Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RAYUWAR ABDUSSAMAD Complete Hausa Novel Document by RAYUWAR ABDUSSAMAD


RAYUWAR ABDUSSAMAD

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 113680



RAYUWAR ABDUSSAMAD

Reading Time: 9 Hours

Added On: 20, Jan 2025

Author: Yar Mutan Zazzau ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 612.32 kb

File Type: txt

Views: 372+

Download: 582+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: ♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)

*Heart you so much*







*labari ne ƙirƙirarre,banyi dan cin zarafin wani ko wata ba,idan yayi dai-dai da rayuwar ki to an samu daidaito ne amma ba wai niyar tozarci ko wani abin ba*.

*Masoyana wa'inda na sani da wa'inda ban sani ba ina miƙo godiya ta a gare ku,sannan ina fatan zaku bani haɗin kai a wannan kamar yadda kuka bani a ƙareenateey,sai dai ina me baku haƙuri domin kuwa wannan zai fi ƙareenateey tsayi sosai duk da wancan ɗin ma yankewa nayi amma wannan babu wannan maganar dan haka ina fatan zaku bani haɗin kai sannan kuma zakuyi jimirin bibiyar shi har izuwa ƙarshe nagode sosai*.

Bismillahir-rahmanir-rahim.

📖📖01-02📖📖

Jejin dake hanyar Abuja idan ka baro kaduna,tafiyar mita ashirin daga ƙauyen banguwa,wani madaidaicin gida wanda yake kusan ginin ba'a ƙarasa shi ba.

Manya-manyan Bishiyoyi sune suka yiwa gidan ƙawanya inda baka hangen komai daya shafi gidan,ƙaton get ne irin na da wanda keda nauyi da kuma daɗewa.

Daga cikin gidan kuwa,wata irin farfajiya ce me girman gaske wanda ciyayi da kuma rairayi suka rufe wajen ba zaka iya gane yanayin ƙasar wajen ba.

Ƙofar da zata sadaka da ciki kuwa ƙofa ce ta ƙarfe me matuƙar nauyi,daka shiga wani falo ne ƙarami me duhun gaske wanda idan baka yi da gaske ba zaka iya bugewa,babu wani tarkace a falon banda kujeru da kuma tum-tum wanda suke ajiye a ƙasan carpet ɗin ɗakin.

Ta ƙaramin corridor kuwa doguwar hanyace wacce ke ɗauke da ƙofofin ɗakuna jere masu yawan gaske,daga ƙarshen corridor ɗin kuwa wani falon ne wanda yake babu kyan gani,saboda komai na ciki kalar ja ne,sannan ga wani irin tururin hayaƙi da yake fita me matuƙar ban tsoro da tashin hankali.

A ƙalla mutanen dake jere tsaye sanye da zani babba kalar ja jikin su babu riga,fuskar kowanne na nuna damuwa da ɓacin rai,sama dasu ishirin,kowanne kanshi babu koda ɗigon gashi.

Wani mutum duka suke kallo wanda yake zaune saman wata ƙatuwar kujera wacce gefen ta kuwa gunkin zakuna ne hannun dama dana hagu,gaban shi kuma ƙwarya ce babba wacce ke saman wuta tana ci sosai da sosai.

Tsayin minti biyar babu wanda yayi magana kafin can wani dake gefe yace cikin fusata da damuwa.

"haba Tuge wai wayo kake son ka gwada mana ko kuwa ɗan naka so yake yafi ƙarfin ka,yau shekara ashirin da biyar kenan da yiwa *oregbu* alƙawarin bashi jinin matar ka da ɗanka amma babu ɗaya daya samu".

Wannan dake zaune saman kujerar ya ɗago idanun shi da suka kaɗa suka yi ja ya zubawa wani mutumi wanda yake durƙushe gaban wannan ƙwaryar,cikin fusata yace; "bakaji tambayar da akeyi maka bane ko kuwa baka da amsar da zaka bayar ne?".

Cikin matsananciyar damuwa yace; "nayi iya yina *Appu* amma abu ya gagara matar nan ko gidan ta bata bari na kusanta kuma kun san hakan sannan dai-dai da rana ɗaya bata taɓa barin jikin su babu kariya ba shi kan shi yaron nawa ba sani na yayi ba,kuma fa kun riga da kun san hakan kuma tunda na yiwa Oregbu alƙwarin jinin sa aikuwa babu makawa jinin nashi ne".

Wannan daya kira da Appu ne ya miƙe tsaye sannan ya ɗauko wata sanda doguwa daga saman ta kuma tsini gare shi kamar kibiya ya ɗaga ta sama sannan yace; "har yanzu Tuge da sauranka,baka cika aƙawarin daka ɗauka ba dan haka sandar zama magaji tana nan a ajiye sai lokacin daka cika sannan Oregbu ya fara gajiya idan har baka kawo jinin ɗaya daga cikin su ba nan da lokaci kaɗan ba zaka fuskanci fushin shi".

Tuge ya buɗe baki zai yi magana Appu cikin tsananin tsawa yace; "maganar Oregbu itace magana baya buƙatar martani ko kuwa gardama,a fara gabatar da wankan tsari",dole yaja bakin shi yayi shiru.

Wani me ƙaton ciki ya taho cikin sauri ya ciri wannan ƙatuwar ƙwaryar dake saman wuta ya ɗaga ya miƙawa Appu shi ya fara sha sannan ya kwarara jinin a jikin shi wanda bana da tabbacin jinin na meye sannan aka miƙawa Tuge shima yayi yadda Appu yayi sannan sauran mutanen dake wajen.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸
*HAYIN RIGASA,KADUNA*.

ƴan mata guda biyu ne suka sauka daga Keke Napep a bakin titi,dukan su suna sanye da pink din hijab wanda ya saukar musu dan har ya wuce gwiwa,ɗayar fuskar ta tasha make-up ɗaya kuwa babu wani kwaliyya a fuskar ta sai dai duk da haka kyawun ta ya bayyana,dukkan su kama ɗaya gare su wanda hakan ya tabbatar mini da cewa ƴan biyu ne kenan.

Wacce tayi make-up ɗin ta ya mutsa fuska tace; "Ramluv,wallahi na gaji sosai",wacce aka kira da Ramluv ɗin tayi murmushi kawai tana buɗe purse ɗin dake hannun ta,ta ciro ɗari biyu ta miƙawa me Keken tace; "malam bamu canjin mu".

Me Keke Napep ɗin ya leƙo da kan shi yace; "haba Hajiyoyi ai bakuda canji,tun daga Tudun nufawa sannan ku nemi canji haba mana".

Wacce tayi make-up ɗin da yawa ta kalle shi ta wurga mishi harara tace"wallahi baka isaba sai ka bamu canjin mu ai dama ɗari da hamsin muka yi da kai sannan koda ka kawo mu baka shigar damu cikin unguwa ba mun kuma ƙyale ka shine zaka ce ba zaka bamu canji ba wallahi sai ka bayar".

Shima ɗan Keke Napep ɗin ya fito ya tsaya cikin faɗa da fitsarar ƴan zamani yace; "idan kuma na hana me zaki yi mini?",ta kalle shi taja tsaki tace; "au tambaya kake ma to wallahi zaka sha mamaki kaɗan daga aiki na wallahi na saka ayi maka dukan tsiya ƙaryar rashin mutunci kake".

Ɗayar ta kalli wajen sannan ta kalle su yadda kowanne keji da ɗanyan kai ga kuma waje ya fara cika cikin murya me rauni tace; "Rimluv dan Allah kiyi haƙuri kizo mu tafi",ta juyo ta balla mata harara sannan ta cigaba da masifar ta.

Yadda suke kamar zasu yi dabbe ga jama'a a wajen,gashi taƙi ta dena ya saka ƴar uwar ta fara hawaye wanda ita bama ta lura da ita ba,ita kuwa daman ƙoƙarin ta taja ƴar uwar tata su bar wajen.

"banza ɗan iska mara mutunci",Rimluv ɗin ta faɗa cikin fusata,hannu ya ɗaga domin sauke mata mari ya sauke akan ƴar uwar ta wacce ke ƙoƙarin raba su,Rimluv ta kalli ƴar uwar tata tace; "ka mare ta wallahi ba zaka ci bulus ba",itama ta ɗaga hannu ta kwashe shi da mari,wanda hakan yayi dai-dai da zuwan wani dattijo.

Cikin sauri yace; Nusreen kece da dambe da maza a titi harda mare-mare?",ganin wanda yayi maganar yasa ta saukar da kanta ƙasa tana cuno baki.

Cikin daka tsawa yace; "kin wuce gida ko sai na ɗauke ki da mari shegiya me baƙin hali",ta ɗago da zummar yin magana ƴar uwar tata tayi saurin matse hannun ta,shiru tayi tana ƙwafa sannan ta kalli me Keke Napep ɗin ta harare shi,hamsin ɗin da yake miƙo mata ta fuzge sannan ta juya tayi gaba tana faɗin"matsiyaci kawai".

Kowa a wajen da abinda yake faɗa,ita kuwa gaba tayi tana tafe tana masifa,dattijon nan yace; "ki rufe mini baki ko kuma nayi miki duka a wajen nan me mugun hali irin na uwar ta",shiru tayi tana jin wani tuƙuƙi a cikin ranta wanda hakan ba ƙaramin takurata yayi ba na rashin bata damar maida mishi da martani da ta hanata yi.

Can ƙarshen layin wani gida na rufin asiri za'a ce dan kana gani ka san talakawa ne,duk da dai ya sha sumunti sannan da ƙofa irin ta zamani a jiki,gaban gidan kuwa siminti ne a shinfiɗe wanda ya ƙara fito da gidan.

Tana shiga ta banko ƙofar wanda
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RAYUWAR ABDUSSAMAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album