Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

KUDURAR ALLAH Complete Hausa Novel Document by KUDURAR ALLAH


KUDURAR ALLAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 200274



KUDURAR ALLAH

Reading Time: 16 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Fatima Adam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.02 mb

File Type: txt

Views: 1723+

Download: 4994+

Last download: 1 day ago

Description/Story: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GsLlgKf7MsD3M4Hoo7U65P


*KUDURAR ALLAH*


*NA*

*FATIMA ADAM*


********

```Godiya ga Allah da ya bani ikon Fara rubuta wannan littafin wanda ya kasance littafina na farko Alhmdllh Masha Allah
Godiya ga reki auntyna hassana iyayi (maman nuur) da Kika bani kwarin gwiwa akan rubutuna Allah ya bar zummunci amin.

______________


```Page 1 ```



Bauchi unguwar dutsen tenshi.

Unguwace ta masu k'aramin k'arfi wanda suke da wadatar zuci,lungu ne wanda baida wasu wadatattun gidaje gida huɗu ne kawai acikin lungun.
gidana karshe shine gidan daya fi kowanne lalacewa aciki.

Wani kyakykyawan dattijo ne wanda bazai gaza shekaru arba in da takwas zuwa hamsin ba yake k'ok'arin shiga gidan da yake da 'yar langa langar kofar gidan,ga dukkanin alamu bai da cikakkar lafiya, kafarsa yake takawa ! ahankali har yashige cikin dan matsakaicin tsakar gidan Wanda yake share Kal tamkar ba kasance na 'kasa ba, sai zabga kamshin kasa yake.

Sallama yayi cikin wata kimtsatstsiyar murya da sauri ya karasa cikin wani karamin ɗaki dan jiyo sheshshekar kukan da yayi kutsa Kansa yayi cikin ɗakin gami da ambatan sunanta " Fatima Bintu subhanallahi !"da sauri ya ajiye ledar dake hannunsa cikin tsananin damuwa yasa hannu ya dago kanta.

Kyakykyawar yarinyace me cike da wata irin baiwa da ilhama Wanda Rabbi ya bata, fuskarta me cike da kwarjini ta dago tare da zubawa mahaifin nata idanunta masu tsananin sheki.

Cikin sautin muryarta me sanyi da dadin amo tace" Fafi fafi Ina katafi kabarni ? Inajin tsoro fafi kadena fita Ina matukar jin tsoran rasaka kabarni in fita Mana ni naje nasamo abin da zamu ci dan Allah fafi na rokeka karkasake fita zanyi duk abunda ya dace kaji fafina!". ta karasa maganar Tana mai hade hannuwanta biyu.

Wani zazzafan numfashi ya fesar sannan cikin lallama yace.

" Haba Bintu dani da ke wayafi cancanta da ya fita?ko kin manta keɗin macece me rauni ? Bintu kisani cewa babu wani abun tsoro sai Allah karki da aranki wani zai cutar dake face abinda Allah ya lamunce ya Zama kaddararki ke yarinya ce mafisoyuwa agareni lallaba rayuwarki nake Bintu kullum addu'ata Allah ya kauda idon Makiyaa akanki yakareminke tare da mahaifiyarki aduk inda take. "

Yana kaiwa Nan yayi saurin goge kwallar da ya cika idanunsa Mik'a Mata ledar hannunsa yayi tare da cewa "maza tashi ki jika Mana garin rogone nasan kina jin yunwa" sosai yana faɗa da murmushi afuskarsa dan samar Mata da nutsuwa, aiko itama murmushi ta saki Wanda hakan yakara fito da zahirin kyanta ga hakoranta da yar siririyar wushirya da Kuma lobawar kumatunta " Ma sha Allah !".haka papinta yace bayan ganin mik'ewarta tana murmushi.



*********

Abuja

Tamfatsetsen gida ne irin gidajen nan nakasashen waje Wanda aka ɗauko tsarinsa tundaga US azo aka ginashi idan ka shiga cikin ainahin cikin gidan anan aljannar duniyar take.

Birgima take tun karfinta tana Shure- shure tare da wani irin kuka me haɗe da ihu mutane, kusan goma ne akanta ana bata baki gami da rarrashi amma tamkar turata suke sai faɗin

"Wooo jixos ka taimakeni ka dawomin da yarona ina son nagan shi cikin Addinina fatash ka dawo hankalinka, katemaki mamanka kaji kaina ko sau ɗaya ne a rayuwa ban turaka karatu dan kasauya ba na turaka ne dan kaji k'aina kadubeni da kulawa amma Kuma gashinka dawo min da abinda zai iyasawa zuciyata ta buga bazan iya laukar wannan abun ba." sai ta kuma kecewa da wani irin gigitaccen kuka.

Dattijo ne ɗan kimanin shekara hamsin da ɗoriya yake saukowa daga upstairs yana karasowa yayiwa mutanen falon alama da su fice, sum sum ɗaya bayan daya suka fita.

Zama yayi cikin k'awatattun kujerun da suka yiwa falon k'awanya
Wani zazzafan kallo ya Willa Mata Wanda hakan yasa bashiri ta Mi'ke zaune tare da gyara zamanta dukda cewa Bata daina sheshshe'kar kukan ba.

Zuba Mata Ido yayi na Yan wasu dak'ika kana ya
numfasa tare da huro iska daga bakinsa ya ce.

"Abigel kin kyauta kenan abinda Kika aikata kin tara mun jama a kina kokarin tona min asiri ko kina tunanin abunda ki kai zai canja shi daga Kan wannan ra'ayin nasa Kin manta waye shine ? Kin manta halaiyarsa ne? sirgiza Kansas yayi cikin takaici yace abigel Baki da tunani tunda harkika manta halaiyar wannan baudaddan Dan naki,se Kuma ya saki wani ɗan muafikin murmushi kana ya cigaba da cewa dama duk Wanda yase rariya yasan zata zubda ruwa muskutawa yadanyi Yana me hada hannayensa guri guda kana ya dubeta har yanzu hawayene suke satata daga idanunta,
Shin kin manta baya ne ?
Ko kin manta wahalar daya sha ahannun jams ? Kin manta ruɗanin da yasa kaki ? kin manta abinda yake Miki idan weekend yazagayo? Abigel be kamata ki manta duk wannan ba ballantana Kuma me Kan Kat yadda fatash be daukeki matsayin uwa ba".

Azabure ta kalleshi idanunta cike taf da kwalla tace " Na rok'eka kadaina faɗan wannan kalmar tacewa fatash bai kallona amatsayin uwa ". kallonta yayi ya ce.

" Ni dai yanzu shawara da zan baki ki sani duk abinda zakiyi ba fasawa zaiyi ba gara ki canja salo ko awannnan Karan Kya dace".

Yana gama faɗin haka ya Mik'e tare da haye wa sama.

Itama mik'ewa tayi cikin wani irin mutuwar jiki da wani irin fargaba dake yawan sawa zuciyarta na bugawa
har haɗa Hanya take saboda yadda tsananin duhu ya mamaye idanunta.

Adai dai wannan lokacin Kuma awannnan rana ta juma' a, ranar da kowane musulmin k'warai keyin haramar tafiya masallaci.

Sai dai Kuma adaidai wannan lokacin ne wasu baragurbin dake cikin musulmai suka hada Kai da Makiya addinin Allah, suna Saɓa masa.
Wata iriyar murya me tsananin Kara.....


*KUDURAR ALLAH*


*NA*


*Fatima y Adam*

Free book.


*page 2*


__________________________


Bismillahirrahmanirra




Dajin me tsananin, duhuwa da dogayen bishiyu, babu abinda zakaji se amon muryar !" nan,wanda hakan yasa dajin yake wani irin gigiza bishiyu na, kadawa, tamkar iskar damuna.
Sautin muryar nan ba daga ko Ina yake fita ba," illah cikin gidan Dake cikin tsakiyar dajin nan, shi daya kwallin kwal.

Abun mamaki, acikin gidan babu wasu kayan kawa, banda wasu muggan ababan tsoro.
duk 'ban garenda da ka kalla to akwai' abin da zakayi tozali dashi wanda ze kusa sa numfashin ka wuyar fita.

Mutanene wanda akalla zasukai kimanin su ashirin,kowan' nen su
Yana sanye da jan zani da kuma 'kwarya, ahannunsu, suna durkushe akan gwiwowinsu, babu me 'kwa'kw'kwaran motsi acikinsu dan sunyi amanna da abinda suke aikatawa shine ze basu nasara arayuwarsu.

Shugaba azikwi Wanda shine yakasance shugaba acikin, kungiyar,
Zaune yake Kan kujerarsa ta mulki, fuskar nan tasa, babu kyan gani
gaba daya ya juye ya koma wata irin mummunar halitta, shi ba mutum ba Kuma ba dodo ba , ita kanta kujerar mulkin da kafar mutum akayita haka ma hannayen ta na mutum ne.

Kai jama a idan daranka kasha kallo.

Cikin wannan katuwar muryar ya bude baki !" se ga wani irin hayaki na ciccidowa tamkar
hayakin turare.

A haka ya Fara magana !" cikin daga sauti Wanda hakan yake nuni da Yana cikin tsananin fushi.

'Yace " haka dama mukayi daku ? bance ku kashe shiba? lallai kuwa to kusani, tun wuri d'an zaki ya riga ya girma , kunyi sake kunyi sakeeee" ya 'karasa fada cikin wani irin mummunan sauti, wanda hakan yasa gidan, da dajin suka Fara wata kakkarfar girgiza.

Mutumin Dake fuskantar shugaba azikwi wanda yayi kokarin Fara goge!" zufar da take ta faman keto mashi tun Fara jawabin shugaba.

Cikin tsananin rudewa da tashin hankali mabayyani
Yace !" shugaba atemaka asamo mana mafita ayi mana afuwa akasi, akasamu' amma' tabbas, mun kasheshi.

Wata irin tsawa shugaba 'azikwi yayi masa yace!" da da' akwai mafitar da' hankalina ze tashi ne? nayi iya'yina amma' nakasa ganin komai se tsananin duhu dodo jack, ma yayi fushi dan be taba,
haduwa, da irin wannan matsalar ba.

Yaci gaba da cewa!" tabbas nashiga rudani. wannan ba, karamar matsala bace dole se munyi wani abu akan wannan gagarumar matsalar."


Gurin yayi tsit bakajin motsin komai se na ka'dawar da bishiyun dajin,sukeyi saboda razanin da muryar shugaba azikwi ya jefasu
aciki.

na kusa da wanda yay magana! afarko shine cikin tsananin biyayya yace ! "shugaba ayi Mana afuwa agafarcemu asamo mana fafita kasan komenene zamu aikatashi indai akan samun masarar mune.

Yana rufe bakinsa wata kakkarfar guguwa
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download KUDURAR ALLAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album