Join Our WhatsApp Group

QADDARATA Complete Hausa Novel Document by QADDARATA


QADDARATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 54292



QADDARATA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 11, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 307.77 kb

File Type: txt

Views: 690+

Download: 257+

Last download: 3 days ago

Description/Story: Qaddarata S3 na Yar Mutan Kankia



_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


_Allah sarki buwayi gagara misali godiya ta tabbata agareka ya ubangijin talikai Allah kayi tsira ga fiyayyen halitta annabi Muhammad da iyalansa sahabban sa baki daya,ameen._


```Tom jama'a kunsan ance rayuwa cike take da kalubale da kuma QADDARARORI Kala Kala, ko wani bawa da tashi qaddarar maikyau da akashin haka, cikaken musulmi shine yayi imani da qaddara maikyau da marar kyau shine cikan imani, to haka rayuwar Amina charanci take kunji yanda labarinta ya kasance tun daga ALKALAMI SEASON ONE kukaji BAKIN JININA YA JAMAN SEASON TWO to gamu a cikin QADDARATA SEASON THREE kenan, sae ku cigaba da biyoni ni YAR'MUTAN KANKIA dan jin yanda Qaddarar Minal charanci zai ta kasance😢, Allah ya bamu ikon yarda da qaddara Amin👏```


```Note kuyi hakuri masu yi man magana ta private da masu comment banda lokaci Ina busy ga karatu shiyasa ban cika baku ansa ba kuma inajin dadin comment din sosae a cigaba da yi hakan na sani nishadi sosae```

*Ya Allah nagode maka da kabani ikon rubuta littafin nan yau 27/9/2021 cikin koshin lafiya da kuma cikin aminci kayafe mana kurakuren dake ciki🙏.*


_NO EDITING_


S3/E1&2




*******Ita rayuwa da kuke gani kowa da tasa Qaddarar,kuma ba yanda bata zoma ɗan Adam saidai ba kowa ke cin jarabawar da ubangiji ya daura masa ba,ni kuma haka tawa Qaddarar tazo mani ban shiryaba,batareda na fargaba,hawayen idanuna kullin suna kwaranya a idanuna idai bansan dadin rayuwa ba,narasa komai nawa,idan nace komai ina nufin farin ciki.

Farin ciki shine cikar kowane burina na Adam arayuwa saidai QADDARATA ta nisantani da duk wani farin cikina!.....

Amina Caranci kenan wadda duniya tai mata daurin goro rayuwa tai tsanani agareta komai ya rikici mata da tarin danasi,kunci,tashin hankali,fargaba,da kidima duk wadan abubuwan su suka taka rawa a cikin Qaddarar ta!


******_CIGABAN LABARI_



Allah mai kowa mai komai shike tsara komi a yanda yaso kuma sadda yaga dama,yau nice cikida farin ciki na anshi Certificate dina na Medicine nagama da sakamako mai kyau,harnayi Intership a sabitin Murtala dake kwaryar birnin Kanon Dabo.

Ina gamawa nahau shirin tafiya NYSC dina a ENUGU can nayi Camp dina na kusan tsawon wata daya daga can nayi relocation zuwa gida Katsina a FMC nasamu nayishi nasamu alkhairi a tsakanin Intership dina Dda NYSC dina,a haka nagama alhmdullh na samu Expriences sosai,yanzun aiki nike nema gadan gadan cikin ikon Allah.


Koda nadawo gida dan zaman da nayi gidan mu banda wata damuwa,musamman wajen mahaifina yana ciki gaba da bani duk wata kulawa daya kamaya uba yaba ya'yan sa hakama Mama tana iya bakin kokarin ta akaina.


Bayan kwana biyu ina zaune tsakar gidan mu ba lula a cikin nazarin rayuwa da yanda take zuwar mani in yau da dadi gobe sai ahankali,wayar hannuna ce ta hau ruri da ido nabi Screen wayar dake hannuna Iphone7 sunan Abdallah ya bayyana.

Fuskata dauke da murmushi na ɗaga wayar cikeda da zolaya nace.
Angon karni anata jiran tsammani ya aminiyar tawa."

Murmushi yayi mai sauti yace.
Amaryar kamshi barkan mu da arziki ansamu baby girl."
Wani uban tsalle na daka da hamdala abakina har saida Baba ya fito jin karata yana lfy.

Amsa ban iya bashi ba tsabar dadi,da kyal na tattaro natsuwa ta nayi kan Baba bansan na rungume shiba nace.

"Husna ta haihu Baba."
Masha Allah,eyeh su Mamana an zama manya wannan murna har haka barka Allah ya raya."

Sai lokacin na sunkuyar dakaina inajin nauyin mahaifin nawa bisa labbana nace ameen.

Ina shigewa dakina,lalubo number Fatash nayi duk da munrabu da gaisawa da ita zuwa yanzun alakarmu tai sanyi hatta Ya Hussein shima munja baya da juna duk da son shi ba abinda ya sauya a cikin zuciya ta saidai abinda nasani Qaddara itace ta raba tsakanin mu.

Dagawa tayi murya kasa kasa kamar mai kuka ko bacci,bandamu sa yanayin taba nagaya mata sakon Husna ta haihu.

Itama tayi murna,nan muka gaisa sama sama na kashe wayata duk da zuciya ta nasan ta tambaye ta Ya Taufiq amman bakina ya gaza tambayar ta har mukai sallama na yanke wayar.


Bayan kwana biyu muka shirya harda mama da Antyn su Asma'u da yan uwa sai gidan Asma'u mukai mata barka ranar farin cikin da muka shiga bai misaltuwa tunda naje narike baby sai da gaske nike badata a dauka,tinda nai tozali da jinin Husna sai Allah ya jarabceni da kaunar yarinyar har cikin zuciya ta sai nike ganin kamar kaunar da nikema Husna ne ya dawo kan yarinyar.


Ranar haka muka wuni har la'asar sannan muka nufo gida Caranci.


_*Noted:-Kafin inci gaba da wannan labarin inasan in sanar daku labarin Qaddara ta,akwai Fiction musamman inda aka tabo Taufiq,shima ba dukaba rabi da kwata is true saidai kadanne fiction,amman duk abinda ya shafi Amina ba fiction a ciki duk true ne hope kungane nufina,infact duk page din dakeda fiction zan sanar daku nagode*_


Ranar Monday ina zaune a falo ina kallon film din Tarkon Kauna na tashar arewa24 nida kannena hankalin mu kwance,wayana ta hau ringing,dauka nayi ina dubawa saidai new number ne kamar ba zan dagaba sai kuma na dauka,da sallama abakina.

Doctor Amina Yusuf Caranci ce online.?"
Yes am the one."
Okay gobe kizo asibiti interview FMC Katsina kizo da wuri."


Wani irin farin cikine ya lulube mani kasan zuciya ta,alhmdullh na iya furtawa.

Allah yakaimu lafiya.
Dakin mama nafada sai farin ciki nikeyi,kallo ɗaya Mama taimin tagane tsantsar farin cikin da nike ciki.

Wane albishir din ne aka zomani dashi Aminatu.?"
Rungumeta nayi nace.
Mama FMC sun nemeni gobe inje interview."

"Kai masha Allahu, gaskia bansan da wane baki zan fara godema Allah SWT ba saidai muyima Annabi Salati Allah yasa albarka ya kaimu lafiya,amman duka duka yaushe kikai CV dinki.?"

Wlh Mama nima nai mamaki kamar dai jira,amman nayi farin ciki,sosai."

Allah abin godiya duk daba abin mamaki bane,aishi Allah ba yanda baima bawan sa kyauta ta inda baiyi zatoba,kinga Allah yai maki gata da rabon ki gama karatu gashi har kinsamu babban rabo Allah yasa albarka."

Ameen Mamana tafi takowa.
Nikam nakasa zaune nakasa tsaye dan murna,fatana Baba ya dawo insanar mashi abin alkhairin daya sameni.


Koda Baba ya dawo anyi sallar isha'i yana gama cin abinci yafara kallan NTA News,da sallama bakina na shigo cikin falon shi.

Maido kallan shi yayi kaina shima murmushi yaimani mai nuna tsantsar so da kauna dake tsakanin ɗa da mahaifi.

Daganin bakin Mamana akwai magana a cikin shi,mike tafe da Mamana.?"
Sadda kaina nayi kasa saidai inata smile.
"Baba FMC sunkira Interview."

Alhmdullh Allah abin godiya Allah yasa albarka ya'ta gaskia bansan irin farin cikin da nikejiba a raina,Congratulation Mamana."

Thank you Sir am proud of you Babana."
Dariya yayi yanajin dadi,cigaba da yimani bayanj yayi akan aiki da rikon amana da kula da patient da duk sauran abubuwan daya kamata ki rike akan aikin ki.


Haka dai yaita yimani nasihohi har zuwa tara nakoma dakina,waya na dago da niyar ingayama Ya Taufiq sai kuma nafasa ganin dare yayi,nabari saida safe kafin in sanar mashi.


Washe gari da safe tunda wuri naje fcm duk abinda yaka mata anmani kuma duk na tsalleki komai succesful ,congratulation akaimani nadawo gida zuwa upper week zanci gaba da aikina,haka na dawo gida cikin aminci mai tarin yawa.

Da yamma kiran Husna nayi na shaida mata nasamu aiki,tatayani murna sosai,har Abdallah saida yatayani murna.

Inagamawa nakira Ya Taufiq kira na ukku ya daga cikin sanyayar muryar shi mai sakani sukuni dajin dadin.

"Princes how are you kin gujeni ko Minal.?"
Sihirtattar ajiyar zuciya na sauke kamar bansan magana nace.

"Aaa kana raina Ya Taufiq,albishirin ka.?"
Goro."
Fari ko ja.?"
Fari kyal mai kyakkyawar aniya kamar ki."

Nasamu aiki."
Alhmdullh ina kika samu aiki .?"
Fcm ne,department of Theater&Surgery."
"Amman natayaki murna Congratulation my cute baby."
Thank you so much my hope."
Murmushi yayi,muka taba fira kadan da haka mukayi sallama ina cikin farin ciki marar misaltuwa.


********Bayan kwana ukku,muka shirya zuwa sunan Husna,kaya na musamman na shiryama Baby da maijego saida nayi akwai guda na kaya,sannan nai mana kala Ukku anko nida Asma'u,shadda Lace,sai atamfa super mai masifar kyau,nida kanwarta muka tafi daren sunan.

muna zuwa mukahau preparation abinda za'aci na sunan,dayake nida Abdallah kusan kullin muna waya aikin mu mi za'aci tun kan inzo duk abinda ya kamaya nasa anware ankai aikin shi,abinda ya rage kadan ne,muna gamawa aka gau yimana lalle(Henna)
ranar wuni mukai muna fira nida Husna zan icewa kusan daren a zaune mukayi shi.

Washe gari da safe kuwa aka radama yarinya suna Aminatu,duk da suna mahaifiyar Abdallah kenan amman kusan ni akaima takwara,domin kuwa ko dangin shi da sukazo kowa cewa yake ina takwarar take sai anunani ana aikuwa sunyi kama da babyn.

Kowa dai yanata zolayata dadi kam wajena bai faduwa,yan caranci duk sunzo suna yan uwa da abokan arziki anci ansha masha Allah.

Kusan kaya iri daya muke sawa nida Asma'u da wanda nayo mana sai wanda taimana guda biyu iri daya,kayan da basuyi iri daya ba bai wuce kala biyu amman komai tare mukeyi gwanin burgewa,bakataba cewa Asma'u ba cikinmu daya ba,dan ta zame mani yar uwata ta jini,bakaramin shakuwa ke tsakanin muba saiya zama yanzun datai aure munfi da shakuwa da junan mu.


Ina zaune kusa da Asma'u sai Rukayya anata pictures din suna ina rike da Amina anata hotuna wayar Husna tai ringing Ahmad Idris (A.I.D) ya bayyana jikin screen din wayar,duk da kaina bai hakaito komai ba hakanan naji gabana yadan fadi kadan dagawa tayi tana Dr barka da yamma."

Yawwa mai jego gani a kofat gidan yanzun na iso."
Okay bari Minal ta shigo dakai."
Kallan tuhuma nike mata.

Dr Ahmad ne dan Allah ki shigo dashi falon Abdul."

Kallan bakida aikin yi nai mata.
Kamar ya waye shidin malama ban zuwa."
Hmm wato kedai Amina bakida kirki Allah shikenan bari mai gidan ya shigo dashi.

Uhmm kawai nace mata naci gaba da sabgogin gabana.

Bada jimawa ba,Hauwa'u ta shigo dakin da muke.
"Antyn wai Yaya yace ace maki bakon yana falon shi...toh shine abinda Husna ta amsa ta,mike tana miko mani Minah.

Tashi muje sai akawo mashi drinks ko.?"
Ke wlh ban zuwa waike wace irice kinyi bako baku fara gaisawa ba kawai sai in kwashi kafa inbiki,kije in kun jima ko lemo kila yasamu arzikin shi wajena.!"


Ohni Asma'u yau mi tawan kejine wannan ruwan rashin kirki Allah ya shiryeki Minal."

Ameen saidai ya kara dan ashirye nike."
Hmm kedai kikasani,taja gyalenta tayi falon Abdallah.

Nikam chart nike na saki posting din pic din suna sai viewing akeyi ana comment.

Masu Woow masha Allah nayi masu Allah yaima baby albaka nayi kowa da abinda yake cewa.

Thank you all narubuta nayi posting saboda DM din dayawa.

Zansauka kenan naga comment Ya Taufiq,hannuna na kyarma na bude.

"U re the best among the stars my Queen tauraruwar mata,i miss u tawan,Allah yaraya little Minal."

Wata siririyar ajiyar zuciya na sauke ina smile a fuskana.

"Thank you my king u re the hero handsome miss u too."

Emojis ya turomani na tsantsar jin dadi haka mukaci gaba da chat cikeda tsantsar kaunar junan mu datarin kewae juna,kiran Abdallah ya shigo wayana hakan yasa na sauka online ina dagawa...


"Angon jego."
Kizo falona kuma kitaho da drinks."
Okay,nace tashi nayi na dauki tray ina daura 5alive akai sai ruwan roba,samun dan karamin flat nayi na zuba snacks a ciki na tafi falon Abdallah.

Da sallama baki ina hankalina kwance kaina na kasa,amsa mani sallamar akayi take naji mummunan faduwar gaba ya dira a cikin zuciya ta,jin muryan daya daki dodon kunnena,a sanyaye na dago kaina na aza bisa fuskar.......




_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls
❣️

_*QADDARATA!🙆🏻‍♀️*_


*NA*


_YAR MUTAN KANKIA❣️_


_*MANAZARTA WRITER'S ASSOC*_


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_


S3/E3&4



Dr Ahmad,wanda ya kafeni da idanun sa ko alamun keftawa baiyi,nima shi nike kallo daga bisani na sauke kaina kasa harna isa wajen shi,bisa center table na aje tire din, ina barsarwa kamar ba wani shock da jikina yayi dan kuwa wani irin nauyin shine ya rufeni tuno rashin mutucin da nai mashi harda barazanar kisa,zama nayi na maida kallona kanshi.

"Dr Ahmad how are you.?"
Am fine ,nice to see you again Aminatu."
Thanks.
Nace ina maida kallona bisa screen din wayata
Shiru ya kaure falon Abdallah ke cewa.
"Honey muji su gaisa ko.?"

Ya mike yana kama hannun Asma'u,nima tashin nayi zan bisu don banga anfanin gaisawar da zamuyiba tunda ba wata alaka a tsakanin mu.
Ki tsaya ku gaisa ina kuma zaki.?"
Kallan mamaki nikebin Abdallah dashi wanda yai maganar yaba hade fuska irin umurni yake bani,bude baki nayi zan mashi musu sai kuma na kasa sakamakon kallan daya sake jifana dashi sai yai mani kwarjini sosai dan dole na koma na zauna,suka fita tareda matar sa.
Shiru ya kaure wajen kowa da abinda yake sakawa.

"Gimbiya ta,nayi missing dinki ban tunanin zan daina daunar ki Aminatu bare in cireki a raina,ina sonki.!"
A raunani ya ida zancen nashi.

Wani kallan up and down nai mashi batare da raini ba, kawai ina mamakin karfin hali irin na Ahmad kaida akace ba'asonka har iyayen ka suka janye zancen auren daya shiga tsakanin mu,taya zaka dawo da wani labarin kuma.

"Nagode nima ina maka fatan alkhairi."
Numfashi mai zafi ya fesar yana dafe kanshi yace.

"Nasan baki sona Amina amman ni ina kaunarki har gaba da abada dan haka bazan maki tilas ba saidai inaso kibani dama ta biyu,mu dinga waya dan Allah."

Batareda naji komai araina ba nace.
Aaa Ahmad kayi hakuri bansan abun daya wuce ya dawo agareni son daka nuna mani ya watadar,na gode maka."
Shiru yayi yana nazari ya kuma cewa.

"Ina neman wannan alfarmar dan Allah Amina ki bari koba kullin ba muna gaisawa sannan dan Allah kitai maka mani idan kina bukatar wani taimako,awajena ko wane irine kofa abude take Amina inasan naga na kyautata maki ko yayane wala da kudina,lokacina ko kuma da karfina,na rokeki kada kice Aaa."

Shiru nayi narasa mi zancema Ahmad nidai Allah yasani bawai na tsane shi bane bansan alaka ta sake hadamu dashi gudun abinda zaije ya dawo,nidai bansan ya zanyi da lamarin nan ba.

Waving face dina yayi na shiga tunani,dawo da kallona nayi kanshi ganin yanata begging dina ya hade hannayen sa alamun roko,hakanan naji wani irin tausayin shi,ya kamani araina.

Shikenan na amince nima inafatan idan kana bukatar taimako kaimin magana matsawar baifi karfina ba zan maka."

Murmushi ya saki mai nuna tsantsar jin dadin shi.
"Inaida alfarma awajenki da yawa gimbiya ta kinsani ni mai barane agareki."
Uhmmm minene fada in maka idan inada hali."

Kina dashi da izinin Allah,inasan ki kasance dani akoda yaushe,ma'ana ki dinga daukar kirani kullin safe da dare ina gaisheki."
Rasa abin cewa nayi saidai jinjina kaina da nayi alamun gamsuwa.

Godiya yai mani muka hau fira kadan kadan."
"Na dauka kinyi aure Amina na shiga rudani da tsananin tashin hankali saidai Asma'u ta tabbatar mani baki aure ba sannan nasamu sukuni araina."

Hmmm aikuwa banba amman na kusa yi insha Allah,Amman kai kayi auren ko.?"
Aaa wlh banba ina nan dai."
Allah yakawo ta kwarai.
Bai amsani ba,duk mukai shiru kowa yana tunani aran shi,mikewa nayi.

"Zan shiga ciki inatayin baki nagode da karamci."
Shima mikewar yayi yace.
"Ameen gimbiyata nikeda godiya da wannan tsadaddan time din da aka bani."
Never mind .
Fita nayi na shiga side din Asma'u mukaci gaba da hidima nan aka hau kidin kwarya,sai biyar na yamma yan Caranci suka fara azamar tafiya harda su Mama dagani sai kanwar Asma'u da Antyn su sai Yayar...


Read / Download QADDARATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album