Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tare da tace mata komai ba itama Nailarh ɗauke idonta tayi, ficewa Nurse ɗin tayi,bayan kamar 2 minutes da fitarta wata Nurse ta shigo ɗauke da gown da body lotion cikin ɗakin ta nufo,gaishe da Aunty Sophia tayi kafin ta kalli Nailarh,ya jiki ta fara tambayarta kafin tace “It's time to take a bath ma'am” Nailarh looked at her before she looked away, da sauri Aunty Sophia tace “ok, bring the gown and I will help her to take a bath, thank you” ba tayi musu ba ta bata gown ɗin,zama tayi kan chair dake gaban bed ɗin, taimaka ma Nailarh Aunty Sophia tayi zuwa toilet,Sosai toilet ɗin ya haɗu kamar a gida,duk wani abu da za su buƙata akwai a ciki,ruwa Aunty Sophia ta haɗa mata,sanin halin Nailarh da koda tana lafiya ba wanka take da kanta bane yasa Aunty Sophia ta taimaka mata tayi,wani iri Aunty Sophia taji wannan shine the first time tayi ma Nailarh wanka bayan ta girma,hawaye ne su ka taru a idanunts lokacin da ta tuna yarintar Nailarh,da sauri tasa hannu ta goge kafin Nailarh ta gani,shaf shaf ta taimaka mata tayi wanka har ta canza mata rigar jikinta ta shafa mata lotion,ficewa su ka yi zuwa ɗakin,Nurse ɗin kaɗai su ka samu su luna sun fice da alama wajen Mrs Malika su ka nufa, taimaka mata tayi ta koma saman bed,kwanciya tayi,duvet Aunty Sophia ta ja mata ta rufe mata rabin jikinta,lumshe ido tayi kamar mai bacci,gown ɗin Nailarh ta cire Nurse ɗin ta kwashe ta fice.
*ABUJA NIGERIA*

gaba ɗayan su ne a bedroom ɗin mom ya Naeem,ya Adnan sai Irfan,mom na daga zaune gefen bed ɗin ta yayin da ya Adnan ke zaune saman stool a gaban mirror sai ya Naeem dake zaune kan sofa shida Irfan,tunda su ka fara magana kan Auren shi da Noor ƙala baice masu ba kanshi na ƙasa,ɗaya bayan ɗaya yake sauraren su
“idan har ba so ka ke kaga ɓacin raina ba,ka ƙyale masu ƴarsu kawai kaje ka nemi wata,Allah zai baka wacce ta fi ta” mom ta faɗa tana kallon Irfan ɗin
“akwai ƙanwar Usman abokin aikina yarinyar tana da hankali ga tarbiyya,Ni zan mashi magana sai kaje ka ganta idan tayi maka shikenan a gidan shi take zaune” ya Naeem ya faɗa yana kallon Irfan ɗin
“idan ba tai maka ba ma ga Kairiyyah nan ɗiyar Aunty Adama sai ka nemeta,tama fi Noor natsuwa da komai,kuma Mahaifinta bazai hanaka ba ko ita Aunty Adama” a cewar ya Adnan
“gaskiya bazan iya da tashi hankalin mama Ameenah ba,kawai ni nayi mashi alƙawarin ƴata indai har yana so,dama tuna farko ita nake da burin ya Aura ba Noor ba” sai a lokacin Irfan ɗin ya ɗago ido ya kalli mom,gaba ɗaya su ka zuba ma mom da tai magana ido,ya Adnan ne yace “dama kina da wata ƴar ne bayan Yumnah bamu sani ba?”
“NAINARH nayi mashi alƙawarin ta muddin yana so” tunda mom ta fara magana gaban Irfan ya faɗi,wani irin mugun ɓacin rai ne ya rufeshi, mom tama rasa wa za tace ya Aura sai wannan yarinyar,ya Adnan da ƙyar ya haɗiye wani abu daya tsaya mashi a maƙoshi,kwata kwata baiyi tunanin mom za tace haka ba,ajiyar zuciya ya Naeem ya sauke yana faɗin
“gaskiya tana da hankali da natsuwa uwa uba tarbiyya da Ilmi, gaskiya naji daɗin jin haka mom,wlh ni ban ma yi wannan tunanin ba saboda ganin halin da take ciki,kinga idan ya Aureta hakan zai rage mata raɗaɗin rashin iyayenta,amma mom dangin Mahaifinta kina ganin za su Amince?”
“wannan ba matsala bace Naeem,tunda mahaifinta ya rasu su ka datse duk wata alaƙa dake tsakanin su da ita”
“duk da haka mom,dole su sani”
“zan sanar da su amma sai in ya Amince itama ta aminta da shi tukun,idan duk sun amince sai na sanar da su yanda idan ba su amince ba ina da right ɗin da zan maka su a Court” kallon Irfan ɗin ya Naeem yayi “kaji abunda tace,minene ra'ayinka akan hakan,kana sonta ko dai mu bari kayi tunani”
“yaya mi yasa baza ku fahimce ni ba, ni gaskiya bazan iya son wata ba bayan Noor” da mugun sauri su ka shiga kallonshi, wato duk bayanin da suke da bashi haƙuri ba fahimtar su yake ba “dan mom fatilah Bata son Auren ai ba ita zata ban Aurenta ba kuma ba da ita zan zauna ba ni gaskiya Noor nake so,dukan ku ba wanda hakan bata faru ba lokacin Auren shi kuma ai kuna zaune lafiya,sai ni za a hana ni,ni gaski...” bai ƙarasa ba ta dalilin marin da ya Naeem ya ɗauke shi da shi,dafe cheek ɗin shi yayi yana kallon ya Naeem da kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar ɓacin da ranshi yayi,tashi Irfan ɗin yayi rai a ɓace ya nufi ƙofa,kuka mom ta fashe dashi,da sauri ya Adnan ya nufo inda take,hannunta ya kama cikin nashi “dan Allah mom Kar wannan abun da yayi ya ɓata ranki,wallahi ko yana so ko bai so bazai Aureta ba” tashi ya Naeem yayi ya nufi Irfan ɗin dake bakin ƙofa
“wannan yanayin ka ke son gani a tare da ita,to bari kaji na faɗa maka, kai baka isa ta dalilinka ka hana mata zaman lafiya ba,dan mun zauna muna baka haƙuri it doesn't mean cewa bazamu iya tursasamaka ba,wllh kaji na rantse baka ba wannan yarinyar”
“haba second father dukan ku kun Auri muradin ranaku sai ni ne zaku hana”
“ka dai ji abunda na faɗa maka,idan kuma ban isa ba to”yana faɗa hakan ya bar wurin ya nufi mom,ya Naeem yana da saurin fushi amma yana da saurin sauka.
                        *Ep 41_42*
____________________________
Ficewa Irfan ɗin yayi rai a ɓace,karo su ka yi da juna,gaba ɗaya mug ɗin Coffeen dake hannunta ya zube mata a jiki,sakin trayn tayi tana fasa wata irin gigitaciyar ƙara saboda azabebben zafin daya ziyarci ganganr jikinta,gaba ɗaya coffeen ya wanke gaban rigarta da hannunta da ƙafarshi,kuka take sosai tana yarfe hannu,kallo ɗaya yayi mata ya bar wurin,A 360 mom ya Naeem, ya Adnan da  dady wanda kusan akan idonshi komai ya faru su ka faɗo parlorn, dan ƙarar da Nainarh tayi har cikin ƙwaƙwalen su, gaba ɗaya kanta su ka yi,a ruɗe ya Adnan yake tambayar mi ya sameta,daƙyar ta iya faɗa masu abunda ya faru da ita, sannu su ka shiga jera mata, ya Adnan ji yake kamar ya cire mata azaban da take ji, kamata yayi zuwa sofa, bin bayansu su ka yi zuwa cikin parlorn, kuka take sosai har ga Allah ba ƙaramin zafi take ji ba
“sannu kinji kukan ya isa haka muga hannun”dady ya faɗa, mayafin dake kanta daya rufe hannun mom ta janye tana kallon  inda ta ƙone,wurin yayi ja sosai, da sauri ya Adnan ya miƙe ya nufi kitchen, da gudu Yumnah ta faɗo parlorn ita da Fa'iza, wurin Nainarh su ka nufa hankali a tashe “sister mi ya sameki?” Yumnah ta faɗa kamar itama za tayi kukan
“mom mi ya sameta?”a cewar Fa'iza
“ƙonewa tayi” mom ta bata amsa, zaro ido Yumnah tayi tana yarfe hannu “wayyo Allah nah, garin yaya ki ka ƙone!?” a hanzarce ya Adnan ya dawo parlorn ɗauke da ɗan madaidaicin silver bucket mai ɗauke da ƙanƙara, da sauri yumnah ta tashi daga gaban Nainarh, hannun Nainarh data ƙone ya kama yasa a cikin ƙanƙarar,sake fashewa da kuka tayi tana faɗin “wayyo hannuna, mom zafi”
“sannu kinji, zai daina in sha Allah” a cewar dady
“yumnah bani towel” ya Adnan ya faɗa, da gudu ta tashi ta nufi bedroom ɗin mom sai gata ta dawo riƙe da ɗan madaidaicin towel, miƙa mashi tayi da sauri ya amsa yana sakashi cikin bucket ɗin,sai da yayi kamar five seconds tukun ya ciro shi, ɗan ruwan dake jiki ya matse, gaban rigar Nainarh ya nufa, da sauri mom ta amshi towel ɗin ganin abunda yake shirin yi “ya isa haka”  ta faɗa
wallahi gaba ɗaya a ruɗe yake shi kanshi bai san mi yake shirin yi ba burinshi kawai ta samu sauƙi, har cikin zuciyarshi yake jin kukanta, gyalen dake saman kanta mom ta zame, ɗan zaro ido tayi ganin wurin yayi ja sosai fatar wurin har ta ɗan taso, da sauri ta ajiye towel ɗin, kama hannun Nainarh tayi tana faɗin “tashi muje hospital kawai,Yumnah ɗauko mana hijab, Adnan muje hospital kawai”  da sauri su ka miƙe gaba ɗayan su, bedroom ɗin su Yumnah ta nufa a hanzarce “lafiya dai ko barrister?”
“to ƙone ne sosai, wurin har ya tashi”
“mom to ki bari a kira dr fawwar sai yazo ya dubata” acewar ya Naeem, da sauri ya Adnan yace “ko kafin ya iso wutan ya gama shiga jikinta, mu tafi kawai” a hanzarce Yumnah ta dawo riƙe da hijab ɗin Nainarh har ta zura nata a jiki, da sauri mom ta amsa ta sa ma Nainarh,bedroom ɗinta Yumnah ta nufa hijab ta ɗauko mata, Nainarh banda hawayen azaba babu abunda take har cikin cikinta take jin zafin, mug uku ne ya zube mata a jiki, dama da suka shigo ya Adnan ya ce ta kawo mashi coffee, ganin suna tare da ya Naeem da mom ne yasa ta haɗo da su dan bata ma san Irfan na gidan ba, coffeen da zafinshi yana turiri, shiyyasa take jin zafi sosai ga fatarta bawai ta saba da wahala bane,amsar hijab ɗin mom tayi ta zura a jikinta,Fa'iza gyara zaman mayafin dake jikinta tayi su ka fice dady kawai su ka bari,Ishrat yayi ma magana ta zo ta gyara wurin kafin ya wuce sama.
Motar ya Adnan su ka shiga, ya Naeem na kusa dashi yayinda yake zaune a mazaunin driver mom da Nainarh na baya, Yumnah kuwa motar Fa'iza su ka shiga, ficewa su ka yi daga estate ɗin, motocin securitys ɗin su na gaba wasu na baya,time to time yake leƙo back seat yana ma Nainarh sannnu ya Naeem sai kallonshi kawai yake.
Irfan yana ficewa daga parlorn motar shi dake parking space ya nufa, rai a ɓace ya buɗe marfin motar ya shiga,a tsiyace ya rufe motar kamar zai balla marfin,kifa kanshi yayi saman Steering wheel wani irin tafarfasa zuciyarsa ke mashi,sai a time ɗin ma ya ji zafin ƙonewar da yayi,kallo ƙafar yayi yana jan wani mugun tsaki,key yayima motar ya fice daga Estate ɗin,direct S I hospital ya nufa,wani mahaukacin horn ya buga lokacin da ya isa bakin gate din hospital ɗin,da mugun sauri securitys su ka buɗe mashi, a 80 ya shiga ciki kaɗan ya rage bai ture ɗaya daga cikin securitys ɗin ba,da ido su ka bishi, parking space ɗin da aka tanada domin su Dr's ya nufa, parking yayi,fitowa yayi bayan ya gama daidaita parking a zafafe ya maida marfin motar ya rufe,da ido ɗai ɗai kun mutanen dake kai kawo cikin hospital ɗin su ka bishi,yana da girma sosai hospital ɗin, abun kamar ba'a 9ja ba,ginin skyscraper ne hawa huɗu,ta ko ina ƙyallin glasses ne masu ɗaukar ido,cikin hospital ɗin ya nufa,yana shiga reception nureses ɗin dake wurin su ka shiga russunawa suna gaishe dashi,ko kallon inda su ke baiyi ba bare su sa ran zai amsa masu,da kallo kawai su ka bishi har ya shige elevator,da yawan ƴan matan dake wurin ji su kayi kamar su bishi suji mike damunshi,da yawansu dakwan wata irin azababbiyar soyayyar shi su ke amma ko kallon banza babu wacce ta ishe shi a cikin su.
katafaren office ɗin shi dake can 3rd floor na hospital ɗin ya nufa,a bakin ƙofar office ɗin ya tsaya,key yasa ya buɗe ƙofar office ɗin ya shiga,sanyayyan ƙamshin dake tashi a office ɗin ne ya daki hancinshi,dum light ne a office ɗin, switch ya nufa ya kunna,haske ne ya gauraye office ɗin, office ɗin yana da girma sosai ga wasu expensive office desk black color,ga book shelf mai matuƙar kyau,sai fridge, cikin office ɗin ya nufa,executive chair dake gaban desk ya nufa ya zauna,kifa kanshi yayi saman desk,wani iri yake ji a zuciyarshi kamar zata kama da wuta tsabar ɓacin rai, bakomai ke ƙara ɓata mashi rai ba face marin da ya Naeem yayi mashi da kafewa da su ka yi akan bazai Auri Noor ba,kawai dan yana masu biyayya it doesn't mean cewa zasu tauye mashi hakki yayi shiru,su lokacin Auren su wa yayi masu hakan,sun Auri maradan ransu sai shi za su nunama fin ƙarfi,abun takaici ma su rasa wa zasu ce ya Aura sai wannan yarinyar,wani wawan tsaki yaja yana tashi daga saman chair ya nufi fridge,buɗe fridge ɗin yayi kwalaben Alcoholic wine dana whiskey, tequila,Vodka and orange juice ne sai container ice cube, kwalbar red wine ya ɗauka tare da cup sai ice cube daya zuba cikin bowl,komawa yayi ya zauna ba tare da ya rufe fridge ɗin ba,buɗe kwalar wine ɗin yayi ya zuba a cikin cup tare da ice cube,rai a ɓace ya shiga shan wine yana fitar da wani irin hucin ɓacin rai,tas ya shanye ya sake zubawa, sai da yasha 3 cups kafin ya ajiye yana fitar da wani irin huci mai zafi,idanunshi sun ƙaɗa jawur har wasu ruwa ruwa ke kwanciya a cikin su, locker dake jikin desk ɗin ya buɗe, Cuba Aliados cigar ne a cikin locker,ɗaya ya ɗauka tare da lighter,a baki yasa yana kunna lighter,zuƙar cigar ɗin ya shiga yi a zafafe,yana fitar da hayaƙi ta baki da hanci,sake tsiyaya wine ɗin yayi a cup,yana sha yana zuƙar cigar,turo ƙofar office ɗin akayi,da yake a buɗe ya bar ƙofar,idanunshi da suka kaɗa jawur ya sauke akan Dr fawar dake shigowa office ɗin,da tsantsar mamaki yake kallon Irfan ɗin,rabon da ƙafarshi ta taka hospital ɗin kusan one month da wani abu kenan,yanzu ma wata Nurse ce ke sanar dashi Irfan ɗin ya zo,maida ƙofar Dr fawar yayi ya rufe,cikin office ɗin ya ƙaraso,kallo ɗaya Irfan yayi mashi ya ɗauke ido
“Irfan dama kana nan?” Dr fawar ya jefa mashi tambaya,ko kallon arziƙi Irfan bai mashi ba, girgiza kai Dr fawar yayi “yanzu da hankalinka kake aikata haka a office ɗinka,baka jin kunyar wani cikin familynka ya zo ya sameka haka??”
“how many time nake warning naka akan sa man ido,get out from my office kafin nayi maka abunda zanyi regretting daga baya” Irfan ya faɗa murya a kausashe, girgiza kai Dr fawar yayi yasan dama zai iya faɗa mashi fiye da haka ma dan daga gani ya fara fita hayyacinshi
“miyasa baka zuwa aiki,kasan cewa yayanka zai turo da supervisors dis week?”
“ban sani ba bana kuma son na sani, Please kafice ka bani wuri”
“Irfan ka kuwa san abunda ka ke, baka son zuwa Aiki idan ma kazo ba aiki ka ke ba,kafi kowa sanin halin yayanka,mi kake tunanin idan ya fahimci abunda ka ke??”
“sai dai idan kai zaka sanar dashi,ɗan sa ido kawai” rai a ɓace Dr fawar yace “dole na sa maka ido,amanar ka yayan ka ya bani dole kuwa na sa maka ido” wata irin iska mai zafi Irfan ɗin ya fisar,cike da tsawa yace “i said get out,if not...” ya faɗa yana nuna mashi ƙofa ba tare da ya ƙarasa faɗar abunda zai faɗa ba,juyawa kawai Dr fawar yayi ya fice yana girgiza kai,a shekaru ya girmi Irfan nesa ba kusa ba,kuma yana bashi girmanshi amma daga inda ya faɗa mashi gaskiya ajiye girmanshi da yake gani yake ya faɗa mashi magana san ranshi.
tashi yayi daga saman chair ya nufo ƙofa da cup ɗin wane da cigar yana ɗan layi kaɗan, alcoholic wine ɗin ta fara kai mashi karo,ƙofar office ɗin ya maida ya rufe harda key,a jikin ƙofar ya bar key ɗin,anan bakin ya zube.
ya Adnan lokacin da su ka iso hospital sun ga motar Irfan amma babu wanda yabi ta kanshi su ka nufo cikin hospital,da Dr fawar su ka ci karo a reception saukowarshi kenan daga office ɗin Irfan,da sauri ya nufesu, fuskarshi da ɗan fara'a,gaishe da su nurses ɗin dake wurin su ka shiga yi,da kulawa su ke amsa masu
“good evining mom,ai da kin kirani ba sai kinzo da kanki ba?” cewar Dr fawar
“ba damuwa fawar, patient gare ni,ƙonewa tayi”
“ayyah sorry” ya faɗa yana kallon Nainarh
“muje ko” ya faɗa yana kiran wasu nurses guda biyu,bin bayanshi su kayi ɗaya na kama Nainarh,su mom kuwa office ɗinsa yace wata Nurse ta kaisu,a bakin office ɗin shi suka tsaya, Nurse ɗin na ƙoƙarin buɗe masu ƙofa ya Adnan ya juya da nufin nufar sama,da sauri ya Naeem ya riƙo hannun shi dan duk tunanin shi Emergency ward din zaibi su Dr fawar
“ina zaka?”
“office ɗin wancan mara mutumcin,ya ƙone ɗiyar mutane amma ko a jikinshi” ya faɗa cikin tsantsar ɓacin rai
“calm down Adnan,ba sai kaje ba rabu dashi kawai,ai zai dawo gidan ya same mu”
“wallahi ka kyaleni na koya mashi hankali tunda shi bashi da hankali” girgiza mashi kai ya Naeem yayi “nace ka rabu dashi ko,zai dawo gida ne ya same mu” iska mai zafi ya Adnan ya fesar,cikin office ɗin su ka shiga dan mom da su Yumnah tuni sun shige sun barsu.
suna a nan zaune office ɗin sunyi shiru kowa da abunda yake saƙawa a ranshi,Dr fawar ne ya shigo da sauri ya Adnan ya miƙe yana tambayarshi wutar dai da sauƙi bata shiga cikinta ba,cikin office ɗin ya ƙaraso
“ku kwantar da hankali,ba wani sosai ne ta ƙone ba,kuma Alhmdllh zafin coffeen baikai har ya shiga cikinta ba,kawai dai fatan ta bata son zafi ne sosai,amma Alhmdllh da sauƙi,magunguna ne kawai zata sha sai cream da zata dinga shafawa a wurin” tunda ya fara jawabin nan hankalin su ya kwanta,dama damuwarsu kar ace wutan ya ƙonata sosai
“na bar Nurse Fatima ta shafa mata cream,data shafa mata zaku iya tafiya,Allah ya bata lafiya” da Ameen duka su ka amsa,ba'a wani jimaba Nainarh su ka shigo tare da Nurse ɗin dake riƙe ledar maganinta, Yumnah ta amshi ledar tana ma Nainarh sannu,sannu su ka shiga yi mata,sallama su ka yima dr fawar ɗin su ka fice,lokacin da su dawo gida,bedroom ɗin su Nainarh ta nufa ita da Yumnah da Fa'iza, ya Naeem tun a parking space yayi masu sallama ya wuce gida.

*UNITED STATE❤*


_*Las Vegas (Nevada)*_


daga ita sai Aunty Sophia ne a ward ɗin,miss Malika tunda ta fita bata sake dawowa ba,fira suke ba wani sosai ba Nailarh na bata labarin yanda taji lokacin da wannan mutumin yayi wining wasan,tana faɗa mata irin yanda zuciyarta tayi mata,lallashinta Aunty take tana bata ƙwarin gwiwa da kuma yi mata alƙawarin sai sun hukunta shi akan abunda yayi mata
“but Aunty ina zargin Dr dake kula dani kamar shine,abunda yasa ban faɗama mom ba na san data sani zata haɗashi da su Noah ne,na fi son saina tabbatar da zargina lokacin na warke,nafi son na hukuntashi da hannuna”
“nima bazan sanar da ita ba,zan so ki hukuntashi da kanki,duk ta yanda za muyi yayi daya sani za muyi,karki damu kinji” jinjina mata kai tayi
“sai ya san wacece ni,sai yayi daya sanin sa kanshi a hanyata” Nailarh ta faɗa
“dole ya san wacece ke,nima dole yaga ɓacin raina saboda wahalar man da princess da yayi” marairaice fuska Nailarh tayi “Aunty Sophi ba kiji zafin dana ji ba,gaba ɗaya naji duniyar ta yiman zafi,lokacin dana shaƙi wuyan rigar ki ji nake kamar zan mutu a lokacin” saurin girgiza mata kai Aunty Sophia tayi tana kama hannunta “kwantar da hankalinki kinji,dole ya gane kuskuren abun da ya aikata”gyaɗa mata kai Nailarh tayi, nocking ƙofar ɗakin akayi, izinin shiga Aunty Sophia ta bada,Nurse ɗin ɗazu ce ta shigo da food trolley,har bakin bed ɗin ta ƙaraso,gaishe da Aunty Sophia tayi kafin ta kalli Nailarh“good afternoon ma'am, it's time for lunch” kauda kai gefe Nailarh tayi,itafa idan zasu cigaba da bata wannan Yogurt ɗin zata daina cin abincin su, warmers ɗin dake saman trolley Nurse ta buɗe,sarving Nailarh ta shiga yi,lafiyayyan sandwich ta bata tare da gasashshen kifi.
Aunty Sophia ta shiga bata, Nurse ɗin na daga kan robber chair tana kallon su,turo ƙofar mrs Malika tayi ta shigo tare da su luna,kallonta Nurse ɗin da Aunty Sophia su ka yi amma Nailarh ko kallon inda take ba tayi ba,harta canza kayan jikinta da alama gida su ka koma dan harda basket ɗin abincin a hannun su luna,gaishe da ita Aunty Sophia da Nures ɗin su ka yi,amsa masu tayi yayin da idanunta ke kan Nailarh kamar zata haɗiyeta,tashi Aunty Sophia tayi daga inda take zaune lokacin data kammala ba Nailarh abinci, magungunan ta Nures ɗin ta bata kafin ta fice,bakin bed ɗin Mrs Malika ta zo ta zauna,hannun Nailarh ta riƙo a cikin nata ba tare da tace komai ba, Nailarh bata kulata ba, around 6 ɗaya daga cikin nurses ɗin ta shigo ta sanar dasu time ɗin da zasu bar Nailarh ita kaɗai yayi dama aroud six su ke rufe visiting,babu musu ko wani abu mrs Malika tace ok,kallon su Aunty Sophia tayi ta ce su tafi kawai,shirin tafiya su ka shiga yi,su luna su ka ɗauki basket ɗin da su ka zo dashi Aunty Sophia ma kaɗai taci abincin,kissing forehead ɗin Nailarh Aunty Sophia tayi haɗi da yi mata sallama su ka fice,mrs Malika ma kissing forehead ɗinta tayi without saying anything to her,fushi take da ita saboda abunda tayi ma mijinta,tun fil'azal Nailarh bata shiri da mijin Mrs Malika tunda ta fahimci ba shi bane Mahaifinta ba ta ɗauki karan tsana ta ɗora mashi,ga haushi da kishin kusantar Malika da yake da take ji,duk da itama ba wai ta damu da abunda ke tsakanin su can sosai dan bata da ra'ayi da ƙarfin tsiya ta hanyar alura Malika tasa abun yayi tasiri a gareta har ya zame mata jiki, har ya kai take kishin Malika,saboda ita yasa basa zaune waje ɗaya da Malika sai dai idan ta bar ƙasar ya bita inda ta tafi,sometimes saboda shi take barin US ta tafi wata ƙasar badan business ba saidai dan kawai su haɗu.
saurin kamo hannunta tayi,kallonta Malika tayi fuskarta a ɗaure,side smile Nailarh ta sakar mata
“are you angry with me because of your that black husband?”
Kallonta Malika kawai tayi,dan ajiyar zuciya Nailarh ta sauke,sake riƙo hannunta tayi tana faɗin “If u continue to be with him, I will break the promise I made to you, I will also get married,I promise u” Nailarh ta faɗa babu alamun wasa akan fuskarta,wani irin kallon Mrs Malika ta shiga binta dashi
“you're going to do what!?”
“I know you heard me well” zame hannunta tayi daga na Nailarh,zama tayi kan chair dake gaban gadon “baby kin fi kowa sanin cewa duk dukiyar da muke takama da ita akwai tasa a ciki,Duk wani kasuwancinmu yana da jari a ciki,shine silar arziƙina”
“i don't care, I told you
If you want me to fulfill promise i made u,just break this useless marriage” wani irin wahalalliyar yawu Mrs Malika ta haɗiye,bata taɓa expecting jin haka daga gareta ba
“please Nailarh ki gane mana,rabuwa da shi tamkar na rabu da kaina ne,shine komai nawa fa”
“alright,but I want u to know that there is no any promise between us,I will marry,ko da baki so hakan ba” ta faɗa tana tsare Malika da ido,kamo hannunta Malika tayi “kiyi haƙuri kinji,kin san ina sonki fiye da kowa a duniyar nan,karki fasa Alƙawarin da ki ka man Please Nailarh,bazan juri ganinki tare da wani ba,kina so nima heart Attack ya kamani??”
“zanfi kowa farin ciki idan ya kama ki”Nailarh ta faɗa ba tare da nuna wata damuwa ba,kallonta Malika ta shiga yi,mi yasa sai da komai ya kusa zuwa ƙarshe Nailarh zata ɓullo mata da wannan tsarin,kenan abunda take zargi zai zama gaskiya
“baby that doctor ne ya ce kice man haka,dama that the reason yasa ya kawo maki flower,dama wannan shine dalilin da yasa yake wanan abubuwan akan ki,sonki yake kema kina sonshi ko?”
“wannan kuma matsalar ki ce,idan ma sona yake I will marry him” wata irin gigitaciyar tsawa Malika ta daka mata “idan har ki ka cigaba da faɗin haka i promise u I will kill him,I sewer” kallonta Nailarh tayi tana sakin wani malalacin murmushi “ if u kill him I promise u I will kill your husband” iska Malika ta furzar mai zafi,dan mi Nailarh zata mata haka sai da ta gama preparing komai zata ɓullo mata da hakan,nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,in a cool voice tace “please Nailarh ki daina faɗa man haka,nifa momynki ce,kuma kin san ina sonki,saboda ke ne kawai bazan iya rabuwa da shi ba,amma ke

Please Login or Register in order to submit comment