Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabanta yayi,muryar tana rawa tace “wane flash,bansan akan wane flash kake magana ba??”
“Nainarh!” ya kira sunanta da ɗan ƙarfe “flash ɗin da dadyn ki ya baki, ko baki son a gano wanda suka kashe shi ne?”
kamar za ta yi kuka tace “wallahi ya Abid babu wani flash da dady ya bani”
“ki tuna Nainarh, ko dai kin jefa shi wani wuri kin manta?”
“wallahi ya Abid ka ji na rantse babu wani flash da dady ya bani,lokacin ma da suka kashe shi bana hayyacina”
“ai ba a wannan lokacin ya baki ba, ki sake tunawa Nainarh, rayuwarmu na cikin haɗari har da ke, bashi wannan flash ɗin shine kawai zai fitar damu daga halin da muke ciki”
“rayuwa ta fa kace ya Abid”
“kwarai kuwa Nainarh wanda suka kashe dadynki sun jima da sanin flash ɗin da suke nema yana hannunki, ki yi ƙoƙari ki tuna inda ki ka ajiye shi Nainarh, kullum cikin bibiyar rayuwar mu suke Nainarh, ki daure ki tuna in da kika ajiye shi,idan baya tare da ke ne ki sanar da ni in da yake zan je na dauko shi ko a ina ki ka ajiye shi”
hawayen da suka taru a idon ta ne suka shiga zubowa “na shiga uku ya Abid wallahi ka tsoratar dani,sau biyu ana turo man message ana man barazana akan flash wallahi babu wani flash a hannu na”
“You see! kinga abun da nake faɗa maki ko?, ki daure ki tuna inda kika ajiye shi” “taya zan tuna ya abid bayan ba'a bani ba”
“to shikenan na fahimta,ki daure ki sanar da CM an turo maki massege, amma kar ki sanar da shi komai game da dawowa ta kin ji”
“in sha Allahu bazan faɗa mashi ba, yanzu kai kana ina?,ina son ganin ka”
“gani na a yanzu ba zai yiwu ba Nainarh, kema ina son ki kula,motsinki kaɗan suke jira”
“shikenan in sha Allah, nagode amma idan ina son nayi magana da kai taya zan same ka?”
“karki damu zan dinga kiranki don naji a wani hali kike ciki,yanzu ki koma ki yi barci, kar ki sa damuwa a ranki kinji ko”
gyaɗa kai tayi kamar tana a gaban shi “goodnight take care,bye bye” ya faɗa yana rejecting call ɗin
zame wayar tayi daga kunnenta gaba ɗaya a tsorace take, to ita wane flash ake tahumarta bayan dadyn ta bai bata komai ba, kuma a ranar da suka shigo gidan duk wani flash na gidan sai da suka ƙone shi hatta laptop din su.
ta shafe tsawon mintuna 40 tana saƙawa da kwancewa kafin dai ta kwanta bayan ta kashe bed-side lamp, addu'a ta sake yi ta shafe jikinta gaba ɗaya, a tsorace take amma deep down tayi matukar farin ciki da dawowar yayanta,sai around 3 am bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita.
barci bai yi nisa ba taji saukar hannun mutum a jikinta,wani irin bugawa zuciyarta tayi,suman kwance tayi ko motsi bata iya yi, jin hannun ya fara yawo a jikinta ne yasa bugun zuciyar ta ya tsananta, ba zato ban tsammani taji saukar hannun mutum a kirjinta bata san lokacin da ta kware baki zata fasa ƙara ba,saurin toshe mata baki aka yi,kokawar fizge hannun daga bakinta ta shiga yi amma ta kasa,bakin mutum taji saitin kunnen ta in a whisper taji muryar data sake jefata cikin tashin hankali
“kada ki tsorata ban zo da nufin cutar dake ba, naga kina cikin damuwa ne yasa nazo dan na ɗebe maki kewa,tun ranar da na fara tozali da ke gaba ɗaya na rasa sukuni na,na shiga halin tunanin zazzafar surar ki mai matukar ɗaukar hankali,ki amince man nayi miki alƙawarin zan mantar dake duk wata damuwarki,zan jiyar dake daɗin da ko ɗa namiji ba zai jiyar dake irin sa ba,ki amince da buƙatata Nainarh, a kullum da tunaninki nake kwana da shi nake tashi,you dominate my mind,I love you Nainarh”
A lokaci ɗaya wani irin tsoro da tashin hankali ne su ka mamayeta,tuni hawaye sun fara zarya a kumatunta.
kokawar yanda zata ƙwace kanta take amma ta kasa, hankalinta ne ya ƙara tashi lokacin da taji tana neman rabata da PJ dake jikinta.
bata sake shiga tashin hankali ba sai da taji saukar bakinta a nata,sosai hankalinta ya sake tashi,kokawa ta shiga yi da ita tana kai mata duka ta ko ina amma kamar tana dukan dutse,ba bu ma alamar ta san tana yi,ganin dai ba sarki sai Allah ne yasa ta shiga laluben yumnah amma taji wayam bata kan bed ɗin,tsoronta ne ya tsananta, gashi har ta so ma rabata da kayan jikinta.
Allah ne ya taimaketa ta samu Sa'a ta daddage ta galla mata cizo a tongue,da sauri ta saki bakinta tana fasa ƙarar azaba, da mugun sauri Nainarh ta zabura ta koma can gefe.
da sauri ta kai hannunta jikin switch,duk da tsoron da take ciki amma ko ba komai zata so tabbatar da zarginta.
ganin abun da Nainarh ke shirin yi ne yasa ta miƙewa,da gudu ta nufi ƙofar fita daga ɗakin,tana kaiwa tsakiyar ɗakin Nainarh na kunna bulbs haske ya gauraye ɗakin,
da kallo Nainarh tabi bayanta har ta fice daga ɗakin da gudu.
a jikin head board ta takure jikinta sai rawa yake kamar wacce sanyi ya yi ma mugun kamu,kifa kanta tayi saman laps tana fashewa da wani irin ku ka mai ban tausayi.
cikin muryar ku ka take faɗin
“mi yasa zaki man haka,dama tsawan zaman mu dake sha'awata ki ke yumnah,why, mi yasa,mi yasa yumnah!!” ta faɗa tana sake fashewa da wani ku kan.
ku ka take Sosai babu mai lallashinta, yumnah ta karya mata zuciya,tayi data sanin sanin yumnah a rayuwarta, a wannan lokacin tayi fatan ace a hannun dangin mahaifiyarta ta zauna ko na mahaifinta,gara mata azabar su da irin wannan ƙazantar.
har aka kira sallar fajr bata sake komawa bacci ba,har lokacin jikinta kyarma yake ga wani ciwan kai da zazzaɓi da ya rufeta lokaci guda.
da ƙyar ta samu tayi ƙarfin halin tashi ta nufi toilet ta ɗauro alwala ta fito, dressing room ɗin su ta nufa, carpet da hijab ta ɗauko,bedroom ɗin ta dawo,anan gefen bed ɗin ta shimfiɗa carpet ɗin tayi sallah.
ko da ta kammala sallah bata tashi a kan carpet ɗin ba anan bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita.

*UNITED STATE❤*
*Las Vegas (Nevada)*

Kamar yanda Mrs Malika ta faɗa washe gari ta tafi, Nailarh har Airport ta rakata,da zata tafi harda kukanta.
tun a ranar Aunty Sophia ta fara mata Allurar a bisa tsarin da Dr daniel ya bada, Alluran na tsawan one month ne,after one one day,15 days kenan.
Tunda akayi discharging ɗinta daga hospital kullum ne sai
C E O ya turo mata da message sau uku a rana morning, evening and night,lokuta da dama shi ke tashinta daga bacci,tun abun nashi na ƙular da ita yanzu har ya koma bata mamaki da baya missing koda rana ɗaya ko lokaci,wasu lokutan kuma kiranta yake,tun bata picking har ta koma tana picking duk da ba wata maganar arziƙi su ke ba,masifa da buge mashi warning sun fi yawa a kalamanta.
duk time ɗin data tace zata ɗauki mataki akanshi, murmushi yake mata yace idan zata hukuntashi tayi mashi sassauci kar shima heartAttack ya kamashi,duk lokacin ɗaya furta mata hakan amsa ɗaya take bashi “zanfi jin daɗin haka,domin ka takura man”.
Yauma kamar kullum tana kwance a bedroom ɗin ta har 10 pass 11 bata farka daga bacci ba,tun ɗazu wayarta ke haske alamar shigowar message,sau biyu Aunty Sophia na shigowa dubata amma bata tashi ba.
kiran daya shigowa wayarta ne yayi sanadiyyar tashinta,a hankali ta buɗe idanunta masu ɗauke da bacci,ɗan tsaki taja tana tashi zaune,ta san babu wanda zaiyi mata wannan kiran at this time bayan shi.
jawo wayar tayi tana duba screen ɗin,kamar yanda tayi zargi shi ne,girgiza kai tayi tana jan wani tsakin.
picking call ɗin tayi haɗin da kara wayar a kunnenta,zazzaƙar muryarshi mai cike da natsuwace ta daki dodon kunnenta “sleeping baby,Are you still on the bed?”
“why are you disturbing me in this morning?”
“you start ko,why are you still on the bed,I take my breakfast but still I'm hungry,ashe beb ce ba tayi breakfast...” bai ƙarasa ba yayi shiru dalilin dariyar da yaji Nailarh nayi, kalaman shi ne su ka yi matuƙar bata dariya,shiru yayi yana sauraron dariyarta dama yayi hakan ne dan ya sata farin cikin,sai da tayi mai isarta tukun tayi shiru,ɗan ajiyar zuciya ya sauke “please wake up and take a shower and come have breakfast baby”
“I won't do it!” ta faɗa kai tsaye
“please cutie pie” ya faɗa cikin kwantar da murya
“I Can't” ta faɗa tana ɗan ɗaga murya haɗin da yin rejecting kiran,jefar da wayar tayi gefe tana furzar da iska mai zafi daga bakinta haɗi da zura hannunta cikin sumar kanta tana yamutsata.
turo ƙofar ɗakin Aunty Sophia tayi ta shigo tana turo food trolley,ɗago da kai Nailarh tayi tana kallonta,har bakin bed ɗin Aunty Sophia ta ƙaraso “baby kin tashi,hope you slept well?” kallonta Nailarh tayi harta zauna gefen bed ɗin without saying anything her,kallonta Aunty Sophia tayi ganin ta zuba mata ido “baby lafiya?”
“he disturbing me” ta faɗa tana ɓata fuska “baby ai duk laifinki ne,kin fasa hukuntashi ne”
“no kawai naga yayi regretting ne”
“saboda yayi regretting ne yasa ki ka ƙyaleshi yake disturbing ɗinki?”
“wani side na zuciyata ne ke cewa na yafe mashi tunda ba yana sane yayi ba” ɗan ajiyar zuciya Aunty Sophia ta sauke
“shikenan baby,bazan hana ki yafe mashi ba,dama yana da kyau mutum ya zamo mai yafiya” ɗan ya mutse fuska Nailarh tayi tana matsowa kusa da Aunty Sophia,kwantar da kanta tayi saman shoulder ta,shafa kanta Aunty Sophia tayi
“sorry,go and take a shower,ga breakfast nan da sauran injection ɗinki” ɓata fuska Nailarh tayi “wai yaushe ne injection ɗin nan zata ƙare?”
“two month ne baby”
“gaskiya am tired Aunty Sophie,wai ma ta mecece?”
“Dr Daniel zaki tambaya”
ɓata fuska Nailarh tayi,hannu ta zura ta jawo wayarta dake ringing, picking call ɗin tayi tana kara wayar a kunnenta, muryar momyn ta ce ta daki dodon kunnenta “baby ke da waye a waya ina kira ba kiyi picking ba?”
shiru Nailarh tayi ba tare da tace mata komai ba “magana nake baby?”
“momy yaushe za ki dawo?”
“next month” Malika ta faɗa
“zan kuwa biyo ki ne” Nailarh ta faɗa tana rejecting kiran
“baby Please wakeup and take a shower” Aunty Sophia ta faɗa “zaki man ne?” wani kallo Aunty Sophia tayi mata “dama ni nake maki?”
“to ai kin hana masu yi man suyi man”
“saboda ina so ki zama cikakkiyar budurwa ba yarinya ba,ko kina so CEO ya cigaba da rainaki?”
taɓe baki Nailarh tayi without saying anything to her,tashi tayi ta nufi bathroom da kallo kawai Aunty Sophia ta bita tana sakin murmushi,tunda suka dawo daga hospital ta hana su lolarh yi mata wanka,da Nailarh tace wani abu sai ta fake mata da kar CEO ya rainata.
tashi tayi daga saman bed ɗin ta gyara mata,har ta kammala Nailarh bata fito ba,wayarta ta ɗauka a dalilin shigowar message da taji.
messages ta gani daga Number da yawa wasu Nailarh ta buɗe wasu na unread,ta sama ta shiga karanta message ɗin ba tare da ta shiga ciki ba, murmushi ta saki lokacin data kammala karanta message ɗin
“i don't know who are U,ban san mi ka ke so a tare da Nailarh ta ba”
saurin ajiye wayar tayi jin alamar Nailarh zata fito,tashi tayi da sauri ta nufi Nailarh tana faɗin “baby have you done?” ta faɗa tana jan hannun Nailarh dake sanye da bathrobe zuwa dressing room ɗinta,da kanta ta shiga shiryata,tunda su ka dawo daga hospital ita ke mata komai.
bedroom ɗin su ka dawo bayan ta kammala shiryata,good trolley data shigo da shi ta jawo,sarving ɗinta tayi,da kanta ta shiga bata abincin harta kammala.
Injection ta haɗa tayi mata,harda yar ƙwallarta da tayi mata,tattara kayan Aunty Sophia tayi tana faɗin “anjima nake son muje Orphanage, nurse laurah tace man yaranki na ta tambayar kina ina”
“Ayyah,shaf na manta da su”
“anjima sai muje”
“okay Nailarh ta faɗa ficewa Aunty Sophia tayi.
*tun ranar da su ka amso kaya a port,kusan kullum ne sai taje ta duba jikin yaran,dawowar Momyn ta yasa ta rage zuwa saboda Momyn tata ta nuna bata son tana zuwa*

*ABUJA NIGERIA*💫

har yanzu kwance take saman carpert ɗin da tayi sallah,turo ƙofar ɗakin Ishrat tayi ta shigo,ganin kowa na gidan ya fito Nainarh ce bata fito bane yasa ta zo duba ko lafiya.
da mamaki take kallonta kwance a ƙasa,har inda take kwance ta ƙaraso,a hankali ta shiga kiran sunanta,da alama tayi nisa sosai a cikin baccin yasa ba taji kiran da tayi mata ba,hannunta ta kai saman kafaɗarta da nufin tashin ta
wata irin zabura tayi haɗi da fasa ƙara,saurin toshe mata baki Ishrat ɗin ltayi tana faɗin “nice Aunty Nainarh” wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar Ishrat a kusa da ita,gaba ɗaya a tsorace take.
kafeta da ido Ishrat tayi “lafiya ki ke Aunty Nainarh?” gyaɗa mata kai Nainarh tayi “lafiya lau nake” gyaɗa kai kawai Ishrat tayi ba dan ta yarda da abunda Nainarh ta faɗa mata ba,tashi tayi daga duƙen da take.
bed ɗin su ta fara gyara masu,tashi Nainarh tayi ta nufi bathroom,mirror ta nufa da sauri,kallon lips ɗinta da shoulder ɗinta da su ka yi jawur tayi,wasu irin hawayen baƙin ciki ne su ka wanke fuskarta,tayi data sanin sanin yumnah a rayuwarta,bata taɓa expecting haka daga gareta ba,ta kai tsawan five minutes a gaban mirror kafin ta cire kayan jikinta,ruwa ta tara a bathtub,wanka ta shiga yi,kamar zata fasa fatar jikinta haka take dirzarta da sponge,gaba ɗaya ƙyanƙyamin jikinta take saboda abunda yumnah tayi mata.
sai da jikinta ya fara mata zafi tukun ta dakata,fatar tayi jawur kamar wacce aka watsama tafasasshen ruwa, fashewa tayi da wani irin kuka mai ban tausayi “mi yasa ƙaddara ta haɗani dake yumnah,mi na aikata ne wannan abubuwan ke faruwa da ni” ta faɗa cikin ƙunar rai,ta kai tsawan 30 minutes a toilet tana aikin ku ka kafin ta wanke jikinta ta fice,har time ɗin hawaye ne ke zarya a fuskarta.
lokacin data fito bata samu Ishrat ba harta kammala gyara masu ɗakin ta fice, dressing room ɗin su ta nufa, idanunta ne su ka sauka akan ƙaton kwalin da su ka yima momynta shopping ita da yumnah,yau su ka yi za su kai mata ziyara amma ta ɓata komai,kauda kai tayi daga kallon kwalin ta nufi wardrobe ɗin su,ɓangaren da kayanta su ke ta nufa,doguwar rigar atamfa ta ɗauko haɗe da hijab,zura kayan tayi a jikinta,
shaf shaf ta shirya a cikin kayan, bag hanger su ta nufa, ƙaramar side bag ta ɗauka, wayarta da atm dinta ta saka a cikin jakar.
parlor mom ta nufa ta yi mamakin ganin falon tsit babu kowa har ta juya da da nufin zuwa bedroom ɗin mom,Ishrat ce ta fito daga kitchen,kallon Nainarh dake ƙoƙarin shiga bedroom ɗin mom tayi “mom ba ta nan” ishrat ta faɗa,dakatawa tayi tare da sakin handling ɗin kofar,dawowa tayi cikin parlorn tana faɗin “ok bari na shiga na gaishe da daddy”
“shima baya nan” Ishrat ɗin ta bata amsa,da mamaki Nainarh ke kallon Ishrat ɗin “to ina suka tafi,Aunty laatifa fa??”
“suna hospital gaba ɗayan su har da Aunty yumnah,Aunty Kainart ce bata da lafiya”
“Aunty Kainart!?” Nainarh ta faɗa jinjina mata kai Ishrat ɗin tayi alamar Eh
gyaɗa kai Nainarh tayi tana faɗin
“Allah ya bata lafiya, amma tun yaushe suka tafi?”
“gaskiya ban sani ba, amma ina tunanin tun cikin dare su ka tafi,dan da safe Aunty yumnah da Aunty Fa'iza sun zo sun ɗaukar masu breakfast,tace idan kin tashi ki kirata a waya tayi ma driver magana ya kai ki”
ok kawai tace mata tana nufar dining room,nufo dinning room ɗin Ishrat tayi da nufin saving ɗinta, dakatar da ita Nainarh tayi tana cewa “barshi kawai zan yi saving kaina” da to Ishrat ɗin ta amsa tana barin wurin, black tea kawai ta haɗa tasha,tashi tayi handbag ɗinta dake kan sofa ta nufa dauka tayi ta fice daga parlorn.
da mamaki Ishrat ke kallon warmers ɗin da ke kan dining,ganin Nainarh ba taci komai ba,tunani ta fara anya lafiya,musamman tsoratan da tayi lokacin da ta tashe ta daga bacci.
warmers ɗin suka shiga kwashewa ita da munirat suna kaiwa kitchen.
Nainarh tana ficewa daga parlorn direct compound ɗin gidan ta nufa ɗaya daga cikin securitys din gidan dake shawagi tayima magana a kan tana son zata fita ne,daya daga cikin drivers ɗin da ke zaune tare da maigadin gidan ya kwalama kira,a hanzarce ya taso ya nufo inda suke, cike da girmamawa ya gaishe da ita,da kulawa ta amsa mashi tana sanar da shi zai kai ta prison ne wurin mahaifiyarta, da ladabi ya amsa mata da to yana nufar parking space ɗin gidan,ɗaya daga cikin motocin dake parking space ɗin ya nufa key yayi ma motar tare da nufar inda take, back seat ta buɗe ta shiga, reverse yayi suka nufi main gate ɗin gidan,suna isowa securitys ɗin dake bakin gate ɗin suka dakatar da su,daya daga cikin security ne ya taso,da sauri driver ya sauke glass ɗin motar,gaisawa su ka yi da security yana tambayar ina za su “prison” ya faɗa, tambayarshi yayi shida wa yana nufar back seat,sauke glass Nainarh tayi da ladabi ta gaishe da shi amsa mata yayi cikin kulawa yana faɗin adawo lafiya haɗi da barin wurin,key driver yayi ma motar su ka fice daga Estate ɗin.
direct hanyar central Jail su ka nufa,sai da su ka yi nisa Nainarh tace “please idan ka samu mall a gaba zan ɗanyi shopping” da ok ya amsa mata.
a bakin wani haɗaɗɗen Mall na yan gayu yayi parking,fitowa tayi,ciki su ka shiga yana biye da ita a baya
within a five minute ta kammala shopping ɗin duk wani abu data san mahaifiyarta zata buƙata,wurin biyan kuɗi su ka nufa driver na tura cart.
Atm ɗin ta ta ciro bayan an gama calculating kuɗin kayan,ATM ɗin ta miƙa masu amma sai mutumin ya sanar da ita ai an biya kuɗin kayan,da mamaki take kallon mutumin “ban gane an biya ba” ta faɗa dan jin waye zai biya kuɗin kayan data saya
“afuwan ba'a bamu damar faɗa ba,zaku iya tafiya”taɓe baki kawai tayi koma waye matsalarshi damuwar da take ciki ma ta isheta,har parking lot ma'aikatan wurin su ka kai mata kayan,a booth driver yasa kayan, reverse yayi su ka bar mall ɗin.
within a time su ka iso Jail ɗin,ɗaya daga cikin securitys ɗin dake gadin Jail ɗin ya nufo motar,sauke glass ɗin motar yayi,gaisawa su ka yi da guard ɗin,daga yanayin gaisuwar ta su zaka fahimci sun san juna,umarni ya bada aka buɗe masu gate,cikin Jail ɗin su ka shiga.
A parking lot su ka yi parking,fitowaNainarh tayi,buɗe booth ɗin motar driver yayi, shopping ɗin da tayi ya ɗauko, office ɗin C G C suka nufa,a bakin ƙofar office ɗin su ka tsaya, ɗaya daga cikin securitys ɗin dake bakin ƙofar ne ya shiga dan sanar da zuwan su,fitowa yayi yana sanar da su za su iya shiga.
cikin office ɗin su ka shiga bakinta ɗauke da sallama, a zaune C G C yake saman chair ɗin shi,da fara'arsa ya amsa sallama da ta yi,ɗaya daga cikin chairs ɗin dake gaban desk ɗin shi ya nu na mata alamar ta zauna,zama tayi driver na ajiye kayan dake hannunshi.
fita drivern yayi,ruwa da lemu CGC ɗin ya ajiye mata, ɗan murmushi tayi tana faɗin “ina wuni uncle”
“lafiya lau Nainarh,yau sai ke kaɗai,ina barisster da yumnah?”
“tana da patient ne a hospital shiyyasa bata zo ba”
“Ayyah Allah sarki, Allah ya sawaƙa”
“Ameen,Momy fa uncle?” ta faɗa dan ta ƙagara taga momynta
“karki damu nasa ayi magana,yanzu zata zo”
jin jina mashi kai tayi
wasu chairs dake can ɗan nesa da desk ɗin shi ya nuna mata yana faɗin “you have 30 minutes” godiya tayi mashi tana tashi ta nufi chairs ɗin,tana zama ana buɗe ƙofar office ɗin officers mata ne guda biyu su ka shigo tare da momynta,da gudu ta nufi mahaifiyar tata ta faɗa jikinta haɗi da sakin kuka,wani irin sanyi jikin Hajiya Asma'u yayi lokaci ɗaya wasu zafafan hawaye su ka wanke fuskarta, hugging ɗin ta tayi sosai tana jin wani irin tausayin junansu, sun kai tsawan minti biyar kafin su ka raba jikinsu har time ɗin Nainarh kuka take itama mahaifiyarta hawayen dake fuskantar basu dai zuba ba,ƙarfin hali tayi wurin lallashin Nainarh, chairs ɗin dake wurin su ka nufa su ka zauna tana cigaba da lallashinta,shiru Nainarh tayi tana kwantar da kanta saman shoulder momyn ta ta
“ina barisster?” hajiya Asma'un ta faɗa
“ba ta zo ba,Momy dan Allah ina so na dawo wurin ki” ta faɗa tana ɗago kanta daga kafaɗar mahaifiyar ta ta
C G C na daga zaune saman chair ɗin shi duk wani abu da su ke faɗa yana ji haka ma officers ɗin da su ka shigo da hajiya Asma'un, wani irin kallo mai cike da tausayi hajiya Asma'un tayi mata “mi yasa ki ke son zama nan,wani abun ya faru dake ne,ko dai Zulaihart tayi maki wani abu?” girgiza mata kai tayi
“A'a kawai dai ina son zama tare da ke,na gaji da zama babu ke a kusa dani”
“Nainarh nima kaina bana jin daɗin rashinki a kusa da ni,amma ya za muyi haka Allah ya ƙaddaro a rayuwar mu,babu yanda muka iya dole mu karbi ƙaddarar mu hannu bibbiyu,kiyi haƙuri kinji,zamanki anan bazai yiwu ba” yanayin fuskar Nainarh ne ya canza har ga Allah abunda zai nisanta da yumnah take so a yanzu,sai dai ya za tayi dole tayi haƙuri tunda hakan ƙaddara ta zaɓar mata, lallashinta sosai momyn ta ta tayi,kamar yanda C G C ya faɗa 30 minutes na cika aka fice da Hajiya Asma'un bayan sunyi sallama da Nainarh ta ɗauki shopping ɗin data kawo mata,harda ku ka Nainarh lokacin da suka fice,sallama tayi ma CGC ɗin ta fice,a bakin ƙofar office ɗin ta samu driver,parking lot su ka nufa inda su ka yi parking motar su.
Ficewa su kayi daga prison ɗin har lokacin da ɗan sauran hawaye a fuskar Nainarh,wani irin tausayinta ne ya kama driver,tsit motar tayi har su ka kama hanyar da zata maida su Estate ɗin dama a haka su ka zo.
da mamaki yake kallon motar dake bayan su idan ba idanunshi ba ne basa gani sosai ba tun lokacin da su ka fito daga Estate ɗin motar take a bayan su,a lokacin bai kawo komai a ranshi ba amma yanzu abun ya ɗan ɗaure mashi kai,ta mirror ya kalli Nainarh dake back seat idanunta a rufe kamar mai bacci.
maida duban shi yayi ga motar har lokacin tana biye da su, street ɗin da zai sada su da Estate ɗin ya shiga still motar na nan biye da su,abun ne ya fara bashi tsoro,bai fita daga wannan tsoron ba sai ga wata mota ta tunkarosu gadan gadan,yayi matuƙar mamakin ta inda motar ta ɓullo, ƙoƙarin kauce mata ya shiga yi yana mamakin ko driver motar ya rasa birkinshi ne.
duk yanda ya kai ga ƙoƙarin kauce ma wannan motar abun yaci tura,duk in da ya matsa sai motar ta bishi.
wani irin mahaukacin burki ya taka har kanshi na haɗuwa da Steering wheel lokacin da motar ta daki gaban motarshi,bai san time ɗin da ya furta innalillahi wa Innah ilaihi raji'un ba salatin da yayi ne yayi sanadiyar buɗe idon Nainarh,ɗagowar da zaiyi yaga motoci har uku sun zagaye motar su “akwai matsala” shine abun da ya furta.
Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyar su shi da Nainarh dake zaro ido kamar wacce tayi ƙarya,ɗaya bayan ɗaya wasu samari masu ƙirar majiya ƙarfi su ka shiga fitowa daga motocin suna tunkaro motar su,da sauri driver yasa ma motar Lock, nocking ƙofar su ka shiga yi lokaci ɗaya Nainarh tabi duk ta ruɗe, da sauri takai hannu da nufin buɗe ƙofar motar,driver ne yayi saurin dakatar da ita “karki buɗe madam,akwai haɗari a tattare da mutanen nan”
a ruɗe Nainarh tace “idan su ka yo harbi fa,baka ganin gun ɗin dake hannunsu ne?,mu buɗe muji abunda ya kawo su”
“karki damu madam ko sunyi harbi babu abunda zai same mu,buɗe masu yafi haɗari”
cikin tashin hankali tace
“anya kasan mi ka ke faɗa kuwa!??”
tana ɗan ɗaga murya
“na sani madam motar tanada kariya daga harsashi,bari na sanar da C M abunda ke faruwa” ya faɗa yana ciro wayar daga front pocket ɗin shi ya shiga neman Number C M ɗin,Nainarh tsabar tsoron da take

Please Login or Register in order to submit comment