Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu bana da wata matsala,dan Allah kayi haƙuri”
kallonta yayi yana girgiza mata kai “karki damu Zulaihart ni ba fushi nake dake ba,kawai dai banji daɗin abunda ki ka yi ba,a ranar da ki ka nuna baki amince ba kasa jurar rasa ɗanki tayi har hakan ya haddasa tashin ciwanta,da ƙyar da taimakon likitoci ta dawo hayyacinta,na san ganin da gaske ta rasa shi ne ya sa tayi ƙoƙarin kashe kanta” mom bata san ciwan Noor ya tashi ba sai yanzu da dady yake faɗa mata
“tunda har ki ka fahimci yarinyar nan tana son ɗanki kuma shima yana sonta da haƙuri ki ka yi ki ka bisu da Adu'a,ko kin manta wahalar da mu ka sha kafin mu samu peace of mind na zama da juna,ke shaidace akan halin da mutum yake shiga idan yaga za'a rabashi da wanda yake so”
“kayi haƙuri in sha Allah bazan sake maimaita kuskure irin haka ba,kayi haƙuri”
“ba komai ya wuce,Allah ya yafe mana baki ɗaya”
“Ameen,yanzu a wane hali Noor ɗin take ciki”
“har yanzu likitoci ne akanta”
“Allah ya bata lafiya,amma ina son ganin mutallab idan ka amince man,ina so na bashi haƙurin halin dana jefa ƴarsa”
“karki damu,yanzu yana tare da Noor ɗin”
“shikenan” ta faɗa tana gyaɗa mashi kai.
suna a nan zaune sai ga uncle Ahmad tare da mom salima,suna gaba yayinda securitys ɗin su ke take masu baya,banda tsiyayar da hawaye babu abunda mom salima take,tun lokacin da labarin abunda zaabith ɗin ya aikata ya riske su take kuka,shi kanshi uncle Ahmad ya shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa.
kallon ɗaya zaka masu ka shaida rashin kwanciyar hankalin da su ke ciki,har in da su dady su ke suka ƙaraso, gaisawa uncle Ahmad su ka yi dady tukun su ka gaisa da mom,mom salima kuwa kukan da take ma ya ƙi bari ta gaishe da shi,burinta kawai taga a wane kainart ɗin take ciki.
Ward ɗin su ka nufa su ka bar securitys ɗin a waje,dady ne ya tura ƙofar ɗakin ya shiga uncle Ahmad na bayanshi tare da su mom,bakin su ɗauke da sallama su ka shiga,a hanzarce mom salima ta nufi bed ɗin da kainart ɗin take kwance tana fashewa da wani irin kuka ganin halin da kainart ɗin take ciki,lokaci ɗaya ta dawo abunda tausayi.
kallo ɗaya mom Maryam tayi masu ta ɗauke kai,har ya mai jiki uncle Ahmad yayi mata amma ko kallon arziƙi bai samu daga gareta ba,babu wanda yaji daɗin abunda ta yi, girgiza kai kawai uncle Ahmad ɗin yayi dama yasan dole hakan zata faru,tashin hankalin shi ma uncle Mustafa,ya san dole ya ɗauki mummunan mataki akan zaabith wanda bazai so hakan ba.
gaishe da shi laatifa tayi,da kulawa ya amsa mata yana kallon Ammar da Aman dake bacci a jikinta.
kuka sosai mom salima take hannunta riƙe da hannun kainart ɗin.
sun ɗan jima a ɗakin,kafin uncle Ahmad ya matsala gaban gadon yayi ma kainart ɗin Adu'a,kallon mom salima dake zaune gefen ƙafafun kainart ɗin yayi “zaki tsaya nan ko?” ɗaga mashi kai tayi alamar Eh,wani kallo mom Maryam ta watsa masu tana kauda kai,ji take kamar ta sauke baƙin cikin da take ciki a kan su dan a ganinta da sa hannun su a abunda zaabith ɗin ya aikata,sallama uncle Ahmad ɗin yayi masu ya fice shi da dady,sai da su ka fita yake tambayar dady ta yarda akai kainart ɗin ta zo gidanshi dan gaba ɗayansu babu wanda ya san da fitar ta.
*Lokacin da motar driver da ya ɗaukota daga aso Villa ta iso Estate ɗin,da zummar zuwa gidan su ta baro gidan sai data tuna halin da iyayen nata za su shiga musamman mahaifinta yasa tace su ajiyeta gidan big dady kawai,ko da su ka ajiyeta sai da su ka ga shigarta gidan tukun su ka juya duk da sun so ta bari su kaita asibiti amma taƙi,abunda ya tada hankalin securitys da driver daya ɗauko ta tun a villa take bleeding,motar data shigo ma duk ta ɓata ta, lokacin data shiga gidan babu kowa gidan yayi tsit,a bakin ƙofar ɗakin mom ta tsaya tana nocking cike da ƙarfin hali,a lokacin laatifa ce ta buɗe mata ƙofa,baƙaramin tsorata laatifa tayi ba ganinta a irin wannan lokacin,ko da taga halin da take ciki ga jinin dake bin ƙasanta bata san lokacin data fasa ƙara wacce tayi sanadiyar farkawar mutane da dama na gidan,ko kafin mutanen gidan su ƙaraso parlorn tuni kainart ɗin ta yanke jiki ta faɗi,babu wanda hankalinshi bai tashi ba da ganin halin da kainart ɗin take ciki musamman laatifa,a cikin daren su ka nufi hospital da ita,suna zuwa babu ɓata lokaci likitoci su ka duƙufa akanta,sun shafe sama da awa uku akanta kafin su ka samu nasarar tsayar da jinin dake zuba daga jikinta,tunda aka shiga da ita Emergency ward laatifa ke kuka kamar ranta zai fita,ko da Dr Lelarh ya sanar da su suna buƙatar jinin da za'a ƙara mata saboda ta zubar da jini sosai cewa laatifa tayi a ɗebi nata amma Dr Lelarh yace A'a saboda halin da laatifa ke ciki,dady ne yace su ɗibi nashi in dai zaiyi dai dai dana kainart ɗin duk da Dr Lelarh ya nuna ƙin amincewa da hakan akan za su ƙara mata wanda su ke dashi saboda Emergency patient,ganin dady ya nace ne yasa su ka amince za su ɗiba,cikin ikwana Allah kuwa suna aunawa jinin na su ya zo dai dai,babu ɓata lokaci su ka ɗibi jinin nashi leda ɗaya duk da ba wai zai ishi kainart ɗin ba,dan sosai ta zubar da jini.
hankali su dady baiƙara tashi ba sai da Dr Lelarh ya sanar da su Kainart ɗin tayi miscarriage na cikin dake jikinta har sai da su ka yi mata aiki a mahaifa saboda raunatar da mahaifartata tayi wanda su ke ganin ba lallai ta sake haihuwa ba,hankalin su yayi matuƙar tashi da jin abunda Dr Lelarh yace,duk yanda dady ya kai da durewa sai da ya zubar mata da ƙwalla,yayi matuƙar tausaya mata,bai taɓa jin haushin wani abu ba kamar yanda yaji haushin zaabith a lokacin da Dr Lelarh ya sanar da shi zubewar cikin na da alaƙa da mijinta saboda ya kusanceta taƙarfi da tsiya.
tun da asuba dady ya kira Abbah ya sanar da shi abunda ke faruwa dan shi ka ɗai ne zai iya tausar uncle mustafa,dan yasan muddin ya sani zaabith ya shiga uku,sai dai tun kafin Abbah ya sanar da shi su Ammar su ka kirashi da wayar kainart ɗin su ka sanar da shi abunda ke faruwa saboda tashin da su ka yi ba su ga Momyn ta su ba da kuma jinin da su ka gani tun daga ɗakinta har zuwa ɗakin dadyn na su, shiyyasa Abbah da dady su ka yi mamakin ta yarda akai ya sani dan Abbah bai kaida sanar dashi ba,ya bari a sai ya koma gida ya kirashi.
“ban san mi ya shiga kan zaabith ba da har ya aikata mata haka”
“kayi haƙuri yaya lamarin zaabith sai Adu'a,ya ma zo kuwa?”
“ya zo” dady ya bashi amsa
“mustafa fa,ya san abunda ke faruwa?” uncle Ahmad ya faɗa
“tun da har kaga matarshi ai ka san ya sani,dalilin zuwan shi ma ne yasa zaabith ɗin ya fice har yanzu bai dawo ba”
dafe kai Uncle Ahmad yayi “ya Allah,dan Allah yaya ka tayani ba Mustapha haƙuri,ina tsoron matakin da zai ɗauka akan zaabith,ka san yanda yake da ƴaƴanshi bai haɗasu da komai ba”
“Ahmad mi zance ma Mustapha,kafi kowa sanin baƙar zuciyar shi, zaabith yayi kuskure da har bai yi tunani ba wajen aikata mata haka ba”
“haka ne yaya,amma yana jin maganarka fiye da kowa”
“duk da haka ban isa na hanashi ɗaukar mataki akan zaabith ba,ya riga da ya aikata kuskuren da ni da kaina zan iya hukuntashi,naji taikaici da baƙin cikin abunda ya aikata,kuma harda laifinka Ahmad babu yarda za'ayi kace baka san abunda ke faruwa a tsakanin su ba,dan wannan abun da yayi mata ya nuna cewa dama can akwai matsala a tsakanin su,kuma gidan gwamnati ka ke zaune in da yafi ko ina ƴan sa ido, motsinka kaɗan ake jira, ko da baka sani ba dole wani daga cikin ma'aikatan gidan ya sanar da kai”
“wallahi yaya kaji na rantse ban sani ba,ko yanzu kiran Ja'afar ( VIP ɗin shi mijin Aunty Safeenah ) da Ubaid ne yasa na san abunda ke faruwa,amma wallahi yaya ban sani ba”
“har Ja'afar ya sani amma kai baka sani ba?” dady ya faɗa yana kallonshi
“shima a labaran safiya ya gani,nayi mamakin da ma'aikatan gidan su ka zaɓi su sanar ma duniya sama dani ubansa,yaja a gari sai zagina mutane su ke,haka shugaban jam'iyya ya nuna ɓacin ranshi matuƙa akan abun,dan Allah yaya ka tayani shawo kan Mustapha nafi jinshi sama da kowa yaya”
“kayi haƙuri Ahmad bazan hana Mustapha hukunta Zaabith ba,Noor na nan kwance itama ba lafiya” dady na faɗan haka yayi gaba,iska mai zafi uncle Ahmad ya fesar,ba komai yasa dady yayi mashi haka ba sai dan ya fahimci zaabith yayi kuskure dan yaga kamar yana son ya shigo da son kai a lamarin,kuma yasan dole yasan abunda ke faruwa,shi kanshi bazai so uncle Mustafa ya hukunta Zaabith ba dan yasan bazai taɓa mashi da kyau ba.
babu yanda ya iya,dama dady yake ganin zai iya shawo kan uncle Mustafa saboda girmama maganar dadyn da suke,amma tunda har dady yace bazai sa baki ba ya san akwai gagarumar matsala.
bin bayan dady yayi har zuwa Emergency ward ɗin da Noor take kwance,lokacin da su ka isa ba su samu su mamy da mom fatilah ba,ba komai yasa ba su gansu ba sai korar da uncle mutallab yayi ma mom fatilah ba tare da ya bari taga halin da Noor ɗin take ciki ba,Dan a ganin shi duk ita tayi causing komai, shiyyasa ya koreta dan baya son ganinta a kusa da su.
lokacin da su ka shiga Emergency ward ɗin wanda Dr Lelarh ne yayi masu jagora,kowannan su sanye yake da surgical gown sun rufe fuskokinsu da mask, Uncle mutallab kawai su ka samu tare da Noor ɗin har yanzu bata san wa ke kanta ba, allurar da yayi mata ko minti biyu bata yiba allurar ta saketa,banda kiran sunan Irfan babu abunda take, bakinta kawai ne ke mosti ba sauti,tun ɗazu yake kiran Irfan Amma baya samun shi, Allurar bacci yake mata amma data fara bacci zata farka hakan yasa ba su fitar da ita daga Emergency ward ɗin ba.
bakin bed ɗin su ka ƙarasa,hannu su ka ba uncle mutallab ɗin su ka gaisa,kafin su ka matsa kusa da Noor ɗin,tausayin halin da Noor ɗin take ciki ne ya rufe su, Adu'a dady ya shiga karantowa yana tofa mata suna amsawa da Ameen har ya kammala.
Kallon uncle mutallab da ya dawo Abun tausayi dady yayi,gaba ɗaya ya koma wani iri kamar bashi ba,tun ranar juma'a da ciwan Noor ɗin ya tashi hankalin shi yake ba'a kwance ba,dafa kafaɗarshi dady yayi “kayi haƙuri mutallab in sha Allah zata samu lafiya”
“yaya jikin nata ne kwata kwata babu sauƙi,gubar ba ƙaramin illa tayi mata ba,yaya bana tunanin Noor zata tashi” ya faɗa hawayen dake kwance cikin idonshi na bin cheek ɗin sa,wani tausayin shi ne ya rufe su,girgiza mashi kai dady yayi “ka daina faɗan haka,ciwo ba mutuwa ba ne in sh Allah zata samu sauƙi, Adu'a ya kamata ka yi mata” gyaɗa kai yayi yana sa hannu ya goge hawayen dake zuba daga idanunshi,kallon Noor ɗin dady yayi “me take faɗa ne bakin ta ke motsi?”
“tunda ta farfaɗo take kiran sunan Irfan,na kirashi a waya amma ban sameshi ba”
girgiza kai dady yayi,wani mugun tausayin Noor na sake shigar sa,ya rasa wane irin so take ma Irfan haka.
“amma ka kira Waseef?” dady ya faɗa
“ai da ka kira shi na san dole suna tare” ajiyar zuciya uncle Ahmad ya sauke “ban san wane irin so suke ma junan su ba,shi kanshi Irfan kwata kwata babu kwanciyar hankali a tare dashi tun ranar da mahaifiyar shi tace bata amince ba,hatta abinci sai nayi mashi da gaske yake ci,ya Tahir dan Allah ka shawo kan barrister tayi haƙuri ta janye furincinta,tabar yaran nan suyi Aure,duba kaga halin da su ka jefa kan su”
dady duk sai yaji wani iri,dama ya san yanzu kowa laifin mom zai gani “karka damu Ahmad ba tun yau ba ta haƙura ta janye ƙudurinta,fatan mu yanzu Allah ya ba Nurjahan ɗin lafiya,in sha Allah data samu sauƙi za'a ɗaura Auren bama sai lokacin da Abbah yace ba”
“A'a yaya a ɗaura yau ko gobe tunda ta amince, lokacin da zata samu sauƙi sai ayi bikin kawai,ko ya kace” ya faɗa yana kallon su
“duk yanda ku ka ce haka za'ayi”
“in sha Allah daga nan gida zan wuce wurin Abbah zan sanar da shi halin da ake ciki,zuwa gobe a masallaci sai a ɗaura Auren lokacin da zata samu sauƙi sai ayi bikin kawai”
“hakan yayi,nima yanzu daga nan gidan zan tafi amma bazan shiga wurin Abbah ba,tuna cikin dare dana fito ban koma ba”
“shikenan sai mu tafi tare”
uncle mutallab dai na jin su bai sa masu baki ba amma deep down ya fisu farin ciki da wannan hukuncin da uncle Ahmad ya yanke,yana fatan Noor idan taji burinta ya cika hakan ya taimaka ma lafiyarta.
sake duba jikin Noor ɗin su ka yi tukun su ka yima uncle mutallab ɗin sallama akan dady zai sake dawowa anjima.
A tare su ka fice daga ward ɗin zuwa parking lot,a bakin gate su ka samu ƴan jarida jiran fitowar uncle Ahmad ɗin kawai su ke.
Motocin su na fitowa su kayi masu rumfa,uncle Ahmad su ka shiga watsa ma tambayoyi duk da kasancewar motar da tinted,umarni yaba driver da su wuce kawai yana mai mamakin munafukin daya sanar da su yana hospital ɗin,duk dan kar asan da zuwanshi ya sa bai fito da motoci da yawa ba.
wani irin farin ciki uncle mutallab ya tsinci kanshi,bakinshi ya kai saitin kunnen Noor ya raɗa mata kaf maganganu da su dady su ka tattauna,wasu siraran hawaye ne su ka shiga fitowa daga idonta,hakan ya tabbatar mashi da tayi farin ciki da hukuncin na su.

*ESTATE*

Yumnah lokacin da su ka bar hospital su ka koma gidan akan za su koma hospital ɗin zuwa anjima,suna shiga gidan da azamarta ta nufi bedroom ɗin su dan ganin a wane hali take ciki,mi ya hanata zuwa hospital ɗin ga ɗokin zuwa prison da za su yi wanda shine maƙasudin dawowarta gidan.
A lokacin da ta shiga bedroom ɗin wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi,da mamakin take kallon ɗakin da ya dawo kamar anyi dambe a cikin shi,gaba ɗaya an sauya mashi kamanni,ga pillows nan da blanket da bedsheet a ƙasa hatta matress ɗin su ba dai dai take ba,teddys ɗin su har bakin ƙofar dressing room ɗin su,tunani yumnah ta fara anya lafiya Nainarh tayi ma ɗakin haka,kai tsaye bata kawo ma ranta bata gidan ba,tunani ta fara ko tana toilet,hakan ya sata rage kayan jikinta, a bakin bed ta zauna zaman jiran fitowarta itama dan ta watsa ruwa tana kuma san taji lafiya take tayi ma ɗakin su haka.
yumnah tun tana zaman jiran Nainarh harta fara gajiya,tashi tayi ta nufi bakin ƙofar toilet ɗin,nocking tayi tana kiran sunanta,tayi hakan kusan sau biyar amma shiru babu alamar Nainarh na ciki,a hankali ta tura ƙofar toilet ɗin dan ta fara zargin kamar ba kowa a ciki,kamar yarda tayi zargi toilet ɗin ba kowa babu alamun wani ya shige sa a lokacin.
ficewa tayi daga toilet ɗin ba tare da tayi wankan ba ta koma cikin bedroom,wayarta ta ɗauka tana nufar dressing room ɗin su,nan taga abunda ya ɗaure mata kai,nan ma anyi mashi kaca kaca har gara ma bedroom ɗin su,kaf kayan su dake cikin clothset ɗin su an watso su hata trolleys ɗin su dake can saman clothset ɗin an zazzage kayan dake ciki anyi jifa da su,takalman su da jakunkunan su gaba ɗaya su ne a tsakar ɗakin anyi jifa da su, dressing mirror ɗin su ma abun ba kyan gani,hata shopping ɗin da su ka yima momyn Nainarh an zazzage su ƙasa, laptop ɗin su ma ga su nan a ƙasa,lafiya Nainarh take kuwa⁉️
ta faɗa,ficewa tayi daga dressing room ɗin ta koma bedroom,hijab ɗin data cire ta ɗauka ta zura a jikinta,ficewa tayi daga bedroom ɗin tana dialing number Nainarh, ringing wayar ta shiga yi,amma har kiran ya katse bata yi picking ba,wani kiran ta sake tana nufar ɗayan bedroom ɗin dake kusa da nasu,nan ma bata nan kuma har lokacin ba tayi picking call ɗin ba, hankalinta ne ya fara tashi,to ina Nainarh ta tafi, bedroom ɗin mom ta nufa duk da ta san zaiyi wuya ace tan can.
babu wani ɗaki yumnah da bata shiga ba neman Nainarh amma bata ganta ba,har garden sai da taje ko tana can amma bata can kuma har time ɗin tana kiranta a waya bata picking.
part ɗin masu aikin su ta nufa,bedroom ɗin Ishrat tayi nocking,buɗe mata ƙofa Ishrat ɗin tayi sai wani lumshe ido take alamar daga bacci take
“ina Nainarh take?” shine tambayar da yumnah ta jefa mata
“ba kuna tare ba Aunty yumnah?” wani kallo yumnah ta watsa mata
“idan muna tare zan tambaye ki ne,Ina ta tafi?”
“tunda tayi breakfast na sanar da ita kuna hospital kin ce ta kiraki ta fice daga gidan nan,nama yi tunanin hospital ɗin ta nufa”
“ta fice daga gidan?” yumnah ta faɗa “eh” Ishrat ɗin ta bata amsa “to kenan waye ya shiga ɗakin mu!?” faɗuwa gaban Ishrat yayi jin abunda yumnah tace “wallahi ban sani ba,mi ya faru?” Ishrat ɗin ta faɗa tana kallon yumnah
“nainarh bata gidan babu kowa sai ku,waye ya shiga ɗakin mu ya hargitsa mana shi⁉️”
“wallahi ban sani ba tunda na gama aiki na dawo ɗaki,ban san waye ya shiga ba,kuma da hannuna na sake gyara ɗakin bayan Aunty Nainarh ta fita”
jinjina kai yumnah tayi ta juya,bin bayanta Ishrat ɗin tayi, a parlor su ka dakata
“ki kira su muneerat ku gyara shi yanzu” da to Ishrat ɗin ta amsa mata,ita kuma ficewa tayi daga gidan zuwa compound dan ta tambayi securitys ɗin ko sun san inda Nainarh taje.
tana isa compound ɗin motocin ya Naeem na shigowa gidan,dakatawa tayi har su ka gama dai daita parking, securitys ɗin shi ne su ka shiga fitowa ɗaya bayan ɗaya,kafin su ka buɗe back seat ɗin motar ya Naeem ɗin.
fitowa ya Naeem ɗin yayi, zagayawa yayi da kanshi ya buɗe ɗayan side ɗin motan,hannunshi ya miƙa mata ta kama ta fito,yumnah na daga can tsaye tana kallon su,da gudu ta nufo parking space ɗin ganin Nainarh tare da ya Naeem wacce kallo ɗaya zaka mata ka fahimci bata hayyacinta,jikita sai wani rawa yake kamar wacce sanyi ke kaɗawa.
“second father daga ina ku ke haka,Nainarh lafiya ki ke?” yumnah ta faɗa lokacin data ƙaraso in da su ke
“bata jin daɗi ne,matsa” shine kawai abunda ya Naeem ɗin yace mata yana jan hannun Nainarh su ka nufi cikin gidan,bin bayansu yumnah tayi.

*Abunda ya faru lokacin da wannan mutanen su ka rufe motar su Nainarh.*

kamar yaƙi haka su ka shiga sakar ma motar bullet,anguwar ba kowa kamar anyi shara,sauƙin su ɗaya da motar ta kasance bulletproof ce.
tsoro da ƙarar harbi ne yasa Nainarh suma,tunda take bata taɓa tsintar kanta a tashin hankali irin wannan ba,ko lokacin da aka kashe dadynta bata tsorata irin na yau ba.
zufa ce ta ko ina ta shiga keto ma driver,tsabar karfin hali yana a duƙe yake ci gaba da dialing number CM,still tana ringing amma baiyi picking ba, bai gajiya ba haka ya cigaba da aika mashi kira,shi kan shi bai san iya adadin kiran da yayi mishi ba.
gajiya suka yi da harbin motar ganin dai babu alamun glass din zai fashe,gashi so suke su gama abun da ya kawo su ba tare da wani ya gansu ba,ganin dai idan ba wani abun suka yi ba har wani ya zo ya same su a wurin ne yasa majiya karfin da ke cikinsu suka nufi wani katon dutse da ke bakin hanya,kama kama suka yi suka ɗauko dutsen,gadan gadan suka nufi glass din gaban motar za su buga mishi dutsen,sai dai kash Allah maji roƙwan bawansa kafin su aikata hakan karar motar sojoji haɗe da harbi ya cika kunnensu,ba shiri suka yarda dutsen a 360 suka nufi motocin su dake wurin,ko kafin motocin sojojin su ƙaraso sun shige motocin su,key su ka yi ma motocin a 80 suka bar street ɗin,lokacin da su ya Naeem suka karaso sai dai suka hangi motocin su tuni sunyi nisa,mota biyu ta sojojin ta bi bayan motocin su,parking ɗin motocin su suka yi, da sauri ya Naeem ya fito ya nufi motar,back seat ɗin motar ya buɗe, a kasan motar ya ga Nainarh babu alamun numfashi a tare da ita, jijjiga ta ya shiga yana kiran sunanta, wata irin wawiyar ajiyar zuciya driver ya saki jin muryan ya Naeem da sauri ya buɗe driver seat ya fito,jikinshi sharkaf da zufa,hannu biyu ya Naeem yasa ya ciro Nainarh,back seat ɗin motar shi ya nufa da ita,usman ne ya ɗauko mashi ruwa daga cikin mota ya miƙa mashi.
A hannu ya zuba ruwan tukun ya shafa mata a fuska,dogon numfashi taja haɗi da zabura zata fita daga motar,da sauri ya riƙota yana kiran sunanta,saurin kallon fuskarshi tayi “lafiya, mi ya faru,mi yasa ki ka fito daga gida??” da ido kawai ta bishi amma ta kasa amsa mashi tambayoyin da yake mata
“ba nace duk inda zaki ki dunga sanar dani ba,mi yasa ki ka fita ba tare da kin faɗa man ba?” ƙalla ba tace mashi ba,banda bin shi da ido ba bu abunda take,ƙyaleta yayi ganin har lokacin bata dawo hayyacinta ba, drivern ya tambaya daga ina suke da kuma abunda ya faru,kaf ya kwashe komai ya faɗa masa.
jinjina kai kawai ya Naeem ɗin yayi ya shiga back seat ɗin kusa da ita,ganin haka ne yasa kowa shiga motar shi su ka bar wurin,motar da su ka zo driver ya shiga.
ta yarda akai ya Naeem ta san suna wurin,bayan kiran da driver yake mashi dama tun ranar daya kira Nainarh gidan shi yasa mata bididdiƙi a wayarta wanda ke sanar da shi location ɗin da take duk wani motsinta yana sane da shi.
Direct bedroom ɗin su ya nufa da ita,tura ƙofar yayi,ganin su Ishrat na gyaran ɗakin ne yasa shi juyawa ya nufi wanda ke kusa da nasu,har bakin bed ɗin ɗakin ya nufa da ita “ki kwanta ki huta kin ji” ya faɗa,ba tayi mashi musu ba ta cire takalman dake ƙafarta ta hau gadon,ita kanta zata so tayi baccin ko kunnuwanta za su dai jiyo mata ƙarar tashin hankali da tashiga,ficewa yayi daga ɗakin yana faɗin “ina zuwa” zama yumnah tayi kusa da ita “sister Nainarh wai mike damunki,daga ina ku ke haka?” ƙala Nainarh ba tace mata ba sai ma rufe idonta da tayi, zuba mata ido yumnah tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.
Ya Naeem ne ya dawo hannunshi riƙe da magani da robar ruwa,bakin bed ɗin ya ƙaraso kiran sunanta yayi, a hankali ta buɗe idonta “tashi ki sha wannan maganin sai ki kwanta” tashi tayi kamar yanda yace,amsar maganin tayi da ruwan,miƙa mashi robar tayi bayan ta sha
“to koma ki kwanta,Auta tashi za ki yi ki bata wuri tana buƙatar hutu” to yumnah tace
a tare su ka fice daga ɗakin, kasa haƙuri tayi har sai da ta sake tambayarshi mi ya samu Nainarh daga ina su ke,duk tabi ta damu da halin da Nainarh take ciki
“ki kwantar hankalinki babu abunda ya sameta,bata jin daɗi ne amma in sha Allah data farka zata dawo dai dai”
“Allah ya sa haka” kawai tace ba wai dan ta yarda da bakomai ɗin da yace ba, bedroom ɗin su ta nufa dan ta watsa ruwa.
Nainarh da shan maganinta ko two minutes ba ta yi ba bacci yayi awan gaba da ita.
Dady lokacin ɗaya shigo gidan ba ƙaramin tashi hankalinshi yayi ba da yayi arba da motar da su Nainarh su ka fita.
A main parlor yaci karo da ya Naeem,hankali a tashe yake tambayarshi lafiya dan yaga yaranshi a kusa da motar,bai ɓoye mashi komai ba ya sanar dashi abunda ya faru
“innalillahi wa Innah ilaihi raji'un,amma su waye su,miye haɗin su da ita da

Please Login or Register in order to submit comment