You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
hug her and tell her all my problems” kusa da ita ya matsa, jawota yayi zuwa jikinshi “as long as that will make your mind calm,cry on my shoulder” zame hannunta tayi daga cikin nashi “mamana nake son gani, Please ka barni na tafi gobe”
“haba Zulaihart miyasa za ki man haka,at ur age kin wuce zuwa gida da sunan wai ranki ya ɓaci a gidan mijin ki,duk abubuwan da ki ka fuskanta a baya baisa kinje ba sai yanzu,kinfi kowa sanin momy bawai tana son Auren mu ba ne,miyasa zaki man haka,ko kin gaji da zama da ni ne??” ɗan dakatawa yayi kafin ya kwantar da murya yana sake kama hannunta
“Please kiyi haƙuri komai zai wuce,in dai son ganin momy ki ke nayi maki alƙawarin zamuje tare lokacin birthday ɗin SAM,sai kar muyi celebration a nan sai muje can, Please kiyi haƙuri kinji”lallashinta ya shiga yi dan ta bari sai lokacin birthday SAM su je,amma kamar ƙaramar yarinya taƙi saurarenshi ta kafe akan dole itafa sai taga momynta har cewa dady ta kirata video call amma fir tace itafa ganinta take son yi a zahiri,kallonta kawai yayi,shi kanshi yasanta tanada matuƙar haƙuri yanzunma kasa jurewa tayi ne,dan abunda ake mata a familyn shi da watace da tuni ta rabu dashi,amma tayi haƙuri tsawan shekaru,sosai ya sake kwantar da murya yana bata haƙuri
“please i want to see my mom” iska dady ya fesar,ganin dai ba daina maganar tafiyar za tayi ba ne yasa shi tashi ya fice ya barta,a parlorn ya samu su ya Naeem in da ya barsu zaune,kallo ɗaya yayi masu ya wuce sama, bedroom ɗin momy su ka nufa,suma kwantar mata da hankali su ka shiga yi,su ka yi mata alƙawarin tunda har bata son Auren dole shima Irfan ya haƙura,ta ɗanji sassauci da kalaman su amma bata fasa maganar tafiya gobe ba,suna nan dady ya shigo da waya kare a kunnenshi,miƙa mom yayi,amsa tayi takai wayar kunenta tana kallon shi, Muryar uncle Jonahs ce daki dodon kunnenta “katte mi yasa za kiyi haka da girma ki,ur not a kid fa,dan mi zaki tada hankali shi,idan kin zo taya zaiyi solving matsalar??”
“momy nake son gani Uncle”
“yace nan za kuyi celebration birthday SAM why baza kiyi haƙuri ba,kefa ba yarinya bace ko Carol da ace tana nan baza tayi abunda ki ke ba,yara nawa ne a tsakanin ku?” ɗan kallon dady tayi kafin tace “five”
“five kids amma ki ke wannan abu like Yumnah,you should be patient, everything will be fine”
“thank u uncle”
“bey take care of ur self” jinjina mashi kai tayi,miƙama dady wayar tayi bayan tayi rejecting amsa kawai yayi ya fice.
*UNITED STATE❤*
_*Las Vegas (Nevada)*_
A round 1:30Am ta shiga buɗe idanunta da su ka yi mata nauyi sosai,ta jima da farkawa ta kasa buɗe idanun ne saboda nauyin da su ka yi mata,a hankali ta sauke idanunta kan ceilling,kallon ɗakin ta shiga yi,biji biji take gani,buɗe idanunta ta ɗanyi sosai tana son tuna abunda ya faru da ita da kuma ina ne nan ,idanunta ne suka sauka akan mutum dake zaune saman sofa, scrub suit ne a jikinshi,ya ɗan jinginar da kanshi jikin head ɗin sofa, fuskarshi har time ɗin da facemask,idanunshi ne kaɗai a waje,ɗan lumshe idanunta tayi kafin ta sake buɗe su akanshi,wayace kare a kunnen shi yayinda hannunshi ke riƙe da wani littafi,zuba ma littafin dake hannunshi ido tayi kamar Bible sai dai kuma rubutun dake jikin littafin sun banbanta dana Bible,saurin kallon fuskarshi dake manne da facemask tayi,idanunshi a lumshe su ke kamar mai bacci,kauda kanta tayi zuwa Ventilator machine da drip ɗin dake hannunta,sai a time ɗin hankalinta ya kai ga oxgyen ɗin dake hancinta,fahimtar a hospital take ko medical room ɗin su ne yasa ta fara tuna abunda ya faru,a hankali ta lumshe idanunta zuciyarta na mata wani irin zafi
“she wakeup now I will call you later” ya faɗa yana rejecting call ɗin,bed ɗin da take ya nufa yana ajiye book ɗin hannunshi da waya saman Centre table dake gaban sofa,ventilator machine ɗin ya fara kashewa kafin
a hankali yasa hannunshi ya zame mata oxgyen ɗin dake hancinta,da sauri ta buɗe idanunta ta sauke su akan fuskarshi,tana iya hangen murmushin shi ta cikin mask,zuba mashi ido tayi tana kallo shima kallonta yake,dafa bed ɗin yayi yana duƙo da kanshi saitin fuskarta a hankali ya furta “wellcome back, how do u feel now?” raba idanu ta shiga yi a fuskarshi without saying anything to him,gabanta na wani irin faɗuwa,sake duƙo da fuskarshi yayi saitin tata breath ɗinta na sauka a face nashi “how do u feel now?” ya faɗa a hankali,faɗuwar gabanta ne ya tsananta dan mi muryar shi ke mata kama da wacce ta sani ko ta taɓa ji,a hankali ta motsa bakinta magana take amma baya iya jin mi take faɗa,kunnenshi ya kai saitin bakinta,a hankali yaji ta furta “who are u, where's my Mom??” ɗago da kanshi yayi yana kallon kyakkyawar fuskarta,tayi fayau har wata ƴar rama tayi,lips ɗinta sun ciza launinsu,she look so pretty a hakan, ɗan lumshe idanunshi yayi yana buɗewa a hankali ya furta “ur destiny” ya furta yana tsareta da idanu,wani kallon rainin wayau tayi mashi,ɗan murmushi ya saki yasan yau da lafiyarta lau daya sha masifa na wannan kalmar daya faɗa
“i said who are u” ta sake faɗa
ɗan lumshe ido yayi kafin a hankali yace
“I'm the doctor who's taking care of u”
kallonshi tayi,ɗaga mata gira ɗaya yayi yana faɗin “what?” lumshe idanunta tayi kafin hankali ta furta “I want to see Aunty Sophia and my mommy” a hankali shima ya furta “are u tired of seeing me?” lumshe ido tayi kawai without saying anything to him,wallahi dan tana jinta sai a hankali amma yau da ya shiga uku,ya taki sa'a da sai taji miye matsalar shi da ita da zai dameta haka,tashi yayi daga bakin bed ɗin ya nufi landline ɗin dake ward ɗin, dialing wasu numbers yayi,an picking ya bada umarnin akawo mata coffee,ajiye wayar yayi ya nufi ɗan ƙaramin table ɗin dake haɗe da bed ɗin,magungunanta dake wurin ya shiga dubawa,injection ya ɗauka yana dubawa,nocking ƙofar ward ɗin akayi,umarnin shigowa ya bada,turo ƙofar ward ɗin akayi da sauri Nailarh ta kai dubanta ga ƙofar shigowa,wata nurse ce ta shigo ɗauke da ɗan madaidaicin tray,mug ɗin coffee ne guda biyu sai gorar ruwa,ɗauke kai Nailarh tayi,cikin ɗakin ta nufo,har gaban bed ɗin ta ƙaraso,ajiye tray tayi saman table ɗin dake ɗakin,cike da girmamawa tace “good evening sir” jinjina mata kai yayi, dubanta ta kai ga Nailarh “how's u body?” lumshe ido Nailarh tayi without answering her
“wish u quick recovery” nurse ɗin ta faɗa,ficewa tayi,trayn ya nufa,mug ɗin coffee ɗin guda ɗaya ya ɗauka,bakin bed ɗin ya nufo,ajiye mug ɗin yayi kan table ɗin dake jikin bed ɗin,wani ɗan button ya danna a jikin bed ɗin,ɗan bending bed ɗin yayi yanda za taji daɗin shan coffeen,saurin buɗe idonta tayi tana kallonshi,mug ɗin coffeen ya miƙa mata,kallonshi kawai tayi ba tare da ta amshi mug ɗin “do u want me to gave u?”saurin kallonshi tayi,gira ɗaya ya ɗaga mata,sauke idanunta tayi daga kallonshi,zama yayi gefen bed ɗin,mug ɗin coffeen ya kai bakinta,bata yi musu ba ta amsa,bata coffeen ya shiga yi har sai da tasha kusan rabi tukun ta kauda kai,ajiye mug ɗin yayi,magungunanta ya shiga bata,da ƙyar ya samu tasha.
“whare's Aunty Sophia and my mom,I want to see them”
Allurar dake cikin magungunan ya shiga haɗawa kafin a hankali yace “not now,u need to have some rest”ɗan zame hannun rigar dake jikinta yayi,saurin kallonshi tayi,rintse ido tayi lokacin da ya tsira mata alurar,siraren hawaye ne su ka shiga zubowa daga idanunta,zame allurar yayi bayan ya kammala mata,maida mata hannun rigar yayi “i'm sorry” ya faɗa
“please I want to see them” ta faɗa kamar za tayi ku ka,lallai Nailarh ba kanta
“I'm sorry ,u need to have some rest now,u can see them later,okay” ya faɗa yayinda yake goge mata hawayen da su ka zubo daga idonta,sofa ya nufa,da kallo kawai ta bishi,wani iri take ji a ranta,ga zuciyarta dake mata zafi,gashi yaƙi bari ta gansu ko za taji sauƙin abunda take ji,mug ɗin coffeen taga ya ɗauka,zama yayi kan sofa yana ɗaukar wayar shi dake ajiye kan Centre table,unexpected taji bacci na neman ɗaukarta,lumshe ido tayi ko two minutes bata ƙaraba bacci yayi awan gaba da ita,bata sake farkawa ba sai a round 8:30Am,baccin awa bakwai tayi saboda magani da alluran da yayi mata,a hankali ta sauke idanunta akan jikinta ganinta lulluɓe da duvet ga drip ɗin da aka sa mata ancire,ɗan lumshe ido tayi ta buɗe,a hankali ta kai hannunta da nufin zame duvet ɗin dake jikinta,idanunta ne su ka sauka akan tafin hannunta,ganin kamar alamar note ne yasa tayi saurin buɗe tafin hannun tana,yes note ne da mamaki ta shiga karanta note ɗin
_I'm so proud of myself for taking care of u_
_do u know how pretty u are when u are sleeping?_
_like an innocent baby, that's how u look when u are sleep_
_Good morning baby_
ɗan zaro ido tayi kaɗan tana sake maimaita abunda aka rubuta,saurin kallon sofa dake ɗakin tayi amma wayam ta gani ba kowa,hatta book ɗin data gani hannunshi jiya da mug ɗin coffeen da yasa aka kawo mata babu, saurin kallon ɗayan side ɗin tayi,idanunta ne su sauka akan bunch of tulip flower mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali dake ajiye saman table,daga ƙasan bunch ɗin a ɗaureshi anyi mashi style kamar ribbon,ɗan card ta gani a jikin flower,lumshe idanunta tayi tana sake buɗe su akan flower,ba ƙaramin kyau flower tayi mata ba,tunani ta fara ko dai momynta sun zo ne,zame duvet ɗin jikinta tayi,hannu ta zura ta ciro card ɗin,note ne a jikin card ɗin anyi rubutu with style,karanta note ɗin ta shiga yi
_whether it's a royal blue satin gown or ordinary blue hospital pajamas u look pretty as always.
Nothing would make me happier an more relaxed than seeing u again in good health! Hope u feel better soon._
_get well soon cutie._
iska ta furzar daga bakinta, lallai mutumin nan bai san wace ita ba shiyyasa yake gigin shige mata,ko dan ya ganta a kwance a hospital yake tunanin bazata iya yi mashi komai ba ne,to yaushe ma duk yayi wannan abun,jin an turo ƙofar ɗakin ne yasa tayi saurin kai dubanta ga ƙofar.
Aunty Sophia ce ta shigo,da sauri ta rufe idonta tana tura hannunta cikin duvet,wani iri Aunty Sophia taji dan duk a kan idonta Nailarh tayi haka,ta san dama dole tayi fushi da ita,cikin ɗakin ta ƙara so,zama tayi gefen bed ɗin,a hankali ta kai hannunta saman fuskar Nailarh,saurin juya mata baya tayi tana ture hannunta dake kan fuskarta
“baby har yanzu fushi ki ke da Aunty Sophi ki?” Aunty Sophia ta faɗa a hankali,banza Nailarh tayi da ita without saying anything ta her
“I'm very sorry Nailarh,ki fahimce ni bana da sa hannu akan wannan abun daya faru, Please I'm very sorry” hannunta dake cikin duvet ta kama da sauri Nailarh ta fisge hannunta duk da ba wani ƙarfi ne da ita ba.
“baby dama zaki iya juya man baya saboda wani dalili?,kinfi kowa sanin a duniya bana da wani buri wanda ya wuce naganki cikin farin ciki,you know better than anyone that I can't do anything to hurt you, please be patient and understand me” still ba tace mata komai ba,tashi Aunty Sophia tayi ta koma ɗayan side ɗin
“please Nailarh kiyi haƙuri,baki san halin dana shiga saboda wannan rashin lafiyar taki ba, Please kar ki sa zuciyata ta buga dan bazan juri ganin kina fushi da Ni ba,kiyi haƙuri ki yafe ma Aunty Sophin ki” magiya Aunty Sophia ta shiga yi mata tana bata haƙuri amma ko kallon inda take Nailarh ba tayi ba,saukar ruwan hawayen Aunty Sophia taji saman hannunta,ɗan rintse ido tayi,duk yanda ta ɓata mata rai baza ta so ganinta cikin damuwa ba,kawai tayi mata hakan ne dan ta fahimce irin yanda taji saboda kalamanta,dan tayi imani Aunty Sophia baza ta taɓa yin abunda zai cutar da ita ba,a hankali ta buɗe idon,juyowa tayi tana fuskantar Aunty Sophia data kifa kanta saman mattress,kuka take amma ba mai sauti ba,wani irin tausayinta ne ya rufe Nailarh ita kanta sheda ne akan halin da Aunty Sophia ke shiga idan wani abu ya sameta,to taya ma za tayi tunanin zata iya cutar da ita,kawai dai kalamanta ne idan ta tuna su ranta yake ɓaci,a hankali ta ɗaura hannunta on his head
“Aunty Sophi!” ta kira sunanta ,da saurin Aunty Sophia ta ɗago,fuskarta duk tayi sharkaf da hawaye,hannunta dake saman kanta ta riƙe “Nailarh” ta kira sunanta yayinda wasu hawaye ke zuba daga idanunta, girgiza mata kai tayi tana sa ɗayan hannunta ta shiga goge mata hawayen
“stop crying, you know that I can never be angry with you,kawai banji daɗin kalaman ki ba”
“I promised you that you will not hear another unpleasant word from my mouth again,I'm sorry dear.
“please to ki bar kukan haka” da sauri Aunty Sophia ta kai hannunta saman fuskar Nailarh,shafa fuskarta ta tayi
“shikenan bazan sake ba,ya jikin naki?”da sauri Nailarh ta kamo hannunta ganin kanula
“what's happening with u?”
“saboda ke ne,amma ba wani abu mai mahimmanci bane na samu sauƙi”
“lafiyarki ce ba abu mai mahimmanci ba?” girgiza mata Aunty Sophia tayi “karki wani damu,ya jikin naki,fatan da sauƙi?”
“na samu sauƙi sosai Aunty Sophi”
“thank God,haka nake son ji,fata samun lafiya maiɗorewa” jin jina mata kai Nailarh tayi
turo ƙofar ɗakin a kayi,da sauri su ka kalli ƙofar,miss malika ce ta shigo,tana sanye da Suit white color,hannunta riƙe da bunch ɗin rose flower mai matuƙar kyau,daga bayanta su luna ne ɗauke da basket,da sauri ta ƙarasa bakin bed ɗin Nailarh,a saman table ta ajiye flower tashi Aunty Sophia tayi ta bata wuri,da sauri ta zauna in da Aunty Sophia ta tashi,kamo hannun Nailarh tayi cike da tsantsar kulawa
“baby!” ta kira sunanta,hannu Nailarh ta kai a fuskarta,shafa fuskarta tayi
“sweetheart!”ta kira sunanta a hankali,da sauri miss Malika ta goge hawayen dake idonta
“Baby, how is your body?”
“I felt relieved”Nailarh ta faɗa
“I miss you so much baby”
“me too sweetheart” murmushi Malika ta sakar mata,da sauri su luna su ka shiga gaishe da Nailarh da yi mata ya jiki,ɗan murmushi kawai ta sakar masu, flower data shigo da ita ta ɗauko, fuskarta da murmushi ta ɗaura mata ita saman jikinta “this for u my baby”murmushi ta sakar mata tana kai flower hancinta,daddaɗin ƙamashin da flower ke fitarwa ta shaƙa,zuba mata ido su ka yi suna kallon yanda ta lumshe ido tana shaƙar ƙamshi flower,wani irin daɗi ne ya rufe Mrs Malika,janye flower tayi tana kallon Momyn ta ta, murmushi ta sakar mata “thank U” ta faɗa, murmushi Mrs Malika ta sakar mata tana kashe mata ido ɗaya,card ɗin dake jikin flower ta ciro tana karanta rubutun dake ciki
_u always told me my hugs are always warm and comfy. I really want to hug u all day to keep warm. I know your fever will go away!_
_get well soon my baby_
da sauri Nailarh ta kai dubanta ga Mrs Malika, murmushi ta sakar mata tana kashe mata ido ɗaya,buɗe mata hannayenta tayi alamar tazo gareta,ba musu kuwa ta ajiye flower gefenta,hugging ɗin juna su ka yi,Sofa dake ɗakin Aunty Sophia ta nufa ta zauna,sun kusan five minutes a haka,idanunsu a lumshe,Mrs Malika ta fara bude ido,a kan wannan tulip flower idanunta su ka sauka,saurin raba jikinta tayi daga na Nailarh,kallon fuskarta tayi
“baby wacen flower fa,ko dai Sophia ce ta kawo maki?” mrs Malika ta faɗa tana kallon Aunty Sophia,girgiza mata kai aunty sophia tayi alamar ba ita bace, kallon Nailarh tayi
“I think doctor brought it to me” Nailarh ta faɗa
“dr! Which doctor?, Dr Daniel?” Mrs Malika ta faɗa
“I don't even know it it's dr daniel,but wanan dai dr dake kula dani”
“dr dake kula dake?” Mrs Malika ta faɗa yanayin fuskarta na canzawa zuwa tsantsar ɓacin rai
“yes” Nailarh ta bata amsa, iska ta fesar mai huci
“baby dole yau mu bar hospital ɗin nan ko da ba suyi discharge ɗin mu ba, ni dama kwata kwata ban yarda da wannan hospital ɗin nan ba da dokokin wannan CEO ɗin na su na banza,kawai mu tafi gida sai sophia ta cigaba da kula dake ko dr Mark”
“yes, sweetheart, I'm tired too, let's just go home”
“ma'am bai kamata mu tafi ba ba tare da anyi discharge nata ba, please mu bari suyi discharge namu, zata fi samun kulawar data dace a hospital, bata jima da farfaɗowa ba fa” Aunty sophia ta faɗa
“gaskiya sai mun tafi, in ya so sai mu koma orphanage can ma akwai professional drs to take care of her”
“please ma'am kiyi haƙuri,tunda har nan muka fara zuwa muyi haƙuri ta ƙarasa samun sauƙi su sallame mu”
“to dan mi za su wani kafa mana doka, ya hana mu shigo inda take, sannan yanzu miye alƙarshi da ita da zai wani kawo mata flower sai kace ce mashi akai bata da wanda za su kawo mata”
“na fahimci damuwarki, amma duk da haka kiyi haƙuri suyi discharge ɗinta, kuma dan ya yi wish ɗinta dan ta samu lafiya ai ba laifi bane, drs da dama suna haka ga patient ɗin su, kiyi haƙuri”
shiru kawai miss malika tayi ba tare da tace mata komai ba amma har cikin ranta bata san zaman hospital dan gani take kamar akwai wani abu da yasa dr nan yake shige ma Nailarh, amma dai ko miye za ta zuba ido sosai akanshi kafin su bar hospital ɗin.
“baby mi za kice na zuba maki?” Aunty sophia ta faɗa
“I'm not hungry” Nailarh ta faɗa
“please,na haɗa maki koda tea ne mana” turo baki kawai Nailarh tayi, basket ɗin da su luna su ka shigo da shi Aunty sophia ta nufa, tea and fried ege ta haɗan mata,tashi miss Malika tayi ta koma kan sofa,inda miss malika ta tashi ta zo ta zauna, cup ɗin tea ta kai bakin Nailarh,kurɓa daya tayi mashi ta kauda kai
“please baby ki sha mana” ta faɗa tana marairaice mata fuska
“coffee nake so” Nailarh ta faɗa,ok kawai Aunty sophia ta ce tana tashi ta nufi basket ɗin, turo ƙofar ward ɗin aka yi,Nurse ce ta shigo tana turo food trolley,da mugun sauri su ka kai duban su gareta har ta ƙaraso gaban bed ɗin Nailarh
“hi Miss Nailarh,how was ur body,hope u feel better now” ta faɗa cike da kulawa tana sakar ma Nailarh murmushi,jin jina mata kai Nailarh kawai tayi,kallon Mrs Malika da Aunty Sophia tayi “good morning” da ƴar fara'a Aunty Sophia ta amsa mata,Mrs Malika kuwa ko kallon inda take ba ta yi ba,dan yanzu gaba ɗaya haushin su take ji, warmers ɗin dake kan trolley ta shiga buɗewa,Wheat Bread,Greek Yogurt,cup of milk,fresh fruit,Chicken and etc.
wani kallo Mrs Malika ta watsama nurse ɗin ganin tana shirin sarving Nailarh tace “hi! wait,We also brought food for her,so take yours and go out”ɗan murmushi Nurse ɗin tayi
“sorry ma'am na sani,amma wannan shi ne ya dace ta ce saboda lafiyarta”
“mu ma wanda mu ka zo dashi zai taimaka ma lafiyar ta,kawai ki kwashe kayan ki”
“I'm sorry ma'am hakan bazai yiwuba”
“saboda mi”
“umarnin CEO ne wannan shine abincin da za taci”
“u and your CEO idiot” murmushi kawai nurse ɗin tayi tana maida hankalinta kan abunda take
“She won't eat this food” Mrs Malika ta faɗa tana nufo bakin bed ɗin,da sauri Aunty Sophia tace “please ma'am kiyi haƙuri,sun fi mu sanin mi ya dace da Nailarh Please”
“baza taci wannan abincin ba Sophia” tsayawa Nurse tayi tana kallon Mrs Malika cike da mamaki tunani ma ta fara anya lafiya take,dan duk wanda ke zuwa hospital ɗin nan ya san cewa su ke ba patient abinci to miye matsalar wannan matar
“sophia haɗa mata coffee ki Bata,ke fita da kayan ki”
“mom please enough” Nailarh ta faɗa da ɗan tsawa duk da rashin ƙarfin jikinta,da sauri ta nufi Nailarh“am very sorry,kawai bana son abunda zai cut...” Bata ƙarasa ba Nailarh ta ɗaga mata hannu
“bana son jin wata hayaniya,be quite” saurin kama bakin Mrs Malika tayi tana faɗin “okay ok ” kallon Nurse ɗin Nailarh tayi a hankali ta furta “sarv me” murmushi Nurse ɗin ta sakar mata, sarving ɗinta ta shiga, milk ta fara haɗa mata kafin ta ɗaura mata two sliced of Wheat Bread a saman plate sai Greek Yogurt with berries sai boiled chicken drumsticks,bayan data kammala haɗa mata,tai maka mata tayi zuwa toilet dan ta wanke bakinta,a hankali take taka ƙafarta har zuwa toilet ɗin,sai da tayi brush ɗin tukun su ka dawo ɗakin,kan bed ɗin Nailarh ta koma yayinda Nurse ɗin ke nufar food trolley ɗin,cup of milk ta fara miƙa mata
“thank u” ta faɗa tana amsa,wani banzan kallo Mrs Malika ta watsama nurse ɗin tana kauda kai gefe,sai data sha ɗan rabin cup tukun ta janye baki
“I'm sorry duka zaki shanye” Nurse ɗin ta faɗa kallonta Nailarh tayi “it's CEO'S odar” murmushi Aunty Sophia ta saki ganin yanda Nailarh ta wani juya ido alamar an dameta fa,tsaki kawai Mrs Malika ta saki tana kallon gefe itafa ba komai ke damunta ba sai kishin Nailarh,ta tsani taga wani na raɓarta,tas ta shanye milk ɗin kamar yanda Nurse ɗin ta faɗa mata, Wheat bread ta nuna mata,sliced ɗin ta ɗauka ta ci,bowl ɗin farfesun kaza ta miƙa mata,Aunty Sophia ta miƙama bowl ɗin,amsa Aunty Sophia tayi,a hankali ta shiga bata,tas ta shanye shi dama dai dai wanda zata iya shanyewa ne,robar greek Yogurt ɗin ta miƙa mata,Aunty Sophia ta buɗe roɓar haɗe yake da fresh barriers,Aunty Sophia ta shiga bata sai ɓata fuska take saboda ba zaƙi unsweetend ne,murmushi kawai Aunty Sophia ke saki,wayar Miss Malika ce ta fara ringing, da sauri marry ta miƙo mata wayar data ciro daga cikin jakan Mrs Malika,amsar wayar tayi tana duba sunan mai kiran nata,ɗan murmushi ta saki tana picking call ɗin,can cikin ɗakin ta nufa dan amsa wayar,sosai ta sha Yogurt ɗin duk da bawai yayi mata daɗi bane sai takura matan da Aunty Sophia tayi,sai da tasha da yawa tukun Nurse ɗin ta shiga bata magungunan ta, injection ɗin dake ciki kuma sai anjima idan Dr ya zo,wurin Mrs Malika ta nufo da waya a hannunta,miƙama Nailarh wayan tayi “baby dady na magan” saurin kallonta Nailarh tayi,hakama Aunty Sophia “amsa mana, yana so ya ji ya jikin ki” kauda Nailarh tayi yanayin fuskarta na canzawa zuwa tsantsar ɓacin rai “please baby ki amsa mana” Mrs Malika ta sake faɗa, ko kallon in da take Nailarh ba tayi ba,wayar tasa a speaker daga cikin wayar Muryar mutumin ta bayyana
“hello Nailarh” wani ɗan iskan kallo Nailarh ta watsama wayar without answering him
“baby are you hear me” ya sake faɗa,banza Nailarh tayi da shi,ajiyar zuciya ya sauke, a hankali yace “ya jikin naki,fatan da sauƙi,ina nan shigowa next week na dubaki” wani ɗan iskan tsaki taja tana ƙoƙarin sauka daga saman bed ɗin,saurin riƙeta Aunty Sophia tayi tana girgiza mata kai,ran Mrs Malika ba ƙaramin ɓaci yayi ba ta tsani wannan wulaƙancin da Nailarh ke mashi “baby are u Angry with your dady?” ya faɗa cikin kwantar da murya,hararar wayar tayi “who are you to said that,you will never be my father forever”
saurin cire wayar Mrs Malika tayi a speaker tana kara ta a kunenta “I'm sorry I will call u later” Bata jira jin mi zaice ba tayi rejecting call ɗin,rai a ɓaci ta kalli Nailarh
“baby mi yasa ki ke haka,ya damu da ya san halin da ki ke ciki shine zaki mashi haka??” ko kallonta Nailarh ba ta yi ba “mi yasa ko wane lokaci ki ke son wulaƙantashi,shifa Kamar mahifinki ne” sai a sannan Nailarh ta kalleta “he's not my father,I hate him”rai a ɓace Mrs Malika ta buɗe baki da nufin magana Nurse ɗin tayi saurin cewa “Be patient Ma'am, this may affect her health, I'm sorry” sai da nurse ɗin tayi magana tukun ta tuna da condition ɗin Nailarh,iska mai zafi ta furzar daga bakinta,har ta nufi sofa sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin rai a ɓace,ko kallonta Nailarh ba tayi ba,kwantar da kanta tayi jikin pillow haɗi da lumshe idanunta,Aunty Sophia just looked at her without saying anything,hannunta ta kama,note ɗin dake jikin hannunta Aunty Sophia ta zubama ido,buɗe ido Nailarh tayi tana kallonta,rufe mata hannun kawai Aunty tayi
Book Chapters
Chapter 22
Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36