Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

YI WA KAI Complete Hausa Novel Document by YI WA KAI


YI WA KAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 201245



YI WA KAI

Reading Time: 16 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Rahma Ladingo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : *+22796515805*. *+22798792126*. *07032817477*

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.11 mb

File Type: txt

Views: 440+

Download: 1355+

Last download: 45 minutes ago

Description/Story: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BoY7L6yHuks8F59z1U4UWd


_YIWA KAI...!_


_Free Novel_

Jumma'ath Mubarak

*Sadaukarwar* _Aishatou Abdulnasir_
Ubangiji ya jik'anki yasa aljanna ce makomarki, Allah ya rayamana Nana A'isha me sunanki.🤲🏼😭
Na maida littafin nan free Novel, Don Allah duk wacce ta karanta tama K'anwata addu'a, Allah ya mata rahama, ya raya abinda ta bari wanda KO fuskar baby girl in bata ganiba.👏🏼😭


_*Bismillahir Rahamanir Rahim*_


*P 1&2*


_Jigawa dutse._
Yanayi ne na lokacin zafi, yau juma'a an tashi da wani irin zafi sosai, ga rana ga shi ba lokacin damuna ba, bare asaka ran saukan ruwan sama ko za'aji sassaucin zafin.
Hakan yasa sosai jama'a dayawa suke mita akan zafin, ga qaran cin wutar nefa bare wad'anda suke da fanka agidan su su kunna ko sa samu sassauci.
Wasu kuma sun fawwalawa ALLAH ikon sa, basa mita sabida suma abinda suka ga dama suke bare kuma Rabbil samawati.
Amman masu akwai wad'anda sukaci suka tayar da kai, gida A.c mota A.c office A.c basusan anayi ba, sai sun fito.

*Bayan sallar juma'a*

_Central mosque_
Duk inda ka kalla jeran gwanon motoci ne, narka-narka masu tsada da masu rangwamen kud'i, ko ina sai tarin sojoji da 'yan sanda suke yawo, alamun akwai manyan k'uso shin k'asar acikin masallacin.
Dan yau yawan cikar al'ummar da yawan motocin sun qaru alamun sun nuna wani babba ne zai aurar da 'yarsa ko d'ansa, abun sai ya zama biyu, sbd limamin mai bada sallar juma'an masallacin, shine mahaifin uban amarya.
'Yan uwa da abokan arziqi sun hallara, abin sai wanda ya gani.

Zaune suke cikin masallacin suna jiran isowar waliyan ango, aurensu ne za'a fara d'aurawa, amman an d'aura dukkan auren da suke da shi a yau, har yanzu waliyan angon Ummulkhairi basu iso ba.
Mai shela sai fad'i yake.
“Ina waliyin ango na wajan Ummulkhairi Abdallah Umar shattima da fatan sun samu isowa?”
Lokacin da me shela ya idar da shelan hankalin minister Abdallah Shatiima yayi bala'in tashi, ya kalli dubban jama'arsa 'yan uwansa da abokanan sa, manyan k'uso shin k'asar nan, ya maida kallonsa kan governor.
Kaifafan idanunsa ya janye daga kallon kowa, na cikin masallacin dan yasan kowa jiransa yake.

Wayoyinsa har guda 3 ne suka d'auki ruri alokaci d'aya, kamar had'in baki, babban sojan da yake na hannun damarsa ya qaraso wajan minister Abdallah, cikin ladabi yay masa magana k'asa-k'asa, dab da kunnen shi ya beqa masa wuleliyar Samsung d'insa.
Jujjuya wayan yay cikin iliminsa kamar yadda yake minister ilimi, ya kai wayan kunnensa Wanda sai da ya katse kiran cikin ilimi tare da kasheta kafin ya fara magana kamar gaske tare da fad'in.
Ok sai kun iso anata jiranku, No! Ba komai anyi muku uzuri.”
Ya k'arashe maganar ya beqawa sojan wayan.
Sai lokacin na gama k'are musu kallo tsaf.
Sanye dukkan family's d'in suke da wata irin d'ayan farar shadda mai bala'in maiqo, sai k'yalli suke, ba kamar ta jikin minister Abdallah Umar Shattima.
Baqi ne, amman jin dad'i da hutu tare da kwanciyar hankali ya saka baqar fatarsa qara murjewa tana sheqi,sai bala'in taushi.
Dogo ne kyakkyawan baqin bafulatanin asali, mai cikar haiba da zati Uwa uba kwarjini, yanada cikar halitta amman baida jiki talaulayi ne, d'an kimanin shekaru, 48.
Manyan idanunsa masu lumshewa ya lumshe ya motsa k'aramin bakinsa tare da kiran sunan ubangijin shi, gabansa ya shiga fad'uwa tsoro ya cikasa, tabbas yasan ya gama kunyata cikin dubban al'ummar da ya gayyato auran 'yarsa, ya kasa bud'e idanunsa.
Yasan kaf cikin masallacin shi aka zubawa idanu.
Muryan mahaifinsa Malam Umar Shattima ya ji yana fad'in.
“Shattima! Wai lafiya har yanzu tawagarsu Alhaji Hashim bata isoba?”

Cikin jarumtarsa da juriyar shi, da barwa Allah lamarinsa, duk da kuwa yasan tafaru ta qare anyiwa mai dame d'aya sata, Salim d'an amininsa Hashim ya fasa auren 'yarsa, hakan bai saka ya ji ya karaya ba, ya bud'e shanyayyun idanunsa ya zuwaba babban malamin wanda yake mahaifinsa, ya saki sansanyan murmushi cikin kamewar shi da juriyarsa da tawakali kamar kullun cikin zazzaqar muryar shi ya furta.
“ALLAH shi temakeka Baffa! Suna hanya aqara haquri da shi mukayi waya yanzu.”
Ya k'arashe mgnar cikin alhinin abinda zai faru jimawa kad'an.
Hannun da ya ji ya dafa shi ne yay saurin maida idanunsa, akan babban aminnsa commissioner Aminu.
Murmushi ya sakar masa yana fad'in.
“Kuyi haquri sun kusa isowa.”
Aminu ya girgiza kasan ya ce.
“Muje daga waje zamuyi magana.”
Ba musu minister Shattima ya miqe yana zuba hannayensa cikin aljihun babbar rigarsa, wadda taci aikin surfanin zamani irin nasu na manya qyalli kawai yake.
Can gefen suka rab'e gefen masallacin, yayin da security's suke tsare dasu da bindigogi a hannayensu suna shawagi.

Alhaji Aminu ya dafa kafad'ar Shattima ya Ce.
“Banyi zaton zaka iya b'oyemin wani abu da ya shafeka ba! Ai ni dakai wlh na d'auka tamkar Uwa d'aya uba d'aya muke, tin yarinta tare muka tashi haka tare muka zama wasu ak'asar nan, shawaramu d'aya mu kashe mu binne, haka matan mu, shin me akazo aka fad'ama da ya d'agama hankali haka? Ni ina gane damuwarka koda kowa bai ganeba.”
Shattima ya zubama commissioner Aminu kaifafan idanunsa, ya fesar da zazzafar iskar bakinsa waje, kafin ya shafi gefen fuskarshi ya furta.
“Aminu! Salim Hashim ya fasa auren Ummulkhairi nah, kasan k'aunar da take masa, ya zanyi da ita? Wlh zan iya jure komai banda ganinta cikin matsanaicin hali. Ya zanyi da jama'ar da suka cika a mosque nan suna jiran su shaida auren gudan 'yata wacce taci burin aurenta da Salim Hashim? Daman sun shirya hakane domin su tozartani nida 'yata KO me hakan yake nufi?”
Minister Aminu ya Ce.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!
Allahumma ajirni fii musiibatihi wa khalifni khairan minha. Mu Hashim zai wulaqanta? Toh wlh bamu yayima ba kansu suka yiwa, akwai ranan nadama tana zuwa, wallahi Abdallah duk wanda ubangiji ya rufawa asiri ba mai tona masa, muje yanzu a d'aura auren da Abdullahi d'ana wanda na isa da shi.. Kuma kakaf dukiyar da aka kashe ma Ummulkhairi, aka kai gidansu aka shirya komai acan bamaso abarmusu, ni zan mata komai sabo, ayau akawota gidana bayan d'aurin aure tayi zamanta can, kafin Abdullahi ya dawo daga Singapore, an shirya mata komai na 'yar gata.”
Ya k'arashe magnar ransa amugun b'ace tamkar Maryam 'yarsa ce akayiwa cin mutuncin nan.
Ya d'agawa securitynsa hannu, cikin rawar jiki ya beqo masa wata zungureriyar waya mai kyau, ya latsa wata lamba bugu d'aya aka d'aga ya furta.
Kawu Bala yanzu akawomin huhun goro biyar da alewa da dabino central mosque kuzo kamar Ku goma azafafan motoci daman nida jama'ar tawa muna nan kawai inason aga wasu sun qaru ne, abun zaifi bada citta.”
Ya k'arashe maganar yana katse kiran, kawai sai ya zura wayarsa cikin aljihunsa.

Shattima ya zubawa alhaji Aminu idanunsa cike da mamakinsa, yana tunanin wata irin k'auna ce Aminu yake masa da zai fitar dasu kunya, yasan shi d'in mai k'aunarsa ne tin tashinsu,duk da Aminu ya basa wajan shekaru biyar ahaife,kawai amince ne suke wanda Allah ne ya had'a jininsu.
Hannayen Aminu ya riqe cikin dattaku yake magana.
“Haba commissioner! Ya zakama my takwara haka baya k'asar ka d'aura masa aure da k'anwarsa? Bayan kasan akwai wacce yake so shima kamar ransa?”
Fuska commissioner Aminu ya had'e ya ce“Dallah can ni fa kaga abinda yake had'ani da kai fulatancin ka, da kawaicin da bazai anfanemu ba, duk da kana ministan ilimi, har yanzu kana nan da fulatancinka, yanzu sbd Allah har na haifi d'an da zan bashi umarni yaqi binsa? Abdulahi ne zan tsaya sai naji ta bakinsa kafin na aura masa wacce nake so? Har yamutu zai samu mace ne kamar daughter Ummulkhairi? Ai kabar mgnar nan kawai Abokina.”
Shattima kasa mgna yayi sosai farin ciki ya gama lulub'e shi ya rungume Aminu yana godiya.
Dukan wasa ya masa abaya ya Ce.
“Kul na kuma ji tsakanin mu ba godiya komai nayi maka ko kamin _yiwa Kai ne.”_

Cikin masallacin suka koma, ba'a fi mintuna 15 jama'ar da Aminun yayi kira suka hallara cikin masallacin tare da dukkan abinda ya buqata.
Nan aka gabatar da dukkan abinda ya dace na neman aure, nan dubban jama'a suka sheda aure tsakanin Abdullahi Aminu kazaure, da Ummulkhairi Abdallah Umar shattimai,akan sadaki mai daraja naira dubu d'ari uku, lakadan ba ajalan ba.

Bayan d'aurin aure akayi tarin addu'o'i na neman Allah ya basu zaman lafiya,da yiwa k'asa addu'a da neman kwanciyar hankali da arziqi me anfani.
Aka raba goro da alewa da dabino, masha Allah abin sai wanda ya gani.
Haka taron ya watse cikin farin ciki da annushuwa, ba tare da jama'a sun ankare juyin mulkin da akayi ba wajan d'urin auren ba, sai malam Umar da wasu daga cikin 'yan uwansu.

Unguwan (commissioners Quarters).
Wani qerarran gida ne mai kyawun gaske, wanda tin daga dogayen shifkokin da suka zagaye da dogayen katangun gidan, zuwa tamfatsetsan gate d'in gidan zaka san gidan na masu fad'a ajine.
Tin daga layin da zai sadaka da gidan kake jiyo kid'e-kid'e tare da busar sarewa na tashi, zaka rante gidan sarkin dutse ake aure,maroqa da mawaqa
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download YI WA KAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album