Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SHIRYAYYAR ƘADDARA Complete Hausa Novel Document by SHIRYAYYAR ƘADDARA


SHIRYAYYAR ƘADDARA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 152630



SHIRYAYYAR ƘADDARA

Reading Time: 12 Hours

Added On: 24, Feb 2025

Author: The Nainarh KD ,Queen Kainert ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09131306012, 08133650574

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 792.07 kb

File Type: txt

Views: 38+

Download: 77+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: 𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫

🎀


_*🔥🔥SHIRYAYYIYAR ƘADDARA 🔥🔥💫*_




_*Season one*_
_*FREE*_❤️🔥


𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛 𝐾𝑎𝑖𝑛𝑒𝑟𝑡..... ✍💫

𝑇ℎ𝑒 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒𝑟 𝑜𝑓 𝐷𝑜𝑐𝑡𝑜𝑟 𝑆ℎ𝑎𝑧𝑖𝑚 𝑎𝑛𝑑 𝑛𝑜𝑤 𝑠ℎ𝑖𝑟𝑦𝑎𝑦𝑦𝑎𝑟 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎

_*Episode 1_2*_


_*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma ɗaukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi.*_

_*Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏*_

❌❌❌❌❌❌❌

_*Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin nan ba ta kowace hanya ba tare da an nemi izni a wurina ba.*_
_*idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi min haƙƙina!*_

_*Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin zarafin wani ba, duk wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi to arashi ne ba da nufi ba*_.


*A big big hug to Khadija Sabi'u yahaya A.k.a Nainarh kd Nkds*

*special thanks to Ameenatu Muhammad Yakasai A.k.a oum Yasmeen the writer of Binta ƴar jagaliya*


_*Dedicated to my family*_


*@Kainaat1733*
*Wattpad*




_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_

1:30 am



*Sydney,Australia*



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘



______________________________




Can cikin bacci taji ana nocking window ɗakin da su ke,a hankali ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nauyi.


sake nocking ɗin window a kayi, gabanta ne ya ɗan faɗi dan duk a tunanin ta a mafarki ne taji nocking ɗin ba gaske ba.


jin an dage da nocking ɗin ne yasa tayi saurin kallon gefanta, baccin shi yake shara abun shi hankali kwance, magidanci ne da a ƙalla zai kai kimanin shekaru 60 a duniya,baƙi ne kyakyawan gaske matar dake gefan shi itama zata kai kima nin shekaru 46 zuwa da 8 a duniya.


fara ce kyakyawa ajin farko, kai tsaye idan ka kalleta ba zaka ce zata kai kimanin wannan shekarun ba.


ɗan bubbuga pillow da yake kwance ta shiga yi tana kiran sunan shi cikin muryar raɗa
“ranka ya daɗe! ranka ya daɗe!!” a ƙalla sai da ta kira sunan shi kusan sau uku ba tare da ya farka ba still ba'a fasa nocking ɗin da ake yi ba.


ƙara sautin kiran sunan shi tayi cikin harshen hausa take faɗin“dan Allah ka tashi, inajin fa babu lafiya yau a ɗakin nan” ko gezau baiyi ba gashi wanda yake nocking yanzu ƙoƙarin buɗe window yake ta ƙarfin tsiya ya shigo.


cikin muryar kuka ta fara haɗa shi da Allah akan ya tashi
“dan Allah yallaɓai ka tashi , babu lafiya”
can cikin baccin shi yaji shashekar kukan ta, firgigit ya faraka, jin dai da gaske kukan take ne yasa shi tashi da sauri yana faɗin“lafiya mi yasa ki ku ka??”


window ta nuna mashi cikin yin ƙasa da murya tace“wani ke ƙoƙarin shigowa ta window” duban shi ya kai ga sliding door dake ɗakin,wacce mutum idan yaje gabanta ko ya buɗe zai iya hangen cikin garin sydney da harabar hotel ɗin.



zuro ƙafar shi yayi daga kan bed ɗin ya sauko wurin window ya nufa, ɗan saurarawa yayi,bugun windowa yaji anyi da ƙarfin gaske can yaji sautin kukan mace cikin harshen turanci tana faɗin“please open the door, help please!”


ɗan ja da baya yayi yana mamakin wacece kuma mi ya kawo ta window ɗakin su duk yawan ɗakunan dake cikin hotel ɗin tarasa in da zata zo sai na su, banda zare ido babu abunda matar dake zaune kan bed take.

ƙara ƙarfin kukan tayi da dukan window tana cigaba da faɗin“please help me,open the door please”


shahada kawai yayi ya nufi window, hannu yasa ya yaye curtain ɗin dake jikin window,matashiyar baturiya ce ya gani tsaye da uban ciki haihuwa yanzu ko anjima,da ƴar madaidaiciyar jaka rataye a kafaɗar ta, a ƙalla zata kai kima nin shekaru 25 a duniya.


fuskar ta sharkaf da hawaye idanunta sunyi jawur hakama hancinta da kumatunta, kyakyawa ce ajin farko tana da manyan idanuwa da tsayayyen hanci har baka sai ɗan ƙaramin baki mai ɗauke da red lips tana da tsayi dai dai misali.


baƙar duguwar riga ce a jikinta, har ƙasa rigar ta kai mata, ta rufe kanta da mayafin rigar.

ganin yayi shiru ya zuba mata idano ne yasa ta sake fashewa da wani kukan tana sake roƙon shi da ya taimake ta.


tasowa matar dake zaune kan bed tayi ta nufo bakin window, kallon baturiyar dake tsaye tayi daga sama har ƙasa.


“yallaɓai mu taimake ta” ta faɗa tana kallon mijin nata dake tsaye.
hannu yasa ya buɗe door, kamar jira take ya buɗe da mugun sauri ta shigo cikin ɗakin kamar zata faɗin,sakin jakar dake rataye a kafaɗar ta tayi, da sauri matar ta taro ta tana faɗin ki kula cikin harshen turanci.


kamata tayi har zuwa cikin ɗakin, jakar data yarda mutumin ya ɗauka yana bin bayan su,sofa da ke ɗakin su ka nufa, zaunar da ita tayi, a gefanta ya ajiye mata jakar, nufar wani ɗan table dake ɗauke da robar ruwa da cup matar tayi, ɗaukowa tayi ta dawo wurin sofar.


tsiyaya mata ruwan tayi a cup ta miƙa mata, hannunta har rawa yake wurin amsar cup ɗin, kallon mijinta dake tsaye matar tayi wani irin tausayin baturiya ne ya kamasu daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba.

da sauri ta dafe ƙaton cikinta tana ɗan rintse ido da fatin “Auch, oh my god”

ƙoƙarin miƙewa take saboda wani ciwan mara daya taso mata lokaci guda, da sauri matar ta ajiye cup ɗin hannunta sannu ta shiga yi mata tana sa hannu ta taro ta.


ƙara baturiya ta fasa tana faɗin matar ta kaita toilet,matar kamar zata fashe da ku ka ta kalli mijinta tana faɗin“haihuwa ce za tayi”ɗan zaro ido yayi

“ya za muyi kenan?”
“nima ban sani ba, da ace a gida muke ina da komai da zamu buƙata”
“haka ne, yanzu babu wani taimako da za ki iya yi mata?”
“akwai sai dai su kasan basa son haihuwa a gida sai a hospital”

“yanzu tana a wannan halin ina ruwanta da inda zata haihu, tunda dai Allah yasa ke dr ce kawai kiyi mata abun da ya dace”


“shikenan”matar ta faɗa,barin wurin mijin matar yayi ya koma can nesa da su sosai.

tai makon gaggawa matar ta shiga bata, banda kuka da kiran sunan mahaifiyar ta babu abun da baturiyar nan ke yi.


sannu matar ke mata tana bata haƙuri, ba ƙaramar azaba baturiyar ke sha ba matar na iya bakin ƙoƙarin ta ganin ta taimake ta.


mijinta ma dake can nesa da su adu'a yake tayi Allah ya sauƙeta lafiya.


wahala sosai take sha gashi har yanzu haihuwar sai a hankali, barin wurinta matar tayi ta nufi mijinta fuskarta duk tayi jagajaga da hawaye

“yallaɓai ina tunanin dole fa sai mun kaita hospital”
“saboda mi?”
“nayi iya yanda zanyi amma haihuwar sai tazo sai ta koma”


“dr yanzu ya zamuyi?, kinga nan ba ƙasarmu bace fita da ita daga cikin hotel ɗin nan haɗari ne, gashi daga gani yana yin data shigo wani ne ya biyota, kuma na san wanda ke binta duk in da yake yana nan cikin hotel ɗin”
“to yanzu ya za'ayi kenan?”
“shine nima ban sani ba”
“ko zaka nemi alfarma wurin dr mark sai yazo da nurses su dubata”


“anya dr kina ganin barin wani ya san halin da ake ciki ba zai jaza matsala ba kinga nan ba ƙasar mu bace kada daga timako mu jefa rayuwar mu cikin haɗari”
“to yallaɓai ya ka ke so muyi?”

ko rufe baki matar ba tayiba kukan jariri ya cika ɗakin da mugun sauri ta juya ta koma can cikin ɗakin, a durƙushe ta samu baturiyar nan riƙe da jaririya a hannu ga wata sabuwar naƙuda da ta taso mata.



da sauri matar ta nufeta tana amsar jaririyar dake hannunta, towel ta ɗauka ta lulluɓe jikin jaririyar ta kwantar da ita saman sofa a hankali,gaban baturiyar ta dawo tana mata sannu haɗi da bata taimakon daya dace,ko minti ɗaya ba'ayi ba ta sake santolo wata jaririyar fara ƙar da ita kyakyawar gaske kamar wacce ta fara haihuwa sai dai wannan bata numfashi kwata kwata babu alamun rai a tattare da ita.


da sauri matar ta karɓi yarinyar ta shiga jujjuyata,kusa da ƴar uwarta daketa tsala kuka ta matsa ta kwantar da ita,ɗaukar mai ran tayi ta shiga goge mata jikinta bayan ta gama ta gogema ɗayar jikin itama,baturiyar tana daga in da take durƙushe ta kafe kyawawan yaran nata da kallo fahimtar ɗaya bata numfashi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SHIRYAYYAR ƘADDARA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album