Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN


HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16086



HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN

Reading Time: 1 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Prof Ibrahim Malumfashi ,Danladi Z Haruna ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 85.37 kb

File Type: txt

Views: 619+

Download: 229+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
01. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN'UWANSA
SHAMSUDDIN.

Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan
Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan
abubuwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga
Manzonsa, Annabi Muhammadu (S.A.W).

Ka sani, ya Sarkin Musulmi, a kasar Misira an yi
wani Sarki, ma'abucin adalci da kyautatawa. Yana
da Waziri mai hankali, mai rarrabe abubuwa da
dabaru, mai tarin ilimi da fasaha, sai dai ya
kasance tsoho ne, shekaru sun yawaita a kansa.
Wazirin nan yana da 'ya'ya biyu maza, kai ka ce
'yan tawaye ne. Ga su kyawawan gaske, babu
kamar su a duk fadin kasar. Sunan babban
Shamsuddin, sunan karamin kuwa Nuruddin.

Karamin, watau Nuruddin, ya zarce wansa ga
kyawo da cikkar halitta. Ya kasance a cikin wancan
zamanin babu tamkarsa ga kyawo. Labarin
kyawonsa ya watsu cikin manyan birane da
kauyuka. Mutane da dama sukan tafi tun daga
garinsu har zuwa Misira, domin ganin kyawo irin
na Nuruddin.
Kwanci tashi, ran nan sai Wazirin Misira ya kwanta
ya mutu. Sarki ya yi matukar bakin ciki a kan
mutuwar Wazirinsa. Sarki ya rungumi 'ya'yan
Waziri a jikinsa, ya ce, "Ku ne a matsayin ubanku a
wurina." Yara suka yi farin ciki. Aka yi zaman
makokin mahaifinsu aka gama.
Shamsuddin da kanensa Nuruddin suka zama su
ne a matsayin Waziri ga Sarkin Misira. Idan
wannan ya hau karagar mulki, bayan sati guda sai
ya sauka dan'uwansa ya hau. Sukan yi canji duk
ranar Jumu'a, idan kuma Sarki zai yi tafiya, sai ya
tafi da daya, ya bar daya yana mulkin gari.
Wata rana daga cikin ranaku, Sarki ya yi niyyar
tafiya wata kasa, aka yi gamo da katar, hukunci ya
fada za a tafi da babban ne, watau Shamsuddin.
Daren da za su tafi, Shamsuddin ya kira dan
uwansa suka zauna suna hira. A cikin hirar tasu
Shamsuddin ya ce da dan'uwansa, "Na yi nufin
idan Allah ya maido mu gida lafiya daga tafiyar da
za mu yi gobe da Sarki, mu yi aure lokaci guda, a
cikin rana guda."
Nuruddin ya ce, "Kai ne babba, kuma kai ne a
matsayin ubana a halin yanzu. Ka aikata duk
yadda ka so, za ka same ni mai biyayya a gare
ka."
Shamsuddin ya ce, "Insha Allahu da zarar na dawo,

zan nema mana 'yan mata biyu, mu aure su rana
daya, mu shiga dakinsu dare daya, su sami ciki
lokaci daya, su haihu rana daya. Matarka ta haifi
da namiji, matata ta haifi 'ya mace. Su tashi tare,
su yi wasa tare, idan suka isa aure mu aurar da su
ga junansu, su zama 'yan bappanni."
Nuruddin ya ce, "Allah ya sa haka. To amma idan
haka ta tabbata, me za ka karba gun dana a
matsayin sadakin 'yarka?"
Shamsuddin ya ce, "A matsayin sadakin 'yata, zan
karba gun danka, dinari dubu uku, da gona talatin,
da gidaje uku."

Yayin da Nuruddin ya ji haka sai ya ce, "Haba!
Wane irin sadaki ne mai tsanani za ka dora wa
dana haka, ko ka manta cewa mu 'yan'uwan juna
ne, kuma Wazirai muke, matsayinmu daya. Ya
zamanto wajibinka ne ka aurar da 'yarka ga dana
kyauta, ba tare da karbar ko dirhami daga gare shi
ba. Ko ba ka san namiji ya fi mace daraja ba?"
Shamsuddin ya harzuka da wannan zance na
kanensa, ya ce, "Babu shakka kai ba ka da hankali,
tun da ka ambata tarayyar Wazirtaka tare da ni,
kuma kana nufin danka ya fi 'yata daraja ne? Ni fa
na roki Sarki ya sa ka Waziri tare da ni saboda
tausayinka da nake ji, shi ne yanzu har kake hada
kanka da ni. Tun da har ka fadi haka, to Wallahi ba
ni aurar da 'yata ga danka, ko da zai biya zinariyar
da ta kai nauyin 'yar tawa a matsayin sadaki."

Yayin da Nuruddin ya ji zancen dan'uwansa, ya yi
fushi, ya ce, "Ni ma dana ba zai auri 'yarka ba, ko
da babu sauran mata a duniya sai ita kadai."
Shamsuddin ya ce, "Ni ma ban yarda 'yata ta auri
danka ba, ko da babu sauran maza a duniya sai
shi kadai. Amma yanzu na yi nufin tafiya, waccan
niyyar ta aurenmu lokaci daya na fasa yin ta, Allah
ya aikata yadda ya so."

A cikin wannan dare, Nuruddin da Shamsuddin ba
su kwana wuri daya ba kamar yadda suka saba,

kowa ya kwana daki dabam saboda bacin rai. Da
gari ya waye, Shamsuddin ya shirya domin tafiya
da Sarki, ya nemi dan'uwansa domin su yi sallama
amma bai gan shi ba. Don haka sai ya bi Sarki
suka tafi.

Ashe kuma tun da asuba Nuruddin ya riga
Shamsuddin tashi daga barci, ya shiga taska, ya
dauki jaka karama ya cika ta da dinari. Ya tuna
maganganun da dan'uwansa ya yi masa a daren
jiya, da kuma gorin Wazirantaka da ya yi masa. Ya
tuna wakar wani mawaki, in da yake cewa:
"Ka yi tafiya cikin duniya, za ka sami musayar abin
da ka rasa.

Ka kafu da kafafunka, farin ciki na ga wanda ya
dogara da kansa.
Ni na ga tsayuwar ruwa wuri daya tana gurbata
shi, ruwan da yake gudu shi yake tsarkaka.
Ba don farin wata yana fakuwa ba, da ba a dube
shi ba ranar tsayuwarsa.
Ba don zaki yakan rabu da surkuki ba, da bai sami
abin farauta ba.
Ba don kibiya takan rabu da baka ba, da ba ta
zama abin tsoro ba.
Komai kyawon sanda, idan tana jikin icce ba a
ganin kyawonta.
Zinariya tamkar kasa take, ba a ganin kyawonta sai
ta rabu da kasa.
Wanda ya zauna gida, ba ya daukaka har duniya ta
san da shi."

Bayan ya dauki abin da yake so ya dauka daga
cikin taska, ya umurci wani bawansa ya daura
masa sirdi ga wani farin dokinsa mai kiba, mai
gaggawar tafiya. Bawa ya daura wa doki sirdi da
likkafu kirar kasar Hindu. Ya shimfida shimfidar
Asbihaniya a kan sirdin. Bawa dai ya shirya doki da
kayan kawa masu tsadar gaske wadanda sai
sarakuna da attajirai ke yin amfani da su.
Da Nuruddin zai fita, ya ce wa bawan nan nasa,
"Ina so in fita zuwa bayan gari, zan tafi unguwar
Kalyubati in kwana uku. Kada kowa ya bi bayana,
ina da bacin rai tattare da ni, idan na sami nutsuwa
zan dawo."

Yayin nan ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike
wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita daga
Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba. Burinsa
kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma dan'uwansa
Shamsuddin, ya shiga duniya, duniya ta gan shi,
shi ma ya ga duniya.
***

Wannan shi ne farkon labarin mai cike da tu'ajibi
da mamaki da ban tausayi. Za mu ci gaba gobe daidai wannan lokaci (karfe 8 - 9
PM), Insha Allah.

A jibaga√002. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Nuruddin ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike
wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita
daga Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba.
Burinsa kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma
dan'uwansa Shamsuddin, ya shiga duniya,
duniya ta gan shi, shi ma ya ga duniya.
Ya fita daga Misira ya shiga daji, Azuhur ba ta yi
masa ba sai da ya shiga birnin Bilbis. Ya sauka
ya huta, dokinsa ma ya huta. Bayan ya ci abinci
ya kuma ciyar da dokinsa, ya sayi duk wani abu
da ya san zai bukata a kan hanya. Ya hau
dokinsa ya fita daga wannan birni ya kutsa kai
cikin daji.

Bayan tafiyar dare daya da yini, ya isa birnin
Kudus. Ya sauka ya huta, dokinsa ma ya huta ya
ci abinci ya ciyar da dokinsa. Ya yi shimfida ya
kwanta domin ya rama baccin da bai yi ba,
zuciyarsa na cike da fushin dan uwansa har
bacci ya dauke shi. Ya kwana a wannan wuri. Da
gari ya waye ya kama dokinsa ya hau ya ci gaba
da tafiya har ya isa birnin Halbi.
A birnin Halbi ya sauka a gidan baki, ya huta
sosai, ya sha iska tsawon kwana uku, bakin
cikinsa ya fara yayewa. Daga nan ya hau
dokinsa ya ci gaba da tafiya, ba tare da ya san
inda za shi ba. Bai gushe ba yana tafiya har ya
iso birnin Basara cikin dare, ba tare da ya san ko
wane gari ne ba. Ya nemi gidan baki ya kwana.
Da gari ya waye Nuruddin ya ce da mai kula da
kofar gidan baki yana so ya tafi da dokinsa rafi
ya yi masa wanka ya shafe shi da mai. Mai kula
da kofa ya kama ragamar doki ya ja ya nufi rafi,
aka yi gamo da katar hanya ta bi da shi ta gaban
gidan Wazirin Basara, yana kuwa zaune a cikin
soronsa.
Da Wazirin Basara ya kyalla ido ya ga dokin
Nuruddin da irin kayan kwalliyar da aka kawata
dokin da su, sai ya ce a cikin ransa, lalle wancan
dokin na wani babban Sarki ne ko Waziri, ko
kuma na wani babban attajiri ne. Ya dubi wani
yaronsa ya ce, ka zo mini da dokin can tare da
wanda ke jaye da shi.
Yaro ya tafi nan take ya zo da mai kula da kofar
gidan baki tare da doki. Da suka zo mai kula da
kofa ya durkusa ya yi gaisuwa ga Waziri. Wazirin
Basara ya kasance tsoho ne sosai, shekaru sun
yawaita a kansa. Ya ce da mai kula da kofa,
wane ne mai wannan doki?

Mai kula da kofa ya ce, "Ya shugabana, mai
wannan doki saurayi ne karami, mai karancin
shekaru, mai kyakkyawan hali na daga 'ya'yan
tajirai, yana da kwarjini da nutsuwa. Jiya ya
sauka a gidan baki, amma na yaba da
kyawawan halayensa, ya shugabana."
Yayin da Waziri ya ji wannan zance ya tashi
tsaye a kan duga-dugansa, ya ce da mai kula da
kofa, "Kai ni inda yake in gan shi." Waziri ya hau
dokinsa suka tafi zuwa ga gidan baki.

Da suka isa gidan baki, suka zarce dakin
Nuruddin, suka yi masa sallama, Nuruddin ya
leko da kansa waje, Waziri ya ga Nuruddin. Da
Nuruddin ya ga Waziri, duk da bai san ko
wanene shi ba, ya fito daga cikin dakin, ya
durkusa a gabansa, ya gaishe shi da lafazi mai
dadi cikin ladabi da biyayya.

Waziri ya sauko daga kan dokinsa, ya rungumi
Nuruddin, ya ce da shi, "Ya dana, daga wane
birni ka zo wannan birni namu? Kuma ina kake
nufin tafiya daga nan?"

Nuruddin ya ce, "Ya shugabana, na fito ne daga
birnin Misira, mahaifina shi ne Wazirin Misira
amma Allah ya yi masa rasuwa."
Nuruddin ya
labarta wa Waziri duk abin da ya gudana
tsakaninsa da dan uwansa Shamsuddin, da
yadda ya yi masa gorin wazirtaka, har ya yi fushi
ya baro garinsu, har Allah ya kawo shi wannan
birni.

Waziri ya ce da Nuruddin, "Yanzu mene ne
burinka a rayuwa?" Nuruddin ya ce, "Buri na
yanzu shi ne in ci gaba da zagaya duniya, ba
zan koma gida ba har sai na ga manya-manyan
birane da garuruka na duniya gaba dayansu."

Yayin da Waziri ya ji haka ya yi murmushi, ya ce
da Nuruddin, "Ya dana, kada ka biye wa bacin
zuciya ta jefa ka ga halaka, sai ka mutu ba ka ko
ji labarin wani birni na duniya ba, ballantana ka
gan shi. Ina rokon ka, ka tashi daga wannan
gidan baki, ka koma gidana da zama."
Nuruddin ya amince da bukatar Waziri, ya hau
dokinsa ya bi shi har suka isa gidan. Waziri ya
sa aka kawo wa Nuruddin abinci da abin sha
masu daraja. Da Waziri ya ga hankalin Nuruddin
ya fara kwanciya, sai ya ce da shi, "Ya dana ka
ga ni tsoho ne mai yawan shekaru, Allah bai
arzuta ni da da namiji ba sai mace, ita kenan na
haifa. 'Yar nan tawa kuwa idan ba ta zarta ka a
kyau ba, to kuwa za ku zo daidai da ita, kuma
ga shi sa'o'in juna kuke. 'Ya'yan sarakuna da
'ya'yan attajirai sun nemi aurenta amma duk na
hana su, domin duk cikinsu ban ga wanda
hankalinsa da halayensa suka dace da 'yata ba.

Tun lokacin da na dora ido a kanka, na san
cewa duk duniya babu wanda ya dace da ya auri
'yata sai kai. Shin ko za ka amince da wannan
tayin na auren wannan 'ya tawa?"
Yayin da Nuruddin ya ji wannan zance na
Wazirin Basara, ya sunkuyar da kansa cikin jin
kunya ya ce, "Na ji na kuma amince da wannan
babbar kyauta taka."
Waziri ya yi farin ciki da haka ya ce, "Tunda na
sami suruki, ni zan yi murabus daga karagar
mulki, a nada ka a matsayin Wazirin Basara, ni
kuwa in koma gefe in ci gaba da bautar Ubangiji
a cikin 'yan sauran kwanakin da suka rage mini
a duniya. Gobe za mu je in gabatar da kai a
gaban Sarki."

Waziri ya tara abokansa, ya yi kiran manyan
attajirai da alkalai na birnin Basara ya ce da su,
"Ku sani cewa ina da dan uwa a birnin Misira
wanda ya kasance shi ma Waziri ne a can.

Wannan dan uwa nawa yana da 'ya'ya biyu
maza, ni kuwa Allah ya arzutta ni da 'ya daya,
kamar yadda kuka sani. Kafin dan uwana ya
rasu ya yi mini wasicci da in aura wa daya daga
cikin 'ya'yansa 'yata, ni kuwa na amsa masa da
haka. Yanzu da na ga ta isa aure, na aika Misira
wannan dan dan uwan nawa ya zo domin cika
alkawarin da na daukar wa dan uwana. Ina so in
rubuta takarda a kan aurensu, ku kuma ku zama
shaida." Mutane suka ce, madalla da wannan
karimci da cika alkawari naka ya Waziri. Yayin
nan jama'suka sha madara da zuma, aka
yayyafa musu wardi, suka watse suna sa wa
Waziri albarka.

Waziri ya sa aka gyara wa Nuruddin wani daki
nan cikin gidan, aka zuba masa kayan kawa da
na ado masu kyau da tsadar gaske, sannan ya
sa aka fara gyaran wani gida daban wanda
Nuruddin zai zauna idan an daura musu aure da
matarsa 'yar Waziri.

Al'amarin Shamsuddin kuwa....

gobe zàmuci gaba Insha allahu

ayi hakuri kwana biyu anjini shuru hakan yafarune. sakßmakon. tàfiya danayi amma yanzu nadawo komai yayi dàidai03. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Waziri ya sa aka gyara wa Nuruddin wani daki
nan cikin gidansa, aka zuba masa kayan kawa
da na ado masu kyau da tsadar gaske, sannan
ya sa aka fara gyaran wani gida daban, wanda
Nuruddin zai zauna idan an daura musu aure da
matarsa 'yar Waziri.
Kashe gari, Wazirin Basara ya riki Nurddin ya tafi
da shi gaban Sarkin Basara. Da suka isa, suka
fadi suka yi gaisuwa gun Sarki. Nuruddin ya
kasance mai fasahar magana, mai natsattsiyar
zuciya da kyan hali, sai ya rera wa Sarki
wadannan baitoci:

"Wannan shi ne Sarkin da ya game jama'arsa da
adalci,
Idan ya yi fushi yakan kori rundunar mayaka
dukkanta,

Ba ya so a yabe shi domin aikinsa gun talaka,
Ya sani aikinsa gun talaka hakkinsa ne a gare
shi,
Ku zo mu sumbanci yatsunsa, domin mabudan
arzukka ne."

Sarki ya yi mamaki a kan fasaha da iya kalamai
na Nuruddin, ya dubi Waziri ya ce, "Wannan
wane saurayi ne, daga ina ya zo wannan birni
namu?" Waziri ya ce, "Wannan yaro dan dan
uwana ne." Sarki ya ce, "Ashe kana da dan uwa
wanda ba mu san da labarinsa ba?"

Waziri ya ce, "Ya shugabammu, dan uwa ya
kasance a gare ni, shi ne Wazirin Misira, ya mutu
ya bar 'ya'ya biyu. Babban dansa ya gadi
matsayin ubansa na Wazirin Misira, shi kuma
wannan karamin ya zo gare ni. Kafin dan uwana
ya mutu, ya yi mini wasici da in karfafa
zumuncinmu ta hanyar aurar da 'yata ga daya
daga cikin 'ya'yansa, na kuma yi masa
alkawarin yin haka. Yanzu da na ga 'yata ta isa
aure, na aika ga wannan yaro ya zo wurina
domin cika wannan alkawari da na yi wa dan
uwana, ya Sarki. Ni ina nufin aurar da 'yata ga
wannan saurayi, ina kuma rokon Sarki ya nada
shi a matsayina, yaro ne mai hankali da dabara
wanda ya gaji sarautar Wazirtaka. A halin yanzu
tsufa ya zo mini, karfina ya kare, ina so in koma
gefe guda in huta kafin zuwan ajalina."

Sarki ya dubi Nuruddin, ya gan shi yaro ne
natattse mai hankali da kuma iya zance na
hikima. Kodayake dai a cikin ransa, Sarki bai
yarda da labarin Wazirinsa ba cewa Nuruddin
dan dan uwansa ne, domin ya san Waziri ba ya
da wani dan uwa a Misira, duk da...


Read / Download HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN
avatar
rabiu-bello

3 months ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album