Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI


HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15833



HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Danladi Z Haruna ,Bukar Mada ,Prof Ibrahim Malumfashi ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 83.05 kb

File Type: txt

Views: 1366+

Download: 340+

Last download: 22 hours ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01 HIK’AYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB
KARIMUDDINI
A zamani mai tsawo da ya shud’e, an yi wani
malami mai hukunci daga cikin mahukuntan
Yunana ana kiransa Daniyala. Ya kasance a
k’ark’ashinsa akwai d’alibai da mabiya
wad’anda ke masa biyayya ga umarninsa
suna hanuwa da haninsa, sun dogara gaba
d’aya a kan ilminsa da fatawarsa. To amma
duk da d’imbi ilmin wannan malami ya
kasance bai tab’a haihuwa ba. A wani dare
ya kwanta yana tunanin halin da yake ciki na
rashin magaji, hankalinsa ya tashi ya rasa
inda zai sa kan sa. Sai ya tuna Ubangiji
mad’aukakin Sarki yana amsa addu’ar
bayinsa ba tare da shamaki ba. Yana azurta
wanda ya so a lokacin da ya so da abin da
ya so. Ba ya maida wanda ya koma gare shi
mawofinci ga biyan buk’ata. Yana alheri ga
mai biyayya gare shi, yana yin baiwa ga
wanda ya so.
Ya mik’e tsaye ya yi sallah sannan ya yi
addu’a. Bayan ya shafa ya kama hannun
matarsa ya sadu da ita, a wannan daren
kuwa ta samu ciki.
A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse
zancenta mai dad'in saurare.
DARE NA 483
A dare na d'ari hud’u da tamanin da uku,
Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai
wannan hamshak’in Sarki, malamin nan ya
sadu da matarsa, a wannan daren ta samu
ciki. Bayan wasu kwanaki sai tafiya ta kama
shi cikin jirgin ruwa. A tsakiyar ruwa jirgin ya
wargaje dukkan littattafansa suka dulmuye
cikinsa, ya tsira da kyar ta hanyar kama wani
allon jirgin. Ya zamana babu abin da ya
saura gare shi na daga littattafai sai ‘yan
takardu guda biyar. Yayin da ya dawo gida
sai ya zuba takardun a cikin wani akwati ya
kulle ya dank’a wa matarsa mukullan wadda
cikinta ya soma girma ya ce da ita, “ki sani
mutuwata ta kusa domin ciwon da ke jikina
yana yawaita. Na kusata da barin wannan
rayuwar zuwa gidan tabbata. Watak’ila ki
haifi namiji daga cikin nan naki. Idan kin haife
shi ki rad’a masa suna Hasib Karimuddini, ki
raine shi da mafi kyawun raino. Idan yaron ya
girma ya tambaye ki gadon da mahaifinsa ya
bar masa ki nuna masa wad’annan takardu
guda biyar. Idan ya karanta zai fahimci abin
da suka k’unsa zai zama babban malamin
zamaninsa.”
Daga nan ya yi mata bankwana ya ja dogon
numfashi ransa ya fita. Allah ya jik’ansa.
Iyalinsa da danginsa da dukkan mutanensa
suka yi ta kuka sannan suka yi masa wanka
suka shigar da gawar cikin likkafani sannan
suka yi masa sallah suka bisne shi.
Bayan sun yi addu’oi kamar yadda aka saba
sai kowa ya tafi ya zuwa sha’anin gabansa.
Bayan kwanaki kad’an da mutuwarsa sai
matarsa ta haifi wani yaro namiji kyakkyawa
aka rad’a masa suna Hasib Karimuddini
kamar yadda mahaifinsa ya ba da wasiyya.
Bayan suna suka kirawo malamai masana
ilmin taurari domin su duba game da
sha’anin wannan yaro. Da suka k’are
bincikensu sai suka ce da ita, “ki sani ya
wannan matar, cewa d’anki zai yi rayu
shekaru masu yawa amma wani al’amari zai
faru gare shi a farkon rayuwarsa, zai sha
wahala kuma zai ga abin mamaki. Amma
idan ya kub’uta daga nan zai zama mai
yawan ilmi na daga sha’anin duniya da na
lahira.” Ta ci gaba da shayar da shi har ya
shekara biyu sannan ta yaye shi. Yayin da ya
shekara biyar ta shigar da shi makaranta ya
soma koyon karatu da rubutu, amma sai ya
kasance bai iya karatun komai ba, kuma bai
koyi rubutu ba. Da ta ga haka sai ta cire shi
daga makarantar ta kai shi wajen koyon
sana’a, nan ma ya kasa koyon komai na
daga aikin hannu. Uwar sai ta shiga halin
damuwa da bak’in ciki, mutane suka ce da
ita, “ki yi masa aure, watak’ila zai natsu ya
aikata abin da ake so da shi na daga
sana’a.” Ta tafi ta nemo masa auren wata
yarinya a nan unguwarsu. Duk da an yi masa
auren amma bai mai da hankali ga aikin
komai ba, ga shi ya soma datawa domin ya
kai shekara goma sha tara bai iya komai ba
na daga karatu ko aiki. Uwar ce ke
d’awainiyar ciyar da shi tare da matarsa.
Wata rana wasu mak’wabtanta masu saro
itace suka ce da ita, “ki sayo wa d’anki jaki
da igiya da gatari ki had’a shi da mu mu rik’a
zuwa daji muna saro itacen wuta muna
sayarwa. Duk abin da muka samu sai mu
rik’a rabawa tsakaninmu. Kin ga sai ku samu
abin da za ku rik’a taimakon kanku.” Da ta ji
haka sai ta cika da farin ciki ta gode musu
sannan ta tafi ta sayo jaki da igiya da gatari
ta had’a Hasib da su bisa amanar su kula da
shi a dukkan inda suka shiga. Suka ce, “kada
ki damu, Allah zai kiyaye shi da mu baki
d’aya. Ko ba komai ai d’an malaminmu ne
dole mu kula da shi.” Suka tafi da shi cikin
daji bisa duwatsu inda itatuwa suka fi girma,
suka sari daidai yadda za su iya, suka lafta
wa jakunansu zuwa cikin gari suka sayar
suka yi wa iyalinsu sayayyar kayan abinci.
Washegari ma suka fita, a rana ta uku ma
suka. Haka suka ta yi kullum suna zuwa
suna sayarwa har wata rana bayan sun shiga
dajin sai gari ya murtuke bak’ik’k’irin hadari
ya gangamo ana cida da walk’iya da iska mai
cike da k’ura. Bayan wani lokaci ruwa suka
sauko mai k’arfi da guguwa. Nan da nan
suka ruga wani kogo suka fake kafin ruwan
ya k’are sauka. Hasib sai ya matsa daga
ragowar abokan tafiya ya matsa can k’urya
da gatarinsa yana bubbuga shi a k’asa. Sai
ya ji k’asan yana amsawa kamar ana buga
ganga, tamkar k’asan wajen akwai wani abu
a ciki. Bai jima da fahimtar haka ba sai ya ji
gatarinsa ya b’urma wajen. Ya sa hannu ya
kwashe k’asar sai ya ga wani dutse ya
d’auke shi sai ga wata k’ofa kamar an danne
ta da wani zagayayyen bak’in k’arfe. Da ya
ga haka sai ya cika da farin ciki, ya kirawo
abokan aikinsa ya nuna musu.

Zamuci gaba gobe insha Allah02 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

Yayin da Hasib ya d’auke
dutsen sai ga wata k’ofa kamar an danne ta da
wani zagayayyen bak’in k’arfe. Da ya ga haka
sai ya cika da farin ciki, ya kirawo abokan
aikinsa ya nuna musu, suka cire bak’in k’arfen
sai suka ga wani d’an kururrumin rami cike da
ruwan zuma. Da suka ga haka sai suka ce,
“wannan zumar tana da yawan gaske, babu
abin da ya fi sai mu koma cikin gari mu samo
salkuna da tukwane mu kwashe ta gaba d’aya
mu je mu sayar mu raba kud’in tsakaninmu.
Amma d’aya daga cikinmu ya tsaya kula da
wajen kada wasu su zo su kwashe mana alhali
ba ma nan.” Hasib ya ce, “ni zan zauna kula da
wurin har ku je ku dawo.” Suka tafi suka bar shi
yana kula da wajen, bayan wasu lokuta suka
dawo d’auke da salkuna da tukwane da
mazubai masu yawa. Suka yi ta cika su suna
laftawa jakunansu zuwa kasuwa. Washegari ma
suka dawo suka d’iba, suka sake dawowa a
karo na uku. Ba su gushe suna kai wa da
komowa ba kwanaki masu yawa har sai da ya
kasance sun kusan kwashe zumar nan, saura
kad’an. Duk wad’annan kwanaki Hasib ne ke
zama a wurin yana kula da shi dare da rana. A
cikin gari kuwa sai suka rik’a magana da
junansu suna cewa, “kun ga Hasib ne ya gano
wannan zumar kuma shi ne yake kula da ita har
ga shi yau za mu k’arasa kwashe ta zai dawo
cikin gari tare da mu. Zai yi mana k’orafin tasa
ce, mu kenan za mu tashi ba mu da komai ko
kuwa rabonsa ya ninka namu.” Sai wani daga
cikinsu ya ce, “idan kuwa haka ne babu
makawa mu shirya masa kaidi yadda za mu bar
shi a cikin ramin zumar. Yunwa da k’ishirwa ma
sa kashe shi daga baya. Kun ga mun magance
wannan matsalar kenan.” Suka amince da
wannan shawara, suka tafi daji a kan haka. Da
suka isa sai suka ce da shi, “shiga cikin rijiyar
ka d’ebo mana abin da ya saura a ciki na daga
zuma.” Ya shiga ya rik’a d’ebo musu zumar
suna tarawa har sai da komai na ciki ya k’are.
Ya ce musu, “ku fito da ni babu abin da ya rage
yanzu.” Ba su kula da shi ba suka lafta wa
jakunansu kaya suka tafi suka bar shi a ciki shi
kad’ai. Ya zama yana neman taimako yana
kuka babu wanda ya ji shi yana cewa, “lahaula
wala k’uwwata illa billahi. Yau na gamu da
wahala. Ya Allah ka fitar da ni!” Wannan kenan
game da al’amarinsa.
Amma game da abokan aikinsa kuwa, yayin da
suka isa cikin gari suka sayar da zumar nan
sannan suka tafi wajen mahaifiyar Hasib suna
kuka suka ce da ita, “kaiton d’anki Hasib!” Ta
ce, “me ya same shi?” Suka ce, “Allah ya yi
masa cikawa, ya mutu a daji!”
“Me ya kashe shi?”
“Muna cikin saran itace a can saman tsauni sai
iska ta taso ruwa mai k’arfi ya sauko muka
shiga wani kogo domin mu fake. To ana cikin
ruwan sai jakinsa ya kwance ya gudu cikin daji.
Ya tashi ya bi shi domin ya dawo da shi, a dajin
sai wani babban kerkeci ya taso ya buge shi ya
kashe shi nan take. Kuma ya kashe jakin ya
cinye shi.” Yayin da uwar ta ji zancen masu
itace sai ta rik’a marin fuskarta tana kuka da
jimami tana tula k’asa a kan ta. Ta tabbata
cikin bak’in cikin rashinsa. Masu itace suka
zama suna kawo mata abinci da abinsha da
sutura. Wannan kenan game da al’amarin uwar
Hasib.
Masu itace kuwa suka sayar da zumar nan
suka sayi rumfuna da jari suka zama attajirai
suna saye da sayarwa, suka zama cikin farin
ciki da nishad’i.
Hasib kuwa ya zauna a rijiyar nan yana ta kuka
gami da kiran neman taimako har ya gaji ya
daina. Ya zauna a ciki ya rasa abin da ke masa
dad'i. Can an jima sai wata kunama ta fad'o
masa, ya mik'e da hanzari ya kashe ta. Sannan
ya d'auke ta yana jujjuya ta yana mamaki, ya
ce, "rijiyar nan na cike da zuma a baya, ta ina
aka samu wannan kunamar?" Ya mik'e yana
duba jikin garun rijiyar hagu da dama, kudu da
arewa ya ga wani rami inda kunamar ta fito
haske na fitowa daga gare shi. Ya fito da wuk'a
da ke k'ugunsa ya rik'a rarake wurin har ya ga
tamkar taga, ya cusa kansa ciki sai ya gan shi
a wani sarari. Ya rik'a tafiya bai san inda ya
nufa har ya zo wata farfajiya mai girma, ya
shiga sai ya gan shi a wani babban zaure. Ya
tafi zuwa ga wata k'ofa ta bak'in k'arfe tana da
makulli na azurfa. Wannan mukullin ya kasance
a jikinta mak'ale yana haske da kwad'on
zinariya. Ya sa hannu ya bud'e ya shiga, ya yi
ta tafiya sa'a guda sannan ya sadu da wani
k'aramin tafki da aka gina domin ado. A nan ne
ya ga wani abu na haskakawa tamkar ruwa.
Bai gushe yana tafiya ba har ya sadu da wani
tudu mai girma na d'anyen zubarjadi da wani
dunk'ulen zinariya an masa tulluwa da kuma
wani babban gado na zinariya an shafe shi
daga dangin yak'utu da zubarjadi. da wani
dunk'ulen zinariya an masa tulluwa da kuma
wani babban gado na zinariya an shafe shi
daga dangin yak'utu da zubarjadi, a gewaye da
shi kujeru ne masu yawa, wasu na zinariya,
wasu na azurfa, wasu na yak'utu, wad'ansu na
d'anyen zubarjadi. Ya tsaya yana k'idaya su ya
ga guda goma dubu sha biyu ne, ya ga wata
babbar kujera a tsakiyarsu babu kowa, ya
zauna a kai. Ya zama cikin mamaki da
wad'annan gadaje da wannan tafkin da irin
adon da aka yi musu. Bai gushe ba bisa haka
har barci ya kwashe shi. Ya farka a firgice
sakamakon wata k'ara da huci da wani irin
motsi da ya ji na nufo shi, ya bud'e idanu ya
zauna ya ga dukkan kujerun nan wasu manya -
manyan macizai na zaune a kan su, girmansu
ya kai k'afa d'ari. Tsoro ya kama shi da ganin
wannan abin tsoro, yawun bakinsa ya bushe
don tsananin tsoro. Ya d'ebe tsammanin
rayuwa don tsoro, ya ga idon kowacce macijiya
jajawur kamar garwashin wuta. Ya duba
wannan k'aramin tafkin nan ya ga macizai
k'anana babu wanda ya san adadinsu sai Allah,
suna ta kai wa da komowa a ciki. Bayan jimawa
wata macijiya kamar alfadara ta gabato zuwa
gare shi, bisa bayan wannan macijiya akwai
wani faifan zinariya. A cikin wannan faifan
akwai wata 'yar k'aramar macijiya tana haske
kamar lu'ulu'u. Fuskarta irin ta mutane ce, tana
zance da fasaha da harshe mai dad'i.
Yayin da ta gabato wurin Hasib Karimuddini ta
yi masa sallama, ya mayar mata da sallamar.
Daga nan d'aya daga macizan nan ya sauko
daga kujerarsa ya kama faifan ya saukar da ita
zuwa wata kujera da ta fi ragowar kyau. Ta yi
kururuwa gaba d'aya macizan suka fad'i suna
masu gaisuwa da irin yarensu. Macijiya ta yi
musu alamar su zauna, suka koma suka zauna.
Ta juya ga Hasib ta ce, "kada ka ji tsoronmu ya
kai saurayi, ni ce sarauniyar macizai, kuma
jagorarsu." Da Hasib ya ji haka sai zuciyarsa ta
natsu ya zauna. Ta sa macizai su kawo masa
wani abu da zai ci. Suka kawo masa tuffa da
inibi da rumman da gyad'a da kuma ayaba
suka ajiye a gabansa. Sarauniyar macizai ta ce
da Hasib, "barka da zuwa ya saurayi, yaya
sunanka?" Ya ce, "sunana Hasib Karimuddini."
Ta ce, "ya Hasib zauna ka natsu ka ci
wad'annan 'ya'yan itatuwa, domin ba mu da
nama ko wani abu daban. Ci sosai kada ka ji
tsoronmu."
Da ya ji haka sai ya natsu sosai ya ci kayan
marmarin nan har ya tumbatsa ya gode wa
Allah. Daga nan aka d'auke farantan abincin
daga gabansa. Sarauniya ta ce masa, "Hasib
fad'a min yadda ka zo wurin nan da abin da ya
faru gare ka ya yi sanadin zuwanka."
Hasib ya gyara zama ya ba ta labarinsa tun
daga kan mahaifinsa da yadda ya rasu kamar
yadda mahaifiyarsa ta fad'a masa, da yadda
aka sa shi makaranta yana shekara biyar ya
zamana bai iya karatu da rubutun komai ba, da
yadda ta kai shi wurin koyon sana'a bai iya ba,
da yadda ta yi masa aure har zuwa lokacin da
ta saya masa jaki ya rik'a bin masu saran
itace. Sannan ya ba ta labarin yadda saukar
ruwa ya tilasta musu shiga kogo domin su fake,
a nan kuma ya rik'a buga gatarinsa har ya ci
karo da rijiyar zuma. Da yadda 'yan uwansa
suka tafi suka bar shi da yadda kunama ta
fad'o masa ya gane wurin da ta fito har ya yi
babban rami ya fita zuwa inda ya ga k'ofa ya
shiga zuwa wannan fadar. Har zuwa inda ya
gamu da sarauniyar macizai. Daga nan ya ce
mata, "wannan shi ne labarina daga farko har
zuwa yanzun nan da nake magana da ke, Allah
shi ne kuma ya san abin da zai faru da ni nan
gaba."
Sarauniyar macizai ta ce, "kwantar da
hankalinka, babu abin da zai same ka sai
alheri." A nan sai Shaharzad, ta katse zancenta
mai dad'in saurare.DARE DUBU DA DAYA (242)
A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse
zancenta mai dad'in saurare.
DARE NA 484
A dare na d'ari hud’u da tamanin da hud’u,
Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai wannan
hamshak’in Sarki, Yayin da Hasib ya d’auke
dutsen sai ga wata k’ofa kamar an danne ta da
wani zagayayyen bak’in k’arfe. Da ya ga haka
sai ya cika da farin ciki, ya kirawo abokan
aikinsa ya nuna musu, suka cire bak’in k’arfen
sai suka ga wani d’an kururrumin rami cike da
ruwan zuma. Da suka ga haka sai suka ce,
“wannan zumar tana da yawan gaske, babu
abin da ya fi sai mu koma cikin gari mu samo
salkuna da tukwane mu kwashe ta gaba d’aya
mu je mu sayar mu raba kud’in tsakaninmu.
Amma d’aya daga cikinmu ya tsaya kula da
wajen kada wasu su zo su kwashe mana alhali
ba ma nan.” Hasib ya ce, “ni zan zauna kula da
wurin har ku je ku dawo.” Suka tafi suka bar shi
yana kula da wajen, bayan wasu lokuta suka
dawo d’auke da salkuna da tukwane da
mazubai masu...


Read / Download HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album