin takunshi na isa da kasaita harya qaraso gabanta.

"You look stunning"

Yafada cikin Sigar rada, yana kama kan Case Yana Kallon Kasa Shima,

Bata dagoba haka zalika bata ansaba amma hankalinta Gaba daya baya kan Mutanen da take Kallo, hankalinta na kanshi tana sauraron duk wani motsi nashi.

Murmushi yasaki sannan yasa hannu ya zame Dan Kwalin kanta, Nan take kyakkyawar gashinta da yasha Gyara ya bayyana.


Dagowa tayi a razane Tana Dan Dube dube a tsorace, cikin Fushi tasa hannu zata karbe Dankwalin ya riko hannun GAM, yana Kallon Hawayen dake kwance a cikin Kwan Idonta.

Cikin sanyin Murya yace

"Garin Saurin zakizo Wajen mijinki ,Kin kasa natsuwa kiyi masa irin Daurin da yakeso"




Nayi Gabas🤗🤗🤗


Bintou

11th Dec😘




[12/17, 2:59 PM] Bintou: *WUKA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_


*058*

Murmushi yasaki sannan yasa hannu ya zame Dan Kwalin kanta, Nan take kyakkyawar gashinta da yasha Gyara ya bayyana.

Dagowa tayi a razane Tana Dan Dube dube a tsorace, cikin Fushi tasa hannu zata karbe Dankwalin ya riko hannun GAM, yana Kallon Hawayen dake kwance a cikin Kwan Idonta.

Cikin sanyin Murya yace

"Garin Saurin zakizo Wajen mijinki ,Kin kasa natsuwa kiyi masa irin Daurin da yakeso"

Ya fada yana murza hannunta dake xikin nashi, daidai lokacin da wni iska mai sanyi ya buso yayi baya da mayafinta ya fadi kasa gashin kanta ya sake budewa.


Bude idanunta tayi ta kalli nayafin nata, sannan ta dubi hannayenta dake cikin nashi ,takalleshi da idanunta da suka cicciko da kwalla, batareda tayi qoqarin janye hannunta ba.

A sanyaye ta sunkuyar da kai tana jin ranta Na da'da baci, abinda ya tokare mata kirji ya sake girma, Sosai takejin wani irin yanayi gabanta Na faduwa .

Murza hannunta yayi ahankali yana kallon yanda lokaci guda yanayinta ya koma abar tausayi.

Saurin dubanshi tayi lokacin da taji ya zare ribbon din kanta,tufkakken gashinta ya war ware ya Sauko har Gadon bayanta.

Lumshe ido yayi yana Jan mashaAllah a cikin ranshi don ji yayi ta tafi dahi lokaci daya,ga Sanyayyan kamshin dake tashi a kan nata.

Dan taune lips dinsa yayi ya zame hannunsa É—aya daga kan hannunta a hankali ya kai hannunsa É—aya zuwa tsakiyar kanta ya shiga shafawa, ya sauke hancinsa akai yana shinshinawa,Saboda burgeshi da gashin yayi, runtse idanunta tayi batareda yayi kokarin hanashi ba.

jikinta ne ya fara rawa sosai lokacin da taji saukar hannunsa a fuskarta yana shafawa a hankali still yana cukuikuya mata gashin kanta, a hankali yake sauke numfashi yana jin yanda tsantsin gashinta ke ratsa hannunsa,a hankali yyi kasa da hannunsa yatsarsa daya ya sanya yana tafiyar tsutsa a gefen kunnenta ya shiga yawo dashi slowly a hankali, kasa jurewa tayi ta buÉ—e idanunta suka haÉ—a Idanu tajada baya tana duban Ayyan da ya zuba masu ido,cikin rawar Murya tace

"S..saleem mene haka?,Bana son iskanci"

Sake nufota yayi , tayi surin Jada baya, binta yayi tayi har ya kure mata, ta kai da bango, Kallonshi tayi, ta dube kusancinsu Sai ta kauda kai tana hadiye hawayen da ya zo mata,hannunsa ya É—aura saman bakinta yana yawo dashi idanunsa yayi jajurr hakan yasa hankalinta yayi matukar tashi.

jikinta na rawa tsoro da fargaba na ratsa zuciyar ta, banda bugawa babu abinda Zuciyarta keyi idanunta ne suka sake cicciko da kwalla ciki rawar Murya tace

"Dan girman Allah kayi hakuri...ka matsa... Allah nace maka dan Allah"

ta faÉ—a muryarta na rawa tana ture hannjnsa dake saman lips din ta, Idanunta a lumshe, tsayawa yayi yana kallon yanda ta firgice, karr karrr haka jikinta ke rawa da É“ari,

Cikin sanyi ta buÉ—e wahalallun idanunta ta dubeshi Jin Shuru ya ratsa wajen, tana hada ido dashi lokaci Guda taji tsananin tsoronshi from nowhere plus some strange feelings sun taso mata, wani abu taji yana yawo tun daga tfin hannunta har na kafarta ,Abinda takeji a cikin jikinta a halin yanzu yafi karfinta sake lumshe idanunta tayi take ta fashe da kuka.

Kallonta yake yana jin yadda take kuka ƙasa ƙasa, idanunta rufe jikinta na rawa.

Murmushin Gefen baki ya saki, Ya duka ya dau ribbon dinta ,Ya zagayo bayanta ya tattara gashin ya dore Mata dashi, Sannan ya dauko daukwalin ya Lankwasata yayi mata Irin daurin da yake so wato ture kaga tsiya, Aikam ba karamin kyau daurin yayi mata ba.

Ta tsakiyan kanta ya yafa mata gyalenta, yana kallon ta


"Tho bude idon an gama...Matsoraciya"

Ware lumsasun idanunta da sukayi jaa tayi tana sakin ajiyan zuciya Saboda kukan da tayi, da kallon maammaki yake binta , wannan ba maryam dinda ya sani bane.

Maryam dinda ya sani bata daukar wargi,ko me zaayi bazata yarda ya taba mata gashi ba, yana zame dankwalin Zaka kwabe shi ,Sai gashi har tana masa kuka akan ya taba gashinta.

Maimaita _*"Dan girman Allah kayi hakuri...ka matsa... Allah nace maka dan Allah"*_ yayi a ransa, wai da gaske ta roke shi?, is she really the one?, anya ba sauyata akayi ba kuwa? this is strange.


Dagowa tayi ta kalleshi da jiqqaqun jajjayen idanunta

"Saleem.."

Daga kai yayi ya kalleta batareda da ya iya amsawa ba, Saboda jin yanda ta kira sunanshi da wani irin passion.

"Kasan Umma na?"

Tafada tana kafeshi da jajjayen idanunta.

Shiru yayi yana kallo yadda ta kafeshi da idanu yana alakanta halayyanta Dana mahaifiyanta, Poor and rude .

Cikin Sigar rarrashi yace

"This is not the right moment for that, Hankalin ki ba a kwance yake ba"

"Ni Na gaya maka hankalina ba a kwance yake ba?"

Ya tabe baki

"What ever....."

Da Alama baiyi shirin snar da ita komai ba, cikin kuka tace

"Meyasa ka turo min location bayan kasan bazaka gaya min ba?"

Yace

"Ni nace kizo...?"

"Haka zaka ce ko?"


"Eh..kikwantar da hankalinki tukunna"

"Ina Ruwnka da Tashin hankalina? Are you me?"
Ta fada helplessly tana hawaye..

Wayarta ya dau ruri,haka kawai taji gabanta ya yanke ya fadi, jikinta Na rawa ta daga cikin tashin hankali da firgici take fadin

"Wane asibiti...."


"Innalillahi....Gani nan zuwa"

Fita tayi jikinta Na bari,DA wani irin gudu ta figi motarta ta nufi Asibitin amma koda suka isa ba'a bar ta taShiga ba saboda Critical condition dinda yake ciki, Likitoci uku ne a kanshi kowanne na gwada nasa basirar wajen ganin sun ceto rayuwarsa, Bamalli Na tsaye gefe hankalinsa a tashe.


Karfe 4:39pm Na rana suka fito kowannen su Na goge gumi, likita yace yana bukatar Hutu kada a shiga sai zuwa gobe.


Karfe shida na yamma yayi daidai da Dirowan Motar Daddyn Maryam dashi da masu taka masa baya, Rungumeshi tayi tana kuka da kyar ya rarrasheta tayi Shuru tana share kwalla, duban Bamalli yayi

"Sannu Mara kunya, naji labarin Abinda ka aikata saboda son ranka kake nema ka halaka min da, tho ta Allah ba taka ba, kuma, Ka sani aurenka da maryam babu Fashi sai dai in bana Raye, mai martaba dakansa ya tsayar da ranar Auren ku nan da Sati biyu "

Maryam Ji tayi kaman an zuba mata garwashi , idonta taji sun kekkeshe tace

"Daddy wallahi bazan auri muzzammil ba,
Daddy bana Sonshi kuma wallahi bana sonshi"

Tana fada tana kuka , nan take daddy ya hau kumfar baki, inda yake shiga bata nan yake fita ba, yana sake jaddada mata aurenta da Bamalli babu fashi,cikin kuka da tashin hankali ta zube kasa ta riko kafansa tana rokonsa, tun da take arayuwarta daddy bai taba saka hannu ya dake ta ba amma ayau sai da Daddy ya mata shegen dukan ba bata taba ji ba, a Asibitin a gaban jama'a haka yake marinta kwallo da ita yana fada tareda jaddada mata aurenta da Bamalli babu makawa sai anyi sai in zata kashe kanta , Maryam tsabar taurin kai bakinta kin mutuwa yayi Sai cewa take

"Wallahi Saidai a kashe ni bazan auri Muzzammil ba"

Bata sonshi, shima baya sonta, tho meye Amfanin Auren?

Daddy yamata dukkan da har duniya ta nade bazata manta shi ba, Don gabaki daya daddy mantawa yayi da matsayinsa, da kuma inda yake wurin jama'a ne, kan kace me Media da bloggers Sun dauka, Tsohon minister Of health kuma recent Director Of nursing and midwifery council Of Nigeria ya saka yarshi a gaba sai ball yakeyi da ita yana marinta, Yan media kam abin nema ya samu, Dukda A leakage din videos din Fuskarta bai fito ba Amma kowa yasan Maryam ita kdai ce babban yarsa mace ..

Kaman daga Sama saiga Saleem ya fado dakin cikin Hankali yazo yana rike Daddy dake ta faman tsolata da Katon takalminsa , gaba ki daya ya kukkumbura mata jiki yana haki yace

"Idan Na aura miki shi Ki mutu! nace ki mutu!!, yar iskan yarinya mai halin uwarta zaki jamin abun kunya, ana ganin mutuncina a gari bazan dauki rainin hankali ba, Aure kaman Anyi an gama ne wlhy, Shiga masarauta kaman kin Shiga an gama ,dole nayi mulki, nima dole inyi sarauta"

ficewa yayi yana huci, kuka takeyi Sosai amma bai ko juyo ya kalleta ba

Saleem da tunda Daddy ya ambaci Kalmar aure yaji komai nasa ya tsaya chak, Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma ya furzar da huci mai zafi jin Sautin Kukanta na daduwa.

Yasa hannu a hankali ya jawota ta fada jikinsa tana cigaba da rera kukan mai ban tausayi.

Da ace Daddy ba mahaifin Maryam bane da yau Sai ya kwana a Emergency da karyayyun kasussuwa, Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi matseta a jikinsa da ƙarfi, firgita tai ta ɗago da sauri tana kallonsa a tsorace tana shessheka ,sake Jawota Saleem yayi tana kuka,cikin sanyi yake rarrashinta har tayi shuru tana sauke numfashin Azaba.

a Ranar da zazzabi mai zafi ta wuni saleem na jinyanya.

*AEESH*

Koda suka koma gida ,dangi da Abokan arziki sai zuwa suke suna jimami, fada kam tashashi tako ina Don duk wanda yaji abinda tayi, da irin Sonda take nunawa Aareef da auren wani akanta, kuma ta san da auren bawai bata Sani bane sai yayi mata fada sosai, wasu harda allah wadaran Da irin halinta na rashin kamunkai a wajen namiji.

Kuka takeyi Sosai tana ganin basu kyauta mata ba, babu wanda ya fahinceta, a ganinta ba laifinta bane, laifin zuciyarta nw, Shikeda control akanta, Gabaki daya Aeesh ta rame ta lalace ta koma abar tausayi.

Kuka Ammie keyi Reey na bata labarin irin soyayyar da Aeesh tayi ma Areef da kuma kokarin da Tayi ganin ta dawo hyyacinta amma taki sauraronta.

Hankalin Ammie yaayi matukar tashi lokacin da taji irin rayuwar da Aeesh tayi lokacin da bata nan, Reey ta gyarazamanta ta cigaba da fadin

"Rayuwar Aeesh abin tausayi da ban haushi,Son da takeyi wa Aareef ya zarce misali Abin ya koma tambar Hauka, komai ta samu shi take damka mawa,wayarta Hotonshi ne a wallpaper Pin dinta Na banki duk ta chanza Shi zuwa Year Of birth dinsa, maganar ta komai Aareef"

Kuka Sosai Aeesh ta fashe dashi ,tana Sosa fatar jikinta dake tsikararta yana mata kaikayi akai Akai, Reey ta cigaba.

" duk da kiri kiri yake nuna baya ra'ayinta amma Duk inda yake tana nan makale daashi, har biyashi takeyi akan Taga dariyarsa"

Kuka Aeesh ta Sake jin kaikayin Na da'duwa, Yau kwata kwata batayi Allurar da ta sabayi ba, hankalin ta gabaki daya ya tashi Sai mutsu mutsu takeyi.

Cikin rauni Reey tace

"Ammie Ita kullum cikin kuka, nima tun tana bani haushi har na fara tayata...."

Ammie ta share hawayen dake Zirya a idanunta, Aeesh ji tayi bazata iya jurewa ba, ta mike da gudu ta Shige dakinta tana Sauke numfashi, Kulle dakin tayi da Makulli tana haki, Jikin rawan jiki and urge ta jawo Akwatinta ta Dauko Ampoule din wata magani ta balla jikinta Na rawa naga ta dauko syringe, ta jawo ruwan Allurar, batayi wta wata ba ta tsirawa kanta a upper arm muscles dinta tana Sauke numfashi a hankli cikin kankanin lokaci bacci yayi a won gaba da ita..

Waro ido nayi ni bintou nabi ampoule din da Kallo, _Penta_ ! _"Innalillahi wainna ilayhirraji'un_ " yaushe Aeesh ta fara Drug?


Iyaka abinda Reey ta sani kenan ta fada ma ammie Akan Soyayyar d Aeesh keyi ma Aareef,duk kusancin dake tsakanin Reey da Aeesh batada idea akan irin soyayyar da Aeesh ta gwada ma Aareef ko kadan, Wanda ido ke iya gani shi ta fada.

Ni kaina bintou ban San da cewa obsession din da take wa Aareef da gaske bane sai da Na bincika naga acct Balance dinta naga 0.12 naira, Kayan sawanta masu tsada duk ta sayar ta kai masa kudaden, Dan kunne da Agoguna ,sarka duk basu, a halin yanzu I was shocked da naga ta fiddo Syringes da Da Ampouls Din Drugs a babbar akwatinta na makaranta ta tsirawa kanta ,kenan itama tana allurar maye?.

Ashe tunda Allura ake masa itama Shi ta koma tanayi ,tayi hakan ne ko zata zama kamarsa ta koma bata Sonshi kaman yanda baya son ta a ganinta Sonsa masifa ce, kiri kiri Aeesh ta zama Drug Addict a makaranta bayan dawowanta daga Canada, babu Wanda yake lura da ita, Musamman takeda Prescription List nata na karankanta kullum sai tayi Prescribing Drug ta siyo da Emergency face, don Ire iren Allurar da takeyi ba'a cika Badawa haka nan ba sai in ya kasance in severe case, Tun tanayin Penta har Abin yayi kamari ta fara hadawa Diazepam kasancewar daga ita sai Reey banda Reey batada mai sa mata ido a rayuwa , ammie batada lfy, ya Sadeeq da Habeeb suna jinyanta a canada, Ashman yana UK lokacin shida Deejah abba yayi masa katanga da ita,shiyasa babu wanda yasani babu Wanda ya damu da yasan abinda takeyi ,lokacin Karatu ya dau zafi Reey ba wani lura da lamarinta takeyi ba.

Yin Alllurar Ya faro ne bayan dawowansu daga Canada itada Ashman ,Zuwan da sukayi babu Wanda ya sani ,Dawowansu Su ya sauya abubuwa da dama a kanta,kadaici harda Cikin dake jikinta yake Neman zautar da ita, Ga uban damuwan da ta daurawa kanta.

tana tsoron allura matuka amma bata shakkanyin ma kanta idan zatayi ,haka take daddagewa ta tsirawa kanta bata ko jin zafi, tana gamawa bacci ke daukanta, tayi tayi kaman jaka, , ranar da ta kusa kwana kofar gidansa saida tayi allurar Sannan Ta tararda fushin da yakeyi da ita, Allurar Diazem tayi Amma tsabar tashin hankali idonta ko rufewa basuyi ba ,bata damuda Munanan side effects Dinda injectables keyi akan Pregnant women ba ,Ita burinta kawai taga ya rinka kulata.

Tsakanin Dawowansu ,da fara abusing Drugs dinta zuwa yanzu dududu wata daya ne kacahal amma har abin ya fara releasing symptoms akanta, idan ta jima batayi ba Sai tayi tajin kaikayi tako Ina, ko kuma ta rinka Hallucinating ana kiranta, brain dinta gaba daya ya rikice Sai tayi Allurar take dawowa normal.

Aeesh bata wasa da karatu Duk shashancinta bata ta'ba Carryover a course ba.

Ammma a tsakankanin lokacin nan ta lallace bata karatu Hakan yasa ta Samu 3c.os a final semester dinsu, da kyar ta haye bayan tayi resitting, Da taimakon Reey wacce tayi kokari wajen kauda hankalinta akan komai ta fuskanci karatu.

A funny thing about Son da take mashi Tanayin All these ne ba don komai ba, Sai don ta Samu attention Dinshi, but tana matukar tsoron Aurenshi, , All she need was his attention shiyasa take biyanshi domin ta samu taga ya kulata, ko kasheta za'ayi a tsareta ta fadi dalilin da yasa take son Aareef bazata CE gashi ba, tana tsoron aurenshi, kuma ba Sha'awarsa takeji ba ,ba kudi gareshi ba ballantana Tace shi take kwadayi , kawai So take yayi ta kulata akoda yaushe, idan kuma yayinesa da ita bata wani damuwa dashi.


Hankalin Mahaifiyar Aareef yayi mugun tashi da taji abinda Danta ya aikata ma Aeesh, Allah sarki Aisha, yarinya Maai hankali hakuri da juriya ga kyauta ,cikin matsanancin fada take masa kansa a sunkuye.

"Kabi duniya a hankali, ka daina kallon abinda kakeyi kaman ado, wallahi zaka yi nadama a rayuwanka, a zamanin yanzu ka samu mace mai sonka don Allah irin Aisha a wannan zamanin da wuya, kai baka tausayinta ne?, Ashe kasan da aurenta kake Binta akan abin duniya?, wlhy ka kiyayi duniya dama bazaka taba sanin amfanin abu ba sai ka rasa shi, wata rana zakayi kuka da idanunka tozarcin da kasa akayiwa baiwar Allah in Allah ya yarda Sai anyi maka, zakayi nadama sosai a lokacin da Allah zaiyi mata sakayya akanka, Kudadenta da kaci ka sani bashi ne, bakaci bulus ba, Sakkayyan Allah Na nan"

hawayen dake makale agefen idonta Suka zubo ya kauda kai yana tabe baki don shi har yanzu bai ji wani darr ba, Cin Amanar da Basir yayi masa shi yafi damunshi, da bai kirata ya hada bomb ba, da tsakanin Ranar da aka kamata Zuwa yanzu yasan abinda ya Tara.

"Ka gaggauta zuwa gidan Su ka roki yafiyanta"

" Tab....Hu'um lallai umma, yo ni laifin me nayi mata da zan roki yafiyanta?"

Ficewa yayi yana fadin

"Ita tajawa kanta da Ta rabu dani tun tuni ta kuma hadani da Muradin raina da duk wannan bai faru da ita ba"


Sureey tazo Nigeria direct Gida driver ya kaita, Ta iske hankulansu a tashe mama taki ta sanar da ita komai dama tasan da zuwanta cewa tayi aikin gaggawa ya samu yaje ya dawo, Sam sureey taki sakin jiki dasu kuma taki amincewa Zeeyk yaje wani aiki ne, Sai kiranshi take yana ringing amma baa dauka ba.

washe gari Umma ta gaya mata Zeeyk na asibiti ta boye mata ne kawai don karta tada hankalinta, tare Suka shirya Suka tafi asibiti, Maryam ita ta kwana dashi Tana jinyar nata Jikin, Tana ganin hotunan Sureey a wayan yayanta, kuma yakan hadasu suyi video call amma dukda haka ,a lokacin da ta ganta Saida ta tsorata kamanninsu Sakk da Aeesh babu abinda ta baro a kamanninta Dana Aeesh saidai sureey tafi Aeesh haske kadan kuma a yanayinta batada sanya irin Aeesh.

Kallon Maryam mama take da mamaki, ganinta da kumburarren jiki, Da mamaki Take tambayanta abinda ya faru, kauda kai Maryam tayi tace

"Mafarki nayi ana dukana, Dana tashi Sai naga da gaske ne"

Maamma ta buga Salati hankalinta a tashe

"Innalillahi yau ni naga takaina... Yanzu Neman magananki bata bar mutane ba har takai kan Aljanu? "

Tuni Sureey ta barsu a Dakin jira ta shiga inda aka kwantar dashi ta tura ƙofar ta shiga ciki ƙirjinta na bugawa, tsoro da fargaba da rashin makomar Zeeyk ɗin nata ya gama ratsa mata zuciya, a hankali ta ɗaga kanta zuwa direction ɗin da take ganin shi kwance a gado, yana kwance flat kaman macacce idanunsa a rufe, sai oxygen da take maƙala a hancisa, Dukk ilahirin jikinsa na'urori ne ,dakin yayi tsitt, Dinn.....Din.....sautin da take iya jiyowa kenanan daga mabanbantun na'urori.

fuskarsa tayi wani irin fari sosai hancinsa ya kara Tsini da tsayi, sharrr hawaye ya silalo mata, rugawa tayi jikinta duk rawa yake ta nufi wajensa ,ta kamo hannunsa ke rawa, jajayen idanunta ta zuba masa Tana kallon yanda ƙirjinsa ke ɗagawa a hankali, cikin kuka tace

"Dama kace in dawo ne Don inyi jinyanka?, meyasa zaka sama kanka damuwa bayan kasan ciwonka baya son haka?"

Ta faɗa tana ƙara saka kuka tareda kankame hannun shi sosai tana sakin matsanancin kuka mai ban tausayi.

Zeeyk zuciyarsa yaji ta tsinke Sanin nature din ciwonsa ne yasa yake kiyayewa daga duk abinda zai daga masa hankali, Shi ba ma'abocin barkwanci bane ada amma Domin ya Samawa kansa Rayuwa ya zama mai yawan Barkwanci ,baya Saka damuwa a ranshi ko kadan.

idanunsa ya buɗe da ƙyar wanda sukai masa nauyi ya diresu akan fuskarta, idanu suka haɗa daidai lokacin da hawayen idanunta ya sauka akan nasa fuskar.

kasa cewa komai yyi sbd mask din Oxygen dake haancinsa, hannunsa yadaga ta fado jikinsa ya rungumota a jikinsa Sosai yana jin yanda take kukan sosai da iya karfinta.

Dagota yayi yana kallon jikakkun idnunta,wani irin kallo yake mata irin nan Na bankwana, wasu hawaye ne Suka Sauko daga idanunsa Suka ziryo ta gefen fuskarsa, Tasa hannu ta shafo hawayen

"Hayaty....bazaka mutu ba, Sai munyi aure mun haifi yara, ka fada min inda Yan uwanna suke da kaina Zan kira madaurin Aurena ya daura mana aure yau yau dinnan ,Ko babu madaurin aurena Na yarda zan aureka ka bani Zoben hannunka a matsayin Sadaki, Na yarda zan Zauna dakai har kashen numfashinka"

Sunbatu takeyi tana kuka Sosai , Shima hawayen ne ke diga a gefen idonsa.
.
Shigowan Maryam yasa ta Dago kanta dake kirjinshi ,ta nufota

"Anty Maryam ,please ina dangina suke?, wanene madaurin aurena?, a daura mana aure yau yau dinnanan ,Wlhy idan ba'a daura mana aure ba Ni zan rigashi mutuwa Saina kashe kaina"

Cikeda karfin hali Zeeyk ya zare Robar dake manne a hancinsa, numfashinsa har wani daukewa yakeyi.

Da gudu Suka Nufoshi Suna hawaye, ya daga ido yana kallon kumburin da fuskar maryam yayi, hannu yasa ya shafa gefen fuskar da yayi jazur yana numfashi sama Sama sakkamakon Oxygen dinda ya cire


"Ki ...lallaba Sss....saleem "

Sai kuma ya rintse ido da karfi yana jan numfashi

"Doc...ument.....FZ20 yana wajenshi"

Bata karasa jin Abinda yake fada ba jin yanda yake nishi dakyar,tayi saurin maida masa robar Oxygen din, ta fice a guje tana kuka, da gudu ta nufi inda ta Parka motarta ta figeshi da karfi, gudu taketa famaan sharawa a titi batareda ta lura da illar hakan ba ,A asibitinshi taja wani wawan burki har saida ta kusa kade wani Gurgu, ko rufe motar batayi ba ta fito tana kwalla, bata iske shi a Gynea dept ba ,Hankalinta a tashe ta fito tana dubashi ta Medical wards nan ma babushi , Fitowa tayi izuwa Surgical ward ta ga fitowanshi daga Gynea theatre da Alama surgery Sukayi ma wta, ganinta a hargitse yasashi Jan burki ya tsaaya yana dubanta da mamaki a fuskarsa.

Cikin matsanancin kuka tace

"Saleem Please....!"

Wani Kallo yayi mata

"What...?"

"The folder ,the documents ,please...please "

Dubanta yake cikin rashin fahimta

"Monstang what's going on ki natsu ki min bayani ban fahimce ki ba "

Kauda kai tayi tana shesheqan kuka mai sauti, matsowa tayi yana jin Shesshekanta har cikin zuciyarsa.

"Maryam please stop crying, Ki nutsu ki gaya mn me ya faru?"

Dagowa tayi ta kalleshi da jiqqaqun jajjayen idanunta

"Dagaske kasan Wanda ya kashe mahaifiyata?...dama kasan komai?"

Ta tambaya tana kallonshi cikin kuka

"Eh Na Sani, amma bana goyon bayan fansan da kuke Kokarin dauka

Please Login or Register in order to submit comment