Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

WATA RAYUWA Complete Hausa Novel Document by WATA RAYUWA


WATA RAYUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28060



WATA RAYUWA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 04, Apr 2025

Author: Sadi Sakhna ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 170.57 kb

File Type: txt

Views: 11+

Download: 16+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: 
(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=Ayeeshatmuhd&wp_originator=zwWkFi8UrQ15wCJ97IpYA%2BgQnfGX9PzVmleI%2FrEP8a5KYyZPDI3Q6FDITR%2F8c8JH%2Bh4M%2FiYfRaUnBHccl04WBnkR5Lgh%2B6M6I417gK74LZ5o2mKGtm64Fl95iySLrmh8

*BY SADI-SAKHNA*

Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟


SANARWA
Wannan littafin kirkirane, domin babu abububwan dasuka ci karo da rayuwar zahiri acikinsa.Amma idan kinga ko kaga yaci karo da rayuwarka dan allah amin afuwa yanayine yasa .Sannan wannan littafin kirkira tace,kuma dan allah akiyaye kwafa ba da yaddata ba.NAGODE sosai makaranta harma da marubuta,domin bazamu cika burinmuba saida yardarku.Ayi karatu lfy.
,
(01)
Mafari......(Garin BARDUGU).

BARDUGU garine wanda yake boyayye a duniyar ta mutane,sanadiyyar surkukiyarsa cikin daji dakuma duwatsu,garin bardugu ya kunshi mutane masu wani irin hali mai wuyar sha'ani a tsakanin mutane,a sanadiyyar halayyarsu har yakai mutane basa son yin mu'amala dasu,sannan kuma basason zuwa inda suke .Aduk inda akasamu abu marar kyau a waje to za'asamu kuma abinda zai burge ko yadauki hankalin al'umma,to hakane yakasance a garin bardugu domin garin na dauke da kyakykyawan muhalli harma da kyawun yanayi wanda ba'a samunsa a wannan duniya tamu,saidai yana dauke da dumbin kabilu masu matukar hadari dakuma tsafi,sannan babban abinda yake bawa mutne tsoro a garin na bardugu shine ;akwai daukar hukunci mai tsauri ga duk wanda ya aikata laifi a a garin sannan yafewa wanda ya aikata laifi tamkar haramunne a garin,wannan shine kadan daga cikin hallaya na mutanen dake cikin garin bardugu,kubiyoni acikin littafin na WATA RAYUWA zakuji abubuwan mamaki harma dasu ban sha'awa ban tausayi dakuma ban haushi acikin wannan littafin,karku manta tare da marubuciyar sadi-sakhna(the legendary novelist)

ACIKIN GARIN BARDUGU ANGUWAR TSARAUNI....anguwace ta makaskantan mutanen dake cikin garin.

Faariya! fariya!! fariya!!!,shaine abinda wata mata take fada daga bakin wain daki cike da masifa,matar bazata wuce shekara hamsin ba a duniyarmu amma yanayin garin na bardugu dayake dauke da abubuwa dasuka yi sabani da hankailnmu,matar na dauke da shekara darine harda yan kai a rayuwar ta bardugu.Yarinyar da'ake kwalawa kirane tafito daga daki fuskarta cike da tsoro dakum fargaba,tsayawa tayi agaban matar duk ilahirin naman dake jikinta rawa yake yi,karar marin data kwadawa yarinyar ne ya firgitar dani matuka ,domin ko babban mutum ya karbi wannan nau'in marin to lallai zaiji ajikinsa ballanta yarinya sannan cikin karfin yanayin irin na mutanen,tagataga tayi tamkar zata fadi kana ta tsaya "menene ya tsaidake ga barin zuwa wajena harkika bari namiki kira uku baki zoba?iyee ba magana nake miki ba ?kuma ai waccar uwar taki bata nan na aiketa deban ice bare ki ce a wajenta kike ko?shine abinda take fada cikeda masifa,cikn kuka yarinyar take bata amsar tanbayarta "kiyi hakuri baaba aryana,na tsaya karisa cinye guntun abincin da maamam tabarmin ne ,kuma idan nabarshi ban cinyeba beraye zasu cinyemin,"shine abinda tafada wa aryana nan "dallah yimin shiru ki tashi kije debomin ruwa a rafi "marin da aryana ta zubawa fariya bai firgittataba kaman sunan rafin da ta ambata,(domin kowa dayake garin bardugu yasan hatsarin dayake dauke da rafin anguwar tsaraunin,saboda halittun dasuke dauke a wajen,wanda ko acikin garin na bardugu ba kowa ne yasan dasuba.Acikin halin na bayanda zatayi ta tashi ta dauki tulun deban ruwan ta nufi hanyar kofar fita waje wanda aka daure bakin kofar gidan da tsumma.
WACECE FARIYAH sannan menene dangartakarta da wannan matar wato aryana?
Ainihin sunanta shine FARIYATUL SHARMEELAH,sannan takasance mutumce daga duniyarmu wanda hakan ya samo asline sanadiyyar zuwan mahaifinta garin bardugu.
Ashekarun baya da suka shuade anyi wani zamani da mutane dasuke garin bardugu suka fara zalintar mutanen da suke doron duniya,sanadiyyar karfinsu daya zarta na mutane ,inda suka fara kama mazaje da mata suna maida su bayinsu karfi da yaji,ganin hakn yanason wuce gona da irine yasa masarautar SARDAHAM (daular da take mulkar dukkan nahiyoyin wannan zamanin karkashin jagorancin sarki HURUDDEEN dan SHAMAM,bayan daidaita matsalar dake tsakaninsu sai yazamana mutanen da yan garin bardugu suka kaisu dan su musu bauta sun samu yancin komawa kasarsu,sannan hakanne ya yanke duk wata alaka ta sanayya atsakaininsu.Saidai babban kuskuren daya faru shine rashin komawar SHURAIM gida sanadiyyar fadawa soyayya dayayi da yar gidan uban gidansa,domin kuwa duk da kangin bautar daya shiga bai saka shi komawa garinsuba saboda wata makauniyar soyyaya daya afka cikinta marar billewa.Ganin da baban HUDA yayi nacewar bawansa yaki komawa ga kasarsa dukda damar da'aka basu na komawa ga iyalansu sai abin yabashi mamaki matuka harya fara bincike akan hakan,lamarin yagirgizashi sosai dayagano cewar soyyaya suke da yarsa HUDA,duk wani aiki dayake bashi na wahala sai yazamto cewar ya ninka akan wanda yake masa a baya,duk wannan wahala da shuraim yake fuaskanta daga wajen baban huda hakan bairage koda kwayar zarrah na soyayyar huda azuciyarsaba,al'amarin ya bakanta ran iyayen huda harma da sauran yan'uwanta,sannan aduk sanda sukayi kokarin kawar da rayuwarsa sai yazamana tamk
ar yarsu suke kokarin kashewa,ana ckin hakanne huda taja saurayinta shuraim akan su gudu subar nahiyar tasu,saidai basukai ga cimma nasara ba mahifinnnata ya fahimci nufinta,inda ananne aka yanke mata hukunci tsinuwar kaskanci a rayuwarta,yazamana duk inda zata shiga a fadin duniya bazata kasance mai mtsayi ba kaman yanda tkae a da ba ,sannan hukuncinta bazai taba barta ta tsallaka nahiyar suba.Wanan abinda yasamu huda yasa shuraim jin tausayinta matuka inda yagudu da ita aanguwar tsarauni ,domin shine anguwar dazasu zauna batare da angane hukuncin dake jikintaba.

Saida shuraim suka dauki wasu shekaru suna rayuwar farinciki inda yazage tukuru yana aiki domin ciyar dasu abinda yasmu,bayan wani lokacine huda tasamu ciki ta haifi yarta mace inda aka sama suna fariyatulsharmilah domin shine sunan datake mafarkin sakawa yarta da ta haifa,inda ake kiranta da farkon sunanta wato fariyah.Fariyah yarinyace da tataso cikin gata sannan kuma da abubuwa mabanbanta da rayuwar mutanen wajen sanadiyyar debo kashi 90 na jinin mahaifinta,sannan kuma dagatan datake samu daga iyayennata.Wargajewar rayuwar farin ciki na rayuwar su fahriya yasamo asaline da mutuwar da mahaifinnnata yayi,saiyazaman ya bada amanr iyalansa a wajen wani abokin aikinsa,saidai bai dade da mutuwaba abokinnasa yagano cewar huda tana dauke da tambarin kaskanci da iyayenta suka mata a matsayin hukuncinta,inda yaci amanar abokinnasa shuraim ta hanyar sayar da ita da yayi a bangarennasu ga wata hamshakiyar yankinnsu wanda kowa yasanta da hulda da manyan mutanen dasuke cikin garin wato ARYANA, matace datake bukatar ta dinga mulkar mutane saidai batasamu hakn ba,hakan yasa lokacin da abokin shuraim din yaci bashinta ta matsa masa daya biyata sai,yashiga damuwa,amma lokacin daya gano hukuncin huda sai yabada ita ga aryana a matsayin bashinsa ,sannan shikuma yatashi yabar anguwar.
Rayuwar huda itada yarta ta yashiga cikin kunci sosai a wajen aryana,amma dukda haka huda bata taba nadamar biyewa soyayyartaba domin indai fariyah na gefenta ji takeyi babu ya ita a duniya,saboda kama da tayi da mahaifinta ,dakuma zallan kayunsa data debo.Duk wani kunci da huda take fuskanta hakan bai hanata farantawa yar ta taba da kuma yimata duk wani abu data ke bukataba,saidai lokacin da fariyah tayi shekara goma aduniya sai yazamana hakalin aryana yadawo kan ta,sannan kuma da wani buri data dauka wanda ita kadai tasanshi akan fariyan.

CIGABAN LABARI.........
SADI-SAKHNA Aka the legendary novelist next chapter loading......


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=Ayeeshatmuhd&wp_originator=zwWkFi8UrQ15wCJ97IpYA%2BgQnfGX9PzVmleI%2FrEP8a5KYyZPDI3Q6FDITR%2F8c8JH%2Bh4M%2FiYfRaUnBHccl04WBnkR5Lgh%2B6M6I417gK74LZ5o2mKGtm64Fl95iySLrmh8

*BY SADI-SAKHNA*


(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

written by sadi-sakhna

(02)
Daukar tulun tayi cikin sanyin jiki ta fita izuwa ga rafin tana sake-saken yanayin rayuwar tasu itada umminnata,da i0rin halin matsin da ta ta
so ta tsincesu aciki,duk da karanci shekarun fariyah amma takasance mai kaifin tunani dakuma basira,sannan tanada sanyi dakuma hakuri,yarinyace mai son taga tana da abokai dazata dinga wasa dasu ,saidai a yanayin data tsinci kanta yasa ta fuskantar tsangwama da kyama daga wajen su ,wanda hakan yasa sha'awar wasa da yaran yafara fita mata akai sai yazamto rayuwanta yazama tamkar ita kadai takeyi ,sanaddiyyar aiki da mahaifiyartata takeyi bata samun lokacin ta sai sanda zasu kwanta,a lokacin kuma yanayin gajiya yashiga jikinsu basu da lokacin tattauna matsalarsu.Dahaka tana cikin tunanine har ta iso ga babban rafin dayake nesa kadan da muhallinnnasu na tsarauni,zaunawa tayi a bakin wani dutsi gefe da rafin tana karewa wajen kallo,zuwanta baifi a kirgaba wajen saidai bata tba cinkaro da abinda ake cewa na hatsarin wajenba wanda hakan yasa wajen yake bata sha'awa matuka ,domin wajen nadauke da wasu irin tsuntsaye masu kyan gani harma da yan dabbobi dasuke kiwo a wajen ,sanadiyyar kyawun wajen dakuma iskar dake kadwa a wajen ga kuma ruwa sai hakan yafara kwantar mata
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download WATA RAYUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album