Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a lumshe.

"Ehen What are you saying"

Sake Lumshe idanu Maryam  tayi tana qoqarin saita muryarta

"You have a Patient at labour Ward"

"Meye Amfanin ku Midwives?”

"We did our Possible best”

"Ohh wow then Episiotomy her vagina and Force the baby Out"

"Dr bazai yiwu ba, Idan Munyi mata episiotomy zata iya samun Bleeding which can lead to death of both The mother and the babies "

"What's Her condition?"

"She's having Placentaprevia Yaran Da Placenta dinta Suke neman Fitowa At the same time, and she's Having Multiple Gestation,Both babies have The same placenta"

Tashi tsaye yayi ya tako ya zagayo gabanta cikin takun qasaita.

"Really? Kina son Ceton Rayuwar ta Right?,Nifa Namiji ne me kike zaton zan iya?,mace ne yafi chantanta da ta duba mace, Amfaninku kenan A health Profession"

Hadiye wani Abu daya toshemata maqoshi tayi kafin tace

"It's Okay, let me go I'll write Report on what happened In yaso Koda wani abu ya faru da ita a ɗora laifin akan ka, daga ƙarshe A kwace License ɗinka"

Banza yayi da ita Gabansa na dukan uku uku tabbas yasan babu makawa idan Ta rubuta report akansa kuma aka tabbatar da Laifinsa Dole a kwace License ɗinsa daga nan shike nan babu shi babu aiki har abada ,karatun da yayi duk sun tashi a banza.

Shi ya Farayin gaba ta biyo bayansa Yana Kunkuni tareda cewa

"Mutum tasan bazata iya haihuwa dakanta ba Meyasa Tayi Auren?mtsww..."

Kafin su kai Labour ward din har Anyi booking Matar For C.S don Zuwa wannan Lokacin Cervix dinta ya Fara rupturing, Tsaki yaja Ya zura Handgloves ɗinsa Yanata Faman Masifa, aikam cikin Sa'a kuwa Mintinan goma da zuwanshi yayi sa'ar Ciro Kyawawan yaran Biyu tareda Placenta ɗinsu Batareda Anyi mata Koda Episiotomy ba.

Mamaki sosai ya kama Sisters Dinda ke nan ,tun jiya Suke Ta kokarin Ganin Sun karba haihuwar Amma abin yaci karfinsu basu taba tunanin matar zata iya haihuwa dakanta kuma ta rayu ba saboda Situation dinda ta shiga Yyi Critical dayawa.

Kafin Saleem ya baro Ward din Kam Saida ya shaƙawa Patient relatives din Kalar tasa Halin don Cewa yayi babu wanda Zai shiga Ward din da Dattin Kaya is either Su koma gida Su sauya Shiga Ko kuma Su Tsaya a wajen har a Sallamota sai Su koma Gida Tare, Zarginsa Sukayi tayi bayan tafiyarsa babu yanda Suka iya dole subi yanda akeso Gida suka koma suka sauya Shiga zuwa kayan sallarsa sannan suka dawo don duna babies Lokacin har an kaisu S.C.B unit don Gyarasu...

Hankalin Aareef sosai ya gaza kwanciya tun jiya Ganin Bata dau Wayarsa ba kuma ya tura mata Text message batayi masa Reply Ba.

Hakan yasa ya shirya da sassafe yyima Asibitin N3p dirar Mikiya Wani cikin Security dinsu ya aika ya kirata Babu jimawa Sai gata ta fito Mamaki sosai ne ya kamata don bata taɓa kawowa a ranta zai iya biyota asibitin Ba sbd zancen kuɗin ba.

Roƙonta ya shiga yi yana haɗata da Allah akan  Ta bashi Kuɗin kudin ne kaɗai best solution dinsu,Kuma shi kadai ne zai Iya tabbatar da gamuwar su ta har Abada, Sosai ya bata Tausayi Ganin yanda yake hadata da Allah Da ace yanada kudin ne da Tuni ya biya an wuce gurin .

Cewa tayi ya jira ta jirata ta Shiga Ciki Babu jimawa sai gata sanye da Dogon Hijab dinta kafaɗarta sagale da ƴar jakarta.

Fitowa tayi tana Takawa a hankali ji tayi an kira sunanta ta baya

"Besty"
Saurin Juyowa tayi tana Murmushi.

"Besty me ya faru?, Are You Off"

Lumshe Idanunta tayi tace

"Am not Off , Fita zamuyi da Sadauki na zan dawo before closing"

"Besty...."

Daga mata hannu Aeesh tayi ta dakatar da ita da cewa

"Reey Please Karki ce komai let me Go!"

Tana Ida Faɗin haka Tayi Gaba batareda ta jira Ta kara cewa Komai ba, da Kallo Reey ta rakata tana Ayyana Abubuwa da dama a ranta sosai Ƙawarta ke bata Tausayi,Ta zurma da yawa cikin Kogin Soyayyar Aareef ba ƙaramin aiki bane tsamota daga ciki.

Machine Ɗinsa Da yazo dashi ya burga Ta hau baya Suka fice daga harabar Asibitin ,Ashman dake kallonsu ta Windown Sama Ya sauke Ajiyan Zuciya yana dan cije Lips dinsa a hankali,tun zuwansa  ya gansu Amma bazai iya takura ta Akan Abinda Takeso ba, Idan Lokaci yayi zai bayyana mata Sirrin dake tsakanin Su a wannan Lokacin Kuwa dole ta rabu dashi ko taƙi kanta.

Kai tsaye Banki suka nufa, Business card din Da Aaash ya bata ta dauko Ta ciro dubu ɗari biyar Cikin tsananin Tsoro ,Tunda take bata taɓa ciro kudin da ya haura Dubu dari ba,Hakan yasata jin wani iri.

A sanyaye ta miƙa masa Kudaden bayan sun fito, Idanunta na tara Ruwa

Ahankali ta dago idanunta ta zubamashi, gabanshi ne yafadi ganin kallon tsantsan Soyayyar datake mashi wanda ya gaza Boyuwa cikin kwayar idanunta.

“Arrow Pls Ka Riƙeni Amana,You Are All I have"

Washebaki yayi yana sake Rungumo Jakar da ta bashi yace

"Don't worry Masoyiya, inshallah In the next Five months war haka kin Zama tawa"

Gyaɗa Kai tayi a hankali Shi kuma ya dora da cewa

"A'isha tah...kece nake so da zuciya ɗaya kuma Dan Allah ba don kyawunki ko kudin ku ba ,Don Allah nina ki Soni ba don hali na ba ,ina Sonki so na haƙika Sonda ban taɓayiwa ko wace mace ba a duniya ,Kece tawa Tauraruwar mata ,Daga ke kyawawan Mata suka ƙare kece mai kyau kyau na asali wanda da babu mace mai irinta a Duniyar nan , inda Zan faɗa miki ki yarda da sai na gaya miki a wannan Duniyar ta mu ta masoya idanuwana basu taba tozali da Mace me kyawun fuska da na Zuciya kamar ki ba"

Wani murmushi ya kufcema Aeeesh kallo ɗaya zaka mata ka fahimci Irin tasirin Da kalaman sa Sukayi a zuciyarta.

Cigaba yayi da faɗin

"Kece daga ke aka Gama ,Kyawawan Mata suna kasan ki ne kece babba a saman su ,ki tausaya wa Rayuwata, Ki Soni don Allah Domin inaso na rayu dake har karshen rayuwata, Mu zama tamkar wani sarki da sarauniya mu gina fadar masoya, wacce take Cikeda Daula mai farinCiki da Annashuwa da Jindadi ,Duk duniya babu wacce nakeso tamkar ke ,Ba'ayita ba Kuma baza'a yita ba, ke kadai nake so ,Kece dai ke kadai Ke din ce ina Sonki"

*Kano*

Zumbur Abba ya miƙe Cikin Razana

"What Saleem Again?, Saleem din ne ya ce Miki Yana son Aisha?"

Murmushin Kasaita Umma saude tayi kana tace

"Eh Tabbas Saleem ya kamu da Son Aeesh Kuma Yana Shirin yin Komai domin ya kasance a tare da ita"

Wani irin Zufe ne ya keto wa Abba dukda Dakin Akwai qadatar AC Amma Hakan bai Hanashi Fidda Ruwan Fuska ba saboda tsananin Razana A fusace yace

"Saleem bazai Auri A'isha Ba, nayi masa Mata, Bai isa ya auri A'isha ba, Akan Aeeesh Baffansu Abubakar Imam ya rasa Rayuwansa, akanta ɗana Sufyaan ya fara daga Mn murya abinda bai taɓa Mn ba tun tasowarsa, Ga Wannan yaron Aareef da mukayi masa Alƙawarin Aurenta ,Bazan amince da wannan batun ba ,ki gayawa dan ki ya haƙura da ita na riga nayi mata Miji...!"



Nayi Gabas🚶🏻‍♀️

Bintou ✍🏼

22jan
♡ ㅤ   ❍ㅤ     ⎙      ⌲
ˡᶦᵏᵉ  ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ   ˢᵃᵛᵉ   ˢʰᵃʳᵉ
[7/18, 9:28 PM] chubby number: 🫀🗡️ *_Wuƙa a Zuciya_*🫀🗡️

( _Bleeding Hearts)_


*015*


A fusace Umma Sadiya ta miƙe tace

"Iyye Lallai Alhaji ka isa, shiyasa Kake Gaya Min Babu Sugar Tho zanga Wanda Ya Isa Ya Hana Auren Saleem Da Aisha "

Sosai Alhaji Naseer ya Tsorata da Ganin yanayin Matar tasa ,yana Tsoron kome zai Bata mata rai Amma har Ga Allah bayajin zai iya Aurama Ɗansa A'isha ba ,A'isha Itace Rayuwarsa Yana Tsananin Sonta Kamar yanda yake don rayuwarsa ,Yanajin koda Zai rasa Ransa ne bazai yarda wanin su ya Aure Ta ba, Ko Aareef Dinda yaba Izinin cigaba da neman ta ba hakanan ya barshi ba ,ya shirya masa Tsuggu kala-kala wadanda zaisa Ya fasa Aurenta da kanshi batareda ankai ruwa nesa ba.

Saita kansa yayi sannan Ya dubi matar tasa Daketa faman Xazzaga buhun bala'i yace

"Na Riga Na yanke hukunci idan Nine Mahaifin Saleem , Bazai Auri A'isha ba kuma na gama magana "

Dariya sosai Umma saude tayi harda tafa hannu

"Hhe Lallai Dr Ka Samu Courage,Ni zakay wa Gorin haihuwa?, da Alama Ka manta ko Ni wacece?, ka kuma manta matsayin Saaleem a gareka Ka kuma  manta deal Dinda ke tsakanin mu Akanshi You Forgot Every thing tho Idan Ka manta bari In Tuna maka.....!"

"Saudat....!"

Abba ya dakatar da ita da karfi, Ɗagowa tayi Ta kalli Cikin idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ,Shima kallonta yake da Rinnannun Idanunsa Da kallo ɗaya zakayi masa Ka fahimci sauyawan Launinsa Nada Alaƙa da Yunkurin rabasa da Ake Shirin Yi.

"Shekaru Talatin Kenan Da Muka Kulla wannan Yarjejeniyar a tsakanin mu,I have been Suffering on It for so long ,I can't Continue purnishing Myself On Something I don't Know ”

Dan Kauda kansa Yayi daga kallonta Yana dan cije Lips

"So Cancel the deal"

Matsowa Umma saudah tayi gab da dashi ta dafa kafaɗar sa  da hannaye biyu tadan matso Fuskar ta Gab da nasa cikin rada tace

"Ka fara Shirye Shiryen Auren Dan HUSSAINA da Ɗiyar Hassan ,If not Daga kai har almajirin dan Uwanka Hamza sai kunyi danasanin zuwanku duniya, Nasan komai ...!, so Have A nice day"

Ta qarashe zancen tana kalkadamata yatsu sannan ta fice A fusace

Binta da kallo yayi har ta fice sannan ya saki wani murmushin takaici wanda yafi kuka ciwo...

_Naseer Kaga abinda kaja ko? Kaga abinda kwadayinka da Son Zuciyarka yaja maka ko?_' Duk acikin zuciya take wannan zancen

Jingina yayi da bango yacigaba da juyawa ya maida idanunsa ya lumshe, zuciyarsa fall da baqinciki da Damuwa hadi da nadamar abinda ya aikata A shekarun baya da bai aikata Abinda za'a zarge shi ba da babu wanda Zai alaƙantasa da Mugun Abu, Har ya Bada 'ya'yansa Don Rufe Boyayyar Sirrin!, duk shi yaja ma kansa .

*Aareef*

Tun a hanya ya Fara Kashe Kudin da Aeesh ta bashi,  Kai tsaye Central Market ya nufa , Babban Shagon Siyarda Manyan Wayoyi ya Nufa ya bada Wayarsa Ƙirar iPhone 11pro max yayi ciko Aka bashi iPhone 13.

Yan Sauran Chanjin Da Suka Rage Kuma ya siyo Rabin Buhun Shinkafa da kayan Miya ya tari Adadaita Sahu ya kai masa Har gida,Cikin Kayan Abincin da ya siyo ya deba ma mahaifiyarsa Kadan Ya kaimata,Aikam Yasha sa Albarka Har saiDa Yayi kuka, Lallai mahaifiyarsa Na cikin wani hali yau Akalla Kwananki Uku kenan Bata samu tasa Wani abu a bakin ta ba, Sai ya kawo take samu taci ,Shi kadai Gareta batada Kowa, Gashi shi din in ya bar Gidan baya Dawowa Sai ya dauki akalla kwanaki Hudu ko biyar bai dawo ba ,Kafin nan Mahaifiyar tasa Ta gama Galabaita, Tsananin Yunwa Kesata fitowa Sometimes Tana Barar Abinda Zataci akan Titi, Gidan da take zaune Ƙaton Gida Ne sosai wanda Mahaifin Aareef ya bata Yace ta zauna tareda Danta ,bai yarda Wani bare Ko bako Ya shigar masa Gida ba dama Tun Lokacin aurensu Danginta suka Gujeta,ya kuma ce idan yaji labari sai ranta yayi mugun Ɓaci, Tasan Halinsa Shi yasa Bata Gayyatan Kowa, Shi kuma ɗan nata kwalli daya da Allah ya bata Yaji bazai Iya rayuwar Yunwa ba ,ya tattara inashi Ya koma Gidan abokai, Nan yake samun Naci, idan akayi Sa'a Ya samu Abu mai tsoka sai ya yankar mata nata rabon Ya kai mata .

To yau Banza ta faɗi a kasuwa ,Kudin da Aka bashi ya Bada Domin a samu Maslaha Bai bar Na ukunsu yaga Fuskar kudin ba ,Tun kan Ya kai gida Ya gama sheƙe su, Abokansa Bash da Kamal Kam Yau aljihunsu ya huta, Sosai sukayi mamakin ganinshi da kayan Abinci Koda Suka Tambaye shi Ce masu yayi Matar da zai Aura Ce ta basu ,Da yake sun san Aeesh da Kyauta kuma Family dinsu nada Kudi Sosai Sai Suka watsar da Tantamar da sukeyi akansa .

Washegari Da sassafe Yana Shirin fita yaga Kiran Abba,Sallama Sukayi Bayan Gaisuwa Na Mutunci da sukayi Abba Ke Shaida Masa Da cewa Ya haƙura da Aeesh yayi mata Miji , sosai Yaji ba daɗi Har ya kasa Riƙe Bacin ransa Ya bayyanawa Abba Bazai Iya Haƙura da ita ba, Wasu Maƙudan Kudade Abba ya yanka yace Next week inshallah Zai shigo Kaduna tareda Iyalansa Zai Bashi Kudaden shidai Burinshi Saleem Ya janye Batun Auren Aeesh ,Habawa daga Jin Zancen Kudi Mutumin ya tsure Yace ya haƙura da Aeesh har Abada ,Amma don Allah kar a gaya mata, Alƙawari Abba ya dauka masa Dama Babban Burinsa Y yarda ya Amince kuma ya Yarda sauran ba mai wahala bane.

*Aeesh*

Tun randa Ammi tayi mata Magana Akan Aareef da Aashman ta rage Kula Ashman A gabanta, idan yazo gidan Iyakarsu magana sama sama, Abinci ma in zasuci batare Suke ciba,in a gidan ya kwana Bata shiga dakinsa, a zahiri ta Rage alaƙa dashi Sosai amma abinda Ba’a sani Ba ,Cikin Wannan kwanakin Wani sabon Mugun Shaƙuwa ce ta daban ta shiga tsakaninsu domin Kuwa t gaya Masa Umma ce bata Son Yawan ganinsu a Tare, Shine ya bata shawarar Su Yarda da Suggestion dinta,Su rage yin Komai a gabanta ,Amma yanzu Shi ke Tashinta daga Bacci koda Ba a gidan Ya kwana ba tana jin Ringing ɗin wayanta tasan lokacin tashi yayi, idan Weekdays ne Tare suke Shiryawa, Yana fitowa wanka Zai kirata suna Shiryawa Suna Videocall Har su gama Tana Ida Shiryawa Kuwa take fita yanzu ta Rabu dayin Breakfast a Gida Sai taje asibiti take karyawa.

Yana Rigata fitowa Sai ya jirata a bakin Titin Bayan Layinsu ya dauke ta a motarshi Su biya Ma Reey Sannan Su tafi, Duk Abinda Sukeyi Saleem na sane Kuma abin na mugun bata masa Rai sosai , amma Ya dau Alwashin Tarwatsa Alaƙar dake tsakanin Su.

Yau Friday kaman Yanda Abba yayima Aareef al'kawari Tun Monday ya Biyashi Akan Ya bar batun Auren Aeesh kuma ya amince,Amma babu wanda Yasan Da batun sai Abba da Matarsa Saude, a yau Abba ke shirin Komawa Kano, Amma Taron Da yayi Niyyar Gudanarwa A Asibitin Aash yasa Sai Gobe da Safe zai koma ..

Tun  ƙarfe Bakwai na safe garin ya fara haɗa gagarumin hadari, wanda alamominsa suke nuna zai zubda ruwa mai yawa.

Duk da yana a Theatre hakan bai hanashi fahimtar canjin da garin ke cikiba, miƙewa yay zuwa jikin window ɗin Theatre ɗin ya leƙa, tabbas hadarine mai ɗauke da alamomin iska kuma, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana huro iska a bakinsa, yana da sauran surgeries, gashi bayason ruwannan ya samesa a Department Dinnan Yana so ya leƙa Paediatric ya Duba Wasu yara.

Barin Window ɗin yayi ya koma Dressing Station, kayan Jikinsa ya Cire Ya sanya Na Shiga Surgery kafin yashiga Ciki da hanzarinsa irinna masu cikakkiyar kuzari lafiya.

Mintuna Arba'in Tsakani sai gashi Ya fito tareda Wasu Surgieonz Yana cire Gloves Dinsa , Attendant Din Gurin ne ya tayashi Cire Surgical Gown dinsa ,Kai tsaye Wurin tap ya nufa yasa ma Hannunsa Sanitizer ya Wanke.

Kai tsaye Office ɗin Abba ya nufa, dan tun kafin ya Shiga Surgery ya aiko kiransa, bai fita bane saboda wani emergency Surgery ne dashi.

   Sallama yayi a ƙofar Office ɗin kafin ya shiga, su uku ya iske a office ɗin, gaba ɗayansu kuma suna cikin manya-manyan Likitoci.

gaishesu yayi ,Gaisuwan girmamawa a garesu, ya miƙama Abba takardun yana faɗin.

“Sir ga Files Din Yusuf Dinda Ka bida , na kammala, kayi haƙuri da lattin da nayi, Aikin Na tsaya emergency surgery ne”.

“Babu damuwa Suff Dama Dr khaleed ya Gaya min hakan shiyyasa ban damuba, duk da kuwa jiranka muke”.

“Sorry Sirs”

Ashman ya faɗa yana maida kallonsa ga sauran mutane biyun dake zaune .

Ɗaya a cikinsu ne yay magana fuskarsa sam babu walwala, cikin tsare Ashman da idanu yace,

“Sufyan Naseer  ko?”.

  Cikin girmamawa Ashman yace

“Yes Sir!”

  Zama wancan ya gyara sosai yana fuskantar Aash, ya fara magana cikin dakiya da kuma tsuke fuska.

  “Sufyan kai likita ne, Likitan Ma Medical Surgical doctor Mai Experience biyu, ƙwazonka da ƙwarewar aiki ke ƙara maka ɗaukaka , kamar yanda mahaifinka ya baka yarda a baya ya dauki Katafaren asibitin nan ya damƙa maka yanzunma munason ƙara baka a kan wannan aikin, dan tabbas inaji a jikina zaka iya Rike amanar da zan baka, saboda kanada nagarta irin ta Mu'minai na ƙwarai, Amma da Alama kana Shirin Watsa Mn Kasa a ido, ya kake ganin zaka iya kuwa?”.

    Ashman  dake tsaye a tsume fuska sam babu fara'a yayi ajiyar zuciya yana sake tsuke fuskarsa, Sam Bai Fahimci inda zancen Mutumin Ya nufa ba, Bai gane nufinsa Ba,Amma da ya ɗago ya dubi Abbansa Sai Ya dukar dakai yace,

“Sir insha allahu ina fatan hakan, sai dai bazan zama mai alƙawari akan abinda bani da masaniya akai ba"

Gyara zama Na farkon yayi

"Nine Mahaifin Khadijah Matar ka to be Inshallah"

Dan russunar da kai Ashman Yayi Cikeda Girmamawa Yace

"Welcome sir"

Mutumin ya cigaba da cewa
"Ni Munyi Aiki tareda Mahaifinka a shekarun baya,naji anyi Kisan Kai a asibitin nan Kwanakin Baya Kuma kaida Cousin ɗinka kune Shaidar gani da ido Right"

Wani Dumm kan Ashman Yayi yaji Gabaki ɗaya Sensories Dinsa Sun daina Aiki.

Cigaba yayi da cewa

"Bakuyi Report ba, a ranar CCTV cameran Asibitin kaf suka Lalace, Still Baku shigarda Complain ba, Ka samu Karaya a kafa tareda Mummunar hatsarin mota da yayi Sanadiyar jawo maka Ciwon Idanu baka Shigar da Report ba,Kuma ka sani as a surgeon Bai dace Kayi Aikin Theatre ba if u are not Medically Okay, You know right"

Nan ma Shuru Ashman Yayi Zufa na  tsattsafo Masa

"Kayi Min Shuru?"

Dayan Yayi magana yana kafeshi da idanu.

“Am Speechless sir"

"So now meyasa kake Purnishing Daughter ɗina?, baka taɓa lekowa gida Da niyyar taɗi ba, You don't care about her!, pls Idan baka Sonta ne ka gaya Min so that I'll take An action tun wuri "

"Sorry sir it's Not how You think B, Inshallah I'll try My possible best to make  her happy, before then ina neman Wata Alfarma Daga gare ka"
  
“Wace alfarma ce wannan?”.

Ɗayan a cikin baƙin yayi tambaya yana kallon Ashman.

Gyara tsaiwa Ashman yayi yana satar kallon Abba, Abba da shima ke kallonsa ya jinjina masa kai alamar ya faɗa.

   Kai Ashman yaɗan ɗaga masa, kafin ya maida hankalinsa sosai garesu yana cigaba da faɗin,

“Alfarma ta farko itace inason a daga Aurena Da Deejah, ina magana ne akan, Khadijah Umar your daughter, sai alfarma ta biyu kuma ku Goge zargin da kuke Mn , Nasan Aiki na Na kuma san Abinda Ya dace, Tun Kafin na kai Baffa Imam asibiti na sako jami'an tsaro cikin maganar Kuma CCTV ba daukewa yayi ba yana Nan saidai Makashin Bai bi ta CCTV ba, Yasan Kan Asibin sosai"
     

Shirun da yayi ne ya basu damar fahimtar ya kammala magana, hakan yasa su duka suka sake zuba masa ido tamkar wani baƙonsu, kusan minti ɗaya da rabi kafin ɗaya a cikinsu ya miƙe, kafaɗar Aash ya dafa yana murmushi da fadin,

“sufyan a tunaninka bamu san Asalin Labarin bane?, nope mun tsara Namu labarin ne, yanda zamu sauya Rayuwar ka nan gaba idan Kayi mana gardama, Diyar Mu ba Kaman Kowa bace You need to treat her like a princess Dole ka damu da ita Kwatankwacin yanda Kake Damuwa da Yar Uwanka A'isha koma fiyeda yanda Kake Sonta , inada kudin da zan iya kulleka akan Case Dinnan Kuma You have no way Out,My daughter is more than  a Gold to me,She love u and u must marry her , Ada mun saka Ranar Aureka nan da Watanni Biyar,Amma Yanzu mun chanza komai mun dawo Dashi nan da sati biyu masu zuwa ,Mun Gama shirye Shiryen , including the invitations"

_lallai ma tsohon nan Ya raina masa Hankali..!, me ya maida shi ne?,Lallai zaiyi Maganin Jin kan nan nasa_

Aash ya faɗa cikin Zuciyarsa.

Cikin izza da jin yakan jarumai na gaske ya ɗago kai yana kallon Abba, sai kuma ya sake wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa duka biyu loɓawa,a hankali ya maida duban sa ga Su Alh Umar da Abokinsa,

“Sir! Meyasa kakejin shakku?”

"Gudun rashin samun nasara,Gudun Abinda zaisa Ɗiyata Cikin damuwa, ina gudun kar Ɗiyata Ta gaza Samun makamancin farin cikin da take samu a Gidana, dan rashin farinCikinta  a gidan Aurenta tamkar zubewar mutuncina ne, samun FarinCikinta kuwa kimace a gareni, sannan kai kuwa ribace a gare ka, zan jiƙa ka da Kudade, sannan zaka ƙara nagarta a idon duniya harma da Manyan Wakeelan Mu, Domin Kuwa Nine na hannun daman Minister Of health na Kasar nan”.
      
“Hummm”

Aashman ya faɗa a can ƙasan maƙoshi, kafin ya kallesu gaba ɗaya cikin takaici.

“Insha allahu zan kokarta, domin Mahimmanci Wacce ta Hadani Da ita a gareni, kasan Da Wayau ake farauto mara wayau, a rayuwa, insha allahu tunda Kunyi Naku nima zan Kokarta inyi nawa , badan komaiba sai dan farauto Nasara ta gaske na dawo da ita Hanya, Kuma babu Abinda nake bukata daga Gareku, babu Abinda Kudin ku zai Amfanar Min,Idan da gaske mutuncin Diyarku shi yasa Kuka Matso da Auren Me zaisa Ku haɗa Da kudi?, A cewar Ku Kuɗi shine Matsayi ko mutunci?”

Ya fada yana Tsare su da kallo,Duk kasa Cewa Komai sukayi Don They are totally Speechless shi kou ya cigaba da cewa.

“And Auren Diyar ku bazai Taɓa bani matsayin da Allah bai bani ba, So Clear the muck in ur eyes And know the person U are speaking with,Amanar ɗiyar ku dai In Kun bani zan Karɓa"

    
“sun riga baka kuwa Suff”

Abba ya faɗa fuska ɗauke da murmushi.

  Dan russunar dakai yayi yace.

"Zan iya tafiya?"

  Sun bashi izinin tafiya, duk da kuwa maganarsa ta ƙarshe tai musu tsaye a zuciya, sam sun kasa fahimtar komai a kanta, domin dai hausace cikin hausa yayi.
          

Duk bin ƙwankwanfonka baka isa ka gane yanayinsa ba, dan fuskarsa jarumar fuskace ma'abociyar adana komai, Office ya koma.

Yana zama Yaga an turo kofa an shigo ko sallama babu, a zatonsa Aeesh ce don ita ke masa Haka in tayi niyyar Tonar faɗa.

  ƙarasowa tayi gareshi, Murmushi fal a fuskar ta.

"Fita Kije kiyi sallama"
  
Tsaki taja Ciki Ciki a ranta tace malam ka kusa Shigowa Hannu zaka gani, Saida tadanyi jimm sannan yabada izinin shigowa

Deejah ne tashigo cikin shigarta na Farar Riga da Farar Guntun hijab sannan Ash din Wando,Shigarta irin na JCEWs

Kallo daya yayimata ya dauke kai yana amsa sallamarta.

Qarasowa tayi ciki ta zauna kan kujerar dake Fuskantar Shi ta ɗora kafa daya akan daya

"Naga Alamar ba son Wannan Auren kakeyi ba shi yasa Na gayyata dad Dina a ciki, and thank God He solve everything Cikin Kankanin lokaci"

Banza Yayi mata yana cigaba da latsa System dinsa.

"Ashman Wai Meke faruwane, kabarni ina ɓaɓatu kamar wata yar iska"

inji Deejah afusace.

Ko motsawa Aashman beyiba,Illa ma Ture System dinda yayi ,Ya ƙara balancing a kujera idanunshi lumshe.

"Ashman!"

"What?!" Ya fada a tsawace kaman wanda aka tsakura.

"Wai meke damunka Ashman?" Inji Deejah cikin mammaki.

"You know what? Nakusan Cin mutuncinki a Hospital dinnan wlh, ina ruwanki dani? Spare me mana!"

Yafada afusace.

"Kaifa Zan Aura bai kamata kana min haka ba!"

Harara ya dalla mata yace

"Ba Kunyi Abinda Ranku keso ba?,Now listening, bazan yarda Da bidi'a ba, Daurin Aure kawai za'ayi ...."

Katse shi tayi da cewa

"Haba Dr Aash kodai baka Sona ne?"

Shima Dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu

" Maganar Soyayya ai babu a tsakanin mu, Aure kike so ,Zan taimaka miki na aure ki ,kuma Dole abini Babu Event ban yarda Da Rako Amarya ba, Mahaifinki dakanshi nake son ya kawo min ke!"

"Daddy na kuma?"

"Offcourse,If not ki kira wannan tsohon banzan kice nayi cancelling dinmu Ki Auri wani"

A mammakince tace

"meyasa?, kodai Mahaifina ya fada maka abinda Bai kamata bane?"

Jingina yayi da kujerarshi yana d'an jujjuyawa

"Nan da two weeks Auren mu....!,hmm you're in hot soup, I swear"

yafada yana tauna le6en qasa cikin Salo na Mutunta .

Buɗe baki Tayi Zatayi magana Ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata Ƙofa,Jiki a sanyaye ta Miƙe ta Fice Masa A office, don yanda taganshi a matukar fusace zai iya Kifeta da mari.

WasheGari

Yau ranar Saturday, as usual taje Gidan Aashman Weekend Suna Fita yawon Shakatawa.

A kasalance ta fito ta rufe motar.

Wata mota tagani a parking space din Wanda ba tasu bace,hakan ya tabbatar mata da cewa Saleem na Nan.

Tsayawa tayi tana kallon motar, Sabuwar mota ce Sosai take kyalli da Daukar ido ,tsayawa tayi tana tunanin to ta wanene?.

Wucewa tayi ta murda kofan falon tashiga da sallama.

Babu Kowa a Parlor Kai tsaye dakin Ashman Ta Nufa.

Kwance

Please Login or Register in order to submit comment