Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankali cikin muryar ku ka tace “ya Naeem momy fa, wallahi bata da sa hannu”
“kar ki damu bincike ne zai tabbatar da hakan, muddin bata da sa hannu zata fita ba bu abun da zai sameta, kar ki damu kin ji” taji sanyi sosai da kalamanshi,hakan ya ɗan kwantar mata da hankali
“Erm.. Erm...” kame kame ya shiga yin gaba ɗaya shakkar amsar da zata bashi yake, daga ƙarshe dai yayi getting courege ɗin cewa “ Are u sure ko bayan da ki ka suma ba bu abunda su ka maki,Erm ina nufin ba suyi raping ɗinki ba kamar yanda Boss ɗin su yace??”
“A'a ba suyi man komai ba” tana jin yanda ya sauke ajiyar zuciya “Alhmdllh,in Sha Allah asirin su zai tonu soon” jin jina mashi kai kawai tayi
“ina wayarki?”
“tana hannun yumnah” ta bashi amsa
“ok muje ki amso man akwai abun da zan duba” ok tace, a tare su ka fice daga ɗakin bayan ya ɗauki wayarshi dake ajiye saman desk.
A parlor su ka samu su yumnah har sun soma gajiya da zaman jiran Nainarh,suna ƙarasawa parlorn Aunty Nafisat na fitowa ɗaga kitchen,kallo ɗaya ta masu ta ɗauke kai tana nufar bedroom ɗin ta,tashi ya Adnan yayi ya nufo su, wayarta dake hannun yumnah ta amsa ta miƙa ma ya Naeem ɗin, amsar wayar yayi,ƴan danne danne yayi na tsawan minti ɗaya kafin ya miƙa mata wayar,amsar wayar tayi ya Adnan kallonta yake ganin yanda hancinta da cheek ɗin ta su ka yi ja alamar tayi kuka ga idanunta da su ka ɗan kumbura.
tashi yumnah da fa'iza su ka yi,saurin kallon su ya Naeem yayi “second father za mu tafi” yumnah ta faɗa
“Auta tun yanzu,baza ku bari kuyi dinner ba?”
“A'a yaya idan mun dawo next sai mu yi” Fa'iza ta faɗa
“ok to shikenan bari nayi ma mom Jamal magana, ko kunyi sallama?”
“A'a” su ka bashi amsa
“ok bari nayi mata magana” ya faɗa yana haurawa sama zuwa bedroom ɗin nata.
da sauri Jamal ya riƙe yumnah yana faɗin “please Aunty yumnah zan biki” da sauri ita ma Aneesah tace zata bi ta
“ba ruwan,ku je ku tambayi iyayenku to” da gudu su ka ruga zuwa ɗakin Momyn ta su.
ya Naeem yana shiga ɗakin tsaye ya sameta gaban clothset ɗin ta, wayace kare a kunnenta da alama waya take amma yana turo ƙofar tayi saurin zame wayar daga kunnenta,cikin ɗakin ya ƙaraso “ki fito ku yi sallama za su tafi” ko kallon in da yake ba tayi ba ta shiga latsar wayar dake hannunta
“nafeesah magana fa nake, ki zo ku yi sallama za su tafi”
“Allah ya raka taki gona” shi ne kawai abunda tace without looking at him, with a surprise yake kallonta he never expect to hear that from her,har ya buɗe baki zai yi magana su Jamal su ka faɗo ɗakin,da gudu su ka nufeta suna faɗin “momy dan Allah mu bi su Aunty gidan big daddy??”
“A'a gobe akwai islamiyya”
“please momy sai muje daga can”
“na ce baza ku je ba” ta faɗa cikin faɗa faɗa,kallonta kawai ya Naeem dake tsaye yake
“dan Allah mom...” ko ƙaraswa ba su yi ba ta daka masu tsawa dole su ka ja baki su ka yi shiru “ku wuce kuje ku yi alwala lokacin sallah ya kusa,yara sai shegen son yawon tsiya” ficewa su ka yi daga ɗakin kamar za su sa ku ka,juyawa ya Naeem yayi shima ya fice.
tsaki taja tana faɗin aikin banza,wayarta ce tayi ƙara,da sauri tayi picking call ɗin dama bata gama wayar da take ba “sorry muna tsaka da waya kinji nayi rejecting,shigowa yayi shiyyasa” on the other side Aunty Nadeeya ta ce “mi kuma ya zo ya ce maki?”
“zuwa yayi wai za su tafi na fito muyi sallama”
“sai ki ka je?” tsaki ta ja “Allah ya kiyaye,ce mashi nayi Allah ya raka taki gona”
“haka shine dai dai wallahi,Gara da ki ka ce mashi haka”
“baza ki gane ba ne Nadeeya na tsani yarinyar nan kamar me,duk abunda ki ke faɗa akanta ban taɓa jin muguwar tsanarta ba irin yau,rungume da juna fa na gansu”
“ai nace maki yarinyar nan zubin karuwai gareta,na fa faɗa maki dadyn Enaaya ba kiga yanda ya ruɗe ba lokacin da bata da lafiya, har da wani ɗaukar Enaaya wai taje yi mata ya jiki”
“ki bar shegiya kawai zata san da mu take magana,wallahi sai tayi data sanin shigowarta Estate ɗin nan”
“lallai dole mu ɗau mataki dan irin su tsoro su ke bani,ki gansu sumi sumi kullum cikin hijabi kamar na Allah”
“karki damu,wallahi sai taci ubanta”
Ya Naeem yana fita daga bedroom ɗin parlorn ya koma, a tsaye ya same su kamar yanda ya barsu
“sorry kuna jiran mu ko,na shiga ma naga mom Jamal ɗin ta shiga toilet,sai da safe kawai ku gaishe da su mom” to kawai su ka ce suka yi mashi sallama suna nufar ƙofar fita.
Ya Adnan ma sallama yayi mashi,har bakin ƙofa ya raka su, su yumnah na fita yayi saurin kamo hannun ya Adnan,ɗan ƙasa da murya yayi “tana buƙatar wanda zai bata kulawa ta musamman, please take care of her,kasan irin wannan abun daga lokacin da aka tuna ma mutum shi sai a hankali”
“karka damu in Sha Allah, Thank you”
“ok good night”
“good night” ya faɗa yana ficewa,a parking space ya same su suna ƙoƙarin shiga motar yumnah da su ka zo,amma sai yace yumnah su tafi da Fa'iza Nainarh kuma ta shiga tashi shima gidan zashi zaije ya gaishe da mom,da to su ka amsa mashi suna shiga motar,yumnah tayi mata key su ka fice daga gidan,da kallo Nainarh ta bi motar yumnah harta ɓace ma ganinta.
front seat ya buɗe mata yana faɗin “let's go home” jiki a sanyaye ta nufo motar ta shiga, maida marfin ya yi ya rufe,driver seat ya shiga,key yayi ma motar su ka fice daga gidan, tsit motar tayi,tunda ta shiga ta kwantar da kanta jikin head rest,gaba ɗaya she was just moody,ɗan farin cikin data samu few days a go ya gushe tas ƙuncin data shiga kwanakin baya ya dawo mata sabo,ji take kamar yanzu ne komai ya faru,abunda ya ƙara jefata cikin ƙunci da damuwa yanzu jin kuma wani sabon sharrin da ake bin mahaifiyarta da yayanta dake kwance cikin kabarin sa da shi.
gyaran murya ya yi mata yana kiran sunanta, saurin kallonshi ta yi
“please Nainarh don't bother your self kinji,kar wani ciwan ya kamaki,na tabbatar in Sha Allah ya Naeem will find out the truth soon, in sha Allah they will regret” gyaɗa mashi kai kawai tayi
“ki dage da yi masu Adu'a kinji,in sha Allah everything will be ok”
“in sha Allah” ta faɗa, sosai ya shiga kwantar mata da hankali kamar yanda ya Naeem ya ce har su ka iso gida, lokacin da su ka iso su yumnah tuni sun jima da shiga ciki,parking yayi a compound,kallonta yayi “promise me baza ki sa damuwa a ranki ba,zaki saki jikin ki kamar baya??”
“in sha Allah,Nagode”
“don't mind” harta kama handle ɗin ƙofar sai kuma ta juyo tana kallonshi “sorry banyi maka godiya ba ranar nan,Nagode sosai Allah ya saka da Alkairi” murmushi ya sakar mata “karki damu you deserve more than that for me”
“thank you”
“ok good night,slept tight” gyaɗa mashi kai tayi tana faɗin “ba kace zaka gaishe da mom ba?”
“no sai da safe zan zo” gyaɗa mashi kai kawai tayi ta fice daga motar “take care” ya faɗa, sai da yaga shigewarta tukun yayi ma motar key ya bar gidan.
lokacin data shiga gidan bata samu kowa ba duk sun shige ɗakunan su saboda lokacin sallah daya gabato,ɗakin su ta nufa samun yumnah tayi tana ƙoƙarin shiga toilet.
Mom bayan da ta kammala sallah magrib part ɗin Abbah ta nufa ganin tunda su ka baro gidan Abbah bai dawo gida ba kuma har kiran shi tayi baiyi picking ba.
tayi mamakin ganin har lokacin bai dawo ba,sake kiran shi ta yi amma bai ɗauka ba,tana shirin sake kiranshi sai gashi ya shigo,da kallo ta bishi jikinshi duk a sanyaye kallo ɗaya zaka mashi ka fahimci akwai damuwa a tattare da shi.
“barka da dawowa” jin jina mata kai kawai yayi ya nufi part ɗin shi,da har ta juya zata nufi bedroom ɗinta sai kuma ta fasa,bin bayan shi tayi,zaune ta sameshi saman sofa a parlorn shi,duk sai taji wani iri ta san wannan yanayin na shi bai rasa alaƙa da ƙin amincewar da tayi akan Auren Irfan,yayi burin haka ta kasance ba dan komai ba sai dan zumuncin shi da ƴaƴan uwanshi ya ƙara ƙarfi.
har gaban sofa da yake zaune ta ƙaraso “yallaɓai lafiya,meke damunka??” ta faɗa tana kallonshi,ɗago da kanshi yayi kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai
“lafiya lau nake” shine kawai abunda yace ya miƙe ya nufi bedroom ɗin shi,da sauri ta bi bayan shi amma sai bata shiga bedroom ɗin ba ganin mamy ta buɗe ƙofar ɗakin alamar tana ciki,ta gefenta dady yabi ya shiga bedroom ɗin,kallo ɗaya mom tayi mata ta juya ta bar part ɗin gaba ɗaya,da harara mamy ta bita har ta fice.
Dady ba komai yayi sanadiyyar shigar shi wannan yanayin ba sai tashin ciwan Noor,tunda su ka kaita hospital likitocin ke kanta sai da ƙyar aka samu ta dawo hayyacinta.

*ASO VILLA*

tunda ta kammala sallah isha take zaune saman sallaya a ɗakin su Ammar wanda yanzu nan ta maida wurin zamanta.
kallo ɗaya zaka mata ka gane tana cikin farin ciki wanda rabonta da shiga irin wannan farin ciki tun farkon Auren su lokacin cikin su Ammar.
idan tana tuna wancan lokacin sai taga kamar ba ya Zaabith ɗin ta ba,kamar an sauya mata shi ne.
A yanzu fatan ta Allah yasa ta samu soyayyar shi kamar wacan lokacin,tana fatan wannan cikin ya zama sanadin da zai sauya halayensa gaba ɗaya.
shafa cikinta tayi tana saki murmushi,turo ƙofar su ka yi su ka shigo, da gudu su ka nufo inda take
“momy ba ki zo mun yi dinner ba?” Jan cheek ɗin su tayi tana faɗin “dadyn ku nake jira ya zo sai muyi tare”
“yau zai dawo ne?”
“eh yana hanya,ku tashi kuyi wanka ku zo ku canza kaya”
“momy zamu jira ya dawo”
“A'a kuyi wanka dai ku kwanta kunga gobe akwai islamiyya” to su ka ce suna miƙewa,da sauri su ka shiga zare kayan dake jikin su kowa so yake ya riga ɗan uwanshi shiga toilet,Fahimtar abunda su ke shirin yi ne yasa tayi saurin cewa
“kai Aman ka tafi bedroom ɗina Ammar ya shiga nan” sanin fitina za su mata ne yasa ta rabasu,da sauri Aman ya fice daga ɗakin Ammar kuma ya shiga nan,tana anan zaune har su ka kammala shirin na su
“oya ayi Adu'a ka kafin a kwanta” to su ka ce.
bata fice daga ɗakin ba sai da ta tabbatar sunyi bacci lokacin sha ɗaya saura,tashi tayi ya linke carpet ɗin da tayi sallah ta maida cikin wardrobe ɗin su kafin ta fice daga ɗakin zuwa bedroom ɗinta bayan ta kashe masu hasken ɗakin.
tana shiga bedroom ɗin toilet ta shiga tayi wanka,zama tayi gaban mirror bayan ta tsane jikinta,ɗan light makeup tayi kafin ta tashi ta nufi wardrobe ɗinta,wata irin haɗaɗiyar sexy silk dress red color ta ɗauko, ɗaga rigar tayi tana kallo lokacin ɗaya ta saki murmushi tana shafa flat tummy ɗinta.
a jiye rigar tayi saman bed, earrings ta ɗauko haɗe da wasu open toe pump black color.
shaf shaf ta shiga shiryawa ganin lokaci yaja kuma zai iya shigowa at any time,kayan ba ƙaramin kyau su ka yi mata ba kamar irin a club ɗin nan, ƙarema kanta kallo ta shiga yi a gaban mirror, perfume ta sake ɗauka ta feshe jikinta kafin ta fice daga bedroom ɗin bayan ta ɗauki envelope ɗin da fawar ya kawo mata, direct part ɗin shi ta nufa.
A hankali take tafiya ƙarar sautin shoes ɗinta mai ɗaukar hankali ya cika ko ina na part, a bakin ƙofar ɗakinshi ta tsaya,tura ƙofar tayi ta shiga,daddaɗan ƙamshin rose flower wanda aka ƙawata ɗakin ne ya daki hancinta,ciki ta ƙarasa hasken candles ne ya haska ɗakin,ko ina na ɗakin an ƙawata shi da roses,daga saman bed ɗin anyi zanen heart da flower,takiyar roses ɗin ta ajiye envelope ɗin,food trolley dake gefen mirror ta tura zuwa bakin bed ɗin,kallon ɗakin ta shiga yi sai data tabbatar komai dai dai tukun ta fice zuwa parlor ta zauna zaman jiran shi saman sofa.
tana anan zaune har bacci ya soma ɗaukarta bai shigo ba sai around 1 am ya shigo lokacin tuni bacci yayi awan gaba da ita,banko ƙofar parlorn yayi wanda hakan yayi sanadiyar farkawar ta daga bacci,saurin miƙewa tayi tana kallon ƙofar,cikin wani irin yanayi dake nuna yau ma a bige yake ya faɗo parlorn, direct sama ya nufa zuwa ɗakinshi bai ko lura da ita ba,tafiya yake yana layi kamar zai kifa ƙasa,da kallo ta bishi tana jin wani iri a zuciyarta,daurewa kawai tayi ta bi bayan shi,tana shiga bedroom ɗin yana faɗawa toilet,wayarsa da rigar suit ɗin sa da ya yasar saman bed ta kalla sai kuma ta kalli ƙofar toilet ɗin daya bari a buɗe.
ƙararar shigowar message taji daga wayarshi sai ga kira kuma,kallon wayar tayi da kamar zata share sai kuma ta ɗauki wayar,abunda bata taɓa ba kenan tsawan zaman su,kallon screen ɗin wayar tayi tana kallon number dake kiranshi wacce akayi serving da Ruth,da mamaki take kallon wayar yanayin da ya shigo ne ya bata ƙwarin gwiwar ɗaga wayar,kai wayar tayi kunnenta,muryar mace taji tana faɗin “Hi beb, I hope you arrived safely?,I sent you your message via WhatsApp,
When will you come back, I'm starting missin you,Please come back soon, I won't drunk anything again until you come back”
Wani irin faɗuwa gabanta yayi ji abun da mai kiran nashi tace,da sauri ta zame wayar daga kunenta tana rejecting kiran,kallo wayar ta shiga yi sai kuma ta ɗaga ido ta kalli ƙofar toilet ɗin,wani message ɗin ne ya sake shigowa wayar via WhatsApp,saurin shiga message ɗin tayi direct ya kaita WhatsApp ɗin shi,wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi lokacin da taci karo da wasu irin nudes masu muni da aka turo mashi da sauri ta dafe saitin zuciyarta,zama tayi gefen bed ba tare da ta shiryama hakan ba,scrolling chart ɗin tayi zuwa can sama,abun da taga gani ma yafi wanda aka turo mashi yanzu muni,gaba ɗaya abunda su ke yi a chart ɗin kenan, maganganun da su ka yi basa da wani yawa suma gaba ɗaya porn yafi yawa a ciki ,saurin fita tayi daga chart ɗin,ɗaya bayan ɗaya ta shiga buɗe charts ɗin dake WhatsApp ɗin shi,ƴan mata ne yake chart da su iri iri wasu ma ba musulmai ba ne,saurin fita tayi daga WhatsApp ɗin gaba ɗaya tana sake dafe zuciyarta dake neman fasa ƙirjinta ta fito,tuni hawaye sun wanke fuskarta,bata taɓa dana sanin Auren Zaabith a rayuwarta ba sai yau,tayi takaicin haɗa zuri'a dashi,wata irin muguwar tsanar shi ce ta rufeta,gaba ɗaya farin cikin da take ciki ya rikiɗe zuwa tsantsar ɓacin rai,wani irin haushin cikin dake jikinta take ji yanzu,ga ƙyamar jikinta da take ji,miƙewa tayi rai a ɓace ta nufi ƙofar fita da wayarshi a hannunta,harta kama handle taji fitowar shi daga toilet.
daga shi sai short ya fito,kallon bayanta yayi,wani irin makirin murmushi ya saki,he is staggering ya nufo inda take,hannunshi ya kai saman bayanta,cike da salon iskanci ya matsa ass ɗinta yana wani sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi yana kai hannu ya kama shoulder ɗinta,a wani irin fusace ta juyo baiyi aune ba sai ji yayi ta sauke masa lafiyyun maruka a cheek,saurin dafe cheek ɗinshi yayi yana binta da idanunsa da kallo ɗaya zaka masu gane he is drunk,sun ƙanƙance tsabar jaraba,kallota yake kamar zai faɗo mata, rai a ɓace cike da tsana take kallonshi from head to toe
“kar ka ƙara kuskuren taɓani,na tsaneka” ta faɗa cikin ɗaga murya,turo baki yayi yana sa ɗayan hannunshi ya tallabo kumatunshi kamar ƙaramin yaron,cikin ƙunar rai take faɗin
“wallahi na tsaneka,bana son ganin ka,banyi tunanin bayan shaye shaye kai mazinaci ba ne,ban san cewa kai fasiƙi ba ne,nayi dana sanin kasancewata matarka na tsawan shekaru,nayi takaicin tara zuri'a da kai,ina baƙin cikin kasancewarka ɗan uwana,fasiƙi,mazinaci kawai, wallahi na tsaneka” with heartbrok take faɗin wannan kalaman hawaye na bin cheek ɗinta,shi kuwa binta kawai yake da ido ba wai dan yana fahimtar abunda take faɗa ba ne.
“na tsaneka, I hate yo you,na gama zama da kai,our marriage is over, ka sawwaƙe man,bazan cigaba da zama da kai ba wallahi” ku ka take sosai tana faɗin ya saketa amma kamar ba dashi take magana ba,tunda ya kafe bakinta da ido ko motsi baya yi.
Jifa tayi da wayarshi dake hannunta,saurin kallon wayar yayi sai kuma ya kalleta,ɓata fuska yayi kamar zaiyi ku ka,sai kuma ya nufota yana buɗe mata hannayenshi yana faɗi “ohh... noo ... ooo wife ta... ta.. yi fushi,why a... are ...
... y u o an... angry, so so sooooryyy stop cary pleaseeeeee” ya faɗa kamar mai koyan magana yana kai hannunshi da nufin hugging ɗinta.
A fusace tasa hannu biyu ta hankaɗeshi har sai da yayi tag taga zai faɗi
“stay away from me, I hate you” ta faɗa tana ɗaga mashi murya, fashe mata da ku ka yayi kamar ƙaramin yaro can kuma ya kwashe da dariya.
wani irin abu ne ya tsaya mata a maƙoshi,tsaki kawai taja tana faɗin “i hate your attitude” buɗe ƙofar ɗakin tayi zata fita,wani irin fisgota yayi jikinsh,zare ido ta shiga yi a fuskarshi gabanta na wani irin duka dan ba ƙaramin tsorata tayi ba.
Lumshe ido yayi kaɗan ya buɗe yana kai hancinshi saman shoulder ɗinta,ƙamshin perfume ɗin dake jikinta ya shaƙa “you smeal damn sexxy,i miss u beb” wani irin baƙin ciki ne ya rufeta jin abin da ya ce.
ko kawar kwace kanta ta shiga yi daga rikon da ya yi mata amma ina yaki ya sake ta,ganin ta kasa ne yasa ta shiga kai mashi duka tana kuka
“stop beating me wife,I miss you,I need to have...”sai kuma yayi shiru bai karasa ba,cizo ta kai mashi arm ɗinshi da sauri ya saketa “na tsane ka har abada ba ni ba kai”
ganin ta na ƙoƙarin fita daga ɗakin ne ya sa ya fizgota a karo na biyu,jifa yayi da ita saman bed kamar ba shi ba.
idanunta ne suka sauka a kan short ɗin da ke jikin shi,saurin kauda kai tayi gabanta na wani irin faɗuwa,da sauri ta yunkura zata sauka daga saman bed din, sai dai kafin ta sauka tuni yayo kanta, gaba ɗaya ya faɗa kanta, zare ido ta shiga yi gabanta na wani irin duka, duƙo da fuskarshi yayi zuwa tata da nufin manne bakinshi da nata.
saurin kauda fuskarta tayi, kokawa ta shiga yi da shi don ta ƙwace kanta amma ta kasa.
duk da he is drunk karfin mace da namiji is not decem,without anything ya afka mata like animal,gaba daya rigar dake jikinta ya maida ta feses ya yi jifa da ita haka short ɗin dake jikin shi.
duka,cizo da yakushi babu wanda bata kai mashi tana faɗin I hate you amma duk a banza,kamar zai kashe ta yake faɗin “why are you angry,stop angry” ganin ba sarki sai Allah ne yasa ta fara bashi haƙuri tana haɗa shi da Allah amma ina kwata kwata bai san tana yi ba, baya ma tare da ita, banda kalmar i love you babu abinda ke fita daga bakin shi,tun tana da bakin bashi hakuri har bakinta ya mutu sai hawaye kawai dake bin cheek ɗinta.
sai da ta dawo ko numfashi da kyar take fitar da shi tukun ya kyaleta bayan yayi satisfy.
Can gefe ya koma yana sauke ajiyar zuciya cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba da shi.
Ta kai tsawan 30 minutes a kwance ko ɗan yatsanta bata iya ɗagawa,ga wani abu da ya zo saitin mararta ya tsaya mata kamar dutse.
gaba ɗaya jin jikinta take kamar an watsa mata ɗanyen barkono tsabar baƙin ciki da takaicin kusantar ta da yayi,da kyar ta yi getting courage ta sauka daga saman bed ɗin.
da sauri ta durƙushe ƙasa saboda kulle matan da mararta yayi ga wani irin azabiben ciwo da take ji ƙasa ƙasa, da kyar da jan ƙafa ta fice daga ɗakin.
bedroom ɗin ta ta nufa, tana shiga hijab ɗinta da ke cikin wardrobe wacce tayi sallah ta ɗauka, zura hijab ɗin tayi a jikinta, da dafa bango ta fice daga ɗakin,lokacin da ta isa compound ɗai ɗaikun securitys ne ke kai kawo, da gudu ɗaya daga cikin su ya nufota yana tambayar lafiya da ƙyar ta iya furta mishi yayi ma driver magana, da gudu ya juya sai gashi tare da drivers har su uku,mota ta sa suka ɗauko, kyar ta ɗaga kafarta ta shiga mota.
cike da tashin hankali securitys ɗin su ke kallon inda ta tsaya,key driver yayi ma motar yana faɗin ina za su
gida tace mashi, ɗan juyowa driver yayi ya kalleta, cike da ladabi yace “amma madam a irin wannan yanayin da ki ke hospital ya kamata mu tafi” da ƙyar ta iya karfin halin ce mashi yayi abinda tace,toh kawai yace yana reverse su ka nufi gate motar securitys biyu na gaba biyu na baya su ka fice daga Villa ɗin.

*Queen Kainart*💫

Ringing din wayar ta ne ya tashe ta,firgigit ta farka tana faɗin innalillahi wa inna ilaihir raji'un saboda ringing ɗin wayar har cikin kwakwalwarta kasancewar wayar tana ajiye ne a saitin kunnenta.
da sauri ta tashi zaune tana kai hannunta ta kunna bedside lamp haske ya ɗan gauraye ɗakin,kallon agogon da ke manne jikin bango tayi wanda ke nuna karfe huɗu da arba'in da biyu na dare,kallon yumnah dake kwance gefen ta tana bacci tayi lokacin har kiran ya katse wani ya sake shigowa.
a hankali ta ɗauki wayar tana duba mai kiran nata privet number ta gani alamar mai kiran yayi hiding number ne.
Bin screen ɗin wayar da ido tayi tana mamakin waye wannan yake kiranta a irin wannan lokacin kuma da ɓoyayyar number,har kiran ya sake katsewa bata yi picking ba.
wani kiran ne ya sake shigowa wayar a karo na uku still da ɓoyayyen Number, shahada kawai tayi ta ɗaga tana ambatar bismillah.
shiru tayi tana sauraron me na cikin wayar zai faɗa, amma taji anyi shiru, jin anyi shirun ne yasa tayi ƙarfin halin cewa “Assalamu Alaikum” on the other side taji muryar da koda za tayi shekaru ɗari bata ji ta ba bazata ɓacemata ba ance “Nainarh!” wani irin duka kirjinta yayi har sai da ta dafe saitin zuciyar ta, janye wayar ta yi daga kunnenta tana kallon wayar don ta tabbatar da abunda ta ji gaskiya ne.
kallon wuyar take sosai ga alamar time nan yana tafiya na kira,da gaske dai abunda taji gaskiya ne,da sauri ta maida wayar a kunnen ta
“Y... ... ya... .. Abid” shi ne sunan da ta ambata cikin rawar murya, kallo ɗaya zaka mata ka hango ruɗani da tsoron da take a ciki
“na'am ƙanwata, kin yi mamakin jin murya ta ne?”
“ya Abid dama kana raye!?” ta faɗa tana zaro ido kamar wacce tayi ma sarki ƙarya
“ƙwarai Nainarh,ina nan a raye”
“amma ya Abid aka ce ka mutu,kuma mutane da yawa sun shaida mutuwarka??”
“haka ne Nainarh amma ina nan a raye”
“don allah ka faɗa man miye ya faru da kai akace ka mutu,kenan daddy na ma yana raye??”
“labari ne mai tsayi Nainarh”
“dady na fa,shima bai mutu ba kamar kai?”
“Allah kaɗai ya san gaskiya Nainarh”
yanayin fuskarta ne ya canza lokaci daya, hawaye har sun taru a idanunta fatan ta ace shima dadyn ta bai mutu ba kamar yayanta
“ina fata Nainarh duk wani bayani da ya kamata kinyi ma CM baki ɓoye mishi komai ba”
“waye cm kuma ya abid?” ta faɗa cikin rashin fahimtar wa yake nufi
“Colonel Major naeem nake nufi,ba ya gayyace ki gidansa ba har yayi miki tambayoyi ina fatan biki ɓoye mishi komai ba har flash ɗin da uncle ya baki kin basa??”
tunda ya fara magana tayi shock,ko motsi ta kasa yi,mamakin ta duk a ina yasan wannan “ina fatan kin basa Nainarh,hakan da zaki yi shi kaɗai zai taimake momyn ki dani kaina”
da kyar ta iya buɗe baki tace “amma ya Abid taya akai ka sani”
“ki ajiye wannan tambayar a gefe ba shine mai mahimmanci ba a yanzu, kin basa flash ɗin ko baki ba sa ba??” wani irin faɗuwa

Please Login or Register in order to submit comment