Join Our WhatsApp Group

BAKIN ARTABU BOOK 3 Complete Hausa Novel Document by BAKIN ARTABU BOOK 3


BAKIN ARTABU BOOK 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 7800BAKIN ARTABU BOOK 3

Reading Time: 0 Hours

Added On: 17, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 42.91 kb

File Type: txt

Views: 563+

Download: 142+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: {BAKIN ARTABU-3 TYPE A }
Lokacin da sarki raihan ya koma turakarsa bayan ya sa an tafi da sarki Uhaisu izuwa kurkuku sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya kasa zama ko tsayuwa ya dunga kai kawo a cikin turakar tasa bakomai ne ya haddasa hakan ba face tsananin tunani bisa abinda da yasa aka aikatawa sarki uhaisu nan take zuciyarsa ta raya masa cewa, "Hukuncin da ya yankewa sarki Uhaisu yayi tsauri da yawa tun da har ya furta cewa yana son jaruma yazila kuma zai yi komai domin ya aureta to kamata yayi ya umarceshi daya karbi addinin allah kawai.
Idan har ya musulunta aka daura masa aure da yazila ai zaici gaba da taimakon addini har ya samu akan abokan gaba. "
Koda sarki raihan yazo nan azancensa sai nadama ta zo masa nan take ya ayyana a ransa cewa lallai gobe da safe zai je har kurkukun ya baiwa sarki Uhaisu hakuri sannan ya bijiro masa da sharadin karbar addinin musulunci kawai, idan har ya amince sai a daura masa aure da jaruma yazila.
Koda sarki raihan yazo nan a zancensa sai ya sami nutsuwa da kwanciyar hankali.
Nan take yaje ya kwanta akan gadonsa.
Kwanciyarsa keda wuya kuwa sai barci mai nauyi ya saceshi
*** *** ***
Al'amarin su sarki Daksur kuwa bayan sun shafe sama da sa'a hudu suna neman sarki Uhaisu a cikin daji basu ganshiba, kuma ko duriyarsu basu ji ba, sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka rasa abin dake musu dadi.
Haka dai suka hakura dole suka dawo sansaninsu, inda sarki daksur ya sake tara gaba dayan sarakunan a cikin tantinsa suka shiga tattaunawa akan wannan bakon al'amari na ban al'ajabi da yafaru dan gane da batan sarki Uhaisu.
Sarki Daksur ya dubi sarkin yaki sannan ya dubi gaba dayan dakarun daya bayan daya yace, "ya ku 'yan uwana kuyi sani cewa muna cikin mummunan tashin hankali bisa rashin ganin sarki Uhaisu a wannan filin yaki, mun duba ko ina acikin daji bamu ga sawun saba, bare muce yana wani wajen ne a cikin wannan daji ko kuma ya koma izuwa kasarsa, amma da muka dawo nan sansanin yaki sai muka ga alamun sawayensa sun nufi hanyar birnin abokan gaba lallai wannan ya nuna mana cewar sarki Uhaisu ya kai kansa izuwa ga makiya, walau ko don ya yaudaresu ya samo wata hanyar da zamu sami nasara akansu ko kuma ya kai kansa saboda wata bukatar.
Yanzu wacce shawara ce kuke ganin zata fishshemu?"
Lokacin da sarki Daksur yazo nan azancensa sai gaba dayan sarakunan suka yi shiru suka kama kallon. Juna aka rasa wanda zai ce kala.
Daga can sarkin yaki yai gyaran murya sannan ya dubi sarki daksur yace, "Ya shugabana kayi sani cewa bai kamata mu dauki wani mataki ba yanzu har sai mun jira zuwa gobe da safe mun ga abinda da zai faru. Idan har sarki Uhaisu ya kai kansa ne wajen abokan gaba domin ya yau daresu ya cutar dasu tofa duk abinda zai shirya a cikin daren nan zai shiryashi kafin wayewar gari ya dawo nan garemu. Idan kuma saboda bukatarsa ya kai kansa ta zai iya karbar addininsu, kun ga kenan shima ya zama abokin gabarmu.
Lallai a yanzu bamu da ikon yanke wani hukunci har sai gari ya waye munga abin da zai faru. Idan har sarki Uhaisu ya barmu ya koma bangaren abokan gabarmu toya zama dole mu janye, wannan yaki domin kuwa ba nasara zamuyiba zai fi kyau mu koma gida muyi sabon tunani akan yadda zamu sami nasara tunda shi yaki dan zanba ne".
Sa'adda sarki daksur yazo nan a zancensa sai sauran sarakunan suka yi tsuru-tsuru suka kama kallon juna cikin tsananin damuwa da takaici.
Shikuwa sarkin yaki sai yayi murmushi yace, "Ni kuwa ina ganin idan muka kuskura muka koma gida batare da munci wannan yaki ba to fa mun yi a sarar babbar dama wacce a bune mawuyaci musake samun kamarta. Kai ina tabbatar muku da cewa muna janye wannan yaki shikkenan mun baiwa wadannan abokan gaba namu babbar damar daza su sami lagonmu.
Abu na farko dai kun sani cewa da yawanmu zuciyarsu zata karaya koda an ce a sake yin gangami a fito wa sunsu baza su fito a wannan karon an ga babu nasara.
Yanzu dai babu a bin da yakacemu face mu jira zuwa wayewar gari mu san matsayin da sarki Uhaisu ke ciki. "
Koda jin wannan batu na sarkin yaki sai kowa yai amanna da shi kowa ya tashi ya watse aka bar sarki Daksur shi kadai a zaune cikin tantin nasa yana tunani.
*** *** ***
AL-amarin sarki Uhaisu kuwa lokacin da ya farfado bayan dogon suman. Da yayi saka makon dukansa da akayi a keyarsa sai ya farka yana sosa keyar tasa sakamakon zugi da yaji tana yi masa. Koda ya bude idanunsa ya tsinci kansa acikin kurkuku sai takaici ya kamashi yace, "A cikin zuciyar yanzu abinda sarki Raihan zai yi mini kenan, na dauki amana na bashi, na shigo garinsa da zuciya daya bada nufin yaudara ko cutarwa ba amma sai ya kafa mini sharadin da ya san cewa ba zan iya ba don kawai na ce ina son 'yarsa da aure?"
Koda yazo nan a zancen zucin nasa sai takaici ya sake turnukeshi ya hada kai da guiwarsa yana tunani.
Nan take ya yanke shawarar ya san hanyar da zai bi ya gudu daga wannan kurkuku kuma ya sace wannan 'yar sarki ya gudu da ita izuwa can birninsa inda zai aureta bisa dole ko da bata so. Gama yanke. Wannan shawarar keda wuya sai ga mai kawo masa abinci ya taho dauke da wani dan karamin akushi.
Koda ganinsa sai mai gadin kofar kurkukun wani narkeken kato ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya zura wata katuwar kuba a cikin kofar ya murda sau uku sannan kofar ta bude
Duk da cewar hannayen sarki Uhaisu da kafafunsa a daure suke cikin sasari sai da ya yunkura da kyar ya mike tsaye.
Koda mai kawo abinci ya shiga cikin dakin ya sunkuya zai ajiye akushin sai sarki Uhaisu yai wuf! Ya kwakumeshi ya shakeshi sannan ya zare wata wuka a kugun mai kawo abincin ya dora ta akan mako garonsa yana barazanar zai yankashi idan maigadin kofar dakin bai bashi damar ya fitaba. "
Nan take maigadin ya wangame kofar dakin gaba daya, a tunaninsa ko sarki Uhaisu ya fito ba zai iya guduwaba a daure yake cikin sarkoki kuma yanzu nan zai shammaci Uhaisu ya buga tambarin da gaba dayan dakarun gidan su rugo izuwa wajen.
A binda bai saniba shine tuni sarki Uhaisu yayi tunanin duk faruwar hakan kuma ya shirya dabarar da zai kare kansa.
Koda Uhaisu yaga mai gadin dakin nasa ya wangame kofar dakin sai ya shammacesu duk su biyun ya gabza musu wawan naushi a muka-miki atare. Nan take mai gadin da mai kawo abincin suka sulale kasa sumammu. Cikin gaggawa uhaisu ya kama sarkokin dake jikinsa ya tsitstsinkasu sannan ya dauresu ya kullesu a cikin kurkukun yasa kubar ya dada kulle kofar sannan ya kara gaba, dama yayi sauyin tufafi dana wannan bawa da ya kawo masa abinci, kuma wata doguwar riga ce mai hade da rawani mai rufe kai gaba daya.
Sarki Uhaisu yaci gaba da tafiya a cikin kurkukun rike da akushin abinci da aka kawo masa.
Duk inda ya wuce dakaru ne a tsaitsaye ko kallonsa babu wanda yayi har ya isa bakin kofar fita daga kurkukun. Nan ma sai kawai yaga an bude masa kofa. Har yasa kafarsa guda waje sai yaji mai gadin kofar yace, "tsaya".
Duk da irin tsananin jarumta ta sarki Uhaisu da dakewar zuciyarsa sai tsoro ya kamashi bisa tunanin asirinsa ya tonu.
Maigadin ya matso daf dashi, inba don duhun daren da ke cikiba da sai maigadin ya shaidashi a fuska, kawai sai mai gadin ya dubeshi yace, "meyasa kafito da abincin wannan bakon fursuna alhalin ya kasance babban mutum? Na tabbata sarki ba zai so a barshi a cikin yunwa ba"
Koda jin wannan tambaya sai sarki Uhaisu yai sauri ya bude murfin akushin ya nunawa maigadin yaga babu komai a ciki.
Ba tare da sarki Uhaisu yace uffanba ya wuce gaba abinsa. Shikuwa mai gadin sai ya bishi da kallo kawai yana mamaki kamar ya sake kiransa yayi masa wadansu tambayoyi amma sai ya fasa ya mai da kofar ya rufe.
Uhaisu yaci gaba da tafiya ya nausa izuwa wani bangare daban na gidan sarautar zuciyarsa na dari-dari.
Babban tashin hankalinsa shine, bai san inda ya kamata ya durfafa ba kai tsaye don ganin dakin da masoyiyarsa take. Sannan kuma yana tunanin yiyuwar saceta a cikin wannan dare har ya sami nasarar fita da ita daga cikin gidan sarautar ba tare da a sirinsa ya tonuba.
Haka dai yayi kundunbala yaci gaba da tafiya yana waige-waige da kalle-kalle. Babbar sa'ar da yayi shine gaba dayan hadiman gidan sarautar masu kai kawo a wannan dare irin tufafin jikinsa ne da su don haka duk inda ya wuce dakaru basa tsai da shi. Yana cikin tafiya ne ya tsinci dami akala, domin Jaruma Yazila ya hango tare da wata mace sun jero suna tafiya a hankali acikin harabar gidan sarautar suna hira a cikin nishadi.
Koda ya kalli fuskar daya macen yayi arba da ita sai zuciyarsa ta buga da karfi kuma hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe.
Ba komai ne ya haddasa hakanba face ganin yadda kamanninta dana wacce suke tare ya zamo iri daya sak tamkar an tsaga kara.
Nan take fa ya dabarbarce ya rasa wacece tasa wadda ya kamu da tsananin sonta.
Cikin hanzari Uhaisu ya buya a bayan wata katanga yana leken su yazila a lokacin da suka je suka zauna akan wadansu kujeru guda biyu suka ci gaba da hira.
A lokacin ne yazila ta dubi dabira tace , "yake 'yar uwata wai shin yanzu me kike tunanin zai faru ne gobe da safe a filin yakin nan tun da gashi mun kamo abin dogaronsu mun tsareshi a kurkuku".
Koda jin wannan batu sai dabira tayi 'yar guntuwar dariya tace, "Ni fa hankalina a tashe yake domin yadda na ga irin tsananin jarumtakar sarki Uhaisu afili daga ina ganin a ko yaushe zai iya guduwa daga cikin kurkukun can da aka tsareshi.
Amma idan har bai samu damar guduwaba tabbas gobe da safe mune zamu ci wannan yaki. "
Da yake sarki Uhaisu yana hangosu dabira daga inda yake labe "
Koda jin wannan sai ya aiyana aransa cewa lallai ita ce masoyiyarsa wacce yakamu da tsananin sonta tunda ita ce ta kafsa yaki da shi ta san irin jarumtakar tasa".
Lokacin da jaruma Yazila taji wannan batu na 'yar uwarta Dabira sai ta kyalkyale da dariya tace, "Ni kuwa ko kadan bana zaton sarki Uhaisu zai yi yunkurin guduwa tunda bai sami damar ganin abin da ya kawo shiba.
Ga dukkan alamu har yanzu baki fahimci irin tsananin zogi da radadin dake cikin zuciyar dake begen masoyi ba. Na rantse da allah sarki Uhaisu bazai taba samun sukuniba face yayi arba da fuskar wandda yake so."
Gama fadin hakan keda wuya sai yazila taji mahaifiyarsu ta kwala mata kira don haka sai ta mike tsaye ta dubi dabira tace, Bari na je naji kiran da umma take mini ki jirani na dawo mu karasa hirarmu tunda nima idanuna sun kekashe bana jin barci"
Dabira tayi murmushi tace, "Ai na san kiran bazai wuce ta tambayeki dalilin da yasa bamu shiga dakinmu mun kwanta ba tunda gashi dare ya raba".
Koda sarki uhaisu yaga an bar dabira ita kadai zaune kuma ya hango gabas da yamma kudu da arewa yaga babu wani bada kare mai kallonsa ko mai kaikawo, kawai sai ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya dauko hodar banju wacce dama tuni yayi guzurinta a aljihunsa tun kafin ya baro sansaninsu na yaki.
Cikin sanda ya lallabo ta bayan dabira ya shaka ma ta hodar banjun ahancin ta.
Nan take Dabira ta bingire zata fado kasa daga kan kujerar da take zaune. Uhaisu yai wuf ya tareta ya a zata bisa kafadarsa.
A sannanne fa ya kama duru-duru ya rasa ta inda zai fice daga gidan sarautar ba tare da an ganshi ba
Aikuwa sai ya hango wadansu dakaru sun durfafo inda yake a guje ya ruga izuwa bayan wata bishiya dakarun suka wuce ta gabansa ba tare da sun ganshi ba.
Suna wucewa ya fito ya kama dube_dube yana kallon katangar gidan sarauta wacce tsawonta yafi karfin ya daka tsalle ya dira akanta ko ya shallaketa.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin sa kenan ya fara tunanin cewa dolene a sirinsa ya tonu.
BASH I TKRW
08105808371{ BAKIN ARTABU»3 TYPE B}
Sarki uhaisu yaci gaba da duru-duru kawai sai ya falfala da gudu kuda dakaru suka ga yana gudau sai suka bishi sarki uhaisu yana cikin gudu a gidan sarauta kawai sai ya hango wani mumbari mai tsayi sai yai sauri ya ya goya dabira a bayansa ya daka tsalle ya hau kansa munbarin yana hawa ya kara daka wani tsallen sai gashi ya haure katan gar gidan sarauta koda masu gadin kofar birnin suka ganshi goye da jaruma dabira sai suka bishi aka kasa tsere.
Al'amarin sarki uhaisu kuwa lokacin da ya kama azababben gudu goye da jaruma dabira a bayansa wadannan dakaru masu gadin kofar na biye dashi amma sai suka kasa cimmasa domin tazarar da yabasu bakadan bace.
Koda suka ga baza su iya cimmasa ba sai suka fara zaro kibiyoyi suna danawa suna kai harbi.
Sai da suka shafe rabin sa'a suna gudu su basu cimmasa ba shi kuma bai bace musuba. Ana cikin hakane wani acikin dakarunnan mai shegen naci yasamu nasarar hatbin sarki uhaisu akafarsa ta hagu
Koda kibiyar ta sokeshi a sangalelen kafarsa ta faso nama ta fito jini yai tsartuwa sai sarki uhaisu ya tsandara ihu sakamakon tsananin zafi da zugi da yaji amma saboda tsananin juriya da jarumtaka bai fadi ba kuma bai tsaya ya zare kibiyar ba, yacibgaba da gudu a hakan, mai makon ma ya sare sai ya sami karin kuzari da karfin gudun nasa ya kara tsananin tamkar iska ce ke kara...


Read / Download BAKIN ARTABU BOOK 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album