Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai hawaye dake zarya a cheek ɗinta “get out from my side useless kawai” ya faɗa yana sakin kunenta,da gudu ta nufi bedroom ɗinta tana kuka, Ajiyar zuciya ya sauke yana huro iska mai zafi daga bakinshi,juyawa yayi da nufin zuwa bedroom ɗin shi,momy ya gani sanye da hijab tana aikin tura box,da tsantsar mamaki yake binta da ido harta ƙaraso tsakiyar parlorn, trolley ta saki ta juya zuwa ɗakin Laatifa,da mugun sauri ya riƙo hannunta,a masifance ta fisge hannunta daga nashi,idanunta sun ƙaɗa jawur hawaye ne kwance a cikin su “how dare you to touch me,don't eve touch me again our marriage is over” juyawa tayi ta nufi bedroom ɗin Laatifa,sake riƙo hannunta yayi,yanzu riƙo yayi mata ba na wasa ba,fisgarta yayi zuwa cikin parlorn a saman sofa ya zaunar da ita
“baki da hankali ne maimunatu,ina ki ke tunanin zaki a wannan lokacin,ko baki san ƙarfe nawa ba ne??” ya faɗa yana nuna mata agogo dake manne jikin bango
“is not your business,ko ina zani bai shafeka ba”
“calm down,idan saboda abunda nayi mata ne ki ke shirin aikata haka,samunta nayi tana ƙoƙarin cusama Balqis wannan yaron har faɗi take zata mata booking flight taje ta sameshi a can”
“bai shafe ni ba,ka sani babu sauran wani Aure tsakanina da kai,yau bazan kwana gidan nan ba,ka biyoni da takardata har gidan iyaye na”
“kina hauka ne saboda wannan abun ki ke faɗin our marriage is over,zaki tafi gidan ku,ko dai kin fara shan wani abu ne ban sani ba”
“abunda ka ke sha shi nasha,wallahi sai na tafi,kuma bani ba kai,yanda ka tsani ƴata haka ni ma na tsaneka” kuka ta fashe dashi mai ban tausayi “kai azzalumin uba ne Hashim kuma azzalumin miji,wallahi haƙi na dana laatifa sai ya ga bayanka,macuci kawai wanda bai san haƙƙin dake kanshi ba,mai nuna wariya a tsakanin ƴaƴanshi,wallahi nayi dana sanin Aurenka a rayuwata,ka sake ni wallahi bazan cigaba da zama da...” tsawa ya daka mata wacce tasa dole tayi shiru,Laatifa na daga bakin ƙofar ɗakinta duk abunda ke faruwa akan kunenta,kuka take sosai bata taɓa jin muguwar tsanar Mahaifinta ba irin yau, tayi baƙin cikin kasancewar shi mahaifinta, tayi fatan ace ta mutu tun da daɗewa bata riski irin wannan baƙin cikin ba “ni ki ke furta ma waɗan nan kalaman?” ya faɗa cikin ɗaga murya yana nuna kanshi
“na faɗa maka haka, fiye ma da haka za kaji daga bakina, wallahi nayi dana sanin Auren ka,ka sawaƙe man” ɗan rintse ido yayi yana girgiza kai,duk fa abunda yake aikatawa da alƙarshi da mamy yana son mom maimunatu kuma baya son rabuwa da ita,tashi tayi daga saman sofa tana goge hawayen dake fuskarta, bedroom ɗin Laatifa ta nufa
“yau ba sai gobe ba zamu bar maka gidanka kai da ƴarka” da mugun zafin nama ya nufeta,fisgota yayi zuwa jikinshi,kuka ta fashe da shi tana ƙoƙarin ɓanɓare kanta daga jikinshi,janta yayi ta ƙarfi zuwa bedroom ɗin shi,ture shi take tana faɗin
“ka rabu dani hashim,bazan cigaba da zama da kai ba”
zaunar da ita yayi saman makeken bed ɗin shi,cikin kwantar da murya yace “ki tsaya ki fahimce ni munarh,ba wai bana son Laatifa ba ne,ina mata hak...” tsawa ta daka mashi “karka kawo man maganar banza,ka sani babu abunda zaka yi da zaisa na haƙura,baka son laatifa kowa ya shaida haka”
“wallahi ina son Laatifa,ki tsaya ki fahimce abunda nake son na faɗamaki”
“hashim ka riga ka makaro,gida dai sai mun bar maka yau ba sai gobe ba” girgiza kai yayi ya lura ba sauraren shi za tayi ba.
kuka sosai take kamar ranta zai fita bata taɓa tunanin tsanar da dadynta ke mata har ta kai yayi mata iyaka da ƴar uwarta ba,ta jima sosai a bakin ƙofar ɗakin sai da kanta ya fara mata ciwo tukun ta sassauta ma kanta,wayarta dake ajiye saman dressing mirror ta ɗauka,missed call ɗin SAM ta gani har biyu,hawayen dake fuskarta ta share,kusan duk time da zata shiga cikin wani hali sai aci sa'a ya kirata kamar yana jin duk wani abu dake faruwa da ita,bin bayan kiran tayi amma har kiran ya katse baiyi picking ba, sake kira tayi karo na biyu still baiyi picking ba, ajiye wayar tayi ta nufi bathroom.
Uncle hashim kusan kwana su kayi zaune yana lallashin mom maimunatu amma kwata kwata taƙi ta saurareshi saima kuka data sa mashi ganin zai dameta, babu yanda ya iya dan dole ya kawo ido ya zuba mata.
Zukatan nan huɗu yanda su ka ga rana haka su ka ga dare har shi kanshi Uncle hashim da shi ne musabbabin komai.
zazzaɓi mai zafi ne ya rufe Balqis ga matsanancin ciwan kai saboda kukan data sha.

*Second father's house*

zaune yake saman chair,yayinda system ɗin shi ke ajiye saman desk yana opreting,shirt ce mai gajeran hannu a jikinshi haɗe da short, idanunshi a manne suke da glass ya zuba su akan system  ɗin shi da yake aiki, Aunty Nafisat na daga kwance saman bed ta baje sai kwasar baccinta take,ƴar baby doll ce a jikinta pink color yayinda kanta ke sanye da black ɗin hula,baccinta take peacefully.
mug ɗin coffeen dake ajiye gefe ya ɗauka ya kai bakinshi,yayinda yake tsayar da idanunshi akan system ɗin, ya shafe kusan awa biyu yana aikin kafin ya kashe system ɗin,saurin ɗaukar wayarshi dake gefe yayi a dalilin ƙarar da tayi na alamar shigowar message,buɗe message ɗin yayi, karanta abunda ya ƙunsa ya shiga yi har ya kammala,ƙyataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, yana shirin tashi daga saman chair sai ga kira ya shigo wayar daga Uncle Ubaid wato sirikinshi mahaifin Aunty Nafisat,kallon kiran yake cike da mamakin ko lafiya yake kiranshi a irin wannan lokacin duk da kasancewar shi shugabanshi a wurin aiki,har kiran ya katse baiyi picking ba, ya Naeem yanda wata ɗabi'a muddin na gaba dashi ya kirashi baya taɓa picking har sai kiran ya katse tukun ya kira da kanshi, kiran na katsewa yayi dialing number, ringing biyu Uncle Ubaid yayi picking,cike da ladabi ya gaishe dashi bayan ya amsa sallamar da yayi mashi,da kulawa ya amsa mashi yana faɗin “Afuwan na tashe ka daga bacci” murmushi ya Naeem yayi yana faɗin “babu komai dady aiki ma nake ban kai da kwanciyar ba”
“ok dama akwai wani case da nake son ka yi aiki a kanshi, shaf mantawa nayi ɗazu a office ban baka ba, yanzu ma gudun karna manta ne yasa na kira ka a wannan lokacin”
“ba damuwa,akan miye case ɗin?”
“case ɗin about kidnapping ne,wasu yara ne aka yi kidnapping tsawan wata biyu kenan, kasan mutanen mu yanda su ke musamman ace marasa ƙarfi ne,sai abu ya lalace tukun za suyi involving force,amma zan tura maka da C D,gobe idan kazo office ka same ni zan baka files ɗin case,sai na maka ƙarin bayani akan case ɗin, Please Naeem na san ka da hazaƙa da maida hankali akan aiki,ba na da shayi ko ɗar akan ka please kayi aikin yanda ya kamata,aiki ne mai matuƙar mahimmanci da haɗari,saika maida hankali sosai”
“in sha Allah dady,zai tafi yanda ka ke so”
“yawwa haka nake son ji,gobe sai ka same ni a office”
“to Allah ya kaimu goben lafiya”
“Ameen,mu kwana lafiya” da Ameen ya Naeem ya amsa, rejecting Kiran uncle Ubaid yayi,ɗan shiru ya Naeem yayi yana tunanin wani abu, message ɗin da aka turo mashi ya sake dubawa kafin ya tashi, switch ɗin ɗakin ya nufa ya kashe hasken ɗakin tukun ya nufi bed,ajiye wayarshi yayi haɗi da cire glasses ɗin dake idonshi tukun ya kunna bedside lamp,kwanciya yayi bayan ya karanta Adu'a kwanciya bacci ya shafe jikinshi da na Aunty Nafisat, murmushi yayi yana jawota jikinshi haɗi da ja masu duvet.

*UNITED STATE❤*

_*Las Vegas (Nevada)*_

tunda su ka dawo daga hospital bayan sun gama shagalin su take zaune a ɗaki ita kaɗai Aunty Sophia ma data shigo fita tayi domin haɗa mata dinner dai dai da lafiyarta,mrs Malika kuwa tunda su ka dawo bata tako zuwa ɗakinta ba har yanzu fushi take da ita kan abunda tayi ma mijinta ga wani sabon tsari data ɓullo mata na sai ta rabu da shi.
zaune take tsakiyar bed ɗinta ta jingina da head board ɗin bed ɗin,idanunta a lumshe kamar mai bacci,PJ ne a jikinta riga da wando masu taushi white color.
wayarta dake ajiye saman Nightstand ce tayi ƙara alamar shigowar message,ɗan kallon wayar kawai tayi da kamar bazata ɗauka ba sai kuma ta zura hannu ta jawo wayar.
shiga cikin message ɗin tayi, scrolling message ɗin ta shiga yi,jifa tayi da wayar saman bed bayan ta kammala karanta message ɗin,tsaki taja tarasa miye matsalar wannan ɗan tahalinkin da ya damu rayuwarta ko dan kawai yaga ta zuba mashi ido ne yasa yake mata wannan shiga hancin ne,wannan kusan message na uku ke nan daya tura mata a yau,sake jan wani tsakin tayi.
A hankali ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta riƙe da wasu papers, da ido Nailarh ta bita har ta ƙaraso gaban bed ɗin,zama tayi tana faɗin “baby ya jikin naki” ta faɗa idanunta na kan pepars ɗin data shigo da su without looking her position,kallonta kawai tayi without answering her,bata damu da ƙin amsa mata da ba tayi ba, pepars ɗin ta miƙa mata “gashi yanzu Joseph ya kawo man,na cike Form ɗin nayi signing zuwa gobe zan aika mashi da nashi saboda ya shigo U S jiya,kome ke nan idan ya dawo da nashi Form ɗin zan kawo maki ki gani,fatan kinyi farin ciki yanzu?” still she's not looking at her,ɗan ajiyar zuciya Nailarh ta saki “saboda haka ne yasa duk ki ka shiga damuwa haka?” banza Malika tayi da ita,matsowa Nailarh tayi kusa da ita,kwantar da kanta tayi saman shoulder ɗin ta a hankali tace “sweetheart idan baki son rabuwa dashi karki cutar da kanki,ki ƙyale ni nayi abunda nake so kema ki zauna da mijinki” wani kallo Malika tayi mata ba tare da tace mata ƙala ba,kallonta itama Nailarh tayi,turo ƙofar ɗakin Aunty Sophia tayi ta shigo hannunta ɗauke da tryan data haɗa ma Nailarh dinner,sadda kanta tayi ƙasa harta ƙaraso cikin ɗakin,a saman table ta ajiye dinner,kallon Malika tayi “ma'am dinner is ready” jin jina mata kai Malika tayi “thanks U Sophia” gyaɗa kai Aunty Sophia tayi tana kallon Nailarh “gud Night baby” tana faɗa haka ta fice daga ɗakin,trayn Malika ta ɗauko,a saman bed ɗin ta ajiye,da kanta ta shiga ba Nailarh,kallonta kawai Nailarh take tana ganin yanda gaba ɗaya mood ɗin ta ya canza saboda kawai zata rabu da wannan mijin nata,ɗaukar trayn tayi ta fice bayan ta kammala bata,da ido kawai Nailarh ta bita,bata sake dawowa ɗakin ba har Nailarh tayi bacci.

*ABUJA NIGERIA*

washe gari tunda asubar fari mom maimunatu ta fice daga ɗakin dady,da zai fita sallah ya manta ya bar ƙofar a buɗe hakan ne ya bata damar ficewa daga ɗakin,direct ɗakin Laatifa ta nufa box ɗinta na nan parlor Kamar yanda su ka barshi jiya ,turus ta tsaya gabanta na wani irin faɗuwa ganin yanda ɗakin Laatifa ya koma,sakin ƙofar tayi ta nufi cikin ɗakin tana bin ko ina na ɗakin da kallo, duk wani abu mai amfani na laatifa babu shi a ɗakin,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba lokacin da idanunta su ka sauka akan box ɗin Laatifa da babu guda biyu.
da mugun sauri ta nufi bakin ƙofar bathroom, nocking ta shiga yi tana kiran sunan laatifa amma taji tsit,sai da ma ta saurara da kyau tukun ta fahimci babu kowa a ciki,tura ƙofar toilet ɗin tayi ta shiga,wayam ta gani kamar ma anyi kwanaki ba'ayi amfani da shi ba,bugun zuciyarta ne ya tsananta,hankali a tashe ta fice daga toilet ɗin kamar mahaukaciya,tun a cikin ɗakin ta shiga ƙwala kiran sunan laatifa kamar maƙoshinta zai tsage,room by room na gidan ta shiga bincikawa tana kiran sunan Laatifa kamar zata fashe da kuka,hankali a tashe laure ta fito dan duk wanda ke gidan yaji yanda momy ke kiran sunan laatifa,tun kafin laure ta ƙaraso momy ta shiga tambayar ta ko ta ga inda laatifa ta shiga,idanunta da bacci bai gama isarsu ba ta shiga murzawa tana faɗin “cikin dare bayan hatsaniyar data faru na fito na kashe bulbs sannan na ɗauki ruwa a kitchen” saurin dakatar da ita momy tayi “ba dogon labari na tambayeki ba,ina Laatifa kin ga inda ta tafi??”
“ai shine zan faɗa maki, tun cikin daren ta fice da da akwatunanta guda biyu” saurin dafe saitin zuciyarta momy tayi “ina tace maki za taje” ta faɗa tana ɗan ɗaga murya
“ceman tayi wani waje mai nisa zata ,harma ta nemi yafiyata tace man ba lallai mu sake haɗuwa ba,tac..” ai tun kafin ta ƙarasa momy ta ɗauketa da mari mai rai da lafiya dai dai nan Balqis da uncle hashim da dawowarshi kenan daga masjid su ka faɗo parlorn,dafe cheek laure tayi tana kallon momy
“saboda kina shashasha ki ka kasa sanar da wani a cikin mu” laure na kuka tace “wallahi hanani tayi ita tace karna sanar da kowa” cikin parlorn balqis da uncle hashim su ka ƙaraso,zubewa momy tayi saman sofa tana dafe kanta “na shiga uku ni maimunah,mi yasa laatifa zaki man haka,mi yasa, wannan wace irin rayuwace” ta faɗa tana fashewa da ku ka mai ban tausayi
“kiyi haƙuri momy” laure ta faɗa,da sauri Balqis ta nufi ɗakin yayar tata,kusa da momy uncle hashim ya ƙaraso, kneeling yayi a gabanta yana kamo hannunta cikin kwantar da murya yace “kiyi haƙuri maimunatu” bai kaida ƙarasa faɗar abunda zai faɗa ba ta fisge hannunta daga nashi tana rufeshi da masifa “dama dole kace nayi haƙuri tunda ka riga ka cuceni,yanzu ai sai hankalinka ya kwanta laatifa ta bar maka gidanka sai ka zuba ruwa ƙasa kasha,amma ka sani tunda har kayi sanadin da laatifa tabar gidan nan nima na barshi har abada kuwa”
“dan Allah kiyi haƙuri,kusan kwana nayi fa ina lallashinki nayi maki alƙawarin hakan bazata sake faruwa ba,kuma laatifa babu inda taje tana cikin Estate ɗin nan,Dan Allah kiyi haƙuri” balqis ce ta fito daga ɗakin Laatifa riƙe da pepar tana kuka,tun kafin ta ƙaraso cikin parlorn take faɗin “momy Aunty laatifa” sai kawai ta fashe da kuka ba tare da ta ƙarasa faɗar abunda zata faɗa ba,da sauri momy ta nufota, pepar dake hannun balqis ɗin ta amsa,karanta note dake jiki ta shiga yi kamar haka
_na san ban kyauta maki ba momy,kiyi haƙuri ya zama dole ne na tafi,bana son Aurenki ya samu matsala a saboda ni,dady bazai taɓa yafe man ba,yayi man iyaka da ƴar uwata a yau,bazan iya cigaba da ganin tsanar da yayi man a idanunsa ba, shiyyasa kawai na yanke shawarar nayi nesa dashi ko hakan zai sa ya yafe man,ki yafe man momy idan da rabon mu sake haɗuwa zan dawo gareki,ki kula man da kanki_
_*Ina sonki uwa ta gari,zanyi kewarki sosai*_
jefama uncle Hashim paper tayi lokacin data gama karanta abunda paper ta ƙunsa,fashewa tayi da kuka tana faɗin “yanzu sai hankalinka ya sake kwanciya Laatifa ta tafi kamar yanda kaso,wallahi Allah sai ya saka mana,ka cuci ƴarka ka cuci kanka” tana kaiwa nan ta nufi ɗakinta tana kuka, Balqis kuka laure kuka kamar ransu zai fita,jiri Balqis ta fara ji ga wani mahaukacin zazzaɓi da ya sake rufeta,kanta kamar zai fashe,sofa ta nufa zata zauna tunkafin ta ƙarasa ga sofa ta yanke jiki ta faɗi,da gudu laure da uncle hashim su ka yi kanta,kiran sunanta ya shiga yi yana jijjigata,laure sai kuka take tana kiran sunan Balqis ɗin itama,suna a haka mom maimunatu ta shigo parlor da wani box a hannunta,ko kallon inda su ke ba tayi ba ta ɗauki wayarta haɗi da jan box ɗinta wanda ta bari tun jiya ta fice daga parlorn duk da tana jin yanda su ke kiran sunan Balqis.
hakan da tayi ba ƙaramin taɓa zuciyar uncle Hashim yayi ba,hannu yasa ya ɗauki balqis ɗin a kafaɗar shi,ficewa yayi da ita a hanzarce,yana isa parking space motar momy na ficewa daga gidan,a mota yasa Balqis ɗin,key yayima motar ya fice zuwa hospital.
Mom fitowarta kenan daga part ɗin dady bayan gama ta ƙaddamar su akan Auren Irfan ɗin da har yanzu dady yaƙi haƙura,sanye take da hijab har ƙasa hannunta riƙe da tasbaha, bedroom ɗinta ta nufa kwata kwata bata lura da mutum dake kwance kan sofa ba harta kai bakin ƙofa,hannunta ta ɗaura kan handle ɗin ƙofa jin an kira sunanta ne yasa ta dakata,ƙarasowa su ka yi har inda take,cike da girmamawa su ka shiga gaisheta “good morning mom” murmushi ta sakar masu tana amsa masu gaisuwar “morning,how was your night,I hope you slept well?”
“Alhmdllh” su ka faɗa a tare, murmushi ta sake sakar masu tana shafa fuskar Nainarh “how was your body,I hope u feel better now”
“Alhmdllh mom,I feel much better now”
“Alhmdllh,Allah ya ƙara lafiya,ya tsare gaba” da Ameen su ka amsa,jinjina masu kai tayi “kuje ku gaishe da dadyn ku”
To su ka ce,barin bakin ƙofar su ka yi,idanun Yumnah ne su ka sauka akan mutum dake kwance saman sofa,ƙara ta saki dan tashin farko tsorata tayi,saurin riƙeta Nainarh tayi tana tambayar lafiya,da sauri mom ta nufo cikin parlorn dan bata kai da ƙarasawa ciki ba Yumnah tayi ƙara
“lafiya Yumnah ki ke wannan ƙarar haka mai makon kiyi salati,kwata kwata wanan ba ɗabi'a bace ta gari” sofa ta nuna masu
“mutum ne a kwance”saurin kallon sofa su ka yi, ɗan zaro ido mom tayi,bulbs ɗin parlorn a kashe su ke sai ɗan hasken bulbs ɗin kitchen daya hasko parlorn hakan yasa basu gane waye ba.
har gaban sofa mom ta ƙarasa yumnah tunda ta maƙalƙale jikin Nainarh ko motsi ba ta yi sai zare ido take kamar wacce aka kama tana satar naman miya.
mayafin dake saman fuskarta mom ta yaye zaro ido tayi tana ambatar sunanta “LAATIFA!” jin sunan data furta ne yasa yumnah sakin Nainarh ta nufo sofa,bayanta Nainarh ta biyo,ɗan bubbuga hannun sofa mom tayi tana kiran sunanta,a tsorace ta farka tana faɗin innalillahi wa Inna ilaihi raji'un,saurin riƙo hannunta mom tayi “laatifa lafiya ki ke, What's wrong with u, why are u slept here??” mom ta shiga jera mata tambayoyi,iya jiya kawai har wata irin rama tayi ga jirwayen hawaye nan a cheek ɗinta bakinta ya bushe sosai,kallon mom ɗin tayi ba tare da tace komai ba
“Aunty laatifa kiyi magana mana” yumnah ta faɗa kamar za tayi ku ka,sadda kai tayi ƙasa hawaye na bin cheek ɗinta ɗan ajiyar zuciya mom ta sauke,kama hannunta tayi
“tashi muje kiyi sallah kinji” bin mom ɗin tayi har bedroom ɗin ta, bayan su su Nainarh su ka bi amma mom tace su wuce kawai wajen dady,juyawa su ka yi zuwa part ɗin dady,sun ɗan jima a part ɗin dady kafin su ka fito duk da ba karatu yayi masu ba,tun da Nainarh ta ƙone ba suyi karatu ba yaune ma taje part ɗin dady dan ta gaishe da shi.
Laatifa bayan da ta gama sallah asuba,kwanciya mom tace tayi ta hutu ita kuma ta fice zuwa part ɗin dady,a zaune ta sameshi kamar yanda ta barshi,ƙarasawa tayi har gaban shi,zama tayi kamar mai ɗaukar karatu, littafin dake hannunshi ya ajiye yana kallonta “lafiya dai ko katte?” ɗan ajiyar zuciya ta sauke tana bashi labarin ganin laatifa da yanayin da su ka ganta
“da alama anan ta kwanta,na tambayeta amma bata bani amsa ba,kasan halin hashim yanzu haka wani abu ya haɗa shi da ita har yayi mata abunda yasa ta bar gidan cikin dare” tunda mom ta fara magana dady ke Binta da ido ƙala baice ba,amma kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar ɓacin da ranshi yayi
“ban san wane irin uba bane ba hashim,kwata kwata bai san role ɗin shi ba a matsayin shi na mahaifi,ya ɗauki karan tsana ya ɗaura ma yarinya saboda Sam,in banda abun shi yaushe rabun Sam ma da ƙasar da zai zauna yana gallaza ma yar sa saboda shi,wallahi har ga Allah bazan iya yafe ma wanda yayi ma Sam wannan ƙazafin ba,sun hana ni zama da ɗana, duk sun ɗauki karan tsana sun ɗaura mashi” ta faɗa kamar zata sa kuka, da alama abun ya daɗe yana damunta
“waye ya ce maki ya tsani Sam?,shifa tamkar ɗan su ne taya za su tsane sa?”
“basa son shi mana,duk kai ka basu ƙwarin gwiwa,da baka wulaƙanta ɗan naka a gaban su ba,ka ƙi tsayawa ka fahimce shi a lokacin da yake buƙatar taimakon ka da duk hakan bata faru,da kaima yanzu haka kana tare da shi,ban san mi yasa kun cika son kanku da yawa ba,ya kamata ku riƙa bincike kafin ku yanke hukunci” nannauyar ajiyar zuciya dady ya sauke “ya isa haka Zulaihart,bana son kina tada abunda ya wuce,komai daya faru kuskure ne,na riga da nayi kuskure,kuma dan kinga Laatifa baki da tabbacin saboda hakan ne yasa ta fito gida” girgiza kai mom tayi
“wallahi ni na san baƙin halin hashim,babu abunda tayi mashi bayan wannan”
“ya isa haka dan Allah,yanzu ina Laatifa take?”
“na barta a ɗaki tana bacci”
“to shikenan,zan kira Hashim ɗin,zanji mike faruwa” taɓe baki mom ɗin tayi ba tare da tace ƙala ba,wayarshi dake ajiye saman sofa ya ɗauka, Number uncle Hashim ya shiga dialing harta katse baiyi picking ba sake kira yayi still bai ɗauka ba.
tashi mom tayi ta fice daga ɗakin,bedroom ɗinta ta koma,with full of surprise mom ke kallon Laatifa dake yafa mayafin abayar dake jikinta,sakin ƙofar tayi ta ƙarasa cikin ɗakin
“lafiya dai ko Laatifa,ina ki ke shirin zuwa haka?” saurin kallon mom tayi sai kuma ta sadda kanta ƙasa,har in da take tsaye mom ɗin ta ƙaraso,hannunta ta kama zuwa bakin bed,zaunar da ita tayi itama ta zauna
“lafiya laatifa,mi ya sa ki ka bar gida cikin dare,ina kuma ki ke shirin zuwa yanzu??” mom ta jera mata tambayoyin tana kafeta da ido cike da son jin amsa daga gareta,duƙar da kai laatifa tayi a hankali tace “mom mun samu saɓani ne da dady”kaf abunda ya faru bata ɓoye ma mom ba,ba ta yi mamakin jin abunda uncle Hashim ɗin yayi mata ba dama ta san zai iya fiye ma da hakan,kamo hannunta tayi cikin nata “amma ai Laatifa da baki fito a wannan lokacin ba ko dan saboda mahaifiyarki”
“mom bana da wani zaɓi ne,bazan iya jurar ganin saɓani a tsakanin su ba saboda ni”
“haka ne amma kinga dare ne,ke macece bai kamata ki fito a wannan lokacin ba” shiru kawai Laatifa tayi ba tare da tace komai,ɗan ajiyar zuciya mom ta sauke “yanzu ina ki ke shirin zuwa dana ga kina yafa mayafi” shiru laatifa tayi tana wasa da gefen mayafinta without answering her “baza ki faɗa man ba” ɗan ɗagowa tayi ta kalli mom ɗin sai kuma ta maida kanta ƙasa“California” ta faɗa a hankali, mom was surprise da magananta “mi za kiyi a can?” mom ta jefa mata tambaya tana tsareta da ido “wajen Sam zan je” wani kallo mom ta jefe mata,tama rasa mi za ta ce mata,ɗan ɗagowa tayi ta saci kallon mom ɗin,kauda kai gefe mom tayi “shi yace maki ki zo,ko kawai ke ki ka yi deciding ki je?”mom ta jefa mata tambaya
“shi yace na zo” ta bata amsa
“kunyi waya da shi kenan?”
“eh tun jiya munyi waya” ɗan ajiyar zuciya mom ta sauke
“Laatifa!” ta kira sunanta in a serious tolk,ɗaga kai tayi ta kalli mom ɗin ba tare da tace komai ba
“laatifa a matsayinki na mace wacce ba muharramarshi ba bai dace ace kije wurin sa ba,ko kin manta shine dalilin wannan matsalar da ki ke samu da dadyn ki??”
“mom dady bazai yafe man ba,kuma zan koma S N J T ne na cigaba da aiki a can”
“a ina zaki zauna kenan?”
“gidan ma'aikata”
“look laatifa maganar zuwanki California wurin sam ma bata ta so ba,ki yi zamanki anan har Allah yasa mahaifinki ya sauko”
“amma mom...” da katar da ita mom tayi
“karki ce komai,kiyi haƙuri dadynku zai yi magana da dadynki, idan ma bai sauka ya yafe maki ba,kiyi zaman ki anan a tare dani har lokacin da Allah kema zai baki miji kiyi Aure,amma maganar zuwa wurin sam ki barta”
“ya riga yayi man booking flight tun jiyan”
“karki damu zanyi magana dashi,ki kwantar da hankalinki kinji”
“to Nagode mom”
“yawwa ki kwantar da hankalinki ni ma momynki ce,zan zauna dake har Aurenki laatifa,nan ma fa gidan mahaifinki ne kuma darajarar ƴa mace gidan mijinta idan ba tayi Aure ba gidan mahaifinta,ki kwantar da hankalinki kinji”
“momy

Please Login or Register in order to submit comment