Join Our WhatsApp Group

GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4 Complete Hausa Novel Document by GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4


GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 92488



GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4

Reading Time: 7 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 479.82 kb

File Type: txt

Views: 1031+

Download: 683+

Last download: 3 days ago

Description/Story: }~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 1
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
................................
Babi Na Dya.
Tana zaune akan katifarta ita kadai a cikin dan qaramin dakinta. Ta dade a haka tun kusan kimanin awa daya tana kallon kundin adana hotunanta (album) Wanda ta riqe shi da hannu biyu kamar littafin karatu.
.
Duk da yake ta rufe qofar dakin nata, hakan bai hanata ganin hotunan ba, ta hanyar hasken qwan wutar dake a goshin dakin. wutar babu qarfi, wani lkcn sai ayi kamar za a dauke, xuwa can Kuma sai ta tsaya. Bata yi mamakin hakan ba, don kuwa ruwa ake ta sheqawa a lkcn kamar da bakin qwarya, ga kuma iska da walqiya. Don haka za a iya dauke wutar a Kowanne lkc bayan ynx.
.
Duk lkcn da aka ce ana ruwa, in dai wannan budurwa tana a gida, Sau da yawa babu abin da ta fi sha'awa irin ta dauko hotunan ta na da, da na ynx, ta riqa kallon su tana tuno abubuwan da suka gabata a rayuwarta.
.
A haka zata wuni a cikin dakin nata, har xuwa lkcn da za a dauke ruwan, idan ta gaji sai ta fito waje ta sha iska, ko Kuma ta je dakin mahaifiyarta su yi hira.
.
Sa6anin Sauran ranakun da irin haka ya sha faruwa da ita, yau ruwan ya sauko ne a daidai lkcn da take shirin xuwa asibiti inda take aiki. Ynx aikin rana take yi, da qarfe sha biyu saura kwata take fita ta isa asibitin da qarfe sha-biyu daidai. Daga nan ba zata dawo ba sai kuma qarfe bakwai na yamma.
.
Gashi yau ruwan ya tsareta, har ta ci kusan awa daya a gida tana jira a dauke, don haka tana dai kallon hotunan ne don kada ta rasa abin da zata yi a dakin nata, amma ba don tana so ba."
.
Sannu a hankali ta ci gaba da bude shafukan hotunan tana cin karo da hotunanta, wadanda ta dauka ita da qawayenta tun a shekarun baya da suka shude. Ta na da qoqarin adana hoto, da wahala ta dauki hoto ta bari ya salwanta. Da haka take tunawa da yawancin qawayenta wadanda suka yi karatu tare, tun a sikandire... Tun Suna aji daya wadanda wasu da yawa a cikin su ynx ita kanta bata san a inda suke ba a duniya. Ko a raye, ko a mace, allah kadai ya sani.
.
Yawancin hotunan ta na da sun fi dadin gani, don kuwa ta daukesu ne cike da farin ciki, Suna dafe da juna ita da qawayenta sun sanya kayan makaranta iri daya, sun dafa juna Suna dariya. Kowacce sanye da hijabi gwanin ban sha'awa.
.
A shekarun baya sa'ar da tana qarama a zahiri ta fi jin dadin rayuwa, sbd a wancan lkcn babu wani abu da yake damunta. Tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali da farin ciki. Amma yawancin hotunan ta wadanda basu wuce shekaru uku ba, ta daukesu ne cikin damuwa Wanda kai tsaye za a iya gane hakan ta hanyar ramewar da tayi a a cikin hotunan, ynx kam ta fi zama mace sosai, amma in har za a dauko hotunan nata a hada su waje daya, da an gansu za a fahimci rayuwa ta canza, da ba ynx ba."
.
Duk da yake hotunan nata Suna debe mata kewa, a 6oye Suna tayar mata da hankali, wani lkcn ma har kuka suke sa ta a cikin dakin nata, ba tare da kowa ya sani ba." shi yasa ba kowanne hoto take so ta riqa kallo ba a kowanne lkc.
.
Hotunan da ta dauka ita da qawayenta sun fi komai debe mata kewa, don kuwa da yawa a cikin su sun yi aure, wadansu ma ynx sun haihu ya kai sau uku, ita kadai ce har ynx tana gida, har ta fara aiki, amma kama-kama auren bai kankama ba tukuna.
.
Ko ynx da ta ke zaune a dakinta tana jiran daukewar ruwan bata yarda tayi nisa a cikin album din ba, shafi uku kawai ta bude, na farko shine shafin da hotunanta suke can zamanin da take a sikandire.
.
Xuwa can kuma sai ta qara bude na gaba, a can ne tayi karo da wani hoton ta guda daya da ta ware shi shi kadai, sbd tsabar son shi da take yi. Tunda take daukar hoto a duniya bata ta6a daukar hoton da ya fito da ita ba, ya bayyana kyawawan siffofinta irin wannan ba." yawanci shi ta fi baiwa duk wani saurayi da ya dameta ta bashi hotonta, don kuwa ta sa an wanke mata wannan hoton yafi kala talatin daga bara xuwa bana, Kuma duk ta rabar dasu, saura wannan guda dayan kuma shi ne dai wanda ya rage a cikin album dinta. Kuma ta yi alqawarin babu wanda zata baiwa, indai ba wani ta sa aka wanko ba."
.
Sanye take da tsukakkiyar jar riga wacce ta kama jikinta, tun daga tsukakkiyar mararta har xuwa bisan qirjinta. Ta lanqwasa dogon wuyanta a cikin hoton tayi tagumi da hannunta daya, sannan tana sanye da baqar hular sanyi, wacce bata yi nasarar suturce yalwataccen dogon gashin kanta ba, da ya xubo har xuwa dokin wuyanta.
.
Tana sanye da farin siket wanda ya dan leqo kadan a cikin hoton, ta hanyar durqusawar da tayi ta dafa guiwarta da daya hannun tana kallon kyamara da kyawawan idanunta dake kama da qanqara. Ba murmushi take yi ba, ta tsayar da hankalinta ne waje guda, duk da haka idan ba lura mutum yayi ba, sai ya rantse murmushi take yi a cikin hoton, wannan ya samo asali ne sbd qyalqyali da le66anta suke yi, a dalilin wani rantsattsen man le6en da tayi amfani dashi sa'ar da ta dauki hoton, shekara daya da rabi kenan da ta wuce.
.
Duk lkcn da wannan kyakkyawar budurwa tazo kan wannan hoto nata, Sau da yawa ta kan 6ata lkc akan shi, tana kallo kafin ta wuce xuwa hoto na gaba. Ko a wannan karon ma ta dan dade tana kallon hoton xuwa can Kuma sai ta yi ajiyar xuciya.
.
Babu shakka ita kanta ta san cewar Allah ya yi mata baiwar kyau da cikar halitta!
.
Hoton yayi kyau, to amma ita ma fa kyakkyawa ce a zahiri, wa zai ganta ynx a haka ya ce ta kai shekara talatin a duniya? Komai yana nan bai canza ba a tattare da ita, jikinta ba rukuta bane, marke ne....! Wanda ya santa a shekaru goma da suka wuce, idan ya ganta ynx zai ga tana nan a yadda ya santa, bata canza ba."
.
A bayyane a iya cewa, wannan ya taimaka mata wajen rage surutun mutane, wadanda suke yi mata maganar aure shekara da shekaru. Jikinta baya bayyana yawan shekarunta, wadanda suka santa ne kawai, suke gane ba yarinya ba ce, amma ga baqin idanu ba Wanda zai ganta ya ce ta wuce shekara ashirin da haduwa.
.
Idan aka ce wannan budurwa bata son aure gskyr magana ba a yi mata adalci ba." tana son aure kamar yadda take son ranta. Matsalar kawai ita ce, tayi rashin sa'ar fadawa tarkon son wani saurayi dake a layinsu, wadanda shi a 6arinsa ko kusa ba ta ita yake yi ba."
.
Abin da ya daurewa mutane kai shi ne, ganin yadda saurayin yake wulaqanta kyakkyawar mace ma'aikaciya, mai aji. Koda yake ba abin mamaki bane idan aka yi la'akari da mugayen halayen saurayin. Sauran da yawa ma idan aka zo layinsu idan ba cewa kayi, Nura aljan ba, ba kasafai ake gane shi ka zo neman ba." akwai dalilan da suka sa ake kiran sa da aljan duk da yake kuwa mutum ne sak! Kamar kowa.
.
Tun yana yaro ya taso da rashin hankali, da hatsabibanci, Wanda hakan ya sa ya yiwa kratu tawaye, ko ynx a sana'arsa ta aca6a yayi qaurin suna a wajen jama'an tsaron kan titi, zai yi wahala nura aljan ya zo wucewa a dakatar dashi ya tsaya. Kuma indai zai fito aiki da safe xuwa dare, qa'ida ne yayi fada da direbobi aqalla goma akan tituna Daba-daban
.
Nura farin saurayi ne wanda yayi sa'a tabar da yake shafi'u babu qaqqautawa bata canza mashi kala ba." don farin jini kam wannan bashi da matsala, maza da mata Suna sonshi duk da mugun halinshi da zafin ransa, yana da kyau, sai dai Kuma halinsa ne baiwa zamo kyakkyawa ba."
.
Wannan kyakkyawar budurwar ta dade tana son Nura aljan, koda yake ita bata yarda aljani bane, ta sha yi masa nasiha kan ya daina yadda anan ce masa aljani, Tunda dai shi mutum ne kamar kowa. Abin da ba ta sanin ba shi ne, Nura yana son wannan Suna fiye da yadda yake sonta...idan ma yana sonta din kenan, don kuwa ita ce take bin shi a Kowanne lkc, ba shi ne yake xuwa inda take ba."
.
Wadanda abin ya dame su, sukan yi mata fada su tambayeta. Me ta gani a wajen wannan saurayi marar tarbiyya da take so shekara da shekaru? Kyakkyawar tana fadar maganganu daban-daban don ta kare kanta a wajen mutane. Idan tana jinjinawa kunyar mutum ta kan ce cikin sunkuyar da kai.
.
"ka san yana da kyau idan daga mutum cikin mawuyacin haii kayi qoqari ka jawoshi ya zama mutum sosai, ni ina sonsa ne tsakanina da Allah, Kuma ina fatan adalilina ya daina duk wadannan halayen na sa ya zama mutumin kirk, ya shiryu."
.
Idan Kuma a cikin qawayenta ne wadanda su bata jin kunyar ta fading komai a gabansu ta kan ta kan yi dariya ta ce.
.
"kai ina son Nura, Kuma ba zan ta6a daina sonsa ba." ni kawai fara'arsa da Kuma qarfinsa ne suke burgeni. Nura ya shiga raina, kawai halayensa ne suke damuna, amma Kada Kuma damu zai bar komai ya dawo (normal) in dai muna tare zan gyara shi."
.
Ita kanta da ta ke fadar haka, a can cikin xuciyata ta fi kowa sanin dalilin da yasa Nura yake saurarenta, Kuma har yake dan ganin mutuncinta, babur din da yake aca6a dashi nata ne wanda ta amshi bashin ma'aikata anan cire kudin a cikin albashinta. Duk duniya babu Wanda ya san wannan zancen, ko mahaifiyarta da suke kwana tare bata ya
.
.
Lp=2}~~~~~~{ Gobe Jar Kasa }~~~~~~{
Page 2
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Babu wanda ya san wannan zancen, ko mahaifiyarta da suke kwana tare bata yarda ta sani ba, don gudun kada ta sha zagi, ta gargadi nura tun a lkcn idan an tambayeshi ya ce, wani abokinsa ya sai masa ya bashi ya riqa kai masa balas, kada ya ce nata ne don gudun surutun mutane.
.
Nura bai ta6a kawo mata balas ba, wani lkcn ma idan mashin din ya lalace bashi da kudin gyara, ita take bashi kudin ya je a gyara, ya ci gaba da aikin, kada dai ya riqa zaman banza kamar yadda take yawan gargadinsa idan ta ciro kudi zata bashi.
.
abin da yafi komai faranta mata rai shi ne, duk lkcn da zata je wajen aiki, nura yake xuwa ya dauke ta ya kaita har asibiti idan kuma ta gama aikinta, sai ta yi masa waya ta ce ya zo ya dauke ta ya mayar da ita gida. Don haka ya sa kawai ta mallaka masa babur din kyauta, domin kuwa in banda haka, ita kanta ta san bata da martabar da nura zai zo ya dauketa ya kaita wajen aiki, ya Kuma je ya daukota ya dawo da ita Kullum
.
To kowa dai da abin da yake fada a game da halin wannan kyakkyawar mace da Kuma wannan dan tawayen masoyi nata da suke a layi daya. Wasu Suna ganin ai ba wani abu bane don ta nace shi take so, tunda dai tare aka taso ga gida ga gida, wa ya sani ma ko irin shaquwar nan ce tun Suna yara? Shi dama so ai haka yake.
.
Wasu kuma suna ganin duk wannan ba hujja bace.
.
Kawai dai yarinya bata da masu fada ma ta gsky shi yasa take abin da ta ga dama. Shi kadai ne saurayi? Kawai idan aka ce mace 'yar mace ce, sai dai haquri."
.
Mahaifinta ya rasu tun tana qarama, kuma mahaifiyarta bata yarda ta rabu da 'yarta ba, ita kadai ta rage mata a raye, da mahaifiyarta ta dan yi aure-aurenta ta gaji, sai ta dawo ta rungumi 'yarta suka gyara gidan su na gado da mahaifin yarinyar ya rasu ya bar masu. Gidan qasa ne, Kuma bai samu wani gyara na azo a gani ba." a qalla dai yafi ace Suna tsugunne a wajen 'yan uwa.
.
Ta wani 6angaren yarinyar tana qoqari, don kuwa ba nura kadai yake qarar mata da albashinta ba, rashin lfyr mahaifiyarta Wanda ke tasowa akai-akai na ciwon suga da kuma sukurkutaccen gidan nasu dake buqatar gyara duka Suna taka rawar gani wajen lashe dan albashin nata. Shi yasa har ynx ta kasa ajiye komai, Suna dai ci su sha kullum, Kuma duk wata sai ta dinka sabbin kaya, Suna cikin rufin asiri daidai gwargwado, matsalolinta dai biyu ne xuwa uku, gskyr mutane ne, tabbas bata da masu yi mata fada ta ji, mahaifiyarta ta kanta take yi, bata cika damuwa da sha'anin 'yar tata ba."
.
babbar matsala ta biyu kuma, soyayyar nura Wanda ko kusa shi ba zancen aure ne a gabansa ba." idan ma tayi masa maganar auren, ko fara'a, yake yi sai ya 6ata ransa.
.
"kin san fa bana son kina yi mani wannan maganar, kawai dai idan zamu yi soyayya muyi, amma bana son zancen aure, don ba shi nasa a gabana
.
Sau da yawa ta kan lallashe shi ta ce.
.
"haka nura, an ta6a yin mutum ya zauna haka ya ce ba zai yi aure ba? Na san baka da kudi, amma kada ka damu, ni zan dauki nauyin komai, ni zan kama mana gidan da zamu zauna."
.
Nura ya ta6a cewa da ita.
.
"ko mota da kaya zaki riqa bani, in dai aure ne ba na so, ni kawai burina in samu kudi na bala'i in take in bar qasar nan in huta...kawai mutum ya ware inda ba za a riqa ganin san ba."
.
Tun daga ranar ta tabbatar tana soyayya da riqaqqen matar hankali a duniya. Son xuciya da Kuma rashin mafadi ne yasa ba zata iya cire nura daga cikin xuciyata ba." ta za6i wani mutumiin kirkin ta aura a cikin mutanen da suke sonta ba tsawon lkc, wadanda da yawansu abokan aikinta ne da suke aiki tare, da Kuma jefi-jefi mutanen da suke biyo ta har gida su san a kirata ta ce ace dasu ba zata zo ba."
.
Tana nan a zaune tana riqe da album din hotunan, sai ta ji an dan tsagaita da ruwan. Tayi sauri ta rufe album din, ta ajiye hotunan akan katifartta. Ta yunqura ta tashi a cikin gajiya don kuwa ta dade a zaune.
.
Da tashinta t kai hannu ta bude qofar cikin sauri, ta qosa ta tafi asibitin, ta san ana can ana jiranta,...


Read / Download GOBE JAR KASA 1,2,3 and 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album