Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫

🎀


_*🔥🔥SHIRYAYYIYAR ƘADDARA 🔥🔥💫*_




_*Season one*_
_*FREE*_❤️🔥


𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛 𝐾𝑎𝑖𝑛𝑒𝑟𝑡..... ✍💫

𝑇ℎ𝑒 𝑤𝑟𝑖𝑡𝑒𝑟 𝑜𝑓 𝐷𝑜𝑐𝑡𝑜𝑟 𝑆ℎ𝑎𝑧𝑖𝑚 𝑎𝑛𝑑 𝑛𝑜𝑤 𝑠ℎ𝑖𝑟𝑦𝑎𝑦𝑦𝑎𝑟 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎

_*Episode 1_2*_


_*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma ɗaukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi.*_

_*Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏*_

❌❌❌❌❌❌❌

_*Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin nan ba ta kowace hanya ba tare da an nemi izni a wurina ba.*_
_*idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi min haƙƙina!*_

_*Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin zarafin wani ba, duk wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi to arashi ne ba da nufi ba*_.


*A big big hug to Khadija Sabi'u yahaya A.k.a Nainarh kd Nkds*

*special thanks to Ameenatu Muhammad Yakasai A.k.a oum Yasmeen the writer of Binta ƴar jagaliya*


_*Dedicated to my family*_


*@Kainaat1733*
*Wattpad*




_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_

1:30 am



*Sydney,Australia*



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘



______________________________




Can cikin bacci taji ana nocking window ɗakin da su ke,a hankali ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nauyi.


sake nocking ɗin window a kayi, gabanta ne ya ɗan faɗi dan duk a tunanin ta a mafarki ne taji nocking ɗin ba gaske ba.


jin an dage da nocking ɗin ne yasa tayi saurin kallon gefanta, baccin shi yake shara abun shi hankali kwance, magidanci ne da a ƙalla zai kai kimanin shekaru 60 a duniya,baƙi ne kyakyawan gaske matar dake gefan shi itama zata kai kima nin shekaru 46 zuwa da 8 a duniya.


fara ce kyakyawa ajin farko, kai tsaye idan ka kalleta ba zaka ce zata kai kimanin wannan shekarun ba.


ɗan bubbuga pillow da yake kwance ta shiga yi tana kiran sunan shi cikin muryar raɗa
“ranka ya daɗe! ranka ya daɗe!!” a ƙalla sai da ta kira sunan shi kusan sau uku ba tare da ya farka ba still ba'a fasa nocking ɗin da ake yi ba.


ƙara sautin kiran sunan shi tayi cikin harshen hausa take faɗin“dan Allah ka tashi, inajin fa babu lafiya yau a ɗakin nan” ko gezau baiyi ba gashi wanda yake nocking yanzu ƙoƙarin buɗe window yake ta ƙarfin tsiya ya shigo.


cikin muryar kuka ta fara haɗa shi da Allah akan ya tashi
“dan Allah yallaɓai ka tashi , babu lafiya”
can cikin baccin shi yaji shashekar kukan ta, firgigit ya faraka, jin dai da gaske kukan take ne yasa shi tashi da sauri yana faɗin“lafiya mi yasa ki ku ka??”


window ta nuna mashi cikin yin ƙasa da murya tace“wani ke ƙoƙarin shigowa ta window” duban shi ya kai ga sliding door dake ɗakin,wacce mutum idan yaje gabanta ko ya buɗe zai iya hangen cikin garin sydney da harabar hotel ɗin.



zuro ƙafar shi yayi daga kan bed ɗin ya sauko wurin window ya nufa, ɗan saurarawa yayi,bugun windowa yaji anyi da ƙarfin gaske can yaji sautin kukan mace cikin harshen turanci tana faɗin“please open the door, help please!”


ɗan ja da baya yayi yana mamakin wacece kuma mi ya kawo ta window ɗakin su duk yawan ɗakunan dake cikin hotel ɗin tarasa in da zata zo sai na su, banda zare ido babu abunda matar dake zaune kan bed take.

ƙara ƙarfin kukan tayi da dukan window tana cigaba da faɗin“please help me,open the door please”


shahada kawai yayi ya nufi window, hannu yasa ya yaye curtain ɗin dake jikin window,matashiyar baturiya ce ya gani tsaye da uban ciki haihuwa yanzu ko anjima,da ƴar madaidaiciyar jaka rataye a kafaɗar ta, a ƙalla zata kai kima nin shekaru 25 a duniya.


fuskar ta sharkaf da hawaye idanunta sunyi jawur hakama hancinta da kumatunta, kyakyawa ce ajin farko tana da manyan idanuwa da tsayayyen hanci har baka sai ɗan ƙaramin baki mai ɗauke da red lips tana da tsayi dai dai misali.


baƙar duguwar riga ce a jikinta, har ƙasa rigar ta kai mata, ta rufe kanta da mayafin rigar.

ganin yayi shiru ya zuba mata idano ne yasa ta sake fashewa da wani kukan tana sake roƙon shi da ya taimake ta.


tasowa matar dake zaune kan bed tayi ta nufo bakin window, kallon baturiyar dake tsaye tayi daga sama har ƙasa.


“yallaɓai mu taimake ta” ta faɗa tana kallon mijin nata dake tsaye.
hannu yasa ya buɗe door, kamar jira take ya buɗe da mugun sauri ta shigo cikin ɗakin kamar zata faɗin,sakin jakar dake rataye a kafaɗar ta tayi, da sauri matar ta taro ta tana faɗin ki kula cikin harshen turanci.


kamata tayi har zuwa cikin ɗakin, jakar data yarda mutumin ya ɗauka yana bin bayan su,sofa da ke ɗakin su ka nufa, zaunar da ita tayi, a gefanta ya ajiye mata jakar, nufar wani ɗan table dake ɗauke da robar ruwa da cup matar tayi, ɗaukowa tayi ta dawo wurin sofar.


tsiyaya mata ruwan tayi a cup ta miƙa mata, hannunta har rawa yake wurin amsar cup ɗin, kallon mijinta dake tsaye matar tayi wani irin tausayin baturiya ne ya kamasu daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba.

da sauri ta dafe ƙaton cikinta tana ɗan rintse ido da fatin “Auch, oh my god”

ƙoƙarin miƙewa take saboda wani ciwan mara daya taso mata lokaci guda, da sauri matar ta ajiye cup ɗin hannunta sannu ta shiga yi mata tana sa hannu ta taro ta.


ƙara baturiya ta fasa tana faɗin matar ta kaita toilet,matar kamar zata fashe da ku ka ta kalli mijinta tana faɗin“haihuwa ce za tayi”ɗan zaro ido yayi

“ya za muyi kenan?”
“nima ban sani ba, da ace a gida muke ina da komai da zamu buƙata”
“haka ne, yanzu babu wani taimako da za ki iya yi mata?”
“akwai sai dai su kasan basa son haihuwa a gida sai a hospital”

“yanzu tana a wannan halin ina ruwanta da inda zata haihu, tunda dai Allah yasa ke dr ce kawai kiyi mata abun da ya dace”


“shikenan”matar ta faɗa,barin wurin mijin matar yayi ya koma can nesa da su sosai.

tai makon gaggawa matar ta shiga bata, banda kuka da kiran sunan mahaifiyar ta babu abun da baturiyar nan ke yi.


sannu matar ke mata tana bata haƙuri, ba ƙaramar azaba baturiyar ke sha ba matar na iya bakin ƙoƙarin ta ganin ta taimake ta.


mijinta ma dake can nesa da su adu'a yake tayi Allah ya sauƙeta lafiya.


wahala sosai take sha gashi har yanzu haihuwar sai a hankali, barin wurinta matar tayi ta nufi mijinta fuskarta duk tayi jagajaga da hawaye

“yallaɓai ina tunanin dole fa sai mun kaita hospital”
“saboda mi?”
“nayi iya yanda zanyi amma haihuwar sai tazo sai ta koma”


“dr yanzu ya zamuyi?, kinga nan ba ƙasarmu bace fita da ita daga cikin hotel ɗin nan haɗari ne, gashi daga gani yana yin data shigo wani ne ya biyota, kuma na san wanda ke binta duk in da yake yana nan cikin hotel ɗin”
“to yanzu ya za'ayi kenan?”
“shine nima ban sani ba”
“ko zaka nemi alfarma wurin dr mark sai yazo da nurses su dubata”


“anya dr kina ganin barin wani ya san halin da ake ciki ba zai jaza matsala ba kinga nan ba ƙasar mu bace kada daga timako mu jefa rayuwar mu cikin haɗari”
“to yallaɓai ya ka ke so muyi?”

ko rufe baki matar ba tayiba kukan jariri ya cika ɗakin da mugun sauri ta juya ta koma can cikin ɗakin, a durƙushe ta samu baturiyar nan riƙe da jaririya a hannu ga wata sabuwar naƙuda da ta taso mata.



da sauri matar ta nufeta tana amsar jaririyar dake hannunta, towel ta ɗauka ta lulluɓe jikin jaririyar ta kwantar da ita saman sofa a hankali,gaban baturiyar ta dawo tana mata sannu haɗi da bata taimakon daya dace,ko minti ɗaya ba'ayi ba ta sake santolo wata jaririyar fara ƙar da ita kyakyawar gaske kamar wacce ta fara haihuwa sai dai wannan bata numfashi kwata kwata babu alamun rai a tattare da ita.


da sauri matar ta karɓi yarinyar ta shiga jujjuyata,kusa da ƴar uwarta daketa tsala kuka ta matsa ta kwantar da ita,ɗaukar mai ran tayi ta shiga goge mata jikinta bayan ta gama ta gogema ɗayar jikin itama,baturiyar tana daga in da take durƙushe ta kafe kyawawan yaran nata da kallo fahimtar ɗaya bata numfashi ne yasa ta tashi a hankali ta nufi jariran,shafa fuskar yaran ta shigayi can kuma ta fashe da kuka tana tambayar matar bata da rai ne.



jinjina mata kai matar tayi hawaye na bin kumatunta dan ba ƙaramin tausayi baturiyar ta bata ba,kuka sosai baturiyar ta fashe dashi matar na lallashinta har ta samu tayi shiru.



ɗaya bayan ɗaya matar ta shiga da yaran toilet ta wanke su a cikin jakar da mahaifiyar tasu data shigo da ita kayan jarirai ne harda su teddys,wasu riga da wando na saƙa farare ta sama yarinyar,gawar kuwa lulluɓeta tayi da farin towel ta kwantar saman sofa kusa da ƴar uwarta,taimaka ma mahaifiyar tasu tayi zuwa toilet danta gyara jikinta,ruwa ta haɗa mata da duk wani abu da zata buƙata tukun ta fice daga toilet ɗin ta bata wuri,cikin ɗakin ta dawo ta gyara wurin kamar wani abu bai faru ba sannan ta nufi wurin jariran,ɗaukar jaririyar daketa faman kuka tayi ta nufi mijinta ta miƙa mashi, hannun biyu yasa ya amshi jaririyar
“masha Allah, Allah ya rayata” ya faɗa



“Ameen,ƴaƴa biyu ne sai dai ɗayar ba ta zo da rai ba”
“Allahu Akbar, Allah ya raya mata wannan ɗin”
“Ameen”
“mahaifiyar ta su fa?”
“Alhmdllh ta haihu,tana toilet ma yanzu haka”ta bashi amsa

“masha Allah, amma ya ki ke ganin za muyi da ita duba da yanda ta shigo gashi kuma time ɗin tafiyar mu na ƙurewa?”

“yanzu dai mu bari ta fito na sake duba lafiyarta sannan sai mu tambayeta daga ina take”

“shikenan ba damuwa” amsar jaririyar tayi daga hannunshi




Zama su kayi kan sofar dake kusa da su
“yallaɓai yarinyar kyakyawa ce ina ma ace ni na haifeta”

murmushi yayi yana kallon fuskar matar ta shi“da kuwa munyi farin cikin da bamu taɓa irin sa a ruyuwar mu ba”

“da sai mun tara shagali irin wanda ba'a taɓayi ba a duniya ko da a finafinai da littafi”matar ta faɗa tana sakin murmushi da shafa kumatun jaririyar, shima mijin shafa kumatun yarinyar yayi da fara'a a fuskar shi.


“yallaɓai dan ma ba kaga ɗayar ba,kyakyawa ce itama ta ƙarshe da ka ganta kaga ƴar uwarta sai dai tafi kama da mahaifiyar su kamar an tsaga kara”
“zan so kuwa na ganta”

sun jima a nan zaune suna jiran fitowar mahaifiyar jaririyan daga toilet amma su kaji shiru har lokacin bata fito ba
“yallaɓai anya lafiya?, naji shirun nata yayi yawa”

“haka ne gashi time na ƙure ma na, ko za kije ki dubata?” tashi matar tayi ta miƙa masa jaririyar da tayi shiru tayi lamo a hannunta.



tun kafin ta ƙarasa bakin ƙofar toilet ɗin gabanta yayi wani mugun faɗi, fara fahimtar a kwai abun da ke shirin faruwa ko ma ya faru tayi, ba ta sake tabbatar da hakan ba sai da taga babu gawar jaririyar data bari,da ƙarfi ta ƙwala ma mijinta kira

“yallaɓai!yallaɓai!!” ta kira sunan shi har sau biyu, a hanzarce ya iso in da take , sofa ta nuna mashi da sauri ya kai dubansa zuwaga sofa amma sai yaga ba komai
“mi ya faru ne?”
“babu gawar jaririyar” ta faɗa cikin rawar murya tana zare ido
“to ina mahaifiyar tasu?”
“tana toilet”
“to kila ita ta ɗauketa”




“anya kuwa?” ta faɗa tana zaro ido
“fara dubata ki gani tukun” a hankali tayi nocking ƙofar toilet ɗin shiru taji, sake nocking tayi nan ma shiru taji babu almun mutum,deciding tayi ta tura ƙofar toilet ɗin ta shiga kawai, tura ƙofar tayi ta shiga wayam taga toilet ɗin ba kowa kamar ma ba'ayi amfani da shi ba, gabanta ne yayi wani mummunan faɗuwa da sauri ta fice tana ambaton Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.



“lafiya?” mijin ya tambaya da alum ruɗu
“ba kowa,bata ciki” ta bashi amsa bakinta na rawa
“ya salam, to ina ta tafi?”
“nima ban sani ba” dube dube su ka shiga yi cikin ɗakin wai ko ta shiga wani wuri har bakin window data shigo mijin matar ya nufa yana leƙa wajen ko ta nan ta fita amma bai ga alamun ta nan ta fita ba, hankali su ne yayi ƙololuwar tashi.




“yallaɓai anya matar nan ba aljana bace?”
“wane irin aljana ana zaman lafiya”
“idan ba aljana ba, taya za ace ta fita bamu sani ba kuma da yarinya a hannunta”


“koma dai minene zama nan bai kama mu ba,mu haɗa kayan mu kawai mu tafi Airport dama lokacin tafiyar ya gabato dan hankalina bai kwanta da wannan lamarin ba”

mijin ya faɗa yana kwantar da jaririyar dake hannun shi saman sofa sai a sannan ya lura da ƴar guntuwar takarda da wani ɗan madaidaicin teddy bear a jikinshi an rubuta mommy a kan sofa.



da sauri ya ɗauki takardar ya duba rubutu ne a jikin takardar cikin harshen turanci, fara karantawa yayi da sauri matar ta nufo shi ganin pepar a hannunshi kusan a tare su ka gama karanta abun da ke cikin takardar, da sauri su ka kalli juna

“anya yallaɓai wannan lamarin akwai tsoratar wa, taya uwa za tayi kyauta da ƴarta daga haihuwarta ba tare da ta ko san wanda ta ba”

“gaskiya abun akwai ban tsoro sai dai yanzu abun da za'ayi kawai mu tafi Airport ɗin idan ya so ma kirata tunda ga number waya nan ta rubuta”

“to shikenan” matar ta faɗa tana cigaba da haɗa masu kayan su cikin ɗan madaidaicin trolly, tana gama haɗa kayan ta ɗauki teddy ta saka cikin bag ɗinta sannan ta ɗauko mayafi mai ɗan girma cikin kayanta ta lulluɓe jaririyar a kafaɗa ta saɓa jaririyar mijinta kuma yaja trollyn su ka fice daga ɗakin....




*Abuja_Nigeria*



_*COURT*_





Mutanene ta ko ina a harabar court ɗin ƴan jaridu ne ƴan gidan radio da television , ƴan social media gasu nan birjik a harabar kowa burinshi ace shine na farko wurin ɗaukar rahoton yanda shari'ar zata kaya.


mutane dake kai kawo a harabar da wanda suke zaune sai faɗin albarkacin bakin su suke wasu na iƙirarin idan har hukuncin koto baiyi masu yanda suke so ba to babu abun da zai hanasu ɗaukar doka a hannun su sai dai duk abun da zai biyo baya ya biyo.


mutanen dake bakin gate security sun hanasu shigowa kansu abun kallon ne wasu galan galan na fetur ne a hannun su yayin da wasu tayoyi ne a hannun su duk yan ɗaukar doka ne a hannu idan court batayi masu adalci ba.


Wasu danƙara daƙaran motacine na gidan television suka dunfaro court ɗin tun kafin su ƙaraso police ɗin dake wurin suka shiga kora mutane gefe dan su basu hanya.


A ƙalla motocin gidan tv zasu kai guda biyar huɗu baƙaƙe ne ƙirar reng rover yayin da suka sako tv broadcasting van car white color a tsakiyar su da gudun gaske suka nufo court ɗin,ganin irin gudun da suke ne yasa mutane darewa suka basu hanya, tuni security's sun buɗe masu gate suna ƙarasowa ciki suka shige , sai da suka gama dai daita parking tukun suka shiga fitowa kowanen su sanye yake da journalist jacket black color a gaban rigar anyi rubutu da farin paint inda aka rubuta press da mayan haruffa.


ba ɓata lokacin suka shiga fito da kayan aikin su cameras ne yan uban su dan duk yan jaridar dake wurin babu masu nagartatun kayan aiki masu tsada kamar na su.


cikin ƙanƙanin lokaci suka gama dai daita kayan aikin su bayan sun gama daidaitawa ne aka buɗe back seat na motar dake gaban tv broadcasting van car, wata matashiyar budurwa ce tafito sanye take da pant suit white color tayi roling da black ɗin veil,high hills ne a ƙafarta black color,fara ce kyakyawar gaske wurin cameras ɗin ta nufo cikin takun ƙasaita.

Kallo fa ya koma sama gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kan su sai ƙus ƙus ke tashi a wurin.


wannan matashiyar budurwar ce ta fara gabatar da shirin nasu cikin harshen hausa amma saboda zaƙin muryar ta kamar bada hausa take magana ba

“masu kallon mu barkan mu da sake saduwa acikin shirin mu mai farin jini GANI YA KORI JI, a inda muke kawo maku shari'ar hajiya Asma'u wacce ake zargin dasa hannunta a kisan mijinta wato CP ( commissioner of police ) na wannan jaha ,masu kallon mu idan baku manta ba a wancan lokacin koto ta ɗaga sharia'ar zuwa goma ga wanta febrairun shekarar da muke ciki bisa ga wasu dalilai, a yaune adadin kwanakin da koto ta yanke dan zartar da hukunci suka cika , ku biyo mu dan jin yanda shari'ar zata kaya”


tana gama faɗa ma'aikatan suka kashe kemarorin, wani daga cikin ma'aikanta ne yace “good job BALQIS babu wanda zaice ba LAATIFA ba ce” ɗan ya mutse fuska tayi tana faɗin “thanks” tana komawa back seat ɗin motar data fito, jinjina kai kawai yayi,yana sakin murmushi tana shiga cikin motar wayarta dake ringing ta ɗauka picking call ɗin tayi haɗi da kara wayar a kunnenta, muryar mai kiranta ne ya daki dodon kunnan ta

“ hello balƙis ya aikin yake tafiya?”

ya mutse fuska tayi tana faɗin “wallahi bawani abun duk wahala ne, kuma ni banga amfanin bin wannan shari'ar ba”


“haba balqis miye abun wahalar aciki, na kalli live kuma naga kinyi ƙoƙari, ke da yake ba yar jarida bace shiyyasa zaki ce haka”

taɓe baki tayi tana faɗin “ni dai wallahi kin haɗani da Aiki Aunty laatifa”

“kai balƙis miyasa za kice haka bana jin daɗi kina faɗin haka sai naga kamar na takura maki ne ba da son ranki ki kayi ba” jin abun da laatifa tace yasa balqis cewa “ni baki takura man ba, dan nayi niyya ne yasa na zo”

“shikenan sai kin dawo amma dan Allah kar kice ma dady ni na nace kizo please”

“zance mashi ni nayi niyya ba ke ki ka sani ba,amma kin tabbata zaki cika man alƙawari na?”

“nagode ƙanwata sai kin dawo karki damu”

“ok sai na dawo” balƙis ɗin ta faɗa tana rejecting kiran iska ta fesar daga bakinta,wayarta ta shiga shafawa tana kallon wallpaper wayar tana sakin murmushi,sai sakin murmushi take tana aikin shafa wayar, matso da wayar tayi zuwa fuskarta kissing screen ɗin wayar tayi tana faɗin

“am eager to see u my hero,i miss u”

tana cikin wannan shauƙin taji hayaniya tayi yawa ga kuma jiniyar motocin security Army's da yake glass ɗin motar da take ciki na gaba a buɗe yake,tsaki taja tana faɗin

“i hate this sound gaskiya Aunty latifa baki kyauta man ba” ta faɗa tana ɗan jan tsaki, nocking ɗin ƙofar motar taji anyi da sauri ta juya tana kallon mai yin nocking ɗin ranta a haɗe tace “what?”

“sorry dama cewa zanyi ki fito ga BARRISTER ZULAIHAT nan ta ƙaraso” ya mutsa fuska tayi tana faɗin ok

fitowa tayi daga motar sai wani sa hannu take tana kare fuskanta saboda zafin rana.

wasu jibga jibgan motacin sojoji ne ke shigowa cikin court ɗin gaba ɗaya sun cika court ɗin da ƙarar jiniyar su yayin da tsakiyar su wasu expensive bullet proof latest car ne masu nufashi guda biyu fara da baƙa.

Anan compound ɗin court ɗin su kayi parking,security Army's ne suka fara fitowa daga cikin motacin su hannuwan su riƙe da manyan bindigu ga wasu soke a ƙugun su.


farar motar su ka nufa, wani jibgegen security guard ne ya buɗe back seat ɗin motar.


wata kyakyawar baturiyar mata ce ta fito daga back seat ɗin a ƙalla zata kai kimanin shekara 50 a duniya, kyakyawa ce ajin farko ƴar gayu kai tsaye idan ka kalleta ba zaka ce tayi waɗannan shekarun ba a duniya,sanye take da fararen flat pant suit a jikinta ta yafa farin mayafi a kanta,tana da dara daran idanu farare wanda cikin su ya kasacen Ash ne a manne su ke da farin medical glasse,fuskarta ɗauke take da ni'imceccen murmushi.




𝑏𝑎𝑟𝑟𝑖𝑠𝑡𝑒𝑟 𝑧𝑢𝑙𝑎𝑖ℎ𝑎𝑡 𝑘𝑒𝑛𝑎𝑛 𝑓𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑤𝑖𝑓𝑒 𝑜𝑓 𝑡ℎ𝑒 𝑓𝑜𝑟𝑚𝑒𝑟 𝑝𝑟𝑒𝑠𝑖𝑑𝑒𝑛𝑡 𝑜𝑓 𝑛𝑖𝑔𝑒𝑟𝑖𝑎,𝑤𝑎𝑐𝑐𝑒 𝑚𝑢𝑡𝑎𝑛𝑒 𝑘𝑒𝑚𝑎 𝑙𝑎𝑘𝑎𝑏𝑖 𝑑𝑎 𝑙𝑎𝑢𝑦𝑎𝑟 𝑎𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎ℎ.



daga front seat na motar security guard ce ta fito hannunta riƙe da black coat da white hand bag sai briefcase rataye a ƙafaɗar ta wanda nake kyautata zaton na barrister ne.

wani daga cikin security guard ɗin ne ya buɗe back seat ɗin baƙar motar dake bayan wacce barrister zulaihat ta fito,ƴan mata ne guda biyu su ka fito, dukan su baƙar abayace a jikinsu anyi mata aiki da golding stones sai sheƙi da ɗaukar ido su ke, sunyi roling da glenta,fuskar ɗaya sanye take da niƙab,ɗayar kuwa sunglasses ne manne a fuskarta dake ɗauke da fara'a,hannunta riƙe da ƴar madaidaiciyar bag ta company Gucci golding color,tana matuƙar kama da barrister zulaihat kamar an tsaga kara.



cikin tafiyar ƙasaita balqis ta ƙaraso wurin su tana sakin murmushi,tana isowa hugging ɗin barrister tayi tana faɗin “good morning mom” raba jikin su barrister tayi fuskarta ɗauke da

Please Login or Register in order to submit comment