Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za su nemi kasheta⁉️”
“shi ne abunda ke ɗaure man kai dady,amma in sha Allah asirinsu zai to nu,nasa a bi bayan su”
“Allah ya kyauta gaba,yanzu a wane hali Nainarh take ciki?”
“lafiya lau take,kawai dai ta tsorata ne sosai,amma na bata maganin bacci in sha Allah data farka zata dawo dai dai”
“Allah ya ki ya ye gaba” da Ameen ya Naeem ɗin ya amsa.
sallama su ka yi dady ya nufi cikin gidan shi kuma ya fice.
Uncle Ahmad lokacin da yake gidan Abbah,rufe shi da faɗa Abbah yayi sosai kan abunda zaabith ɗin ya aikata dan yana ganin sakacin shi ya fi yawa a ciki,ba komai ya ƙara ɓata ran Abbah ba sai yanda mutanen gari ke faɗan munanan kalamai akan uncle Ahmad ɗin musamman abokan hamayyarsa na siyasa,wa su ma wanda su ke da kusanci da Abbah harda kiran shi su ka yi a waya,dake sharrinshi ne babu in da abun bai zagaya ba lungu da saƙo,mutane sun fi saurin yaɗa sharrin mutum sama da Alkairin shi,da ka shiga social media maganar da ake kenan,wasu harda ƙara ma zancen citta wasu ma maganganun da su ke faɗa ba su da alaƙa da al'amarin wa'iyazubullah
ya ƴan uwa mu zamanto masu ƴada Alkairi ba sharri ba.
faɗa sosai Abbah yake mashi yama ƙi bashi Accesse ɗin da zai ce komai,ban da haƙuri babu abunda ya ke bashi har ya gama mashi faɗa ya koma yi mashi nasiha,sai da Abban ya sauko tukun uncle Ahmad ɗin ya sake baki haƙuri yana sanar da shi Maganar Auren Noor da Irfan.
Sosai Abbah ya yi farin ciki da jin mom ta haƙura “gaskiya naji daɗin jin haka,Allah ya sakama Zulaihart da Alkairi,su kuma Allah yasa ma Auren na su albarka,amma mi yasa ku ke son rabashi da na Waseef?,kamar zaifi ayi shi lokaci ɗaya??”
“ba komai Abbah,kawai saboda halin da Nurjahan ɗin take ciki ne,kamar ɗaura Auren na su zai taimaka ma lafiyarta tunda fasa Auren shi ne sanadiyyar ciwan nata zuwa bayan sallah sai ayi shagalin bikin tare da na Waseef ɗin”
“hakan ma yayi Allah ya bata lafiya in sha Allah zuwa gobe bayan sallar zuhur sai a ɗaura Auren,zan sanar da Shaikh Ibrahim da duk wani wanda ya kamata ya sani,Allah ya ba su zaman lafiya”
“Ameen Abbah,ni zan koma gida”
“to shikenan ba damuwa” har parking space Abbah ya rakashi,sai da yaga tashin motocin shi tukun ya koma ciki cike da farin cikin Auren Irfan da Noor da za'ayi, murmushi ya saki yana faɗin “Zulaihart Allah ya faranta maki kamar yanda ki ke farantama bayin sa Ameen.
Mom fatilah lokacin da su ka koma gida taruwa su ka yi ita da su mamy su ka yima masu aikinta shegen duka kan dole sai sun faɗa masu ubanda yaba Noor guba,Banda ku ka da faɗin ba su san komai babu abunda masu aikin suke,amma hakan baisa sun ƙyale su ba, ƙarshe da su ka gaji su ka kuma fahimci baza su taɓa faɗa masu gaskiya ba,da securitys ɗin gidan mom fatilah ta haɗa su,ai kuwa ba ƙaramar azaba su ka sha a hannunsu ba,ta in da Allah ya taimake su mai gadin gidan ne ya kira uncle mutallab ya sanar da shi abunda ke faruwa hakan ne yasa ya kira securitys ɗin yace su ƙyale su,hakan ba ƙaramin ɓata ran mom fatilah da su mamy yayi ba.
Kainart sosai ƴan uwa da abokan arziƙi ke zuwa gaishe da ita duk da har time ɗin bata farka ba, da yawan su sai sun zo gaishe da ita su ke sanin Noor ma bata da lafiya,wasun su sun samu ganinta wasu kuma sai dai su ka tafi akan za su dawo idan an fito da ita daga emergency ward,mama Ameenah ko da ta zo iyakarta wurin Noor amma bata shiga ta duba halin da kainart take ciki ba, hakan kuwa ba ƙaramin ɓata ran Abbah yayi ba da yake a tare su ka zo amma sai tayi kamar bata fahimci ranshi ya ɓaci da abunda tayi ba,tun ba yau ba basa ga maciji ita da uncle mustapha tun yana ƙaramin sa.
Nainarh sai bayan sallar isha ta tashi yumnah har ta gaji da zuwa duba ko ta tashi,gaba ɗaya ta damu da halin da take ciki, Alhmdllh ta tashi taji sauƙin abunda ke damunta ta dalilin baccin da ta yi, bedroom ɗin su ta koma, yumnah tasha ruwan mamaki ganin yanda Nainarh gaba ɗaya ta sauya mata,wata irin tsanarta ta hango a cikin idanun Nainarh,roƙon Nainarh ta shiga yi da bata haƙuri dan duk a tunaninta saboda ta tafi ta barta take wannan fushin sai data ga abun ya wuce tunaninta tukun ta fara zargin kanta.
Uncle mutallab tun bayan tafiyar su dady ya kira waseef yaji ko su na tare da irfan,amma sai waseef ɗin ke sanar dashi shima rabonshi da irfan ɗin tun safe da su ka zo office,har office ɗin shi yaje amma baya nan kuma ya kira wayarsa bai same shi ba,mamaki ne ya kama uncle mutallab to ina Irfan ɗin ya shiga da har waseef bai sani ba.
sanar dashi halin da Noor ɗin take ciki yayi da kiran sunan Irfan ɗin da take
“dan Allah waseef idan ka ganshi kace na ce ya zo,ina son ganinshi” sosai hankalin waseef ya tashi jin halin da Noor ɗin take ciki,wani mugun tausayin su ne daga ita har Irfan ɗin ya rufe shi “in sha Allah uncle zan sanar da shi,Allah ya bata lafiya sai mun shigo”
“Ameen waseef,sai na ganku” da to waseef ɗin ya amsa yana mashi sallama. 
Number Irfan ɗin ya shiga kira still a kashe take,ficewa yayi daga office ɗin shi direct office ɗin Irfan ɗin ya nufa,a rufe ya samu office alamar bai dawo office ɗin ba,parking lot ya nufa motarshi ya shiga direct estate ɗin su ya nufa ci ke da sa ran zai samu Irfan ɗin a can,sai dai ko da yaje bai same shi ba,babu inda bai duba shi ba har gidajen su da za su zauna idan sunyi Aure dake kusa da gidan uncle Ahmad sai da ya duba amma baya nan rabonshi ma da estate ɗin tun ranar friday.
duk yanda ya kai wurin neman Irfan sai dai ya haƙura har dare yayi sosai Irfan bai dawo gidan ba kuma har lokacin wayarshi bata ta fiya dan dole tasa ya haƙura,gida ya koma ya shirya ya nufi asibiti wurin Noor da kainart da itama bai samu zuwa ya dubata ba, uncle mutallab bai ji daɗin rashin samun Irfan da Waseef ɗin baiyi ba,ya jima a hospital ɗin kafin ya tafi,heart of Vegas ya koma neman Irfan ɗin duk da yaje ɗazu,still bai zo ba Muhsin kawai ya samu,bai wani jima ba ya nufi gida,gaba ɗaya tashin hankalin in da Irfan ya shiga ya dameshi duk da ya san Irfan bazai ɓata ba dole wani wurin ya tafi.
Irfan bai dawo gida ba sai washe gari around 12 PM,Waseef na bedroom ɗin su yayi shirin fita ya shigo,da mamaki Waseef ɗin ke kallon Irfan ɗin da kallo ɗaya zaka masa ka fahimci baya cikin natsuwar shi.
Daga yanayin yanda yake tafiya zai tabbatar maka da he's drunk,ko kallon Waseef dake kallonshi baiyi ba yayi jifa da key ɗin motarshi dake hannunshi ya nufi bathroom,girgiza kai kawai Waseef yayi yana zama gefen bed ɗin su,daga bedroom ɗin yana jin yanda Irfan ɗin ke kakarin amai yana fitar da wani irin nishi,kallon ƙofar toilet ɗin yayi cike da tausayin ɗan uwan nashi.
ya shafe tsawan 40 minutes bai fito ba,tashi Waseef yayi ya nufi bakin ƙofar toilet ɗin
ganin har lokacin bai fito ba ga wani irin nishin wahala da yake fitarwa,ɗan nocking ɗin ƙofar toilet ɗin yayi yana kiran sunan shi “Irfan lafiya ka ke,mi ke damunka ne??” ya faɗa,tsit yaji Irfan ɗin ya daina nishin da yake sai ƙarar ruwa da yaji,barin bakin ƙofar yayi ya koma cikin ɗakin,a bakin bed ɗin ya sake zama,bai jima da zama ba Irfan ɗin ya turo ƙofar ya fito sanye da bathrobe,bed ɗin ya nufo jiki ba ƙwari ya faɗa saman bed ɗin,dafe cikin shi yayi yana ɗan ya mutse fuska,matsowa Waseef yayi kusa da shi “Irfan lafiya ka ke,ina ka kwana ne,jiya kasan irin neman da nayi maka kuwa??”
Irfan ɗin na jin shi amma bai ce mashi ƙala ba shi kanshi bazai iya cewa ga halin da yake ciki ba
“magana nake Irfan kayi shiru,wannan rayuwar da ku ka ɗaukar ma kanku ba mai ɓullewa bace,ku musulmai ne dukan Musulmin ƙwarai an san shi da yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,a rayuwa ba komai muke so mu ke samu ba,tunda har kaga abun ya zo a haka to Allah ne bai ƙaddara akwai Aure a tsakanin ku ba,ya kamata ace kunyi imani da ƙaddarar data same ku kunyi haƙuri,amma wannan halin daka jefa kanka ba mafita ba ne,idan da mutuwace ta ɗauki ɗaya daga cikin ku fa,ya za kuyi,ko wani zai bi ɗan uwanshi ne tsabar so??” Waseef ɗin ya faɗan yana ɗan yi ƙwafa haɗin da kallon fuskar Irfan ɗin,idanunsa a lumshe su ke amma duk abunda Waseef ɗin yake faɗa yana jin shi
“dan Allah Irfan ka dawo cikin hankalinka dubi halin daka ka jefa kanka,kullum cikin ɗurama kanka abunda zai zame maka matsala ka ke,gaba ɗaya nema ka ke ka mayar da kanka mahaukaci,kuma hakan ya sauya ƙaddarar da Allah ya ƙaddaro maku ne?” ya faɗan yana kallon Irfan ɗin da har lokacin bai motsa ba,girgiza kai yayi yana cigaba da faɗin “hakan bai sauya komai ba,Noor na kwance gadon asibiti tayi poisoning kanta duk dan saboda an rabaku still hakan bai sauya ƙaddarar ku ba” tunda ya ambaci Noor tayi poisoning kanta Irfan yai zambur ya miƙe yana kallon Waseef ɗin da yayi magana,kallo ɗaya zaka ma fuskarshi ka san abun ya taɓashi
“dan Allah ku dawo cikin hankalin ku kusan cewa duk abunda Allah yayi akan bawansa mai kyau ne,kar kuje ku rabu da imanin ku a banza” girgiza kai kawai Irfan ɗin yayi yana nufar ƙofar fita saurin riƙo hannunshi Waseef yayi yana faɗin “ina zaka a haka?”
“hospital”shi ne kawai abunda yace mashi yana zame hannunshi dake cikin nashi,sake riƙo hannunshi Waseef ɗin yayi “a haka za kaje wurin ta?”
kallonshi Irfan ɗin yayi “dan Allah Waseef ka ƙyale ni”
“gaskiya bazan taɓa bari ka fita a haka ba,ko ba kaga halin da ka ke ciki ba ne?”
“please Waseef! dan Allah” Irfan ɗin ya faɗa a hankali daurewa kawai yake amma shi ka ɗai ya san ya yake ji,ga kuma halin da Noor take ciki
“ka bari ka fara dawowa normal tuku”
“please Waseef”
“shikenan naji amma ka wuce ka sa kaya tukun” kallon jikin shi yayi can kuma ya juya ya koma cikin ɗakin, clothset ɗin su ya nufa,Waseef na tsaye har ya kammala shiryawa ya fito,key ɗin motarshi daya jefar ya ɗauka ƙofar fita ya nufa bin bayan shi Waseef ɗin yayi.
A parking space su ka haɗu da su dady da alama masallaci za su shi da Alhj Ja'afar da PA ɗin sa,har drivern shi ya buɗe masu mota amma ganin su Irfan ɗin ne yasa su ka dakata,ƙarasowa su ka yi cike da girmamawa su ka shiga gaishe da su,da kulawa su ka amsa masu uncle Ahmad na tsaida idonshi akan Irfan “Irfan Ina ka shiga jiya aketa nema ka?” sadda kai ƙasa Irfan ɗin yayi yana faɗin “ina tare da Amjad ne dady”
“amma shi ne ka kashe wayarka aketa kira ba'a samun ka?” shiru Irfan ɗin yayi baice komai ba,gyaɗa kai kawai uncle Ahmad yayi “ina za ku haka?” Waseef ne yayi saurin cewa “masallaci daga can zamu wuce hospital wurin Noor ne,bai san bata da lafiya ba” ɗan kallon Irfan ɗin uncle Ahmad yayi tukun yace “ohk mu ma masallacin zamu tafi daga can zamu wuce hospital ɗin,ku shiga mu tafi” da to su ka amsa suna nufar ɗaya daga cikin motocin su dady,su ma motocin su suka shiga.
key driver's ɗin su ka yima motocin su ka fice tare da motocin securitys ɗin su wasu na gaba wasu na baya,direct masallacin da su ke sallah su ka nufa.
A can su ka samu Abbah da dady da su uncle Hashim harda su ya Naeem,Irfan tunda ya ga ya Naeem da ya Adnan ya wani haɗe fuska kamar bai taɓa dariya ba,ko in da su ke bai je ba bare su samu arziƙin gaisuwa daga gareshi,hakan kuwa ba ƙaramin kunna ya Naeem yayi ba.
gaba ɗaya ahalin Abbah su ka haɗu a masallacin wa su daga cikin su sun san da maganar ɗaurin Auren Irfan da Noor ɗin da za'ayi wa su sun su ne ba su sani ba,har shi kanshi Irfan ɗin bai sani ba sai da aka gama sallar su ka ji sanarwa daga bakin Sheikh Ibrahim,bazan iya misalta maku irin farin cikin da Irfan ya tsinci kanshi a wannan lokacin ba,fashe masu kawai yayi da ku ka kamar ƙaramin yaron Uncle Hashim na lallashin shi,babu wanda bai ji tausayin shi a masallacin ba,sunyi mamakin wane irin so ne wannan su ke ma junansu,Waseef shi kanshi sai da ya matse ƙwalla ta taya ɗan uwan na shi murna,ya san yanzu ɗan uwan shi zai dawo cikin natsuwar shi.
500k Uncle Ahmad ya biya sadakin Noor uncle Mustapha ya amsa.
ya Naeem tunda aka fara sanar da ɗaurin Auren mamaki ya cika shi,zargi ya fara anya kuwa mom ta sani,ana kammala ɗaurin Auren ya riga kowa ficewa,a parking space ɗin masallaci ya tsaya dialing number mom ya shiya yi Amma har Kiran ya katse ba tayi picking,bai sake kiranta ba,mota su ka shiga shida ya Adnan su ka bar masallacin suma hospital ɗin su ka nufa.
fitowa su dady su ka yi harda Irfan da Waseef sai tsokanarshi Abbah yake banda sakin murmushi ba bu abunda yake,motocin su suka nufa,uncle Ahmad back seat na motar da ya zo driver ya buɗe mashi amma sai bai shiga ba yana faɗin ina zuwa,motar uncle Mustafa ya nufa,yana ƙoƙarin shiga motar ya dakatar da shi,dakatawa yayi har ya ƙaraso,tsaye su ka yi uncle Ahmad ya rasa ta wace hanya zai fara ma uncle Mustafa magana,wani irin shakkar sa yake ji,gajiya uncle Mustafa yayi yace “yaya lafiya dai ko?” ɗan ajiyar zuciya uncle Ahmad ɗin ya sauke
“lafiya lau Mustafa,dama nace ban samu munyi magana ba,lokacin da naje hospital har ka tafi” jin jina mashi kai kawai uncle Mustafa yayi
“ya jikin kainart ɗin”
“Alhmdllh” kawai uncle Mustafa ya ce
“dan Allah Mustapha kayi haƙuri akan abunda ya faru,ban san akwai matsala a tsakanin su ba da hakan bata faru ba,dan Allah kayi haƙuri zaabith yayi kuskure amma In sha Allah hakan bazai sake faruwa ba,kayi haƙuri ka ji” jin jina mashi kai uncle Mustapha yayi yana faɗin “ohk ba damuwa” ya faɗa yana buɗe car door ɗin shi ya shiga,duk sai yaji badaɗi da irin amsawar da uncle Mustafa yayi mashi,yana a nan tsaye har motarshi ta fice daga masallacin,ya so ya tambaye shi ko Zaabith na tare da shi dan tun jiya rabonshi da shi ga wayar shi da yake kira baya samu,ganin reaction ɗinshi ne yasa kawai yayi shiru,motocin shi ya nufa,suma barin masallacin su ka yi direct hospital su ka nufa.
Irfan tunda su ka shigo mota yayi shiru idanun sa na akan side road,kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar farin cikin da yake ciki,jin abun yake kamar mafarki wai yau shi da Noor ɗin shi sun zama mata da miji,mafarkin da su ka daɗe suna yi ya zama gaskiya,kallon shi Waseef yayi ya na sakin murmushi “Ango kasha ƙamshi,tunanin mi ka ke?” ya faɗa yana kallonshi, murmushi kawai Irfan ɗin yayi ba tare da ya ce mashi komai ba
“yanzu dai ba sauran tashin hankali da ɓacin rai,finally dai burinku ya cika,Irfan angon Nurjahan,gaskiya nayi farin ciki bro,Allah ya baku zaman lafiya,har na ƙosa Noor ta samu sauƙi musha shagali” murmushi Irfan ya saki yana girgiza kai.
A jere motocin su suka shiga cikin hospital ɗin,a compound su ka yi parking,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fitowa daga motocin suna nufar cikin hospital ɗin,ɗakin da aka kwantar da kainart su ka fara zuwa Laatifa da yumnah sai fa'iza kawai su ka samu mom da mom Maryam sunje ward ɗin da aka kai Noor,a jiya aka canza mata ɗaki,tunda aka kawota ba su samu damar zuwa ba sai yanzu da aka fito da ita daga Emergency ward,har yanzu Kainart a kwance take,data farka nurses ke sake mata Allurar bacci a bisa umarnin Dr Lelarh.
gaban gadon su ka ƙarasa Adu'a su ka shiga yi mata su yumnah na amsa masu da Ameen sun ɗan jima a ɗakin kafin su ka fice zuwa ward ɗin da aka kai Noor ɗin babu nisa daga nan, Irfan gaba ɗaya ya ƙosa ya yi ido biyu da Amaryar tasa dan zaman da su kayi a ɗakin da kainart take daurewa kawai yake dan ji yake kamar ana tsirarshi,ya so ace wurin Noor ɗin su ka fara zuwa.
A bakin ward ɗin su ka tsaya,su mom ne su ka fito,tunda su ka fito idonta ke kan Irfan shima kallonta yake rabon da su sa juna a ido tun ranar Friday.
Abbah da su dady ne su ka shiga,sai dai su dunga shiga ɗaya bayan ɗaya saboda sun yi yawa.
Ƙara sowa su mom su ka yi wurin,cike da girmamawa su ka shaga gaishe da su suna amsa masu da kulawa,zama su ka yi akan waiting chairs ɗin dake wurin banda Irfan da duk a ƙagare ya ke su Abbah su fito.
kamo hannunshi mom tayi tana kiran sunanshi ba ƙaramin kewarshi tayi ba,ta san fushi yake da ita amma yanzu ta san komai ya wuce tunda ya samu abunda yake so,faɗawa yayi jikinta yana hugging ɗinta “am sorry mom,kiyi haƙuri idan na ɓata ranki dan Allah ki yafe man nayi kuskure bazan sake ba” ya faɗa a hankali,murmushi mom ta saki tana shafa bayan shi “karka damu Irfan komai ya wuce,fatan Allah ya ba Noor lafiya” tana jin saukar hawayenshi a bayanta wanda ba na komai ba ne sai na farin ciki
“Ameen nagode Sosai mom, Allah ya ƙara girma ya kare gabanki da bayan ki,Allah ya haskaka maki mom,Allah ya bamu ikon faranta maki kamar yanda ki ke faranta mana,kin sani farin ciki mara misaltuwa,nagode sosai mom” jikin su ya Naeem ne yayi sanyi da jin irin Adu'ar da Irfan yake mata kai ka san yana cikin farin ciki,ya Naeem duk sai yaji wani iri lokacin da ya tuna ranar da su ka tasa Irfan ɗin a gaba akan sai ya rabu da Noor,bai san cewa har haka yake sonta ba.
ɗan bubbuga bayan shi tayi “godiyar ta isa haka Irfan,nauyi ne a kaina na faranta ma ku,ya isa haka kaji Allah ya sanya Albarka a cikin Auren ku ya ba ku zaman lafiya” da Ameen ya amsa,raba jikin su tayi, murmushi tayi tana kallon fuskarshi yayinda take goge mashi hawayen da ke fuskarshi,su mom Maryam sai sakin murmushi su ke,wurin su ya Naeem ya matsa ɗaya bayan ɗaya ya shiga ba su haƙuri musamman ya Naeem, murmushi kawai su ka mashi suna masu Allah yasa Alkairi da fatan zaman lafiya.
wurin Kainart su mom su ka koma,su dady sun ɗan jima tukun su ka fito daga ɗakin,tashi su ya Naeem su ka yi su ka shiga Irfan na bayan su,da sallama su ka shiga,a zaune su ka hango uncle mutallab gaban gadon da Noor ɗin take kwance, sallamar da su ka yi uncle mutallab ya amsa masu yana kallon Irfan,har gaban gadon su ka ƙaraso Banda Irfan da ya toge a bakin ƙofa,tunda ya sauke idonshi akan Noor ɗin da idanunta ke a lumshe ya kasa ko da motsi mai ƙarfi,wani mugun tausayinta da kewarta ne haɗe da ƙaunarta ke shigar shi a lokaci guda.
ya mai jiki su ya Naeem su ka shiga yi ma uncle mutallab ɗin bayan sun gaisa,da Alhmdllh ya ke amsa masu,ba su wani jimaba su ka fice,kallo Irfan da har lokacin yana bakin ƙofar tsaye uncle mutallab ɗin yayi “Irfan!”ya kira sunanshi,kallonshi Irfan ɗin yayi
“ƙaraso mana” uncle mutallab ɗin ya faɗa,sai a lokacin ya ƙaraso gaban gadon,da ladabi yace “ina wuni uncle,ya mai jiki” da Alhmdllh ya amsa mashi “ina ka shiga jiya nake ta kiran ka Irfan?” sadda kai ƙasa Irfan ɗin yayi ba tare da yace mashi komai ba “ka yi shiru?”
“bana tare da wayar ne uncle” jin jina mashi kai yayi “ok,matsa ga Noor ɗin can, kwana tayi tana kiran sunanka,nayita nemanka ne saboda halin da take ciki,banji daɗin hukuncin daka yake ba Irfan,a dalilin guje matan da kayi yasa ta shiga wannan halin?”
“kayi haƙuri uncle,nayi hakan ne saboda hukuncin da mom ta yanke a lokacin,amma kayi haƙuri ban san hakan zai sa ta aikatama kanta haka ba”
“shikenan ai Irfan,komai yanzu ya wuce,zo ka zauna” ya faɗa yana tashi daga saman chair da yake zaune,matsawa Irfan ɗin yayi ya zauna kan chair,kallon Waseef dake tsaye gefen gadon uncle yayi yana faɗin“waseef tunda kun zo bari naje gida na dawo,ban samu na koma ba tunda jiya”
“to shikenan uncle ba komai,nima tafiya zanyi Irfan ɗin ma ya isa ya kula da ita kafin ka dawo”
“to shikenan,Irfan sai na dawo” da to Irfan ɗin ya amsa,Waseef ma ce mashi yayi sai ya dawo,ficewa su ka yi daga ward ɗin.
ba komai yasa uncle mutallab tafiya ba sai dan ya ba su damar kasancewa da juna ko hakan zai taimaka Noor ɗin,Waseef ma dalilin tafiyarshi kenan dan ya san idan suna wurin Irfan ɗin bazai samu sakewar da zai ba Noor ɗin kulawar data kamata ba.
tunda ya zauna ya kafeta da ido yana kallon kyakkyawar fuskarta da duk ta faɗa ga wani irin haske da tayi,ya kai tsawan 5 minutes ƙalla baice ba,ɗan ajiyar zuciya ya sauke yana kamo hannunta cikin nashi,a hankali ya kira sunanta yana kai ɗayan hannunshi saman fuskarta,shafa gefen fuskarta ya shiga yi yana sake kiran sunanta,slowly ta shiga buɗe idanunta da su kayi mata nauyi ta sauke akan fuskarshi,tunda aka kawota hospital ɗin wannan ne karon farko data buɗe idanunta duk zuwan da ake gaishe da ita idonta a rufe yake.
sake kiran sunanta yayi yana faɗin“ya jikin na ki?” ɗan lumshe ido tayi tukun ta buɗesu tana sake kallon fuskarshi
“da sauƙi?” ya sake jefa mata tambaya,hawaye ne su ka taru a idonta,sake shafa fuskarta yayi da hannunshi dake saman fuskar yana girgiza mata kai alamar kar tayi,gyaɗa mashi kai ta shiga yi tana ƙoƙarin tashi zaune,sakin hannunta dake cikin nashi yayi yana miƙewa tsaye,taimaka mata yayi ta tashi zaune,zama yayi gefen bed ɗin yana sake kamo hannuwanta,a hankali ya fara magana“why Noor,mi yasa za ki yi haka,dubi halin da ki ka jefa kanki,kin kuwa san halin da zan shiga idan na rasaki?” zuba mashi ido kawai tayi “ko dana daina kiranki ba wai hakan na nufin na rabu dake ba ne ko na daina sonki,Noor bazan taɓa iya daina sonki ba,kuma ki sani babu wata mace a rayuwar nan da zata maye man gurbinki,bazan iya rayuwa da wata ba bayan ke,mi yasa ba kiyi tunanin halin da zan shiga ba lokacin da zaki sha poison,ke ɗin wani ɓangare ce ta rayuwata Noor,rasaki abu ne wanda ruhina bazai iya ɗauka ba,karki sake maimaita kuskure irin wannan kinji”
kallonshi kawai take yayinda hawaye ke sake taruwa a idanunta “please Noor kiyi man magana,ina so naji muryarki” ya faɗa yana kissing hannunta dake cikin nashi.
hawayen da su ka taru a idanunta ne su ka shiga zubowa,lallashinta ya shiga yi yana goge mata hawayen
“kiyi haƙuri idan maganganuna ne su ka ɓata ranki,ban maki faɗa dan na saki kuka ba kawai banji daɗin abunda ki ka yi ba ne amma yanzu komai ya wuce” lallashinta ya shiga yi har ya samu ta daina kuka,murza hannunta dake cikin nashi ya shiga yi yana faɗin
“ban sani ba ko uncle ya sanar dake mom ta janye furincinta akan Auren mu,komai ya wuce Noor daga ƙarshe dai burinmu ya cika,a yau mu ɗin mallakin juna ne,daga yau na tashi daga matsayin saurayinki na dawo mijinki,Noor yanzu ke matatace ba budurwata ba,ban san mi yasa su ka fasa ɗaura Auren mu bayan sallah kamar yanda Abbah yace ba,amma na san hakan bazai wuce yana da nasaba da halin da ki ke ciki ba,Noor su dady yau sun sani farin ciki mara misaltuwa,jina nake kamar

Please Login or Register in order to submit comment