Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

katse kiran tana qara faɗaɗa Murmushin ta.

Satan kallonshi tayi da wutsiyar ido taga hankalinshi Gabaki ɗaya baya kanta fuskar nan kamar anmashi Albishara da jahannama.

Ta6e baki tayi ta maida kallonta ga windown motar tana kallon Tsakar Gidan su a ranta tana cewa *_Mutum Kullum Fuska a haɗe kamar Gobarar Ta***shi_* ,Da ƙarfin tsiya tada motar suka fice.

Gudu sosai yake zubawa a hanya bayaji baya Gani,  gudu yake kaman zai tashi sama, yana isowa asibitin yaja wani uban Burki.

Hakan yasa ta tsorata Sosai Ta Rungumeshi tana ihu.

Ji yayi ya Kasa ko motsawa , jikinshi yayi liqis jiyake kamar babu sauran lakka ajikinshi, hannu na rawa ya ɓanɓarota daga Riƙon da tayi masa,Ya fito Sannan ya zagaya ya bude Mata ta fito Jikinta babu inda baya rawa har yanzu a tsorace take,Bai damu ba ya buɗe Booth Ɗin motar ya dauko Basket a booth, Hannunta yaja Suka Shige Cikin Asibitin tsoro fal a ranta, tunda take dashi bata taɓa Ganinshi Cikin irin wannan Yanayin ba Shiyasa ta tsorata Sosai.

Zaune suka tadda Reey Anty Fatee yayarta Zaune kusa da ita tana ɓare mata Ayaba.

Murmushi Reey ta saki Ganin yanda tawani kankame Hannunsa Idanunta Sun firfito da Alama a tsorace take.

Saurin Ƙwace Hannunta tayi ta qaraso bakin gadon  ta kamo hannun Reey murmushi fall fuskarta.

"Inye Jiki yayi sauki kenan?" Tafada cikin murna

Guntun murmushi kawai tayimata tana dan lumshe idanu.

Qarasowa shima Ashman yayi yana fadin

"Ya Jikin?"

Yafada shima yana ajiye Basket din hannunshi kan locker dake kusada gadon Reey.

Murmushi kawai Reey tayi don haryanzu batada kuzari sosai.

"To sai a tashi a Fara Shirin Aure dan na kira yaya Sadeeq na Sanar Dashi ciwonki Aure yake so yayi ya dawo asan yanda za'ayi"

inji Aeesh Cikin tsokana

Dan waro idanu Reey tayi tana rufe bakinta da tafin hannu ita Aeesh bata ma san tanayi ba cigaba tayi da cewa.

"Ai da Kin faɗa mana Aure kikeso da Tuni munsan yanda muka yi dake kafin Abin ya tsir...."

Waro idanun da Reey tayi yasata saurin sakama zancenta linzami tana zazzare idanu cikin rashin gaskiya.

Ashman da Anty Fatee dai kallonsu suke kallon tuhuma, ganin haka yasa Aeesh saurin duqawa ta ciro flask din cikin basket din tana yaqe.

"Bari in haɗa mki Tea Nasan Babu Abinda kikaci"

Ta fada tana Ciro cup ta haɗa Mata Shayin.

"Allah kaman kin sani tun jiya taki cin Abinci"
Cewar Anty fatee

"Haba Besty Wai duk Meye haka?,Sai kace Wata ƙaramar yarinya? ,Oya buɗe baki"

Aeesh ta faɗa tana kai Tea ɗin bakinta,Kauda kai Tayi Tana ɓata fuska.

"Lallai Ma yarinya , Dure kike so in miki kenan”

Ta faɗa tana cire mayafin ta,ai babu Shiri Reey ta miƙe zaune, ta karɓi kofin shayin ta kafa kai sai da ta Shanye ta dire kofin tana sauke Ajiyan Numfashi.

"Ko ke fa, Bari in haɗa miki wani nan...."


Ringing din wayarta ya katseta.

Dauka tayi tana duba mai kiranta.

Saida ta saci kallon Reey, Aashman da Anty Fatee Taga duk hankalinsu baya wajenta sannan ta ɗaga wayar cikin fara'a
"Assalamu alaikum"

"Wa alaiki salam, jewel" aka amsa ta dayan bangaren ciki fara'a.

"Ka iso ne?"

"Eh"

"Tho ka shigo Gynecology Department,ka tambayi ina ne Amenity dinsu muna Nan"

Tana Gama faɗin haka ta datse wayar tana sauke Ajiyan Zuciya, Saƙo taga ya Shigo wayarta, yi tayi kamar zata basar Sai ta daure ta duba Ashman ne.

Saurin Ɗagowa tayi ta kalleshi hankalin sa na kan waya Kamar bashi ya turo saƙo ba.

Hannu na rawa ta Buɗe Saƙon

*_IDAN YAZO YA SAMENI A OFFICE ƊINA_*

Tana Ida Karantawa taga ya miƙe ya fita ransa a ɓace.

Binshi da kallo tayi tana Ayyana abubuwa da dama a ranta, Tunda ya dawo daga Kano yake neman Ya chanza hali,kodan yaga An saka masa rana ne?,In yayi haƙuri itama bada jimawa ba Aareef ɗinta zai Turo asa msu ranar Suma.

Ita dai Reey bata ce komaiba sai binsu kawai datake da kallo

Suna haka kofar ta bude Aareef ya shigo hannunsa Riƙe da wani ƙaton leda.

Tsaki Reey taja taja bargo ta Rufa tayi kamar bacci take, tana jinsu suna Gaisawa da Anty Fatee harda sa musu Albarka.

"Sadauki na kaga Bacci take bari Mu fita Kar mu tashe ta Aeesh ta faɗa Suna ficewa daga ɗakin"

Suna Fita ta sanar dashi yayanta na neman sa, Babu bata lokaci Suka Nufi Office din Ashman Yana zaune ya zuba ma ƙofa ido yana Jiran Shigowar Su .


Da sallama Suka Shigo.

Gaban Ashman ne yafadi dayayi tozali da unique handsome Guy, dukda shigar kaftan yayi ba qaramin kyau yayiba, gashi bai sa ko hula ba ,Amma kyan dayayi baya misaltuwa Lallai in Dan so da iya wanka ake So dole Aeesh ta faɗa dayawa ko kadan bai ga laifin ta ba.

Ashman ji yayi kamar ya shaqeshi don takaicin yadda yake wani takawa A natse kamar wanda yaje gasar Natsuwa.

Zama sukayi kan Kujerun dake facing din Ashman

Wani irin shiru office din yadauka, itama kanta Aeesh a yau Ashman yayi matuƙar tsorata ta,ko kadan Fuskarsa babu annuri Ya maida Hankali wajen latsa System.

Kusan mintuna biyar Amma shiru babu wanda ya motsa cikinsu, sai danne danne yake a system, Miƙewa tayi zata fita har takai bakin Ƙofa ta tsinkayi muryarsa yana faɗin

"Kina Sonshi?"

Wani kulutun yawu ta haɗiye tukunna sannan tace

"Eh...ina Sonshi kamar Raina"

"You can Go"

Ya faɗa still Hankalin sa na kan System dinsa,fita tayi tana Fargabar abinda zasu tattauna da Aareef, Shima Aareef Bangarensa Haka ya kasance Cikeda fargaba.

Fitarta da Minti biyar...Goma,Amma still ba wanda ya motsa.

Aareef jira yake Ashman yayi magana,Ashman kuma jira yake yayi masa introducing kansa.

Sauke tsoro Aareef yayi ya dago Y dubi Ashman dake ta faman latse latse yace

"Sir..."

Banza yayi masa kaman baiji shi ba, Cigaba yy da cewa

"In Laifi nayi maka kayi haƙuri Tuba nake Amma don Allah kar ka rabani da Aeesh"

Dagowa yayi Daga system din tareda komawa yayi jingina sosai a kujerar Cikin izza.


Zubamasa sharp dinshi yayi ya qureshi da kallo.

"Na baka Nan da Sati daya ka turo magabatan ka a sa rana nan da watanni Biyar Zamu baka ita"

Yasan babu yadda za'ayi yayi rejecting dinshi inya shirya Aurenta, Idan kuma bai shirya ba this will be the best way da zaibi ya raba su cikin sauki.

Lumshe idanu Aareef yayi hankali a tashe

"But si......"

Dakatar dashi yayi ta hanyar daga masa hannu, Ya nuna masa hanyar Fita.

"Na gama Magana So Out...!"








Nayi Gabas🤸

31st may
Comment
And
Share



Bintou ✍️
[7/18, 9:25 PM] chubby number: *_🗡️🫀Wuƙa a zuciya🫀🗡️_*
_(Bleeding hearts)_



*009*


Miƙewa Aareef yayi ya Fice Masa a Office Hankalinsa a tashe.

Kallo ɗaya Aeesh tayi masa tasan Lallai yayanta ya bugawa Aareef Hauka, Fuskar nan Bbu Annuri Ko kadan,bata taɓa ganin Bacin ransa ba ko kadan, haka Fushinsa da damuwar sa.

Jikinta a matukar sanyaye ta ƙarasa wajen sa tana Tambayan sa Me suka tattauna?, Yaƙe kawai yayi mata batareda ya iya cewa komai ba,

Ko sallama bai jira sunyi ba yayi wucewarsa ,hakan yasa ta tabbatar ma kanta babu lafiya, Office Din ASHMAN ta nufa cikin damuwa .

Sallama tayi zata shigo ya daka mata tsawa yace ta fitar masa a Office .

Ashman yayi matuƙar tsorata ta sosai,ko kadan bata son tsawa Kuma Bata Saba dashi ba, da gudu ta fice a Office ɗinsa tana kuka komawa Wajen Su Reey tayi tana kuka sosai,ganinta tana kuka ba karamin Tada hankalin Anty fatee yayi ba Reey kou ko ajikinta Hasalima murna ta hauyi a zatonta Rabata da Aareef Aash yayi saida taci kukan ta ta ƙoshi tayi shuru don kanta Sannan Ta zayyana masu Abinda Ya faru ta ƙara da cewa

"Niba komai yasani kuka ba sai Share nin da sadauki yayi,Allah yasa ba wani Mugun Abin Yaya ya faɗa Masa ba, Wlhy Fushin sadauki babbar masifa ce a gareni"

Tayi maganar cikin Tur6une fusaka kaman zata sake wani kukan Reey ta kwashe da dariya irin wadda tadad'e basuga tayiba,Dariyar cusa takaici

"Allah yasa ce masa yayi kar ya sake kulaki"

Pillow Aeesh ta ɗauka ta buga mata aka "Aniyar ki tabiki muguwa''

Bata Ida Rufe baki ba itama taji saukar pillow A ka,Nan fa suka shiga Wasan doke doke da Pillow Cikin kan Ƙanin Lokaci Sukayi kaca kaca da ɗakin babu yanda Anty fatee batayi ba don Ta rabasu Amma Ƙarshe Sai Abin yaso ya dawo kanta ,Babu yanda ta iya dole ta ƙyalesu Suka bari dakansu Bayan kowannensu ya chasu Sai Nishi suketa Zubawa.

*Pollokshields GLASGOW* (United Kingdom)

_Alhaji Faisal Yakub Kurah_
Shahararre Cikin Ƙasar UK kuma shiɗin dan kasuwa ne wanda duniya take jidashi.

Zaune yake Cikin Rantsassiyar Katuwar parlonsa wanda Kallo ɗaya zaka masa ka gane mamallakinsa yayi sadaukarwa dadama ga duniya kafin ya mallakeshi.

Wasu Jigajigan Bouncers ne ta koina a Parlorn, Wasu mutane uku ne zaune dashi Suna tattaunawa.

Miƙewa ɗaya daga Cikinsu yayi ya dubi Alh Faisal cikin Gazawa yace

"Alhaji Gaskiya Akwai matsala fa, banajin Zamu iya Taɓa Ahalin Alhaji Hassan Saboda Sunada wata Garkuwa tare dasu Gaskiya yawan Ibada da Tashin daren da takeyi yasa bazamu iya yin komai ba Alhaji Idan Muka matsa Zamu kuka da kanmu Wlhy Ni In zaka bi tawa Mubar Ahalin Shettima haka Tun kafin ya zama masifa a taredamu ,Ka duba ka samu Dukiya da daukaka Fiyeda Adadi ta sanadin Ahalin, Ka kashe Alhaji Hassan ka maida Hussainarsa yar aiki a gidan Mijinta ,kayi nasarar wargaza Zumuncin dake tsakanin zuri'ar mijinta , ka haddasa Gaba mai tsanani Tsakanin Yayyi da Kanne ,Har yanzu Alhaji Naseer da ƴar uwansa basua Jituwa Haka yaran Alhaji Naseer Sun ware kansu Basu ɗauki Babban Yayansu da Komai ba,Ahalin Hassan ne dai ka kashe shi Ka haddasa Gaba a tsakanin Matarsa da Dan uwanta Amma ka kasa Cinma burinka,Ina rokon ka don Allah dakatar da wa......"

Bai Ida Furta Kalmar da ta fito bakinsa ba yaji an wanke shi da wani Gigitaccen mari,Cikin tsawa Alh Faisal ke cewa

"Rufe mn baki,A tunanin ka zan iya janye Kudurina akan Zuri'ar Mayaudaran nan ne?,Inaa Wlhy bazan Taba ƙyalesu su huta ba, Mahaifiyar SADEEQ,SURAYYA DA AEESH harda HABEEB itace taja musu da bata Sokawa  _*zuciyata wuƙa*_  ba da hakan bata kasance ba,a rayuwata babu macen da naso kamar Noory har yau har Gobe kuma babu wacce zanso samada ita, Abubuwa da dama sun faru a sanadinta Na fifita Soyayyarta Akan Mahaifiyata Amma Daga bisani ta Soke WUƘA A ZUCIYATA tayiwa zuciyata Gunduwa Gunduwa Auren Amini na Alhaji Hassan Shettima Da tayi shine babban Kuskuren da ta Aikatawa Rayuwarta, Shi kuma Alhaji Naseer Kuskurensa tayin auren Hassan da yayi mata duk Don banida kuɗi a lokacin, Saboda ita nake zaune a wannan Ƙasar, Saboda ita na Tara duk tarin dukiyata, Zan iya Ƙarar da dukiya ta don Ganin na tarwatsa Zuri'ar ta,Yau shekaru 21 kenan da na sace diyarta Surayya (Sureey) Da ita zan Tarwatsa Nata Bugun zuciyar , a Ranar Sunan yan biyun da Ta haifa (Aeesh da Sureey) nasa Aka Sato Suree Mai hasken Aka bar mata mai duhun, a ranar nasa Aka ɗaura mana Aure da ita, kuma Ranar ce Ranar da na bar Nigeria"

Dan Dakatawa yayi yana Sauraron Bugun zuciyar shi,hakan ke kasancewa dashi aduk sanda ya tuna First and last love dinsa Nooriyyah wacce aka fi saninta da Noory.

"Hasashe na ya nuna min nan da Watanni Biyar Zata Aurar da Diyarta Aeesh, Shima Naseer Zai Aurar da yaransa Aash da Saleem, a Ranar za'ayi shagali Sosai Nima Ranar zan Maida matata Amarya A Ranar da zan Sauke Mata abubuwan da nake Adanawa na tsawon Shekaru fin hamsin daga nan Kou har sai Allah ya nufemu da samun Rabo.....naji zafin Abinda Noor ta min sosai, har yanzu kuma inajin zafin hakan Shiyasa bazan bar Noor da Naseer suji daɗin Rayuwa cikin wanchan Ahalin ba saina cigaba da farautar rayuwarsu ta Sanadin Ahalin su da ƴaƴan da ta Haifawa Hassan ya zama dole ta ɗanɗani kwatankwacin Zafin da naji a zuciyata Saina karar da dukiyata Don Daukar fansa....."

Tattaunawa suka Cigaba dayi da Sauran Mutane ukun babu jimawa Sureey ta dawo daga Wajen Aiki Kamanninsu ɗaya da Aeesh Kaman An tsaga kara saidai Wannan Fara ce Aeesh kuma wankan tarwaɗa ce.

Faɗawa jikinshi tayi a shagwaɓe tana Turo baki kaman Zatayi kuka ,Take Hankalin Faisal ya tashi ya sallamesu suka wuce.

Ɗagowa yayi yana Tambayan Ta me akayi mata turo baki ta sakeyi

"Nidai daddy kaje kayiwa Sir Zain magana ,ya kasa Approving Story ɗina Wai sai na Rubuto Masa Labarin Soyayya mai taɓa zuciya yana nufin, Duk Sleepless nights ɗinda na Kashe wurin neman Labarin Romeo and Juliet ya zama A banza kenan?"

Ta ƙarshe maganar tareda Fashewa Da matsanancin Kuka mai ban tausayi, inda abinda Alhj Faisal ya tsana bai wuce Yaga Bacin ranta ba ballantana Yaga Kukanta take ya ruɗe ya fara rarrashi,hakan yayi tasiri Matuƙa wajen sake Hure mata kai Hawayen Suka Cigaba da kwarara a idanunta.

"Dole ayi Rejecting ɗinki Babynah, Romeo mutuwa yayi akan Juleit a wannan Zamanin kuma kai ya waye ba'a mutuwa akan so,, Kiyiru Babynah in Allah ya yarda Ni dakaina zan Rubuta mki Labarin Da zaisa Zain yayi approving dinki,Zaki Zama Yar jarida in Allah ya yarda..."

Yasha Wahala sosai kafin ya samu ta daina kukan, sai a lokacin Hankalinsa ya kwanta.

Miƙewa tayi Tana miƙa

"Daddy yunwa" tafada kamar zatayi kuka

Daya daga cikin bouncers dinsa ya Kira da niyyar ya Samo mata abinda zata ci ta dakatar dashi da cewa ta ma fasaci ,tashi shima yayi yana cewa

"Muje ga abinci can dining wasa nake mki how can a guard perform daddy's duty"

Binshi tayi tana tum6are baki

Shi da kanshi yayi serving dinta ya dinga bata sai zubamashi shagwa6a da ta6ara take shikuma yana biyemata

*kaduna (Nigeria)*

Kwana Aeesh tayi tana kuka Kafin safiya kuwa Idanunta sun Kumbura Ciwon kai mai Zafi ya kamata saboda baccin da bata samu tayi ba,jiya Gabaki ɗaya bataji ta bakin Aareef ba ko kiranta baiyi ba ,koda ta kira shi sau uku yana Rejecting Daga ƙarshe ma kashe wayar yayi Gabaki ɗaya, hakan ba ƙaramin Tada hankalinta yayi ba tayi ta kuka, ko kadan Reey bata san Tayi ba sai da asubah da taga Idanunta sun kukkumburo saboda Jiya ciwonta ya tashi an kira doctor On call ya mata Allurar Barci.

Fitowar ta kenan daga ban ɗaki da Alama wanka tayo tana ɗan Cuccuɗa Kanta da Farar towel,Binta da kallo Reey tay tayi har ta Gama kimtsawa yau kam Farar Uniform ɗinta ta saka Rabonta da ta saka farar Uniform kuwa tun Farkon Fara Practical dinsu,Saida ta Gama Kimtsawa Sannan ta zauna Gefen Gadon Reey tana Saka BlackSneaker Ɗinta a sanyaye kallo ɗaya zaka mata ka hango tarin damuwan dake tattare da ita.

Kasa Haƙuri Juwee tayi ganin tana Shirin Shiga Asibiti batareda taci komai ba, Gashi da Alama akwai abin dake damunta

"Kin karya ne?"

"Na koshi"

"Umma taje dauko mana abinci Ki jirata ta dawo"

Banza ta mata ta cigaba da Shirinta

"Besty wai me ke damunki ne?"

Reey ta faɗa cikin damuwa tana matsowa kusa da ita Tare da dafe kafaɗar ta,Shuru Aeesh tayi zuciyarta na suya.

"Please ki faɗa mn Koma me ke damunki kekanki kinsan Saka damuwa a rai babban Illace ga lafiyar Mutum”

Wasu siraren Hawaye ne suka Zubo mata,ɗago kai tayi ta dubi Reey

"Aareef Maraya ne bashida kowa a duniyar nan, Ni da Abokansa kadai yake da,ina tausayinsa Wlhy ,rashina ba ƙaramin Illa zai masa ba ,Don Allah kicewa Yaa Maan kar ya Raba mu, Aareef bazai iya jure Rashina Ba"

Cupping fuskarta Reey tayi da hannunta Hakan yasa Aeesh zubamata idanu itama tana kallonta

"dear, please calm down, ban Fahimceki ba,ya Aash din cewa yayi ya rabu dake?"

"Koma Dai menene Baya ƙaunar Aareef ɗina jiya fa saura kaɗan ya mareni harda Daka mn tsawa karo na farko a Rayuwar mu, Kuma Tunda Aareef ya fice daga Asibitin nan Cikin damuwa ban sake ji daga gareshi ba, Ni banga Laifin bawan Allah Nan ba duk kunbi kun tsaneshi,You guys Are making me feels bad"

Ta ƙarashe maganar cikin rawar murya.

Tunda ta fara mgn take Binta da kallo ,Tausayinta yasake lullu6e Reey ganin kamar ma ba'a hayyacinta take ba.

"Ba nufin Mu Musaki Cikin Wani yanayi bane,You know we all love You bamua son wani ya nesanta Mu dake barin ma yaya Aash Yafi kowa ƙaunarki Bayason ya bada ke ga kowa da so samu ne Ki ƙyale Aareef ki Auri Ya Ashman z...."

"Besty.....!"

Aeesh ta Katse ta

"Kinsan Abinda kike faɗa kuwa?, In ƙyale Aareef in Auri ya Maan fa kk ce?, Kinada hankali kuwa?,koni na Amince zan Aurenshi Shi bazai iya Aure na ba,yafi karfi na ,nayi masa kadan me zaiyi da yarinya?,Yarinyar ma wacce ya rena!, Yafi Ummana sanin Rayuwata Yafi kowa sanin Koni waye, ki sani akwai Banbanci tsakanin So da soyayya Idan kanaso ba'a sonka ko kuma baka so Ana sonka wannan Shi ake kira So Amma idan kana so Ana sonka wannan shine soyayya Soyayyar dake tsakanina Da Aareef bai kai Na sadaukar dashi g.. .!"

Turo kofar da Akayi ne yasata Dakatawa,Ƙamshin Turarensa ya doki hancinta.

_Na shiga uku_ ta faɗa a ranta.

Shigowa yayi Fuskarnan a daure tamau, sanye yake Cikin Navy blue Suits, mai farar Shirt daga, yasa necktie navy blue Mai digo digon fari, Ya Ɗora labcoat dinsa akai Gefen Aljihun Labcoat din dauke da Tag Mai dauke da rubutu kaman haka *Dr Suff Shettima*  ya aje sumar kanshi daketa walqiya saboda gyara.

Ko kallon Inda Aeesh take baiyi ba ya shiga duba Reey, da Alama yaji duk abinda suke cewa wasu magungunan ya rubuta mata ya fice.

Kasa motsi tayi har ya fice kunya duk yabi ya Rufeta Bata so ya kamata tana Magana akansa ba, Tun daga Ranar bata sake bari Sun haɗa Ido ba,Kunyar sa da tsoronsa wanda bata taɓa ji akan wani ba ya dirar mata a lokacin Guda,Shima kusan hakan ne ta kasance a ɓangaren sa baiyi Tunanin Tajiyo tattaunawansa Da Rabeel b Kwanaki da ya kawo masa ziyara Suna Hira ta shigo nan take Hirar ta koma akanta inda Rabeel ke cewa da Ace Aeesh zai aura dashi dakanshi zai dau nauyin komai amma budar bakinsa sai cewa yayi

"_Rabeel Kasan Abinda kake faɗa kuwa?, Kanada hankali kuwa?,Na auri Ukhteey fa kace?, Nafi karfinta wlh ,tayi mn kadan me zanyi da yarinya?,Yarinyar ma wacce na rena!, Nafi Ummata sanin Rayuwarta Na kuma fi kowa sanin Ko ita waye...!_

Yau Kwanaki Uku kenan da faruwar hakan Jiya Akayi ma Reey Aiki, Haka yau Saleem ya tsara Zai fara Aiki Tun da yazo Babu Aikin da yayi sai Kuntatawa Ma'aikata Babu ma'aikacin da Bai san Dr SN Shettima ba Gurin Wulaƙanci jijjidakai Da Rashin Sanin Ƙimar ɗan Adam , Aareef kuwa tun Randa Ashman ya bashi zaɓi bai sake kula Aeesh Ba,Sosai ta damu Da Rashin ji daga Gareshi.

Dawowarta kenan daga Asibiti Umma ta Fita HABEEB na ɗakinsa yana Zane.

Zaune take Ta zabga uban tagumi, Abinci ne a gabanta Amma ta kasaci Sosai take kewan Aashman a ko wane lokaci Tare Suke cin abinci Yau Kwanaki uku kenan Rabonda ya tako Gidansu tana yawan Ganinshi in taje Asibiti Amma bata yarda su haɗa hanya.

Wayarta tajawo ta Kunna data tahau WhatsApp

Kamar jira ake saiga message din  Aashman da Aareef duk a lokaci guda.

Zaro idanunta tayi a matuƙar mamakince, hannu na rawa ta buɗe Message ɗin Ashman, Reply yayi mata Akan Wani Status ɗin da ta ɗora ɗazu da Emoji

😌

Itama maida masa Martani tayi da Emoji

😮

Sai ta fita ta shiga Message ɗin Aareef Tarin messages Dinda ta tura masa Tun Ranar ta duba bata san ta tura masa Sunyi yawa ba sai yanzu Murmushi tayi ta duba new message dinsa

Aslm Rabin Rai

Shima hannu na rawa ta maida masa Martani

Wslm Hayatee
Ka bani tsoro.

Tana Turawa Sai ga Reply

Tsoro kuma?

Saurin Typing tayi itama

Yeah...!, You punish My heart

Tana Turawa ta fita ta duba message ɗin Ashman da ya shigo yanzu.

*_Uhkty Fushi kikeyi yayan ki?_*

Sticker din Shagwaɓa Aeesh ta aikomashi, sannan ta Ƙara da voice note

"_ba Kaine ka Ɓata ma sadauki na rai ba_*

Shima voice note din yayi mata Cikin Wata murya mai dauke da Abubuwa da dama

*_Sorry_*

Ya faɗa a takaice

Ban haƙura ba

Ta fara turawa Sannan Wani Message ɗin ya biyo baya

"*Yawwa yaya me kace masa ranar Naga ya fito Cikin fushi haka?* "

Voice note ya turo Mata , Instead ya Bata Amsar Tambayar da tayi masa Sai ya rera mata waƙar Murmushi Kinyi mn ado da fuskarki.

_Soyayya ke natsayar ban miki kishiya ba_

_yan mata duk na kawar bazan Kula dasu ba_

_zuciya ke na shigar A ciki ba zan Fitar ba_

_kulawa zan bayar ban nuna gajjjiya ba_

_saurauta ta_
_tuntuni na baki_

_ke na wakilta_

_don kece adila ta_

Tsayawa Aeesh tayi ta saki baki tana Sauraron Voice ɗin Cikin mugun mamaki, a iya saninta Ashman baya sauraron Waƙoƙin Hausa to taya ya iya waƙar nan.

Taji Voice din Yafi sau biyar

Ga mammakina sai gani nayi wani qayattacen murmushi ya su6uce mata wanda rabon da na ga irinshi a fuskarta harna manta.

A kasalance tayi masa Reply da

*Yaushe ka fara Sauraron Hausa Music?*

*Tunda kika Sama mn Abokiyar Rayuwa Deejah*

Yaƙe tayi bayan Ta karanta ta fice batareda ta masa Reply ba,Ta shiga  message ɗin Aareef

*_idan Bazan takura ki ba inaso Please zamu iya haɗuwa yanzu?_*

Hannu na rawa cikin zumuɗi ta masa Reply da why not

Address y turo mata Tsalle ta buga tana rawa Finally yau zata Fita da Rabin ranta.

Bathroom ta faɗa tayi wanka ,Sannan Ta Chaɓa Ado Irin Kwalliyar da ta mance rabon da tayi irinshi.

Kiranshi taga ya shigo Saurin dagawa tayi ce mata yayi ya isa Inda Zasu haɗun ita yake jira

Saurin  feffesama jikinta turare tayi ta fito a gurguje

Direct ɗakin Habeeb ta nufa yana zaune sai zane yake,

"Habeeb in Ammee ta dawo kace na tafi Unguwa"

"Wow Masha Allah Tsarki ya tabbata Ga Allah da ya halicci kyakkyawar Surar nan Ya kuma damƙa mn ita a matsayin Wa a gareni ba don Kuɗina ba ba don Wani Abu nawa Ba...."

"Kai Dallah Rufe mn Baki"

Ta dakatar dashi tana Murmushi.

Kyalle mata ido ɗaya yayi Uncle "Aareef ne ya ce ku haɗu ko?, I guess"

Zaro ido tayi
"Ni na gaya maka haka?, Saura in Umma ta dawo ka gaya mata haka Wlh Saina Babbalaka"

Dariya ya saki yana Zipping bakinshi, ita kuma ta Fice, Napep ta tsare ya Kaita Twingle Pizza 🍕, Tana Sauka a Napep ta hangoshi Zaune a ciki saboda Gabaki ɗaya Wurin An Ƙawatashi da transparent Glass ne na waje na iya hango na Ciki haka na ciki ma haka.

Sanye yake cikin Kananan Kaya  wando dark blue da Baƙar riga mai ratsin fari sai takalma Baƙaƙe, yar sumar kanshi tasha gyara sai salqi take, Fuskar sa Dauke da baƙaken Tabarau, Abinka da Fari sai Shigar Black yayi masa kyau.

Jin Tsayiwar Napep  yasashi Dagowa ya kalli wajen

Lumshe idanu yayi akanta yasake budewa cikin zuciyarshi yana fadin "masha allah"

Sanye take cikin dark blue arabian gown da duk jikinta stones ne , rigar mai irin fadin hannu ne mai jela ,ta yane kanta da Gyalen Rigar, tayi Irin Yanda larabawa keyi , baƙar purse ce a hannunta sai takalmi suma baƙaƙe wanda baka iya hangensu sosai sai idan tana tafiya saboda tsawon rigar, Ita ba Ma'abociyar yin makeup bane Amma yau sai ta tsinci kanta dayin Simple makeup Wanda hakan ba karamin Kawata pretty Face dinta yayi ba.

Ya Shafa'a  sosai wajen kallonta ,Baisan kallonta yakeyi ba har Saida ta Iso Gareshi ta ɗanyi Masa tafi a bisa Fuskar sa

Da sauri ya dawo duniyar kallonta daya shiga ya juyo ya kalli Aeesh dake tsaye riqeda qugu tana kallonshi.

Harararta ya danyi yace
"Meye na kallona?"

Dan Wara idanu Aeesh tayi

"Ina kallon ka ko kana Kallo na?"

Rufe idanuwansa yayi da tafukan hannayensa

"Tho na daina Kallonki kema ki daina kallona"

Dariya ta saki cikin jin daɗi,Her happiness is back.

"Allah baka Isa ba"

Tayi maganar a shagwaɓe, SHIMA Dariyar yayi Waiter yazo ya karɓi list dinsu babu jimawa ya Kawo msu abinda suka Biɗa.

Suna Ci Suna hira cikin nishadi kamar babu Saɓanin da ya taba Shiga tsakanin Su.

Ɗagowa Aareef yayi ya dubeta Cikin Murmushi yace

"Amaryata"

Itama Murmushi tayi tace

"To be inshaAllah"

"Nan da 5mounths Ba"

Wasa ta dau maganarsa Tace

"Allah yasa"

Murmushi ya sakeyi yace

"Ya ma Sa ,Umma bata faɗa miki bane?"

Girgiza kai tayi innocently

Ajiyar zuciya Aareef ya saki a sanyaye
"Alright then tell me What is it"

"Na tura magabata na An tsaida Ranar Auren mu zuwa nan da 5months"

Ihun murna Aeesh ta saki Don Gabaki ɗaya ta mance a public place Suke ,Saurin kame bakinta tayi da ta tuna Ina take .

Ajiyan Zuciya Aareef ya Sake Saukewa A karo na biyu yace

"Amma fa akwai Matsala"

"Matsala Kuma?"

Binta da kallo yayi jiki a sanyaye batareda Ya iya cewa Komai ba.

"Please tell me Meye Matsalar"

Iska ya Furzar daga bakinshi cikin Raunanniyar murya ya kira sunanta

"A'isha Hassan Shettima"

Dammm taji Gabanta ya faɗa dajin ya kira Asalin Sunanta da Sunan mahaifin ta, kasa Amsawa tayi

Please Login or Register in order to submit comment