Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

A GARINMU Complete Hausa Novel Document by A GARINMU


A GARINMU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 156639



A GARINMU

Reading Time: 13 Hours

Added On: 13, Nov 2024

Author: HAERMEEBRAERH ,Haermeebrah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 762.96 kb

File Type: txt

Views: 562+

Download: 1030+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: *A GARIN MU*




WRITTEN BY HAERMEEBRAEH




PAGE 1:

Jihar Zamfara, jiha ce mai tarin albarka, jiha ce mai cike da arziqi, na noma, na ma'adanai, da kiwo, Allah ya azurta Zamfara da mutanen kirki tun kafuwar ta, ya sanya ta zama qasa mai tarin albarka, da ruqo da addinin musulunci, jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Nigeria da suka yi tashe a tsaida shari'ar Musulunci shekaru masu yawa da suka gabata.

An san mutanen jihar Zamfara da son zaman lafiya, gaskiya, amana, juriya, jarumta,ilimi, kasuwanci, sana'o'i, sarauta, da dik wani abu na jin dadin rayuwa.

Zamfara gari ne na zaman lafiya a baya, gari ne da aka yanke shi daga jihar Sokoto,a zamanin General Sani Abacha, a 1st October 1996, shine shugaban qasar da ya ba ta 'yancin ta, ta zama jaha kamar sauran jahohi a qasar nan ta Nigeria.

Jihar Zamfara ta tara sarakuna, da shuwagabannin gwamnati masu adalci a baya, ta yanda qasar ta zamanto a koda yaushe cikin aminci take, kowanne dan jahar kuma kowanne yare, da addini ya ke zaune cikin kwanciyar hankali, ba fargaba, ba tashin hankali, balle tsoro.

Wannan ita ce jihar Zamfara a shekarun da suka gabata.

Garin Gusau shi ne babban birnin jihar zamfara, gari ne da ya qunshi al'umma kala kala, mabanbanta, yaruka daban_daban, da addinai daban-daban.

Gwamna Halliru Murtala Gusau, shi ne Gwamna mai ci, ya na zaune da iyalan shi a unguwar GRA, Gwamna Halliru ba shi da abin so a duniya sama da iyalin shi, dan haka komai ya ke yi a duniyar siyasa domin su ne, Hajiya Ikilima wadda aka fi kira da Hajiya Ikee, ita ce matar shi, sai yaran su biyu Sultan me shakara Ashirin da tara, da Sultana Mai shekara Ashirin da biyar,dikkan su sun yi karatu ne a University of Westminster London, in da Sultan na da BSc a Architectural Technology, Sultana Kuma na da BA a Arabic and linguistics.

Dikkanin su sun samu gata, kalar wanda in da za a hada su da sauran yaran gwamnonin Nigeria, za a yi wahala a samu ya su, kama daga dukiya,da tsaro, saboda tsaron da suke samu in Sun samu amincewar iyayen su har su ka fita, to sai mutum ya rantse Gwamna ne da kan shi ke yawo, motocin sojoji da 'yan sanda ne kawai mutum zai hango su na biye da su dik inda suka dosa.

Yau kusan sati biyu kenan, Sultana na roqar mahaifiyar ta da su bata dama ta fara aiki itama, dan kasar ta ta mori ilimin da Allah ya hore mata, yau ma kamar kullum, Hajiya Ikee shiru ta mata ta ci gaba da ɗaukan inibin ta ta na jefawa a baki, hankali kwance, qafar ta kuwa mai aikin su ce Me Buruji ke matsa mata, kan ta a qasa, saboda tsoron had'a ido da uwar gidan nata.

Cikin tausaya wa Sultana ta ce,

" Baaba je ki kitchen za mu yi magana da Hajiya"

"To ran ki shi dade"

A duqe ta miqe kamar wadda take a fadar matar sarki.

Da sauri Hajiya Ikee ta kalli Sultana ta ce,

"Na hwa san mi kike yi Sultana ,wato Ina Sanya Me Buruji wahala ko? Shi na kin ka kore ta, tau ki kiyaye ni, kar ki koma yi min haka nan, and da ki ke damu na akan ki hwara aiki,Ni misshamin kai da aikin ki? Daddyn ku ya ce ba za ku yi aiki ba, kuma na goyi da bayan shi, % saboda ku ba diyan talaka kuke ba, albashin ga dai in shi ki ka bida ana baki duk wata, dangi ma aka basu albashi ba tare da sun tai aikin komi ba balle ke? Daga yau kar ke ko dan uwan ki ku sake tunkara ta da wanga batu, kin ishen da d'umin banza, haba"

Cikin fushi ta tashi za ta bar tafkeke kuma qayataccen parlourn na su, wanda tsayawa ma fadin had'uwar shi, bata lokacin mai karatu ne.

Da sauri Sultana ta rungume Mahaifiyar tata ta baya, tare da dora kan ta a saman bayan ta, cikin kalamai masu sauqi Sultana ke magana.

"Mum Dan Allah ki hakuri, indai ni ta, ban koma yin magana akan aiki, zan hakura, ba zan sake maganar ba, ki dena hushi pls"

Juyawa ta Yi ta na Dan murmishi, sannan ta zauna a kujerar da ta tashi, sannan ta ce,

"Ni wallah mamaki kuke ban diyan ga, kamar ba kuyi karatu qasar waje ba, kamar wadan da sun ka yi cudanya da talakawa, Allah ya daukaka ku, amma kullum burin ku bai wuce ku ga kun wulaqanta kanun ku ba,"

Murmushin takaici Sultana ta yi, dan ta san in tai magana, yanzu ran mahaifiyar ta zai qara ɓaci.

Amma tabbas ko a dangi ana mamakin yanayin tarbiyyar su, wadda ta sha bam_bam da ta iyayen su.

Su kuwa ba su ga abun mamaki ba, dan sun san yanda akai suka samu tarbiyyar nan, sannan sun sani Ubangiji Allah ya na yin yadda ya so, a sanda ya so ba tare da neman izinin kowa ba, sun sani da izinin shi, da ikon shi ne suka zamo yara na gari, tarbiyyar da suke da ita ta sha banban da halayyar iyayen su.

Lokacin da aka kai su Sultana makaranta a qasar waje, sun kammala primary a nan Nigeria a Abuja, makarantar hade take da islamiyya, mai matuqar tsada ce, dan haka yara suna samun ilimi na kowane fanni, sun haddace qur'ani tun su na Nigeria, wanda iyayen su ma basu wani damu da hakan ba, fatan su su samu kyakkyawan result da zai kai yaran babbar makarantar gaba da primary, dake qasar turawa.

Kuma sun samu nasarar hakan, an kai su makarantar gaba da Sakandire a London,ba su samu damar ci gaba da karatun Islama ba, sai bayan da suka shiga jami'a lokacin hankali ya shige su, Sultan ya ga haddar su na zubewa, shi ne ya sama masu wani malami Bature ne,amma Musulmi masanin addini sosai, ya ke koyar da su addinin su, ba tare da mahaifan sun wani damu ba, su dai abinda suka fi damuwa da shi shine, yaran su su zama masu ilimin boko, ta yanda daraja da qima, tare da ajin su zai dagu a cikin sa'annin su.

Hira suka ci gaba da yi, amma ran Sultana ba bu dadi, ta so matuqa ta yi lecturing shi ne babban burin ta a rayuwa.

**********************

Me Buruji na komawa bangaren masu aiki,ta ja hannun kishiyar ta me suna Lamishi, suka koma gefe,nan ta labarta mata me ya faru a ciki, kama baki Lamishi ta yi, sannan t ce,

"Ohhh diyan ga na Gwauna ba su samu iyayen kwarai ba wallah, wadda ki ka san ba su na sun ka haihe su ba, Allah shi kyauta, mu je ki isuwa aikin ki, da kin ka tai kin ka bari, walle ban qarasa maki,Nima nawwa ya isan"

"Lamishi hoo, yanzu dan goge kici (kitchen) din shi abbaki iya isuwa mini?"

"Ke walle ban iyawa, tai dai ki isuwa, yanzu ki na gamawa mu tai gida,wancan dan mutuwar zuciyan da yaran shi na can na jiran mu samo mu kai musu su lasa, bada aniya ki isuwa (kammala,gamawa) mu ta tahiya gida"

Ba bu bata lokaci kuwa Me Buruji ta kammala aikin ta, suka yi wa sauran ma'aikatan sallama, dauke da ledojin da suka cika da abincin da aka ci aka rage, sai masu aiki su tattara su raba a tsakanin su, saboda yawan abincin da kuma kala kalan wanda ake dafawa, shi ya sa yake isar masu aikin, watarana ko sun dafa nasu, na masu aiki, se dai su tafi da shi, gidajen su.

Sai da suka tsaya a gate aka duba kayan su, sannan suka fita.

Dan sahu suka tsayar suka dauki hanyar unguwar su da ke a TUDUN FAILA.

A qofar gida suka tadda mijin su, zaune da abokan shi, suna manne da gini, sanye da wasu jemammun tufafi, mijin su na hango su ya washe baki, ya dago daga jikin katangar ya na lashe busassun labban shi.

Lamishi ce ta saki guntun tsaki ta ce,

"Kalli mijin ki,mai matacciyar zuciya, sai wani lashe baki shi kai awaw-wani baqin maye, sun bi sun wani maqale ga gina awwad-dangin qadangaru....kaiii Allah shi wadaran wanga mutuwar zucciya walle"

"Ameen ke dai"

Ko gaishe da abokan mijin nasu ba su yi ba suka fada gidan, su na jin su na gaishe su, tare da yi masu sanu amma ko kallo ba su ishe su ba, bata rai Dan Talo ya yi, ya tattare qasan rigar shi ya afka cikin gidan nasu ya na fadin.

"Ina zuwa na iskamma wadan can lalatatun, ba dan na amince ba ko titin gidan Gwauna ba ku bi wallah, dan tsabar raini, abukkai na za ku walaqantawa haka? To ba wata sheeee....."

Maganar shi ce ta maqale, ganin wata sharbebiyar kaza na maiqo, Lamishi na aje wa a farantin silver.

Kallon shi suka yi a tare cikin daure fuska, Lamishi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download A GARINMU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album