Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM


HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9070



HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Bukar Mada ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 45.92 kb

File Type: txt

Views: 540+

Download: 121+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

DARE DUBU DA DAYA (187)
HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM
A cikin wani dad’ad’d’en zamani da ya shud’e an yi wani babban sarki mai girman sha’ani da sarauta. Yana da waziri ana kiransa Ibrahimu wanda ke da wata ‘ya wadda ta kai matuk’a wajen kyawo da kwarjini da cikar halitta. Tana da baiwar fasaha da yalwar harshe. Sai dai tana yawan sha da son wasanni da wak’e – wak’e da son jin labarai. Irin baiwar da take da ita ne ya sa jama’a ke mata wak’a suna cewa:
Na je wajenta mai fitinar Turkawa
Har da Larabawa duk ba ta kyale ba
Tana jan hankalina zuwa a gare ta
Tana cewa ni zam mata ba wasa ba
Na ce mata raina fansa ne wurinki
Ba ki san zamani ba shi da sabo ba?
Idan yau kin zama kin haskawa
Gobe zai zamanto ba ke ce ba
Sunanta Alwardi, sunan ya biyo bayan irin kyawonta da cika da kwarjinin da ke gare ta. Sarki ya kasance yana son ganin ta saboda kyawonta. Ya kasance duk shekara sarki kan shirya wani taro wanda ake had’uwa a yi wasanni a motsa jiki a yi farin ciki. Da ranar da ta zo jama’a suka taru da dukkan manyan sarakunan k’asar, ‘yar waziri ta lek’o ta taga tana kallo, ana tsakar wasan sai ta hangi wani saurayi kyakkyawan gaske a cikin masu tsaro wanda ba ta tab’a ganin kyakkyawa kamar sa ba. Ga shi cikin kayan aiki masu kyau sun dace da shi, ga shi da fuska mai ban sha’awa, mai fararen hak’ora da wushirya daidaitacciya yana da yawan fara’a. Mai dogon wuya da faffad’ar kafad’a. Ta dube shi ta sake dubar sa har ta ji ba za ta iya daina kallon sa ba. Da aka jima sai ta cewa uwar goyonta, “wanene wancan saurayin mai kyawon gani haka?”
“Wanne kenan kike nufi?” Uwar goyon ta tambaye ta.
“To bari ya zo wucewa ta nan zan nuna miki shi.” In ji Alwardi
Ta d’auki tuffa ta daidaice shi ta jefe shi da ita, ya waiga da sauri ya d’aga kai inda ya ji jifa, sai ya had’a ido da ‘yar waziri tamkar wata a lokacin da dare ya yi duhu. Ya kalle ta ya sake kallon ta, ya kasa d’auke kai daga kallon ta, yayin da ita ma ta kasa daina kallon sa har sai da ya ji son ta na kwarara cikin zuciyarsa, ya rera wad’annan baitoci:
Kin jefe ni da baka ta idonki,
Kibiya ta harbe ni da ganinki
Ganinki ne ya kashe ni ta taga
Ko kuwa kibiyar da kika harbe ni?
Yayin da aka gama wasa kowa ya kama gaban sa, sai ta ce wa uwar goyonta, "yaya sunan wannan saurayin da na nuna miki?" Ta ce, "sunansa, Anasul Wujudi." Daga nan Alwardi ta tashi ta zauna a kan kujera, zuciyarta na huruwa da wutar bege. Ta yi ajiyar zuciya tana rera wadannan baitoci:
Wanda ya gan ka bai tab'e ba,
Ya Anasil Wujudi kyakkyawa
Na tsinkayi fuska tasa a taro
Ya zamto wata mai haskakawa
Taro ya yi kyau da zuwansa
Ya sa taro armashi shi ne dan baiwa
Yayin da ta gama wak'ar ta rubuta a wani siliki mai kyau ta ninke ta ajiye k'ark'ashin matashinta. Da uwar goyonta ta ga haka sai ta zo kusa da ita tana ba ta magana har ta samu ta yi barci sannan ta sace wannan takardar ta karanta abin da ke ciki ta fahimci lallai ta auka cikin kogin son Anasil Wujudi. Sannan ta mayar da takardar inda take ta koma mazauninta. Da yarinya ta farka sai ta ce da ita, "ya shugabata kin san ni ce mai shawartarki a wasu lamura, nakan shiga damuwa saboda ke. Ki sani shi so shu'umi ne, kuma b'oye shi ba ya k'ara komai sai sake narkar da zuciya tamkar yadda k'arfe ke narkewa idan ya sha wuta, ni ba zan shiga tsakanin so ba." Alwardi ta ce, "menene maganin bege da ciwon so." Uwar goyon ta ce, "maganinsa shi nesaduwa da masoyi."
"To yaya hakan zai samu?" Ta ce, "hakan na samuwa ta hanyar aike tsakanin masoya da tattausan zance da yawan gaisuwa. Wad'annan ke had'a kan masoya abu mai wahala ya zame musu mai sauki. Ni na cancanci na kiyaye sirrinki, kuma a shirye nake na zama 'yar aike tsakanin ku." Da yarinya ta ji haka sai zuciyarta ta cika da farin ciki amma ta yi shiru da maganar ta k'I fad'awa kowa. Ta ce a ran ta. 'Babu wanda zan fad'awa komai kuma babu wanda zan amince wa a wannan lamari tukunna. Wannan d'in ma sai na jarraba ta." Tsohuwa ta ce mata, "ya shugabata, ni na gani a cikin mafarki cewa wani mutum ya zo gare ni ya ce min, 'uwargijiyarki da Anasil Wujudi suna son junansu, ki tashi ki zama jakadiya tsakaninsu, ki b'oye lamarinsu alheri mai yawa zai faru gare ki idan kin aikata haka.' To kin ji mafarkin da na yi. Yanzu al'amari na gare ki. Alwardi ta ce bayan ta ji irin mafarkin da tsohuwa ta yi.
A nan asuba ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 372
A dare na d’ari uku da saba’in da biyu, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshaƙin sarki, Bayan yarinya ta ji bayanin tsohuwa game da mafarkin da ta yi, sai ta ce da ita, “da gaske kike za ki b’oye sirrina ya uwar goyona?” Tsohuwa ta ce, “ ta yaya zan kasa b’oye sirri alhali ina daga ‘ya’ya tsarkaka?” Sannan yarinyar ta d’aga matashin kanta ta d’auko takardar nan da ta rubuta ta, ta da ka wa tsohuwa ta ce ta tafi ta kai wa saurayi Anasul wujud. Sannan ta ce ta tsaya ta karb’o amsa. Tsohuwa ta d’auki takarda ta tafi zuwa wajensa ta ba shi, ya karanta ya fahimci abin da ta k’unsa sannan ya rubuta a bayan takardar amsa kamarhaka:
Ina maimaita begenki a zuciyata,
Amma na kasance ina b’oyewa
Halin da nake ciki yana fassara
Hawayena suna ta faman zubowa
Idanuna na ciwo da gudun zargawa
Ni na kasance mai yawan kewarki
Tun lokacin nan da muka zam ganuwa
Zuciya na cikin duhu k’warai da ita
Begena da kewar ki kullum na k’aruwa
Ya ninke takardar ya sumbace ta, ya ba wa tsohuwa ya ce, “ki isar min da gaisuwata ga Gimbiya.” Ta juya ta tafi ta kai mata sak’o. Bayan ta karanta ta fahimci sak’on sannan ta rubuta a k’arkashin takardar baitoci kamar haka:
Ya mai k’unar zuciya da ganinmu,
Yi hak’uri ka rabauta daga gunmu
Mun yi sanin cewa son ka gare mu
Yana nan kamar yadda yake wajenmu
Zuciyarka tana cikin k’aunarmu
Ka jira dare ya zo domin had’uwarmu
Sharad’in kenan mu hadu ni da kai
Domin kashe wutar begen ranmu
An zuba k’aya a wurin kwanciyarmu
Hak’ark’arinmu ba maraba da jikinmu02 HIKAYAR ANASIL WAJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

Ta ninke takarda ta ba wa magoyiyarta ta tafi domin zuwa wajen saurayi. Tana isa k’ofa ta had’u da mai tsaron k’ofa wani baba ne mai girman jiki. Ya daka mata tsawa yana cewa, “ina za ki?!” Ta ce, “gidan wanka za ni.” To amma yadda ta ba shi amsa jikinta na rawa ba ta san lokacin da ta jefar da wasik’ar ba. D’aya daga babanni ya gan ta a k’asa ya d’auka. Yayin da uwar goyon ta fita waje ta duba babu takarda, sai ta juya baya ta shaida wa uwargijiyarta abin da ya wakana.
Waziri na zaune a kujera cikin zaurensa sai baba ya shiga wajensa ya dank’a masa wannan takardar ya ce “na tsinta a nan waje yanzun nan.” Waziri ya karb’i takarda ya karanta, ya duba ta sosai ya gane hannun ‘yarsa. Ya fashe da kuka sannan ya tashi ya tafi wajen uwar yarinyar yana kuka duk ya jik’a gemunsa. Ta ce masa, “me ya faru kake kuka haka?” ya ba ta amsa ya ce, dubi wannan takarda ki gani.” Ta karbi takarda ita ma ta gane cewa wasik’ar soyayya ce daga ‘yarta zuwa ga wani mai suna Anasul Wujudi, ita ma sai ta kama kuka, amma daga bisani sai ta dangana ta natsu duk da hawaye na kwarara a idanunta ta ce da mijinta, “ya shugabana kuka ba zai mana amfani ba, abu ma fi muhimmanci shi ne yadda za ka kiyaye martabarka da mutuncinka game da al’amarin ‘yarka.” Ta ci gaba da ba shi magana har zuciyarsa ta d’an yi haske daga k’uncin da ya shiga. Ya ce da ita, “tsoron da nake game da wannan yarinyar saboda ban san halin yaron ba. Kuma shin kin san cewa sarki na matuk’ar son ta kuwa? Tsorona guda biyu ne, na farko game da ni kaina, na biyu kuma saboda sarki yadda Yake ji da Anasul Wujudi idan wannan zancen ya je kunnensa kashinmu ya bushe. Me kike gani za mu yi?”

Waziri ya tambayi matarsa game da al’amarin ‘yar su ya ce, “Me kike gani za mu yi?
Ta ce masa, “yi hak’uri tukunna har na yi istikhara.” Ta d’aura alwalla ta yi sallah raka’a biyu sannan ta yi addu’ar istikhara kamar yadda ma’aiki mai tsira da aminci su tabbbata a gare shi ya koyar. Bayan ta kammala ta ce da mijinta, “a cikin tsakiyar bahar kogin taska akwai wani dutse ana kiran sa dutsen sakla. Dalilin ambatonsa da wannan sunan shi ne babu wanda zai je gare shi face ya sha wahala. Ka yi mata wurin zama a can.” Waziri da matarsa suka amince za su gina fada a can su kai ‘yarsu da dukkan abubuwan buk’ata. Za a rik’a kai mata komai na shekara guda tare da dukkan kuyanginta da babanni da sauran hadimai. Ya samu masasska’a da magina da masu zane suka gina wani babban gida wanda ba a tab’a ganin irin sa ba. Sannan ya sa aka shirya dukkan komai aka yi shirin tafiya, waziri ya shiga wurin ‘yarsa cikin dare ya ce ta fito domin su tafi yawon bud’e ido. Ta fito ta ga an kammala shiri tsaf ana jiran ta. Zuciyarta ta yi k’unci saboda rashin sanin wajen da za a je, ta ji kewar rabuwa da mutanenta. Ta yi ta kuka mai tsanani, ta rubuta wad’annan baitoci a k’ofar gidan domin sanar wa Anasil Wujudi halin da ta tsinci kanta. Tana mai fatar idan ya zo wucewa ko ya yi nufin ganin ta ya ga wannan abin da ya zagwanye mata zuciya, ya yank’wane mata fata, ya narkar da nama gami da sanya kwararar hawaye. Ga abin da ta rubuta:
Domin Allah mutan gidanmu,
Idan masoyina ya zo wajenku
Ku gaishe shi da kyau da kyau
Daga gu na ku fad’a da kanku
Ku fad’a masa na tafi wurin nesa
Ban san inda za a kai ni ba gare ku
An d’auke ni cikin dare mai duhu
Hatta tsuntsaye tuni sun barcinsu
Ku ce masa da sannu hali zai samar
Da had’uwar masoya biyu a ranaku
Na gani an cika kaskon nisantar mu
Amma hali da sannu zai bar shakku
Ni kam na da’u hak’uri sai wata ran
Kai ma ka yi hakuri da sannu ma sadu
Yayin da ta gama rubuta wak’ar ta hau bisa abin hawan da aka tanadar mata suka d’unguma suna wucewa da keta jazirori da fak’uk’uwa da jigayi da kwaruruwa da wurin tudu da burji har suka sadu zuwa ga kogin gab’ar taska. Suka sauka a nan suka kafa laima suka huta sannan suka shigar da ita wani babban jirgi suka tuk’a zuwa dutsen sakla. Waziri ya umarce su da idan sun kai ta gidan da aka gina a shigar da ita da jama’arta sannan a dawo a karya gadar da ke sadar da mutum zuwa gidan. Jirgin kuma a d’auke shi daga kogin. Suka aikata umarninsa sannan suka dawo suna kuka. Wannan kenan game da al’amarinsu.
Amma Anasul Wujudi kuwa da ya farka da asuba ya yi sallah sai ya shirya ya hau dokinsa ya tafi wurin aiki, a hanyar dawowarsa ya biyo ta k’ofar gidan waziri bisa zummar ko zai samu yin ido hud’u da abar k’aunarsa ko kuwa wani abokin aikinsa domin ya zauna nan wurin sa. Da ya iso gidan bai ga kowa ba, ya d’aga kai k’ofar gidan da ya ga rubutu ya karanta. Yana gama karantawa ya ji hanjin cikinsa ya d’auki zafi, zuciyarsa ta yi tsanani. Ya juya zuwa gidansa bai san halin da yake ciki ba, ya kwanta bai fad’awa kowa halin da yake ciki ba. Da al’amarin ya tsananta gare shi, wutar soyaya ta ruru a zuciyarsa, sai ya tashi ya yi shigar masu bara ya fita daji bai san ininda yake tafiya ba cikin dare. Ya yi ta tafiya a wannan daren har gari ya waye da tsakar rana bai fasa tafiya ba. Zafin rana ya tsananta, duwatsu suka zama tamkar wuta, ga gajiya da yunwa da k’ishirwa na gallabarsa. Can ya hangi wata bishiya wadda ruwa ke gudana a k’ark’ashinta. Ya tafi ya zauna k’ark’ashin inuwarta ya yi nufin shan ruwan amma ya rasa mad’ebi hannunsa bai kai ba ballantana bakinsa. Tuni yanayin fuskarsa ya sauya, ya motse, ga k’afafunsa sun kumbura saboda tafiya da wahala. Ya karkata kai yana rera wad’annan baitoci:
Masoyi ya sha giyar begen masoyi,
Wanda ya dogari da shi a farin ciki
Soyayya ta azabtar da mu k’warai
Mun yi nisa ba ruwa balle abinci
Yaya rayuwa za ta yi dad’i babu ke,
Masoyiyata kin tafi tamkar mafarki
Na k’one da wutar so kewar Gimbiya
Ga ni nan tafe ko’ina ina neman ki
Da ya gama wak’ar ya fashe da kuka, ya yi ta kuka har k’asar inda yake zaune ta jik’e da hawayensa. Daga nan ya tashi ya bar wannan wuri ya yi ta tafiya yana keta daji da tudu da kwari har gab’b’ansa suka gaji, gashin kansa ya jik’e da gumi, idanunsa suka yi rauni. Yana wannan hali sai ga wani zaki ya b’ullo mai ban tsoro, gashinsa kamar mashi, kansa kamar k’ubba, bakinsa kamar k’ofar d’aki, hak’oransa kuwa kamar na giwa. Yayin da Anasil Wujudi ya ga wannan dabbar ta taso gare shi haik’an sai ya sakankance da mutuwa, ya kalli ka’aba yana maimaita kalmar shahada. Ya karanta a littafi cewa duk wanda ya gamu da zaki a daji idan ya yi masa ladabi, ya yi masa zance cikin k’ask’anta kai za su rabu lafiya. Saboda haka ya tausasa harshe yana cewa, “ya babban zaki, zakin zakoki, zakin dukkan dabbobi daji kai ne babbansu ko sun k’i ko sun so. Ya kai babbar halitta uban samari da tsofaffin dabbobi. Sarki mai mulkin dabbobi. Ka sani ni mai bege ne wanda na rabu abar begena, na karkata ga barin kyakkyawan halina, na bar muhallina mai dad’i na taho nan. Ka ji tausayina, ka dubi wahalata da begena. Yayin da zaki ya ji wannan maganar sai ya jinkirta gare shi ya zauna tsugunne a kan kafafunsa ya d’aga kansa sama kamar yana sauraren wani abu. Can an jima sai ya rik’a kartar k’asa da daginsa, daga nan ya rik’a wasa da su. Yayin da Anasil Wujudi ya ga haka sai ya rera wad’annan baitoci:
Ya zakin daji kana son...


Read / Download HIKAYAR ANASIL WUJUDI DA MASOYIYARSA ALWARDI FIL AKMAM

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album