Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR SINDIBAD DAN DAKO DA SINDIBAD MAI TEKU Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR SINDIBAD DAN DAKO DA SINDIBAD MAI TEKU


HIKAYAR SINDIBAD DAN DAKO DA SINDIBAD MAI TEKU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 35887



HIKAYAR SINDIBAD DAN DAKO DA SINDIBAD MAI TEKU

Reading Time: 2 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 185.35 kb

File Type: txt

Views: 621+

Download: 233+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

1. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.

An yi wani mutum a cikin Birnin Bagadada,
lokacin mulkin Halifa Haruna Rashid, mai suna
Sindibad. Wannan mutum ya kasance talaka ne,
ba shi da wata sana'a sai dako - watau ya rika
daukar wa mutane kaya bisa kansa daga wani
wuri zuwa wani wuri ana biyansa. Wata rana
Sindibad ya yi dakon wasu kaya masu nauyi,
lokacin kuwa ana koda rana, kafin ya isa wurin
da zai kai kayan nan ya yi gumi sharkaf, ga shi
kuma ya gaji likis, sai ya biyo ta gaban wani
babban gida. Da ganin wannan gida na wani
babban attajiri ne, mai ji kudi. An share gaban
gidan tas, an zuba wa shuke-shuken da ke wurin
ruwa. Kodayake ana tsananin zafin rana amma
gaban wannan gida sai wata iska mai sanyi ke
kadawa kamar lokacin hunturu. Sindibad ya hangi
wani dandamali a gaban gidan cikin shuke-
shuken nan, ya ce a ransa, "Bari in dan zauna
wurin nan in sarara kadan." Ya ajiye kayan
dakonsa ya zauna bisa dandamali yana kwasar
sassanyar iskar da ke tashi, sai ya ji wani irin
kamshin abinci mai dadi na jifarsa daga cikin
gidan nan. Can kuma sai ya rika jin kidan molo
da busar sarewa na tashi. Ya jiyo muryoyin 'yan
mata na rera wakoki, sai dai bai jin abin da suke
fada saboda nisa. Daga cikin lambun gidan kuma
tsuntsaye ne iri-iri bisa furannin suna ta rera
nasu wakoki. Da ya duba kasa kuma sai ya ga
wadansu 'yan kananan kwari masu ban sha'awa
suna ta kai da komowa a cikin ciyawar da ta fito
kasan furannin. Sindibad ya yi mamaki matuka
da yadda Allah mai girma da daukaka ya tsara
wadannan abubuwa daki-daki, kowane gwanin
ban sha'awa. Zuciyarsa ta yi fari bisa ga
wadannan abubuwa da ke debe masa kewa.
Amma kuma da ya tuna da halin da yake ciki na
talauci sai ransa ya baci. Ya tashi ya leka cikin
lambu sai ya hango bayi suna ta aiki sai ka ce
gidan wani Sarki, wasu na ban ruwa, wasu na
nome ciyayi, wasu na tsinkar 'ya'yan itace.
Hancinsa kuwa ya ce me zai shaka in ba
kamshin soyayyen nama ba.
Da Sindibad ya ga irin wannan daula da mai
gidan nan ya ke ciki sai ya daga hannayensa
sama yana cewa, "Godiya ta tabbata gare ka ya
Ubangijin talikai, mai arzuta wanda ya so a
lokacin da ya so. Ya Ubangiji ina rokonka, ka
yafe mini dukkanin zunubaina, gare ka kadai nake
neman gafara. Ya Ubangiji kai ne mai yin yadda
ka so ba tare da shawarar kowa ba, kuma babu
wanda ya isa ya tambaye ka don me. Kai ne
Ubangijin sammai da kassai da abin da ke
tsakaninsu. Kai ne mai arzuta wanda ka so, ka
kuma talauta wanda ka so. Kai ne mai daukaka
wanda ka so, ka kuma kaskanta wanda ka so. Na
tabbata babu wani abin bauta wa da gaskiya sai
kai. Hakika kana daukaka wanda ka so kamar
yadda ka daukaka ma'abucin wannan gida. Kana
talauta wanda ka so kamar yadda na tsinci kaina
a ciki." Sai ya wake wadannan baitoci:
Mutum nawa ke wahala tamkata,
Ga wasu sai hutu da sakewa.
Kowace rana ga ni wahalce,
Dauke da kaya babu dagawa.

Dubi wadansu suna nan kwance,
Kullum shan gara da dadawa.
Ba su tunanin daukar kaya,
Mai nauyi ko mai sabawa.
Asalinmu da kai duka daya ne,
Ruwa na maniyi mai turawa.
Banbancinmu akwai shi da dama,
Tamkar na madaci ko zumuwa.
Ya Allahu gare ka na roka,
Ba ka zalunci cutarwa.
Lokacin da Sindibad dan dako ya gama rera
wannan waka sai ya dauki kayan dakonsa ya
dora a kai zai tafi. Sai ga wani bawa ya fito daga
cikin gidan, mai kyakkyawar fuska da
madaidaicin jiki, da tufafi na alfarma. Ya kama
hannun dan dako ya ce, "Shigo ciki shugabana
na kira."
Dan dako ya yi tsaye ya ki shiga cikin gida, ya ce
wa bawa shi sauri yake yi ya kai kayan da ke
bisa kansa. Bawa ya ce babu makawa sai ya
shiga cikin gida. Da dai ya ga bawan nan ba zai
bar shi ya tafi ba sai ya ajiye kayansa a bakin
kofa, inda wani bawa ke gadi, ya bi bawan da aka
aiko suka shiga cikin gida tare. Dan dako ya yi ta
ware ido yana kallon kayan kawar da aka sanya a
cikin gidan. Suka shiga cikin wani babban dakin
shakatawa, suka tarar da mutane zazzaune bisa
ababen zama, kowane daga cikinsu yana sanye
da tufafi na alfarma masu tsadar gaske. Kallo
daya za a yi musu a gane cewa babu daya daga
cikinsu da ya san wani abu wai shi talauci. A
gaban kowane mutum an ajiye akushin nama, da
goran abin sha, da 'ya'yan itace, da furanni masu
kamshin gaske. Ga kuma kuyangi kyawawa suna
kada molo suna waka da rawa a gaban
wadannan mutane. Mutanen nan na zaune ne
sahu-sahu, gwargwadon yawan dukiyar kowa.
Manyan attajirai su ne a sahun farko, masu bi
musu a sahu na bayansu, su ma masu bi musu a
sahun bayansu. A gaban sahun farko akwai wani
mutum dattijo mai tsawon gemu, wanda hurhura
ta fara fitowa jefi-jefi a cikin gemun. Tufafinsa
sun fi duka na sauran mutanen da ke wurin kyau.
Yana da fuska mai annuri da yawan fara'a. Ga
shi da kwarjini da farin jini. Wannan mutum dai
shi ne mai wannan gida. Sindibad dan dako ya
dubi dakin shakatawar nan ya yi ajiyar zuciya, ya
ce a cikin ransa, "Wallahi da a ce mutuwa na yi,
na tashi na gan ni a wannan wuri, da na ce
Aljanna ce. Babu shakka wannan wuri fadar wani
babban Sarki ce, inda yakan zo domin
shakatawa." Ya matsa gaban dattijon nan da ke
gaban mutane ya durkusa ya gaishe shi, ya kuma
gayar da sauran attajiran da ke cikin dakin. Ya
mike tsaye a gabansu kansa a sunkuye yana
duban kasa. Shugaban attajiran, dattijon da yake
zaune a gaban sauran attajirai, ya umurci dan
dako ya matso kusa gare shi. Ya yi masa barka
da zuwa sa'annan ya sa aka kawo masa abin
zama, ya umurce shi da ya zauna. Bayan ya
zauna sai aka kawo masa abinci da abin sha.

Dan dako ya wanke hannunsa, ya yi bismillah ya
gini abinci har sai da ya kai masaba gatari. Ya
wanke hannunsa ya yi hamdala, ya kuma yi wa
attajirai godiya.
Mai gida ya ce masa, "Mun yi murna da
zuwanka. Amma menene sunanka?"
Dan dako ya ce, "Ya shugabana, sunana Sindibad
dan dako. Amma Sindibad din har ya kusa
bacewa sai dai a kira ni da dan dako, domin ita
ce sana'ata."
Mai gida ya wangame baki, alamun mamaki, ya
ce, "Ka kuwa ga sunanmu daya da kai. Ni ma
sunana Sindibad bahariyi ko kuma mai teku. Ana
kirana da mai teku ne saboda yawan tafiye-
tafiyen da na yi a cikin teku. Ko za ka rera mana
wakar nan da muka jiyo kana rerawa a waje?"
Dan dako ya sunkuyar da kansa cikin jin kunya,
ya ce, "Ya shugabana, ka sani cewa idan talauci
ya dabaibaye mutum bai san lokacin da yake
furta wasu kalamai ba."
Mai gida ya ce, "Kada ka ji kunya, ai yanzu ka
zama dan uwana. Na ji dadin wakar ne lokacin da
kake rera ta, shi ya sa nake so ka kara rera mini
ita yanzu." Dan dako ya karkace kai ya kara rera
waka. Yayin da sauran tajirai suka ji wannan
waka sai suka cika da mamaki.
Mai gida ya ce, "Ka sani ya kai dan dako,
labarina abin mamaki ne. Zan gaya maka irin
wahalhalun rayuwar da na shiga har Allah ya ba
ni wannan tarin dukiya da kake gani. Kamar
yadda ka ji ana cewa, zomo ba ya kamuwa daga
zaune, to, wannan gaskiya ne. Domin na sha
wahalar rayuwa iri daban-daban, kafin in zama
yadda nake yanzu. Ba don Allah ya kaddara ina
da tsawon kwana ba ai da tuni an manta da ni
saboda hadurran da na shiga Allah ya kubutar da
ni. Na yi tafiye-tafiye har guda bakwai a cikin
teku, kowace tafiya daya tana kunshe da labari
mai ban tu'ajjibi. Kamar yadda na ce ma ba don
Allah ya kaddare ni da tsawon kwana ba da tuni
na halaka a cikin wadannan tafiye-tafiye." Daga
nan sai Maigida ya daga murya da karfi, yadda
duk wanda ke cikin dakin ke iya jin sa, ya ce, "Ya
ku abokaina attajirai, yau zan gaya muku labarin
tafiye-tafiyen da na yi guda bakwai masu
hatsarin gaske da ban mamaki a cikin teku." Sai
ya ci gaba da labari:

TAFIYAR SINDIBAD TA FARKO A CIKIN TEKU
Mahaifina attajiri ne na gaske mai ji da sulalla.
Dukkan mutanen gari na son shi saboda yawan
kyautarsa da kyawun dabi'unsa. Babban abin da
ke ba mutane mamaki game da mahaifina shi ne
duk da tarin dukiyar nan tasa ba ya da girman kai
ko kadan. Ban girma na yi wayo tare da
mahaifina ba, ya rasu lokacin da nake yaro, ya
bar mini gadon tarin kudinsa da gidaje da gonaki,
kasancewar ni kadai ne dan da ya haifa.

Da na girma na yi wayo, sai idona ya bude da
kudi. Na shiga cikin dukiyar nan ina bundum-
bundum. Ba na cin abinci sai lafiyayye mai kyau
mai tsada, haka ma abin sha. Sutura kuwa sai
irin ta 'ya'yan Sarakuna nake sanyawa. Wurin da
nake kwanciya kuwa ko sarauniyar duniya duka
sai haka. Na yi abokai da yawa, kullum sai in ta
kashe musu gara suna kwasa a fayu. Su kuwa
sai su yi ta zuga ni suna tara mini kasa ina
hayewa, ina jin dadi. Ni kuwa na ci gaba da
facaka da dukiya, a tsammanina ba za ta taba
karewa ba. Haka na dawwama tsawon wani
lokaci, har aka wayi gari ran nan ko dirhami bai
rage mini ba. To, wanda ma ya tattali dukiya ya
ya kare da ita, balle ni da na shiga barnatar da
ita?
Ko da na farga lokaci ya kure mini, domin ban da
gidan da nake ciki babu wani abu da ya rage mini
na dukiya. Hankalina fa ya tashi, ga abokaina duk
sun guje mini saboda yanzu ba ni da sule. Da ma
an ce kuda ba ku biyar mai kayan gawai. Ban ga
laifinsu ba, domin hannu mai miya ake lasa. Wata
rana na yi zaune zugum ina tunanin inda zan
sami dan dirhamin da zan sayi abinci, sai
maganar Shugaba Sulaimanu Dan Dawuda (Tsira
da amincin Allah ya tabbata a gare su) wadda
nakan ji mahaifina yana yawan karantawa ta fado
mini, "Gwamma abu uku da abu uku: gwamma
ranar mutuwa da ranar haihuwa; gwamma kare
mai rai da mataccen zaki; gwamma shiga kabari
da bakin talauci."
Da na tuna da wannan magana sai na tashi na
tattara 'yan sauran komatsan da na mallaka har
da suturata duka, na kai kasuwa na sayar a kan
kudi dirhami dubu uku. Niyata in bi fatake in
shiga duniya wurin fatauci, domin an ce babu
maraya sai raggo, kuma sai an nema akan samu.

Za mu ci gaba.2. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.

... Da na tuna da wannan magana sai na tashi na
tattara 'yan sauran komatsan da na mallaka har
da suturata duka, na kai kasuwa na sayar a kan
kudi dirhami dubu uku. Niyata in bi fatake in
shiga duniya wurin fatauci, domin an ce babu
maraya sai raggo, kuma sai an nema akan samu.
Kamar dai yadda mai waka ke fada a cikin
wadannan baitoci:

Sai an sha wuya akan sha dadi ku ji,
Mai neman kudi duka sai ya sha wuya.

Mai son jauhari a teku yakan zan nitso,
Mai son dukiya yakan shiga can duniya.
Kowacce a kan gado zai sami dukiya,
Wannan ya zama abin yi wa dariya.
Na tafi wurin madugun fatake na gaya masa
niyata ta bin su, na nemi shawara gare shi a kan
hajjar da ya kamata in saya in tafi da ita. Bayan
ya gaya mini hajjar da zan saye, na tafi kasuwa
na sayi dukkan abin da ya fada mini na kai gida
na ajiye ina jiran ranar da ayarin fatake zai tashi.
Da ranar ta zo na kwashi kayana muka shiga
wani babban jirgi tare da fatake, muka fada teku
muka tasar wa Birnin Basara. Muka isa lafiya,
muka dan taba ciniki a nan. Daga nan kuma
muka shiga jirgi muka tsunduma cikin teku. Gaba
da baya, dama da hauni, ba abin da mutum ke
gani sai ruwa. Muka yi ta keta ruwa kwana da
kwanaki, idan muka tarar da gari a bisa tsibiri sai
mu yada zango nan, mu dan taba ciniki sa'annan
mu yi gaba. Haka muka kasance muna tafiya
cikin teku, har wata rana muka iso ga wani dan
karamin tsibiri mai yawan tsire-tsire da furanni
masu ban sha'awa. Ga koramu na gudana da
tsuntsaye na shawagi. Kai! wannan tsibiri da
kyawo yake, ka ce shi wani yanki ne na Aljanna.
Madugunmu ya ce a sauka a wannan wuri a
daure jirgi.

Aka tsayar da jirgi bakin gaba, kowa ya sauka.
Da yake lokacin hunturu ne, sai wasu suka kunna
wuta domin su ji dumi, wasu kuma su dafa
abinci. Wasu kuma, har da ni, muka shiga zagaya
wannan tsibiri domin kashe kwarkwatar ido.

Muka shagala, muka sakankance a cikin wannan
yanayi. Can ba zato ba tsammani sai muka ji
Madugu na kwala mana kira da karfi, "Ya ku
jama'ar fatake! Ku yi gaggawar ceton rayukanku,
ku komo cikin jirgi da sauri! Ku sani wannan wuri
ba tsibiri ba ne face doron bayan wani katon kifi
da ya yunkuro domin shan iska. Ya dade a haka,
shekara da shekaru har rairayi ya taru a bayansa,
tsire-tsire suka fito. Wutar da kuka kunna ta kona
shi, zai nutse cikin ruwa tare da ku. Ku yi sauri
ku tsira da rayukanku kafin ya nutse da ku cikin
ruwa."
Wadanda suke kusa da jirgi suka watsar da abin
da suke yi, na dahuwa da wankin tufafi da
wanka, suka fada cikin jirgi babu shiri. Amma mu
da muke nesa da jirgi kafin mu kawo wurinsa sai
muka ji tsibirin nan ya yi girgiza ya yi kasa da
mu cikin ruwa. Tozayen ruwa suka hadiye mu,
muka nutse cikin teku. Dukkan mutanen da muka
nutse tare suka halaka, amma ni da yake Allah
ya nufe ni ina da sauran shan ruwa a gaba,
wajen buge-bugena sai na ji na bugi wani
gungumen ice, na yi karfin hali na kama shi na
haye. Allah kuwa ya sa icen nan ya taso sama
da ni. Na yi kwance bisansa, ina iyo da kafafuna
iska na ingiza ni. Na hangi jirginmu can nesa
kwarai yana tafiya da wadanda suka tsira. Na ga
ko na yi kira babu wanda zai ji ni, don haka sai
na dogara ga Allah. Na yi ta kallon jirgi har ya
bace daga ganina, daga nan sai na sakankance
ga halaka.
Na kasance bisa wannan ice, tun ina iya iyo da
kafafuna har karfina ya kare, na gaji na bari, na
yi kwance kawai ina jiran mutuwata. Duhun dare
ya lullube ni cikin wannan hali. Iska da rakuman
ruwa suka yi ta tafiya da ni cikin daren nan har
gari ya waye. Allah mai girma da dauka ya nufi
iska ta tura ni kusa ga wani tsbiri mai yawan
itatuwa, wasu daga rassan itatuwan sun sunkuyo
cikin ruwa. Na yi karfin hali na kama reshe daya
na hau saman bishiyar na sauka cikin tsibirin. Da
na mike tsaye domin in yi tafiya sai kafafuna
suka ce ba su san wannan ba, sanyi ya kame su
da mijirya, sun kumbura suntul. Na yanke jiki na
fadi kasa kamar matacce. Jikina ya dime, daga
nan sai wani duhu mai tsanani ya mamaye
idanuna, tunanina ya tsaya cik, ban kara sanin
abin da nake ciki ba. Ashe suma na yi.
Ban farfado daga suman da na yi ba sai da gari
ya waye, bayan rana ta fito ta fara koda ni,
zafinta ya sa na farfado. Na tashi zaune na dubi
kafafuna, na gansu har yanzu a kumbure. Da
naga dai babu dama in mike tsaye in yi tafiya, ga
shi kuma cikina na ta kiran ciroma, sai na fara
rarrafe kamar dan yaro ina tsintar 'ya'yan itace
da suka fado kasa ina ci. Haka na kasance cikin
wannan tsibiri tsawon wasu kwanaki, na...


Read / Download HIKAYAR SINDIBAD DAN DAKO DA SINDIBAD MAI TEKU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album