Join Our WhatsApp Group

BAD BOYS Complete Hausa Novel Document by BAD BOYS


BAD BOYS

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 15259BAD BOYS

Reading Time: 1 Hours

Added On: 05, Nov 2023

Author: Oum Aphnan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09065990265,

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 85.52 kb

File Type: txt

Views: 2821+

Download: 1762+

Last download: 6 hours ago

Description/Story: *_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

Bismillahir rahmanir rahim
___________________
001
3.30 Na tsakar dare.
“Salima!
Salima!!
Salima!!!”

Cikin wannan talatainin daren Salima ta jiyo Muryar mijinta Sheikh Al_Miqdad yana kwarara mata kira .
A furgice Salima ta dirko daga kan mashahurin gadonta fari fari tarrr lulluɓe da fararen lausassun zanniwan gado .
Tana haki tayi kichin dinta da gudu ta inda take jiyo muryarsa yana kwarara mata kira ,Duk zaton ta Ya Sheikh ne ya ƙone da ruwan zafi. Ko shocking din lantarki ta kamashi.

Da gudu ta hankaɗa kofar ta shiga kicin ɗin ,tsaye ta ganshi yana tafa hannu yana kaiwa da dawowa Sai kuma ya shafa dogon cikakken gashin gemunsa ya sake rafka salati

“Innalillahi wainna ilaihir rajiunnnn....wohoho ! Uhm uhm....ke duniya ke duniya!!”

Salima ta tsorata matuka gaya don haka a tsorace ta ce “Ya Sheikh ma Asabak?( Me ya faru da kai?)” ta tambayeshi da larabci

Nuna mata dust bin yayi da yatsa ,wannan yasa ta kalli wajen zuba sharan da sauri . Sai kuma tayi turus don bata ga komai ba
“Ya Sheikh manil hadha?” (Menene wannan kenan)

Tsawa ya doka mata da ya saka hanjin cikinta karkaɗawa a tsorace wasu hawayen azaba suka tsilalo mata a ido

“Baƙi_Baƙin me na ke gani a nan?”

Wani sanyayyen ajiyar zuciya tayi kana tasa hannu ta goge ƙwallan tsoron da ya zubo mata

“Ya sheikh Burnt rice ne (Ƙanzo)”

“Mene? Ƙanzo ? Ke kuwa kika zauna kika babbaka mun shinkafa ,a wannan rayuwar da ake ciki? Kinsan yanzun nawa ne tiyan shinkafa a kasuwa? Kinsan fetur yayi tsada kuwa lita 640₦😳amma a haka kika ƙone mun shinkafa duk tulin nan?”

Rausayar da kai tayi cike da ladabi
“Ya Sheikh meye na shouting ,ɗan kaɗan ne fa bai wuce ludayi biyu ba”

Hangame baki yayi yana kallonta cike da mamaki

“Au Salima da so kikayi ki ƙone Kamar plate ɗaya wanda ya isa a baiwa wani magidancin yaci ya ƙoshi?”

Shiru tayi saima ta sunkuyar da kai tana ta salati da addu'ar Allah ya yayyafa ma fitinar nan ruwa a daren nan

“....Ya Salam! Yanzu Ni sai in fita in nemo kudi ,ke da zaki taimake Ni wajen tattalawa amma sai ki babbaka?”
Caɓe fuska tayi da Alamar gundura

“Ya Sheikh Ladainan kharrr sa tasma'una ma aƙul...La dhair lillah....”(Ya Sheikh muna da makota don Allah kayi shiru ,Makota duk zasuji abinda muke cewa ,Plz darene yanzu kowa barci yakeyi....)

Wage Baki yayi yana ihu yana zage glasses ɗin windows ɗin kitchen din

“A ji mana sai me?...sai me? Ina sha nan gida na ne?”

“Sheikh kayi haƙuri kowa yasan jollof rice yana Ƙanzo ba yanda zanyi ”

“Au ke baki da dabarun girki? Meye amfanin abun ƙari da ragin dake jikin gas ɗinki? Ya kamata ,idan kikaga ruwa yayi ƙasa sai ki ta ragewa kita ragewa har ya tsotse ,shikenan fa!!”

“Tom ya Sheikh haka bazai kara faruwa ba ,Isbir lillah (Kayi hakuri don Allah)”

A husace ya wage ƙofar saura ƙiris ya hankaɗe ta sannan ya koma bedroom ɗinsu.

Tsayawa tayi turus tana tunani ,wanda inda sabo yaci ta saba da halin Sheikh kuɗi ne gasunan an tara amma fa baa ci.

A sanyaye ta shigo ɗakin still idonta na rike da barci . Tana shigowa taji yana ƙunƙuni
“Yanzu kana magana kuma sai ace ka cika masifa ,gaskiya ne dai ba'a so mu kuma Inshallah sai mun faɗa”

“Me kuma ya faru?”

“Ji ba fa ,kin fito ɗaki ,kin bar AC a kunne,bazaki iya kashewa ba in kin dawo ki kunna? Wai kinsan nawa ya ja kuwa? ”

“Haba Sheikh naji kana ihun kirana da salati ,na ɗauka ka ƙone ne ko wani matsalan shiyasa nayi gudu naje ...”

“Shiru! 🤫 Karki sake fitamun daki baki kashe AC ba ,koda mutum zai mutu ki kashe AC kafin ki fita ,ko kuwa rayuwarsa yana hannunki ne? Me yasa baki ganewa ne ehen ,bawa bai isa ya tunkuɗe ƙaddarar da Allah zai ma wani bawa ba,don haka karki fake da wannan ki jamun asara!”

Cikin gundura tace “To shiknn naji nidai inaso inyi barci” ta wuce kan gado taja bargo” .
Tsaki yaja ya ɗauki remote ɗin Ac en ya kashe ya dawo ya shige bargon Shima.

“Ha'ah🥹Sheikh meye na kashewa kuma?”

“Ina sha sanyi kike ji? Karewa ma gaki a cikin bargo,ki bari in kinajin zafi sai a kunna ,du Allah ku koyi yanda ake tattalin kuɗi ,Ni koda nayi rayuwa ta a Sa’udiyya fiye da shekaru goma ,bana Almubazzaranci ina ganin Ac a kunne nake kashewa har a maktibah(Library) To balle nan nigeria....Don haka in ke Baki tausayina zan fara tausayin kaina !”


****
Ynz Dai kowa yasan Talatainin dare ne.
Ko'ina yayi shiru bakajin kukan komai ,gari yayi Lilis .
Kaso 85% Na talakawa masu fagauniyar neman na kansu ,sun samu natsuwa,ta hanyar yada kafadunsa don warware gajiyar yinin ranar .
A yayin da manyan masu kuɗin duniya suka nitsa cikin meeting tare da manyan masu kuɗi Don haɓɓaka arziƙinsu ...Ƴan siyasa sun nitsa cikin tunanin mafitar cigaban Mulkinsu da yanda zasu cigaba da cusa tsoro da kwarjininsu a cikin ƙirajen Talakawansu...,Mugayen Mutane kuma tuni sun nausa wajen niman arziki ta hanyar amfani da dodanni da zubda jini don neman duniya(Cultism) wasu kuma ta hanyar ƙwacen Arzikin Al'umma,ta hanyar amfani da muggan makamai harma da kisa (Arm robbery).....Kuma a daidai wannan Lokacin ne bayin Allah suka sunkuya kan darduman su cikin tsananin ƙanƙan da kai Don neman biyan buƙatunsu da neman kusanci daga wajen me duka...(ALLAH)

DUNIYA! Zaman ƴan marina kowa da fuskar da ya dosa!!

Yaro ɓata hankalin dare kayi suna ,wannan karin maganar tayi daidai da rayuwar Yarima ABBAD Ɗan Sarki,kuma ɗan takarar GWAMNAN jihar Kaduna a halin yanzu,Daya kasance cikin sujuda Sanye da fari tar ɗin Jallabiya,da hirami da ya lulluɓa a saman kansa ,wannan yasa sam komin ƙwaƙwan mai karatu bai isa ya gano Fuskarsa ba.
Ɗakin yayi tsit banda sanyin Ac dake hura daddaɗan turaren ɗakin babu abinda zai ringa dukan fuskar ka.
Yayi Liiissss a sujudi tamkar ba wannan ARROGANT Prince🤴 ɗin ba ,the Almighty gomna da mutane ke masa inkiya da ZAKI (Lion)

Shekarunsa 34 ,Amma ya shiga cikin manyan masu kuɗin Nigeria ,banda shugabanci ,ya samu Izzah da buwaya da take duk wani talaka dake ƙarƙashin yankinsa,wannan yasa har wasu suke Alaƙantashi da Mugun Yarima😡
Su biyu ne tak ɗiyoyin mai martaba Shi da ƙanwarsa Gimbiya Jasmine .
Kuma duk sun fito ne daga ɗakin uwargidan srki ,Gimbiya mai babbar Ɗaki.

A sanyaye ya ɗago daga sujudan yayi tahiya ya sallame sallah ,kana ya ɗaga hannunsa sama,har zuwa sannan baka iya ganin fuskarsa saboda ƙanƙan da kai

“Ya Allah ka bani Mulki ,Mulki da baka taɓa baiwa wani makamancin sa ba a wannan ƙarnin ,Ya Allah ka bani Sarauta in zama Sarki a lokaci guda in Kuma zama GOMNAN Al'umma,abune da ba'a taɓayi ba ,amma Allah ka nuna musu isuwarka ya Allah!🤲”

Topah🤔Haka zai yu? Zalamar batayi yawa ba? Ga mulki ga sarauta?
Muje zuwa!.

Muje zuwa
It's Oum Aphnan
Karku jirga ,sharen fagen labarin ne dai.
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

002
___________________
Motocine Manya manya baƙaƙe wulun wulun suke giggiftawa da gudu akan kwaltar ,kowanne maƙale da plate number ɗinsa an rubuta Prince 1...Yarima 2...Yarima 3 haka har Yarima 5 ,Iyakan Rubutun da akayi a jikin plate maimakon plate number din kenan ,sai wani tanfatsetsen Farin Mota ƙirar Land Cruiser a tsakiyarsu shikam baida plate number a ta gaba Sai aka kafe ƙatoton Kan Zaki 🦁 Wanda aka Sassaƙashi (Molding) da Zallan Zinare.
Wannan Kambinsa ne dake faɗar ma duk wanda ya gansa Gaba,Basai an faɗa maka wanene ke tafe da tawagarsa ba daka hango walƙiyar kan zakin dake wulwulawa asamar farin motarsa kasan YARIMA ABBAD ne.

Sharara gudu suke tamkar basu shigo titin unguwa da zai sadaka da tangamemen Masarautar ba,wannan yasa duk wani mahalukin dake son tsira da mutuncinsa yake kaucewa .

Haka suka dangana har tsakiyar Fadan Bayin ƙofa na tale gets suna zubewa a wajen har suka shige tsakiyar rungujejen fadar maɗaukaki ,mai ƙunshe da tarin bayi maza da mata cikin uniform iri ɗaya ,Daf da ƙofar ɗakin Mai babbar ɗaki motarsa ta tsaya a yayinda sauran motocin bodyguards ɗinsa suka kwalmaɗa zuwa parking lot.

ATHEELAH budurwar Yarima Abbad ko ince matarsa da ake dab da aure ,fitowar ta kenan cikin kwalliya da fararen sutura na Alfarma ,gefenta surukuwarta ne ,wato mahaifiyar Yarima zata rakata gaban farar motarta da tazo a ciki ,tana ganin motocin yariman sun shigo ,shaukin ta ya karu fara'arta ya kasa ɓuya ta fara washe haƙura kamar wacce akayiwa bushara da Aljannah ,taja ta toge a gefen mamansa tana jiran fitowar Prince daga mota.


Motarshi na tsayawa ,drivernsa da ya kasance Amintaccensa ,ya fito da gudu ya ɗauko jan carpet ya malala tun daga farkon ƙofar motar har gaban ƙofar ɗakin mamansa

Sarkin busa kuwa tuni ya fara busa mabushinsa ,don Ankarar da duk wani mai lunfashi dawowar yarima. Tuni kowa ya soma kamewa a inda yake gwuiwoyinsa a ƙasa ,wannan Dokan yarima ne ko kana kan toilet ne yazo waje dole ka sunkuya ka dinga masa kirari daga inda kake, har sai yakai inda zai kai ya zauna sannan kowa zai kama gabansa .

Ƙiftawa da bissmillah kowani mai numfashi na gidan ka ganshi hululu a ƙasa ana jiran fitowar Yarima... Sarkin Busa yana ganin yarima ya sawo ƙafa ya tsaya akan jar carpet din digrigir ,ya ruga da gudu yaje ya sunkuya yana zuba masa kirari .

“Allah yaja da ran yariman dudduniya ,ɗan sarki kake jikan sarki takawan ka lafiya gwamnan gobe da ikon mai duka”

Shaƙan wani iska mai kauri yayi tamkar Oxygen ɗinsa ne ya siya a karti ,kana ya ɗage kai yana kallon kowani bil'adama Dake rusune a lungu da saƙo na gidan ,yanajin kansa na sake gingiringin ,babu wanda yake a tsaye akan ƙafafunsa daga mamansa ,sai ATHEELAH ,Budurwarsa.

Sarkin Magana na ƙare zuba kirarinsa ,sauran ɗaukacin bayin gidan suka fara rigerigen gaishesa murya a tare da alamu ma sun hardace kirarin da aka saba yin masa tamkar National Anthem

Yanda suke Zabga masa kirari yasa mamansa ,budurwarsa dashi kansa ɗan murmusawa kana ya fara Takowa cike da ƙasaita .

A guje ATHEELAH ta taho inda yake tana buɗe hannu alamun zata rungume shine.

Da sauri ya ɗaga mata er matsakaicin kambin girmansa mai kwalliyar gold. Wannan ya sata ja ta tsaya
“Keeee!🙄”

Ya doka mata wani wawan tsawa da ya sa hanjin cikinta hautsinawa ,taja burki ta tsaya
Cikin Muryar ɗagawa da fizgar rai ya soma mata magana
“Me ya hanaki rissinawa ki gaisheni kamar saura?.....

Das gabanta ya fadi ,bai duba halin da take ciki ba ya cigaba da cewa

“Anya kina da tarbiyya....? Anya ke cikakkiyar ɗiyar Ahalinku ce kuwa?”

Rassss ,ƙirjinta ya cigaba da bugawa ,a furgice ta ɗago ido tana kallonsa

“Anya ba Alamar fitsara a ƙwarar idonki?..” da gudu ta rausayar da ƙwarar idon ta ƙasa

Daka mata tsawa tayi wanda yafi na farko tada hankali

“Bani Amsa!!!!”
Jikinta rawa ya fara yi ,kar kar kar .
Da sauri mai babbar Ɗaki ta kwatse shi amma cikin laushin murya.

“Haba Yarima Take it easy ,matarka ce fa da zaka aura”

“Wife to be You said mama,she's yet tobe ” (Matar da zan aura kikace mama amma ba Matana bace a yanzu)

Dawo da kallonsa yayi kan ATHEELAH
“Ke kuma ,zoki rissina a gabana ki sumbaci yatsotsin ƙafana”

Ba ATHEELAH ba ,harta bayin gidan saida suka firgita ,amma kawai sai mai babbar ɗaki ta hankaɗe kafada irin ko a jikina ɗin nan

Tana ji tana gani ta matsa gabansa ta sunkuya ta ɗaura kyawawan tafukan hannunta a ƙasa ,ta kai laɓɓanta saman rufaffen takalminsa sau ciki ,ta yi kissing takalmin nasa .

Sautin kiss dinta na dokan kunnen sa ya saki wani ajiyar rai yaja numfashi sama gami da miƙar da kansa ya kalli sararin samaniya kana ya kalli ƙasan inda take turmushe ta kasa ɗagowa saboda yanda tana kissing takalmin wani kuka mai ciwo ya turniƙe mata maƙoshi .

Tsawa ya daka mata irin na rainaswa da wawantarwa

“Tashi ki bamu waje ....sha....sha.....sha!!”

Haka kikaji sautin muryarsa a yayin zaginta da shashasha yana amsa kuwwa a ilahirin gidan.....lallai ran en maza ya ɓaci.

Da gudu ta mike ta falla da gudu wajen motarta ta buɗe motar ta shige ta zauna ta daura kanta akan kambin motar ta goce da kuka.

Tana barin gabansa ya wani washe baki kamar bai taɓa fushi ba a duniya,ya buɗe hannunsa ya taka ya rungume mamansa

“Oyoyo my love Na sameku lpy”

“Lafiya lau Yarima na,Mu shiga daga ciki” suka rankaya ɗaki.
Saida suka bace sannan kowa ya mike ,masu mota suka shiga suka mata key ,itama sai sannan ta kunna motarta ta fice a karce ,tana jin ranta kamar zai tsalle ya fice waje.
*_BAD BOYS_*


Na...
Oum Aphnan🌸

Tsokaci
Idan kiɗin ya sauya rawar ma dole ta sauya,Now we're talking about House wives😍Kowa na cewa matan aure sunfi en mata baɗala!! Wai haka ne?? Amma Ni oum Aphnan nace Life style Matters.

Hello Guys it's me Again Oum Aphnan ,your amazing writer da ta saba fiddo maku da hazikan books ɗin ta masu tsayawa a zuciya I'm here with New Legitimately good Erotic Novel ,that I know you must read!!!!

A wannan Labarin na fiddo muku zafafan Jarumai Irinsu...
*NASEEBA* Ta kasance Uwar Adashe, cikakkiyar matan Gida,Ƙazamiya ce ita ,bata kula da gidanta bare mijinta ,Amma fa Vendor ce,business woman awwwn😃🤌 Akwai tarin barkwanci a Episode ɗin NASEEBAH da mijinta...Yaya tafiyar zata kasance ne?Gsky ina don scene dinki 🥰

Next Episode will be on
*NURSE KHAIREE* Kyakyawar Budurwa ma'aikaciyar Gwamnati,very smart hard working Young metron,Dake aiki ƙarƙashin Arrogant Neurosurgeon Doctor (Likitar ƙwaƙwalwa)wata wainar ake soyawa? Allah yasa kowa yasan rikicin Doctors/Nurses wato clinical bias🤦‍♀️🙆‍♀️Hmmm ,Muje zuwa.

Duka dai a cikin littafin BAD BOYS zamuji Episode ɗin Saleemah...Tantantantan *SAYYADA SALEEMA🤣* Ke daga jin sunan kinsan akwai ƙura.
Matar Sheikh ne ,Ƙasurgumin malami da yayi shura a Nigeria ya tara tarin dukiya ,duk shekara yana aika tarin Al'ummah Saudiyya aikin Umrah da Hajj. Duk wani taron manyan malamai da zaayi Yaa Sheikh sune kan gaba....amma fa ya Sheikh mugune🤔🤪 Akwai kulle baya barin fita unguwa ,ba...ba...ba yayi yawa a gidan nan? Mai zai faru da sayyada saleemah?😁da take zargin mijinta da aikin riya( Badon Allah ba sai don mutane su yabeshi?)

Plz A gyara zama a karkaɗe zani,Littafine mai dogon zango ,ƙawayena ,Hajiyoyina Ko kina missing littafina Karki yarda baki karanta Littafin nan ba,akwai cakwakiya ,Nishadi da madarar soyayya a ciki....and above all Oza room part😉awwwwn bara in rage murya Littafin matan aurene ,Na kusa ɗakin Oga


Zaki iya biyan kudin littafinki ta ɗaya daga cikin wannan Hanyoyin
FCMB BANK
7782217014
MOHAMMED HASSANA

KO KATIN MTN
TA WANNAN NUMBER
09065990265

Littafi Cikin sassauƙar Farashi
Regular 500₦
VIP 1000₦
SPECIAL ₦2000


Don't Forget Oum Aphnan ɗinku ce da ta Kawo maku Littatafan ta kamar

GIDAN DAƊI
YARON GIDANA
HARIJI
JARABABBEN NAMIJI
QASAITATTUN MATA
INDO MAƘATA
AKAN DADIRONA
BARIKI GADONA
RAMUWAR GAYYA
LAYLERH
BAGIDAJIYA
BANANA ISLAND
SUGAR MUMMIES
GWAURO
ABU UKU 🤫

Mai wa'innan Littafan ne dai da sauran ma wanda ban fada ba,zata dawo maku da Wannan sabon Littafin mai suna *BAD BOYS*....Hajiya karki sake ayi tafiyar babu ke ,Rush and be the first to Grab your copy
Thnk you all🤍Oum Aphnan
09065990265
*_🐹BAD BOYS🐹_*
By...
Oum Aphnan

003
___________________
Sayyadah
Washekari da sassafe kafin Salima ta farka daga barci ma har Ya Sheikh ya dangana da dinning ,Fridge din...


Read / Download BAD BOYS

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
1 Comments On BAD BOYS
avatar
fatima-muhammad-1-4

4 months ago

Reply

So sweet

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album