Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zunguran luxury dinner tables ne guda biyu masu ɗauke da chairs guda ashirin akan kowane table,daga saman floor ɗin wasu irin manyan crystal chandelier ne masu shegen kyau dogayen da su kamar za su sauko ƙasa,gaba ɗaya hall ɗin a zagaye yake da manyan curtains masu matuƙar kyau an zuge su.



hall ɗin an ƙawatashi da wasu tukwanan ƙasa dake ɗauke da furanni masu matuƙar jan hankali,chefs ne maza da mata da a ƙalla zasu kai su goma sai aikin jera warmers suke a saman tables ɗin,cikin hall ɗin dady su ka shigo bakin su ɗauke da sallama.


da sauri chefs ɗin su ka dakata da abunda su ke,cikin girmamawa su ka shiga gaishe su,da kulawa suke amsa masu,tunda su ka shigo suka sauke idon su a kan uncle Mustafa dake can zaune saman ɗaya daga cikin kujerun dinner table ɗin,ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai aikin jijjigata yake,bini bini yake kallon wayar shi haɗi da jan tsaki.



dinner table ɗin su ka nufa kwanansu kujera yaja ya zauna dady ne kawai bai zauna ba ya nufi uncle Mustafa,kujerar dake kusa da wacce ya zauna yaja ya zauna,dafa kafaɗarshi yayi,saurin kallonshi uncle Mustafa da baisan da zuwanshi wajen yayi ba.


“yanzu Mustafa duk dan saboda ƴarka ka shiga wannan yanayin?,
rashin lafiya ne ba wani abu ba amma duk kabi ka tada hankalin ka?”
“bazaka gane bane ya Tahir,ni ka ɗai na san yanda nake ji”
“taya zan gane tunda ni ban haifa ba, Al'mustafa ka rage wannan mugun son ƴaƴan da kake,duk kabi ka ɗaurawa kanka damuwa saboda ƴaƴa sai kace kai kaɗai Allah yaba ƴaƴa,akan ƴaƴanka ba kaji baka gani,haba!?” ɗan dakatawa dady yayi yana kallonshi kafin ya ɗaura da cewa


“yanzu abunda kayi ma matar Ahmad kana ganin ka kyauta kenan,karka manta yanzu kainart ta tashi daga ƙarƙashin kulawarka ta koma hannunsu,sun fika iko da ita,sannan ina so ka sani ko babu Aure a tsakanin su Ahmad mai iya riƙe kainart ne haka Zaabith,ka zamo mai kawaici a kan ƴaƴanka”



tunda dady ya fara magana ƙala Uncle Mustafa bai ce ba sai yanzu
“kayi haƙuri ya Tahir in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba,hankalina ne ya tashi ban san wane irin ciwo take na”
“koma wane irin ciwo take Adu'a ya kamata kayi mata ba abunda kayi ba”
“in sha Allah zan kiyaye,kayi haƙuri”
“shi zaka ba haƙuri ba ni ba” Dady ya faɗa,waige waige uncle Mustafa ya shiga yi ko zaiga Uncle Ahmad


“yana waje tare da Abbah,kaje ka bashi haƙuri”
“to” uncle Mustafa ya faɗa yana miƙewa ya fice daga hall ɗin.

tun suna ƙananansu suna matuƙar girmama umarnin dady har kawo yau da su ka mallaki hankalin su kuwa.


tashi dady yayi ya nufi in da su uncle Ubaid su ke ya zauna,matan ne su ka fara shigowa hall ɗin,Mama Ameenah ce a gaba yayinda su mamy ke biye da ita a baya,sai da su ka gama shigowa mom da mom maryam da mom Maimunatu su ka shigo bayan sun shigo ne yaran su ka fara shigowa.


Su Yumnah ne su ka shigo hannunta riƙe da hannun Ammar da Aman yayinda da Jamal ya maƙalƙale hannun Nainarh sai turo baki yake shi adole fushi yake yumnah bata riƙe hannunshi ba.

ɗaya bayan ɗaya su ka shiga shigowa, kowannan su ya shigo wajen zama yake nema ya zauna, table ɗin da su dady ke zaune su mom su ka zauna, kowaccen su na fuskantar mijinta yayinda mamy da su hajiya fatilah su ka cure waje ɗaya su da Mama Ameenah bako ta mazajen na su suke ba, sai hura hanci su ke sunama mutane kallon tara saura kwata.

ɗayan Table ɗin su Yumnah su ka zauna da sauran jikokin Abbah, a tare Abbah da Uncle Ahmad da Uncle Mustafa su ka shigo, suma wajen zama su ka nema su ka zauna,saida kowa ya gama samun wurin zama ya zauna tukun chefs su ka shiga serving ɗin su, cika masu gaban su su kayi da Abinci kala kala na Alfarma.


tunda su ka shigo Aunty Safeenah ta kafe mom Maryam da kallo,wani irin kallon mamaki take binta dashi,tsaki taja tana kallon mama Ameenah


“dan Allah mama dubeta,sai wani hura hanci take kamar wani ta fi,mai Abun duniyar ma ba tayi ƙafafa ba sai ita”

“ai ni wallahi lamarin Maryam mamaki yake bani,wai ni baku lura da ita ba yanzu tafi ƙarfin zuwa ta gaishe da mama bare mu data gama rainawa mu samu arziƙin da za tayi mana magana” A cewar hajiya halima


“rabu da ita kawai zanyi maganinta ne”acewar mama Ameenah



firarsu su ka shigayi wacce banda zagin su mom ba abunda su ke, Hajiya Salima na cikin su amma kwata kwata bata saka masu baki ba haka mamy ma tunda ta zauna hankalinta na can wani waje daban,bamata san akan mi su ke magana ba,ta ƙurama waje ɗaya ido,suma da su ka gaji shiru su kayi hall ɗin yayi tsit banda ƙarar spoon da plate baka jin komai.



Noor tunda ta zauna dinning ɗin Banda juya spoon babu abunda take gaba ɗaya ta kasa cin abincin saboda rashin shi a kusa da ita duk tabi ta damu,kallonta laatifa dake kusa da ita tayi.


“lafiya dai ko Noor?” murmushin yaƙe ta sakar mata tana faɗin lafiya.
“mi yasa baki cin abincin,ko dai wannan baiyi maki ba chefs su canza maki wani??”


girgiza mata kai Noor ɗin tayi
“A'a, bana jin daɗi ne ”
“Ayyah!,sannu mike damunki?”
“jikina nake ji babu daɗi” ta bata amsa, murmushi Kairiyyah ta saki dan ta san ba komai yasa noor faɗin haka ba sai dan saboda Irfan.



Ringing ɗin wayar laatifa ne yaja hankalin mutane da dama dake hall ɗin har da dadyn ta,wani kallo ya shiga watsa mata,kwata kwata bata lura da irin kallon da yake mata ba, ganin sunan mai kiranta nata ne ya sata saurin miƙewa daga saman chair ɗin da take zaune,ƙofar fita daga hall ɗin ta nufa yayinda take picking call ɗin.


a bakin ƙofar shiga hall ta tsaya tana amsa wayar
“hello sister,kamar kin san duk ina nan na damu da rashin zuwanki” laatifa ta faɗa,on the other hand ta cikin wayar tace

“bana jin daɗi ne ƴar uwa shiyyasa ban zo ba”
“subhanallah! mike damunki naji ma muryarki wani iri, fatan dai ba wani abun ba ne ya sake faruwa ba dan naga ya Zaabith na gari”
“please sister ki zo idan babu abun da ki ke”


“wai mike faruwa ne,duk kin sa hankalina ya tashi”
“babu komai ki zo dai Please”
“ok gani nan zuwa”
“sai kinzo” rejecting call ɗin tayi,hanyar fita daga garden ɗin ta nufa ba tare da ta koma cikin hall ɗin ba,daga inda dadynta yake cikin hall ɗin yana hangen ficewar ta.



miƙewa yayi ya fito daga hall ɗin,bayanta yabi, parking space ɗin gidan ya nufa,yana isa motar ta na ficewa daga parking space ɗin,wayar shi ya zaro daga cikin Aljihu yayi dialing wata number, bugu biyu a kayi picking.


“gata nan ta fito ina son kutabbatar da in da taje” on the other hand wata irin kakkausar Muryar ce mara daɗin jin ta daki dodon kunnenshi
“angama ranka ya daɗe” rejecting call ɗin yayi ba tare da yace komai ba.



yana a nan tsaye kamar daga sama yaji anyi hugging ɗin shi ta baya tightly, murmushi gefen fuska ya saki ba tare da ya juya ba dan ya san bazai wuce ita ba ce dan babu mai mashi irin wannan rungumar idan ba ita ba.


“ai nayi tunanin sai na kira ki zaki fito?” ya faɗa cikin wani irin yanayi kamar ba barisster ba
“ni na isa, kawai jiran damar da zan fice nake ba tare da wani ya lura da ni ba”


taɓe baki yayi yana faɗin “fushi nake dake,yau wajen kwana nawa da alƙawarina amma baki ciki ba”

“kafi kowa sanin halin yayanka kwata kwata baya bani damar da zan matsa daga gidan,yanzu ina sa ƙafa na fita zaisa abi masa diddiƙin in da na tafi,kuma nasha faɗa maka ka riƙa zuwa gidan babu mahaluƙi da ya isa ya zargeka akan zuwa gidan yayanka,kuma har ka gama abun da ya kawoka ka fice ba tare da ya san ka zo ba.



hannunshi yasa ya jawo hannunta ta dawo gaban shi, ƙare mata kallo ya shiga yi tun daga sama har ƙasa kafin ya tsaida lumsassun idanunshi a kanta, wani irin shaiɗanin kallo ya shiga binta da shi,ba ita da yakema kallon ba hatta ni dake laɓe sai da naji kunyar irin kallon da yake mata.



kasa jure kallon da yake mata tayi,tafin hannunta tasa ta rufe idanuwan shi
“barisster irin wannan kallo haka, sai ka sa gaban ya faɗi” murmushi ya saki yana janye hannunta daga idanunshi,baki ta buɗe da nufin yin magana amma yayi saurin manne bakinshi da nata.


*Tashin sense Barisster Hashim,mamy 😳😳😳😳*


Zagayo da hannayenshi yayi ya riƙe ƙigunta,itama ƙanƙameshi tayi kamar za su koma abu guda,a ƙalla sun shafe tsawan five minutes a haka kafin ya raba jikin su,jan hannunta yayi su ka nufi ɗaya daga cikin motocin dake parking space ɗin,front seat ya buɗe mata ta shiga,zagayawa yayi ya shiga driver seate,Key yayi ma motar su ka nufi cikin estate ɗin.



*ASO VILLA*



Bata sha wata wahala ba wajen shiga, saboda ita ɗin sannance a idanun securitys ɗin kuma bayan haka sun san alaƙarta da mazauna gidan.



A katafaren parking space ɗin Villa ɗin tayi parking, kusan a tare su ka fito da wani matashin ba indiye dake zaune a cikin motar shi,bai jima da parking ba tayi parking.



in da take ya nufo hannunshi ɗauke da briefcase, fuskarshi ɗauke da fara'a ya ƙaraso,murmushi itama ta sakar mashi.

“Dr fawar dama kana ƙasar?” ta faɗa da almun mamakin ganinshi, murmushi ya sakar mata cikin hausar shi da bata gama daidaita ba yace
“ina za ni, Ina nan hajiya laatifa, dama yaran irin mu na ganin ku?”


dariya ta fashe da ita wacce ta ƙara fito da ainihin kyawun fuskarta “daɗina da kai zolaya fawar, in da ka so gani na ai ka san in da zaka same ni”
“kina son dadyn ki yayi ƙarata kenan?” ya faɗa,dariya kawai laatifa tayi ba tare da tace komai ba.


juyawa su kayi da nufin barin wajen zuwa ciki, horn ɗin da a kayi a bayan su ne ya dakatar da su,parking space ɗin matuƙin motar ya nufo, parking yayi, zuba ma motar ido su kayi dan ganin wanda zai fito.



Irfan ya fito,da sauri ya nufo su yana faɗin “sorry Dr, na san na ɓata maka lokaci” ɗan hararar shi dr fawar ɗin yayi
“haba Irfan ka san yanda tsarin gidan nan naku yake amma ka barni a tsaye a bakin gate da ba dan nayi hausar kiran Zaabith ba da tuni ina can rana na duka na”



“sorry na tsaya amsar wani saƙo ne, muje ko, Aunty Laatifa ina wuni”

“lafiya lau Irfan, kwana biyu” da Alhmdllh ya amsa mata yayinda su ke shiga cikin gidan,babu kowa sai masu aiki dake kai komo, direct part ɗin Zaabith su ka nufa, parlorn su tsit yake babu kowa sai masu aiki dake ƴan hidindimun su, gaishe da su masu aikin su kayi, a saman sofa fawar da Irfan su ka zauna yayinda laatifa ta nufi bedroom ɗin Kainart.



bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ta shiga tana ambaton “my own sis gani na ƙa...”
dakatawa tayi da maganar ganinta a kwance saman bed harda su rufa,ƙarasawa tayi bakin bed ɗin.


“Kainart lafiya?” ta faɗa tana ɗan yaye blanket ɗin data rufa,tashi tayi zaune ta jingina da head board ɗin gadon.


wani irin mummunan faɗuwa gaban laatifa yayi ganin sawun duka a saman neck ɗinta gana mari da har yayi baƙi saboda hasken fatar ta.


“kainart mi ya same ki haka, kardai kice har yanzu ya Zaabith bai daina dukanki ba??” Laatifa ta faɗa da tsantsar damuwa
“har yau Laatifa ya Zaabith yaƙi ya canza halinshi”
“kainart idan har da laifin ya Zaabith naki yafi yawa, ni banga amfanin zaman nan da kike da shi ba, mutuminnan baya sonki amma ke har yau kin kasa ganewa, so ki ke ki salwantar da rayuwarki a banza?” Laatifa ta faɗa ranta a ɓace.



“bazaki gane bane Laatifa”
“dama taya zan gane tunda soyayya ta rufe maki ido har kina shirin salwantar da rayuwarki a banza, wallahi Kainart ko ni da nake fuskantar tsangwama daga dady gara ni dake, duk ranar da Allah ya bani miji mai sona nayi Aure shikenan, amma ke fa?, karki manta zaman Aure ba zama ne na ɗan lokaci ba zama ne na har abada, kuma tuda har ya Zaabith bai sonki ko kun ɗau tsawan shekaru tare ba ganin mutuncinki zaiyi ba, gara tun wuri kisan Abun da ya dace??”



“ina sonshi ne Laatifa shima yana sona bazaki gane ba, kuma idan na barshi ya ki ke so nayi da su Ammar?”

“matsalar ki kenan soyayya,wlh ya Zaabith baya sonki da yana sonki bazai riƙa wulaƙantaki ba, sannan su Ammar da ki ke magana, karki manta ko babu Aure tsakaninki da ya Zaabith zai iya riƙe abun da ki ka haife barema ƴaƴan sa ne, kuma kin san cewa duk tashin hankalin da za'ayi dady bazai taɓa bari a rabaki da su ba hakama Abbah, ki nemama kanki mafita Kainart,ba kiga yanda ki ka koma ba kamar ba ke ba duk kinbi kin lalace”


“wace mafita zan nema Laatifa?” ta faɗa da alamun son ƙarin bayani daga Laatifa
“na san zaki ce bazaki iya rabuwa da shi ba, amma ya zama dole dady ya san irin zaman da kike a gidanan”
girgiza mata kai tayi “gaskiya Laatifa bazan iya sanar da dady ba kin san halinshi, muddin ya sani ya Zaabith ya shiga uku”



“to ya shiga ukun mana ina ruwan wani, ke sau nawa yana saki a ukun” Laatifa ta faɗa a hassale da alama dai ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba
“bazan iya ba, ina tausayin hukuncin da dady zai yanke mashi,zanta kai kukana wajen ubangiji, in sha Allah wata rana zai daina”


“ai shikenan sai ki tashi dr fawar na nan dady ya turoshi ya dubaki” wani irin faɗuwa gabanta yayi, saurin dafe saitin zuciyarta tayi

“na shiga uku! waya faɗa mashi bana da lafiya?”

“kema kin san dole yaji ba'asin abunda ya hanaki zuwa gidan Abbah,may be mom salima ce ta faɗa mashi baki da lafiya, kin san kuma komi a kayi maku idan ba shi yayi ba baya ganin daidain shi, ki tashi kawai kije”


“amma bata faɗa mashi dr James ya dubani ba?”
“kinfi kowa sanin waye dady, kawai ki wuce kije” hijab ta ɗauka ta zura a jikinta, ficewa tayi zuwa parlorn, gefen bed ɗin Laatifa ta zauna.


A zaune ta same su saman sofa kamar yanda laatifa ta barsu masu aikin sun kawo ma Dr fawar abun motsa baki.


cikin girmamawa su ka gaishe da juna ita da Dr fawar,bayan da su ka gaisa ne ya shiga yi mata ƴan tambayoyi tana bashi amsa.


duk wani abun da ya kamata yayi mata yayi mata,baisha wahala ba saboda duk wani da zai buƙata wajen duba patient ya zo da shi,sallama yayi mata akan idan ya kammala binciken zai ba Irfan sakamakon ya kawo mata,godiya tayi mashi sosai.



sallama yayi mata su ka fice shida Irfan,a parking space yana shirin shiga motar shi uncle Mustafa ya kira dan yaji mike damunta,sanar da shi yayi zazzaɓi ne dai yanzu sai sakamakon test ɗin da yayi mata ya fito sannan ya san taƙamaimai abunda ke damunta.


godiya sosai uncle Mustafa yayi mashi kafin su kayi sallama,ficewa su kayi daga Villa ɗin motar Irfan na gaba yayinda ta Dr fawar ke bayan shi.


Estate Irfan ya koma lokacin har sun kammala lunch suna part ɗin Abbah,Noor tayi fushin tayi fushin har ta gaji,sai da ƙyar ya samu ya shawo kanta.


Barisster Hashim da mamy da su ka fita ba sune su ka dawo ba sai da yamma liƙis ana gab da kiran magrib,sai ma da suka dawo sannan wasu su ka fahimci ba sa nan.


Bayan sallar isha su kayi dinner kowa ya kama shirin tafiya gida,Ammar tunda lokacin tafiya suka fara murnar yau a gidan big daddy za su kwana Jamal ma rigima yasa shima dole ya bisu,wayau Aunty Nafisat ta so yi mashi kan ya bari idan sun koma gida dadyn shi zai kawo shi amma fir ya tubure shi dole yanzu yake son bin su duk yanda ta so ya bari sai wani week ƙin amincewa yayi dole tasa su ka haƙura.


motar su na bayan ta Irfan daya ɗauko mom,Yumnah na back seat tare da yaran yayin da Nainarh ke front seat kusa da Fa'iza dake driving.


Yumnah tun kafin su ƙarasa ta kira Ishrat ta sanar da ita zuwan su Ammar saboda su gyara masu bedroom ɗin dake kusa da na Yumnah,sosai Ishrat tayi murna da zuwan su Ammar yaran na matuƙar burgeta.


A tare motocinsu su kayi parking,a tare su ka shiga fitowa daga motocin,cikin gidan su ka nufa su Ammar na riƙe da hannun Yumnah, Jamal ma Nainarh ya maƙalemawa tunda Aunty Yumnah ta yadashi,ɗaya daga cikin security ɗin gidan ne ya shigo da kayan su Ammar.


Irfan har bedroom ya raka mom da jakatar a hannunshi mom har mamaki take miye alaƙar Irfan da son riƙe jaka,duk za su fita tare baya barinta riƙe jaka ko kau ina za su je haka zai riƙe jakarta,Fa'iza har iya shage take mashi saboda riƙe jakar mom.


Basu wani jima su ka fice shida Waseef da alama sauri suke zuwa wani waje, bedroom da Yumnah tasa aka gyara masu ta nufa da su Ammar, bedroom ɗin yana da girma sosai dan yafi na Yumnah girma ƙaton king size bed ne a cikin shi.


ruwa Yumnah tasa su ka watsa su ka shirya cikin pajamas ɗin su,a nan ɗakin su kwana harda Nainarh dan rigima su ka masu akan sai sun kwana tare da su...


_*HEART OF VEGAS CLUB AND CASINO*_

*12:00 AM*


_*HEART OF VEGAS CLUB AND CASINO*_


Ƙarfe shabiyu na dare daidai motar su tayi parking a ƙaton parking space ɗin dake club ɗin, maƙil yake da motoci kasancewar yau Friday duk wani mashahurin da yake ganin ya shahara ayawan club zaka same shi a nan.


Kamar yanda sunan ya kasance iri ɗaya haka tsarin ginin ma iri ɗaya ne,banbanci kawai wacan yafi girma sai dai ba wani sosai ba,gaba ɗaya photocopy wacan ne.


Kusan a tare su ka fito,jeans da T_shirt ne a jikin Waseef yayinda Irfan ke sanye da shirt haɗe da short iya gwiwarshi,kanshi a sanye yake da Ivy Cap idanunshi a manne su ke da baƙin shade mai shegen kyau.


Entrance ɗin shiga club ɗin su ka nufa,wasu irin jibga jibgan security guard a gaban katafariyar ƙofar shiga club,tun kafin su ka ƙaraso securitys ɗin su ka rissinar da kai alamar girmamawa a gare su,kallon in da su ke babu wanda yayi tsakanin Irfan da Waseef,bakin ƙofar su ka ƙarasa, Waseef ne ya ciro card ɗin shi daga cikin aljihu,a jikin na'urar dake jikin ƙofar ya zura card ɗin,zugewa ƙofar ta shiga yi bayan na'urar ta kammala acknowledging card ɗin.



ciki su ka kunna kai Irfan na baya yayin da Waseef ke bayan shi,tsarin club ɗin ɗaya ne dana US duk abunda ke a wancan a kwaishi a wannan banbanci abubuwa kaɗan ne, mata da maza ne ta ko ina kowa na harkar gaban shi, wasu na rawa wasu na shaye shaye,babu wanda ya lura da shigowar su har su ka isa bakin galss elevator dake club,maddanan dake jiki Waseef ya danna nan take ƙofar ta buɗe,ciki su ka shiga,sama elevator tayi da su zuwa floor ɗin ƙarshe.


fitowa su kayi bayan ƙofar ta zuge,a bakin wani office su ka tsaya,wasu nombobi dake a jikin na'urar dake jikin ƙofar ya danna,nan take ƙofar ta buɗe,ciki su ka shiga, katafaren office ne kamar ba'a niger ba komai na cikin shi extraordinary ne, Executive chair ɗin dake gaban haɗaɗɗen glass desk Irfan ya nufa,zama yayi yayin da Waseef ke jan ɗaya daga cikin chair ɗin dake gaban desk ya zauna.



mac book ɗin dake ajiye saman desk ɗin ya buɗe,babu ɓata lokaci ya shiga operating ɗin ta.


“wai yaushe Muhsin yace maka Boss zai dawo ne,akwai kayan da babu ga tarin customers da muke da su?”Irfan ya faɗa ba tare da ya ɗago daga abunda yake ba

“kasan ba kowa ke sanin lokacin tafiyar shi ba haka lokacin dawowarsa” jinjina kai Irfan ɗin yayi
“gashi Muhsin ɗin bai shigo ba,amma bari na kira wayar shi naji” ya faɗa yana zaro wayarshi daga aljihu,number Muhsin ya shiga dialing, ringing wayar ta shiga yi har kiran ya katse ba'ayi picking ba, Yana ƙoƙarin sake kira aka turo ƙofar office ɗin.


“ina jin gashi nan” Waseef ya faɗa yana kai dubanshi ga ƙofar dan ya san idan ba Muhsin ɗin ba to Boss ne su kaɗai keda lasisin shigowa ba tare da na'ura ta dakatar da su ba.

Wani matashin saurayi ne ya shigo cikin shigar ƙananan kaya,ƙaƙƙarfa ne na gaske,cikin office ɗin ya nufa, kujerar dake kusa da wacce Waseef ke zaune yaja ya zauna,hannu ya miƙa masu su kayi musabaha


“kamar kuwa kasan nemanka nake”irfan ya faɗa
“shigowata kenan naga kiranka,neman mi kake man fatan dai lafiya?”
“dama tambayarka zanyi yaushe boss zai dawo, akwai tarin customers a gaban mu”

“ka san halin yaya idan zai tafiya baya faɗa, nama yi tunanin ko kai ya faɗa maka”
“ya dai faɗa man zaiyi tafiya amma bai sanar dani time ɗin da zai dawo ba”
“ok abunda ya kamata kawai ka kirashi kaji yaushe zai dawo dan akwai tarin schedules na meeting wanda dole ya halarce su”



“ok bari na kira naji” Irfan ya faɗa yana ɗaukar wayar shi yayi dialing number boss, ringing wayar tashiga yi har sun fitar da ran za'a ɗauka akayi picking,wata irin buɗaɗiyar murya ce ta daki dodon kunnenshi.


“hello Irfan,fatan lafiya ka kira ni?” na cikin wayar ya faɗa
“lafiya lau,dama cewa nayi yaushe ne zaka dawo,kaya da yawa fa sun ƙare gashi yau muna da guest da yawa?”
“ sai next week nake sa ran dawowa ina las Vegas ne,akwai key a hannun Muhsin ku duba store na san baza'a rasa wa su a ciki ba”


“amma meeting ɗin ka fa,kasan fa dis week kayi masu alƙawari”
“haka ne,ina sane,kai nake so kayi Attending ɗin su”
“nikuma boss?” Irfan ya faɗa da alamar ruɗu
“eh,na san ai zaka iya dan ya kamata ka fara wasu abubuwan da kanka ba dole sai da ni ba”
“amma Boss kasan bana da gogewa a abun, infact ma ban taɓa Attending meeting irin wannan ba”


“karka damu idan zaka je za muyi amfani da communicative devices,zan dunga sanar da kai abunda ya kamata ka faɗa”
“ok Boss,sai ka dawo”
“thanks” Boss ɗin ya faɗa yana rejecting call ɗin.


saurin tambayar shi su kayi dan jin yaushe yace zai dawo
“sai next week” ya basu amsa
“kayan fa?” Muhsin ya faɗa
“yace akwai key a hannunka mu duba store baza'a rasa ba”
“ok,bari muje tare da Waseef,amma meeting ɗin fa?”
“ni yace nayi Attending ɗin su”


Ok kawai Muhsin ɗin yace,tashi su kayi su ka fice daga office ɗin zuwa store,maida kanshi yayi a kan mac book ɗin dake gaban shi.



*ASO VILLA*


A kwance take saman makeken gadonta ta rufe jikinta da duvet,tunda laatifa ta tafi take a kwance sallah kawai ke tashin ta.


Turo ƙofar ɗakin yayi ya shigo,Black suit ne a jikinshi looking smart,cikin ɗakin ya ƙaraso,a bakin bed ɗin ya zauna,hannu yasa ya yaye duvet ɗin da tayi rufa

in a low voice ya kira sunanta “kainart!” tsit tayi kamar batajishi ba,sake kiran sunanta yayi still bata amsa mashi ba
fuskarta ya leƙa dan yaga bacci take ko kuwa,motsi ya ga tana yi da idanunta alamar idonta biyu.


shafa fuskarta yayi da tafin hannunshi “ya jikin naki?” ya faɗa cike da kulawa,banza tayi da shi kamar bata san da ita yake ba
“kainart na san kina jina,fushi kike dani ne?” nan ma ƙin tanka mashi tayi a ranta tana faɗin “watau ma bai damu da abunda yayi mata ba har yake tambayar fushi take.

tashi yayi ganin da gaske ba kulashi za tayi ba,ƙofar fita ya nufa ɗan buɗe idonta tayi a hankali ta saci kallonshi,har ya kama handle ƙofa zai fice sai kuma ya dakata yana juyowa ya fuskance ta,saurin rufe idonta tayi.

“zan fita akwai yiwuwar sai gobe zan dawo ki kulaman da kanki” yana gama faɗa ya fice haɗi da jan ƙofar ya rufe.


a hankali ta buɗe idonta tana bin ƙofar da kallo,gaba ɗaya takaice ne ya cikata ko ina zaije da wannan tsohon daren kuma har yake faɗa mata wai sai gobe ma zai dawo,baƙin cikinta da takaicinta idan ya tashi dawowa abuge zai dawo mata ya shuka mata rashin mutunci, shikenan ita

Please Login or Register in order to submit comment