Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DEENAH Complete Hausa Novel Document by DEENAH


DEENAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30554



DEENAH

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Feb 2025

Author: Khadeeja Candy ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 172.38 kb

File Type: txt

Views: 93+

Download: 88+

Last download: 1 day ago

Description/Story: DEENAH

BY

KHADEEJA CANDY


PAGE ONE TO END .....



Da sauri sauri take tafiyar ganin unguwar babu mutane sosai ta tada kai ta kalli sama sai ta kara bata fuska ganin hadarin daya lullube garin!

Bata ankarava taji an sako da ruwa mai karfi nan da nan ya fara jikata da gudu ta nufi wata bishiya dogon yaro tafake aiko ruwan kamar ita suke jira suka kara karfi!

Kankame jikinta tayi ta bata fuska kamar zatayi kuka

Ruwan suka cigaba da zuba harda kankara duk sun jka mata kaya

Wata kafirar mota ta wuce ta gabanta sai kuma naga tayi reverse ta dawo daidai inda take tsaye ta tsaya!

Ahankali naga ana sauke glass din motar ni khadeeja candy nace”Allah gwanin iya halitta”

wani kyayyawan saurayi ne na gaban kwatance da bazai wuce 33 yrs ba na gani a driver seat!

Fari fes mai manyan ido da dogon hanci akasan hancin an yanka masa madaidaicin bak’i!

Cikin sanyayyar murya mai taushi naji yace”my dear deenah shigo” kallonsa da yaga ta tsaya masa ne yasa yace” plz shigo mana kar ruwan ya kare a kanki”

Tattaro rigarta tayi mai kamada ta indiyawa ta shiga tare da rufe ganbun motar!

Handkerchief ya ciro ya mika mata,sannan ya ja motar! 

Ya dauki hanyar da zata fitar dasu unguwar baice da ita komai ba itama batace mishiba har suka bar unguwar sannan ya samu gefen t-t yayi parking! Ya kalleta a karo na biu yana murmushin da ya fitarda beauty point dinsa ya bude baki kamar zaiyi magana!

   Sai kuma naga ya ciro wayarsa ya ya shiga dane dane,,

Suna haka aka watso wata irin walkiya da saida dinah ta razana ba shiri ta rufe idonta!

 ya a hankali naga ya kalleta yayi. Murmushi mai sauti,

Ta dago suka hada ido wani yarrrr taji lokacin da idonta suka shiga cikin nashi,da sauri ta kawarda fuskarta,

Shima ya Mai yarda dubansa gurin wayar ya cigaba da dane dane sa! Sunyi minti 5 ahaka sannan ta dago ba tare da ta kalleshi ba tace” waye kai” yayi kamar bai jitaba, ta kalleshi tace” kai wanene” yayi banza da ita yana buga game

   Wannan karon kallon tsaf ta masa sannan tace akaro na uku ” ina nufin ya sunan ka ina kake kuma ina kasan ni” ko dagowa baiyiba balle ya bata amsa shirun da taji yayi har na wani lokaci baice mata komaiba yasa ta sake Kallonsa a fusace tace ” wai kai wani irin miskiline ina maka magana zakayi min shiru kamar kurma ” 

nan ma shiru, 

Bude motar tayi zata fita da sauri ya riko hannunta yace” haka zaki fita ruwan fa bai dauke ba ” tana harararsa tace ” aeh din to ina ruwanka dan rainin hankali ina magana zakayi banza dani” “I’m srry my dear rufe motar zan baki amsa ” saida tayi kwafa sannan ta rufe motar, dora hannunsa yayi saman sitari yana Kallon t t yace ” ni mutum ne irinki kuma musulmi kuma yanzu haka ina garin SOKOTO tare dake ” ba tare da ya kalleta ba yace” nabaki amsarki sai mie kuma”? Mtswww taja tsaki ” ni bazan kara tambayarka ba balle kamin yanga”!

Ya kalleta yana murmushi yace ” ni namijine ba mace ba dan haka bamu hada hanya da yanga ba” harara ta watsa masa ya dauke kansa ya kunna motar suka hau t t,

ahankali yake tafiyar kamar mai L batare da ta kalleshi ba tace ” ni ka sauke ni a nan dan sauri nakeyi” 

Hannu naga yakai ya dauko wati plate din DVD yasa, ya kure volume nan da nan wakar ‘kirrish’ ta fara tashi,,

Dagowa dinah tayi ta kalleshi taga ya kafeta da ido tace ” ni guiwa locos zaka kaini ” kai kawai ya daga mata ya fisgi motar kamar zai tashi sama!

Ganin yanda yake gudun ya tsora tata Kuwa ta shiga masa harda kukanta kamar ma haukaciya ” na shiga uku wai ina zaka kaini da wannan mugun gudun haka ai mun kusa kawo fa ka rage gudun haka dan Allah “!

Bai kula taba har suka shigo cikin unguwar sannan ya tsagaita gudun dayake … Gaban wani katafaren gida mai katon gate naga yayi parking,, 

Takai hannu ya rage volume sannan ya kalleta yace ” my queen nan ya isa ko mu shiga ciki dan naga akwai sauran yayyafi ” kallonshi tayi cike da tsoro tace” ya isa na gode “,

 ta bude motar ta fita ta nufi cikin gidan  sauke glass din motar naga yayi yana kallonta har shige sannan yaja motarsa yayi gaba

Da gudu dinah ta karasa cikin parlor,, bata tararda kowaba! Kai tsaye ta nufi stairs dakinta ta shiga ta fada bathroom saida tayi wanka sannan ta fito daure da towel,

Gefen gado ta sauna tana yarfarda gashin kanta,, 

Sannan ta nifi wadrope ta dauko gown din sari mai stones maroon color tasa tare da red ribbons ta daure gashinta,,

Sannan ta nufo dakin mahaifiyarta! 

Tana ganinta ta daki kirgi tace” yanzu cikin ruwan nan kika tafo hajiya ” Saman jikinta ta fada tana fadin” tun kamin a fara ruwa na fito kuma wani ne ya rage min hanya ruwa bai jika niba ” murmushi mama tayi tace” toh alhamdulillah yar albarka tashi kije kici abinci sai na baki tsara bar da babanki ya aiko miki” kai kawai ta daga mata ta tashi ta nufi kofar fita! 

  WACE CE DEENAH?? 

   
[11/16, 10:13 AM] Khadeeja Candy: WACE CE DEENAH??? 


Alhaji. Umar salisu tanko shine mahaifin Deenah tsohon ambassador Nigerian ne to Japan dan majalisa ne a yanzu kuma babban dan kasuwa dan yana daya daga cikin manyan yan kasuwan dake shigowa da nigeria kayan masarufi matansa 2 aisha ce uwar gida wanda suke kira da hajiya bata taba haihuwaba haka yasa ya auro halima wanda itace mahaifiyar su Deenah ta haifa masa yara biyar !

Abdullah ne na farko abuja yake saune da matarsa yaransa biu yana aiki a central bank of Nigeria,sai samira dake aure a kaduna da yaranta 4 sai mai bimata faruk dake shirin kammala karatun likitan cinsa a india sai DEENAH dake karatun low a usman dan fodiyo university sai auta zara dake iman international school,

Mahaifin Deenah haifafen ba sakkwace ne amman yanayin aiki bai barshi ya zauna haka yasa ya tare da uwar gidansa aisha a abuja,

A kabar halima wanda ita ta zabawa kanta zama a nan dan mace ce maison zaman lfy ganin basa shiri da aisha yasa taki binsa a chan, kuma gashi duk wasu harkokin kasuwancinta ana SOKOTO take guda nardasu

Deenah farace faes tana da kyau saida ba sosai ba dan ta biyo mahaifinta ta dauko farin fulanin mahaifiyarta, bata cika tsayiba kuma ita ba gajeruwa ba coca cola ce dan tana da shaf ga gashinta har gadon baya ta dauko halin mahaifanta na son addini da jama ah da far ah ga kuma farin jini agurin kowa dan ko iyayenta tafi soyuwa a ransu sama da sauran yayansu shiyasa mahaifiyarta ta hana akaita ko ina karatu dan tafison tana kusa da ita a koda yaushe suna nuna mata gata musamman mahaifinta shiyasa ta sagarce,,, in tana abu kamar ba yar shekara 22,

Su biyar suke zaune a gidan yanzu ita da zara sai cousins dinta  Zainab da nafisa da abul-khair dan shekara 13  dukansu yayan kanne mahaifinta ne in aka cire zara

Gidan sama suke zaune mai rai da lafiya mai hawa 2 kowa da dakinsa,

 part din mahafinsu daban babu abunda ba a zuba a cikin gidan ba ga yan aiki kalakala basa aikin komai daga ci sai wanka,

Duk abunda take so shi ake mata ba tada matsala da ko ina,!

Rayuwar india ta zabawa kanta kamar wanda ta taba zama cikinsu,

Koda yaushe cikin kayan india take da sauraren wakokin su shiyasa ta iya rawar india kalakala gashi in tayi dress ba zaka banbanta ta da indiyawa ba,

        !! Wannan kenan!!

Back to labari!!!

Deenah tana fita dakin mahaifiyarta ta nufi daning room,

Kujera taja ta zauna sannan ta zuba white rice da sauce din kaji ta zuba juice din pineapple and coconut hadin gida,ko spoon bata saba ta shiga aika lomomi, 

bata tsaya ba saida taji ta koshi sannan tayi hamdallah ta tashi ta nufi kitchen ta wnke hannuta, sannan ta nufo dakin momi sai gyatsa take.

Da sallanar ta shigo momi na zaune gaban laptop sanye da glass tana nazarin harko kinta na kasuwanci ta saman jikinta deenah ta kwanta tana fadin ” momi na kare ina tsarabar take” dagowa momi tayi ta kalleta tana murmushi ta nuna mata bedside drawer, ta sauri ta tashi ta nufi gurin,

wani dan cute box ne pick colour ta dauko ta dawo gefen gadon momi ta zauna tana hadi yawu jikinta sai zazzan yake duk taga nawar ta bude,

Da karfi da balle lid din wata kyakkyawar sarkal gol ta fado!

Wata kara da saki ta chafki sarkar tana rawa..

 da sauri momi ta rufe kunnuwanta tana kallonta tace” dinah ar u out of ur mnd
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DEENAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album