Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu suka taso suka Bambare Aeesh daga Riƙon da yyi mata Tana Kuka, tana ji tana Gani Suka Ɗaureshi ,Allah Sarki dattijon Sai Cewa yake _kome zaka Mn Bazan Baka ita ba, ita din Amana ta ce_

Mahaifin Sa da Uncle dinsa na zaune sun Kasa Hanashi dukda bajin dadin Abinda yake Aikatawa suke ba ,Amma suna tsoron tanka Masa ransa ya ɓaci,Abba kuma Yana zaune ko motsi ya kasayi banda mazari Babu Abinda jikinsa keyi,ba abin y tanka ba asirinSa ya tonu a idon Duniya.

Wasu igiyoyin Ƙarfe ne yasa Aka jona da Electric Fuse ,Suka Mannawa Baffa a Fuska Wuya da baya, ya fara jijjiga Shocking na janshi, kashe Fuse din yayi

Gabaki daya Jikinshi yayi week,veins ɗinsa sun saki sai numfarfashi yake saki a wahalce

Bamalli ya kalle Baffan Yace.

" Yanzu fa? ,zaka bani ita ne ko sai na ƙarasa ka? "

Girgiza kai Baffa yayi a wahalce yace

"Me kake Jira?,ka ƙarasani"

Wani razanannen Ihu Aeesh ta saki ta nufo Baffa da gudu tana kuka tana cewa

"A'a Uncle ,bazaka mutu ba Ni ce nayi masa Alƙawari, Na Amince zan Aureshi ,wlh zan Aureshi, Bamalli na amince a daura mana aure don Allah ka ƙyale Baffa na 😭"

Dariya sosai Bamalli ya kwashe dashi,Yayin da Hawayen tausayin Aeesh suka zubo daga Idanun Baffa Imam cikin Raunanniyar murya yace

"A'isha Rayuwar ki ta nan gaba tafi ta yanzu mahimmanci"

Aeesh ta Girgiza kai hawaye suka sauko mata

"Baffa Koda Sun kashe ka zasu sa Abba ya daura Auren,Nasan Bamalli baya yafiya idan yace zai yi abu dole sai yayi"

Dariya Bamalli ya sakeyi a karo na babu Adadi Cikin Jindadi,yayiwa Yaransa Alama da su taho, suka taho Yace su tafi da Aeesh su bata zumar Amare tasha Ana Gama ɗaurin Aure yasha Nata Zumar.....

*Ashman*

Ganin yamma yayi Abba bai dawo ba yasa ya maida Umma Gida kafin nan yayita kiran layin Aeesh a kashe ,hakan yasa bayan yakai Ammie gida ya duba ɗakinta kai tsaye Amma babu ita, ya tambayi habeeb ko ta fita yace Tun kan ayi ruwa ta fita,ba Ƙaramin tashi Hankalin sa yayi ba, dukda Baisan Abinda Ya faru ba Amma yasan ba lafiya ba, Aeeh bata daɗewa a waje In Anyi Ruwa .

Duk inda yasan Zai iya Samun ta yaje har asibiti Gun Reey Amma Bata nan Hankalin sa Ya yi matuƙar tashi sosai, da Tambaya Ya gano gidan Aareef nan ma ya tabbatar masa Da bai ganta Ba, Wayar ta yayita kira amma an kunna tana Ringing baa dauka.

Dawowa yayi, yayi parking A gefen titin junction na hanyar Gidan Su Aeesh hankalinsa a tashe, kaman Ance ya waiga sai ganin Umbrellan Aeesh yayi yayi a yashe a ƙasa ,duƙawa yayi ya ɗauka yakai hancinsa, Ƙamshin Turarenta ya bugi hancinsa Babu shakka Aeesh ta bi tanan, kuma wani Mugun Abu ya sameta.

Wayarsa ya dauko yayi Sa'a GPS dinta a kunne yake Take ya fara Tracking location dinta,Yasha Wahala sosai kafin ya gano Unguwar da Aka Kaita,yana Shiga Unguwar Wayarsa Ta mutu babu chargi, Maƙalata yayi a charger motansa.

Babu kowa a layin,Garin yayi Tsit ko ina na Unguwar Kewaye da farar Street light, daga chan nesa ya hango wata Mota a Parke ƙofar Wata Gida kaman Motar da Abba y Fita dashi, Tada Motarsa yayi Ya ƙarasa Gaban Gidan,Tabbas Motar ce Abba ya fita Dashi Amma ya kasa Gane Dalilin Zuwan Abba nan ,Idan Zargin sa Ya tabbata Abba na nan Thofa lallai Aeesh ma na nan.


_hankalinsa ya soma tashi, kodai saceta Abba yayi don ya Cin ma burin sa akanta?_

Cikin matsanancin tashin Hankali ya fito ya kwankwasa gate din,Amma ba'a buɗe ba, Dawowa yayi Ya buɗe Booth Ɗin Motarsa Ya dauko helmet dinsa ya Rufe fuskar sa dashi Sannan ya dauko Wata ƙaramar Container a booth Ɗin, sannan ya dauko wayarsa ya kira yansanda

Hankalinsa a tashe ya haura katangan Gidan Batareda fargaba ko tsoro ba , baya ji baya gani idanunsa sun riga sun rufe Abba yake hangowa tareda Aeesh dinsa.

Azaba sosai Bamalli yasa Ake ganawa Baffa Imam ,Saboda yaƙi Amince ya Bashi Aeesh, yayinda Ma'aikatansa Sukayi ma Aeesh Duren Zuman Amare kaman yanda Ogan nasu ya Umurce su.

Anan Parlor kuwa Ganin Baffa bashida Niyyar Bada Auren Yasa Bamalli ya juya Akalar sa kan Abba,Aikam Tun kan ya gama Neman Izininsa ya yadda zai zamemata Wakeeli.

Take aka fara ShiryeShiryen Daurin aure, Mahaifinshin bamalli da Kawunshi suka matso, Aka Buɗe taro da addu'a.

Gani sukayi an murda handle din daga waje sai aka fara turo kofar ahankali

Duk suka maida hankalinsu kan Ƙofar ,Leƙowa Ashman yayi, ganin Ƙattin maza yasa ya ɗan ja baya.

agogon dake daure a Hannunsa ya  danna Take Motarsa dake Waje ya Fara Bada Sautin Jiniyar Yan Sanda ,Tuni tawagar Guards din Bamalli  suka Tarwatse, zuciyar Bamalli kuwa bugawa take kamar zata faso qirji ,Ashman Dake laɓe a bayan ƙofa Ganin basu ida Tarwatsewa ba yasa ya jefo ƙaramar container Hannunshi ko ina ya kaure da hayaƙin Barkonon tsohuwa.

Tari Suka Fara yi cikin ƙanƙanin Lokaci Duk suka Fice a hayyacinSu da rarrafe Bamalli ya Samu ya Sulale ya Shige ɗaya daga cikin Bedrooms ɗinsa Yana Haki Abba ma tuni ya gudu.

Sai a lokacin Ashman ya Shigo,Ganin Baffa A daure ba karamin Tada hankalin sa yayi ba, Saurin Kwance shi yayi ya dauko ruwar Gora cikin wadanda ya gani a gere, ya kara masa A baki, yasha Ruwan Sosai har Saida ya Kusa Shanyewa Sannan ya zare Robar daga bakinsa,cikin matsanancin Firgici yake cewa

"Baffa Meke Faruwa?, ina Aeesh ? ,Please Baffa Open Ur Eyes Ina Aeesh?”

Da hannu Baffa yayi masa nuni da Dakin Da aka kaita batareda ya iya cewa Komai ba.

Da gudu yayi dakin ya hankaɗe ƙofar ya shiga, Kwance yaganta kan Gado tana rawar ɗari da Alama Sanyi takeji.

Cikin Sassarfa ya ƙarasa kan Gadon Kallo ɗaya yayi mata ya Gane sun bata wani Abu, Tausayinta ne ya kamashi So yake ya tambaye ta Dalilin da ya kawo su nan Amma Da Alama Bata cikin Hayyacinta.

A firgice ta d'ago kanta ganin Ashman saita fad'a jikinsa ta saki kuka.

Shima rungumeta yayi sosai yana sakin Ajiyan Zuciya Ji yayi kaman Shima yayi kuka, sannan ya d'auketa cak zuwa inda Baffa yake chan sitting Room d'in ya ajiyeta a saman sofa, kuma rungume Shi tayi ta cigaba da kukan a tsorace.

       Tsawon lokaci suna haka,ya kasa Dakatar da ita, Sai da ta samu Nutsuwa sannan ta ɗago kanta tana hawaye.


Daure zuciyarsa yayi ya shiga lallashinta.

"Ashman Da ace ka ƙara Minti ɗaya da Yanzu A'isha ta zama Matar Wani"

Muryar Baffa ta doki kunnensa, Juyowa yyi A mammakince ya zuba masa Reddish Eyes dinsa mai firgita wanda aka kalla dasu, saurin Kauda Kai Baffa yayi a kasalance yace

"Muyi Sauri Mu fice daga nan Kafin Shu'umin Ya fito ya Iske mu anan"

Dukda Ashman Bai san Inda zamtukansa Suka nufa ba yasan Zaman Su anan ba Alheri bane.

Daukan Aeesh yayi yaga tayi Luuuu tayi baya ,Jijjigata ya shigayi yana Ambaton Sunanta Amma a banza Babu Amsa ta riga ta Suma.

Saɓata yayi a kafaɗa yana jin zuciyarsa na Suya.

Fitowa harabar Gidan Sukayi nan Suka tarar da Abban Bamalli da Kawunsa suna tattaunawa cikeda jiimami

Buɗe bayan Mota Ashman Yayi ya shimfidar da Aeesh Sannan ya dawo inda ya baro Baffa imam dake takawa Daƙyar don Azaba,Ba karamin Wahala yasha a hannun Su Bamalli ba.

"Ashman ...."

Baffa ya kira Sunan shi a hankali,Ɗagowa yayi ya dubi Baffa a sanyaye.

"Ina So ka Mn Wata Alfarma"

Shiru yayi yakasa cewa komai saboda yadda zuciyarsa ta tsananta bugu jiyake kamar da zai bude bakin zuciyarshi zai biyo shi wajen ya fito

Ganin bai ce komai ba hakan yasashi Cigaba da cewa

"please, ka Yarda in Aura maka A'isha Yanzun nan"

qarashe yana kallonshi da wani expression mai wuyar ganewa a fuskarshi ,Shi kanshi yasan Abinda ya bida nada Wuyar karɓuwa a Gareshi.

Saurin dagowa Ashman yayi ya kalleshi trying to believe what he heard

"haba Uncle Imam, ya zakace haka kuma?, Ina ka taba ganin an daura aure a yanayi irin haka?,ina ga May be Sun dokeka a ka, bari mu wuce asibiti A maka brain scan Mugani Ko akwai matsala"

"Ashman Mahaukaci kamaidani ko mara Hankali?, Da gaske nake A yau zan sauke nauyin da Hassan ya Dora Min, idan Muke da yau bamu ke da Gobe ba ....."

"Idan ya Amince Ni ne zan zama wakilin ka"

Cewar Abban Bamalli ta Bayan su

"Ni kuma zan bada Sadaki Naira Dubu ɗari da Hamsin"

Kallon mamaki Ashman yabisu Dashi Yayinda Baffa keta Murmushi.

"No I can't do this...!, Bazan iya ba, Aure Ba Abin wasa bane fa...!, Taya zan Auri Aeesh?, yarinyar da yanzu ta fara ƙirgar dangi?,me ta sani? Haba kuma daina wannan Zancen "

Duƙawa har Ƙasa Baffa Yayi ya kamo Ƙafar Ashman Hawayen tausayin Aeesh suka silalo Masa cikin Rawar murya yake cewa

"Ashman Ban taɓa roƙon wata Alfarma daga Gare ka ba, Wannan Itace karo na farko and maybe karo na Ƙarshe don Allah ka taimakawa Rayuwa Ta ka ceci Rayuwar yar uwarka,ka cire batun bata daɗe da Fara ƙirgar dangi ba,Don Allah save her Do this for me...."

Ya ƙarashe maganar da fashewa da kuka mai tsanani.

Tausayin dattijon ne ya kamashi, Tunda yake bai taɓa ganin Dattijo na Roƙon Alfarma Harda kama Ƙafar Dan Saurayi irin Shi ba,Wannan itace karo na farko kuma Shine na ƙarshe inshallahu, bazai iya kallon tsohon Wani na duƙa masa ba, At least Baffa yayan mahaifiyarsa ne, yafi karfin Komai a wajenshin shi

Saurin Duƙawa Ashman yayi ya ɗago Baffa ya sa hannu ya share masa hawaye Cikin rani yake cewa

"Baffa na Amince Zan Aureta,Na Amince ka Aura Mn Aeesh yanzu Yanzun nan ,Bazan tambayi dalilin da yasa Ka yanke hukunci ba, Nasan bazaka cutar Damu ba”

Yana Rufe baki yan sanda Suka Shigo Gidan ,Dama Ashman ne ya kirasu.

"Ku Zo nan ku shida Daurin Auren ɗiyata"

Baffa ya faɗa yana Yafito yan sandan Da hannu, Take aka daura Auren Aeesh da Ashman akan Sadaki Naira dubu ɗari , babu Yanda uncle din Bamalli baiyi ba Akan su barshi ya biya sadakin kaman yanda ya dau Alƙawari Amma Ashman yaji Amincewa A cewarsa , _hakan Ba mutuncinsa bane_ koda ace yasan Shi Balle kuma yau ne farkon Haɗuwarsu Wama ya sani ko shi yasa a sace Aeesh, Salon Ya karɓi kuɗinsa Abin Ya zama yar raini!.

Ana gama Daura Aure Aka rarraba Goro,Ashman yasa Baffa a mota suka nufi Asibiti don har yanzu Aeesh bata farfaɗo ba, yayinda yan sanda suka Shige Ciki Don Binciko Criminals...🏒

Kai tsaye asibiti ya nufa dasu Akayi treating ɗinsu, tareda Rubuta msu magunguna, har Suka fito Asibitin Aeesh bata farfaɗo ba, har gida Ashman ya kai Baffa ya sauke shi, Har a lokacin bai daina Zuba masa godiya ba shi har Kunya yaji Wlhy Baffa bai cancanci hakan daga Gareshi ba.

Ada har ya kama hanyar Gidan Su Aeesh sai ya tuna a halin yanzu matarsa ce ,Shikeda Alhakin Kula da Ita, Take ya sauya Shawara ya kaita gidansa ,a kan Gadonsa ya shimfida ta ya kashe fanka ya kunna mata warmer , sannan yayi mata setting Line ya sa Mata drip yayi Hanging Fluid din a Jikin Drip stand din gefen Gadonsa.

Bathroom ya faɗa Saida yayi wanka ya gudanar da sallar Isha'i da ya riga ya wuce shi ,Sannan yayi shirin barci ya haye gado ya kwanta Ya kwanta Gefen ta ,Baici Abinci ba kuma ko kadan bayajin yunwa.

Kwanciya yayi shiru idanunshi akan p.o.p.

Yakasa yarda haryanzu wai shi Ango ne, Angon Aeesh ,Yau Shi ya Auri Aeesh ,just like that? Saikuma ya tuna Shekaran Jiya Suka je aka Saka Ranar Bikinta da Aareef.

Murmushi yadanyi, tunowa yayi da yanayin da ya ganta ɗazu Abin tausayi da Kuma Yanda Baffa ke roƙonsa Da ya Amince a daura auren,Take Murmushinsa Ya disashe ya fara tunanin dalilin da zaisa baffa ya buƙaci Ya aura masa ita cikin gaggawa.

Tashi zaune yayi ya zabga tagumi ya kafe fuskarta da Kallo.

Tunawa yayi da wayarshi Hakan yasa ya miqe zaune ya na waige waigen inda zai ganta.

Chan ya tuno ashe ya barota a mota ,Tashi yayi yaje ya dauko ya turawa Umma saƙo  _*Na samo Aeesh bata da lafiya muna Asibiti chan zamu kwana*_

Daga nan sai ya kashe wayar Gabaki ɗaya.

karfe 2:09am Ta farka tana Sumbatu

" _Baffa Don Allah Ka Amince bana So In Rasa ka wayyo Baffa na_ "

Saurin Rungumeta yayi yana bubbuga bayanta,Saida ta samu natsuwa sannan ya Cikata ya zuba mata Ido yana Ganin yanda take sauke Ajiyan Zuciya da sauri da sauri.

Dakin tabi da Kallo tana Mamakin yanda Akayi ta bar bakin Gidan bamalli,bata ida Tunani ba taji Hanjin cikin ta sun dan kaɗa, yatsine Fuska tayi

"Yaya Yunwa nakeji"

"Ki shiga Bathroom Kiyi wanka,ki dauro Alwala Kiyi Sallolin da Ake binki"

Yayi maganar yana cire mata Line din hannunta ,Babu musu ta miƙe ta faɗa banɗaki tayo wanka ta fito ɗaure da Towel,Shaf ta mance ta Baroshi a bedroom,Aikam tana Ganinshi ta Koma a guje.

Murmushi Yadanyi Ya Sosa keyansa a ransa yace

"Amarya ta kenan"

Bude closet din shi yayi dauko Hijab Da Black Arabian Gown dama baya rasa Kayanta a Closet dinshi.

Sai yanzu yaji Cikinsa ya ɗan Murɗa alamar Yunwa.

Shayi ya haɗa mata Shima hada coffeen yayi yazo ya zauna kan gado yana kur6a.

Yana Zaune ta fito sanye cikin kayan Da ta Cire ,Jallabiyar da ya ciro mata ya Nuna Mata kana ya fice batareda yace komai ba.

Kitchen ya nufa kai tsaye ya haɗo mata Night meal na Mara Lafiya.

Koda ya dawo ya samu har ta Idar da Sallah tana Lazimi har yanzu ta kasa tuna abinda ya faru, Kwakwalwar ta ta Tsaya chak iya Abinda ke faruwa yanzu take iya tunawa.

Dire Plate din yayi kan table.

"Laaah yaya Duk wannan Nawa ne"

Aeesh ta faɗa tana Zare Hijab din Jikinta.

Murmushi yayi ya dauko mug din tean da ya haɗa mata, dakanshi yayita bata a baki yana haɗa Mata da snack har ta ji ta koshi.

Ƙureshi tayi da Kallo ta kasa Tuna abinda takeyi a gidanshi har Wannan Lokacin.

Bude idanun yayi ya kalleta yaga itama  take kallo, daga mata gira daya yayi alamun 'ya?'

Murmushi kawai yayi ya kuma diban farfesun yana hadawa da yankakkun kananun nama ya Kai Bakinta,Ta ƙoshi Amma she can't ignore this Tana son nama Sosai,Ko mutuwa take taga nama saita danci kafin ta mutu.

Miƙa tayi bayan ta cinye

"Ohsh yaya na ƙoshi fa"

Dan daga gira daya yayi
"really?"

Gyaɗa Kai tayi alamar Eh.

Kauda Tray din yayi Ya dawo ya zauna Gefenta yana Tambayan ya jikin bata bashi Amsa ba Illa ma wani tambayar da ta Tsiro masa

"Ahky Fuskar ka tayi Haske Kayi kyau yau Meye Sirrin"

Murmushi yadanyi ya Shafa Gemunsa a ransa yace

_Hasken Angwanci ne,Sirrin kuma Shine Aure_

Kamo hannayenta yayi Cikin sanyi murya a raunane yake cewa

"Ihkty ba komai ne ake tuntu6e dashi bisa shiryawa kaiba, wani abun tunkan kasan tuwarmu gudan tsoka rubutaccene a littafin k'addararmu, babu wani ɗan Adam da alƙalamin ƙaddararsa ke a tafin hannunsa, gudun zuciya yafi ta Agogo sauri, idone kawai ke iya banbance fari da baƙi, baki kuwa ɗanɗano kawai yake tantancewa, aikin kunne kuwa jine kawai da banbance ƙirar sauti, Mune Muke Zaɓar Abokan Rayuwar Mu Amma bamu iya gujewa zaɓin Allah.."

Wara idanunta Aeesh tayi don sai da ya Ambaci *Abokan Rayuwa*sannan ta tuna abinda ya da ya faru.

Wani irin kuka mai tsuma kuka tafashe dashi tana qara Qanqameshi

"wayyo yaya!,Shikenan an Aura Mn Bamalli,  Sun kashe Baffa? Please Help me Ahky, take me out of here, zasu kasheni..."

tafada cikin fitar hayyaci jikinta na rawa sosai

Dago fuskarta yayi cikin taffukan hannunshi yana bin fuskarta da kallo a gigice take sosai .

"Babe Calm Down Basu Aura miki Kowa ba, Kuma Baffa na nan Lafiyarsa Ƙalau...."

"No A'a wlh Ƙarya ne a gabana Suka daureshi,Sun dakeshi,Sun sa Mai Shocking ,Sun sassareshi Ya Mutu"

"No calm down Bai Mutu ba ,Ni da kaina na kaishi gida ,Kema babu Abinda Sukayi miki Ki nutsu Mana"

Fashewa tayi da wani kukan tana sake komawa jikinshi ta Qanqameshi, Awanni ƙalilan da suka Gabata ta saddaqar rayuwarta tazo qarshe Shikenan zata dawwama a ƙarƙashin Wani cikin Ƙangin bauta, amma yanzu ganinshi yasama mata hope, hope na cigaba da rayuwa Cikin yanci.

"Akhy ina son Ganin Baffa na Pls video call Him, hankali Na bai kwanta ba"

Wayarsa ya zaro yayi dialing Line din Baffa (video call ), Ringing ɗin farko matar sa ta ɗaga cikin tsananin Tashin Hankali take cewa

"Ashman Don Allah kazo ka taimake mu ,Wasu yan ta'adda Sun Shigo sun Sassare Alhaji da ƴa'yan mu basu bar kowa da rai ba, Nima da kyar Nasha Sun Datse Min Ƙafa ɗaya"

Daga nan Sai Connection ɗin ya fara Shaking.

Innalillahi Wainnailaihirraji'un kadai Ashman Ke ta maimaitawa, yayinda Kukan Aeesh ya daɗu, cewa take _"Wlhy Su Bamalli ne, Sune Suka Kashe Mn Baffa na"_






*_Thofa_*

***Shin Kuma su Bamalli kuke zargi da Kisan nan Ko kuma Kun hango wani suspect ɗin?.

**Gashi dai an daura aure Amarya bata sani ba,madaurin auren ya rasu ,Ango Baisan Shaidun ba,Dare ne Baiga fuskokin Su sosai ba koda ya gansu ba gane su zaiyi ba🧘🏻‍♀️.

*Ya kuke ganin za'a kaya Shin In ya faɗa za'a yarda dashi Ko kuwa ?...



*Please Share*
And

Comment 🤙🏼


Nayi gabas,🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️


June 13th 2022

Bintou ✍🏼
[7/18, 9:26 PM] chubby number: _*Wuƙa a zuciya*_
_(Bleeding Hearts)_


*012*


*Waiwaye*

Alhaji Umar Muhammad Kasheem ,Sananne kuma Shahararren Ɗan kasuwa wanda Duniya Tasan da zamansa A fannin kasuwanci ,ya taka matakai Dayawa a rayuwa, Ya shahara Sosai ya Tara Dukiya Sosai Amma kafin Ya kai Ga samun Wannan matsayin yasha Gwagwarmaya Dadama Don Tun yana Ɗan Shekara Biyar ya Rasa Iyayenshi, Dakansa Yake Samawa kansa Ci da Sha Da sutura Yanada Dangin Uwa da Uba Amma Babu wanda ya Taimaka masa Hakan yasa yasa a ransa Bashida dangi Shi ɗaya ne.

Yasa hakan a ransa har Gwagwarmayansa Ta kaisa Matakin da yake a  yanzu ta sanadin  ,Mace ɗaya Gareshi da Yara Hudu.

Abubakar Imam Shine na Farko ,Sai Hassan Da hussaina ,da kuma Auta Ajmal

Abubakar Wanda akafi sanida IMAM Mutum ne mai sauƙin kai Bashida hayaniya Ko kadan, Biology Computer ya karanta a FCE zaria kafin daga Bisani ya dora da B'Ed din shi inda y karanci Biology Education a Kasu  Kasancewarsu Mazaunar Nan Cikin Garin kaduna ne.

Hassan( Ghiath) Da Hussaina(Giathah) yan Gatane Wajen Iyayensu, Sun Taso cikin Gata sosai Na mahaifinsu da mahaifiyarsu(haj Aisha) Sosai Akeji dasu Ba'aso aga Ɓacin Ransu ,Gashi Allah ya zuba msu Farinjini Sosai Jama'a na Ƙaunarsu.

Babu Abinda Suka Nema Wajen Mahaifinsu Alh U.M Kasheem da basu Samu ba, sun taso cikin gata da soyyaya tako wane 6angare saidai duk gatan da suke samun hakan be hanasu samun inganttaciyar tarbiya ba don duk yadda suke dasu idan sukayi ba daidai ba suna tsawatar mashi kuma msu nasiha, in ya kama Na Kwaɓa ta wata hanyar ma Duk sunayi, Gabaki ɗayansu sun taso ne Da Burin Karantar Medicine sai Allah bai nufa ba, Giath Ya Samu Giathah bata samu ba dole Ya haƙura Suka chanza Course Zuwa Optalmiology fannin Idanu.

Auta Kuwa Heart Surgeon ne ,a India Yayi KaratunSa a halin yanzu cikekken Likitan zuciya ne a Chan ƙasar Egypt.

A ɓangaren arziqin Alhaji U.M kasheem kuwa sai abinda yayi gaba don har ya bar duniya sananne ne har a Ƙasashen Europe .

Alhaji Ahmad Shettima Aminin U.M Kasheem ne ,Tare Suke harkar Kasuwancinsu, Aminai ne sosai Tun tasowarsu Tare suka Sha Wahalar Rayuwa Amma Kasheem Yafi A.shettima Arziki da zafin Nema.

Shima A.Shettima Kaman Umar M Kasheem Mace daya Gareshi da Yara Hudu.

Naseer, Nooriyyah, Hamzah, Da Mardiyyah.

Naseer Tun yana Yaro  miskili ne, Shida dan Uwansa Hamza ga rashin son hayaniya, miskilanci, k'asaita da basar da Abu tamkar bai damesuba, rashin mutunci idan aka Shiga Gonarsu, ga salon Dizgi da wulaƙaci Gunsu ba komai bane, hakan yasa Nooriyyah da Mardiyyah suka taso Cikin tsoron yan uwan nasu.

Naseer Med Surg doctor ne wato Medical Doctor mai Ƙarin ilimi ta Fannin Surgery ,Shi kuma hamza babban Lawyer ne ,Mardiyya mass com ta karanta Yayinda Nooriyyah ta karanci basic Midwifery Sannan ta dora da post basic Nursing tana Gamawa Ta samu admission a ABU zaria inda ta karanci Obst & Gynea.

Akwai wani abokin noor na tun yarinta Faisal Tare Suka taso Komai tare Sukeyi tun Nursery har Secondary, Koda Ta Samu Adm na karantar Basic Midwifery Tare Suka Samu A makaranta Ɗaya Shi ya karanci Basic Nursing, a hankali Shaƙuwarsu ya fara Riƙidewa zuwa Zazzafar Soyayya mai ban Mamaki a lokacin da Suka Gama kuwa tare Suka Samu Admission Inda suka cigaba da karantar Course daya wato postbasic nursing.

A shekararsu ta ƙarshe Allah ya nufi Auren Naseer da Giatha (Hussaina), Naseer ɗan A.Shettima da kuma Giatha ɗiyar   U.M kasheem bayan Wata ɗaya akayi na Imam da Wata ɗalibarsa Maryam,Bayan Bikinsu da sati ɗaya Allah yayiwa Alh A.Shettima da U.M Kasheem Rasuwa a hanyarsu na zuwa Canada Sakamakon wani mummunan haɗarin Jirgin sama da sukayi.

Sosai 'ya'yansu Suka Rike Zumunci tsakanin Ahalinsu biyu tunda sunsan Basu da kowa sai junansu don kuwa Tunda Hassan yaga yar Uwarsa ta Auri Naseer Shima Ya kwallafa wa ransa Sai ya Aure masa Ƙanwa , Haka Shima Auta Ajman Yace Duk faɗin duniya babu wacce zai Aura in ba Mardiyya ba ,Hamza ne Dai bai samu Nasa Rabon cikin Zuri'ar ba.

Hkn yasa koda Faisal ya Fito Cewa ya Shirya Auren Nooriyya Yayanta Naseer Shafawa Idonsa toka yayi yace baisan wannnan maganar ba, Bazai aurawa Ƙanwarsa Talaka ba yaje ya nemi Kudi in yayi Kuɗi ya Dawo za'a bashi.

A lokacin gani yake kaman Albashinshi da yake karɓa a asibiti na Aikin Jinya bazai isheshi Auren Noor ba Dubada Irin tarin dukiyar da Mahaifinsu ya tafi ya bar musu, Ga mahaifiyarsu itama Tana ji da nata nairan , harkar Kasuwanci ya Faɗa Lokaci Guda Allah y Daukakashi ya bar Ƙasar Zuwa U.K inda yake safarar Wayoyi daga Ƙasar zuwa nan Gida Nigeria.

Naseer Kuwa yana jin Labarin Faisal ya bar ƙasar ya Aurawa Ƙanwarsa Hassan ,Tsoron yayan nata takeyi Sosai bazata iya musu akan Abinda ya bijiro mata dashi ba dole ta Amince .

Gaggarumin biki akayi nagani na fada inda babu laifi ansha shagulgula sosai sannan aka kawo amarya Nooriyya dakin mijinta Hassan(muhammad Giath ) .

Hassan Gwani  ne wajen iya Ririta mace kaman Gold da Kuma Iya Tattali Hakan yasa Bai sha wahala ba Wajen Sace Zuciyar Noor.

Bayan shekara daya da aurensu Dr Naseer sai Allah ya azurtasu da samun Yan biyu kyakyawa Masu kamada juna sak kakansu A.Shettima.

A lokacin Dr naseer ya tafi Umra, Labari na Isowa Gareshi , a ransa ya ce An Samu sufyan Da Rabeel.

garin Murna ya ɓatar da wayar tasa ya zama Basu samu sun tattauna ba har Ya dawo gida Nigeria kuma bai samu ya dawo ba Sai d akayi suna da Kwana biyu.

Samu yayi har an Raɗawa yaran Suna Ashman Da Ashraf, Aikam kyekyashewa yayi yace Inaa bazata Saɓu ba, shikeda Alhakin Zaɓawa Yaransa Suna babu Wanda ya isa Dole a chanza a maida msu Sufyan da Rabeel.

Suma chn kafewa Sukayi akan bazasu yarda ba An riga an yanka Raguna an sa suna babu mai chanzawa ,Wasawasa Magana har yakai gaban Alƙali, Alƙali ya yanke Tunda uban yara ya nace sai a sake Yanka wasu Ragunan A maida msu Wa'ennan Sunayen In yaso wa'enda aka sa Da farko su zama nickname.

Sam haj Giatha bataji daɗin  yanda Dr Naseer ya kai ƙararta gun Alƙali ba a ganinta Su biyu sun isa su gama wannan mgnr,Haka yasa ta daina Sakin masa Fuska, Shi kuma da yaga Haka sai ya auro mata 'yar Aikinta mai tayata Renon su Ashman ,Hakan dayayi ba Ƙaramin Gigita ta yayi ba, bata san Zaiyi Aure ba saidai kawai gani Tayi Saude ta daina Zuwa reno kwana biyu sai ga Saude Mai reno an Rakota da Guɗa.

Dama kunsan Naseer Akwai Wulaƙanci Da Rashin sanin darajar Dan adam Iya su Kansu kadai suka sani bai damu da halin da wani Zai shiga A sanadinsa Ba, Shidai indai aka taɓoshi yanke Hukunci yake babu waiwaye,Ko mahaifiyarsa ba Raga mata yakeyi ba baya shakkarta Ko kaɗan da ya biɗa abu ta hanashi yanzun nan sai ya kai ƙaranta gurin Alƙali, Tunda ya zama Medical Director Wulaƙancinsa ya daɗu baya Ganinkowa da gashi .

Rashin Mutuncin Naseer yaso Ya taɓa zumuncinsu Don Hamza Ƙanin naseer Shima Goyon Bayan yayan nasa Yakeyi kome yayi daidai ne.

Bayan wata Biyu Allah ya Azurta Hassan da Samun ɗa namiji .

hassan baki yaqi rufuwa don murna, ranar suna na zagayowa aka radama baby sunan *Sadeeq*.

Shima Abubakar Imam A Cikin watan Allah ya Azurtashi da mace Wacce taci Sunan Mahaifiyarsu Wato Maryam.

Bayan auren Dr naseer

Please Login or Register in order to submit comment