Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunshi ya nuna ma uncle mustapha “daga gida nake,na tsaya yima Noor takeaway ne,amma lafiya uncle,ina za ku?” ya faɗa yana bin fuskokin su da ido dan kallo ɗaya zaka masu ka hango tashin hankali da su ke ciki
“bakomai gida za mu,kaima juyawa za kayi mu tafi”
da mamaki ya kalli uncle mustapha “amma uncle babu kowa a tare da Noor ɗin,ni nace uncle ya tafi zan kwana tare da ita”
“karka damu Irfan Noor bata buƙatar kowa a tare da ita,mu tafi gidan kawai,akwai dalilin da yasa nace muje”
tsintar kanshi yayi a wani irin yanayi jin abunda uncle mustapha ya faɗa,tuni tsoro da fargaba sun mamaye zuciyar shi.
wani irin tausayin shi ne ya rufe dr Lelarh hakama uncle mustapha,daurewa kawai yake yana wannan maganar.
“to uncle amma dan Allah ka bari na ganta tukun sai mu tafi,kuma ga abinci da na zo mata da shi”
“karka damu ba jimawa za kayi ba,bari a ba nurses sai su bata kafin ka dawo” gyaɗa kai kawai irfan ɗin yayi amma ba dan yaji daɗi hanshi ganinta da uncle mustapha yayi ba.
amsar ledar takeaway uncle yayi ya miƙama nurses ɗin dake reception ɗin kafin ya kama hannun Irfan ɗin su ka fice,lokacin da zasu iso compound tuni an saka gawar Noor ɗin a Ambulance,motar uncle mustapha su ka nufa,passenger seat dr Lelarh ya buɗe ya shiga Irfan ya shiga back seat yayinda uncle mustapha ya zauna a driver seat.
reverse yayi ya nufi gate ɗin hospital ɗin motar securitys ɗinshi na gaba yayinda Ambulance ke bayan su tare da wata motar securitys ɗin.
Irfan tunda ya shiga motar ya sadda kai ƙasa ya rasa gane taƙamaimai halin da ya ke ciki,abunda kawai ya sani shine ya san wani babban Al'amari ne yake faruwa koma ya faru wanda yake zargin ya shafeshi dan har lokacin hankalinshi bai kaiga ambulance ɗin dake bayan su ba.
a bakin main entrance ɗin shiga part ɗin Abbah su ka samu su uncle Ahmad harda uncle mutallab wanda har gida su ka je su ka ɗauko shi sai dai ba su sanar da shi abunda ya faru ba,a tsaitsaye su ke ko wanne ka kalla tashin hankali ne a fuskar shi.
parking motocin su suka yi a compound,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fitowa.
A hanzarce su uncle Ahmad ɗin su ka nufi Ambulance ɗin.
fito da gawar nurses ɗin su ka shiga yi.
wani irin bugawa zuciyar uncle mutallab tayi lokacin idanunshi su ka sauka akan gawar Noor ɗin,gaba ɗaya ya nufi baya zai faɗi da sauri uncle Ahmad da Uncle Ubaid su ka taroshi,da wani irin yanayi yake bin fuskokin su da ido kafin ya sake kallon gawar Noor ɗin kawai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro
gaba ɗaya jikinsu ya sake yin sanyi.
Irfan ko da ya fahimci abunda ke faruwa yanke jiki yayi ya faɗi sai dai su ka ji faɗuwarshi,da gudu dady da uncle mustapha su ka yi kanshi,jijjigashi dady ya shiga yi yana kiran sunanshi amma ina.
Uncle hashim ne ya ba su ruwa dan a yayyafa mashi amma har ruwan container ya ƙare babu alamun zai farfaɗo.
tashin hankali da ba'a sa mashi date tuni hawaye sun shiga zarya a fuskar dady,Abbah ne yace su shiga da gawar,uncle mutallab ma ciki su uncle Ahmad su ka shiga da shi,ɗaukar Irfan uncle mustapha yayi suma su ka shiga ciki duk da dr Lelarh ya so su bari kawai su ko ma hospital da Irfan ɗin dan akwai haɗari a tattare da halin da yake ciki. 
parlor Abbah  su ka nufa,anan tsakiyar parlor su ka ajiye gawar,uncle mutallab sai sambatu yake kamar wanda ya samu taɓin ƙwaƙwalwa.
sofa uncle mustapha ya nufa da Irfan ɗin ya kwantar dashi.
Dr Lelarh ya shiga bashi taimakon gaggawa dan ganin ya farfaɗo,ba ƙaramar wahala ya sha ba kafin ya samu Irfan ɗin ya farfaɗo dan har sun fara cire rai da zai farfaɗo ba tare da sun danganta da hospital ba.
kusan a tare su ka shiga sauke ajiyar zuciya da godiya ga Allah dan sun tsorata sosai da irin suman da ya yi,sai dai tunda ya buɗe ido akan gawar Noor ɗin bai sake wani motsi ba baya cewa uhm bare uhm uhm.
sallama dr Lelarh yayi masu shi da nurses ɗin akan za su dawo gobe da safe saboda dare yayi dole sai dai a bari gobe akai Noor ɗin.
a nan parlorn su ka yi jugum jugum baka jin motsi komai sai sambatu uncle mutallab da ya cika parlorn sunyi lallashin amma ina,kamar suna daɗa tunzurashi ne,sosai ya haukace masu,Adu'a Abbah ya shiga karantowa yana tofa mashi a kai haka Irfan ma Adu'a dady yake mashi dan gaba ɗaya hankalinshi a tashe yake da yanayinshi.
ba su sanar da matan halin da ake ciki ba dan ko Innah dake gidan bata san abunda ke faruwa ba sai a washe gari su ke samun labarin mutuwar Noor ɗin.
Ni kaina bazan iya misalta maku irin tashin hankalin da su ka tsinci kansu a ciki ba. mom fatilah Lokacin da labarin mutuwar Noor ɗin ya risketa suma tayi wanda daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba,da an samu tafarfaɗo zata sake wani suman,dole tasa aka nufi hospital da ita ba tare ma da ta samu ganin Noor ɗin ba.
Babu wanda mutuwar Noor ɗin bata girgiza ba a family, Nainarh harda kukanta musamman data tuna ba taje ta gaishe da Noor ɗin ba lokacin da aka kwantar da ita,taji takaici da haushin kanta na ƙin zuwa,Waseef ma yaci kuka na alhinin mutuwar da tausayin halin da ɗan uwanshi yake ciki.
Driver Abbah yasa ya ɗauko mom da mom Maryam daga hospital domin yima Noor ɗin wanka.
A nan part ɗin Abbah su ka haɗu matan su mamy ne kawai babu suma suna tare da mom fatilah a asibiti,babu ɓata lokaci su ka shiryata cikin likafaninta,anan compound ɗin gidan aka mata sallah,ba laifi mutane da yawa sun halarci sallar jana'izar,gaba ɗaya mazan su ka kwashe zuwa maƙabarta,ko kafin su dawo tuni gidan ya cika da mutane, kan kace me ƴan uwa na nesa da kusa sun zo kamar part ɗin zai tsage ko ina ka ɓulla mutanene.
Irfan tunda su ka dawo ya shige ɗakin Abbah,wunin ranar ko ruwa bai gitta ta maƙoshinshi ba gashi har lokacin babu wanda yaji wata kalma ta fito daga bakin shi a washe gari dady yasa Dr Fawar ya dubashi amma babu wani cigaba yana nan ba uhm bare uhm uhm kuma anyi anyi ko da ruwan tea ne yasha amma yaƙi,dole tasa dady kawo ido ya zuba mashi sai dai ya dunga mashi Adu'a dama ya san abun is not easy to him.
Matan da dare yayi su ke tafiya gida mazan ne kawai ke kwana nan har akayi Adu'ar kwana uku,aranar Kainart ta farka daga nan Dr Lelarh ya ce a dakata da yi mata allura.
Mom maimunatu tunda aka yi rasuwar kullum ne sai ta zo,sai a sannan Abbah ya san bata gidan uncle hashim,saboda taron mutane yasa Abbah baima uncle hashim ɗin magana ba.
A daren ranar su dady kowa ya koma gidanshi uncle mutallab kawai su ka bari a part ɗin Abbah,shima Abban ne yace ya bari sai anyi sati tukun ya koma gida tunda ba kowa ga halin da yake ciki,da za su tafi ne bayan su dady sun fita daga part ɗin uncle Ahmad ya kasa haƙuri har sai da ya tambayi uncle Mustafa zaabith da tun ranar da aka kwantar da kainart bai sake ganinshi ba ya kira wayarshi baya samu yayi binciken amma bai gano komai ba da ya shafi inda yake shiyyasa yake zargin uncle Mustafa na da sa hannu a ɓatan shi kuma yaƙi yace komai,shirun ma da yayi game da abunda ya faru da kainart ɗin ne yasa shi ƙara tabbatar da zargin zaabith ɗin na tare da shi,saboda halin da su ke ciki ne yasa bai sanar da kowa ba,amma ganin idan yayi shiru abun zaizama babba ne yasa yayi ma uncle Mustafan magana,amma da yayi mashi magana ko kulashi baiyi ba saima yima Abbah sallama da yayi ya fice daga gidan.
ran uncle Ahmad ba ƙaramin ɓaci yayi ba,haƙuri Abbah ya bashi akan shi da kanshi zaiyi magana da uncle Mustafa in dai zaabith ɗin na tare da shi zai sa ya sake shi,sallama yayi ma Abbah ya koma gida.
dady tunda su ka koma gida kulawa ta musamman su ke ba Irfan shi da mom uncle Ahmad ya so Irfan ɗin ya koma gida amma dady yace ya bari sai zuwa wani lokaci shima a yanzu yana buƙatarshi a kusa da shi,sanin halin da Irfan ɗin yake ciki ne yasa kawai yace to dan ya san yana buƙatar kulawa ta musamman,shi baya da lokacin da zai bashi kulawar data dace.
Mom tun ranar da aka yi rasuwar ta sanar da uncle Jonas,su ma sunyi alhinin mutuwar Noor ɗin musamman data kasance mata ga Irfan dan tun ranar da aka yi Auren su ta kira uncle Jonas ɗin ta sanar da shi.
tun a ranar ya kira dady yayi mashi gaisuwa ya kuma buƙaci da ya ba Abbah da su uncle Ahmad,ɗaya bayan ɗaya yayi masu ta'aziyya ya kuma sanar da su suna nan zuwa nan da sati biyu dan suyi masu ta'aziyya,Alyar da James ma tun a ranar su ka kira su ka yi masu ta'aziyya su ka kuma sake tabbatar masu da suna nan zuwa nan da two week,Sam ne kawai babu wanda ya kira,har kiran shi ya Naeem yayi ya rufe shi da faɗa akan idan yana fushi da dady ai bai kamata yace su da su uncles ɗin su bazai masu ta'aziyya ba,ko ba komai Noor ɗin ai ƴar uwar shi ce kuma matar ƙaninshi,duk wannan faɗan da yayi mashi baisa ya kira su uncle Ahmad ba Abbah kawai da uncle Mustafa da mom ya kira sai uncle mutallab ɗin shima Abbah ne ya bashi wayar lokacin da ya kirashi su uncle Ahmad kuwa ko tambayarsu bai yi ba dan ko Irfan ɗin bai kira ba,dama can su ne favorite ɗin shi dan tun ranar da aka kwantar da kainart da laatifa ta sanar da shi ya kira uncle Mustafa ya mashi ya mai jiki kuma dama time to time suna waya da juna ko ya kira uncle Mustafa ko shi ya kira shi.
dady yayi matuƙar farin ciki da jin labarin za su zo dan harda Sam ɗin uncle Jonas yace mashi a masu zuwan dan yayi alƙawari wannan karon ko me sam ɗin zaiyi sai ya kawoshi Nigeria.
Kwanan mom fatilah biyar a hospital aka sallameta,jikinta da sauƙin sai abun da ba'a rasa ba dan ba ƙaramin taɓata mutuwar tayi ba.
A ranar da aka sallameta Abbah yace Uncle mutallab ya koma gidan shi tunda mom fatilah ta dawo ko ba komai ganinshi a kusa da ita zai gare mata raɗaɗin mutuwar Noor ɗin.
ko da Abbah yace haka baiyi musu ba ya tattara yanashi yanashi ya koma gidan,mom fatilah tayi matuƙar farin ciki da dawowarshi sai dai wani abu da ya ɗaure mata kai tunda ya dawo gidan ya canza mata gaba ɗaya,ko magana tayi mashi sai ya ga damar amsa mata,wani irin fushi yake da ita duk akan wulaƙancin da tayima mom Dan a ganinshi da ba tayi hakan ba da duk hakan bata faru ba.
tsawan kwana huɗu a haka su ke a rana ta biyar ne ƴan uwanta suka zo gidan dan sake dubata da su ka tashi tafiya cewa yayi ta haɗa kayanta ta bisu,da farko tayi tunanin wasa yake sai da taga ya haɗata da takarda ya saketa saki ɗaya ta tabbatar da abun nashi da gaske ne,kuka sosai tasha kamar ranta zai fita tana bashi haƙuri yayinda ƴan uwanta keta zazzaga masifa suna zage zage suna kiranshi da butulu mara tausayi,banza yayi da su bai sauraresu ba sai ma ficewa yayi ya bar masu gidan.
haɗa mata kayanta su kayi suna faɗin wallahi baza ta sake dawowa gidan shi ba har abada,a washe garin ranar ya bar ƙasar ba tare da kowa ya sani ba dan ko Abbah bai sanarmawa ba sai da yayi kwana biyu da tafiya tukun Abbah ya sani .
Sati ɗaya da kwana biyar da rasuwar Noor aka sallamo Kainart daga hospital,uncle Ahmad so yayi daga hospital ɗin su wuce da ita gida ta ƙarasa jinyar a can amma uncle Mustafa yace sam bai san wannan ba,dan yayi rantsuwa kainart ta gama zama da Zaabith har abada kuwa
kusan faɗa abun ya so ya zamar masu,ganin haka ne yasa dady cewa a gidan shi zata zauna harta ƙarasa warkewa,ba hakan su ka so ba musamman uncle Mustafa da a yanzu baya son abunda zaisa tayi nesa da shi,maganar dady ba maganar da za suyi jayayya bace dole tasa suka haƙura, uncle Ahmad da za su tafi ƙin binshi su Ammar su ka yi suma sunfi son zama da kakan nasu.
bai hanasu ba ya tafi ya barsu.
Kainart tunda ta koma gidan dady take samun kulawa ta musamman daga mom da laatifa yumnah da Fa'iza ma ba'a barsu a baya ba,motsi kaɗan za tayi sai sunji me ke damunta,hakan ba ƙaramin daɗi yake mata ba duk sai ta nemi damuwarta ta rasa sai dai duk lokacin da ta tuna abunda Zaabith ɗin yayi mata sai duk taji damuwa ta mamayeta,fahimtar hakan ne yasa Laatifa kullum take cikin yi mata abunda zai ɗauke mata tunaninshi,Dr fawar har gida ya zo ya gaishe da ita, balqis ma har gidan ta zo wurin yayarta daga nan ta sake duba jikin kainart ɗin,duk bayan ƴan kwanaki tana zuwa wurin yayar tata bayan nan kullun sai sunyi waya,kullum cikin ba Laatifa haƙuri take kan abunda dady yayi mata da roƙwanta akan ta ba Momy haƙuri ta dawo gida.
babu irin haƙurin da Laatifa da mom ba su ba mom maimunatu akan tayi haƙuri ta koma gidanta amma tace sam bazata koma ba suma bar ɓata bakinsu, bakomai yasa taƙi haƙura ba sai tun ranar data tafi ko kiranta uncle Hashim bai taɓa yi ba ko yaje gidan su hakan yasa take ganin baya da buƙatarta ne sai dai abunda bata sani ba yana fushi da ita ne saboda nuna halin ko in kula da tayi da balqis a ranar da zata bar gidan da balqis ta suma.
Mom tunda ta dawo gida ta fahimce Nainarh na cikin damuwa,janta ta dunga yi a jiki duk dan ta faɗa mata abunda ke damunta amma sai tace mata bakomai,ƙyaleta mom tayi ba dan ta yarda da babu komai ba.

*UNITED STATE❤*
*Las Vegas (Nevada)*


A hankali Aunty Sophia ta turo ƙofar ɗakin ta shigo a zaune Nailarh take saman sofa dake can gaban window ɗakin,wayarta ce a hannunta tana opreting.
da mamaki Aunty Sophia ke kallonta harta ƙarasa ciki
“baby lafiya ki ke zaune har yanzu,ko dai kin manta da zuwa airport ɗin ne??” Aunty Sophia ta faɗa tana tsareta da ido dan tayi mamakin rashin shirin nata.
“ban manta ba,kawai bana jin zan je su Naoh kawai suje su ɗaukota” zama Aunty Sophia tayi kusa da ita
“baby wai lafiya ki ke kuwa kwana biyu,me yasa ki ke ma momyn ki haka,ko kiranki tayi a waya baki son picking kuma ke baki kiranta,yanzu ta kira tace zata dawo kince baza kije ɗaukota ba bayan duk tayi tafiya ke ke zuwa ɗaukota??” tunda Aunty Sophia ta fara magana ta ya mutse fuska,gaba ɗaya Nailarh ta sauya ma mahaifiyarta bata san kiranta idan ta kira bata picking,kullum Aunty Sophia cikin nuna mata hakan bai dace ba take amma abun ma nata sai ƙara gaba yake.
“idan wani abun tayi maki ba fushi ya kamata kiyi da ita ba,bayan nama san babu abunda tayi maki kawai kin ɗauki wani hali ne wanda bai dace ba,Please Nailarh ki daina hakan ba mai kyau bane ita mahaifiyarki ce”
“ni ba fushi nake da ita ba,kawai bana sonta ne a kusa dani” da mugun mamaki Aunty Sophia ke kallon Nailarh jin abunda ta faɗa
“anya baby kin san me ki ke faɗa kuwa?”
“da gaske nake Aunty Sophia har cikin raina bana son ganinta a kusa da ni,haushi ma nake ji idan na tuna da ita”
with a shock take kallonta rasa me ma za tace mata tayi she became speechless,Aunty Sophia bata gama fita daga mamakin da Nailarh tasa ta ba ta su ka ji an turo ƙofar ɗakin,da sauri Nailarh ta miƙe ta nufi toilet da mamaki Aunty Sophia ta bita da ido.
Mrs Malika ce ta shigo hannunta riƙe da bag ɗinta ta kasa haƙurin halin da Nailarh take mata ne yasa jirginsu na isowa tayi shatan taxi.
a hanzarce ta karaso cikin ɗakin tana kiran sunan Nailarh,murmushi Aunty Sophia tayi tana mata barka da dawowa,a takaice ta amsa mata tana tambayar ina Nailarh take,dan sam bata lura da lokacin da Nailarh ta shiga toilet ba.
“ta shiga toilet ne yanzu zata fito” Aunty Sophia ta faɗa,ok Mrs Malika tace tana nufar sofa da Nailarh ta tashi ta zauna,ficewa Aunty Sophia tayi daga ɗakin, Mrs Malika tun tana jiran fitowar Nailarh har ta gaji ta nufi bakin ƙofar toilet, nocking ƙofar ta shiga yi tana kiran sunanta,tsit taji kamar ma babu kowa a ciki,gajiya tayi da nocking ɗin,tura ƙofar tayi ta shiga a zaune ta hango Nailarh gaban bathtub,ciki ta ƙarasa “baby!” ta kira sunanta saurin tashi Nailarh tayi daga wurin,hannu ta kai da nufin taɓa Nailarh tana faɗin “baby baki san na dawo bane” ɗaga mata kai kawai Nailarh tayi alamar eh,mamaki ne gaba ɗaya ya kama Malika
“amma shi ne ba kije kin ɗauko ni ba?” ɗan ya mutse fuska Nailarh tayi tana faɗin “ban jin dadi ne” yanayin fuskar Malika ne ya sauya “Ayyah sorry,me ke damunki?” malika ta faɗa tana kai hannunta da nufin taɓa Nailarh dan taji temperature ɗin jikinta,saurin kaucewa Nailarh tayi,abun ya ɗan ɗaurema Malika kai ganin kamar Nailarh bata son ta taɓa jikinta,ƙofar fita Nailarh ta nufa bin bayanta Malika tayi,a tsakiyar ɗakin su ka tsaya,kallon Malika Nailarh tayi tana faɗin.
“mom akwai gajiya a tare da ke,You need to have some rest,ki tafi zan zo na sameki”
“baby kamar ba kiyi farin ciki da dawowata ba ko?”
“am very happy Momy just am not feeling better”
“ok,Amma mi yasa nake kiranki baki picking”
“please Momy kina buƙatar hutu,ki bari zuwa anjima sai muyi maganar” kallonta Mrs Malika take ba tare da tace komai ba, lamarin ne ke matuƙar bata mamaki,ta kasa gane me Nailar take nufi da wannan halin,ita dai a iya saninta ta san bata mata wani laifi da zaisa ta gujeta ba.
“baby ko dai nayi maki wani abun ne ba tare da na sani ba?”
“babu abunda ki ka man”
“to me yasa nake ganin kamar kina guduna,tsawan fa two month kenan bama tare amma kamar ba kiyi kewata ba”
“momy nayi kewarki mana”
“idan har da gaske ki ke to ki barni a nan na fi buƙatar kasancewa tare dake sama da komai” ta faɗa fuska a marairaice.
bed Nailarh ta nufa ta zauna bata san ya za tayi mata ba ta gane ko ganinta ba ta son yi.
bed ɗin Malika ta nufa,zama tayi kusa da Nailarh,hannunta ta kai saman hannun rigar dake jikin Nailarh,saurin ture hannunta Nailarh tayi tana faɗin “please mom,bana so” ran Malika ne ya ɓaci har bata san lokacin data rufe Nailarh da faɗa ba abunda bata taɓa mata ba kenan.
kuka Nailarh ta fashe mata da shi,hakan ba ƙaramin ƙara ɓata ran Malika yayi ba,ganin idan ta biyema Nailarh zata iya mata wani abun ne yasa ta fice daga ɗakin rai a ɓace.
Tana fita Aunty Sophia na shigowa kusan duk abunda ya faru a kunenta,rufe Nailarh da faɗa itama tayi dan me zatama Malika haka.
“Aunty Sophi bana sonta,na tsaneta,bana son taɓa jikina da take”
“kar na sake jin bakin ki ya sake furta baki sonta,karki manta Aure za ku yi nan da two weeks”
“a iya sanina baki son abunda take man,me yasa zaki sauya yanzu Aunty Sophia”
“ke ce ki ka sauya Nailarh,ki sani momynki na sonki,kuma wannan abun ba wani abu ba ne,nima ada ban fahimci son da take maki bane yasa bana so”
“ni dai bana sonta kuma bazan taɓa Aurenta ba”
“waza ki Aura kenan?” Aunty Sophia ta faɗa da sigar tambaya
“CEO ni shi nake so ba ita ba” wani irin kallo Aunty Sophia tayi mata “kin san kuwa abunda ki ke faɗa baby,mutumin da yayi sanadiyar kwanciyarki hospital shi ki ke so?” jinjina mata kai Nailarh “ina matuƙar son shi,ji nake bazan iya rayuwa ba idan babu shi” jin jina kai Aunty Sophia ta shiga yi,lamarin Nailarh ya fara bata tsoro,idan ba neman tashin hankali da momynta take ba taya zata faɗi haka.
lallashinta ta shiga yi tana nuna mata hakan ba mai yiwuwa ba ne,amma sam Nailarh ta kasa fahimtar ta.
Aunty Sophia ba su sake sanin abun na Nailarh da gaske ba ne sai data fara wasan ɓuya da momynta,duk wata hanya data san zata haɗata da ita tayi blocking,Malika tun tana ɓoye damuwarta harta kasa ga wata muguwar sha'awar Nailarh dake ɗawainiya da ita gashi Nailarh ta ɗauki karan tsana ta ɗora mata.
karshe data kasa haƙura mamayar Nailarh tayi cikin dare ai kuwa ranar taga tashin hankali dan sosai Nailarh ta nuna tsanar da tayi mata a fili.
hakan kuwa baƙaramin ɓata ran Malika yayi ba har ya kaita da marin Nailarh abunda tunda uwarta ta haifeta wani bai taɓa mata ba,sosai saɓani ya shiga tsakaninsu Nailarh na iƙirarin komai Malika za tayi sai dai tayi amma Aurenta da CEO kamar tayi ta gama kuma sai ta bar mata gidan a yau.
murmushin Malika ta saki tana faɗin “yau na sake tabbatar da cewa Nailarh baki san ko wacece Malika ba,amma you will see the other side of me,zan tabbatar maki da ko ni wacece,you will regret” Malika ta faɗa tana gyaɗa kai.
wani shegen kallon Nailarh ta mata “i don't care about ko wacece ke,na riga na yanke hukunci bani babu ke,komai za kiyi Malika kin daɗe ba kiyi ba” Nailarh ta faɗa tana nufar dressing room ɗinta Dan ta rantse yau komai zai faru saita bar gidan.
A masifance Malika ta figota gaba ɗaya ta kifa ƙasa ƙugunta da kanta su ka bugu da ƙasa,ƙara ta saki ta azabar zafi,Aunty Sophia ce ta faɗo ɗakin hankali a tashe,luna ke sanar da ita abunda ke faruwa da Malika da Nailarh.
Malika bata damu da halin da take ciki ba ta fara magana.
“ke har kin isa kici Amanata, idanma bacci ki ke to ki farka,ki sani duk wani gata dana baki da ji dake da nake inayi ne dan biyan ɓuƙatata bawai dan kin kai matsayin nayi maki hakan ba,ke ba kowa bace a wurina face abun biyan buƙatata,ki sani akan biyan buƙatata zan iya kawar da duk wanda yace zai kawo man cikas,dan haka ke baki isa lokaci ɗaya ki sauya man ba,Aure tsakani na dake kamar anyi shi an gama,kuma shi wannan mutumin da ki ke magana ki sani daga yau babuke babu shi,idan kuma kin musa ki sani zan iya kawar dashi daga doran duniya?”
tashi Nailarh tayi daga ƙasa tana kallon Malika hawaye kwance cikin idanunta
“malika ban damu da abunda za kiyi ba amma ki sani muddin ki ka kashe shi nima saina kashe ki❗”
dariya Malika ta kwashe da ita “haka ki ka ce ko?”
“haka nace Malika,kuma a yau ba sai gobe ba zan bar maki gidan ki” jin jina kai Malika tayi “big mistake Nailarh” harara Nailarh ta watsa mata tana juyawa zata shiga dressing room ɗinta.
saurin riƙo hannunta Aunty Sophia tayi “Nailarh kina hauka ne,da mahaifiyar taki ke ke faɗa akan mutumin da baki san ko shi waye ba,ba kuma kisan dalilin da yasa ya shiga rayuwarki ba har ki ke iƙirarin zaki bar gida, kuskurene wannan Nailarh idan kin bar gidan ina zaki,kaf duniya baki da kowa bayan mahaifiyar ki,idan wani abu ke damunki tun wuri ki dawo hayyacinki”
“ban damu da dalilinshi na shiga rayuwata ba,ko shi waye iya abunda na sani ina sonshi ko da kuwa da wata manufa ya shiga rayuwata”
“baby wannan hauka ne, mahaifiyar ki ba abar da zaki wulaƙanta bace”
“Aunty Sophia wannan matar ko zata kashe ni bazan mata abunda take so ba,na tsaneta kima bar ɓata bakinki” tana gama faɗa ta shige dressing room ɗin.
kallon Mrs Malika Aunty Sophia tayi harta buɗe baki za ta yi magana Malika tayi saurin ɗaga mata hannu
“ba sai kince komai ba Sophia dole

Please Login or Register in order to submit comment