Join Our WhatsApp Group

BA ZAN BARSHI BA Complete Hausa Novel Document by BA ZAN BARSHI BA


BA ZAN BARSHI BA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 167088



BA ZAN BARSHI BA

Reading Time: 13 Hours

Added On: 19, Sep 2023

Author: Billy Giro ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 835.57 kb

File Type: txt

Views: 579+

Download: 666+

Last download: 2 days ago

Description/Story: Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)


``🔮BAZAN BAR SHI BA!🔮```

*Na Billy giro😊*

🔮🔮🔮🔮񛠊
_*page 1*_And 2.


Rayyanat! Rayyanat!! Rayyanat!!!
Er 16 yrs ce ta fito da gudu tana fad'in "Na'am Baffanah"
Shiru baffan nata yayi yana mai kallon Rayyanat wacce ta kasance chocolate ba qiba ba rama tana da kyau daidai gwargwado tana sanye da riga da zane bara da bana sae dankwalin kanta da shima ba kalarkayan jikin ta bane ga zanen jikinta duk gabad'ayan sa dashi ne ba masoka tsintsinya gashi ta riqe wani gurin da ya yage bata son aga jikin ta yace"Rayyanat baki sami allura da zare bane wannan karon? Abba ban samu ba naje suka ce baza su ara min ba sun gaji da siya ina qare musu zaren"cikin muryar kuka ta qarasa maganar ,Baffan ta yace"kar kiyi kuka Rayyant inshaAllah yau idan mai gari ya biyani kud'in noman da nake masa zan saya miki allura da zare domin ki huta da aro maqota kinji"to Baffanah na gode Allah yasa ayi nasara fiye da kullum"
yace "Amin Rayyant, zan tafi ki kula da kanki banda yawon maqota"inshaAllah amma Abba yau baka so na raka ne?Rayyanat ta yaya zaki fita bayan zanin ki ya yage ga samarin da ke dandali a tsakiyar gari"Haka ne Baffa Allah kiyaye hanya"Amin Amin.
Daga haka ya fita rataye da fartanya kan kafad'ar shi inda Rayyant tabi mahaifin nata da kallo wanda shima tufafin jikin sa duk sun tsufa sun tamure.
sae da ta daina hango shi sannan ta koma d'aki tayi zaune
tana qarewa d'an akurkin d'akin ta kallo wanda ba wasu kayan kirki a ciki face d'an kunshin tufafin ta da baza su wuce kala biyu zuwa uku ba sae tsofuwar tabamar da take kwanciya da wani pillow akai mai kama latsatstsen biredi sae gidan sauro da aka dunqule shi aka soka jikin taga sae wasu kwallaye guda biyu da ke cikin d'akin da bansan meye a cikin su ba.
Tana cikin qarewa d'akin kallo cikin ta ya shiga qugi sbd yunwar da ke addabar ta wacce tun safiyar jiya da suka ci abinci ita da Baffan ta har yau washe gari basu sake samun abinda suka ci ba.

Kwanciya tayi ko zata samu bacci ya d'auke ta kafin Baffan ta ya dawo amma yunwa ta hana ta bacci kamar yanda tayi fama a daren jiya wanda sae da ta cika cikin ta da ruwa ta samu tayi bacci haka ko yanxu tashi tayi taje waje gurin randar ruwa ta cika cikin ta tap ta koma ta kwanta .
Har bacci ya soma d'aukar ta ne taji sallamar wata qawar ta mai suna "Sarat"

Sae da Rayyanat ta amsa mata sallama sannan ta shigo .
Yarinya ce doguwa er sililiya baka wacce ita ma tana da kyaun ta dai dai gwargwado zama tayi tace"Rayyanat kiyi haquri fa tun jiya naso ace nazo amma shiryen shiryen tafiyar da muke yi na komawa Birni bai barni ba "
D'an guntun murmushi Rayyanat tayi taji kamar ita ce zasu je Birni ita da Baffan ta sbd ta kasance tana mugun son zuwa Birni amma ko sau d'aya bata ta6a samun zuwa ba.

Sarat ta miqa mata wata er baqar leda wacce ake kira cefanen mutum d'aya tace"dan Allah kar ki ce baza ki kar6a ba sbd nasan halin ki kuma ban saya miki don wata manufa ba sae don nasan kina bala'in son rogo inda har ka kasuwa naje na saya miki amma kiyi haquri nasan ba kya son haka "
ba komai Sarat a yau zan kar6i kyautar ki sbd zaki tafi ki barni ban kuma san yaushe zamu sake had'uwa ba nagode amma yaushe ne zakuyi tafiyar ?a yau d'in nan kuma a yanzu shiyasa na baki haquri kan rashin zuwa na tun jiya nima ban so haka ba wlh...kar ki damu domin nafi kowa sanin yanda kika damu dani shiyasa a kullum bani da wata qawar da ta fiki...Uhm na gode Rayyanat ni zan tafi su Abba na a bakin qofar gida da mota suna jiran fitowa ta .
Nan Rayyanat ta tashi suka fito inda Rayyanat ta russuna cikin ladabi ta gaida iyayen Sarat kafin wani d'an matashin saurayi ya fito a cikin motar wanda sak Sarat ce da alama yayanta ne.
Da sauri Rayyanat ta duqar da kanta qasa cikin jin kunya tana d'an kame kame gayen yayi murmushi yace"ako yaushe ina sonki Rayyanat ba kuma zan daina ba duk rintsi duk wuya ina tare da sonki a cikin zuciya ta koda kuwa bana raye.

Ga wannan na roqe ki ki kar6i kyauta ta ta farko da na ta6a baki wanda a duk lokacin da ki ka sanya abinda ke ciki zaki kasance cikin farin ciki sbd tamkar kina tare da nine,
ina fatar masoyiya ta zata kar6i kyautar da na mata ko don tsalkakekken son da take min,,,cikin tausassar muryar ta mai sa shi natsuwa tace "yaya Anwar ban ta6a kar6ar kyautar ko wane d'a namiji ba face ta mahaifina amma yau zan fara a kanka kuma nayi maka alqawari kai kad'ai ne d'a namijin da zan ci gaba da kar6ar kyautar sa har abada kuwa bazan ta6a sa6a alqawarin da na maka ba, ka riqa tuna hakan ako yaushe domin nima na riqa kiyaye wa"
A hankali ya lumshe kyawawan idanun sa yace"InshaAllah Rayyanat bye mu zamu tafi dan Allah ki kula min da kanki "
Daga haka ya shiga mota ya zauna seat d'in driver ya tashi mota yana danne hawayen da ke qoqarin zubo mishi yayinda yake kallon fuskar Rayyanat ta jikin mirror.
Sarat kuwa bye bye take yiwa Rayyanat yayinda kowannen su ke fitar da hawaye a idon shi .
Tsaye take har suka 6ace ma ganin ta nan ta kalli Viva ledar da ke hanun ta ta rungume ta tsam a qirjin ta wasu zafafan hawaye suka gangaro kan kumatun ta inda a hankali ta furta cewa"ina sonka yaya Anwar ba kuma zan daina sonka ba har abada duk rintsi duk wuya ina tare da kai koda kuwa bana raye to kuwa ruhi na zai kasance tare da kai"

🔮🔮🔮🔮🔮

_*Page 2*_

Komawa tayi daga ciki cike da kewar Anwar da Sarat .
Bata yarda ta bud'e ledar ba ta ajiye kusa da ledar rogon da Sarat ta kawo mata a cewar sae Mahaifin ta ya dawo ko za a bud'e komai.

Har guraren la'asar mahaifin ta bai dawo ba haka taci zama duk yunwar da take fama da ita bata ci rogon ba iya karta ta qara sakawa cikin ta ruwa .

Sae guraren qarfe biyar mahaifin ta ya dawo yayinda fuskar shi take cike da damuwa.
Rayyanat taje a natse cikin murna tana tarbon mahaifin ta inda ta kai hannu ta d'auke fartanyar da ke kan kafad'ar sa ta kuma d'obo ruwa ta bashi,
bai sha ruwan ba sae hannun sa ya tara ya wanke ya zauna a sukwane tare da dafe kan shi.
Rayyanat da ko kad'an bata son ganin mahaifin ta cikin damuwa nan take idanun ta suka ciko da qwallah ta durqusa a gaban shi tare da jaye hannayen sa da ya dafe kansa.
Muryar ta na rawar kuka tace "me yake faruwa ne Baffa dan Allah ka sanar da ni"
A hankali mahaifin ta ya d'ago idanuwan sa da sukayi jajir ya goge en guntayen hawayen da ke gefen su yace"Rayyanat na kasance bani da wani buri a rayuwa sae don ganin na faranta miki hakan yasa tun lokacin da mahaifiyar ki ta rasu ta barki kina jinjira naqi nayi aure don kawai kar ki shiga quncin rayuwa domin bansan matar da zan auro wace iri bace shiyasa na haqura da aure gavad'aya sbd zan iya zamowa auri sake idan har na had'u da matan da ke quntata miki ni kuma bana son kasance wa haka kuma gashi bani da wasu en uwa da zan kaiki a gurin su shiyasa na za6i na raine ki da hannu na,yayinda na zame miki tamkar uwa na kuma so na kasance uban da ba wani abu da zaki nema ki rasa amma talauci bai bar na miki haka ba kiyi haquri Rayyanat da na kasance uban da kullum sae kin nema kin rasa ba yin kaina bane wannan jarabtar ubangiji ce wacce a kullum nake roqon Allah ya kawo muna qarshen ta muna masu lashe jarabawar ba tare da mun sa6a masa ba.
Rayyanat nasan ke 'yace ta gari zaki fahimci abinda nake nufi da kuma abinda zan fad'a a yanzu.
Rayyanat a yau zamu kwashe komatsan mu mu koma daji da zama can gurin gonar mai gari da nake masa noma....Baffa me yasa zamu koma inda ba kowa ?dole ne Rayyanat sanin kan ki ne wannan gidan ba nawa bane kuma bani da wani gida na kaina haya muke kuma sanin kanki ne duk wata na kanyi qoqarin ganin na biya kud'in haya koda kuwa su kad'ai ne suka rage mana na abinci amma a yau Bala yaje har gurin mai gari yakai qara ta kan cewa bana biyan shi kud'in haya wai har ma yana bina na wata biyu naqi na biya shi, duk da cewa nayi ma mai gari bayanin cewa ba gaskiya ya fad'a ba amma mai gari ya zare kud'in noman da nake binsa na wata d'aya ya bawa Bala na zamo bani da ko sisi kuma Bala ya nemi na bar masa gida wai yana so zai saka wad'an da ke biyan sa duk wata.
Ba irin haqurin da ban bashi ba amma yaqi shiyasa mai gari yace idan har zan iya ya bani dama naje can kusa da gonar shi na haqa bukka mu riqa zaman mu a can tunda ba wasu namun dajin da ke cutarwa a gurin.
Cikin kuka Rayyanat tace"Allah yasa haka shi yafi Alhairi Baffa"Amin Rayyanat bari naje cikin gari naga ko zan sami wani aikin da zanyi a biyani mu samu abinda muka ci kafin mu kwanta"
Kallon mahaifin ta tayi kafin take share hawayen da ke kan fuskar ta tace"Baffa akwai rogo da Sarat ta kawo min ka bari kaci tukun ko zaka fita"
Aa Rayyanat ki dai ci in yaso idan Allah yasa nayi nasara sae mu qara cin abinda ya samu,, Baffa rogon fa mai yawa ne kuma tun safe na ajiye shi sae kazo muci tare,,,girgiza kansa yayi yayinda yake qara jin son er shi sbd yasan halin Rayyanat komai qanqantar abu bata yarda taci ita kad'ai sae tare da shi.
Nan ya dafa kanta yace"Allah yayi miki albarka Rayyanat ya kuma sanya nasara da albarka a cikin al'amurranki ya kuma sauya miki wannan rayuwa da muke ciki ma'ana nan gaba kad'an ki kasance cikin wadata da walwala had'e jin dad'i mai d'orewa har izuwa qarshen rayuwar ki"Amin Baffa na gode.
Nan ta d'auko musu rogo suka ci bayan sun kammala ta d'auko ledar da Anwar ya bata ta bawa Baffan ta ba tare da tace da shi komai ba yace"Rayyanat daga ina wannan ledar ta fito? Cikin jin kunya ta duqar da kanta ta kasa cewa komai wanda hakan yasa nan take ya fahimci inda ledar ta fito yace"Anwar ko sun tafi kenan? Eh sun tafi tun d'azu ,,to Allah ya kiyaye hanya ,,Amin Baffa,,tace"Baffa kayi haquri ban kar6a ba sae don ya had'a ni da Allah"ba komai kuma ai ba a maida hannun kyauta baya.
Nan Abban ta yace ta bud'e kayan koda ta bud'e kala biyu ne masu kyau less da atamfa kuma da hijab kala biyu wato kalar kayan sae takalmi taki d'aya da kuma tokar wanka mai had'e da set d'in turare sae wata envelope da aka d'ora akai wacce ta bawa Baffan ta tace shi zai bud'e sbd tana ganin kamar kud'i ne a ciki koda mafahaifin ta ya bud'e en dubu dubu ne sabbi dal har dubu biyar sae wani tsadadden zoben azurfa black an white da wata er guntuwar takarda soke a cikin zoben.
kasa had'a ido tayi da Baffan ta yayinda yake miqa mata kayan bata kar6i kud'i ba sae zobe ta kar6a had'e da takarda tace"Baffa ai a gurin ka kud'in ya kamata su kasance da kuma wad'anan tufafin"Rayyanat ki ajiye komai a gurin ki sbd kinga fita zanyi naje naga gurin da ya kamata mu haqa bukka na fara aikin kafin gobe sbd tun da safe yake so mu bar gidan"
Baffa muje na taya ka ba musu yace "to adana kayan muje"
kwalla taje ta bud'e ta saka kayan suka fita.

Da suka fita basu suka dawo ba sae yamma liqis.

Da dare Rayyanat bata iya bacci ba sae da ta d'auko wannan takardar ta fara karantawa kamar haka
*_"Rayyanat ina so ki saka wannan zoben a yanzu kuma kimin alqawari baza ki ta6a cire shi ba har abada domin cire wannan zoben tamkar kin cire ni a cikin zuciyar ki ne_*

Murmushi ne ya bayyana a fuskar ta yayinda take sanya zoben inda ta rufe idon ta a hankali tace"
*_yaya Anwar nayi maka alqawari wannan zoben ba zai ta6a fita a yatsa ta ba sae dai idan mutuwa nayi aka cire shi_*

Daga haka ta kwanta sae kallon yanda zoben yayi matuqar kyau a yatsan ta take har ta shiga magana a ranta cewa
_"Da ace ko mutuwa nayi baza a raba ni da zoben nan ba da nafi kowa farin ciki"_
Yaya Anwar ina ma ace zoben nan mai 6acewa ne da na bashi umarnin ya 6ace a lokacin da na mutu har akaini makwanci na don dai kawai ya kasance ina tare da kai a duk inda nake ko da yake ko ba zoben nan kana tare da ni sbd kana cikin zuciya ta ba kuma zan ta6a iya fitar da kai ba kamar yanda hanta bata iya rabo da jini.
Tana maganar ne a fili cikin natsuwa tamkar anwar na kusa da ita.

Washe gari tun da asuba ta had'u da mummunan labari su Anwar sunyi had'arin mota kuma ba wanda ya rayu a cikin su kuka taci tamkar ranta zai fita Baffan ta kuwa sae bata baki yake yana aikin rarrashi.
Suna cikin haka ne Bala yazo cike da masifa yasa aka yi ta fitar da kayan su ana watsi da su wanda hakan ya qara sa Rayyanat cikin wani yanayi ganin yanda ake wulaqanta mahaifin ta...


Read / Download BA ZAN BARSHI BA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album