Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanar dasu koshi waye.

*Gynecology Department*
Nan office dinsa yake, Post operative ward dinsu ya Shiga kai tsaye Wasu nurses ke tsaye kan wata Mara lafiyar Dake ta faman ihu Tun jiya akayi mata aiki Sai Yanzu ta farka, Azabar da taji ne yasata Ringa msu ihu,duk sun dukufa akanta sun kasa shawo kanta tayi Shuru.

cikin takun nan tasa mai Cikeda k'asaita da izza yake tafiya, Attendants sai satar kallonsa suke, kai tsaye wajensu ya nufa yana faɗin

"What's Going on...?"

"Who're you...!"

Wata nurse ta daka masa tsawa.

Lips d'insa ya ciza, ya juyo yana kallonta, tabbas Zai gyarawa nurses da yawa hankali a asibitin nan, idanunsa yakai kan Tag din rigarta S.S Maryam ya gani a rubuce, murmushin takaici yayi, yace

“clear the bed Allow her to rest”

Kallon Sama da ƙasa Sukayi masa,he dressed decently Amma Sunfi danganta sa da Patient Relative don he's Too young to be a doctor.

Bakinsa ya ta6e yana murmushin gefen baki, batare da ya Furta komai ba ya juya cikin Tafiyar isa Saida ya Isa Bakin ƙofa Sannan ya juyo yace

"S.S Maryam meet me in my office”

Zazzaro ido duk sukayi a mamakince
_is he The New doctor?_

Suka tamabyi kansu a tsorace.

Tsaki sis Maryam taja fuskarta normal Amma deep down she's dying da Alama wannan doctor ɗin da ƙarfin hali yazo.

Ba tare da ta ɓata lokaci ba tabi bayansa Suna matan Fatan Allah ya dorata akansa.

Hannu tasa a handle din kofar ta murda saigashi yabude, tura kofar tayi tashiga bakinta dauke da addu'o'i.

Wani sanyi da ni'imtaccen qamshi yaimata maraba Wanda saida ta lumshe ido don dadi.

Bin qayyatacen office din tayi da idanu tana jinjina 6arnar kudin da akayi wajen kayata office din.

Jerin Award tagani Birjik an kayata Office din dasu mamaki ya kamata taya Yaro irin wannan ya samu Awards Haka?,, Amma da ta tuna yanzu Social media ma Suna badawa Sai tabar mamaki ,ta cigaba da karema Office din kallo.

Wasu hotuna tagani manne a bango,Kallon hotunan tayi Hotonsu su hudu ta gani dashi dasu Wasu Uku ta gefe.

Hoton farkon shine Sanye cikin Shigar likitoci,Sannan ta tsakiyar Abba sanda yake Ɗan saurayi shima sanye cikin Shigan Likitoci na ukun kuma ASHMAN Ne Shima sanye Cikin irin shigarsu ta likitoci.

Ji tayi Gabanta ya faɗi (dama Ƙanin Doctor Ashman ne?)

"In kin Gama Kalle kallen ki gaya mn"

Muryarsa ta tsinkayo Kaman daga sama, Zaune yake yana Kallon ta tun shigowar ta ,Taji kunya da ya kamata tana Kalle kalle amma sai ta maze.

"Am here...."

"What's your Qualification?"

"RM,and RN(Renal nurse)"

Kallon Raini yayi mata ya watsar kana yace

"Me Renal nurse keyi a Gynecology dept?"

"Patient din nada Renal failure History ne and she has a Complicated child birth Recently"

Binta yayi da kallo harta dasa Aya, wani irin haushi yakeji azuciyarshi wai yau yar yarinyar nan wacce bata Da kwatankwacin Qualification dinsa itace ta daka masa tsawa?,Gashi yana tambaya ta tana Amsa masa Cikin isa? wai me yarinyar nan ke taqama dashi ne? Me ta dauki kanta ne? Dole yayi mata wankin babban bargo yau daga rana mai kamada ta yau zata koyi Girmama na gaba da ita.

Qwafa yayi yana jinjina kai,  _zan koyamiki hankali ne_ .

"Kinada Office?"

Girgiza masa kai tayi alamar a'a

"Bakida baki?"

"No banida office"

"Daga yau kin dawo karkashin Office ɗina"

"How Dare You?, Kai Gynecologist ne am a Renal Nurse Meye haɗina da Office ɗinka"

Daga gira daya yayi still yana kallonta murmushin kuma bebar fuskarshi ba,Sosai yaji daɗin tunzuratan da yayi.

"Idan bazaki iyaba then Quit!"

Jitayi jinin jikinta na kafewa yayinda wani daci daci ke ziyartar maqoshinta, idan ta rasa Aikinta batada tabbacin samun wani aikin daga Ko ina ga halin kunci da suke fama dashi a gidan su, Tabbas Saleem jinin Ashman ne don Shima Ashman ɗin haka yake taka Duk wanda yaso a asibitin babu mai kwaɓarsa.

"Kin ɗumama mn Office da Wari You can go ....."

Ya fada yana toshe hanci da Farar hankinsa mai ɗauke da Turarensa mai Mugun ƙamshi.

Wani siririn murmushin takaici tasaki ta ta juya zata fita, ji tayi ya kirata,

"Miss Renal Nurse"

Chak ta tsaya Batare da ta juyo ba

"Kije Staff canteen ki haɗo mn Black Coffee and sandwich,Banason Albasa Make it spicy"

Gyaɗa Masa Kai tayi batareda ta juyo ba.

"You have just 10mins starting From now"

Ficewa tayi da sauri har ta nufi staff canteen ta haɗa Coffee dama Akwai Sandwich Wanda Ashman yasa a kawo masa ,ta dauko ta nufo Office din nurses da Attendants sai kallonta ake ana 'yan kuskusss Tuni labari ya Baje ko ina sabon doctor yasa A.maryam ta haɗa masa Coffee.

Bubbuga ƙofar tayi Amma ba'a bata izini ba,haushi ya cikata har ta juya zata tafi sai wata zuciyar ta Kwaɓeta Da ta dawo ,Bugu daya, biyu, uku amma yanzu ma tsit ba'ada niyyar amsawa hakan yasata Jan tsaki ta tafi confidence ta murda kofar tashiga da sallama.

Zaune ta hangoshi da Tab a hannu yana Buga Game.

dagowa yayi yana kallonta, batareda tabari sun hada idanu ba ta nufi Table dinsa ta dire Masa.

Dauke Kai yayi ya maida kan game din dayake acikin zuciyarshi kuma yana ayyana yadda zai koyamata hankali,kenan she's too big tajira yabata izinin shigowa?

Tunda yake Mace bata taɓa daka masa tsawa ba, mace bata ta6a nuna halin ko-in-kula dashiba kamar yadda takeyi, Tunda ya shigo Nurses da female doctors Suke Dying akansa ta samu ya kulata Kamata yayi ta gode Allah ba Girman kai zata nuna ba.

"Zan iya tafiya?"

Ta fada a ladabce.

"Saurin me kikeyi?"

"I have a patients to attend To"

Murmushin Gefen baki yayi yana jinjina Kwazonta da son Aikinta.

"I see ,but you stinks So kike ki kashe mana Patients da ɗoyi?"

Wani Abu taji ya zo daidai maqoshinta ya tsaya yaqi wucewa, Tunda take ba'a taɓa Wulaƙanta ta irin Yau ba,tana gani Ashman na Wulaƙanta colleagues dinta Tana Ganin Laifinsu na rashin Zuciya da Kamun kai, koda wasa Bata taɓa tunanin akwai Ranar da wani namiji zai Wulaƙanta a bakin Aikinta ba.

Sandwich dinda Leather Glove yasa Ya jawo Plate din Sandwich dinda ta dire Masa, kallo ɗaya yayi ma Sandwich ɗin ya tuna irin Sandwich dinda Ashman yafi so Dole akwai albasada Too much pepper, kaiwa baki yayi ya tauna,Aikam yanda yayi tsammani Akwai albasa da yaji sosai , tissue ya yago ya tofarda bakinshi a ciki.

Nuna mata Sandwich din yayi ta yanda zata hango Tarin Albasa da yajine da aka zuba a ciki

"Innalillahi....!"

Kalmar da ta fito a bakinta ke nan Cikin yanayi na damuwa.

Discarding Yayi a Dust bin din kusa dashi

"Did you know the kind of people that annoy me in the world?,talakawa Masu aiki a ƙarƙashin Mutum Suna iyayi idan an Koresu su gayama duniya ba'a msu adalci ba"

Ya ƙarashe maganar da Ƙarasawa Kan Table dinsa ya dau Coffe dinsae zaiyi sipping yaji Tiririn Zafin kamar Zai kona masa Yar Gemunsa.

Kasa Kaiwa baki yayi, batayi aune ba sai jin saukar Tea din tayi a fuskar ta.

Jin Dirar Zafin taji har Tsakar  gigitaccen ƙara ta saki cikin tsananin Azaba.

Ko kallonta baiyi ba ya fice yana Faɗin

"Clear the mess"

...........

*_paediatric Department_*

Surgical Ward

Tun Ƙarfe Goman safe Suka shiga theater Suna ma wani yaro aiki anyi wa yaron Scanning anga kwankwalati a Cikin sa.

Sun ɗauka Aikin zaizo msu da sauƙi ne sai da suka fara suka gane ba Kwankwalati bane wani abu yaron ya haɗiye har ya fara forming Mucus a Cikin Cikinsa.

Basu Suka gama Aikin ba sai around 1:00pm Da gyar Suka samu suka ciro Abin.

A lokacin har mai afternoon tazo ta karɓi dutyn Su Aeesh, Office din Ashman yaje tana jiran fitowar sa su tafi gida tare.

Saida ya fara Shiga masallaci Yayi sallah sannan ya shigo Office ɗinsa Zaune ya ganta tana Game a wayarta.

Wata 'yar drawer ya buɗe ya dauko Kwalin Cornflakes da Bowl ya Mika mata Bowl din yace ta wanko msu, Mamaki ya kamata sosai tunda take bai taba Sata dauko masa Koda cokali ba.

Babu musu ta miƙe ta buɗe ttap ta wanke tana turo baki.

Corn Flakes ɗin ya haɗa msu yasa Cokula biyu nan take suka fara sha tana zuba masa surutu, tayi missing ɗinshi Sosai.

"Ina Reey"

Ta tambaye ta Ganin Tunda ta fara surutu bata sakota a ciki ba.

Kwashe Labarin Abinda Ya faru Tsakanin Su tayi ta gaya masa.

Jinjina kai yayi yana hango wawta irin nasu,ita Deejah Tayi ne don Ta samu ta raba tsakanin Ashman da Aeesh su kuma sun kasa gane haka Sun bari ta shiga tsakaninsu ta wargaza msu Zumunci.

Baice komai ba ya cigaba da sauraron Surutanta,saida ta dasa Aya kana y nisa yace " ku kuka sani"

"Yanzu da zan Shigo naga Mum din Reey Da Alama sun kawo Patient ne"

"What..!
Kasa kai Spoon dinda takai Baki tayi

"Yan gidan su Reey basua zuwa private Hospital, Reey ce kaɗai me kati a asibitin nan"

Shuru yayi batareda ya sake tanka mata ba, dire spoon ɗin hannunta tayi Hankali a ta miƙe ta nufi hanyar fita,bayanta yabi yana Kiranta Amma ko Amsashi batayi ba ta fice a guje hankalinta a tashe.

Direct Female medical ward ta nufa Ta fara Dudduba fuskokin marasa lafiyan dake kwance a gurin chan ta hango Reey Zaune kan Admission bed hannunta daure da Cannula Ana ƙara mata ruwa dayan hannun Kuma Riƙeda Farar hanki ta toshe hancinta dashi Jini na bin hannun nata da Alama Hancinta ke jini.

Ɗagowa Reey tayi Idanunta suka sarke da na Aeesh,tayi saurin kauda kai runtse idanunta da ƙarfi.

Matsowa Aeesh tayi Cikin tsananin tashin Hankali tana ƙoƙarin kamo hannun Reey

“Aeesh get Out...!"

Ta daka mata tsawa.

"Am going no where, no matter what" tafada tana kallonshi tanajin hawaye na neman taruwa a idanunta .

"Then ni zan bar miki asibitin"

Ta fada tana Cire hannun da ta kare Jinin dake zuba a Hancinta hakan yasa Jini ya fara ɓata mata Kaya, bata damu ba Sai ma Ƙoƙarin Cire Cannulan hannunta takeyi.

Hannunta Aeesh ta riƙe tana ƙoƙarin dakatar da ita.

Kama hannunta tayi cikin nata ta matse , Hawayen da take ƙoƙarin dannewa ya zubo

"nayi, Alƙawarin bazan taɓa barinki ba Besty,Pls don't Go... I'll never let you down please Stay, Please Ur health is !"

" If I could chose between you and My Last Breath I would use my last breathe to say I Hate you...Go..!,Go...!!,Go...!!!, Kije gunshi Shi Da kika zaɓa akai na"


Lumshe idanunta tayi ahankali wasu zazzafan hawaye suka gangaro kuncinta yanajin kamar ta maido ciwon Jikin Reey ya dawo jikinta Ko zata samu sasssaucin hukunci Daga gare ta,Son Aareef yayiwa zuciyarta ƙawanyar da babu mai iya rabata dashi ko Umma ce ,Gefe guda kuma tana jin raɗaɗin fushin da Reey takeyi da ita.

Ture hannunta Reey tayi ahankali jikinta na rawa rawa Saboda Zafin zazzaɓin da takeji tana sauraron sautin kukanta, cikin kasalalliyar murya irin ta mara lafiya tace

"Leave, banason ganinki! Please leave!!"

Tafada cikin Azabar ciwo Jini na cigaba da ɗiga daga hancinta.


"Reey ki fahimceni, bazan iya rayuwa batareda shi ba Shi ɗin Rayuwana ne..!”

Aeesh ta faɗa daidai lokacin da Ashman ya turo ƙofar Dakin.

"I knew I was so stupid for choosing love Upon Friendship, a lokacin babu abinda nake hasasowa sai zama dake Zai iya Kawo rabuwa a tsakanina da Arrow, rabuwa ta har abada kuma Hakan shine abu na qarshe da zanso yafaru damu Shiyasa na zabeshi akanki But u'r The strongest Part Of my life Besty Ki fahimceni Shine Rayuwata 💔"


Ashman dake tsaye yana kallonsu ji yayi kaman an zare masa lakka
Shine Rayuwarta? Dama har Soyayyar Aareef yayi ƙarfin da zata iya danganta ta da Rayuwarta? Wannan wace iriyar qaddarace?.

Runtse idanunsa yayi da ƙarfi ambaton sunan allah a zuciyarshi harya samu Abinda Ya tokare masa Maƙoshi ya sassauta masa.

Turo ƙofar da akayi ne yasashi Saurin Matsawa ya ba mai shigowa Dama ta shigo.


Mum din Reey ce dauke da ledodojin Magungunan da ta siyo mata.

"A'isha babu Abinda zaki gaya mn na fahimceki So let me Go"

Reey ta faɗa cikin hawaye sosai tana takaicin kalaman Aaesh, tasa hannu ta fincike cannulation dinda aka mata a hannu da shike Reey Akwai Zuciya ga taurin kantsiya ba kowa ke iya shawo kanta ba in tayi Fushi.

Ƙoƙarin Mikewa take Amma ta kasa saboda Nauyin jiki da zafin zazzaɓi, idanunta ta Runtse da ƙarfi Hawayen takaici suka zubo mata.

rungumeta Aeesh tayi Hakan yasa Reey tafara shesheka

"Am sorry, am so sorry kinji, am sorry I hurt you, please forgive me ,na fasa Soyayyar Please don't hurt ur self bazan sake son Shi ba,I choose you now tomorrow, Yesterday Every moment and forever" Aeesh ta fada tana kamo hannun Reey ahankali sannan ta dora saitin zuciyarta daketa halbawa Da sauri da sauri.

"Ba laifi na bane laifin zuciyata ne, i can't control it"

Saurin kauda Zame hannun ta tayi hawayen suka zubo mata sai kuma ta sa hannu tajawo Aeesh a jiki ta rungume qamm

Qara cusa kanta Aeeah tayi a wuyan Reey ta maida idanunta ta lumshe tana sauraron sheshekar Reeey da Zafin Jikinta, tana jin dama Zata iya controlling Kanta akan Aareef kaman yanda Reey tayi Controlling Anger dinta da komai yazo mata da sauƙi.







Nayi Gabas🤟👐🏼

Comment
And
Share

Sunday
29th may

Bintou ✍️
[7/18, 9:22 PM] chubby number: _*🗡️🫀WUƘA A ZUCIYA🫀🗡️*_
_(Bleeding hearts)_




*008*

Ƙoƙarin Mikewa take Amma ta kasa saboda Nauyin jiki da zafin zazzaɓi, idanunta ta Runtse da ƙarfi Hawayen takaici suka zubo mata.

rungumeta Aeesh tayi Hakan yasa Reey tafara shesheka

"Am sorry, am so sorry kinji, am sorry I hurt you, please forgive me ,na fasa Soyayyar Please don't hurt ur self bazan sake son Shi ba,I choose you now tomorrow, Yesterday Every moment and forever"  Aeesh ta fada tana kamo hannun Reey ahankali sannan ta dora saitin zuciyarta daketa halbawa Da sauri da sauri.

"Ba laifi na bane laifin zuciyata ne, i can't control it"

Saurin  Zame hannun ta tayi hawayen suka zubo mata sai kuma ta sa hannu tajawo Aeesh a jiki ta rungume qamm

Qara cusa kanta Aeeah tayi a wuyan Reey ta maida idanunta ta lumshe tana sauraron sheshekar Reeey da Zafin Jikinta, tana jin dama Zata iya controlling Kanta akan Aareef kaman yanda Reey tayi Controlling Anger dinta da komai yazo mata da sauƙi.

*Cont..*

Ashman da Mum din Reey kallonsu suke cikin tsananin tausayawa, jikinsu duk yayi sanyi.

Numfashi Reey taja cikin Raini

“Na Gane,I know how you feel,Ba laifinki bane Laifi na ne Please Forgive me I could have support ur union Ki yafe mn Besty......."

Tana kaiwa nan Numfashinta ya fara seizing ta fara Shivering, Kanƙame Aeesh Sosai Tana Kokarin samo Numfashi ta baki Da gudu Ashman ya ƙarso 😗,Ya Bambare Aeesh Daga Riƙon da tayi mata.

Oxygen yasa mata tareda Allura,Cikin kankanin Lokaci Bacci ya kwasheta.

Mum dinta da Aeesh na gefe in banda kuka babu Abinda Suke yi.

"Umma kiyi Haƙuri, inshaAllah Zata samu sauki cikin yardan Allah"

Share hawaye Umman Reey tayi tace

"Dr me Suka ce yana Damunta, jiya ko rintsawa Bamuyi ba ,Ciwon ciki ya hana mu Kwanciyar hankali, Ga jinin da ya Keta Zubowa a hancinta tun dasafe na rasa me ke Damunta, Hankali a tashe yake wlh don Allah Dr ka taimaki rayuwar Ɗiyata"

Sosai Matar ta bashi tausayi,Yaji gabaki ɗaya jikinshi yayi sanyi,bashi ya dubata ba don haka bazai iya cewa Ga Abinda ke Damunta ba.

Ledar maganin da Umman ta siyo Aeesh ta karɓa ta shiga Dudduba Magungunan

"What Anti cancer Drugs....!"

Shima Ashman zaro ido yayi yana dubanta da Tsantsar Mamaki a hankali ya maimaita

"Anti cancer Drugs?.."

"Umma Muga Presentation Script Dinda kika siyo maganin dashi?, Wane mahaukacin Dr ne ya Rubuta mata magungunan Cancer Bayan bakuda Cancer history a family Ɗinku"

Rufe bakinta tayi cikin fargaba ganin Sunan Dr Sabo a jiki , Hankali tashe ta ɗago ta dubi  Reey dake kwance tana Saukarda Numfashi a  hankali jini ya bata mata kyakyawar fuskarta.

"Ina Result ɗin test Dinda Aka baku?"

Ashman ya tambaya hankali a tashe.

Result ɗin Umma ta miƙa masa hankali tashe, karɓa yayi ya Dudduba sannan ya juya bayan takardar ya Sake Rubuta mata wasu Magungunan ya Danna Waya Sis yace a turo masa Wata Nurse, Nan take batarefa Bata lokaci ba nurse Precious ta bayyana Takardar Maganin ya jefa mata batareda ya furta wata kalma ba, Jiki na Ɓari ta dau takardar ta nufi Pharmacy.

Aeesh Jin zuciyarta take Wani iri _Me Dr Sabo yake nufi dasu ne?_

Zuciyarta taji Yayi rauni, mummunar rauni don yanzu

“Ina Tunanin Ovarian Cyst ne Ya tsiro mata,Zakuje Ayi mata Scanning Dan A Tabbatar ”

Jinjina kai tayi ta share Hawayen ta At least Ovarian Cyst is better than Cancer

"Tho shi jinin Dake Zuba daga hancinta Kuma na menene?"

" Epistaxis ne due to Stress"

"Dan Allah Doctor kamin bayanin Sosai ,Kaga fa harda Oxygen ka sa mata hakan na nuni da cewa Ciwon ba ƙarami bane"

Dafe kai Ashman yayi Ya furzar da huci, Cikin yanayi na rarrashi yace

"Jinin da kikagani a Hancinta Haɓo ne ,Normal Haɓo, yanzu na samu na shawo kan komai,dama Stress ne da  baccin da bata samu tayi ba jiya, Numfashinta da ya dauke kuma jinin ne ya toshe Mata mashaƙar iska,Kuma tayi inhalling Jinin Sosai har yana kokarin Blocking lungs sanadiyar Hakan yasa Numfashinta yayi kasa sosai ,Amma alhmdllh Komai yazo da saiƙi"

Dafe kai Umma tayi tana kallon yanda Reey ta zabge lokaci Guda without saying anything, ita kadai tasan halin datake ciki .

Yau S.MaryamWuni tayi tana Aiki Bata samu damar Duba Patient ɗinta ko ɗaya ba, Instead Saleem sawa yayi ayi Replacing Ɗin ta da wata,Tuni labari ya kewaye ko ina Ƙanin Ashman Ya faso kuma da Alama da wulaƙanci yazo.

1:17pm ta gama Ayyukan da ya sata Na gyaran Office dinsa yana zaune yana kallonta Duk motsin da take yi akan idanun sa takeyi Gabaki ɗaya uniform dinta ya sauya launi daga fari Zuwa dirty Color yana jin kiran Sallah ya miƙe ya nufi masallacin Asibitin.

Tana Ganin Fitarsa ta Shige Bathroom Din Office din tayi wanka Ta dauko Bakar jallabiyarta a jaka ta saka tayi Discarding Uniform ɗinta ,,ji  tayi kanta  na sarawa sosai Kai tsaye phamacy ta Nufa don ta karɓo Paracetamol.

Daidai lokacin Sis Precious ta Iso Wurin, Tana cewa

"Laaah kaga manya Masu Aiki Under Office ɗin Masi kuɗi"

Banza Maryam tayi mata ta miƙama mai chemist Prescription ya Bata PCM.

"A'ah Duk Ciwon kan da yasa miki ki rasa Abinda zaki Sha Ki warke Sai PCM”

Nan ma shuru tayi mata ta juya zata tafi,Tsinkayar Muryar Precious tayi tana cewa

"PCM tab ɗaya bazai isheki ba, da kin sani Bakizo dakanki ba Instead Akwai Attendants dayawa a cikin Asibitin Dama kinsani Basai kinzoba ,Kin aika a kawo mkk,  Duk Matsiyaciyarda wannan opportunity din yasameta saitaji kamar ta kashe kanta don dadi, Saidai dafatan kin san DrSaleem da Dr Ashman ba 'yan goyo bane, Sun san kan duniya, zai baki kudi Amma sai Kin Gummace bakiyi Aiki a Asibitin nan ba,i might Sound some how but am not Jealous, Am just reminding you Of who you Are Diyar talakawa,sani wutsiyar raqumi ke kanki kin sani baki isa ki jera dani ba ballantana Ƙanin Dr Aashh.....mtsww"

Chak ta Tsaya ta kasa tafiya Ta juyo,Tunda take ba'a taɓa Wulaƙanta ta irin haka ba!, har wata kucaka irin Precious ta Isa ta Wulaƙanta ta?.

Ƙamshin Turarensa taji Saurin dagowa tayi tana kallonsa a mammakince, Nan ma biyota yayi?.

Tuni jikin Precious Ya Fara rawa Kaman Mazari ta kama kame kame

"Good Afternoon Sir"

Ta gaya tana ɗan russunawa, Banza yayi mata ya dubi Pharmacist Dinda ke pharmacy din yace

"Bani PCM Syrup, Injection da tablets Each package Kwali Goma"

Babu musu Pharmacist Din ya hado jiki na rawa don Tun kan ya Ganshi Yaji labarin shi Gun Nurses dindake kawo masa Gulma.

Mamaki ya kama Precious da Maryam me zaiyi da uban magungunan nan?,kodai ɗan kwaya ne

"I need a bucket"

Saleem ya fada yana Aunawa Precious mugun kallo,Taso ta tafi Amma Kallon da yake mata ya mata nuni da yaji duk abinda take cewa Gara ta tsaya ta karɓi hukuncin ta,babu bata lokaci Aka kawo masa Bokiti.

"Mr pharmacist Nawa ne Kuɗin Magungunan?"

"250k sir...."

"Ta biyaka"

Ya fada yana nuna Precious.

Saurin kallonsa Tayi jiki na rawa

"What Sir...Ni b.."

"Zaki biya yanzu ne ko insa a zara cikin Salary ɗinki Yar masu kuɗi?”

yayi maganar yana kallonsu, Precious sai zufa take dukda sanyin A.c din Wurin , ita kuma Maryam is expressionless, baka iya gane yanayin datake ciki, ba da dan Kashedin da yayi mata dazu ba cewa idan yana Wuri Sai ya bata izinin Barin wajen kafin Ta tafi Ba da Ta tafi ta barsu.

Tablet din paracetamol daya ya dauka ya ɓarosu duka ya zuba a Bucket, Haka na Injection ya ɓalla AmpouleDin ya zuba a Ciki Syrup din ma haka ya cire marfin ya Sake dukka ya Kwamutsasu.

Ɗagowa yayi ya dubi Maryam dake masa Kallon mamaki yace

"Kiyi ma sauran haka ki kai mn Office,Am off for Today, Kai Kuma Mr pharmacist ka Shaƙeta ta bamu kuɗin mu Nasan 250k bazai gagari ɗiyar Masu kuɗi ba"

Yana Gama faɗin haka ya juya ya tafi Cikin tafiyar nan tasu ta isa,Bin uban Kwalayen Magungunan Maryam tayi da kallo, taya zata fara Babballa uban magungunan nan Har kwalaye Talatin Kuma ko wanne Kwali ba Ƙaramin magani ne  a ciki ba Gara ma Syrup din Marfin kadai zata Cire Ta Zubar ,Amma tab da Ampoule da Sai ta zauna tayita Ɓarewa in batayi sa'a ba Kwalbar Ampoule ya Fasa mata hannu.

Jitayi wasu sabbin hawaye na zuwamata, saurin maidasu tayi tana girgiza kai No Maryam, don't cry, you're strong, be strong,You can do it ,in kikayi haƙuri watanni *Biyar* ya rage miki ki bar Asibitin Gabaki ɗaya.

Kwashe Kwalayen tayi ta shiga Cikin Wani dakin dake cikin Phamacy ɗin ta fara Aiki.

Precious Kuwa badan taso ba ta ciro katin ta Ta je inda ake biyan kudi ta biya kudin magungunan,sannan ta kaima su Reey magungunan Su.

Qarfe Biyar saura ta Gama Ta dau Bocket ɗin da ta zuba magungunan ta Kai masa Office ɗinsa, Daidai kan Deck Ɗinshi ta Dora Masa ,ko kadan bataji nauyin Shi ba Burinta gobe idan yazo ta Kunsa masa haushi kamar yanda ya Kunsa mata ita ma, Tun da ta fara aiki yau shekaru biyu kenan Babu likitan da ya taɓa sata Aikin dole da har zai sa Ta kai ƙarfe biyar a Asibiti bata je Gida ba ita ba Afternoon duty ba ita da Komawa lokacin tashin su, Lallai Saleem Bai San ko ita waye ba Dole ta nemo Gidan su ta Ci masa Mutunci ,a ranar Kuwa koda ta koma gida tasha Faɗa Gun Ummanta Abbanta kuwa cewa yayi ta bar aikin Gabaki ɗaya shi bai yarda da aikin da mace zata fita tun Takwas saura ta dawo karfe biyar na Yamma ba, haƙuri tayi ta basu daƙyar suka haƙura daganan Ta shiga Shirye Shiryen tarbar Na gobe.....

Bayan Scanning dinda akayima Reey an Tabbar Ovarian Cyst ne ke haddasa mata tsananin Ciwon Cikin,hakan yasa babu ɓata lokaci Aka maidata Gynecology department da cewar nan da kwanaki Uku za'ayi mata Aiki, sosai hankulansu ya tashi, kwantar msu da hankali Likitocin sukayi da ƙyar Ashman ya samu Aeesh ta Bishi suka koma Gida, Shi gabaki ɗaya ya manta cewa tare sukazo da Saleem.

Qarfe Biyar daidai tafito daga dakinta sanye da wata jallabiya Maroon colour mai adon Black agaba tayi rolling din gyalen jallabiyar, hannunta daya riqeda Basket din Abinci dayan kuma Riƙeda waya tana Amsawa.

Saukowa tayi  jikinta sai tashin qamshi yake.

Dakin Umma ta nufa tayi Mata Sai da safe don yau a asibiti zata kwana tana Jinyar Besty ,sannan tafito waje catwalking kamar ba ita ake jiraba.

Ashman ya qulu iya quluwa, tundazu yake jiranta a mota Ta side mirror yake kallonta ta taho kunnenta kare da waya da alamu waya take ga wani sihirtaccen murmushi datake saki Wanda ya bayyana jerrarun haqoranta farare Tass ga dimples ɗinta dake loɓawa aduk lokacin da ta Murmusa.

Tsayawa yayi yana kallonta don a iya Sanin sa da ita be ta6a ganin tana Waya tna murmushi haka ba, a iya sanin shi Shi kaɗai yake iya sata irin Murmushin nan,Wani abu ne yaji ya tokare shi Da Alama da Aareef take waya.

_Reey ki fahimceni, bazan iya rayuwa batareda shi ba Shi ɗin Rayuwana ne_  Kalamanta na dazu suka dawo Masa,Huci mai zafi ya furzar yana Sake Tunano Kalaman Abbansa  _Mun Riga Mun Gama komai har Sadaki mun kai Ranar kadai muke jira_

Qarasowa ta buɗe baya ta shigarda Basket din hannunta.

Dawowa tayi ta buɗe Gaban motar, Qamshin turarenta dayaji gab daishi ne yasa gabansa faduwa ,bata ma san yanayi b Rufo ƙofar tayi

"Ok sadauki na ,Sai Mun haɗu a chan...ka Kular mn da kanka..... Love You More...., muah"

tafada tana blowing mashi kiss ta wayar

Sannan ta

Please Login or Register in order to submit comment