Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara, a razane yayi saurin rufe mata baki da tafin hannunsa ɗayaya ɗayan kuma yana qoqarin janye bargon cizo ta manna mishi a hannu yaji zafin har tsakiyan kanshi, amma yaqi ko gezau sai ma ƙara ƙaimi yayi wajen janye bargon da hannu ɗaya,dayan hannun nasa dai yana rufe da bakinta ,kuka ta saki tana Ture Hannunshi

"Ahky don Allah kayi Hakuri na Tuba, Wlhy bazan Sake ba...."


Shi dai bai sarara ba, Saida Ya gama Birkita Yar mutane, ya Kashe bakin Tsiwan sannan Ya sarara Mata .

Kuka take sonyi Amma ta Kasa, Ta wani Kame jikinta idanun nan Sunyi zuru zuru, Sai sauke numfashi take kaman wacce tayi wasan Tsere.

Yaja hancninta fuskar sa ɗauke da Murmushin mugunta ya sunkuya ya mannawa goshinta kiss sannnan ya sauka a gadon ya nufi Inda ya kwantar da Aeerah itama ya manna mata kiss a goshi.

"Baby na hope kin Daina kukan dare"

Ya faɗa kaman Mai tsammanin answer daga Gareta,Sannan a hankali buɗe ƙofa zai fice ya jiyo Muryar ta ƙasa ƙasa tana cewa

"Idan Ka fita tafi kar ka dawo ,ka Koma wajen matar ka na yafe mata Satin gabaki ɗaya"

Ta fada tana maida numfashi , Murmushin mugunta ya saki ya Shafa sajensa, Sannan Ya sakai ya fice.


*MARYAM*

Tunda taji labarin Saleem Ya ɓata Hankalin ta ya gaza Kwanciya, Ayyan Kullum sai ya Tambaye ta ina daddyn Shi? ,Bata da amsar da zata bashi Haka Take rungume shi suyita kuka _Nima ina tayasu_ 😭😭

Ga kadaici da ya addabi Rayuwar ta, She feel alone sosai take kewan Mutane biyun nan da suka zame mata Garkuwa a Rayuwar ta.

*Zeeyk da Saleem*

Yau Sunday, tunda ta tashi ta yanke shawarar yau saitaje saloon ayimata retouch daga nan tawuce supermarket tadanyi sayayya, Don Gobe Take sa Ran Zata sa Ayyan a makaranta.

Tunda Zeeyk ya rasu bata fitaba so take ta fita yau ko zata dan motsa kafa.

Fitowa tayi daga bathroom ƙirjinta daure da milk towel iya gwiwa kanta sanye da net cap.

Fitowan Ta kenan Daga Wanka fuskantar nan A daure tamau, face dinta sai Glowing Yake.

Gaban mirror ta nufa tana gyara daurin towel din qirjinta,Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror gani tayi ta rame Sosai .


Murmushi tadanyi sannan ta dauki body cream ta shafa tadanyi simple makeup sannan ta saka Gown na atamfa ta yi daurin da ta saba Wato ture , tayafa mayafi tafita.


Direct dakin mama tanufa don tasan tana ciki,zaune ta isketa bisa Sallaya tana Jan Charbi, Ayyan na jikinta fuskar nan yayi Jame jame da Hawaye, a hankali mama Ta amsa Sallamarta, ta shigo fuskar nan Babu yabo babu fallasa.

Zama Maryam tayi gefen Mama, suka sata a tsakiya tana shagwa6e fuska.

"Menene?" Inji mama tana kallonta

"Zan fita" tafada a shagwa6e tana dan turo baki.

"Kuka zakiyi?" Inji mama tana dan harararta , Kaman Jira take nan Take hawayen dake makale a gefen idonta Suka Sauko.

"Yau naga ikon Allah, Mero kukan Me kikeyi , Gardiya dake zaki sani a gaba Da shagwaɓa?"

Duban Ayyan tayi hawaye na bin Fuskar ta, murya a dishe tace

"Son...Zoka rakani"

Ai Kan Ta rufe baki har ya Mike, Ta riko Hannunshi suka Fita dama Bata jima da Chanza masa kaya ba, a wajen Tap suka tsaya, ta wanke masa Fuskarsa Sannan suka shiga Mota tajasu suka fice daga Gidan .

Kai tsaye Bintou Hair Saloon Suka nufa, Cikin Kankanin Lokaci aka wanke mata kai sannan suka Nufi supper market suka yi Siyayya, Ayyan Dakanshi yake zaban Duk Abinda Yake so ita kuma tana Tayashi

Sosai Sukaji dadin fitan da sukayi don This's the first outing da Sutayi da 'Danta.

Fitowa Sukayi Kowannensu Riƙe da manya manyan Shopping bags Fuskar su dauke da Murmushi.

"Daddy...!"

Ayyan ya kwala kira daidai lokacin da yaga ya Sauka a motarsa.

Ta ware idanu ta bishi da kallo yana sanye da shadda Sky Blue babbar riga da jamper bai saka hula ba, ya Rame sosai Kila dalili kenan Da yasaka Babban Riga dn a iya ganin da na mai, bai cika sa babban Riga ba,.

A hankali ya dago,Fuskar sa mai ɗauke siririn sanje zuwa gemunsa ta Bayyana, Mtuwan tsaye tayi ta kasa Kauda Idanunta akansa, Tuni Ayyan Yayi watsi da kayan Hannunsa Ya nufeshi a guje....




Nayi Gabas🚶

2nd January 🇳🇬

[1/7, 23:10] Bintou Abdul: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_

*65*

Fitowa Sukayi Kowannensu Riƙe da manya manyan Shopping bags Fuskokinsu dauke da Murmushi.

"Daddy...!"

Ayyan ya kwala kira daidai lokacin da yaga saukowanshi a motarsa.

Ta ware idanu ta bishi da kallo yana sanye da shadda Sky Blue babbar riga da jamper bai saka hula ba, ya Rame sosai Kila dalili kenan Da yasaka Babban Riga dn a iya ganin da na mai, bai cika sa babban Riga ba,.

A hankali ya dago,Fuskar sa mai ɗauke siririn sanje ya zuba mata, Mtuwan tsaye tayi ta kasa Kauda Idanunta akansa, Tuni Ayyan Yayi watsi da kayan Hannunsa Ya nufeshi a guje....

Cak bugun zuciyarta ya tsaya,ta zuba msshi idanu Bata ko kyaftawa.

Bakin Ayyan yaqi rufuwa don tsananin murna, ya karasa wajenshi ya Rungume sa Yana tsalle, Shima Saleem Rungume shi yayi dukda baiso ya hadu da dayansu yanzu ba, Amma Yayi matukar shaukantuwa da ganinsu a tare ,Cikin takun Nan nasa Wanda nayau yafi na kullum ya qaraso gabanta, ta saukar da idanunta tana Bata fuska, as if batayi murnar ganinshi ba.

Shidai binta kawai yake da kallo without blinking, bai ta6a sanin yayi missing dinta sosai ba sai yanzu daya ganta,wani irin abu da bai tabaji game da ita bai ta6a ji game da ita ba Yana fizgarsa, jiyayi kamar ya rungumeta tsabar shauki, ji yake kamar yana melting ahankali, soyyayarta na Ratsa zuciyarsa, jini da ɓargonsa lokaci guda yajishi a wani yanayi Mai wuyar fasaltuwa,yanayin da bai taɓa Jin kanshi a ciki ba.

Yayi ta maza ya saita tunaninshi amma tunaninsa ke neman saita sa, ya taka kusa da ita ,kamshinta ya bugi hancinsa,ya lumshe Ido wata natsuwa na shigarsa , ya tsura mata Ido Yana kallon Fuskar ta dake sunkuye tareda son Gano wani tattare da ita, Kaman bata Murnar ganinsa Fuskar ta babu yabo babu fallasa, da taga kallon Ba Mai karewa bane sai ta ce

"Sannu"

Kaman an tilasta mata batareda ta dubeshi ba, cikin sanyin jiki ya lumshe Ido ya buɗe su akanta Muryar sa da alamar mamaki yace

"Sannu.....?"

Kai tsaye tace "Uhm... Ya akayi?"

Da ya Lura yau Yan ajin ne a kusa Shima sai ya Yafa nashi na Yan Sarakin ya maida Natsuwarsa, cikin tsare gida yace

"So why are you here?, Da izinin wa Kika zo Nan?"

Da sauri ta dago idonta ta watsa masa Kallon da yasa yayi saurin kauda nasa idon

"A matsayin ka na wa fa?"

"A matsayina na Mijinki"
Ya Fada Yana Murza hannun Ayyan dake cikin nasa, taja guntun tsaki da ƙoƙarin kama hannun Ayyan

"Ayaan let's Go"

Kuka ya saki Yana Kankame Daddyn nasa, Saleem ya kama dayan hannunsa ya rungume shi a jikinsa, hakan yasa ta cika shi tana auna masu wani kallo Mai wuyar fasaltuwa

"Free my son Ko in Tara maka jama'a"

Da mamaki Saleem yace
"What...!"

"Eh kajini sarai ka kyale minshi mu tafi"

Yanayin yanda take magana sosai ta burge shi, har yanzu tna Nan a Maryam dinta Mai Jan aji da nuna Isa Bata shakkar komai, yanda ta nuna sonda takeyi wa ayyan ya burgeshi.

Da taga kallon da yake mata sai tace

"Malam ka sakar min ɗana tafiya zamuyi"

Saida ya murmusa har fararen haƙoransa suka byyana, rabon da yayi murmushi har ya manta

"Da Alama kina son Wannan yaron naki da yawa"

Harara ta Galla Mai batareda tace komai ba,

"Kiyi hakuri bazan Iya barin ɗana ba, alhalin Mahaifiyarsa Na gudun Mahaifinsa"

Maryam ta Bata Rai tace
"Me kake nufi?"

Ya dage gira daya yace

"Baki gane hausar ba?, Oh na manta ashe baturiya ce, gashi ni ban iya turancin ba ballantana in sauya harshe, hakuri kawai zakiyi bazan iya Baki Ayyan ba, idan kina sonsa da gaske ki dawo ɗakinki ,na gajida follow up"

Idanun Maryam suka ciko da hawaye, ta sassauta murya, a raunane tace

"Haba Saleem please Saleem Ka banishi mu tafi yamma na karato wa"

Saleem Ya Girgiza Kansa yace
"Saidai ki bini mu je..."

Bai jira cewarta ba yyi gaba abinsa hannun Da rikeda na Ayyan, Yana takawa Kaman bayason take kasa, fuskar Nan a tamke tamau,Ayyan harda Juyowa yana Mata bye bye.

A kufule Tabishi da kallo har ya shige motarsa yaja yabar wajen dukawa tayi ta kwashe kayan da Ayyan ya zubar ta saka a motar ta, sai yanzu abinda ya faru yayi dawo kwakwalwarta, ya tafi ya bar su for a month Bai waiwaye su ba and yanzu, Yazo ya karɓe Ayyan does it make sense?.

Sai yanzu taga Wautar da tayi na kyaleshin da tayi ya tafi dashi, To tsoron sa takeji ko Yaya?sai kace Wanda yayi amfani da Juju akanta, aikam idan ta kyale shi tayi wauta yacita a gasa, Nan take ta figi motar da karfi ta bi bayansu a Da wani irin Gudu kaman mai shirin Tashi sama.

Sunyi mata nisa sosai don Shima gudun yake sosai, Amma hakan Baisa ta hakura ba, binshi take a duk inda taga yabi da gangar yayita wahalar da ita sai corner corner Yakeyi, har ya iso gaban Sabon gidan sa, Kafin Ta karaso har ya Shige, Mai gadi na Shirin Rufe ƙofa ta Danna Hancin motarta ciki, tayi parking tana sauke numfashin gajiya don ba ƙarya ya wahalar da ita Sosai, Kafin ta kashe motar ta ɗago, sai hangenshi tayi Yana Shirin Shigewa gidan.

Cikin hanxari ta fito ko kulle motar batayi ba ta fito har tana tuntuɓe,ta bibayan shi har ciki.

Tana shiga ya ɓacewa ganinta,Kalle kalle ta fara tana Neman Ta inda yabi, gafe guda tana ƙarewa tsarin parlourn Kallo,ɗan madaidaci ne mai ɗauke da ƙayatattun Kayan alfarma wanda aka Ƙawata Ɗakin dashi Komai Golden and milk ne, Gidan Gaba ɗaya ya gauraye da hasken Wutar lantarki wanda lamarinki Golden Yasa Ya bada golden light ƙamshin Turaren wuta da Aka jona shi da burner sai tashi yake.

A hankali ta lumshe idanunta
Masha Allah, ta furta a fili, Karan makullin Da taji ne yasa ta juyawa da hanzari ,Saleem Ta gani yana kulle Ƙofa , ya zura Makullin a aljihun wandonsa fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

"Welcome To Your Home"

Take idanun ta suka firfito waje cikeda tashin hankali tace

"Saleem meye Haka?"

Ya ɗan raysayar da kansa

"Am not kidding, kin Kawo kanku"

Duk Girman Kan da takeji dashi saukesu tayi ta fara rikonsa ya buɗe Mata ƙofa ta tafi, Amma yayi burus, ƙarshe ma ya Haye sama inda take da tabbacin ɗakinsa ne ya barta a tsaye.

ta bishi da kallo tana maida hawayen da suka taru a idonta Tausayin kanta ya kamata, wannan sabon salon duk na menene?, Ya gujesu for almost a month sannan Ya kulleta a gidan sa, Tho yayi mata me?, *_kin manta ke matarshi ce?_* taba Kanta Answer kai tsaye, ta taɓe baki Hawayen da take ƙoƙarin maidawa suka zubo

" Lallai saleem 😢,iska na wahalar da mai kayan kara, taya kake tunanin zan Tare a haka?, Ko ka manta ban karɓi sadakina ba?"

Idan ma mafarki kake to kadaina, Babu kwanan da zanyi a gidanka, a gidan Mu zan Kwana.


Kiraye kirayen Sallahr magrib yasa hankalin ta ya tashi, ta rasa ya zata yi Nan take hawaye suka fara Bin fuskanta, ji tai kaman ta haura sama ta Zazzage Cikinta ya buɗe mata ƙofar, Amma da ta tuna abinda binshi ya haifar mata sai ta Fasa, tana durƙushe banada hawaye babu abinda takeyi, Taga ya sauko, sanye yake da farar jallabiya hannunsa , fuskarsa da ƙafarsa a jiƙe alamar Alwala yayi, idanunsa ta kalla ƙirjinta ya buga ya kara girma da kwarjini a idanunta, Ayyan na biyedashi hannunsa riƙe da lollipop Yana lasa.

Tana zaune ta zabga uban tagumi, idanunta yayi rau rau kaman zatai kuka, yunwa takeji kaman ana kwashe yan hanjinta.

"Malam me kke nufi?, Ka buɗe min Kofa na tafi"

Tayi maganar Cikin ɗage murya, idanunta na cigaba da kawo ruwa , hannayensa duka zube a aljihu ya daidaita Tsayuwan sa yana kallon kwayar idonta da hawayenta Suka daɗa ƙawata Shi

Sama ya nuna mata da yar yatsarsa ɗaya, ki hau sama, Zakiga 4bedrooms na Biyu ta ɓarayin Hagu shine naki.

Ta ɗago watery eyes dinta ta zuba su cikin nasa wato har ɗaki gareta, wanda kallon da tayi masa ya haddasa Masa wata faduwar gaba, ya kauda kai yana fadin

"Please bar kallona haka, Karki karya min alwala, Boy Let's Go ... Sai Mun dawo"

Ya karashe maganar da jan Hannun Ayyan suka nufi hanyar fita Ayyan na faɗin

"Bye Mum....."

Saurin tarar Gaba shi tayi, cikin matsanancin Tashin hankali Hawaye na zuba a idanunta


"Don girman Allah Saleem karka min haka!"

Ya tsareta da Sharp eyes ɗinsa masu haske

"Kar In miki ya wifey....?"

Yanda yayi maganar babu alamar Zai tausaya mata, ta lumshe ido hawaye suka Zubo saman Kuncinta.

"Menene amfanin Zamanki a gida da Aurena akanki?, Ni kadai nasan Halin da nake ciki, ke mace ce kuma bakisan Rayuwa ta ba....,ba Lallai ki fahimci halin da nake ciki ba, Amma Rashin mace a rayuwata ba karamin Illa ya min ba"

Yayi shuru tausayinta na Ratsa shi, Amma da tasan halin da yake ciki da sai ta zubar masa da hawaye, Muryar sa a raunane yace

"Na san na rasa mahaifiyata, idan nayi Sake kema rasaki zanyi, na bar garin ne so that I'll clear my head, Sannan na baki Lokaci ki dawo hayyacin ki bana so na Takura miki a lokacin da kike cikin damuwa, bayan wannan Ya kike so nayi da rayuwata?.

Shuru tayi ta kasa cewa komai, shi kuma ya Buɗe kofar ya fice ya kulle ta waje, sulalewa tayi tana kuka Tausayin Kanta ya kamata

Bai jima sosai ba ya dawo, hannunsa ɗauke da ledar Vingo Restaurant,Har Yanzu tana durƙushe a inda ya barta, ya zauna bayan ya ajjiye ledar, wajan deep freezer yaje ya ɗauki fresh milk da cups ya dawo ya zauna, a cup ɗin ya tsiyaya idanunsa akan ta yana dubanta yace "kinyi sallah?"

Kai ta gyada masa alamar "eh"

Ya taɓe baki don baiga Alamar ta motsa daga yanda ya barta ba.

gefenta ya zauna ya jawo plate din gaban su zuba musu Fried Rice Dake ta faman tashin ƙamshi, ga Fried Chicken Sai Walƙiya yake yana daukar ido, take taji Ta haɗiye wani Yawo ,hadi da lumshe ido, ya saka spoons Biyu aciki ya tura plate din gabanta yana cewa
"Let's eat"

Bata dagoba tayi banza dashi, Ayyan kou tuni ya dau Spoon daya ya fara kai abincin cikinsa, ji tayi ƙamshin abincin na kokarin tayar mata da kwantacciyar yunwarta,yan hancin cikinta suka motsa suna son a Basu nasu hakkin ,Amma ko kallon Abincin batayi ba Illa ma sake ɗaure fuska da tayo.

Ganin taƙi kulashi yasashi debo abincin a spoon yakai bakinta, sai Yanzu ta Dago ta kalleshi for a second saikuma ta kauda kai tana taɓe baki

"C'mon open up " yafada yana sake kusanto bakinta da abincin , Wanda hakan ya sake sanya cikinta hautsinewa ƴaƴan cikinta suka nufa, kauda kai tayi tana tana taɓe baki da cewa
"A ƙoshe nake"

"Malama Buɗe Bakin ko in matse Mutum in ma Mutum ɗure"

Saka haɗe rai tayi taba janye fuska, ganin yana sake danna spoon ɗin a bakinta, ta ture Hannunshi da fadin

"Da gaske nake na qoshi"

"Ɗanki na kallo, is either ki Karɓa ta aminci kafin na baki ta Tsiya"

Taja yar gajeren tsaki tare da Mikewa zata bar wajen ,ya jawota ta faɗo jikinsa yayi pulling dinta ajikinshi sosai har tana jiyo Ɗumin jikinsa.

Ta waro idanuwanta in shock, Zuciyar ta na racing, tasa hannu tana tureshi

Akaron farko rayuwarsa da ya tsinci kansa cikin shock din dabaita tsammanin jiba Koda a wutar lantarki ne Dan wanna yafi wutan lantarkin

Abinda yakeji yafi karfin kansa ,da ƙyar yayi hanzarin Saita Natsuwarsa yana maida Spoon Din Cikin abincin ya Lumshe idanunsa yana ƙoƙarin yakice kasalar dake ƙoƙarin dirar masa

"Kina jin Yunwa,ki nutsu...kici Abinci" yafada cikin muryarshi data fara chanzawa,Atsorace take tureshi tana kallon yanda tsigar jikinta ke tashi, kwantanttun gashin fatarsa Summmimmike

Ta kauda Dubanta daga gareshi tana sauke numfashi, murya a kasalance tace
"Ka kyale Ni zanci"

Sakinta yayi kadan ya maida hannunshi ta bayanta ya rungumeta yana sauke Ajiyar zuciya, ta gefen Ido ta saci kallon Ayyan da Hankalinsa ke kan abincin da yakeci ko kallon Su bayayi da Alama shima yunwa yakeji sosai,

Gajiya tayi da ture Hannayenshi ta lafe a jikinshi idanunta a lumshe tana sauke ɓoyayyen ajiyan zuciya, wani baccin mai cike da natsuwa na Neman ɗaukan ta.

A hankali yayi tapping bayanta ya rada mata a kunne

"Wake up and eat babu kyau kwana da yunwa"

A hankali ta ware Gajiyayyun idanunta, ta mike zaune bayan ya cire Hannunsa a bayan ta, ta dau Spoon ta fara ci tana yatsine fuska, shikou ya bita da ido yana kallon yanda take ci tana yatsine fuska kaman an mata dole

*Aeeesh*

Yana Fita ta faɗa Ban daki tayi wanka sannan ta nufi dakin Goggo, Goggo na kwance ta saita Radio wayarta taga shigowar ta kaman An jefota

"A'a yar nan Saukan yaushe"

Aeeesh ta bata fuska

"Tun dazu, waike Goggo yaushe zaki koma ne?,nifa na gaji da ganinki, haba Na haihu har na fita wanka gaskiya ya kamata ki koma"

Goggo ta mere Baki tace

"Ja'ira dama ai ba Zamanki nake ba, Don haka zaman gidan nan daram babu inda zani"

Aeeesh ta jinjina kai

"Tabdi, Allah in naki zamanki a Gidan nan da kanki zakija kafarki ki fice.."

Har dare Aeeesh na dakin Goggo sai faman tsokanar ta take, tare suka shiga Kitchen Goggo ta ɗumama tuwon da ta tuƙa da rana don Deejah Indomie ta dafa Goggo tace a ci Lafiya.

Suna zaune Aeesh Ta baje sai saka loma take Don rabonta da Tuwo har ta manta, Saida takai loman tuwo sannan tace

"Old woman Ina son Magana dake"

Goggo ta dangwali miya sannan tace

"Ina jinki"


"Wai da gaske Bake Kika haifi Ammie ba?"

Tuwon da take kokarin kaiwa bakinta ya Subuce ya fadi cikin miya, cikin in Ina tacd

"Wa..ww..waya gaya miki wannan Maganar?"

Aeesh ta tsareta da idanu wondering yanda maganar ya Tsorata ta

"So its true?


"Indo....gaya Min a Ina Kika San wnnN Maganar?, Ko ammien ki bata San Cewa bamu muka haife ta ba"

Goggo ta Fada Muryar ta na rawa
A takaice Aeeesh ta bata labarin abinda Surrey ta gaya mata , Goggo bata ji mamaki ba don Tasan halin Faisal sarsi, ba Iya kisan Kai ba zaiyi abinda yafi hakan Ma, akan Ammie taji mamaki da ya tsaya iya haka ma, hawaye ne suke zirya a idanunta abubuwa da dama na dawo mata, Aeesh ta cika da mamakin dalilin Hawayen Goggo, kuka Takeyi sosai

Har dare Aeeesh na zaune a Parlo Goggo taƙi tafiya , Goggo ta kalleta cikin Mamaki tana goge kwala tace

"Bazaki tafi ba?"

murmushi tayi mata tace

"Anan zan Kwana, Yau kwanar Deejah ne"

Goggo ta jinjina kai tana jan numfashi.
"Ya kamata ki tafi ki barni nima na kwanta"

Aeesh ta jinjina kai jikinta duk yayi sanyi ta Miƙe don harga Allah itama baccin tkeji sosai, Muryar ta cikeda bacci tace

"Night" Goggo tace "mu kwana lfy" Miƙewa tayi a hankali a hankali ta fice daga ɗakin.

Ashman na bedroom ɗin Aeeesh tun ɗazu yake zaune yana jiranta.

Bakinta d'auke da sallama ta shiga yana zaune bisa sofa, System dinshi akan lap dinsa, ta yi tsaye a jikin qofar tana kallonsa ba tare da taƙarasa inda yakeba.

Shima bai ko kalli inda takeba.
Tana tsaye har ya gama danne dannenshi,Bayan yagama yatashiga toilet ya shiga ya dade sanan yafito sanye da bathrub jikinsa na ɗigar ruwa alamar wanka yayi ya zauna gaban mirror ya shafa mai sannan ya kwanta tare da jan blanket ya rufe jikinsa ruf amma aƙasan ransa sam baiji dad'in yadda ya shareta ba.

Itama Ranta ya sosu da barin iskan da yayi da ita amma kuma sai tayi mishi uzuri ƙila Deejah ce ta buga masa hauka, aikou ta cinka daidai, Don yanzu ma kacakaca ya mata kafin ya shigo ɓarayin ta, don cewa tayi bai isa ya kwana wajen Aeeesh Ba, yau Ranar ta ce.

Ahankali ta tako zuwa bakin bed din ta zauna tasoma magana cikin sanyi

"Ahky don Allah kayi haquri ka koma ɗakin matarki...."

Kallon da ya watsa mata yasa ta hadiye maganar tana Turo baki

Ya ture bargon da yarufa ya tashi zaune yana cigaba da auna mata wannan kallon tayi saurin sauke kai tana cigaba da turo bakin, ranta a ɓace ta Haye gadon ta kwanta chan ƙuryar gado tana gunguni

" _Mutum da matarsa amma ya nace sai ya liƙewa Uwar wata_ "

"Me kikace?"
Taji Muryar sa a bayanta, ta turo baki tana juya masa baya, taja blanket ta rufe jikinta

"Cewa nayi a daiyi addu'a kafin a kwanta don gujewa mafarkan gauraye"

Ya cije lebe yana girgiza kai

"Dole in kawo mai ruqiyya yayi miki ,don na lura matsalar ki bata asibiti bane"

A hankali ta juyo ta kalleshi Cikin sanyin Murya tace

"Ahky don Allah Kafita, ka tafi wajen matar ka, na saba Kwana Ni ɗaya, bazan iya kwana da ƙato a ɗaki daya ba"

"Nine ƙato...?'

Ya Fada yana kallon Fuskar ta, ta taɓe baki

"Ahky kai ai kafi ƙato"

Ta cikin bargon ya lalubo Hannunta ya riqe, cikin dushewar murya tace

"sakeni....!"

Ƙin sakin ta yayi,yana mamakin tsaurin idon nan nata.

"kaga malam banson Ithkanci, dan Allah ka cikani ka fita"

A hankali ya cika ta, da gyara kwanciyar sa

"Kayi hakuri Ahky, Amma wallahi har yanzu Zuciyata bata gama aminta da auren nan ba,An ɗaura aure shaidu sun Rasu, na yarda da wannan , Amma har yanzu banji ƙamshin sadaki na a hannuna ba, a lokacin nan bani kayi a matsayin wedding gift So I gave someone as a gift, da ka fito fili ka gaya Min Sadakina ne kuma an ɗaura mana aure, Bazan jefa zuciya ta cikin Halaka ba, don Haka Yanzu Dole sai ka Bani Sadaki na tukunna"

Kallon ta yake idanunsa sun kaɗa Sai kuma jikinsa yayi sanyi, Sosai yaji ba daɗi, da gaskiyan ta Baiga laifinta ba don ta nemi hakkinta Tunda zurfin cikinsa yaja masa.

Ta hararesahi

"An daina auren bashi, ka koma wajen matarka wacce Akayi aurenta da ƙaida"

Ya jinjinaa kai

"Okay.. "

Ya faɗa a takaice yana lulluɓaa kansa cikin bargo.

"Ka tashi ka koma wajen matarka".

tace cikin had'e fuska.

Banza yayi mata, yana jinta sai gunguni take yi a haka har barci ya ɗauke shi, itama kwanciya tayi ta matsa chan ƙuryar gado zuciyarta cikeda Tausayinsa, Haka kawai don Bala'i ta birkita Lissafin bawan Allah, Mutum da matansa har biyu ta maisheshi gauron Dole.

*Maryam*

Ranar kwanar tayi tana kuka ta kira wayar mama, amma tun kan tayi magana ta rufeta dafada daga zuwa Siyayya tabi miji sukayi tafiyan su.

Dama tsoronta kenan, fargabar datakeyi kenan gashi yasa mama ta fara ganin laifin ta.

A ranar kwana tayi tana kuka, tsabar baƙin ciki a Sitting Room ta Kwana, taƙi shiga ciki, dukda rarrashin da yayita Binta dashi.

Shi kou Sosai ganinta dayayi yayi sanyaya zuciyarshi, dawowanshi kenan Daga NORWAY ,firgicin zancen da yaji daga bakin abban nasa yasa yasa ya fita a hayyacinsa ya tsani kansa da ma kasar gabaki ɗaya, wajen abokinsa *yin Gonzales* tare sukayi karatu a Turkiyya,ya tafi a NORWAY iyayensa yan chan ne, a nan Gonzales ya samu aiki, Watan Saleem ɗaya a Wajen shi, kullum Gonzales cikin bashi shawara yake akan gudun dangi bashi ne solution ba ,ya koma cikin family ya nemo mhaifiyarsa tunda bata mutu ba, ya nemi yafiyarta zata yafe mai, kuma ya maida matarsa domin rashin mace a rayuwarsa babban Matsala ce, da wannan shawarar ya baro NORWAY, da daren jiya jirginsu ya sauka a Nigeria , Ya fito siyayyan foods stuff ne don babu komai a gidansa, shine Allah ya haɗa shi da Maryam.

5:00 ya fito jikinsa sanye da Green pyjamas masu kyau, hannunsa zube cikin Aljihu, a hankali yake tafiya kamar mai tausayin ƙasa har ya iso Sitting Room, ɗakin ya ƙarewa kallo kafin ya shigo ciki without making any sounds ya tako ciki sosai.

kwance ya ganta bisa doguwar Golden Royar chair ta lulluɓa da mayafinta, a hankali ya zaune kusa da kanta tare da zame mayafin da ta rufa dashi, tun daga kan yatsun ƙafarta yake kallonta har zuwa ƙirar jikinta, a hankali ya sauke idanunsa akan fuskarta dake a yatsine alama batajin daɗin baccin da takeyi ,fuskarta yake kallo a kwaɓe sai hawaye dake zuba , lumshe idanunsa yayi kafin ya buɗe a hankali ya daga hannu ya shafa suman ta dake buɗe sakamakon zmewan da Ɗankwalinta yyi.

Cikin Takurarren baccin da takeyi taji hannunsa cikin sumanta, a hankali ta

Please Login or Register in order to submit comment