Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DEEJEEMA Complete Hausa Novel Document by DEEJEEMA


DEEJEEMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 104364



DEEJEEMA

Reading Time: 8 Hours

Added On: 05, Sep 2024

Author: Farida Bashir Ummu Safwan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 607.45 kb

File Type: txt

Views: 904+

Download: 1426+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [28/04, 20:50] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar Gidan tsohuwa_😅)



Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)




*AM BACK AGAIN BY THE GRECE OF ALLAH*



_Alherin da ke ciki Allah yasadani dashi, shairin dake ciki Allah ya tsareni dashi_
_Muje zuwa masoya ana bugun tare🤝🏻_ *UMMU SAFWAN CE*






*1*









Cikin sand'a tashigo cikin zauren gidansu, tana wasar b'uya, ita da k'awayenta

Lab'ewa tayi tasha jinin jinkinta kamar wacce tayi k'arya, tana tafiya a hankali yanda baxaka iyajin sautin takun k'afartaba."

Gafda zata shiga cikin gidan ne
Saiji tayi taci karo da wani abun,a gabanta."
turus tayi,
Taja ta tsaya gefe d'aya tana turo baki kasan cewar zauren gidan duhu ke gareshi,

Ta d'auka *Kaka* ne, kaka Kwaishi da fitinar tsuha,
Tashiga gunguni tana magana k'asa k'asa, " kai wannan tsohun kacika rigima yazaka taka min k'afa, idan kuma akace da kai ka kusan mutuwa, ka d'ora hannu a kai kace kai ba yanzun zaka mutuba."

Shuru taji anyi Bataji antanka mata ba."

Dogon tsaki taja harda d'an murgud'a baki taci gaba da tafiya
zata shiga cikin gidan kenan taji ta kuma taka k'afar mutum a karo na biyu."

Jikinta ya soma rawa fitsari ya fara d'iga a wandonta, saka makon marin da taji an kwad'a mata a fuska."

Wata irin k'ara tasaki ta fad'i k'asa tana birgima, "Wayyo idona na shiga uku tsohuwa kizo ki ceceni."

Mahmud dake tsaye cike da takaicinta, yace "Ke wace irin yarinya ce,wadda bata kallon gabanta, tunda kika shigo soron gidan nan naketa k'ok'arin naga na kauce mki amma duk da hakan saida kika taka min k'afa."
Oh kin d'auka *kaka* ne da kike fad'awa magana yanda kikaga dama?"
to bashi bane ni kika tak'ewa k'afa, wawuya kawai marar hankali wadda bata kallon gabanta bare bayanta,
Ni maganin rashin kunyarki zanyi kafin na bar gidan nan."

Tsohuwa dake sallah,
Sallamewarta kenan taji sautin kukan Dije a zaure."

Da sauri ta mik'e tsaye tafito daga d'akin tana fad'in "deejama wani mugunne ya dakeki?"

Ai kuwa deejama najin muryar tsuhuwa ta kuma bud'e baki had'ida sanya hannu d'aya ta dafe b idonta d'aya, "wayyo idona nashiga uku tsuhuwa idona ya tsiyaye."

Mahmud tsaye yayi ya tsura mata ido yana kallon ikon Allah, k'azafi takeso tayi mashi yanaji yana gani."

Ta mik'e tsaye dafe da ido sai kuwa takeyi tana tsalle tana fad'uwa, sai da tazo dafdashi ta kuma taka masa k'afa da k'arfi
ta xuba a guje tanufi wurin tsohuwa dake tsaye a k'ofar d'aki tana ruwan masifa."

Tanufi wurin tsohuwa tana fad'in "wayyo idona tsohuwa ki taimakeni yaya muhmud ya tsiyayar min da ido d'aya."

"Tsohuwa tace "burinka ya cika mamuda ka tsiyaye mata ido d'aya saika zuba ruwa k'asa kasha,
Ni wlh bnsan irin k'iyayyar da kakeyiwa deejama ba,
kwata kwata baka k'aunar ka bud"e ido ka ganta tana walwala a gida ko a waje."

Tunda burinka ya cika ka makantar da ita, saikazo ka kwashe kayanka ka koma gidanku. Mungode da ziyarar Allah amfana."

Muhmud da zaifita, jin k'azafinda dijana tayi masa yasashi dawowa ya fasa fitar.

Yace "Allah tsohuwa ki daina biyewa wannan yarinya, kwata kwata batajin magana kuma batada kunya. Tun da nazo garin nan kullum sai ankawo maki k'arar dijama, amma kullum sai d'aure mata kikeyi bata laifi."

"Saboda kana jin zafinta shiyasa ka tsiyayar mata da ido d'aya?"
Tafad'i hakan had'ida kamo dijama dake gefenta tsaye kamar ta shige mata a ciki dafe da ido d'aya."

Ta janye hannun deejama daga kan idon nata tana fad'in naga idon naki dije, idan ta kama mutafi asibity sai na kira ubanshi duk inda yake yazo ya d'aukemu ya kaimu asibitin."

Ganin babu abunda idon nata yayi, tsohuwa ta kuma kallon muhmud dake tsaye gefe d'aya yana kallon ikon Allah.

"To burinka bai cikaba baka makantar da itaba."

tarik'a hannunta "mutafi deejamar tsohuwa kisha hura ki nemi wuri ki kwanta kirabu da wancan Azzalumin."

Kallon mahmud deejama tayi ta fakaici idon tsohuwa tayi masa gwalo had'ida murgud'a mashi baki."

Nuni yayi mata da hannu a lamar zanrik'eki."

Bai d'aga daga inda yakeba. Sai sallama yaji anayi,
wata mata ce tashigo da yaronta janye a hannunta wanda bai wuce shekara goma ba da bokitin markad'e a hannunta duk ya b'aci da k'asa alamar b'ari yayi."

Tana fad'in "ina tsohuwa take?"
Fito fito dan yau na rantse da Allah bazanyi asaraba. Kullum na aiki yarona wurin markad'e sai dijama ta tareshi a hanya tayi mashi dukan tsiya sannan daga k'arshe ta zubar min da markad'e to yau hak'urina ya k'are Dan bazanyi asaraba sai anbiyani ehe "

Mahmud yadubi matar yace "d'aga murya kwarai yanda zasujiki suna ciki yanzun suka shiga."

Tsohuwa tafito deejama ta biyo bayanta,
Tsohuwa tace Abu mai waina mekike fad'i?"
Me kuma deejama tayi?"

Abu mai waina tarik'e k'ugu, ta maimaita mata b'arnar da deejama tayi mata."

Tsuhuwa itama ta hau masifa tana fad'in Sam ba Deejama ta aikata hakan ba."

"Na lura a garin nan babu wanda aka sanyawa ido irin deejama, yarinyar da na aika tasayomin sikari. Tayaya zatabi ta k'ofar gidanku?"

to Wani irin sokon yaro ne gareki da har zai saki baki,
Deejama tayi masa duka kuma har ta zubar mashi da markad'e." dan Allah Abu mai waina kifita a gidan nan tun cikin muna mu biyu, dan babu wani ranko da zan maki ehe."

Ai kuwa Abu mai waina tashiga ruwan bala'i,
"Ayi maka asara kuma baxa'a baka hak'uriba, to yau duk yanda za'ayi sai dai ayi amma sai anbiyani markad'ena."

Mahmud da yaji fad'an ba mai k'arewa bane, ransa ya b'aci yaciro d'ari biyar ya mik'awa Abu mai waina had'ida bata hak'uri."

Baki ta bud'e ta fara dariya takarb'i kud'in tana godiya,
Sai ta koma yin magana cikin lalama da taushin murya, "aisu yaran ne basajin magana, amma ya kamata a k'ara jawa deejama kunne saboda kaf a cikin k'auyen nan ta hana yara walwala idan ta fito kowa tsoronta yakeji."
Babu Wanda ya kuma tanka mata, sai Deejama da tace "kedai ki wuce kiba mutane wuri, tunda anbiyaki kud'in markad'anki, karki damemu da suruto."

Ta dubi Sale yaron Abu mai waina, ta harareshi tace "kai kuma sale duk na rik'aka saina karye maka k'afa d'aya."

Abu mai waina najin hakan kuma tasan halin dijama zata iya, zata fara wata sabuwar masifar mahmud ya bata hak'uri. SnnTa tafi,

a hasale yanufi wurin dijama zai daketa tsohuwa ta turata d'aki tana fad'in wlh karka daketa. Meye ruwanka, to muddun ka daketa saina sab'a maka a gidan nan."

Mahmud ya dawo baya, yana hararar dijama yana fad'in zan rik'akine saina d'ebi d'arina biyar a jikinki. Dan bazan biya mki kud'i a banzaba."

Yanajin tsohuwa ta fara ruwan masifa ya fito ya baro masu gidan."

Bayan sallar isha'i kamar yanda suka saba kowace yarinya zataci ado tanufi dandali,
Haka dijama tayi kwalliya tasanya atamfa riga daban Zane da d'ankwali daban, tazane fuskarta da kwalliya kasan cewar dijama kyakkyawace kuma bafulatana ce, domin ba sosai hausarta ke fitowaba."
An d'aure k'ugu da gyale."

Da gudu tafito gidansu tana rera wak'a, k'awayenta najin sautin wak'arta kowa ya fito daga gidansu suka tareta
Suna fad'in ga 'yar gidan tsohuwa nan ta fito, aikuwa da murna suka tareta suka jera suka nufi dandali."

Dijama ce gaba k'awayenta suwaiba da lantana da ladidi, da luba a bayanta suntake mata baya domin itace boos duk Wanda yaja magana ita ke tare mashi."

Gefe d'aya suka samu suka zauna a kusa da wani mai kifi,
Mai kifin yana ganinsu , Sai da ya kuma dallara fitila ya duba da kyau ya tabbatar da sune,
Ya sauke wani numfashi a ransa yace "Ashe yau zanyi kwantai bazan samu cinikiba. Saboda wad'an nan hatsibiban yaran."

'Dijama ta turo ido had'ida turo baki cikin tsiwa ta dubi mai kifi tace "lafiya meya faru kake haske mana ido da fitila?"

Mai kifi da saida gabanshi ya fad'i dajin maganar dijama, dan ba k'aramin aikinta bane ta bad'e basa kifi da k'asa taja masa asara kuma ba yanda zaiyi. Ya k'ak'aro dariyar dole yace "yi hak'uri 'yar gidan tsohuwa ai bansan kece ba."

Ya d'auko leda yasanya mata kifi. Yace 'yar gidan tsohuwa ga wannan kici,
Ta dubeshi ta ya mutse fuska tace "ya'u kabar kifinka kawai yau bana ra'ayin cin kifin."

Abokananta suna su, amma saboda tsoron da suke mata yasa ko wacce ta had'iya yawunta."

Ya'u mai kifi yana ganin haka yatashi tsam ya d'auki tiren kifinshi ya bar wurin ya
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DEEJEEMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album