Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Naeem Abbah ya yi yace ya rufe masu taro da Adu'a,miƙewa yayi Naeem yayi
“Abbah ina ne Alfarma kafin a rufe taro” mom ta faɗa kanta a ƙasa,gaba ɗaya parlorn su ka kai dubansu gareta,wani irin mummunan faɗuwa gaban Irfan yayi haka ma Noor dady kuwa zuba mata ido kawai yayi
“muna jinki Zulaihart, wace irin alfarma ki ke nema,faɗi muna saurarenki”
dady sai kallonta yake burin shi ta ɗago ta kalle shi ko ya hanata abun da take shirin yi amma taƙi bashi Accesse ɗin da zai yi hakan
“ina mai baku haƙuri gaba ɗayan ku,Alfarmar da nake nema ba lallai taima wasu daga cikin ku daɗi,amma ina fatan ku fahimce ni ku kuma yi man uzuri”
“ba komai Zulaihart muna sauraren ki” kallon su uncle Ahmad tayi
“a karo na biyu ina mai sake baku haƙuri,ban so a wannan karan nayi jayayya akan wannan hukunci da ku ka yanke ba amma ya zama dole,Irfan ɗanku ne kun isa ku yanke ko wane irin hukunci akansa,amma a matsayina na mahaifiyar shi ina neman alfarma maganar Auren shi da Noor a barta” dady ne yayi saurin cewa
“amma Abbah tana so...” saurin dakatar da shi Abbah yayi “barta tayi magana” shiru dady yayi,yana jin wani iri a ranshi bai taɓa tunanin haka daga gareta ba,Abbah dama tunda ta shigo part ɗin ya fahimci kamar akwai abunda yake damunta,sai yanzu ya fahimci mike damunta,tunda ya ke da ita wannan ne karan farko data nuna hukuncin da ya yanke bai mata ba,har ta kasa haƙuri ta iya faɗa da bakinta,ko bikin su ya Naeem bata so ba amma tayi haƙuri,a wannan karan ya kamata suyi mata uzuri kamar yanda ta buƙata
“ba'a san raina naƙi amincewa da umarnin ku ba sai dai bani da wani zaɓi ne,ni kaina zan so zumuncina da mutallab ya ƙara ƙarfi sai dai haƙura da Auren shi ne mafi Alkairi sama da ɗaura shi,nayi haƙuri na jure komai da Auren Naeem sai dai a wannan karon nakasa wannan haƙurin da juriyar,ku gafarce ni idan har alfarmar dana nema batai maku daɗi ba,ina mai baku haƙuri,banyi hakan da nufin wani abu ba”
“babu komai Zulaihart ai ɗanki ne,babu wanda zai mashi Auren da baki amince da shi ba,babu damuwa Allah yasa hakan shi ya fi zama Alkairi”
Irfan tunda Abbah ya faɗi haka wata irin zufar tashin hankali ta rufe shi,gaba ɗaya ji yayi duniyar ta daina mashi daɗi,Noor ma maƙale momynta ta yi jikinta na wani irin shaking kamar wacce fever ta kama,su uncle Mustafa babu wanda maganar mom tayi ma daɗi,amma duba da abunda ya faru rannan a gaban su sai su ka yi mata uzuri,wannan ne karan farko data taɓa nuna ƙin amincewarta akan wani abu.
mom fatilah har wani sauke Ajiyar zuciya take tana sakin murmushi,su mamy babu wanda fasa Auren bai ma daɗi ba,kallon juna su ka yi ita da mom halima suna sakin murmushi,ba ƙaramin daɗi suka ji ba.
tashi ya Naeem yayi ya rufe masu taron da Adu'a kamar yanda Abbah ya bashi umarni,yana kammalawa matan su ka fara tashi suna fita.
kama hannun Noor mom fatilah tayi amma taƙi tashi, duƙawa tayi tana kallonta “Noor lafiya, tashi mu tafi mana” kallon Momyn ta ta tayi numfashinta na sama da ƙasa
“Noor lafiya?” ta faɗa tana jijjigata ganin yanda ta fara gasping Kamar breath ɗinta zai ɗauke she's asthmatic since she was a child
kamota tayi ta ɗago da ita amma kwata kwata jikinta ba ƙwari gaba ɗaya ta koma ƙasa gasping ɗin da take na tsananta,dafe chest ɗinta tayi,hankalin mom Fatilah ba ƙaramin tashi yayi ba,hankali a tashe ta shiga kiran sunanta gaba ɗaya su dady su ka yo kansu su mom har sun fice ba su san ma mike faruwa ba, hankali a tashe uncle Mustafa ya shiga yi mata fifita da gefen rigarsa,ƙirjinta sai sama yake yana ƙasa,Irfan kasa motsi yayi daga in da yake zaune,shi kanshi bazai iya cewa ga taƙamaimai yanda yake ji.
ruwa uncle mutallaf ya shiga bata amma ina numfashinta neman ɗaukewa yake,hannu biyu uncle Mustafa yasa ya ɗauketa,ficewa yayi da ita daga parlorn gaba ɗaya su ka bi bayan shi Irfan da Waseef kawai aka bari,magana yake ma Irfan ɗin amma kamar baya hayyacin sa,kama hannunshi yayi su ka fice daga parlorn,lokacin da su ka zo parking space da yawan su sun tafi gida mom ma sun tafi ita da su Aunty laatifa da Aunty Kainart da za taje gidan saboda Laatifa,gaba ɗaya ta sanar da ita abunda ya faru bata ɓoye mata ba,su dady kuma hospital su ka nufa tare da Noor, Nainarh da yumnah da Fa'iza kuma sun wuce gidan ya Naeem wanda shi yace Nainarh ta sameshi su ka rakata.

♠♣♠♣♠♣♠♣♣

“haba laatifa mi yasa zaki man haka,kin tada man hankali sosai”mom maimunatu ta faɗa wacce a gidan su ka sameta tunda taga text ɗin da mom ta tura mata kancewa laatifa na nan ta wanko ƙafa ta zo.
“kiyi haƙuri mom ba ni da wanni zaɓin ne bayan nayi nesa da ku, bazan juri ganin tsanar da mahaifina yayi man ba”
“amma ai Laatifa sai ki duba halin da ni zan shiga idan babu ke”
“yanzu kiyi haƙuri maimunatu tunda har Allah ya sa su ka yi shawarar cewa ta zo nan ta kwana,kiyi haƙuri ba inda Laatifa zata tafi ta barki” mom ta faɗa
“hakane mom, ba tayi shawara da kowa ba ne shiyyasa amma da ba zamu bari har Sam yayi mata booking flight ba” kainart ta faɗa tana sake kwantar ma mom maimunatu da hankali
“yanzu ya jikin balqis ɗin naji barrister yace bata jin daɗi” mom ta faɗa
“wacece kuma Balqis,ni ban sani ba,na bar masa gidansa da yarsa tun jiyan”
gaba ɗaya su ka kalleta jin abunda tace “amma munarh saboda me,bai kamata ace kin bar gidan saboda haka ba” mom ta faɗa cike da nuna rashin jin daɗinta akan abun
“zulaihart ba za ki gane ba,Hashim ya wuce inda ki ke tunani shiyyasa kawai na yanke shawarar rabuwa da shi”
“kul karki faɗi haka dan Allah,ko dan saboda ƴaƴanki ai kya zauna,duba fa ki ga shekarunki,dan Allah dai kiyi haƙuri”
“duka yaran nawa ne, Laatifa ce kuma laatifa ba yarinya bace,Ni gaskiya na gama zama da hashim har abada”
“dan Allah momy kiyi haƙuri,bazan ji daɗi ki kashe Aurenki saboda ni ba,dan Allah kiyi haƙuri ki koma”
“eh momy dan Allah haƙuri za kiyi”Kainart ta faɗa
“shikenan naji amma ba yanzu ba sai nayi shawara”
“mom...” saurin dakatar da Laatifa dake shirin magana tayi “ba yanzu ba,faƙat na gama magana” ta faɗa tana ɗaure fuska da ido mom tayi mata alama data ba su waje,tashi su ka yi ita da kainart su ka fice daga ɗakin zuwa main parlor.
wayar kainart ce ta fara ringing,da sauri ta zura hannu cikin jakar ta fito da wayar,duba sunan mai kira tayi,Dr fawar shine sunan daya bayyana a gaban screen ɗin, picking call ɗin tayi tana kara wayar a kunne.
amsa sallamar da fawar ɗin yayi mata ta yi kafin tace “ok ka iso?” on the other side fawar yace mata eh
“ok kana iya shigowa” da ok ya amsa mata yana rejecting kiran.
“wai mi fawar ɗin zai maki ne,ko baki da lafiya ne?” Laatifa ta faɗa tana kallon kainart ɗin
“for now lafiyata lau, result ɗin gwajin da yayi man zai kawo man”
“ai nayi tunanin an wuce wurin tun time ɗin daya baki magani?”
“nima nayi tunanin haka,to sai daga baya ya kirani yace man wai ya gano wani abu amma ni kaɗai yake son faɗamawa,wallahi shiyyasa duk nabi na damu Allah yasa ba wata mummunar cutar ba ce ta kamani ba”
“in sha Allah babu wani abu sai Alkairi”
“Allah ya sa” kainart ɗin ta faɗa,da sauri su ka kalli ƙofar shigowa adalilin sallamar da suka ji anyi, Dr fawar ne ya shigo cikin shigar pathani Suit golding yellow haɗe da White trouser,kanshi yasha gyara sumar sai wani sheƙi take,ga wani haɗaɗɗen jutti dake sanye a ƙafarshi kalar rigar,sosai ya fito a ba indiyen shi sak, sallamar da yayi su ka amsa,cikin parlorn ya ƙaraso fuskar shi ɗauke da murmushi,hannunshi ya haɗa waje ɗaya yana faɗin 🙏 “Namaste” murmushi su kayi gaba ɗayan su Laatifa na faɗin “namaste too” kwashewa kainart tayi da dariya,zaro ido fawar yayi yana kallon laatifa,dan da ya shigo sam bai lura da ita ba
“vaah lateefa tum bahut sundar lag rahee ho” ya faɗa yana haɗe fingers ɗin shi biyu👌,saurin kallon jikinta tayi sai kuma ta kalleshi tana faɗin “ni kar ka zageni fawar” dan bata fahimci mi yace ba,fashewa yayi da dariya kainart ma dariyar take,cikin parlorn ya ƙaraso,zama yayi saman sofa yana faɗin “ni na isa nayi insulting naki,kawai u look beautiful” girgiza kai tayi tana faɗin “ban yarda da kai ba, kai dai kawai ka zage ni dan ka san ba gane abunda ka ke faɗa nake ba” murmushi kawai yayi without saying anything to her
“good evening fawar” kainart ta faɗa murmushi ya saki “evening,how are you”
“Alhmdllh” ta faɗa,gaisawa su ka yi da laatifa,wayar landline dake parlorn ta ɗauka, dialing number kitchen tayi ta bada umarnin a kawo mashi ruwa da lemu.
“sorry fa na shiga lokacinki” ya faɗa yana kallon kainart
“ba komai fawar,Allah dai yasa lafiya?”
“lafiya lau” ya faɗa yana zaro wata envelope daga cikin aljihun shi,miƙa mata yayi,amsa tayi tana kallonshi
“za ki iya buɗewa” ya faɗa,buɗe envelope ɗin tayi pepar dake ciki ta ciro,buɗe takardar tayi abunda ke ciki ta shiga karantarwa,da sauri ta ɗago tana kallon Dr fawar ɗin bayan ta kammala karantawa, murmushi ya sakar mata yana faɗin “congratulations mrs Zaabith” murmushi ta saki a lokaci ɗaya hawaye na zuba daga idanunta, bata taɓa expecting wannan ne dalilin kiran nata da yayi ba
“thank you so much fawar, amma mi yasa baka sanar da ni tun tuni ba?”
“because Ina so na amshi tukwici na da kaina ne” murmushi ta saki
“karka da mu gaskiya am really happy, thank you”
“don't mind mrs zaabith,but sai dai ban sanar da sir ba”
“hakan yayi, thank you” murmushi ya sakar mata,bin su da ido kawai laatifa take ba tare da tasa masu baki ba,ɗaya daga cikin chefs ɗin gidan ce ta shigo hannunta ɗauke da tray data ɗauko ma fawar ruwa da lemu sai cup cake, cikin parlorn ta ƙaraso cike da girmamawa ta gaishe da shi kafin ta fice,Laatifa ta zuba mashi lemu a cup ta miƙa mashi, murmushi ya saki yana faɗin “thank you Jaan” murmushi kawai ta saki tana girgiza mashi kai, ta rasa mi yasa fawar yake mata haka shi bilhaƙƙi sonta ya ke,ita kuma bazata iya soyayya da age mate ɗinta ba dan idan bata girmeshi ba za su yi sa'anin juna.
ya jima sosai a gidan banda tsokanar Laatifa babu abunda ya ke Kainart kuwa kallo ɗaya zaka mata ka hango tsantsar farin cikin da take ciki, sai da yamma tayi sosai tukun ya tafi, har parking space Laatifa ta rakashi sai da taga tafiyar shi tukun ta dawo.
zama ta yi kusa da Kainart ɗin tana faɗin “da alama abun farin ciki ne ya faru ba kamar yanda mu kayi tunani ba?” murmushi Kainart ɗin ta saki tana miƙa mata envelope ɗin tana faɗin “laatifa am pregnant, four months pregnant” with a shock laatifa ke kallonta ba tare ma data buɗe envelope ɗin ba
“am really happy, na san wannan news ɗin zai tashi kan ya Zaabith,am eager to tell him this news” wani kallo Laatifa ta shiga binta da shi kafin ta ce “ke yanzu har farin ciki ki ke zaki sake haihuwa da ya zaabith?”
“ban gane ba, da baƙin ciki ki ke so nayi?” girgiza mata kai Laatifa tayi ganin kamar ranta ya ɓaci kuma ta san komai zata faɗa mata ba wai zata fahimta bane,ta riga ta gama mutuwa akan ya Zaabith
“congratulations,Allah ya kawo mana shi ko ita duniya lafiya” Laatifa ta faɗa
“Ameen my best” Kainart ɗin ta faɗa tana sakin murmushi.

*second father's house*
Tunda su ka shigo gidan a zaune suke a parlor,Aunty Nafisat kusan a tare su ka shigo da ita tunda ta haura sama bata sake fitowa ba Jamal da Aneeserh ne kawai su ke zaune kusa da yumnah yayinda Fa'iza ke can ɗan nesa da su tana amsa waya, za su yi 30 minutes da zuwa gidan amma har time ya Naeem bai shigo ba.
Nainarh tunda su ka shigo ta nemi wuri ta zauna tayi shiru,bakomai ke yawo a kanta ba face message ɗin da aka turo mata jiya,abun ya tsaya mata a zuciya,miye manufar message ɗin waye ke mata barazana dan kai tsaye baza ta kira shi da kashedi ba, suna a haka ya Naeem ɗin ya shigo tare da ya Adnan.
“afuwan na barku kuna jirana” ya faɗa yayinda yake nufa wani corridor,ya Adnan kuma ya ƙaraso cikin parlorn
zama yayi a saman sofa dake facing wacce Nainarh ke zaune.
gaishe da shi su ka shiga yi yana amsa masu cikin kulawa
“ya jikin ki Nainarh?” ya faɗa
“naji sauƙi”
“Allah ya ƙara afuwa” da Ameen ta amsa mashi,wayar shi ya Naeem ya kira kan ya tura mashi Nainarh, da kanshi ya rakata har baki ƙofar ɗakin da ya Naeem ɗin yake ciki tukun ya koma parlor.
a hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta shiga.
ɗan madaidaicin ɗaki ne mai ɗauke da desk da chair kamar investigation room,a tsaye ta hango ya Naeem ɗin a gaban wata ƴar book shelv mai ɗauke da tarin books da files.
wani files ya ɗauko,chair dake gaban table ɗin ya nufa ya zauna yana nuna mata wacce ke kallon wacce yake zaune,zama tayi sai satar kallon ɗakin take, gyaran murya yayi mata hakan yasa ta maida hankalinta gare shi.
“Nainarh!” ya kira sunanta
“ba komai ya sa nace ki zo gida ki same ni ba sai wasu ƴan tambayoyi da nake son yi maki,kuma ina fatan zaki bani haɗin kai kamar yanda ki ka faɗa a baya?”
“in sha Allah nayi alƙawari”
“masha Allah,kafin na maki ƴan tambayoyi zaki iya shaida waɗannan fuskokin?” ya faɗa yana zaro wasu photona guda uku daga cikin file ɗin dake gaban shi,tura mata su yayi a gabanta.
da sauri ta kai hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin hotunan,wani magidanci ne da aƙalla zai kai kimanin shekaru 57 zuwa 60 a duniya yana sanye da police uniform,dan da nan hawaye ya kawo idonta,kallon hoton ta shiga yi bata ko ƙiftawa,hawayen da su ka taru a idonta ne su ka shiga zubowa, gyaran murya ya Naeem ɗin yayi mata,ɗago idanunta tayi ta kalleshi “zaki iya faɗa man ko waye shi” da sauri ta sa hannu ta goge hawayen dake zuba daga idonta “ko zanyi shekara 100 banga mahaifina ba duk ranar dana ganshi zan iya gane shi” jinjina kai ya Naeem
“masha Allah” ya faɗa yana ɗaukar ɗayan hoton yace “wannan fa,zaki iya shaida wanene”
“uncle Abdulrashid ne,shine A C P daddy,sati biyu da mutawarshi su ka zo har gida su ka kashe daddy”
“good,miye alaƙarshi da dadynki bayan ta aiki?”
“tamkar ɗan uwa haka yake a wurin dady”
ta kai ƙarshen maganar hawaye na zuba daga idanunta,tissue ya bata ta goge fuskarta
“sorry about that” ya faɗa yana ɗauko mata wani hoton
“sunan sa Inspector Hussain, wurin aikin su ɗaya da dady”
“akwai wata alaƙa tsakanin su kamar A C P?”
“babu wata alaƙa tsakaninsu bayanta uban gida da yaronshi” jinjina kai ya Naeem yayi,duk wani abu da take faɗa yana recording a wayarsa dake ajiye saman table ɗin
“akwai wani saurayi da akace yana yawan zuwa gidan ku,kuma ance basa ga maciji da dadynki,ko zaki iya faɗaman miye alƙarshi da mahaifinki?”
hannu tasa ta goge hawayen da su ka kasa tsaya mata mutuwar mahaifinta abu ne wanda ta kasa mantawa da shi duk ta tuna sai ta zubar da ƙwallah
“ina jinki miye sunansa sannan miye alƙarshi da dadynki??”
“cousin ɗina ne,ɗan yayar momy ne,sunansa Abid,babu wata alaƙa tsakanin shi da dady kawai basa jituwa ne saboda dady baya son halayen ya Abid”
“good,miye gaskiyar kasuwancin da aka ce momynki da Abid ɗin suna yi”
“iya abunda na sani momy suna business ita da Aunty Fatima mahaifiyar ya Abid wanda shi yake kula masu da shi”
“wane irin business ne?”
“gaskiya ban sani ba” jinjina kai ya Naeem yayi
“a binciken Court an tabbatar da Abid yana smuggle drugs Wanda akwai sa hannun mahaifiyarki a ciki!” ya faɗa yana tsareta da ido.
wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi jin abunda ya Naeem ya faɗa, sosai hankalinta ya tashi tunda take bata taɓa jin wannan mummunan furucin akan momynta ba dan duk abunda ya faru a Court ba wai ta sani ba ne.
ganin yanda yanayinta ya canza ne da shirun data yi yasa ya Naeem cewa “karki manta kinyi man alƙawarin zaki faɗi gaskiya kuma faɗar gaskiyar ita zata tona asirin wanda su ka kashe dadynki da A C P Abdulrashid”
“wallahi ban san komai game da business ɗin su ba,hasali ma babu wanda ya taɓa faɗa man kalar business ɗin da su ke” kallonta ya Naeem yake kamar mai observing wani abu a fuskarta ko kalamanta
“kar ki ɓoye man komai Nainarh,ki sani mahaifinki mutumin kirki ne bai kamata ki rufa ma wani asiri a kisan shi ba” fashewa tayi da ku ka, cikin muryar ku ka take faɗin “ba bu abunda na ɓoye maka, wallahi iya abunda na sani kenan” ta faɗa tana sake rushewa da wani kukan, ba komai ya sata ku ka ba sai jin wani sabon sharrin da ake bin mahaifiyarta da yayanta da shi.
tashi yayi daga mazaunin shi ya nufi ɗan madaidaicin fridge ɗin dake room ɗin, water bottle ya ɗauko mata tare da cup, dawowa yayi ya zauna,zuba mata ruwan yayi ya miƙa mata.
amsar ruwan tayi ta sha duk da haka bata fasa kukan ba, tissue ya sake miƙa mata yana faɗin “sorry kukan ya isa haka” lallashinta ya shiga yi har tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya
“ko zaki iya sanar da ni abunda ya faru a ranar da dadynki ya rasu”
muryarta gaba ɗaya tayi laushe irin ta wanda yasha ku ka sosai “ina sauraronki mi ya faru a ranar??” jan hanci tayi kafin tace “ba komai na sani a game da abunda ya faru ba”
“ba damuwa faɗa man iya abunda ki ka sani” gyaɗa kai tayi tana goge hawayen fuskarta
“a ranar da misalin ƙarfe biyu na dare,ina tsaka da bacci aka banko ƙofar ɗaki na,a firgice na farka saboda ƙarar dukan ƙofan,wasu irin jibga jibgan maza ne su huɗu na gani a cikin ɗakina,ɗaya daga cikin su ne ya daka man tsawa yace na sauko daga saman bed,a gigice na sauko jikina na' ɓari,mutum biyu su ka tasani har main parlor biyu kuma suka shiga bincike ɗakin,a main parlor na samu momy da dady wanda wasu maza guda biyu su ka rirriƙe,momy kuma wani na tsaye a kanta da gun yayinda wani ke zaune saman sofa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya hannunshi riƙe da gun ga wasu maza majiya ƙarfi dake tsaye dama da hagunshi dukkansu gun's ne a hannunsu,da gudu na nufi dady ina kuka ina tambayarshi mi ke faruwa, murmushi dady yayi man yana faɗin na kwantar da hankalina ba bu komai,tsawa wanda yake zaune saman sofa ya daka mana,da sauri na ɓoye bayan dady saboda na tsorata sosai,in da muke ya nufo ko ina na jikinshi na motsi,ƙato ne sosai dan duk yafi mazan dake wurin girma,duƙawa yayi a gaban mu yana kallona sai kuma ya kalli dady yana sakin wata irin dariya mara daɗin jin yace wato dady ya zaɓi ya turashi inda ya tura A C P Abdulrasheed sama da ya faɗa masu gaskiya, murmushi dady yayi mashi yana faɗin in dai akan rayukan bayin Allah ne da ba suji ba basu gani ba barazanar su baza ta taɓa tsoratar da shi,wannan furuci na dady yayi matuƙar ɓata ranshi hakan yasa yasa yaranshi su ka rufe dady da duka,Ni da momy kuka muke muna roƙonsu amma babu wanda ya saurare mu,sai da su ka yima dady dukan mutuwa,duk sai da su ka sauya mashi kamanni amma hakan bai sa dady ya miƙa wuya yayi masu abunda su ke so ba,roƙon dady muka shiga yi ni da momy kan ya basu abunda su ke so amma yace muyi haƙuri basu isa suyi mashi abunda Allah bai nufa ba,muna a haka sai ga mazan dake can sama sun shigo da laptop ɗin mu duka da duk wani flash da su ka samu a gidan da wasu files wanda daga ɗakin dady su ka ɗauko su,Boss ɗin su da ya koma kan sofa su ka nufa,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga bincike laptop ɗin mu bayan sun sa mun cire masu password duk da dady sai da ƙyar su ka samu ya cire nashi password ɗin,jifa yayi da laptop ɗina data momy bayan ya tabbatar da babu wani abu da zai amfane shi a ciki,wani Flash ya ciro daga cikin aljihun rigar sa yasa a system ɗin dady,yaran shi ya ba system ɗin su ka fice da ita bayan ya gama ɗaukar duk wani abu da zai ɗauka,files ɗin da su ka ɗauko daga ɗakin dady ya shiga dubawa,sai da ya du basu tas tukun yasa masu wuta ya ƙone su duka,dady harda ƙwallarshi saboda mahimmancin files ɗin da su ka ƙona,tasowa yayi ya dawo in da dady yake,ɗago da kanshi yayi yana kallonshi fuskar shi a ɗaure,ba muyi aune ba muka ji ya sauke ma dady lafiyayyun maruka har biyu ya kuma rufe shi da duka,da gudu na nufi dady ina kuka ina haɗa mutumin da Allah kan ya ƙyale dady,fisgo gashin kaina yayi ban san lokacin dana fasa ƙara ba saboda azaba,yaran shi dake wurin yace...”
Kasa ƙarasawa tayi saboda shaking ɗin da muryarta ta fara kuka na neman yaci ƙarfinta
“He said they should rape me a nan tunda dady yaƙi ya basu abun da su ke so” ta kai ƙarshen maganar tana fashewa da kuka,wani irin mummunan faɗuwa gaban ya Naeem yayi da sauri ya daki desk ɗin dake gabanshi saboda tsabar shock...
wani irin ɓacin rai ne ya rufe shi idanunshi su ka kaɗa jawur,kallon Nainarh dake ku ka yayi, lokaci ɗaya tsoron ƙarshen labarin ya mamayeshi,da ƙyar yai getting courage ɗin faɗin “ina fatan babu abunda su ka maki?” ya faɗa cike da tsoron amsar da zata bashi, girgiza mashi kai tayi tana goge hawayen dake zarya a fuskarta “ fashewa nayi da kuka lokacin da naji furucin Boss ɗin na su,haka ma dady da momy kuka su ke muna roƙon su amma ba su saurare mu ba,fisgata su ka yi zuwa tsakiyar parlorn,unclothing PJ dake jikina su ka fara,ganin da gaske su ke ne yasa dady ya shiga ƙoƙarin ƙwace kanshi daga riƙon da su ka yi mashi dan ya kawo man ɗauki,dame su ka shiga da shi yana son zuwa inda nake suna riƙeshi har Allah ya bashi sa'ar kaima ɗaya daga cikin su duka a ido hakan yasa su ka sake shi,da gudu ya nufo inda nake,kokawa ya shiga yi da wanda ke kaina,a haka ba muyi aune ba sai jin karar gun muka yi a falon tsoro da firgici ne yasa na suma nan take,ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni a hospital tare da mom,a nan nake samun labarin sun kashe dady momy kuma na station ana zarginta da kashe...” kasa karasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta a lokacin,ya Naeem ba ƙaramin karaya zuciyarshi tayi ba,lokaci ɗaya wani mugun tausayin ta ya rufe shi,fatan shi dai ya zama gaskiya ba abin da suka mata
recording din da yake ya kashe, tashi yayi daga mazaunin shi ya nufo inda take zaune,kamo hannunta yayi ya miƙar da ita,tissue ya ɗauka,hawayen dake zuba daga idanunta ya shiga goge mata,amma kamar yana tunzurata ne,ɗan jawota yayi closer to him,faɗawa tayi jikin shi tana sake fashewa da wani kukan.
A hankali ya kai hannunshi bayanta,hitting bayanta ya shiga yi yana lallashinta,turo ƙofar ɗakin aka yi da sauri ya juya yana kallon ƙofar amma baiga kowa ba wanda ya turo ƙofar har yayi saurin maidata ya rufe, lallashinta ya shiga yi sosai,har sai da tayi shiru tukun ya rabata da jikin shi,da hannu ya shiga goge mata hawayen da su ka kasa tsaya mata “daina ku ka kinji,nayi maki alƙawarin duk wani mai sa hannu a wannan al'amarin bazan barsa ba ko waye shi, don't bother your self kinji” a

Please Login or Register in order to submit comment