Join Our WhatsApp Group

AJALI Complete Hausa Novel Document by AJALI


AJALI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17335



AJALI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 89.86 kb

File Type: txt

Views: 769+

Download: 179+

Last download: 5 days ago

Description/Story: AJALI
Marubucin littafin
Shafi'u Dauda Giwa
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 1
.
BABI NA FARKO
.
"A gaskiya Nazifi sai dai ka yi haquri da
abinda zan fada maka ni dai shawarar da zan
ba ka ita ce, ka yi haquri ka manta da
al'amarin wannan yarinyar domin kuwa a
gaskiya ba abokiyar tafiya ba ce"
.
Nazifi ya dubi abokin hirar tashi cikin
mamaki da kaduwa, "Kamar yaya in yi haquri
Jamilu, ban gane abinda kake nufi ba."
Jamilu ya muskuta a kan dogon bencin da
suke zaune,
"Ka gane ko Nazifi, ba wai ina
nufin yarinyar ba ta da kyawawan halaye ba ne,
a'a tana da halaye nagari. To amma, ni dai
halayen babanta nake hango maka Nazifi.
Na san halin mutumin domin kuwa tunda ka yi
mini kwatancen yarinyar, na fara zulumin ka
yi zaben tumun dare."

.
Nazifi ya sake duban sa cikin rudani.
"Haba Jamilu wannan wace irin magana ce?
Yaya ma za a ce in ga yarinya jiya-jiyan nan,
sannan kuma in ji ina son ta a raina, har mu
gama tattaunawa mu yi alqawari ni da ita,
amma kuma ina fada maka ka ce da ni in
rabu da ita. Kai ma kanka ka san cewa
wannan magana taka Jamilu ba mai amsuwa
ba ce."
.
"Ba ina qoqarin raba ka da yarinyar ba ne
Nazifi. Abinda nake qoqarin nuna maka a nan
shi ne wannan yarinyar ba baquwa ba ce a
wurina. Na san gidansu domin kuwa mun
taba zama a unguwar. Hakan shi ya sa na
fahimci cewar ba za ka iya jurewa da halayen
mahaifinta ba."
.
Samarin biyu suka qurawa juna idanu. Nazifi
ya ce da shi, " To ai ni ban gane matsalar da
kake so ka nuna mini na rabuwa da ita din ba
ne, kuma ka qi ka sanar da ko wane ne
mahaifinta, domin kuwa ni gidansu kawai ta
kwatanta mini ba ta fada mini sunan
mahaifinta ba."

.
Jamilu ya dan saurara sannan ya ce da shi,
"Mahaifinta ba wai voyayye ba ne, sunansa
Alhaji Dage, wataqila ma dai ba za ka rasa jin
labarinsa ba."
"Ban san shi ba, Jamilu, to amma dai tunda
ka sanar da ni a halin yanzu, ina ganin kana
iya ba ni taqaitaccen bayani game da halayen
nasa don in fahimci irin matsalolinsa da kake
magana a kai."

.
Jamilu ya kai ganinsa dama da hagun harabar
qofar gidan, ya tabbatar babu wanda yake
sauraron hirar tasu, sannan ne to ya dawo da
hankalinsa kan Nazifi, wanda ya yi fakare
yana sauraronsa.

.
"Ka gafarce ni Nazifi, zan fada maka
halayensa gaba daya. A gaskiya Alhaji Dage
ba ya baiwa talaka auren `ya`yansa, domin
kuwa ya aurar da `ya`yansa aqalla guda
biyar, amma kuma na ji an ce duk a cikin
wadannan `ya`yan nasa, babu wacce ta auri
talaka irinka Nazifi. Kuma a wata majiyar ma
an ce wai idan har ka auri 'yar gidan Alhaji
Dage, dole ne ka riqa samar masa da albashi
kowanne wata. Ka ga dai kai talaka ne Nazifi,
don Allah ka yi wa kanka qiyamul laili, kada
ka jawowa kanka abin tsiya kana zaune lafiya.
Kawai ka mance da zancenta, ka nemi wata
budurwar daidai qarfinka."
.
Nazifi ya yi shiru yana tunanin maganar, zuwa
can sai ya ce, "Amma fa al'amarin nan ya
daure min kai Jamilu, domin kuwa jiya a
wurin fatin nan kada ka so ka ga yadda
yarinyar nan ta manne mini, duk inda na
nufa tana liqe da ni kamar cingam. Kuma har
ma mun yi alqawari da ita cewar zan kai mata
ziyara a yau din nan."

.
Jamilu ya fashe da dariya.
"To daga haduwar fari kuma kawai sai ka
tsaya kana damun kanka Nazifi? Sai ka ce za
ta kai ka qara idan ka ce ka fasa yin soyayyar?
Ni dai ka ji shawarar da zan ba ka. Idan ka
dauka ta yi maka amfani. Idan kuma ka yi
kunnen uwar shegu da wannan shawara tawa,
to wannan kuma ya rage naka. Ni dai na fita
haqqinka a matsayina na abokinka, tunda dai
ka tambaye ni gaskiya na gaya maka."
.
Koda ya kammala sanar da shi sai ya juyar da
fuskarsa wani bangaren don ba shi damar yin
tunanin maganganun.
.
Nazifi ya yi tagumi
yana tunanin wadannan maganganu na
wannan aboki nasa Jamilu. Sannan ya sake
dawo da farkon haduwarsu da yarinyar a
daren jiya sanda ake fatin wani abokinsa.

.
Tana daya daga cikin manyan qawayen
amarya. Tana sanye da shudin gwaggwaro.
dan saurayin ya yafito ta tun daga nesa cikin
qwarewa da sabo da kiran kyawawan 'yan
mata a wurin fati na yau da kullum.
.
Kyakkyawar yarinyar ta taso daga cikin
qawayenta ta same shi, suka dan kebe,
sauran jama'a kowa nata harkarsa.
"Idan ba za ki damu ba 'yan mata, zan so ki
ba ni 'yan mintuna koda biyar ne haka,
domin kuwa ina da wata 'yar magana da ke."
.
Yarinyar ta yi masa fari, ga alamar wayayyiya
ce, ta ce "In ban da abinka malam, ka taba
ganin wanda zai damu da sauraron baqon
shi? Ba komai kai dai yi bayaninka ina
sauraron ka."
.
Nazifi ya yi mata murmushin farin ciki.
"Na yi farin ciki da kika nuna mini yarda
kuma na ji dadi sasai da sakin fuskar da kika
nuna mini."
.
Ya dan saurara sannan ya ci gaba da cewa da
ita.
"Ni dai sunana Nazifi kuma dan asalin garin
nan ne ni, domin kuwa iyayena ma a nan aka
haife su. A zahirin gaskiya ni ba wani mai
wadata ba ne, domin kuwa sana'ar kafinta
nake yi, a nan nake ci in sha, sannan kuma in
yin wasu 'yan buqatuna. Wannan shi ne dan
taqaitaccen tarihina da zan sanar da ke. Na
fada miki ne don ki san ko ni wane ne kafin ki
ba ni amsar tambayoyin da zan yi miki."
.
"Wacce tambaya ce Malam Nazifi?"
Ya yi mata murmushi, "Mhm! Tambayar ba
wata boyayyiya ba ce. Da ma so nake yi na ji
ko kina so na, sannan kuma za ki iya aure na?
Ni dai gaskiya ina masifar qaunar ki malama,
domin kuwa ba ki lura ba ne tunda aka fara
wannan fati ke nake ta kallo?"
.
Zan cigaba Abokai
AJALI
Marubuci
Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 2
.
Ta yi dariya, "Na ji bayaninka Malam Nazifi
kuma ina yi maka albishir da cewar ka sami
karbuwa a zuciyata, domin kuwa ni kaina ina
matuqar sha'awar namiji irinka mai ban
dariya."
.
Suka tintsire da dariya a lokaci guda.
"Kada kuma ki ziga ni mana, in riqa fasa kaina
a wurin 'yan mata."
"Ba maganar ziga Nazifi, gaskiya nake fada."
Ya sunkuyar da kansa sannan ya ce da ita
yana murmushi.
.
"Ban san iyakar godiyar da zan yi miki ba
wallahi, ga shi kuma ban san sunanki ba."
Ta dan yi farin cikin kissa, sanna ta ce da shi.
.
"Kada ka damu Nazifi, kana iya kira na da
A'isha."
"Mhm! sunan naki akwai dadi wallahi, da ma
wata rana na tava mafarkin zan auri wata
kyakkyawar mace mai suna A'isha."
.
Suka sake yin dariya, ta ce da shi.
"Kai dai Malam ba ka rabo da abin dariya
wallahi."
Abu kamar wasa a cikin 'yan mintoci biyar din
da suka yi suka saba da juna sai ka ce sun
shekara biyar da fara soyayya.
Bayan ta yi masa kwatancen gidansu, shi ma
ya sanar da ita inda gidansu yake. Sai ya ce da
ita.
.
"Ina fatan dai daga wannan bikin ba mun
rabu kenan ba, A'isha?"
Ta sake duban shi ta ce.
"Ni dai a bangarena ba mu rabu ba, amma
idan kai ma haka abin yake a zuciyarka, me
zai hana kai ka fara kawo min ziyara don in
tabbatar da gaske kake yi."
.
Nazifi ya ce da ita.
"Yaushe to zan zo in same ki, A'isha?"
Ta jefe shi da wani sabon murmushin.
"Ko gobe ma kana iya zuwa Nazifi, kowanne
lokaci ina nan a gida ba inda nake zuwa."
"Ki saurare ni da yamma A'isha, in Allah ya
so za ki ganni."
.
Ta sake cewa da shi.
"Don Allah ka zo Nazifi, wallahi ka shiga
raina. Ba na gajiya da sauraron maganarka,
kamar kada mu rabu."
Suka yi dariya cikin farin ciki
.
Wannnan shi ne mafarin wannan al'amari.
Har aka tashi fatin ya koma gida, bai daina
tunanin 'yar budurwar ba. Duk ya qosa gari
ya waye don yamma ta yi ya je ya same ta.
.
To amma ko a cikin ranshi, dama ya yi
alqawarin kafin ya je wurinta sai ya shaida wa
abokin sana'arsa Jamilu. Domin kuwa har
suka bar wurin fatin a daren jiya bai sanar da
shi abinda ya wakana a tsakaninsa da yarinyar
ba
.
Tunanin Nazifi ya katse a yayin da ya ji
Jamilu ya girgiza kafadarshi. Ya dube shi cikin
tsananin kidimewa.
.
"Wanne irin tunani ne wannan Nazifi? Daga
na dan ba ka mintoci biyu ka yi nazari amma
ka share wajen mintoci goma?"
.
Nazifi ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce da shi.
"Wallahi tunaninta nake yi Jamilu."
"Tunanin wacce kuma?" Jamilu ya tambaye
shi.
"Maganar me muke yi da kai, Jamilu?
Tunanin masoyiyata A'isha mana, ko ka
mance ne"
.
Jamilu ya dube shi cikin rudani.
"Au Wai da ma duk shawarar da na ba ka, ba
ka dauka ba Nazifi? Ai ni na yi tsammanin ka
mance da al'amarin. Ni wallahi da na ga ka yi shiru na dauka tunanin wani abun kuma
kake."
.
Nazifi ya kawar da kansa cikin wani yanayi
mai kama da damuwa, sannan ya dubi abokinsa
Jamilu.
.
"A gaskiya ba zan boye maka ba Jamilu, ba na
jin zan iya rabuwa da A'isha, tunda dai tana
so na. Na san dai duk tsiyar baban nata ba dai
zai kashe ni ba don na ce ina son 'yarsa."
*************
Ya fito daga cikin dakinsa, a lokacin da ya ji
Burarin 'yarsa A'isha, riqe da jarida a
hannunsa, sanye da qaton farin tabarau a kan
ramammiyar fuskarsa. A daidai wannan
lokaci ne mafadaciyar matar ta ci wa
kyakkyawar yarinyar kwalar riga ta girgiza da
Karfi, sannan ta daka mata tsawa.
"Don ubanki wane ne saurayin da kika canza,
fada min?"
.
Yarinyar ta sake fashewa da kuka, ta dora
hannayenta bisa kanta.
"Lallai A'isha kin zama 'yar iska, ni zaki dubi
tsabar idanuna ki sanar da ni cewar wai ba
kya son Gali, kin samu wani sabon saurayin
To ki fada mini ko dan gidan uban wane ne a
garin nan ko in ci ubanki."
.
Ta sake cukuikuyarta ta kayar da ita a kan
lallausan kujerun da ke zagaye da tsararren
falon.
,
"Ya isa haka nan."
Tsamurarren mutumin ya fada a sanyaye.
Babu alamar damuwa ko farin ciki a fuskarsa.
To amma dai da ganin guru-gurun idanunsa
da ke cikin faskeken tabaran ka san cewar ba
a son ranshi matarsa take dukan 'yar tasa
Kwallin kwal da ya fi kauna a duniya ba, duk
da yake dai bai san laifin da yarinyar ta yi ba.
.
Matar tasa mai suna Juma ta dago kai ta dube
shi tana numfashi sama-sama kamar ranta
zai fita, kwata-kwata ba ma ta san lokacin da
Alhaji Dage ya shigo falon ba, sai dai kawai
maganarsa da ta ji.
"Laifin me ta yi miki kuma Juma, kike yi
mata irin wannan mahaukacin duka? Irin
wannan in tsautsayi ya ratsa ai sai ki karya ta
a banza."
.
Ta sakar mata wuyan riga, A'isha ta miqe tana
sharbar kuka. Ta nufi dakinta da gudu-gudu.
Alhaji Dage ya bi ta da kallo, duk da yake
idan yana sanye da farin tabaronsa ba kasafai
mutum zai iya karanto wani yanayi a fuskarsa
ba, to amma dai a wannan karon duk da
wannan uban tabaron da ya tsare harabar
kusan ramammiyar fuskarsa gaba dayanta,
hakan bai hana bayyanar da alamomin
damuwa ba a kan fuskar tasa.
.
"Wai laifin me ta yi miki ne, iye?"
Juma ta dube shi cikin tsananin damuwa.
"Ba ka ji magana da muke ba ne da ita a
lokacin da ka shigo?"
"Ba wannan na tambaye ki ba. Ko na ji ko ban
ji wannan ni ta shafa, ke dai ki fada mini
abinda na tambaye ki."
Mafadaciyar matar ta sake numfasawa, duk
fuskarta ta yi sharkaf da zufa sai ka ce ta ci
uban aiki.
.
"Wai Alhaji, wannan 'yar banzar yarinyar
saura kwana takwas kenan fa a daura aurensu
da Gali, shi ne don rashin albarka ta same ni
har daki ta shaida mini cewar wai ba ta son
shi, ta samu wano sabon saurayi wanda take
so."
.
Alhaji Dage ya cire qaton tabaron cikin
tsananin kaduwa da jin zancen matarsa Juma,
saura qiris jaridar ta sullube daga hannunsa
ta fadi qasa. Ya tambaye ta a tsorace.
"Ta canza wani saurayi fa kika ce...?
"Qwarai kuwa, idan kuma ka tababa sai in
kira maka ita ka tambaye ta ta fada maka kai
ma ka ji."
.
Ramammen mutumin ya ja doguwar ajiyar
zuciya. Abu na farko da ya fara darsuwa a
zuciyarsa shi ne, yanzu dai idan wannan 'ya
tasa ta bijire har maganar auren nan ta
lalace, a ina zai lalubo dubbban daruruwan
kudin da suka cinye wa wannan saurayi da zai
aure ta? wanda akalla ba akasara ba, in dai
lissafi za a yi dalla-dalla to sun ci wa saurayin
kudi ya kai miliyan guda, duk don kawai za su
aurar masa da 'yarsu daya, sai kace 'yar
zinare. Shi kuma da yake Allah ya jarrabe shi
da son ta, haka nan yake ta bayarwa, tunda
dai ya san in dai aka riga aka yi auren duk
masifa dai kuma ba za a ce ya riqa ba da
albashi duk wata ba.
.
"Amma fa wannan yarinyar tana neman
dama mana lissafi, domin kuwa idan zancen
auren nan ya lalace ban san yadda zan yi da
wannan yaro ba."
.
Ya yi ta sambatu shi kadai matar tana tsaye
tana kallon sa.
.
Abokai kuyi mani afuwa kwana biyu ina skul shi yasa kuka jini shiru
Shuraih usman

AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 3
.
Duk da yake da ita ma irinsa
ce, ba wai auki gare ta ba, to amma dai ta fi
shi cika fuska, domin kuwa duk da tambarin
da sunanshi ya yi a gari, wajen masifa da
rashin hakuri, to idan ya dawo cikin gidansa
kuma sai ya yi lagwaf kamar tsumma.
.
Domin kuwa matarsa Juma ta fi shi masifa nesa ba kusa ba. Kuma ko tsiyar tasu ta taso shi da
ita, ba ya wani cin riba, don kuwa ta fi shi
baki. Shi ya sa yake lallaba ta tunda dai ya san
cewar jiya ba yau ba ce.
.
Da ace sanda yake da dukiya ne, kafin ya samu karayar arziki, ai itama ta san cewar ba abokiyar takawarsa ba ce.
To amma tunda ta ga cewar dan abinda yake
takamar ya kare, sai dai 'yan dabaru a gari,
ita ma ta daina raga masa a cikin gida
.
"To wai a ina ma ta samu wani saurayin,
kuma ma dan gidan wane ne a garin nan?"
Alhaji Dage ya tambaye ta cikin karaya.
.
Juma ta turo baki a fusace ta ce da shi.
"Ni fa ba ta fada mini ko wane ne ba. ta dai
ce da ni ba za ta auri Gali ba. Kuma ni ina
tsammanin duk yadda aka yi a wajen wannan
tsinannen fatin bikin kawarta da ta je jiya, ta
hadu da saurayin domin kuwa ba ta dawo nan
gidan ba sai da talatanin dare."
.
Alhaji Dage ya warware jaridar ya soma
fifita, domin kuwa a halin yanzu shi ma zufa-
zufa yake ji.
.
"To in ban da abinki Juma me ya sa kike
barin yarinyar nan tana zuwa wani fati? Kin
san fa yanzu zamani ya canza. A wurin
wannan fate-faten na alatsine, a nan 'yan
mata suke lalacewa, su kangare a yi ta fama
da su, ko kuma ma su je su kunsowa mutane
abin kunya."
.
"To yanzu dai aikin gama ya gama." Juma ta
ce da shi. "In dai kangarewar ne ita dai A'isha
ta riga ta yi tunda har ta dube ni ido da ido ta
ce a canza mijin aure, don haka yanzu ya
rage namu mu nemi mafita, amma wannan
cacar bakin da muke yi ba za ta fisshe mu
ba."
.
Alhaji Dage ya sake jan doguwar zuciya,
sannan ya ce da matar tasa.
"Eh to ke ma a nan kin kawo shawara mai kyau
Juma, domin kuwa ko da a ce al'amura sun
lalace ita yarinyar ba ruwanta, mu za a tsare
don haka lallai dabara ta rage tamu."
.
Ya sake numfasawa, zuwa can ya tattara
hankalinsa wuri guda, ya ce...


Read / Download AJALI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album