Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MAFARKIN FARIDA Complete Hausa Novel Document by MAFARKIN FARIDA


MAFARKIN FARIDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 159424



MAFARKIN FARIDA

Reading Time: 13 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 8061929616, 08033933642, 09032409668, +227 90795939

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 811.36 kb

File Type: txt

Views: 855+

Download: 2284+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [1/1, 10:23 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭
COPY BY ZAINAB BUTALAWA







BISMILLAH


INA MATUKAR GODIYA GA ALLAH DA YA BANI IKON RUBUTA MUKU NOVEL KYAUTA BANA KUDI BA FANS,WANNAN SADAUKARWA NE GAREKU MASOYANA NA AMANA.






BA NA KUDI BA NE




WANNAN NOVEL SADAUKARWA NE GA YAN GROUP DINA NA


DUNIYATA AAMNA FANS GP.








1-3







LITTAFAN DANA RUBUTA
SUNE

GASKIYA CE
MA'AIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
ME MAGANI
TUBABBIYA
HADIN KAI
RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA
DANGIN RABI
DUNIYATA AAMNA
MAFARKIN FARIDA....








Official










By
AsmaBaffa












Page naku ne

UMMI DEEJAT
MAMU GALADIMA
ALHUSNA (MRS IDRIS)
AUTA
HAFSATOU
NAFEE














Baki ta cuno gaba tana baccinta tana mutsutsu tare da kankame jikinta waje Daya tana sake cinno bakinta gaba,Juyi tayi tare da Bude hannaye kamar zata Rungume wani tana Kara turo labbanta gaba,wata Dattijuwa ce wankan Tarwada ta fito Daga daki sanye da t-shirt da zanin wata jar atamfa Wanda atamfar da t-shirt din sun Gama Jin jiki,sun kode sun jeme sun fita a hayyacinsu,wuyan rigar har ta farke,daga bakin wuyan kamar bera ya gwigwiye,Kanta ba Dankwali gashinta Kamar shekar Ungulu,an Masa kitso Amma kitson ko jela babu sabo da Rashin gashi na wannan dattijuwa,Kitson ya Gama tsufa tukuf shima.

Yarinyar da baza ta wuce 19yrs ba wacce ke bacci a saman wata fukatacciyar Tabarma karkashin bishiyar mangoro,Dattijuwar ce ta shiga tashinta Farida....Farida....ke Faridaaaaaa......a firgice Budurwar ta farka ta Mike zaune tana wani murmushi ita kadai ta kalli kasa Kawai tayi wani mutuwar zaune tace Hajiyanmu.... Hajiyata wani mafarkin ne,wallahi wani mafarkin ne,mafarkin da nake tayi kusan kullum,mafarkin hadadden,zukeken,santalelen charming prince,the Handsome prince,The Honey Prince and Amazing prince Hajiya,Iyyeeeeee...Dattijuwar da aka Kira da Hajiya ta furta,tana wani washe Baki tana murna ka rantse itace tayi mafarkin,Farida tace Hajiya karki so ki ganshi kamar Aljani sabo da kyau,fari wani irin haske me wani sa Ido dum da shi Hajiya,Dattijuwar ta karyar da Kai gefe tana uban murna tana kallon Yarta tana Iyyeeeeee,Ehemmm....Ina jinki Farida ta.....

Farida taci gaba da furta yau mafarkin ya banbanta Dana kullum Hajiya,yau a wata duniya na hango mu Ni da shi,munsha fararen Kaya,Yana cikin wata shegiyar suit fara zata Kai million Hamsim,Eyemmmm Hajiya ta Furta da karfi tana murna tana washe Baki,Farida taci gaba da cewa Hajiya da mota fa naje Wajensa wata baka zata Kai ta Million dari da wani Abu,shi Kuma tasa motar fara zata Kai wajen million dari uku da wajen saba'in da Yan kwandaloli, Dattijuwar rawa ta fara da Juyi sabo da Murna tana Waka
Lale Iye rambada
Lale Iye Rambada
Wallahi 'yata ta Haye,kwana Nan Zan fara gani na cikin Lace da manyan shaddoji,ai matar Gomna ma Uwata karya ne ta kaini hutawa,kwana Nan Zaki rushe Mana wannan gidan na talauci ki Gina Mansion,Takawarki Lafiya Gimbiya Farida.

Ai Farida wani Dadi ya sake kumeta Jin kirarin da Hajiya ke Mata,Farida Tace Hajiya ki tsaya kiji karashen mafarkin Mana,Hajiya tana ihun murna Tace Ina jinki Yata ta kaina,Farida tace Ina fada Miki da naje da motar million dari din Nan shima yazo data million dari uku da haya haya ai sai Muka fito Hajiya Ina Jin kunyarki Amma Zan fada Miki tunda bana boye Miki komai,Hajiya da sauri tana wangale Baki tace Allah na tuba Farida me kike boye min ai nice mahaifiyarki Kuma kawarki,wannan Abu ma da ya samu idan mafarki ya tabbata ai Zan shiga daula karki ji komai fada min ko kunyi aure ne a cikin mafarkin? Farida tana dariyar murna tace Ashe kina da kwakwalwa Hajiya ta munyi aure Muna soyayya,ya Rungume ni fa a jikinsa kam,Hajiya tana rufe Baki Amma tana tuntsurewa da dariyar murna ta furta kudi suna Kan hanya mun kusa Zama masu kudi,daga Nan sai aka Yi Yaya Kin Haihu a cikin mafarkin? Farida tace a'a an dai daura Aure Muna soyayya Ina jikinsa Hajiya yayi min wani mahaukacin Kiss sai na ganni a wata Aljannar duniya gaba Daya wajen American Dollar ne sun baibayeni sune grass din wajen,Ai Hajiya sai ta saki rawa da Juyi bilhakki sabo da Murna.

Farida Tace a wajen yace Baby ki bani Jerusalem naki,Ihu Hajiya ta kurma tana wayyo wannan yasan soyayya na Gane Jerusalem din da yake nufi yo in da kudi me zai Hana,Farida tafin murna tayi tare da mikewa tsaya tana Juyi tana Taku dai dai tana yanga,Hajiya tana kaga gimbiya Takawarki Lafiya ta prince ikon Allah,Alherin Allah ya Kai Miki wata tafiyar sai a Birnin tarayya,Farida Tace hmm ai kafin a Kai ga na bashi Jeru din Hajiya sai na farka,Hajiya da tausayi Tace wayyoooo banji Dadi ba,Amma karki damu Dole mu tafi gidan Malam Haru Haru ya fassara Mana wannan mafarki,wannan Bai kamata ayi ta mafarki shekara kusan biyu Amma Bamu San ma'anarsa ba,nasan ma mijinki ne,shine Zaki aure,ai tunda na tsuguna na haifeki kika Fado duniya naji a jikina ke matar manya ce,ke matar Hamshakin me kudi ce, Farida tunda na haife ki naji a jikina da ke Zan jingina,a jikinki Zan huta,kece silar arzikinmu,nasan ma ya kusa kawo Kansa gareki,nasan kwanan Nan zaizo Neman aurenki.

Farida ta sheka da gudu ta Kai karshen bangon gidan ta dawo wajen Hajiya sabo da Murna ta rasa inda zata sa kanta tana haki Tace Hajiya ya kamata na fara koyon tafiya da takalmi choge,ya kamata na iya yanga da karairaya,sannan yanzu ne ya kamata na fara canja salon Taku da magana a city din Nan,so nake kowa ya kalleni yasan Ni ba matar Kana Nan Yara bane,maganata ta koma ta Yan gayu sabo da kar Prince yazo ya Iske Ni ba Yar gayu ba,kin San su manya ne sun Saba da Yan gayu,Hajiya Tace yo ai ba ke kadai ba Farida har Dani sabo da Nima Kar Iyayensa suzo Yan gayu ban iya magana da taking gayu ba,Maganar Hajiya ta fara gwadawa itama.

Sassanunku da zuwa...kit Farida ta katseta Tace turanci fa Zaki Yi Hey ku shigo haka Zaki ce,Hajiya tace Hey ku shigo sannunku da Hanya,Sai ki Kara da Wow cewar Farida tana Gyarawa Hajiya,Hajiya Tace to Kinga dai Farida ke Baka ce Amma kyakyawa Black Beauty,Yan Uwanki Kuwa Manal da Yazed ne kadai Farare sabo da kyan Yarinyar Nan bana so ta rabe mu,to yanzu ma ke gashi Allah ya kusa yanke Mana zakiyi aurenki da wuri gobe sai mu shirya muje wajen Malam Muji Mene ke tafiya.

Daga cikin wani dagargajenjen daki Wanda gaba Daya ya Gama rubewa dakin Kamar zai Rufta duk Kuwa da cewa na Bulon Siminti ne,wani Mutum ne ke buga Kofar ta ciki wacce a kulle take gaba Daya,sai lokacin Hajiya da Farida Suka kalli Kofar Dakin suka ja tsaki a tare ,Hajiya Tace na Gama tsanar tsohon cen wlh ban San kaddarar da tasa na aure shi ba wlh,tunda nake sai yanzu na gane tsohon Nan bashi da mutunci sam, Farida Tace kece Hajiya kika cuce mu ke da Zaki auri me kudi da yanzu a can gidan me kudi aka Haifo mu Amma sai gashi kin Kare a malam,Wai shine Baban mu,wlh Ina Jin kunya Ni bana son nuna shi ma,shi yasa bana so Kawayena su dinga zuwa suna ganinsa a matsayin Mahaifi na wallahi Ina su Alhaqatu ne da su Masatura?Hajiya tace ai duk suna makarantar Allo Falaqi ne Kawai Yana dakinsu zazzabi ya rufe shi,Ina Uban Iyayin Nan Yazed? Hmm Hajiya ta tabe Baki Tace Yana lecture Bai dawo ba sai wani dagawa yake shi a Dole ya kusa Gama Degree Dan Iskan fikalallen banza,Degree din banza ya Gama Degree dinsa yazo na bashi Aiki cewar Farida.

Wata yarinya ce ta shigo zata Kai a kalla 9yrs,Farida tace Sa'iha ta dawo ga Sa'ihar mu ta dawo,Sa'iha ta karaso da gudu da Allonta tare da fadawa jikin Farida tadagata sama suna dariya,Kofar da Malam yake ce ta sake Kara yana ta dukan kofa babu Wanda ya kulashi sai da Yazed ya dawo daga lecture sanye cikin kana Nan kayansa Wanda sun Sha jiki da gani kasan Yana fama da talauci gashi kyakyawa fari tas da shi da gani shi ya fita zakka a gidan,da gudu ya karasa dakin Malam ya bude ya Iske Dattijon har ya Fado ma daga saman kujerarsa ta guragu wheelchair wanda shi ba gurgu bane da kafafunsa Amma baya iya hasalawa Kansa komai Dan Ma Allah yasa hannunsa Yana Dan aiki,Yazed yace Malam Ina Za'a kaika kayi Hakuri bana gidan Ina
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MAFARKIN FARIDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album