Join Our WhatsApp Group

FARIN CIKI SAU DAYA Complete Hausa Novel Document by FARIN CIKI SAU DAYA


FARIN CIKI SAU DAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22715



FARIN CIKI SAU DAYA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 117.58 kb

File Type: txt

Views: 579+

Download: 206+

Last download: 4 hours ago

Description/Story: %%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 1
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
.
SHIMFIDA
Ilham bata san yau ne ranar da mijinta Ma'aruf zai bar duniya ba."
.
Sun tashi barci lfy kamar kullum. Ya je masallaci ya yi sallar asubahi yana dawowa sai ta ga ya dauko jakarshi ya fara xuba takardunshi na aiki yana sauri. Tun kafin ta tambayeshi inda yake shirin tafiya, ya fada mata cewar yana so ne zai koma Katsina inda yake aiki.
.
"Ba jiya ka dawo ba, ko ka mance ne yau fa asabar, sai jibi litinin zaka koma da safe."
.
Ma'aruf ya dakatar da matarsa Ilham ba tare da ya juyo ya kalleta ba."
.
"Manaja ne ya kira ni a waya ynxn nan wai wani aikin gaggawa ya taso. ya ce in yi sauri in koma Katsina yana son gani na."
.
Ilham ta 6ata ranta, sbd lkc-lkc irin wannan aikin gaggawar ya kan taso wanda yake sa mijinta Ma'aruf ya tsallake ya barsu a gida ya koma Katsina inda yake aiki a hukumar wutar lantarki ta qasa. Yana sashin gudanarwa ne a hukumar matsayin muqaddashin manajan shiyyar cikin birni. A duk sati ya kan yi kwana hudu a Katsina, sannan sai ya dawo Malumfashi inda gidan sa yake....inda iyalinsa suke. Matarsa Ilham da 'ya'yansu biyu Khairat da Aiman yayi kwana uku tare dasu.
.
Wadannan kwanaki uku da Ma'aruf yake dawowa gida ya yi tare da iyalinsa' sune ranakun so a wajen Ilham
.
Juma'a....Asabar.....lahadi..... Sau da yawa ta kan yi fatan xuwan qarshen mako.
.
"Don Allah juma'a ki yi sauri ki zo."
.
Sbd a ranar ne mijinta Ma'aruf yake dawowa gida ya same su, suyi ta murna da tsalle ita da 'ya'yansu. Duk sanda zai koma a ranar litinin da safe sai kuma duk farin cikin su ya koma su shiga damuwa.
.
"Dan Allah litinin kada ki zo."
.
Idan zai tafi sai ta kamo hannun Khairat babbar 'yarsu, wacce ke da shekaru hudu, sannan ta dauki Aiman a kafadarta su hadu su duka su rako Abba kamar yadda 'ya'yanta suke kiran mahaifinsu. Har xuwa inda yake ajiye motarsa a harabar gidan
.
"Ku cewa Abbanku sai ya dawo."
.
A lkcn ne Ma'aruf zai kamasu daya bayan daya ya daukesu, yana yi masu wasan rarrashi da maganganu don kada suyi kuka idan sun ga ya shiga mota ya tafi.
.
Ilham ba zata iya jurewa ba yau da wannan tafiyar gaggawa da ta tasowa Ma'aruf mijinta. sbd tayi zaton a wannan makon zai zauna tare dasu ya yi kwana ukun da ya saba yi. Ya koma ranar litinin da safe. Bata yi zaton zai koma yau da sauri haka ba daga kawai yayi kwana daya.
.
Ma'aruf ya gama shirya takardunsa da yake buqata a cikin jakarsa. Ilham tana tsaye tana kallonsa. Ya gama daukar komai har da mabudin motarsa ya juya ya dubeta a lkcn da ya dauki jakar zai fita.
.
Bai sa rai yau zata iya yi masa murmushi ko kuma ta dauki jakarsa ta kama hannunsa suyi bankwana ba." bai sa ran yau zata iya rakashi har inda motarsa take ba a can waje...kusa da qofar shigowa gidan...bai sa rai yau zasu rabu yana dariya tana dariya ba." sbd ya san in har bata son su rabu to bata da qwarin guiwar da zata iya jurewa ta saki jikinta ta bar abin a xuciyarta.
.
Ya san idan ya tafi a nan zai barta a dakinsa....ko kuma ta fita falo ta zauna ta yi tagumi. Ko ta fita can bayan harabar gidan inda suke da shuke-shuke tayi zamanta akan kujera. Yau Ilham wunin zata yi a cikin damuwa, don kuwa bata yi zaton wannan tafiya ta gaggawatunda sassafe zata bijirowa Ma'aruf ba."
.
Bayan ya fuskanceta sai ya ce da ita.
.
"ki yi haquri Maman Aiman, duk da ban san me yasa manaja ya ce in je in same shi ba, ina sa ran ba wani aiki bane mai wahala da zai daukemu wani dogon lkc. Anjima da yamma zzan dawo inshaa Allah. Bai fi in yi awa biyar a can ba."
.
Ma'aruf yayi dariya ganin yadda Ilham ta 6ata ranta bata so ya tafi....bata so su rabu. Sbd qaqqarfar soyayya da shaquwar dake a tsakaninsu. Ilham bata ce masa komaI ba." idan ta ce masa bata damu ba tayi qarya.
.
Ma'aruf ya juya ya tafi, ya fita ya barta cikin sauri har ya je inda motarsa take Ilham tana nan a daki bata motsa ba." tana tunanin sai yaushe Ma'aruf zai mayar dasu Katsina tare da 'ya'yanta su zauna a can ya daina xuwa yana dawowa?
.
Sai da ya shiga motar ya tayar da ita. Sannan ta fita waje ta tsaya a bakin qofar tana kallonshi. A lkcn ne Khairat ta fito daga dakin barci tana kiran mahaifiyarta Ilham
.
Ta kunno kanta waje ta kama jikin mahaifiyarta, suka qurawa Ma'aruf ido, a lkcn ne shima ya juyo ya kallesu yana a cikin motar. Ya daga masu hannu. Ilham ta dan saki ranta kadan, 'yarta Khairat ta dagawa mahaifinta hannu tana sanye da rigar barci fara, kanta zane da kitson (Calabar)
.
Su duka biyun suka taru suna kallon mutumin da ba zasu sake zama tare dashi ba daga wannan ranar...kamar yadda shima ba zzai sake ganinsu ba...ba zai sake zama tare dasu ba har bada.....
.
.
.
Lp=2%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 2
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn Ishak
(madun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Kamar yadda shima ba zai sake zama tare dasu ba har abada.
.
Ilham ba ta ce da mijinta Ma'aruf ya sauka lfy ba kuma bata tambayeshi abin da ta san suna buqata ba a gidan kafin ya dawo, ba don bata yi masa ladabi ba." sai don kawai tana so ta riqa nuna masa damuwarta qarara a Kodayaushe na barin su da yayi a garin baya zama Kullum. Me zai hana shi ya mayar dasu Katsina, tunda dama can ne garin su?
.
Bayan zaman aure, ta san zata zauna a kusa da 'yan uwanta....qawayenta da kuma 'yan uwan mahaifinta. Sbd a can aka haifeta.
.
Ma'aruf bai damu ba ya tuqa motarsa ya fita daga gidan ya hau titi. Yana sa ran zai dawo, bai san cewar har abada ba zai sake dawowa gidan sa ba." Ilham ta kama hannun 'yarta khairat ta janyeta suka koma cikin gida. Da shigarsu ta saki ranta kamar babu abin da yake damunta. Ba da 'ya'yanta take fushi ba, da mahaifinsu take fushi. Ma'aruf ne yayi mata laifi gashi kuma ya tafi. Ba ta san abin da zai faru ba shi yasa bata tsare shi sun yi magana ba...ba su yiwa juna bankwana ko da kallon qarshe ta yi masa ba." Ilham ba ta san cewar yau ne ranar da mijinta Ma'aruf zai bar duniya ba."
.
.
.
*** ***
.
A haka ya kama hanya yana tuqi yana tunanin rayuwa shi kadai a cikin motarsa. Lkc ya yi da ya kamata ya dauke iyalinsa su koma Katsina don hankalinsa ya kwanta. Bai ta6a ganin laifin matarsa Ilham ba akan damuwar da take nunawa idan zai tafi ya barsu ba." ya san irin zuzzurfar soyayyar soyayyar da ke tsakanin su." musamman idan suna zaune tare da 'ya'yansu biyu suna kira a falo ko kuma idan suna cin abinci.
.
Khairat tana xubo surutu cikin gwarancinta suna yi mata dariya. Ko kuma idan Aiman yana qoqarin jawo wani abu suna kai hannu suna hana shi.
.
Ma'aruf ya yi nisa a tafiyarsa, ya wuce Mai gora. Ba a jima ba ya zo ya wuce Dayi. Ya wuce marabar Musawa kafin ya kai Jiqamshi ne yazo daidai wani qaramin qauye wanda yake da qarancin mutane a gefen titi ya iske wata doguwar motar jigilar man fetur ta lalace a tsakiyar titin, ta kashe rabin titin baki daya dole sai wata motar ta tsaya sannan idan wasu sun zo su ke wucewa.
.
Ma'aruf bai lura da babbar motar ba sai da ya qurace ta, ya dago kai ya kalleta kamar an jefo masa ita. Ya yi saurin taka burki a lkc guda. Har sai da tayoyin motar suka yi kuwwa a titi. Kafin ya samu nasarar tsayar da motar ne, ta cimma bayan doguwar motar tankin. Ma'aruf ya yi salati a tsorace sanda motarsa ta cusa kanta a bayan babbar motar, ta tarwatse hade da wata qara mai furgitarwa. Abin da Ma'aruf kawai zai iya tunawa kenan, amma sauran abin da ya biyo baya bai sani ba."
.
Ya dai farfado ya samu kanshi kwance a wani fili kusa da ciyayin dake a bakin titin, mutane sun zagaye shi sai surutai suke yi kowa yana fadar albarkacin bakin sa cikin jimami da tausayawa da kuma tsoro. Wani Dattijo ya ce....'
.
"Da qyar muka samu muka 6an6aro shi daga jikin sitiyarin motar, duk haqarqarinsa sun karairaye. Muna gama ciroshi motar ta kama da wuta tare da tankin."
.
Wani mutum ya ce....'
.
"kamata ya yi a hanzarta kai shi asibiti."
.
Wani ya ce....'
.
"An gano ko'ina yake kuwa?"
.
Wanda ya yi magana da farko ya ce....'
.
"Mun duba duk aljifansa bamu samu wani abu da zai taimaka mana ba wajen gano inda yake. Da wayarsa da takardunsa duk suna a cikin motar sun qone."
.
Wani a cikin mutanen ya sake cewa.
.
"Don Allah a taimaka a samu mota a tsayar da wani ya kai shi asibiti. Ku duba halin da yake ciki, yana buqatar taimakon gaggawa."
.
Ma'aruf bai sake jin komai ba tun daga wannan lkc. Baya iya motsa ko'ina a jikinsa. Kuma bai san inda ya samu rauni ko karaya ba." bai san ko a wane hali yake ciki ba."
.
Ba a dade ba mutanen da suka zo wajen da hadarin ya faru, suka dauki Ma'aruf a mota suka tafi dashi asibitin Musawa, amma kuma duk wanda yaga halin da yake ciki sai dai ya kawar da kai ya yi masa addu'a kawai. Sbd Ma'aruf ya samu karaya a kusan ko'ina na jikin sa.
.
Motar da ta tafi da Ma'aruf ta bar daidai wajen da hadarin ya faru a daidai lkcn da motocin biyu suke ci da wuta rigi-rigi. Mutanen da suka tsaya taimako suka yi dandazo daga baya suna kallo. Titin ya cunkushe babu damar xuwa ko dawowa sai dai wadanda suke yi ribas suna komawa inda suka fito.
.
Motocin da suka fito daga Katsina xuwa malumfashi ko kuma motocin da suka fito daga Malumfashi xuwa Katsina.
.
.
*** ***
.
.
A can gida Ilham ta ji ta kasa samun sukuni a xuciyarta tun bayan tafiyar mijinta Ma'aruf. Ta ji haka kawai Ma'aruf yana bata tausayi. Me yasa sanda zai fita bata saki ranta sun dan yi wasa da dariya ba, me yasa tayi fushi suka rabu cikin damuwa?
.
Har bayan awa daya da tafiyar Ma'aruf Ilham tana zaune a falo ta kasa tashi ta yi wani aiki. Ta ji duk jikinta ya mutu. Tana jin Aiman yana ta kuka a daki amma ta kasa tashi ta je ta daukoshi. Tana ta kallon Khairat na ta kaiwa da komowa ta zo ta hau jikinta ta kira sunanta.
.
"Mama."
.
Ilham ta dafa kan 'yarta ta kira sunanta.
.
Ilham ta dafa kan 'yarta ta kira sunanta itama.
.
"Ya aka yi ne Khairat?"
.
Ta dauketa ta dora akan kujerar dake a falonsu. Khairat ta rabu da mahaifiyarta ta mayar da hankalinta akan hotunan mahaifinta adanda suke cikin (Frames) masu ban sha'awa an kafe su a kowanne bango na falon.
.
Ilham ta kai hannu kan (Tv stand) dinta ta dauko wayarta ta nemo lambar wayar Ma'aruf don ta kira shi ta ji muryarsa....don ta bashi haquri ta nuna masa ta saki ranta, sbd shima ya saki nasa ran tunda dai yana can xuciyarsa tana cike damuwar halin da ya barta.
.
Ta kira wayarsa ta ji a kashe. Abin ya bata mamaki sbd ta san Ma'aruf baya kashe wayarsa don yana cikin mota, ko akan hanya yake idan ta kira shi zai dauka ya fada mata yana mota ne, ya fada mata garin da yake, ya fada mata zai kirata idan ya sauka.
.
Ilham ta yi murmushi da ta yi zaton ynx haka Ma'aruf ya kashe wayarsa ne don shima ya bata haushi tunda ya san dai dolene ta kira shi kafin ya kai Katsina. Bata sake kiransa ba." ta rabu da shi, tana ran idan ya bude wayar shi da kanshi zai kirata ya fada mata ya isa Katsina lfy.
.
Koda a ce ma ya dauki wayar dama maganar da ta saba fada masa idan yana kan hanya, zata fada masa a halin ynxn.
.
"Don Allah Abban Aiman ka tafi a hankali kada ka yi gudu. Allah Ya sa ka sauka lfy."
.
.
.
***
.
An kai Ma'aruf asibitin Musawa, har xuwa lkcn bai san inda kanshi yake ba." lkcn da aka dorashi akan gadon marasa lfy ka gungurashi xuwa dakin 'yan hadari ne ya farfado a karo na biyu.
.
A lkcn ne ya yi qarfin hali ya bude baki da qyar ya fara qoqarin yin magana jini yana xubo masa ta hanci ta baki. Ma'aruf ya kama rigar daya daga cikin mutanen da suka kawo shi asibitin.
.
Ganin haka sai suka dan saurara don su ji ko zai iya yin magana ya fai ko shi mutumin ina ne?" Ma'aruf ya ce da wanda ya riqe wa rigar.
.
"...ku je Malumfashi.....ku sami matata....ku fada mata na yafe mata....kuma ina sonta."
.
Mutanen da yake bar wa wasiyyar suka tambayeshi.
.
"zaka iya tuno lambar wayar matar taka?"
.
"A wacce unguwa kake a Malumfashi?"
.
Ma'aruf bai samu damar iya amsa masu ko daya cikin tambaoyin da mutanen suka yi masa ba. Ya yi tari jini ya xubo. Ya yi kalmar shahada ya sake maimaitawa. Tun daga nan bai sake cewa komai ba." jikinshi ya yi laushi ko'ina ya daina motsawa.
.
Mutanen da suka taimaka suka kawo shi asibitin basu yi gaggawar nemo wani likita a cikin ma'aikatan asibitin ba, sbd sun san wannan mutumin da basu san ko wanene ba ya rasu tun kafin likitoci su amshe shi.
.
.
.
Lp=3%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 3
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafIn ba."
.
Sbd sun san wannan mutumin da ba su san ko wane ne ba ya rasu tun kafin likitoci su amshe shi.
.
Mutanen suka yi cirko-cirko suna tunanin abin da ya kamata su yi. Ina zasu fara xuwa? Kuma wa zasu damqawa wannan gawar tunda dai su hanya kawai ta biyo dasu inda aka yi hadarin suka taimaka suka kawoshi asibiti?
.
Kowa ya yi ta xubar da hawaye a cikin su." mutane suka zagaye gawar Ma'aruf suna tambayar ko wane ne?" amsa daya ce kowa zai iya bayarwa akan shi.
.
Kafin ya rasu ya ce shi mutumin Malumfashi ne a nan jihar Katsina. Ya ce a je a samu matarsa. A fada mata ya yafe mata kuma yana sonta.
.
Ma'aruf ya rasu yana begen matarsa Ilham
.
.
***
.
.
Ynx Ilham ta gama yi wa yaranta wanka, ta share dakin barci da falo ta gyara ko'ina. Ta hada shayi ta xubawa 'yarta Khairat ta dauka. Ilham ta hada nata har zata kur6a sai kuma ta ji tunanin Ma'aruf ya sake fado mata a rai....


Read / Download FARIN CIKI SAU DAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album