Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an sauke man wani ƙaton dutse daga saman kaina,ina fatan kema kina jin abun da nake ji” zame hannuwanta dake cikin nashi,motsi ta shiga yi da bakinta tana mashi alama da ya zo gareta,a hankali ya matsa sosai kusa da ita,jawota yayi zuwa jikinshi,tightly yayi hugging ɗinta,saukar hawayenta yaji saman shoulder ɗin shi.
hitting bayanta ya shiga yi a hankali yana faɗin “please ki daina kukan nan it's paining me” shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya,sun ɗan jima a haka kafin a hankali ta kai bakinta saitin kunnen shi,magana ta shiga yi mashi,da ƙyar take furta kalmomi,baza ka iya jin mi take faɗa mashi ba saboda muryarta da tayi ƙasa sosai,shi kanshi sai yayi da gaske yake gane abunda take furtawa,saurin ɗago da kanta yayi daga jikinshi jin furucin da tayi.
Cike da tashin hankalin furucin da tayi ya shiga bin fuskarta da ido,kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar damuwar da yake ciki
“mi yasa zaki faɗi haka Noor, ciwo ba mutuwa bane, Adu'a ya kamata kiyi kinji” girgiza mashi kai tayi hawaye na bin fuskarta,ƙarfin hali tayi wurin furta “ka yafe man ya Irfan,ni kaɗai na san halin da nake ciki” girgiza mata kai ya shiga yi
“tunda har baki mutu lokacin da ki ka sha guba ba yanzu ma ba zaki mutu ba,babu abunda zai sameki Noor,in sha Allah zaki samu sauƙi,think about me mana, idan ki ka tafi ya ki ke so nayi da rayuwata,baki tunanin halin da zan shiga?” ya faɗa yana share mata hawayen dake zarya daga fuskarta
“Noor we are husband and wife now,think about our unborn babies kin ji,ki daina faɗan mutuwa in sha Allah we will fulfill all our dreams soon,Allah zai baki lafiya,ko kin manta irin rayuwar da muke fatan muyi bayan Auren mu?” hawayen dake zuba daga idanunta ne su ka ƙarfin gudu,girgiza mashi kai ta shiga yi,ita kaɗai ta san halin da take ciki,duk bayanin da zata ma Irfan ba wai zai fahimceta bane.
lallashinta ya shiga yi “ki daina kukan nan dan Allah kina karyaman zuciya,ko nima kina son ganin nawa hawayen ne?” girgiza mashi kai tayi “to dan Allah ki dai na kinji,in sha Allah zaki samu sauƙi” hannunshi dake saman fuskarta ta kama ta kai kan surgical cap ɗin dake kanta,cike da kulawa yace “ya aka yi,ciwo kan yake maki ne??” girgiza mashi kai tayi a hankali ta furta “ka cire man”
“hulan?” ya faɗa da sigar tambaya,ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ohk ya faɗa yana zame mata hular,kitson zane ne guda huɗu akan ta ɗan tufke ƙarshen kitson,ba laifin Noor akwai yalwar suma Masha Allah,kitson ya ɗan zamo saboda santsin da kanta yake da shi,kallon kitson yake da mamaki dan ya kasa fahimtar abunda take nufi da hakan
“me kitson yayi,yana maki ƙaiƙayine?” ya faɗa cike da kulawa, girgiza mashi kai tayi tana kai hannunta saman kitson,a hankali ta shiga cusa fingers ɗinta cikin kitson kamar mai shirin zaro wani abu,saurin riƙe hannunta yayi
“mi yasa ki ke son warware kitson,yana damunki ne?” a hankali ta furta “wani abu nake so na baka” da mamaki ya furta
“wani abu,a cikin kitson??”
“eh” ta bashi amsa
“ohk bari na ciro da kaina” ya faɗa yana kai hannunshi saman kitson,lumshe ido tayi tana ɗan kwantar da kan saman chest ɗin shi yanda zaiji daɗin ciro abunda take son bashin.
a hankali ya shiga ɗaga tsoran kitson yana mai mamakin miye ta ɓoye a cikin kitson,mamaki ne ya kamashi lokacin da ya ciro ɗan madaidaicin flash daga tsakiyar kitson dake kanta
“Noor ma ye wannan ɗin?” ya faɗa yayinda yake ɗago da kanta daga saman chest ɗin shi
“flash ne yaya” ta bashi amsa
“na san Flash ne,amma na minene?” ya faɗa cike da son jin ƙarin bayani daga gareta
“zai taimaka maka a duk lokacin da kaji kewata”
“ban gane mi ki ke nufi ba,wai Noor mi yasa ki ke faɗan haka,baki son yin rayuwa da ni ne yanzu?”
“ba haka bane ya Irfan,a duniyan nan bana jin akwai wata ƴa mace da zata so yin rayuwa da kai kamar yanda na so,kayi haƙuri ba a san raina nake faɗa maka haka ba amma ya zama dole ne,rayuwata ba mai tsayi bace,Allah bai ƙaddara za mu rayu da juna a matsayin ma'aurata ba,kayi haƙuri da rashina a rayuwarka” tunda ta fara magana ya zuba mata ido yana kallo,ya rasa mai zai faɗa mata ta fahimci ƙunar da kalamanta ke ma zuciyarshi,kamo hannunshi da ya riƙe Flash ɗin tayi tana cigaba da faɗin
“nasan ba lallai ka iya jurewa ba,amma karka damu wannan Flash ɗin a cike yake da abunda zai baka ƙwarin gwiwa da juriyar rashina,
ka man alƙawari bayan ba raina zaka cika man burina,duk wata alfarma dana nema a gareka zaka yi man ita,na maka zaɓi wanda nake ganin Alkairi a rayuwar ka,kayi haƙuri in sha Allah ina da tabbacin zaka so zaɓina”
zuba mata ido kawai yayi
“ka yafe man duk wani laifi da na maka,sannan ina neman Alfarma no matter what a rayuwar da za kayi ba tare da ni ba karka manta da ni ya Irfan dan Allah” ta faɗa yayinda wa su zafafan hawaye ke yar tseren fitowa daga idanunta,saurin manneta yayi da jikinshi yana jin wani iri a zuciyarshi,he can't imagine life without her,mi yasa sai da burin su ya cika Noor zata kasa jurewa,wace irin ƙaddarace wannan ke yawo da rayuwar su,mi yasa Noor ba tayi tunanin halin da zata jefa rayuwarshi lokacin da zata sha poison ɗin ba.
“please Noor ki daina faɗan haka,kina ƙona man zuciya da kalamanki,in sha Allah baza ki mutu ba,za mu rayu da juna kamar yanda mu ka yi fata,zanyi magana da dady na fitar dake outside of the country,in sha Allah zaki samu lafiya kinji” kwantar mata hankali ya shiga yi duk da shima yana buƙatar mai kwantar mashi da hankalin,dan gaba ɗaya ta gama jefashi a cikin wani hali da kalamanta.
Uncle mutallab sai around 6 na yamma ya dawo tare da mom fatilah,ba komai ya sa su ka zo tare ba sai kukan data tasashi gaba tana mashi kan ƙin barinta da yayi taga Noor ɗin,kamar yanda uncle mutallab ɗin ya bar Irfan haka ya same shi Noor ɗin har ta koma bacci,tunda ya samu lallasheta ta daina ku ka yake faɗa mata kalamai masu daɗi da sake kwantar mata da hankali,ya kuma yi mata alƙawarin in sha Allah gobe ko zuwa jibi zai fita da ita waje danta sake samu kulawa daga wasu likitocin duk da nan ma ba wai basa da kayan aiki mai inganci ba ne,kawai yana ganin kamar zata fi samu kulawa dai dai da yanda yake so duk da nan ɗin ma suna iya bakin ƙoƙarin su a kanta.
ko da ya sanar da uncle mutallab hukuncin da ya yanke na son fita da ita,sosai uncle mutallab yayi farin ciki da jin hukuncin da Irfan ɗin ya yanke,hakan ya sake tabbatar mashi da Noor zata samu kyakkyawar kulawa daga gare shi,ya kuma sake alfahari da kasancewar shi miji ga Noor ɗin
“nima nayi wannan tunanin Irfan,Amma ganin nan ɗinma akwai kayan aiki ma su inganci kuma likitocin mu na da ƙwarewa sosai akan aikin su”
“haka ne uncle,Amma halin da take ciki za'a duba,kamar canjin zai taimaka mata,amma duk yanda kace ba bu damuwa uncle” ya kai ƙarshen maganar a hankali alamar dai hankalin shi sai yafi kwanciya idan aka fitar da ita ɗin.
“bana da ta cewa Irfan,matarka ce kanada ikon fitar da ita ba tare da ma kayi shawara da kowa a cikin mu ba dama shawarace kawai na bada,amma naga kamar kafi son ka fitar da ita ɗin?”
ɗan sadda kai ƙasa Irfan ɗin yayi yana sakin murmushi
“ba haka bane uncle” murmushi shima uncle ɗin yayi,mom fatilah dai na jin su ƙala ba tace ba.
“karka damu,nayi matuƙar farin ciki da ganin irin kulawar da ka ke bata,na sake tabbatar da cewa zaka kula man da Noor yanda ya kamata,shikenan amma kafin komai ka fara sanar da ya Tahir da barrister tukun”
“eh uncle zan sanar da su,amma passport ɗin Noor ɗin?”
“karka damu,ka bar komai a hannuna yanzu dai ka fara sanar da su kawai”
“to shikenan uncle,muna godiya” murmushi kawai uncle mutallab ɗin ya sakar mashi.
Bayan sallar magrib Irfan ɗin yayi ma uncle mutallab sallama ya tafi gidan dan ya sanar da dady hukuncin da ya yanke,mom kuma tunda tana nan sai ya dawo dan yana da tabbacin baza tace komai ba haka ma dady,sallama yayi ma uncle ɗin akan zai sake dawowa zuwa anjima dan anan yake so ya kwana.
sai da ya tsaya a masallacin Estate ɗin yayi sallar isha tukun ya ƙarasa gidan,ko da yaje bai samu dady ba yana gidan Abbah,direct part ɗin shi dake gidan ya nufa dan yana buƙatar ya watsa ruwa ya canza kayan jikinshi,bayan nan yana buƙatar abun da zai sakama cikin shi, rabonshi da abinci mai ɗan nauyi tun jiya.
yana fitowa wanka ko bathrobe ɗin dake jikinshi bai cire ba ya fice daga part ɗin ya nufi part ɗin mom,tsit gidan yake kamar babu kowa a cikin shi,dining room ɗin part ɗin ya nufa riƙe da wayar shi yana kiran layin Waseef rabonshi da shi tunda ya bar hospital,har kiran ya katse Waseef ɗin baiyi picking ba.
fasa nufar dining room ɗin yayi,zama yayi saman sofa yana jawo landline da nufin kiran masu aikin gidan,idanunshi ne su ka sauka akan mutum cikin dining room ɗin, mamaki ya fara waye dan ya san su yumnah na hospital wurin Kainart, tashi yayi daga saman sofa ya nufi dining room ɗin,tun kafin ya ƙarasa ya fara jin shashshekar kuka,a hankali ya ƙarasa ciki,da mamaki yake kallonta ta kwantar da kanta saman dining table,ƙasa ƙasa take fitar da sautin kukan,ya kai tsawan 2 minutes a tsaye yana kallonta ba tare da ya ƙarasa gareta ba,mamakin wacece yake da kuma mi akai mata take wannan kukan.
A hankali ya kai hannunshi saman kanta da nufin ɗago da ita,a firgice ta ɗago tana haɗiye kukan da take,zazzare ido ta shiga yi saman fuskar shi,shima kallon fuskarta data ɓaci da ruwan hawaye yake yana mai mamakin ganinta a wurin da abunda ya sata kuka,dama bata bi su yumnah hospital ba?
sun ɗauki tsawan 40 seconds a haka kafin a hankali ta janye idanunta daga kallon shi,samun kanshi yayi da faɗin “me aka maki ki ke kuka?” ɗan kallonshi tayi kafin ta kauda fuskarta tana ƙoƙarin tashi ta bar wurin
saurin kamo hannunta yayi yana faɗin “ba ki ji ina magana, me aka maki ki ke kuka, wani yayi maki wani abu ne??” da kulawa ya jera mata tambayoyin, a hankalin tasa ɗayan hannunta ta zame hannunshi dake riƙe da na ta,barin wurin tayi ba tare da ta bashi amsar tambayoyin da yayi mata ba, da kallon mamaki ya bita har ta shige corridor da ɗakin su yake, dubanshi yake kan wayarta dake haske na alamar kira, yaji haushi wannan share shin da tayi,ko dan taga ya nuna kulawarshi a gareta yasa zata mashi haka,bata san cewa ba wai matsayinta ne yakai har ya nuna kulawarshi a gareta ba kawai yana da wani abu a rayuwarshi, baya son ganin mutum cikin damuwa saboda sanin halin da zuciyar mutum ke shiga a lokacin da mutum ke cikin ƙunci,duk sai ya ji ba daɗi.
kallon wayarta da har lokacin mai kiran nata bai daina ba yayi,hannunshi  ya kai ya ɗauki wayar privet Number ya gani alamar mai kiran nata baya da buƙatar a san kowaye shi.
ficewa yayi daga dining room ɗin da nufin zuwa ɗakin su dan ya sake tambayarta abunda ke damunta.
yana isa parlorn sallamar su yumnah ta daki dodon kunnenshi, da katawa yayi yana amsa masu sallamar,ɗan zaro ido yumnah tayi tana kallonshi fa'iza kuwa murmushi ta saki tana faɗin “angon patient, kai ne a gidan?” murmushi ya saki yana faɗin “fa'iza ni ki ke ma wannan cin mutuncin ko?” ƴar dariya tayi tana faɗin “miye abun cin mutunci angon hospital” dariya kawai irfan ɗin yayi yan girgiza kai,dariya yumnah tayi haɗi da matsowa ta mashi side hug tana faɗin “congratulations ya Irfan, Allah ya baku zaman lafiya” murmushi ya saki yana jan hancinta “thanks you so much Auta” murmushi itama ta saki tana raba jikinsu,miƙa mashi hannu fa'iza tayi suka yi handshake tana faɗin “congratulations bro,Allah ya kawo zuri'a ɗayyiba” murmushi yayi yana shaking hand ɗinta dake cikin nashi “Ameen ya Rabb sistor,kema Allah ya kawo miji na gari”
“Ameen,ya mai jikin?” ta faɗa tana zame hannunta daga nashi
“taji sauƙi”
“Allah ya ƙara afuwa” da Ameen ya amsa,gaba ɗayan su suka juya jin sallamar dady,cikin parlorn ya ƙara so yana faɗin “Irfan yaushe ka shigo gidan?”
“ban jima ba,ina wuni”
“lafiya lau,ya jikin Noor ɗin”
“taji sauƙi dady”
“Allah ya ƙara sauƙi” da Ameen su ka amsa su fa'iza na gaishe da shi,amsa masu yayi yana nufar sama,Irfan wayar nainarh dake hannunshi ya miƙa ma yumnah yana faɗin “wayar waye wannan aka bari a parlor?” hannu yumnah tasa ta amshi wayar,ɗan jujjuya wayar tayi tana faɗin “wayan nainarh ce,amma me yasa ta barta a parlor?” ok kawai Irfan ɗin yace yana faɗin “Auta yunwa nake ji,kima Ishrat magana ta kawo man lunch a part ɗin dady” da to yumnah ta amsa,sama ya nufa zuwa part ɗin dady.
da landline ɗin dake parlor yumnah ta kira Ishrat ɗin,bayan ta sanar mata da saƙwan Irfan ɗin ne su ka nufi bedroom ɗin su,a zaune su ka samu nainarh saman bed ta zabga uban tagumi,damuwace kwance ƙarara a fuskarta,ga wata irin rama da tayi,abubuwan ne sun haɗe mata da yawa
an kashe mahaifinta ga mahaifiyarta a prison ta sa mu yayanta da ya dawo amma babu halin ta faɗa mashi halin da take ciki ko zata samu sassauci abunda ke damunta,dan har yanzu cikin tsoro da firgicin abunda ya faru da ita take,yumnah ce da man mai lallashinta ta faɗa mata kalaman da za su kwantar mata da hankali  yanzu itama ta sauya tashiga sahun masu tara mata damuwa.
har idan take su ka ƙaraso dafa kafaɗarta yumnah tayi tana faɗin “wai ni kam nainarh me ke damunki ne kwana biyu,duk kin bi kin ɗauki damuwa kin sa a ranki,nayi tambayar duniyar nan amma kinƙi faɗa man sai fushi da ki ke da ni wanda na rasa dalili” tunda ta dafata ta ɗago tana kallonta,lamarin yumnah mamaki yake bata sai ta dinga yi kamar bata san abunda tayi mata ba
“dan Allah nainarh koma me ke damunki  kiyi haƙuri ki daina sa ma ranki damuwa Allah yana tare da ke” wani kallo ta watsama yumnah tana kaɓar da hannunta dake saman kafaɗarta, girgiza kai kawai yumnah tayi kwana biyun nan kullum a haka su ke,ko magana nainarh bata yi mata,kusan zata iya cewa gaba nainarh ke yi da ita,ɗan ajiyar zuciya yumnah ta sauke “Allah ne shaidata nainarh ban san me na maki ki ke wannan fushin dani ba,amma kiyi haƙuri a bisa laifin da na aikata maki ba tare da na sani ba” kauda kai Nainarh tayi tana ɗan jan tsaki,fa'iza tunda ta shigo tana tsaye tana kallonsu ƙala ba tace ma su ba amma ba taji daɗin halin da su ke ciki ba musamman Nainarh
“ga wayarki nan a parlor ki ka barta” yumnah ta faɗan tana ajiye mata wayar haɗi da ficewa daga ɗakin dan zata iya fashewa da kuka a gaban su,ba ƙaramin kunnata Nainarh take da wannan halin da take mata ba.
ƙarasawa fa'iza tayi gaban gadon,zama tayi kusa da Nainarh “ban san miye ya shiga tsakanin ki da yumnah ba,amma ina sake baki haƙuri a madadinta,kiyi haƙuri Nainarh na san kuskuren fahimta ne ku ka samu amma yumnah bata da matsala” tunda fa'iza ta fara magana ta kafeta da ido tana kallonta,da ace zata iya faɗa mata abunda yumnah tayi mata da bata zauna tana bata haƙuri ba,sai dai duk yanda take jin tsanarta bazata iya tona mata asiri ba ko ba komai ta taimaketa a lokacin da take buƙatar taimako. 
“ki yi haƙuri kin ji” jin jina mata kai tayi tana faɗin “nagode sosai”
“karki damu” fa'iza ta faɗa.
Irfan ya ɗan jima a part ɗin dady dan har kusan 10 pass 30 yana can duk akan maganar fitar da Noor ɗin waje da yake son yi,ko da ya sanar da dadyn baice komai ba sai ma Adu'ar Allah ya ba Noor ɗin lafiya da yayi,sosai irfan ɗin yayi farin ciki ya kuma godema Allah da ya bashi su a matsayin iyaye,nasiha dady  yayi mashi mai ratsa zuciya ya kuma ce ya kamata ya sanar da uncle Ahmad, da to Irfan ɗin ya amsa dama yana da nufin hakan,a tare da dady su ka yi lunch kafin yayi mashi sallama ya koma part ɗin shi dan ya shirya ya koma hospital ɗin.
Shaf shaf ya shirya,key ɗin motar shi ya ɗauka  ya fice daga ɗakin,motar shi dake compound ɗin gidan ya nufa ya shiga, ba ɓata lokaci yayi ma motar key ya fice daga estate ɗin gaba ɗaya.
Uncle mutallab sai Around 10 ya bar hospital ɗin tare da mom fatilah bayan ya sake duba jikin Noor ɗin,ya kuma umarci nureses ɗin da su kula da ita kafin Irfan ɗin ya dawo.

*NOOR*😢

wani irin mummunan zafi jikinta ya ɗauka bacci take amma azabar data gauraye jikinta ce ta farkar da ita,numfashinta ne ya fara fita sama sama,hannunta take son ɗagawa dan taji ko akwai wani a kusa da ita ya taimaka mata da ruwa amma ta kasa,maƙoshinta ya bushe kamar tayi sati rabonta da ruwa,wasu zafafan hawaye ne su ka shiga fitowa daga idanunta lokacin data fahimci babu wata gaɓa a jikinta dake motsi bayan idanunta,bugun zuciyarta ne ya tsananta wanda ita kanta bata san dalili ba,zufa ce ta shiga keto mata ga wani irin zafi dake fitowa daga ko wace ƙofa ta jikinta,hawayen dake zuba daga idanunta ne su ka ƙara yawa dan ta fahimci wani al'amarin ne ke shirin faruwa  da ita gashi babu kowa a ɗakin,tayi fatan Irfan na kusa da ita wannan al'amarin ke faruwa da ita.
Jin motsi a cikin ɗakin ne yasa ta shiga raba idanunta dan ta san bazai wuce Irfan ba ne sai dai lokacin da idanunta su ka sauka akan wanda ke yawo tsakar ɗakin ta fahimci ba shi ba ne.
sanye yake da baƙaƙen kaya ya rufe ko ina jikinshi,da alama ta wata ƙofa ya shigo ba ainihin wacce ake shigowa ɗakin ba dan ba taji alamar buɗe ƙofa ba,da ido kawai ta shiga binshi,magana take son yi amma bata iyawa.
bakin gadon da take kwance ya ƙarasa, zama yayi kan chair dake gaban gadon,idanunta ne ta sauke akan evil mask ɗin dake fuskarshi,a hankali ya zere mask ɗin daga fuskarshi,zaro ido Noor ɗin tayi ganin ko waye,kamar an kunna tap haka hawaye su ka shiga gudu akan fuskarta.
a hankali ya kai hannunshi saman fuskarta yana goge mata hawayen,da raunanniyar murya ya fara magana“Noor ba komai yaja maki ba face taurin kai,ban san mi yasa ki ka zaɓi jefa kanki a cikin matsalar da bata shafeki ba,kinyi kuskure babba na  biye ma zuciyarki,ba wai dan bana sonki ba ne zan kashe ki,ina sonki kamar rayuwata amma ki ka zaɓi mutuwa sama da ni,
zanyi takaici da baƙin ciki na rasaki da zanyi a rayuwata amma babu yanda na iya kasheki shi ne mafita a gare ni” ya ƙarashe maganar yana goge hawayen dake gefen idonshi,kuka kawai Noor take bata taɓa data sanin saka kanta a abunda bai shafeta ba sai a wannan gaɓar,tayi takaicin biyema zuciyarta ko dan saboda Irfan,ta san ko kafin ya jure rashinta a tare da shi za'a ɗauki lokaci,amma data tuna bayin Allahn da ba suji ba ba su gani ba ne ta taimaka sai taji sauƙi ta kuma sake yarda da haka Allah ya ƙaddaro rayuwarta ba mai tsayi ba ce, ko tasa kanta a masifar ko kar tasa kanta dama iyakar kwanakinta kenan.
hannunshi ya zura cikin trousers pocket ɗin shi ya curo wata ƴar madaidaiciyar allura,binshi da ido kawai take har lokacin hawayen dake idonta ba su daina zuba ba
“kamar yanda na maki alƙawari na zan barki ki mutu da Auren Irfan akan ki a yau wannan alƙawari ya cika ina fatan kinyi farin ciki?,zan sake yi maki wannan allurar ne saboda bazan iya jurar ganin halin da zaki shiga ba  a lokacin da ruhinki zai bar gangar jikin ki,kiyi haƙuri Noor haka ƙaddara ta zaɓar mana amma ki sani duk wani bugu da zuciyata za tayi da sonki take yin shi bazan taɓa yafe ma kaina alhakin kasheki da nayi ba,na san zan kasance cikin ƙunci har lokacin da ƙasa zata rufe idanuwana,ina maki fatan samun dacewa” ya faɗa yana kamo hannunta dake sanye da cannula bayan da ya kammala haɗa allurar,tana ji tana gani yayi mata allura wacce take zargin ta guba ce kuma da dukan alamu tana bacci yayi mata wata dan ta fara zargin itace ta kashe duk wata gaɓa ta jikinta.
ko 5 seconds ba'ayi ba allurar ta fara aiki a jikinta,gaba ɗaya jijiyoyin jikinta su ka fito waje  idanunta su ka kakkafe  bakinta na fitar da kumfa,miƙewa yayi tsaye,kissing forehead ɗinta yayi a hankali ya furta “am sorry Noor,zanyi kewar ki” yana gama faɗa ya ɗauki mask ɗin shi ya fice ta ƙofar da ya shigo.
bayan ten minutes da fitarshi dr lelarh tare da nurses guda biyu su ka faɗo ɗakin a kiɗime kamar sun san abunda ya faru,hankali a tashe dr lelarh ya shiga bata taimakon gaggawa sai dai ina ƙaddara ta riga fata tuni ruhinta ya bar gangar jikinta.
Inna lillahi wa Inna Ilaihi Raji'un,waye ya aikata ma Noor haka,wace masiface ta sa kanta a ciki ya Allah.  Irfan kai da su uncle mutallab Allah ya baku haƙurin rashinta😭😭😢😢
Gaba ɗaya ba bu wanda jikinshi baiyi sanyi ba a ɗakin,nurses ɗin dake ciki har sai da su ka matse ƙwalla ta tausayin Noor ɗin,dr lelarh ma daurewa kawai yake amma mutuwar ba ƙaramin taɓashi tayi ba musamman da ya tuna irin son da Irfan da uncle mutallab su ke ma Noor ɗin,ya tausaya masu matuƙa.
ɗaya daga cikin nurses ɗin ce ta rufe ma Noor idanunta dake kallon ceiling,a hankali taja mayafin dake jikin Noor ɗin ta rufe mata fuska.
jiki a sanyaye dr lelarh ya fice.
Yana ficewa daga ɗakin Number dady yayi dialing dan bazai iya sanar da uncle mutallab labarin mutuwar Noor ba.
Dady ya shiga tashin hankali matuƙa lokacin da Dr Lelarh ya sanar da shi mutuwar Noor ɗin
“yallaɓai ba sai kun zo ba saboda dare mu da kan mu zamu kawo gawar gidan Abbah in sha Allah” Dr Lelarh ya faɗa,dady bai iya ce mashi komai ba kawai yayi rejecting call ɗin,ba ƙaramin taɓashi mutuwar tayi ba babban ma tashi hankalin shi halin da Irfan zai shiga,rabasu kawai aka yi ya shiga wani hali inaga yanzu yaji cewa ta bar duniyar baki ɗaya.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un dady ya faɗa yana dafe kansa.
ya jima yana saƙawa da kwancewa kafin ya iya daurewa ya kira su uncle Ahmad ya sanar da su halin da ake ciki,sai daga ƙarshe ya kira Abbah.
babu wanda baiji mutuwar Noor ba a cikin su.
Uncle mustapha yana gama waya da dady ya nufi ward ɗin da aka kwantar da Noor ɗin da yake yana cikin hospital ɗin.
Dr Lelarh yana nan tsaye a bakin ƙofar ward ɗin nurses maza guda biyu suka nufo ward ɗin da stretcher, ba kowa ne ya sanar da su ba sai shi,ƙofar ward ɗin kawai ya nuna masu.
ciki su ka shiga,a tsaye su ka samu nurses ɗin nan mata kamar yan da dr lelarh ya barsu.
a saman bed ɗin su ka ɗaura Noor kafin su ka fice da gawarta daga ɗakin.
gyara ɗakin nurses ɗin su ka shiga yi su ka haɗa duk wani kaya da su ka danganci Noor ɗin.
suna fitowa da gawar uncle mustapha na ƙarasowa,jikinshi ne ya sake yin sanyi lokacin da yaga gawar Noor ɗin.
tura stretcher ɗin nurses ɗin su ka yi su ka nufi hanyar ficewa daga hospital ɗin,mara masu baya uncle mustapha da Dr Lelarh su ka yi.
Suna isowa reception Irfan na shigowa a hanzarce  hannunsa riƙe da ledar eatery da alama ya tsaya yi ma Noor takeaway ne duk da ya san balallai ta iya cin komai ba.
tsabar saurin da yake ne yasa bai lura da nurses ɗin dake tura stretcher ba,nufar uncle mustapha da dr Lelarh,hannu ya miƙa ma su suka gaisa,uncle mustapha ne yace
“daga ina kake haka?”
ledar dake

Please Login or Register in order to submit comment