Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA


HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 25215



HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Bukar Mada ,Prof Ibrahim Malumfashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 128.14 kb

File Type: txt

Views: 653+

Download: 221+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

001. HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

Wani namiji ya kasance mai daukar kaya (dako) a cikin birnin Bagadada. Ya kasance gwauro ne, ba shi da mata. Ana nan wata rana daga cikin ranaku, yana tsaye a wata rumfa ta kasuwa ya na neman wanda zai daukarwa kaya, sai wata mace, kyakkyawa, ta zo gare shi, tana lullube da mayafi, wanda aka yi wa kwalliya da zane-zane na alharini, an yi masa ado da zinariya, ta ce masa, dauko gammonka ka biyo ni.

Dan dako bai gasgata abinda kunnuwansa suka jiye masa ba, daga bakin wannan kyakkyawar mace, har sai da ta kara cewa da shi, dauko gammonka, ka biyo ni. Sannan ya dauka ya bi bayanta, suka shiga cikin kasuwa.

Bai gushe ba yana biye da ita har suka zo gun rumfar wani Banasare, ta dauko dinari ta ba shi, ya karba ya ba ta zaituni. Ta saka a cikin kwandon Dan dako. Ta ce, dauko biyo ni.

Ya dauki kwando ya bi ta, suka tsaya a rumfar mai sayar da kayan marmari. Ta sayi dukan abin da take bukata na daga kayan marmari ta zuba a cikin kwandon Dan dako. Suka wuce gaba har zuwa rumfar mahauci, ta sayi nama awo goma, ta nade shi a cikin ganye ta saka a kwandon Dan dako. Ta ce dauko biyo ni, ya kai Dan dako. Ya dauka ya bi ta.

Ta tsaya kan rumfar mai alawa, ta sayi faifai ta cika shi da alawa kala-kala, da soyayyun abubuwa, da dadada, da zakaka, da kamsasa, duk ta jefa su a cikin kwandon Dan dako. Ta ce da shi, ka dauko mu tafi, ka amince da bi na!

Ta tafi, shi na biye da ita, ya na cewa, “Da kin sanar da ni za ki yi sayayya da yawa ai da na taho da alfadarata na dora mata wannan kaya, ya shugabata.” Ta yi murmushi, ta tafi, yana bin ta a baya.

Yayin nan ta tsaya bisa ga rumfar mai turare, ta sayi ruwaye goma na daga ruwan wardi, da ruwan sandal, da shashimi, da wadansun wadannan, ta karbi sukar, ta wuce, Dan dako ya bi ta. Ta ce ta manta, ta komo ta karbi lubban, da ambar, da miski, da shama’ar askandariya, ta aza dukkan wadan nan a cikin kwandon Dan dako, ta ce ka dauko ya Dan dako, ka biyo ni, yanzu kam na gama sayayya, gida za ka kai mini kayan.

Dan dako ya dauki kaya ya bi matar nan har suka iso wani gida, mai kyawo, mai doguwar katanga, da fararen soraye, da madaukakan sassa. Kofar gidan ta kasance shafaffiya da labunus, gogaggiya da zinariya, gambunta na jan dinari. Yarinya ta tsaya a gaban gidan, ta kwankwasa kofa, kwankwasa mai taushi, kamar ana kida dundufa.

Daga nan kofa ta bude, ta ce da Dan dako ya shigo. Suka shiga ciki, Dan dako ya yi duba izuwa yarinyar da ta bude musu kofa, ya ganta yarinya ce shiryayya, mai kyakkyawar fuska, da kwarjini, da haiba tamkar jinjirin wata. Idanunta dara dara, farare tas, tamkar na barewa, fuskarta na haske, tamkar wata daren goma sha biyu.

Yayin da Dan dako ya ganta, sai hankalinsa ya tashi, kayan da ke bisa kansa suka yi kusan faduwa saboda kyan wannan yarinya da ya gani, ya ce a cikin ransa, “Da dai idaniyata ba ta taba ganin wani abu mai kyau da ya kai kyawun wannan yarinya ba.”
Yarinya, mai jiran kofa, ta ce, “Marabanku.” Suka tafi har suka isa ga wani daki yalwatacce, adantacce, mai wuraren zama da yawa. Suna shiga dakin, sai Dan dako ya ga wata yarinya kuma, tana kwance bisa wani gado na azurfa mai dan karen kyau. Gadon na rufe ne da rumfar zannuwan mirmir madaukaki, anyi musu ado da lu’u lu’u da jauhari. Wanna rumfar gado ba ta hana ganin wanda ya ke kwance a kan gadon ba.

Yayin da wannan yarinya ta kan gado ta ji shigowar Dan dako da Jekadiya mai siyo kaya, sai ta bude labulen gadon, ta fito. Idanunta tamkar raba, da fuska marinjayiya daga rana, mai haske, ka ce ita tana daga taurarin duniya. Dan dako yaga kyawun da bai taba ganin irinsa ba.

Tana saukowa daga kan gado, sai ta yi tafiya kadan, ta zauna a kan kujera, ta ce da wadda ta siyo kaya da kuma wadda ta bude kofa, “Ya kuka yi tsaye? Me kuke jira ne? Ku sauke kaya daga kan wannan miskini ku biya shi sallamarsa, ya tafi.”

Jekadiya ta zo ta gaban Dan dako ta rike kwandonsa, yarinya mai jiran kofa ta rike kwandon daga baya, ita kuma ta ukun, shugabarsu, ta taso ta rika musu daga tsakiya, suka sauke kayan daga kan Dan dako. Suka zube kaya, suka aje kowane ga muhallinsa, suka ba shi kwandonsa tare da dinari biyu. Suka ce da shi, “Ka fuskanta kan tafarkinka, ya kai wannan miskini.”

Dan dako ya yi dubi izuwa ga wadan nan yam mata guda uku, da abinda suke ciki na daga kyawo da dabi’o’i kyawawa, da dai bai ga kyawawa tamkarsu ba, amma babu maza a gare su. Ya duba abinda ke gare su na daga sha, da abin marmari, da abin maye, da wadansun wadannan, ya yi al’ajabi, gayar al’ajabi. Sai ya ki ya fita daga gidan.

Shugabar yan matan nan, wadda aka iske kwance bisa gado, ta ce, “Me ke gare ka, ya kai wannan miskini, da ba ka fita? Ko kudin dakon kayan sun yi maka kadan ne?” Ta waiwaya ga wadda ta siyo kayan, ta ce, “Ki kara masa dinari daya ya fita ya ba mu wuri.”

Dan dako ya ce, “Wallahi ya shugabata, kudin da kuka ba ni sun fi karfin jingar dakon da na yi muku, domin jingata rabin dirhami ce, amma ga shi kun ba ni har dinari biyu. Cewa ni, zuciyata ta shagala ne da farin cikin ganinku. Kuma ina cikin tunanin ya ya kuka kasance ku uku haka, kyawawa, amma babu maza a tare da ku, babu namiji daya mai debe muku kewa? Shin ko kun san rumfa bata tsayuwa face da akwai shishshiniya hudu? Ban ga hudun ba a gareku.”

Sai yan matan nan suka ce da shi, “Mu yam mata ne, muna tsoron kada mu ajiye asiri ga wurin da ba a kiyaye shi. Mu, mun karanta wakoki a cikin labarai, sun ce: ‘Kiyayi asiri da wanin asiri, kada ka ajiye a gare shi, wanda ya ajiye asirinsa ga wani abokin asiri, ya tozarta kansa'”.

Da dan dako ya ji jawabinsu, sai ya ce, “Ni, namiji ne, mahankalci, amintacce, na karatanta littattafai, munana da kyawawa, sun bayyana gareni, ni, mai bayyana alheri ne, mai boye mugunta, cewa asiri a gareni ya kasance a cikin daki kublalle, wanda mabudinsa ya bata kofar ta na rufe. Me zai hana ku barni na kasance tare da ku, in zama mai debe muku kewa, har zuwa wayewar gari?”

Ko da suka ji zancensa, da tsarinsa, suka ce da shi, “Kai ka sani, mu, muna da bukata da dukiya bisa ga wannan matsayi, ko kana da abinda za ka bamu? Mu ba mu barinka ka zauna garemu, sai in zaka bamu dukiya mai yawa, wanda kuma kai ba mu ga alamun kana da ita ba. Ko kana tsammanin haka nan zamu bari kana kallon fuskokinmu, kyawawa ba tare da ka bamu komai ba.”

Mai gidan ta ce, “Idan so ya kasance ba da dukiya ba, bai yi dai dai da kwayar kasa daya ba.” Mai jiran kofa ta ce, “In wani abu bai kasance a gareka ba, na daga dukiya, ka maraita, ba ka samun kome garemu.” Jekadiya, mai siyo kaya, ta ce, “Ya ‘yan uwana, mu rike shi a garemu, tunda ya zo garemu ya bayyana so, mu aje shi, ya rinka ba mu dariya. Idan kuwa ya fada ma waninsa sirrinmu, ransa ba zai yi tsawo ba, balle zama tare da mu.”

Dan dako ya yi murna, ya ce, “Wallahi ba ni da wani abu na daga kudi, wanda ya isa in gabace ku da shi.” Yam mata suka ce, “Zauna tare da mu, mun karba bisa ga kai da ido.”

Suka ci gaba da shan kayan shaye-shaye da tande-tande, suna hirar duniya, suna masu annushuwa da jin dadi. Ba su gushe ba cikin wannan yanayi har duhun dare ya shigo. Yam mata su ka ce da Dan dako, “Tashi ka fuskanta ya zuwa tafarkinka.” Dan dako ya ce, “Wallahi fitar rai ita ta fi sauki daga fitata wannan gida a cikin wannan dare.”

Suka ce, “Hala ba ka san ko gidan wane ne ba wannan?” Ya tambayesu ko gidan wa ne? Suka ce gidan Abal Mansur. Ya ce na gode da Allah ya sa na zama makwafinsa. Sai Jekadiya ta ce, “Na rantse da raina sai ku bar shi ya kwana a nan gidan, yayi barci a kan gadon da bai taba kwanta irinsa ba, mu na yi masa dariya, gobe da safe sai ya kama gabansa.”

Sauran yam mata suka ce da shi, “Za ka yarda ka kwana garemu bisa ga sharadi, ka yarda da umurninmu, kome ka gani, kada ka tambaya, kada ka nemi sababinsa.” Ya ce, na’am!

Suka ce, “Tashi ka karanta abin nan da ke rubuce a kofar gida!” Ya tashi zuwa ga kofa, ya iske rubutu bisa ga kofar gidan da ruwan zinariya da cewa, ‘Kada ka kula da abin da babu ruwanka, kada ka yi zance cikin sha’anin da ba naka ba, ka ji abin da ya yarda da kai, ka yi abin da aka sa ka’

Bayan Dan dako ya karanta rubutun nan, sai ya ce da su, “Ku shaida ni ba ni zance ga abin da bai shafe ni ba.” Yayin nan Jekadiya ta tashi ta dauko musu abinci, suka ci, suka kunna shama’a da itace, suka zauna cikin ci da sha. Daga nan sai suka ji ana kwankwasa kofa.

Ba su jima ba a cikin zamansu, sai mai jiran kofa ta tashi daga garesu zuwa ga kofa, yayin nan ta komo, ta ce da yan uwanta, “Ni, na iske a bakin kofa Ajamawa uku, masu ido daya-daya, kowane daya daga cikinsu ya aske gashin gemunsa da sajensa. Wannan al’amari ya na da ban mamaki, su mutane ne baki, sun sun ce sun fito ne daga wajen kasar Rum. Akwai ga kowanne dayansu kama da sura abar dariya. Idan ku ka amince su ka shigo, hakika za su nishadantar da mu da dariya.”

Mai jiran kofa, ba ta gushe ba ta na rudin sauran yam matan nan, har ta ce da su, “Mu bar su su shigo, amma mu shardanta musu kada su yi magana ga abin da babu ruwansu a ciki.” Saura suka amince. Ta koma ta shigo da su.

Bakin nan maza ne guda uku, halshensu na rawa ga zance, gashin bakinsu abin dariya, dukkansu suna da ido daya-daya, ko wane dayansu ya aske gemunsa. Suka shigo, suka yi sallama, suka jima su na tsaye, su na jiran izni. Yam mata suka zaunad da su. Mazajen nan uku suka ga Dan dako, da irin tufafin da yake sanye da su, suka ishe shi yana cikin maye. Suka ce da junansu, “Wannan talakka ne, dan uwammu, me ya kawo shi wurin wadannan kyawawan yan mata?”

Koda Dan dako ya ji wannan zance nasu, sai ya ce da su, ku zauna babu yawan magana, hala ba ku karanta abin da aka rubuta a bakin kofa ba?

Yam mata suka yi dariya, suka ce da junansu, mu yi dariya ga talakkawa da Dan dako duka, sun zama abin dariya. Yayin nan suka ajiye kabakin abinci ga talakkawan da Dan dako, suka ci suna zance. Mai jiran kofa na shayar da su abin sha. Yayin da kasko ya zaga tsakaninsu, Dan dako ya ce wa mazan nan uku, “Ya ‘yan uwana, shin ko akwai wata hikaya a gareku, koda daya, abar marmari da debe kewa ku zanta mana ita?”

Mai jiran kofa ta halarta musu da molo, Ba-Irakiyi, da gurmi, Ba-Ajamiyi. Bakin nan suka tashi, dayansu ya zauna bisa ga tambari, dayansu ya riki molo, dayansu ya riki gurmi, suka buga da launi mai tada hankulan ma su jinsa. Yam mata suka yi waka, da muryoyinsu masu dadi, suka daukaka sautinsu. Suna cikin wannan hali, na maye da annushuwa, sai suka ji ana kwankwasa kofa.

Mu hadu gobe domin kashi na 2002. HIKAYAR DAN DAKO DA YAM MATA

Yam mata da bakinsu, Dan dako da Samari uku masu ido daya-daya, sun rafkana cikin kida da waka, sai suka ji ana kwankwasa kofar gida. Yarinya Mai jiran kofa ta tashi domin duba me kwankwasa musu kofa cikin wannan dare.

Ashe masu kwankwasa kofar nan sun kasance Halifa Haruna Rashid da Wazirinsa Ja’afaru da sarkin fada Masrurus Siyafi. Ya kasance daga al’adar Halifa, ya juye siffa tasa, ya shiga gari domin ji da ganin abin da ke faruwa a tsakanin talakawansa.

A wannan daren ma, Halifa da Wazirinsa da Sarkin Fadansa, sun juye siffarsu, suna yawo cikin gari, sai tafarki ya kawo su a unguwar da gidan yan matan nan ya ke. Za su wuce ke nan sai suka ji ana kida da waka mai dadi a wannan gida, shi ne musabbabin kwankwasa kofar gidan.

Yayin da yarinya mai jiran kofa ta bude kofa sai ta ga mutane guda uku, tsaye a bakin kofar. Yayin nan Waziri Ja’afaru ya gabata, ya ce da ita, “Ya shugabata, mu fatake ne, matafiya, kwananmu goma cikin Bagadada muna siyar da kayan fataucinmu, mun sauka ne a dakin baki. Babban maigidanmu ne ya kirayemu a cikin wannan dare, ga wannan sa’a, ya yi mana iznin tafiya. Muka fito cikin daren nan, sai demuwa ta kama mu, muka mance hanyar masaukinmu. Muna so a cikin alherinku, ku saukar da mu wannan gida, mu kwana gare ku, ku samu ladarmu.”

Mai jiran kofa ta dubesu, ta gan su da siffar fatake, ta ce, “Ku jinkirta in sanar da ‘yan uwana!”

Ta shiga ta sanar da sauran yam mata akan wadan nan fatake. Suka ce, “Je ki, ki shigo da su.” Ta bude musu kofa, suka ce da ita, “Yalla mu shigo da yardarki?” Ta ce da su, “Ku shigo!” Halifa ya shiga da Ja’afaru da Masruru a halin suna a siffar fatake.

Yayin da yam mata suka gan su, kuma suka ga suna da almar dukiya a tare da su, sai suka tashi suka tare su da fara’a, suka gaishe su, suka girmama su. Suka ce, “Marhabin, maraba da bakinmu, mun yi murna da ganin ku, amma mu na da sharadi guda a wannan gida, kada ku yi magana a kan abin da babu ruwanku a ciki.” Su ka ce, “Na’am, mun amince da wannan sharadi.” Suka zauna, yam mata suka kawo musu abinci da abinsha.

Bayan sun zauna, sai Halifa yayi duba izuwa ga dan dako da samari uku, sai ya ga samarin nan uku duka ido daya-daya ke gare su, kuma duka na hagu ne. Ya yi al’ajabi a...


Read / Download HIKAYAR DAN DAKO DA YAN MATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album