Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raina ya ɓaci”

“ai naga alama, wai dama mabaruka har yanzu baki daina hargagi da zulaihart irin wannan ba?”

“yaushe kuwa zan daina, ai idan kinga na daina to na sake sender ta ƙasar su kamar shekarun baya” kallon baki da hankali matar ta shiga binta dashi.


“ke har yanzu kina tunanin zaki iya raba Tahir da zulaihart ne, to wallahi idan ma bacci ki ke tun wuri ki farka kar kije garin tsige igiyar Aurenta ke ki tsige taki a banza”


“ban gane ba, mi kike nufi”
“ko wannan matakin daya ɗauka yau akan fa'iz a gabanki saboda zagin ƴaƴanta da ki ka yi ya isa yasa kiyi hankali kisan cewa da da yanzu ba ɗaya bane”

“ni wallahi Hajiya salima kin barni a cikin duhu,dan ban gane inda maganar ki ta dosa ba”

“ kin manta bala'in da ki ka shiga lokacin baya?, da ba dan mama Ameena ba da yanzu kina wani gidan ba wannan ba, idan zaki canza salon kishin ki ki canza idan kuma haka ki ke ganin ya fiye maki tam, shi dai yaƙi ɗan zamba ne”


jinjina kai mamy ta shiga yi alamar gamsuwa da maganar hajiya salima “shikenan naji zanyi ƙoƙarin ganin na sauya”
“hakan dai shi ya fi, ni na shigo ko gaisawa ba muyi ba,kin wuni lafiya?”

“lafiya lau, ya yau ban ganki da tawagarki ba?”
“ki bari kawai ni na hana su biyo ni nace suyi zaman su jaje zanje ba ɗabbaka siyasa ba, ko security cewa nayi su jira ni a waje”


“kina sha'aninki ta wajen Ahmad, ai wallahi ni lokacin da janar na kan kujerar shugaban ƙasa duk in da zani da tawagata nake zuwa ai shine girman”


“ban manta ba” matar ta faɗa, mai aiki mamy ta ƙwalama kira dan ta kawo ma hajiya salima ruwa da lemu.

“ai barshi kawai mabaruka nasha a part ɗin zulaihart tafiya ma zanyi”

“nifa kinga abun da ke haɗani dake kenan,dan mi zaki sha ruwa a wajenta”

“ni dai yanzu idan na sake dawowa na sha, amma yanzu kam gaba nayi”
“shikenan Allah ya nu na man lokacin da zaki sake dawowar” da Ameen hajiya salima ta amsa, a tare su ka miƙe ita da mamy.



har parking space mamy ta rakata, sai da taga tashin motocin ta tukun ta koma ciki.


*ASO VILLA*


Kusan a tare motocinta da motar da aka ɗauko su Ammar daga school ta shigo.

A bakin main entrance ɗin shiga part ɗin su motocin su kayi parking, drivern da yayi driving ɗin su ne ya fito ya buɗe masu,da gudu su ka fito suna nufar motar kakar tasu,suna isowa security na buɗe mata ƙofa ta fito.


da gudu suka faɗa jikinta “oyoyo granny,shine ki ka fita bama nan ko” murmushi ta saki tana shafa fuskokin su
“ayi man afuwa gidan big daddy naje”

shagwaɓe fuska su kayi “amma granny kin san cewa muma muna son zuwa shine ki ka tafi bama nan”

“ayi man Afuwa,ai gobe za ku haɗu dashi a gidan Abbah” ta faɗa tana jan hannunsu suka nufi cikin gidan
“ai gidan Abbah ba gidan shi bane,mu gidan shi muke son zuwa”

“karku damu idan kuna son zuwa sai nasa dadyn ku ya kaiku gobe da kun dawo daga school,kunga sai kuyi ma Aunty Yumnah weekend ko” tsallan murna su kayi


“yeee har gidan papa ma sai muje”
“na san Aunty Yumnah zata kai ku ko ina,amma fa sai dady da momynku sun amince”

ɓata fuska su kayi “dady bazai amince ba mu dai kawai kice ya kaimu”

“to naji muje na duba jikin momyn ku” ɗan zaro ido su kayi suna kallonta

“mi ya samu momy?”
“bata jin daɗi ne” Hajiya Salima ta faɗa dai dai tana tura ƙofar ɗakin kainart ɗin,wayam su ka gani bata ciki har ƙofar toilet sai da Aman yayi nocking amma bata ciki, Ammar ne yace kila tana bedroom ɗin su ,ficewa su kayi zuwa bedroom ɗin na su.


A kwance su ka sameta saman bed ɗin su Aman, idanunta a rufe kamar mai bacci,gaba ɗaya ta rasa mike mata daɗi a duniyar nan,har ta ƙagara ya tattara kayan shi ya koma Lagos.



da gudu su ka ƙarasa in da take,faɗawa su kayi saman jikinta
“momy mun dawo” a firgice ta miƙe zaune dan ba ƙaramin tsoro su ka bata ba, ajiyar zuciya ta sauke ganin su.


“amma yaran nan anyi ja'iran yara,ba kuga bata jin daɗi ba shine zaku faɗa mata haka” Hajiya Salima ta faɗa yayin da ta ƙarasowa bakin bed ɗin.



da sauri kainart ɗin taja gyalen abayarta ta rufe gefe da gafen fuskarta tana kai dubanta ga Hajiya Salima
“momy har kin dawo?”

“na dawo kainart,ya jikin naki?”
“Alhmdllh,ya su mom ɗin?”
“suna lafiya,tana ma gaishe dake”
“ina amsawa”
“mi Dr yace yana damunki?”
“zazzaɓi ne kawai”
“to Allah ya sawaƙa” da Ameen kainart ɗin ta amsa,tashi hajiya Salima tayi



“ku kuzo ko muje can sarah ta shirya ku,kunga momy ba lafiya”
da gudu su ka sauka daga saman bed ɗin suna nufar ƙofar fita,bin bayan su hajiya salima tayi tana sakin murmushi, murmushi itama kainart ɗin ke saki har su ka fice daga ɗakin.




*Uncle Hashim's House*😡



A zaune su ke saman dinning chairs a katafaren dinning room ɗin gidan,baka jin ƙarar komai sai na spoon da plate ɗin da su ke cin abincin.


gaba ɗaya a takure take saboda kafetan da ido da dadynta yayi,hakan ya hanata sukuni,momy da balqis sai cin abincin su suke hankali kwance dan basu san abun da ke faruwa ba.


a hankali ta ajiye spoon ɗin hannunta tana miƙewa da nufin barin wajen,table ɗin ya buga da ƙarfi wanda yayi sanadiyar dawo da hankalin momy da balqis kan su.

“koma ki zauna” ya faɗa da kakkausar murya yana nuna mata chair ɗin data tashi,da ɗan rawa rawar jiki ta nufi chair ɗin ta zauna,duƙar da kanta tayi ƙasa gabanta na faɗuwa.

“barrister lafiya?” momy ta faɗa tana ajiye spoon ɗin dake hannunta,maida kanshi yayi kan abincin da yake ci ba tare da ya tanka mata ba kamar ma ba dashi take magana ba.


sanin bazai tanka mata bane ya sata kallon laatifa,da ido tayi mata alama da lafiya, girgiza mata kai laatifa tayi alamar itama bata sani ba hawaye na taruwa a idonta.


“Allah ya kyauta” shine kawai abun da momy tace tana cigaba da cin abincinta,sun kai tsawan 20 mins kafin kamar daga sama su kaji ya kira suna balqis murya a kausashe.


da sauri balqis ɗin ta ajiye spoon ɗin dake hannunta

“na'am dady”
“last day mi ya kai ki court??” ya faɗa babu alamun wasa a fuskar shi,kamar saukar ardu haka laatifa taji tambayar duk da ba ita yayi mawa ba,tayi tunanin ya bar maganar tun lokacin ashe ba haka ba.

gabanta na faɗuwa ta kai dubanta ga balqis tana mata alama da ido data rufa mata asiri.



“naje saboda Aunty laatifa ne”
wani mugun kallo yayima laatifa
“saboda mi?”
“bata jin daɗi ne shine nace ta zauna gida ni na wakilceta” jinjina kai barrister yayi.


“mi na faɗa maki laatifa??” ya faɗa yana tsareta da idanu
“dady ba fa ita ta tura ni ba, da kaina nace zanje”
“tambayar ki nayi?” girgiza mashi kai balqis tayi


“dan Allah kayi haƙuri dady wallahi bani nace taje ba”laatifa ta faɗa a hankali

“laatifa kin raina maganata ko,bance maki idan za kiyi yawan iskancinki ki daina sa ƴata a ciki ba”
kamar zata fashe da kuka tace “kace dady”
“wato saboda ban isa ba shine ki ka turata cikin ƙattin da ki ka saba yawo da su ko?”



“kayi haƙuri dady bazan sake ba”

rai a ɓace momy tace“wai lafiyar ka kuwa barrister,itama ba ƴar ka bace ,mi yasa k..?” bata ƙarasa ba yayi saurin daka mata tsawa yana ɗaga mata hannu,hakan yasa tayi shiru tana kallon shi cike da mamaki.


“wannan ya zama rana ta ƙarshe da zan sake maki warning akan ƴata,duk yawan banzan da za kiyi kiyishi ke kaɗai amma banda ƴata kinji na faɗa maki”
“in sha Allah hakan bazata sake faruwa” laatifa ta faɗa hawayen da su ka taru a idonta na zubowa.


tashi yayi ya nufi bedroom ɗin shi,da wani kallo momy ta rakashi,tashi laatifa tayi ta nufi bedroom ɗinta yayin da take fashewa da wani matsanancin kuka, balqis ma kuka ta fashe da shi sun rasa yaushe dadyn su zai rage wannan ƙiyayyar da yake ma laatifa.


bayan laatifa momy tabi hakama balqis,a kwance su ka sameta ta kifa kanta saman matress tana fitar da wani kalar kuka mai ban tausayi,zama momy tayi kusa da ita hannunta ta ɗaura saman bayan laatifa,a hankali take shafa bayanta.



“momy wai mi yasa dady ya tsaneni,mi yasa baya sona kamar yanda yake son balqis, nima ba ƴarshi bace ko ina da wani uban wanda ni ban san shi,momy dan Allah idan ba shine mahaifina ba ki faɗa man???”

saurin toshe mata baki momy tayi da tafin hannunta “kul laatifa kar na sake jin bakin ki ya furta wannan kalaman,ki daina tunanin baya sonki ne, mahaifinki na sonki fiye ma da yanda yake son balqis,yana yi maki haka ne saboda ya kasa mantawa da abun da ya faru shekarun baya,ki dage da Adu'a wata rana sai labari”


“momy mi yasa dady har yanzu ya kasa gane cewa ba abun da yake zargi ba ne,momy har sau nawa zan faɗa mashi babu abunda ya faru dani kawai taimako na SAM yayi”

“saboda shi mahaifinki ne abun na damun shi shiyyasa ya kasa mantawa,kiyi haƙuri kinji in sha Allah wata rana gaskiya za tayi halin ta dadyn ki zai gane baki da laifi”

“momy amma ke mi yasa ki ka fahimce ni,dady baya sona ne kawai”
ta kai ƙarshen maganar tana sake fashewa da wani matsanancin kukan.



momy bata san lokacin da itama hawaye su ka wanke fuskarta ba, balqis ma ƙarfin kukan da take ne ya ƙaru,gaba ɗayan su rasa me lallashin wani a kayi,sai da su kayi mai isar su tukun momy ta shiga lallashin su,da ƙyar ta samu su kayi shiru,tashi laatifa tayi ta nufi toilet.



tashi momy tayi ta fice zuwa ɗakin barrister, a tsaye ta sameshi gaban wardrobe ɗin shi fitowarshi kenan daga wanka ƙugunshi ɗaure da towel.


“kaji tsoron Allah barrister,ka sani wannan aibatatan da kake ba shine mafita ba,itama ƴace a wurin ka kamar balqis,kuma ka sani ɗan Adam bai isa ya tsallake jarabawar da Allah yayi mashi ba,ko da ace abunda kake zargi gaskiya ne, kai ba mahaifinta bane dan mi bazaka ɗauki ƙaddararta hannu bibbiyu ba,amma ace tsawan shekaru ka kasa mantawa da abu,kullum cikin aibatata da nuna mata tsana kake, Allah ma munayi mashi laifi ya haƙura sai kai ne bazaka yafe ma ƴarka ba kan laifin da zargi kawai kake baka da tabbaci, haba barrister ka zama mahaifin ƙwarai mana”


“kin gama?” shine kawai abun da yace,wani ƙululun baƙi ciki ne ya tokare mata maƙoshi wato ma ta gama
“get out from my room” ya faɗa yana nuna mata hanyar fita,rai a ɓace ta juya ta nufi ƙofar fita har ta kama handle ɗin ƙofar sai kuma ta tsaya,rai a ɓace ta juyo tana kallonshi.



“ka sani balqis da laatifa Amana ce Allah ya baka,kuma zai tambayeka akan yanda ka tafiyar da rayuwar su,ka sani muddin baka gyara alaƙarka da ƴarka ba za kayi daka sani ne mara amfani” tana gama faɗa haka ta fice daga ɗakin baki ɗaya,tsaki yaja kawai yana cigaba da abunda ke gaban sa.


shaf shaf ya shirya cikin pajamas ɗin shi white color masu fatsi fatsin baƙi,feshe jikin shi yayi da perfume ɗin shi masu ƙamshi,bed ɗin shi ya haye yayi kwanciyar shi bayan ya kashe light ɗin ɗakin.


wayar dake kan nightstand ya ɗauka,dialing wata number yayi,bugu biyu a kayi picking call ɗin,kara wayar yayi a kunne,in low voice yake waya yanda ko kusa dashi ka tsaya bazaka iya jin abunda yake cewa ba,idan ka shigo ɗakin sai ka rantse da Allah bacci yake.

barrister kenan ko matashin saurayi bazai gwada mashi iya kashe murya idan yana waya ba.



*Big daddy's House*



“ko fa mi za kice sai dai kice amma yau sai kin fita dinning kinyin dinner tare da kowa na gidan nan,na gaji da wanna ƙunshi kan naki da ki ke”


“please Yumnah ki fahimta mana,bana jin yunwa ne ba wai ban son fita ba”
“to naji,muje ni ki raka ni koda ba kici komai ba ai za ki gaisa da mom da dady,kuma zaki rage wanann yawan tunane tunanen da kike”

duk yanda ta so zille ma Yumnah akan ta ƙyaleta Yumnah taƙi bata dama dan dole ta miƙe,hijab ɗinta dake saman bed ɗin ta ɗauka,zurawa tayi a jikinta

“muje to” ta faɗa tana kallon Yumnah
“ko ke fa,amma wannan hijab ɗin da ki ka sa saikace wacce zataje gaban sirikai, dinning fa zamu je ba wani waje ba”


“ni dai haka zanje”
“ai saiki ta tafiya haka”yumnah ta faɗa tana jan hannunta su ka fice.



Mom da dady ka ɗai su ka samu a dinning ɗin, Ishrat na daga tsaye tana serving ɗin su,bakin su ɗauke da sallama su ka ƙarasa cikin dinning room ɗin,zama su kayi saman chairs yayinda su ke gaishe da dady da mom.


murmushi dady yayi yana kai duban shi ga Nainarh,cikin kulawa su ka amsa masu gaisuwar da su kayi dady na faɗin


“ɗiyata kinyi wuyar gani,tun ranar da muka dawo daga wajen mahaifiyar ki ban sake saki a idona ba,ina fatan dai lafiya?”

“lafiya lau dady” Nainarh ta faɗa tana duƙar da kanta ƙasa
“yanzu ma fa da ƙyar na samu ta fito,kullum tana ɗaki daga kuka sai tunani” Yumnah ta faɗa tana kallon Nainarh data sadda kai ƙasa.


“wai haka ɗiyata?” shiru Nainarh tayi tana wasa da gefen hijab ɗinta

“ki dai na sa damuwa a ranki kinji, mahaifiyar ki zata dawo gareki,in sha Allah asirin wanda su ka kashe mahaifinki zai tonu”

“in sha Allah” Nainarh ta faɗa
“bana son kina sa damuwa a ranki kinji ko,ke da ma ki ke da wata mahaifiyar a kusa dake miye na sa damuwa a ranki” dady ya faɗa yana nuna mom da tunda su ka shigo dinning ɗin ta kafe Nainarh da ido ko ƙyaftawa ba tayi dan duk maganar da dady ke yi bata sani ba hankalin ta baya wajen.


“zulaihart!” dady ya kira sunanta,ɗan saurin kallon dadyn tayi
“lafiya ki ka kafe ƴar taki da kallo” murmushi mom ta saki
“wani lokaci sai nake ganin tana man kama da ƴar uwata,sai dai ita bata kai ta kazar kazar ba Nainarh ta cika sanyi” mom ta faɗa tana sake kai dubanta ga Nainarh data sadda kai ta sauraron su.


“nima na jima ina ganin kamaninta da Carol, da ace ban san mahaifiyar ta ba kuma a ce Carol ta taɓa Aure da babu abunda zai hana nace ƴarta ce”

murmushi mom ta saki “nima ina yawan faɗama mahaifiyar ta haka,wani lokacin idan nace haka sai tace dan kawai ina son Nainarh ne yasa nake ganin kamanin su”


“ta iya yiwuwa” dadyn ya faɗa, Yumnah da Nainarh dai na jin su,fa'iza ce ta shigo dinning room ɗin,tsaye tayi tana riƙe ƙugu fuskarta a turɓune
“shine yau aka rasa wanda zai kirani ko?” ta faɗa tana sake tsuke fuska.


“sorry Aunty Fa'iza nayi tunanin a part ɗin mamy za kiyi dinner shiyyasa ban kira ki ba” Yumnah ta faɗa tana ɗan kama kunnenta alamar sorry

“nima ayi man Afuwa na rashin faɗa maki da banyi ba” Ishrat ta faɗa wacce ke serving ɗin Yumnah da Nainarh,ɗaya daga cikin kujerun Fa'iza ta nufa ta zauna.


“ni dama na san ai kun rigada kun gama rainani gidan nan” murmushi kawai dady da mom su ka saki.


gaishe da su dady fa'iza tayi, murmushi dady yayi yana faɗin
“ai da nayi tunanin baki gannu ba”
ɗan murmushi tayi tana sosa ƙeyar ta.



serving ɗin ta itama Ishrat tayi kafin ta bar dinning ɗin,tsit wurin yayi ba wanda ya sake magana.


mom ta fara tashi kafin dady ya miƙe yana kallon Yumnah yace “Autar mom ina fatan baki manta gobe juma'a ba?”
“ban manta da gyaran part ɗin shalelen dady ba,gobe tunda safe zansa a gyara shi”
“good,haka ne son ji,sai da safe ku”

har haɗa baki suke wajen furta good night,jinjina masu kai dadyn yayi yana fice daga dinning room ɗin.


suma basu wani jimaba su ka tashi, Ishrat ta zo tare da su munirat su ka kwashe kayan da su kaci abinci su ka gyara wajen tsaf.


part ɗin mamy Fa'iza ta nufa sai da safe Yumnah da Nainarh su kayi mata suma suna nufar bedroom ɗin su.



Toilet Nainarh ta shiga tayi brush haɗe da alwala,kusan kullum za tayi bacci sai tayi Alwala abun ya zame mata jiki.


tana fitowa Yumnah na shiga,wanka tayi haɗe da Alwala kafin tayi brush,lokacin data fito har Nainarh ta kwanta, dressing room ɗin ta ta nufa, pajamas ta zura a jikinta kafin ta dawo bedroom ɗin.


kashe light ɗin ɗakin tayi,kwanciya tayi tana jan duvet ta rufe jikinta.

“yau ba wayar kenan?” Nainarh ta faɗa
“tun ɗazu mu kayi waya sai gobe kuma”
“Allah ya nuna mana goben lafiya” da Ameen Yumnah ta amsa.



ɗan shiru su kayi kafin Nainarh ta juyo tana fuskantar Yumnah
“wai wacece Carol da naji mom na faɗin muna kama?”
“ƙanwar mom ce” Yumnah ta bata amsa,gyaɗa kai kawai Nainarh tayi tana juya mata baya...
_*Ep 17_18*_


*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘

______________________________



*Washe Gari*



A zaune suke saman sallaya da alama basu jima da kammala sallah ba,tashi Nainarh tayi,hijab ɗin dake jikinta ta cire ta linke ta nufi bed,kwanciya tayi tana ɗan jan blanket ta rufe rabin jikinta.


yumnah na daga zaune har gari ya ɗan fara haske,tashi tayi itama ta cire hijab ɗin dake jikinta, toilet ta shiga,bata fi five minutes ba ta fito, dressing room ɗinta ta nufa,kayan jikinta ta canza zuwa gwon mai hannun armless,low bun tayi ma kanta da ƙaramin ribbon,mayafi ta ɗauka ta yafa saman kanta sannan ta fice daga ɗakin ta koma bedroom ɗin, Nainarh na nan kwance kamar yanda ta barta.


wayarta dake ajiye saman nightstand ta ɗauka ƙofar fita ta nufa,tashi Nainarh tayi zaune “sister Yumnah sai ina haka da safe?” juyowa Yumnah tayi

“wai da ba bacci ki ke ba?”
“kwance kawai nake,baccin ne yaƙi zuwa”
“ok part ɗin dady zanje na ɗauko key,za ayi gyaran part ɗin shalelen dady ne,tunda kin tashi sai ki zo muje”



“A'a sai kin dawo”
“wannan ne kuma baki isa ba,ki tashi kawai mu tafi abunda yasa ban tasheki ba nayi tunanin bacci kike,ta so mu tafi gari na waye wa bana son mu makara zuwa gidan Abbah”

saukowa Nainarh tayi daga saman bed ɗin,hijab ɗinta ta ɗauka,ficewa su kayi daga ɗakin.


direct sama su ka nufa zuwa part ɗin dady,a Parlor su ka same shi zaune saman sofa da Qur'an a hannunshi yana karatu,ciki suka ƙarasa suna mashi sallama ɗagowa kawai yayi ya kalle su ba tare da ya katse karatun da yake ba, bedroom ɗin shi Yumnah ta nufa Nainarh kuma ta zauna kan ɗaya daga cikin sofas ɗin,shiru tayi tana sauraran yanda dady ke furta ko wane harafi cikin ilimi,sai da ya kai aya tukun ya kai dubanshi gareta.


fuskar shi ɗauke da murmushi yace “ɗiyata yau kece a part ɗin na” murmushi Nainarh tayi tana ɗan rissinar da kai tace
“ina kwana dady,an tashi lafiya”
“lafiya lau Alhmdllh,fatan kema kina tashi lafiya”
“lafiya lau” ta bashi amsa
“masha Allah, Yumnah ta hanaki bacci ko?”



murmushi tayi tana faɗin “A'a dady da kaina na tashi”
“ai nayi tunanin ita ta taso ki”
girgiza kai Nainarh tayi fuskarta ɗauke da murmushi,fitowa Yumnah tayi hannunta riƙe da key's,wurin su ta ƙaraso.


“dady ka tashi lafiya?” ta faɗa yayinda take ƙarasowa inda yake side hug tayi mashi, kissing forehead ɗinta yayi fuskarshi ɗauke da murmushi
“lafiya lau,fatan kema kina tashi lafiya?”


“lafiya lau dady, key's ɗin part ɗin Autan ka na ɗauko za'aje a gyara” murmushi dady yayi yana dungure mata kai
“zaki sani idan yaji ki ne” murmushi Yumnah tayi
“taya zai sani,shida yana can”
“ai zai dawo kuma zan faɗa mashi ne”


“Allah ya Amince,nima nayi kewarsa na ƙosa naga ya zo”
“in sha Allah,yana nan zuwa”
“Allah ya kawo shi lafiya” da Ameen dadyn ya amsa,tashi Yumnah tayi tana kallon Nainarh

“muje,dady sai mungama”
“yawwa Nainarh harda sabon part ɗin yau ku shiga ku gyara shi”
“dama yau ko bakace a gyara ba sai na shiga naga abun da ka zubama shalelen naka bayan wanda kayi mashi”

“zaki kuwa gani,amma fa karki ta kallo dayawa bana son a cinye mashi kyau tun mai shi bai gani ba”

“karka damu dady,amma fa idan yafi nawa kyau tam” ta faɗa tana jinjina mashi kai
murmushi dadyn ya saki yana faɗin“dan Allah kisa su gyara da kyau kin ji”
“in sha Allah”ta faɗa suna ficewa daga part ɗin.




staircase ɗin dake can ɗan gefe da part ɗin dady su ka nufa,hawa su kayi zuwa can floor ɗin ƙarshe.

“ina so su kammala gyarannan da wuri dan mu samu zuwa part ɗin Abbah a kan lokaci” Yumnah ta faɗa dai dai time ɗin da su ke kawo bakin wata ƴar madaidaiciyar ƙofa ta glass.


wasu madannai Yumnah ta danna a jikin ƙofar
“ina tajin ana faɗin Abbah da part ɗin shi,yayan dady ne?”
“granfa ɗin mu ne, mahaifin su dady,duk ranar Friday gaba ɗaya family ɗin mu a can muke wuni,tundaga safe har dare a can muke lunch da dinner”

jinjina kai Nainarh tayi a lokacin da ƙofar ke buɗewa, wani irin katafaren parlorn ne su ka shigo,launikan dake cikin parlorn Royal blue, light brown and white color ne, an ƙawatashi da manya manyan sofas set biyu na gani na faɗa masu matuƙar taushi da daɗin zama,sai throw pillows dake kan ko wace sofa, daga tsakiyar parlorn round glass table ne an jera flower vase masu matuƙar kyau, daga saman ceiling ɗin wasu irin crystal chandeliers ne masu girman gaske , sai faskekiyar flat creen tv mai matuƙar girma sai kayan sauti dake gefe da gefen tv, sparkling floor lamps ne ajiye a ƙasa suna bada haske mai launika daban daban, ga dogayen curtains zagaye da parlorn an zuge su,daga can bakin glass wall wanda daga nan kana iya hangen main entrance ɗin shigowa part ɗin daga compound ɗin gidan,armchairs ne guda biyu ajiye daga tsakiyar su ɗan madaidaicin glass table ne,idan ka kalli ƙasan parlorn zaka ɗauka mirror ne yanda yake ɗaukar ido dan kana iya kallon kanka tsab.



Daga cikin parlorn kana iya hangen katafaren dinning room, wanda aka ƙawatashi da haɗaɗen dinning table,ƙyataccen glass table ne mai mazaunin mutum shidda,wasu haɗaɗun chairs ne kewaye da table ɗin,daga saman ceilling ɗin dinning room ɗin ƙaton bulb ne ya haskaka ko ina na dinning room ɗin,ga wata irin zungureriyar floor lamp.


cikin parlorn su ka ƙarasa Yumnah na gaba yayinda Nainarh ke biye da ita tana ƙarema parlorn kallo,tayi mamakin wannan part ɗin wanene dan yafi ko wane part dake gidan haɗuwa da tsaruwa duk da ba ko ina na gidan ta sani ba,wayar landline dake ajiye cikin parlorn Yumnah ta nufa, number kitchen ta kira,daga can ɗaya ɓangaren a kayi picking call ɗin.



“na buɗe part ɗin ku nake jira” Yumnah ta faɗa tana rejecting ba tare da ta tsaya jin amsar da za'a bata ba,wata ƙofa Yumnah ta nufa ganin haka ne yasa Nainarh binta a baya,nan ma wani parlorn ne su ka shigo wanda yafi na farkon haɗuwa,komai na cikin shi blue White and gold color ne,glass door ne guda biyu a jere sai wasu corridor guda biyu dake hannu dama da hagu can ɗan nesa da ƙofafin,wanda na hannun hagu ya kasance gym room ne ɗayan kuma wani part ne mai zaman kanshi.



ɗaya daga cikin ƙofofin dake jere Yumnah ta nufa tun kafin ta ƙarasa ƙofar ta shiga zugewa da kanta,cikin ɗakin ta kunna kai Nainarh na biye da ita a baya,wani irin haɗaɗen bedroom ne su ka shigo komai na cikin shi black,white and gold color ne, bedroom ɗin yana ɗauke da Royal bed mai matuƙar ɗaukar hankali,bed ɗin a shimfiɗe yake da tausassan bedsheet ga ƙaton blanket mai gashi gashi a jikin shi,gefe da gefen gadon nightstand ne mai ɗauke da bedside lamp,daga gaban gadon Ottoman table ne color ɗaya da bed ɗin,ƙasan ɗakin shimfiɗe yake da rug carpet mai taushi,wani irin ƙayataccen dressing mirror ne a cikin ɗakin daga gaban shi stool ne mai taushin gaske.


cikin ɗakin su ka ƙarasa,dogayen curtains ɗin dake a sake Yumnah ta shiga zugewa,kafin ta nufi wata ƙofa wacce nake kyautata zaton dressing

Please Login or Register in order to submit comment