Join Our WhatsApp Group

RIBAR BIYAYYA Complete Hausa Novel Document by RIBAR BIYAYYA


RIBAR BIYAYYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38032



RIBAR BIYAYYA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 06, Oct 2023

Author: Sawwama Qawwama ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 204.43 kb

File Type: txt

Views: 693+

Download: 434+

Last download: 4 days ago

Description/Story: Compiled by Princess Aysha Muhammad

💖RIBAR BiYAYYA💖






By Sawwama A.






Page 1.






_Bismillahir rahmanir rahim_





Kanta a duk'e yake tana k'ok'arin karatu amma hakan ya faskara,duk yanda tayi k'ok'arin cire hankalinta da tunaninta akan abinda ke faruwa a tsakar gidansu tsakanin mahaifinsu da yayarta abin ya faskara.


Tsaki taja tare da toshe kunnuwanta da yatsunta dan jin irin dukan da baba ke yiwa yayarta khadeeja yana fad'in " wallahi ban haifi abinda zai fi k'arfi ba dan rashin mutunci ni zaki kalla kice ba kya son d'an 'yar uwata?"

Ita kam bakinta bai mutu ba ihu take tana " fad'in ni dai bana sonshi kuma wallahi ba zan aure shi ba" shi kuma baba bai fasa dukanta ba.

Kusan kullum abinda ke faruwa a gidanmu kenan kullum sai ya daketa yace sai ta auri d'an 'yar uwarshi ita kuma ta dage bazata aureshi ba. Ni kaina mamakin yanda adda adija ta fitsare nake dan baban mu wani irin mafad'acin mutum ne hakan yasa duk muke tsoronsa kai ba mu da muke yaransa ba har yaran anguwa na tsoronshi dan shi in yaga yaro na abu mara kamashi yake ya tsutsula mishi dorinarsa da take rataye d'akinsa hakan yasa ake tsoron sa sosai amma abin mamaki adda adeeja tsoron nan ya kau bata damu da irin dukan da yake mata ba wanda tun yana dukanta da dorina har ya koma da icce amma ita ta tubure tana kan bakanta na baza ta aureshi ba ya mata yaro ita tana da wanda take so,ya hana ta fita ya hanata zuwa makaranta amma hakan bai ko sa ta sakko ba. Duk abinda akeyi mamanmu bata tab'a kula su ba harkar gabanta kawai take yi in tana zirga-zirganta yake jibgar adeejan bata ko d'aga kai ta kallesu tana gamawa kuma zata k'ulle d'akinta.

Ajiyan zuciya ta sauke ta mi'ke ta je k'ofar d'akin tare da d'aga labulen abin takaici baba ta gani yana sunkuye yana d'aure 'yar uwarta kan adeejan a duk'e tana kuka ciki ciki saboda yanda muryanta ya shak'e gefe guda kuka mama ce ke tsugune tana alawlan magriba, hawayena ya gangaro kan dakalin fuskarta na tausayawa 'yar uwarta baba na fita sallah tayi saurin zuwa gaban adeeja ta tsuguna tare da d'ago hab'arta idanunta duk sun kumbura sun koma ciki saboda azabar kukannda take yi kullum.

Murmushi ta sakar mata wanda hakan yasa hawayen fuskanta ya k'aru cikin kuka tace " adda adeeja ki taimaki rayuwarki ki karb'i zab'in baba wata rana zaki ci *ribar biyayyan* da kika mishi." Wani murmushi ta kuma yiwa kanwarta murya a shak'e tace " Fateema ke yarinya ce baza ki gane halin da nake ciki bana son shi ni Abdulhameed nake so shine burin zuciyata shi nake fatan inyi rayuwar aure da shi ba wannan d'an yaron ba"

Kafin tayi wani magana mamansu ta k'wala mata kira hakan yasa ta mik'e da hanzari ta tafi d'akin maman sallah tayi mata umarnin taje tayi.


Washegari fateema na shirin makaranta hankalinta na kan adeeja dake kwance tana baccin wahala ta duk'unk'une a cikin bargo da alama sanyi da zazzab'i sun shigeta dan jiya abin na baba ya wuce tunaninsu dan a tsakar gida ya barta ta kwana duk irin sanyin da ake tsulawa a garin jos na farkon watan sha biyu. Wuyanta ta tab'a taji shi zafi zau gashi sai rawan sanyi take d'an tsaki taja ta fito d'akin mamansu ta gaya mata toh shine abinda maman tace.

Haka ta dawo ranta na k'una yanda maman bata nuna b'acin ranta kan abinda baba ke yiwa adeejan ai ba shi kad'ai ya haifeta ba ana auran nan dole ne? Haka ta cigaba da shirin makarantanta cikin blue din skirt dai dai guiwa da farar riga sai blue din waist couth sai farar doguwar safa da ta saka har guiwa sannan tasa wan guntun safan kafin ta saka sandal dinta na fata ta saka farar hijabi gayu ta fito d'as da ita.


Ko kafin ta fito daga d'akin har ta jiyo muryar 'yar uwarta kuma abokiyar tafiyanta charity tana gaishe da mama cikin yaren su na birom, fitowa tayi suka kama hanyan makarantar au Bishop collage a k'afa suke tafiya kasancewar baau da nisa sosai da makarantar.

A hanya charity ne tace "wai har yanzu baban ku bai hak'ura ya bar adeeja ba ?" Bata bari ta ansa ta ba tace "kai ku kam hausawa kuna da matsala wallahi wai ace mutum da rayuwarsa amma ace za ayi mishi dole, adeeja d'in ma yaushe ta kai aure just 17 years in ss2 ace za ayi mata aure for Christ sake this is not fair. Ita dai bata kula ta ba hankalinta na kan yanda zata taimakawa 'yar uwarta.

Charity dince ta kuma cewa "ni gaskiya na gaji da gani sist adeeja haka zan sami ngo d'inmu in gaya mata abinda ke faruwa in yaso sai ta sami ngo d'in ku ta gaya mata tayiwa baba magana what he is doing to adeeja us not fair just because he gave birth birth to her does not mean he have control over her(abinda yake yiwa adeeja ba adalci bane dan ya haifeta ba yana nufin yana da iko da rayuwarta bane)"

Duk da kalamanta sunyiwa fateema zafi amma hankalinta yafi raja'a akan cewan da tayi zata gayawa kakarta ta samu kakarsu da magana dan dama duk abinda akeyi kakarsu mahaifiyar mamansu bata sani ba maman ta hana a sanar mata tace 'yarsa in yaga dama ya kasheta, yanzu kuma in charity ta fad'a mata ai shikenan sai tazo ta tsawatarwa da baba.


Da wannan shawaran suka isa makarantarsu suna shiga gate d'in da david ta fara cin karo da alama sune da duty duk seniors d'in suka fara kiranta da sunan tsokananta dan ita mai farin jini ce a wajeb d'alibae makarantar da malamai Chinese girl chinese girl turo dan k'aramin bakinta tayi tana cire hijab d'in wuyanta ta tura a cikin jaka. David ne yazo gabanta yana magana k'asa k'asa yace "how far?" "Fine " shine abinda tace tayi gaba dan ta tsani yaron arnen da ya sata a gaba da sunan so toh ita d'inma guda nawa take mtswww ta ja tsaki.


Yammacin ranan tana zaune tana assignment d'inta adeeja na kwance dan har lokacin zazab'in bai saketa ba taji sallamar kakarsu da sauri ta rufe littafin ta fita a guje ta d'ane 'yar tsohuwar tana murna.

B'anb'areta tayi daga jikinta tana fad'in "oh ni sakeni kaman baki san hanyan gidana ba sai mutum yazo ku fara murnan k'arya" dariya tayi ta k'ara mannewa jikin kakar tasu tace " haba ngo na kin san school ba barin mu yake ba in na dawo ga assignment wanki uniform karatun islam weekend kuma asabar da lahadi kinga ai ba lokaci"

"Toh naji kanari ai ke daman ba a k'ureki ko da yaushe kina da excuse" dariya tayi suna shiga d'akin mama

Ko da mama ta fito daga ban d'aki bayan sun gaisa da ngo masifa ta rufeta da ita cikin yarensu na birom ta inda take shiga ba tanan take fita ba tun ba da taje ta ga yanda jikin khadeejan ya kumbura ba ga zazzafan zazzab'i da take fama da shi ba wanda ya kulata.

D'aukanta tayi ta kaita asibiti tare da rakiyar fateema aka mata allura aka bata magunguna sannan suka dawo gida inda suka tarar da baba ya dawo daga aikinshi na drivern taxi.

K'ulewa d'aki suka yi da ngo tayi ta mishi nasiha tare da fad'a a haka ta samu ta shawo kanshi ya hak'ura zai barta ta auri wanda take so da sharad'in ba ruwanshi duk abinda yaje ya dawo tunda ita taurin kaine da ita tak'i d'an uwanta ta dage sai bare mai mata, haka dai tayi ta lallab'anshi kasancewan yana girmama surukar nashi ya haqura.

Zaune yake bayan tafiyan ngo yana tunanin ta yaya zai fara runkarar yayarshi da batun y'arsa bata son d'anta da ya nuna yana sonta shi kam ya shiga uku ya haifi abinda ya tozartashi me k'watanshi a hannun hajiya sai Allah dan duk masifarshi ta fishi tunda abin a jininsu yake.

'Yar wayarsa ya zaro touchlight phone ya danna numbern baba k'arami bayan sun gaisa yace mishi in ya sami lokaci yazo yana nemanshi amsa mishi yayi da toh inshaa Allahu zai zo.

Tsaki yayi tare da jefar da wayan bayan ya gama ansa kiran kawunshi shi wallahi yayi dana sanin cewa yana son yarinyan nan shi fa dama ba wai ya wani zurfafa akan sonta bane kawai tana burge shi ne gata da kyau jan ajinta ya k'ara janyo hankalinshi kanta baiyi zaton zata k'ishi ba da bai furtawa hajiya yana sonta ba gashi yanzu ta k'wallafa rai da wannan had'in wani tsakin ya kuma ja ya rungumo pillow dinshi yan so yayi bacci amma ranshi sai suya yake baya son abinda zai tab'a ran hajiya wallahi da yace a bar maganan auren nan toh yanzu sai hajiya ta k'ullace ta yanzun ma ya aka k'are cewa take uwarsu ce ta zugata tak'ishi bayan shi bai ga alamun k'inshi a wajen mamansu ba amma zai samu lokaci yaje jos d'in yaji koma meye.









SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖






By Sawwama A.






Page 2.







Kallon mamaki kawai fateema ke bin adeeja dashi ganin yanda ta sake tana ta hirar soyayya da saurayinta Abdulhameed sai shagwab'a take zuba mishi kaman ba ita take shan jibga ba a ranta tana tausaya mata rashin miji kaman baba k'arami au yah sagir ta manta ya rok'eta kar ta dinga kiranshi baba k'arami kaman yanda sauran zuriyarasu keyi ko in ce mafi yawancin su.

Tuno da randa ya fara zuwa garin tayi wata biyu da suka wuce kenan.
Wani yammaci ne suka ji dirin motoci biyu a k'ofar gidansu daganan kuma suka ji muryar baba na shigowa da wani fuskan mama ne ya fad'ad'a da fara'a ganin wanda suka shigo da baba.


Kama hab'a tayi tace" ikon Allah baba k'arami kaine ka girma haka" murmushi yayi ya tsuguna yana gaisheta su kam yaran sai kallonsa suke da mamaki dan basu wani sanshi ba gwara ma adeeja tana ji kaman ta sanshi suma gaisheshi suka yi.


Nan da nan mama ta fara hidima da shi abin ya k'ara basu mamaki yanda mama bata bar musu hidiman ba dakin baba duk suka shiga saboda yayyafi da aka fara kuma suna son jin k'wak'waf d'in waye wannan d'in.

Fateema kam da ta kasa hak'uri dan taga sai hiransu take da alama dai daga bauchi yake dan taji baba na tambayanahi su hajiya masifaffiya sunan da suka saka mata kenan

"Baba wai ahi wannan d'in waye?" Fateema ta tambayi babansu dariya duk suka yi mama tace" toh kaji kai baba k'arami saboda rashin zumunci k'annenka basu sanka ba."

Murmushi yayi yana shafa gashin kanshi bak'i sid'ik da yasha gyara da ka ganshi kaga gashin fulani yace " mama ai suma basu da zumuncin dan ban tab'a ganin sunje bauchi hutu ba"

Tab wa zaije gidan hajiya masi..." Pap mama ta buge bakin fatima jin tab'okaran da take shirin yi musu sarai ya gane me yarinyan take shirin fad'a a zuciyarsa yace ator ba dai tace juninta mita ba yaushe yara zasu so zuwa gidan tana cewa an raba ta da 'ya'yan d'an uwanta a fili kuma yace " ai kuwa fateema yanzu kin kula da bauci kenan."

"Hmmm" shine abinda tace dan tana tsoron yin wani magana mama ta k'ara buge mata baki amma da ta tofa.


Kwanan sagir biyu a jos a kwanaki biyun nan sun saba da fateema sosai dan shegen surutu gareta da abin dariya shi d'in kuma an dace mutum ne mai sauk'in kai gashi da barkwanci sai su zauna suta shiririta adeeja ce dai bata shiga shirginshi dan acewarta ya fiye rawar kai da shegen kallo ita bata son raini.

Suma basa kulata su sha kallonsu a laptop dinshi su ji wak'a ranan yake ce mata yaji wani wak'a mai dad'i da aka yi da sunanta tsalle ta daka ta tsuguna a gabanshi tace "wakar sabo ne ? Dan akwai wani waka da na sani da ina son wak'an sosai". Yace "gaskiya ban sani ba nima ji nayi a wayan wata k'awata" kallonshi tayi tana d'an hararanshi ta gefe tare da murmushi a fuskanta ta nunashi da d'an yatsanta tace a wayar budurwarka ko" dariya yayi sosai yace " wa yace miki a wayan budurwata naji k'awata nace me idon y'an china kawai" turo baki tayi ta sa kukan shagwaba tace wai ni me yasa ake had'a ni da 'yan china ne ?" Dariya ya kuma yai yace saboda idonku iri d'aya kuna kama amma dai kinfi kama da yan korea da d'an k'aramin pink bakinki." Kukan shagwaba ta sa tana bubbuga k'afa can kuma ta tuno tace to ka sa min wak'an ni dai wayarsa ya ciro yace" bari ince ta turo min a whatsapp dan ban da ita ni a wayana" bayan ya kira yace ta turo mishi ne yace" toh yi min wancan kafin.ya shigo inji ko shine."

Zama tayi a gabanshi ta tank'washe k'afa ta fara rero mishi _" fatima bintu fatima sai wata rana so mafarkine da ba tabbas ba bankwana bintu sai wata rana kukan zuciya da bana ido ba_ " tafa mata ya fara ai yace "iyyeee lallai kam bintu wak'an da dad'i amma ban tab'a ji ba yawwa wannan d'in ma ya gama downloading" danna mata yayi muryar m sharif ya fara amon wak'an _zahra zahra zahra_ ihu ta sa bayan ta gama ji tace "wallahi wannan yafi dad'i haka dai suka ta shirmensu wani sa'in da baki zai dinga mata wak'an _zahra zahra zahra kece sarauniya zahra_ ita tayi ta juyi tana kad'a mishi k'aramin waist d'inta.

B'angaren karatu ma da ya tab'ata yayi mamakin kwanyar yarinyan shi yasa suka k'ara shk'uwa.

Ko da wasa adeeja bata shiga shirginsu har ya gama kwanakinsu ya tafi.

Sai me sai ga hajiya masifaffiya ta zo da kanta acewarta autanta yaga mata a gidan wai khadeeja yake so kowa yayi farin ciki ba ma kaman fatima.

Bayan tafiyan hajiya ne adeeja ta tayar da borin bata sonshi ya mata yaro gashi d'an kauye da shi baba yayi masifar yayi fad'an yayi nasihar taki shi ko da bai d'aukan wargi tuni ya fara had'a mata da duka haka bai sa ta canza ba.

B'angaren fatima tayi ta kod'a mata halayenshi rufeta tayi da masifa tace "ke kije ki aureshi mana ni nace bana sonshi ko ana dole ne?"

"Adda adeeja to me yasa ba kya sonshi gashi d'an gayu kyakyawa zaki ce mishi d'an kauye da idanunshi masu kyau manya"

"Dallah can rufa min baki mayyar manyan ido dan ke kam da zakiyi maita da masu manyan ido sun shiga uku shegiya kinayi da wasu k'ananan idanunki a wajen Allah ma shi yasan me ya gani ya hanaki manya ido ya baki na 'yan chinese" ranta ne ya b'aci taji haushi zagin da adeejan tayi mata toh ai dai *bani nayi kaina ba* da zaki dinga zagina dan...


Read / Download RIBAR BIYAYYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album