Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

SHADE OF RUFAIDAH Complete Hausa Novel Document by SHADE OF RUFAIDAH


SHADE OF RUFAIDAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 298929



SHADE OF RUFAIDAH

Reading Time: 24 Hours

Added On: 27, Feb 2025

Author: Surayya HMS ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08060712446

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.58 mb

File Type: txt

Views: 75+

Download: 276+

Last download: 1 day ago

Description/Story: *™✓SHADE OF RUFAIDAH*


_BY_
_SURAYYAHMS_


_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.


_Dedicated to HRH Malama Hau'wa mu'az omar._


Part1:chapter 1
*Guns and roses*


*District mogue no 25 Ahmadlawal street:6:34am* .


Kuka yake sosai gurfane a gaban wani kabari wanda yanayin kukan nasa kadai zai iya tabbatar maka cewa haqiqa wannan mutumin yayi babban rashi,musamman ma yanda idanuwan sa suka kumbura sukayi wani irin jajur ta yanda duk wanda ya kalle sa bisa kallo daya to dole sai nashi idanun shima sun ciko da qwallah tsabar tausayi.

A nan gurfanen da yake,wani kyakkwar saurayi ne mai masifar kama dashi yazo shima idanun sa sunyi jajur tsabar kukan dayaci,a sanyaye yake tahowan har ya karaso daf dashi jikinshi yayi matuqar yin laqwas bai iya daurewa ba sai kan kukan shima yakeyi,hannu yasa ya Dan dafa shi ya kuma rungume shi sosai a jikin sa ayayin da suka buda suka rungume junan su cikin wata iriyar kasalallen shauki da rauni mai tafe da ciwo da azabtarwa,babu abunda suke zubarwa junan su face hawaye masu saukowa da turirin numfashn su mai zafi da ciwon rashi.

Na tsayen da kyar ya soma iya bude muryan sa,rarrashin na tsugunen ya shiga yi yana bashi kalamai masu taushi da sanyi acikin kunnen sa wai koda zaiji sanyi aransa amma sam shima ya kasa daina kukan har sai da yaja shi da qarfi kawai suka fita daga maqabartar.._.


*Baya Kafin faruwar hakan*.


Da Yamma ne lis gari yay sanyi yara suncike kan tituna da hayaniya da alamun lokacine na sakosu daga babban islamiyar dake anguwarsu ta bayan gari dake garin kano,wasu Yan mata uku na hango suna tafe bisa tsarin takawa juna hanyar komawa gida,duk jikin su a killace yake acikin dogayen dark green hijab dake shine kalar uniform din islamiyan sun, kalar bakaramin yi musu balain kyau tayi ba saboda yadda ta amshe hasken doguwar fuskarsu da tsarin su na yan mata masu fallin tasowa,a shekaru dai dukan su bazasu wuce shekara goma sha bakwai ba,dogaye ne kyawawa kuma kawayene na tun asali tun suna yan kanana,gaban su gadi suke takawar su cikin nitsuwa dan inda sabo yanzu sun saba da yanayin yadda idanun kowa ke satan kallon su daga nan ma zaka san sudin nadaban ne acikin yan matan dake yawo a cikin makarantar.

Sunayen su Amal da batul sai na ukun sun ita akecewa RUFAIDA wanda ita kawai tafiye killace fuskarta acikin niqabi kuma dama tafiyin tafiyarta a gefe gefe musamman ata gefen dama..

Yau ma Tafiya suke suna yar hirarsu akan jaruman maza wayanda zasu dace da su da kuma irin auren zamani da akeyi yanzu wanda suke so suma ayi musu,Kaf anguwar su har yau ba ataba yin auren kece raini irin auren manyan yayun rufaidar ba,ga na dayan dadantan wato Adda suhan shima ya gabato wanda ake cikin shirinyin sa a yanzu...


Ita dai rufaida za'a iya bayyanata acikin irin siffar matan nan masu kamala da mugun son boye kyaun fuskar su acikin hiqabi,she is very reserve duk dama ba sanyayya bace,sai dai ita maganan ta baya kamawa sai a inda ya dace da kuma wanda ya dace.

..rufaida tana da kyakkwar fuskar shagwaba wanda kota boyeshi baya fiye boyuwa,she is soo smart nd very romantic at heart,rufaida tana da burin tayi rayuwar ta mai kyau mai tsari..mai aji..kuma na wayayyun mata.

Saidai yanayin yadda ta taso shiya boye duk wani alama da zai bayyana maka hakan atattare da ita,duba da ita yar malami ne,malamin ma qarza, mai bala'in mugun son abun duniya,shiyasa a duk hirar dasu Amal sukeyi ita sam bata fiye saka musu baki aciki ba,dan har yau a Zuciyarta batajin sha'awa ko kwadayin yin auren gaggawa kamar yadda taga ko wace budurwa na burinyi bayan gama secndry schl dinta ,awajen ta auren gaggawar is a never an option for her,sabida tana da mugun burin nemar ilimi domin ta gabatar da rayuwar ta cikin inganci da nagarta,kawayen ta har sun gaji da jin ra'ayin nan nata sun kyaleta Shiyasa koda sun fara hirar samarukan su ita batace musu cikan ku,bata ma iya kula namiji arayuwarta musamman ma dake asalinta ita ba a far far bane.

Kamar yadda suka saba kullum adaidai hanyar da yabi kwanan lungunan gidajen su sukeyin sallama da juna bayan sun rabu sai kowacce ta nufi cikin gidar iyayen ta.

Shigar rufaida gidan su ke da wuya ta tarar da tsakar gidansun a kacame da zalamamun mata kwadayyu anata rabza uwar surutu har ba ajin kunne,atake saita tuno da cewa ashe tun jiya aka kawo lefen dadarta suhan wanda ake ribibin shirin bikinta a satin nan,kaf taron matan anguwar ne a gidan su wai anzo ganin lefen mace mai goshi,g'uda kawai akeyi ana shewa wanda hakan yake kara sa gaban rufaida fadi...

Kanta ta sauke kasa cikin sauri sanin bamai yin lokacin kula gaisuwar ta,tafiya ta shigayi cikin saibi da sanyin jiki tanajin yadda kananan zunde da gulma kala kala yake tashi ako wani tsirkon taron mata dake tsakar gidan sun,tabbas mafi yawan matan dake zuwa shagalgulan biki agidan su ba dan Allah suke zuwa ba sai dan gulma munafurci da nuna hassadar su a fili,kaf anguwa an ririta cewa yayan yaa MALAM wanke hannun kataba ne shiyasa saiwa masu kudi kawai yake bawa auren su bai taba ba marar karfi ba,but she just hates when ppl wll talk abt her parents dat way.

Kullum gulman mutane bai wuce yadda mahaifinsu yaa malam yake ruwa da tsaki wajen neman masu hannu da shuni ba, da yadda yake saka tsantsan jahilci da rashin bincike da azababben nuna kwadayin kudi aryuwar sa wanda har ya mayar da hakan kamar wani future ambition dinsa na tafiyar da sha'anin rayuwar sa akan auren yayan sa mata.


A hankli ta saka hannunta ta bude kofar dakinta so slow tamkar wacce bata son asanda shigowarta gidan,a nitse ta shige ciki bakinta yana mai dauke da Salam duk dama bataga alaman wani halitta a ciki ba,kallon scnd biyu kacal ta bi koina dashi tana mai wara kyawawan fararen idanunta Wani ajiyar xuciya ta sauke na samun relieve dan yadda ta fita ta bar dakin a kimtse hka ta zo ta same shi dauke kanta tayi sannan ta sake jakar islmiyarta dake rataye a kafadarta ta nemi waje ta zauna a bakin katifarsu ta zabga uban tagumi,Wani uban shiru ne ya gifta har na dan wani lokaci ayayin da takejin sautin kirjinta da kanta na kara tsananta bugunsa wanda batasan dalili ko aufin sa ba..,tun sanda aka fara maganan aurar da Adda suhan takejin kamar hanklin ta na balain tashi tunanin ta gaba daya sai yake gushewa hakama duk sanda ta dosu kofar gidan su taji hayaniyar mata sai taji kirjinta da zuciyanta na bugawa da karfi sosai har tamkar wanda zai fado waje.

Ta dade ahaka tana meison sanin dalilin dayake jefata cikin wannan bakon yanayi,ganin kamar hakan bazai samu ba ta miqe tsaye ta zaga bayan gida tayi tsarki tayi alwalan sallan magrib sannan ta dawo ciki ta shimfida sallaya ta hau gabatar da sallah magriban ta a tsanake, Bayan ta sallame waje ta nema ta zauna akan sallayar tana yan aduoi.

Daga tsakar gidan su kuwa A hankli sautin muryoyin mata ke dishewa da alama kowacce mace tana shirin kama gabanta sai kuma gobe in anzo a dora daga inda aka tsaya....

Koba dan haka bama Yaa malam bai kaunar ya shigo gidansa bayan sallar ishai ya tarda wani baqo ko taron matan makwabta Dake ma ansan al'adarsa ne kowani dare saiya zauna yin karatu wa almajiran sa kuma yadan musu jawabi game da qur'ani wanda yake yinshi da tsantsar harshensa na warash,a fadar sa ta tsakar gidan sa yake koyarwa inda kowani almajiri zaina bitar karatun sa amma fa duk iyawarka bazaka taba kama kafar yaa malam ba dan shi gadon karatun yayi ba tsantsar iyawa yay ba.

..hakan ya dade dasa shi jin wani irin girman kai da son nuna isa,ganin kansa yake a matsayin babban malamin addini da Allah ya riga ya daukaka bayan ilimin nashi baikai har nan ba

Kaf anguwar gidansa ne kawai akwai dokan shige da fice matar sa umma hadiza Tace gadon hakan yayi a wajen mahaifinsa shiyasa duk rintsi duk tsiya baqo baya wuce sallan magrib a cikin gidansa.

Har yanzu zaune take akan sallayar tana kammala idar da addointa bata miqe tabar wajen ba, shiru tayi kanta na cigaba da kallon qasa,Wani tunani ne ya bijiro mata wanda bata tsaya kula shi ba tasa hannu ta jawo jakar islmiyarta ta dauki qur'anin ta ta budeshi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download SHADE OF RUFAIDAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album